Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saidai ba karamin daɗin kunun takeji ba, saida ta gama sha yafara bata jan gashin hantar da romo yana mata tausa da ɗayan hannun shi cikin kwarewa itako taki ta haɗa ido da shi, dan nauyin shi takeji sosai

."Hayati."
ƙin kallan shi tayi, saita fara murza zoben hannun ta da tafara.
sake kiranta yayi yace. "Nurol hayat."
"Naam, Ya Malik ina kwana."
Kin amsata yayi yace.
"Rike gaisuwar ki banso."
Da sauri ta kalle shi wani irin kwarjinin sane suka lullube ta, sake sadda kanta tayi tace.
"Ya Malik kayi hakuri ka amsa kagafa ban lafiya."
Kwantar da ita yayi saman kirjin shi yace.
"Sannu gimbiya ta, muje insake haɗa maki ruman ɗumi zakiji sauki kinji yar aljanna."
"Uhmm nidai da zafi ruwan, ina tsoro ƙonani yakeyi."

a shagwaɓe tayi maganar,
Shima kwaikwayar ta yafara yace.
"Uhmm inasan gimbiya ta, ta worke da wuri ina bukatar ta akoda yaushe, ki daure kinji Jaruma ta?"
Sake make kafada tayi tace.
"Allah da zafi, Ya Malik bacci nikeji."
Bai kuma yimata musu ba ya sake kwantar da ita dan yasan zata bukaci yin bacci, saidai zama yayi yana danna mata jikin nata, a hankali itako daɗin yanda yake danna mata takeji dan duk sassan jikin nata ciwo suke mata sosai, baccin ne ya sake ɗauketa, a hankali ya tashi ya shiga bathroom yayo wanka ya fito, canza kaya yayi ya saka wani sky blue din yadi mai kyau da sheki yana gama shafa mai, ya fesa turare mai daɗin shaka, komowa yayi wajen break fast din ya zuba madara yafara sha, sannan ya fara cin farfesun yan ciki saida ya lumshe ido a bayyane yace.
"Wannan dagaji girkine na musamman Ummu Malik tayi shi da kanta, Allah yabar minke Ummu na."

Haka ya gama kalacin, sannan ya tattare kayan, komowa yayi gefen bed yaci gaba da kallan kyakyawar fuskar Bahijja dake ta baccin ta cikin salama, murmushi mai sauti yayi musamman da daren jiya ya dawo cikin zuciyar shi, cewa yayi.
"Yan matan Ya Malik badai raki ba, inada aiki kuwa, Allah sarki kanwar Malik yar aljanna."
Haka yaita kallan ta cikin shauƙi

Itako Jakadiya Hajara tana isa, sai murna takeyi ta wuce cikin bedroom ɗin Sarauniya Zulaiƙa isketa tayi tagama shiri tsaf tana sakala yan hannun a zurfa a hannun ta, yanda taga fuskar Hajara da sauri ta mike tana tarota tace.
"Andace kuwa?"
Dukawa tayi tana cewa. "Alhmdullhi ranki shidade andace andace kuwa."
Ansar ledar tayi, cikin tsananin farin ciki ta zauna a nutse ta buɗe ledar fiddo da kyallen tayi taga jini ya bata shi wani murmushi mai haɗe da sautin farin ciki ya subuce mata, saukowa saman gadon tayi, tayi sujudar shukur tana kara godema Allah ta jima tana addu'a da dacewa da zuriya ɗayyiba, dagowa tayi tana kallan Jakadiya Hajara tace.

"Ummin su, bansan mi zance ba Allah yaima Bahijja albarka tacika 'ya ƙangin bauta da wahala baisa ta zubda mutuncin taba, lallai Bahijja ke kikafi kowace ya mace cancanta ta zamo mata kuma uwar 'yayan Sarki MalikusSaif ɗan Saifulislam jika ga Sulaiman ɗan Sufyan, ke kikafi kowace zarra Allah ya biyaki da aljanna."
"Ameen y rabbi cewar Jakadiya Hajara, snnan tace
"Saidai dagani tana cikin yanayi tana bukatar kulawa."
Fuskar Sarauniya Zulaiƙa fal da annuri tace.
"Kije ki kaima iyayen Abdulmalik suga shaidi sannan a shaida duk wanda ke cikin Masarautar Daborah kaf dangi asa Sarkin shela ya sanar kowa ya shaida a haɗa mani walima tagani ta fada aci asha ba bawa ba mai mikami, kowa daya ne, domin baiwa ta hasku a idon duniya baiwa ta zama abin alfahari a cikin zuriya ta, baiwa ta zama jigo a cikin rayuwar ɗana baiwa ta shaidawa duniya cewa *BAYIMA 'YA'YA'NE* tabbas ni Zulaiƙa na shaida hakan, Hajara kubawa Aisha kayan gyaran budurwar da takai darajar ta ɗakin mijin ta tafara yimata gyara na musamman insha Allah cikin kwana ukku zata worke."
wani sanyin daɗi ne ya dabaibaye tace.
"Tabbas Bahijja kinyi goshi kinzama yar gata."

"Kwarai kuwa Hajara anjima kizo a haɗa mata kyauta ta alfarma da ba'ataba hadama kowace "ya mace ba a fad
ɗin Masarautar Daborah ba, yana daga cikin karamar kyautar gimbiya Bahijja ni Zulaiƙa na mallakama iyayen Bahijja tsohon gidan ɗana,wanda sai Yariman Daborah ne kaɗai yake da ikon shiga cikin sa, ainahin gidan kakana Sarki Khamil, saidai bansan ko Abdulmajid zai iya barin turakar bayi?"
Jinjina kai Jakadiya Hajara tayi tana mamakin irin farin cikin da Sarauniya Zulaiƙa keyi dan bada tsohon sashen Yarima ba karamin abu bane, saboda ba mai zama cikin shi sai Yarima mai jiran gado, lallai Bahijjja, kin cika 'yan tattar 'ya'.

Sauke ajiyar zuciya tayi tace.
"Mi zai hana zai komo insha Allah."
"Maza Hajara kifara kaima Saifulislam da Baffana shaidin mutuncin surikar tasu."
Maidashi tayi cikin leda zata tafi kenan saiga Jakadiya Aisha ta shigo, itama nuna mata akayi harda kwallan farin ciki tayi tana godema Allah daya bawa Bahijja kariya akan farmakin da ta haɗu dashi lokacin da tana baiwa, har Allah yasa takawo kimar ta ɗakin mijin ta."

Tafiya Jakadiya Hajara tayi, Sarauniya Zulaiƙa ce ta haɗama Aisha kayan gyaran jiki tace.
"Gashi Umman Bahijja, kije keda cikin kannen Binta, ku kula da ƴarku, tanajin jiki."
Amsa tayi tana farin ciki ta juya ta tafi sai murna takeyi kai tsaye turakar bayi ta nufa dan tafiya da Mairo.
tana isa cikin turakar bayi ta iske Binta da Mairo sai Ladidi, sunata aikin abinci, sallamar Jakadiya suka amsa, kujera Mairo ta dauko ta aje mata, zama tayi cikin kulawa tace. "Sannun ku da aiki."
"Yawwa Umman Bahijja, ya hakuri, da mutane."
"Alhmdullh, yauwa Mairo ki shirya zamuje wajen Bahijja batajin dadi."
Kallan juna sukayi tsakanin Mairo da Ladidi, fuskar su ɗauke da annuri tace.
"Badamuwa, bari intai mata da abincin nan."
"Aaa ai ankai mata abinci fa tun safe."
Murmushi Mairo tayi tace. "Eh wannan haɗine na musamman ne zuriyar Jafar akema irin shi, shiyasa farfesun naman kaine Umman Bahijja."
Murmushi Jakadiya Aisha tayi tace. "Ku ida sai mutafi."

Haka suka ida cikin wani kwanon silver ne suka juye naman kan daketa kamshi yaji haɗi, ɗauka Mairo tayi suka tafi sashen gimbiya Bahijja."
Itako Hajara side ɗin Kangiwa ta wuce sai annuri takeyi tana murna, tana isa da sallama a bakin ta, suka amsa mata, zama tayi bisa kafat, Saifulislam ne yace
"Ummin Malik ina fatan lfy, dagani akwai abinda ke tafe dake?"
Faɗaɗa murmushin ta tayi tace.
"Allah yataimaki Kangiwa shaidin Bahijja ne aka kawo maku."
Wani sanyayyen murmushi ne ya sauke, danko Sarki Abu-Jalal matsowa yayi yace.
"Alhmdullhi Allah na gode maka yau Abdulmalik ya zama cikakken mutun magidanci Allah ya albakace su da zuriya ɗayyiba."
"Ameen ya rabbi."
Ɗago kyalen tayi ta gwada masu, shidai Saifulislam murmushi kawai yayi baice komai ba, dan kara da yake nunawa akan ɗan shi Malik.

Sallamar Matawalle da Sarki Muhammad ne suka tsinke Maganar da Sarki Abu-Jalal zaiyi, amsawa sukayi da sauri Matawalle ya karaso cikin falon ya zauna bakin shi yaki rufuwa dan farin ciki, murya na rawa dan ɗauki da zumudin zuwan wannan ranar yace.
"Masha Allah komai yai kyau Allah Sarki yar albarka, Bahijja Allah yasa albarka."
Ameen cewar Sarki Muhammad, shiko sai tunanin sadda yaso ketawa Bahijja haddi yakeyi da yanzun ta zama kaskantattar mutun a cikin Masarautar Daborah ba karamin godema Allah yayi ba da bai bashi iko ba da galaba akan Bahijja, da yanzun yaji kunya kuma da yayi danasani marar anfani.

Murmushi mai faɗi yayi yace. "Gaskia Bahijja ke jajirtattace 'yata Allah yasanya albarka, burina ya cika dan haka gobe in Allah yaso zamu koma gida."
Sai lokacin Saifulislam yace.
"Dan sonkai, daman 'yar ka ce ta tsaida ka kenan."
Murmushin gefen kunci yayi yace.
"Ba sonkai bane, kasan tsakanin ɗa da mahaifi."
"Gaskia kam Allah yasa albarka."
Ameen ya rabbi cewar Jakadiya Hajara.

Tashi Saifulislam yayi yakira Jakadiyar shi, bin bayan shi tayi har cikin wani ɗaki, dagani bai anfani dashi kayane masu matukar anfani da mahimmancin gaske, wani katan tasar kumbone yasa ta ɗauko makare yake da kaya, fitowa sukayi yasa ta'aje a gaban Sarki Abu-Jalal tsakiyar falo zama sukayi ya kalli Baffan nasu yace.

"Kawu wannan kyautar shaidi ce ga 'yata Bahijja halak malak, wannan kayan kayane na gadon gidan mu, na fatake na damƙasu ga matar ɗana Abdulmalik."
Wani irin murmushin farin cikine ya mamaye zuciyar Sarki Abu-Jalal da sauran jama'ar cikin falon hannu yasa ya dauko wata tamfatsetsiyar sarka ta ɗanyan gold tasha ado da wani irin zane mai masifar kyau, kallan Matawalle yayi yace.
"Gimbiya Bahijja kinyi goshi Allah yajikan ka mai girma Sulaiman ɗan Sufyan, wannan shine gadon gidan mu mai cike da tsantsar addini, Hajara wannan kayan da kike gani idan kin kaima Bahijja kice takara kula dasu sosai kada tayi sakaci akan su."
''Insha Allah gimbiya Bahijja zataji."

Jingina kai yayi yace.
"Bahijja na godiya aminina masoyi na, Saifulislam Sulaiman Sufyan, Allah yakarama rayuwa albarka Kadimulislam."
Rausayar dakai Kangiwa yayi, tareda murmushi a saman fuskar shi.

Shima Sarki Abu-Jalal, wata katuwar leda ce ya fiddo ya mikama Jakadiya Hajara yace.
"Wannan na kakanni ne akaima 'yata daga Masarautar Runo Allah yaima rayuwar Bahijja albarka."

Sunkuyowa Jakadiya tayi ta amsa, wasu a warworo ne masu tsada da kyau na Jawhar sai wasu kaya na alfarma da suka ƙayatu da duwatsun lu'u lu'u da takalmansu sai kuma zoben azurfa."
Shima Matawalle, sarkar azurfa da yan hannun su sai zobe ya bada, amsa Jakadiya tayi sai washe baki takeyi.
Daga karshe Sarki Muhammad ne ya dauko wasu dakakkun kaya na kirar Masarautar Raifasu da sarkar murjani yace.
"Wannan kyautace daga iyayen gidan gimbiya Bahijja, muna mata fatan alkhairi."
Bakin Jakadiya yaki rufuwa dan murna tace.

"Angaishe da iyayen Bahijja kyauta tayi kyauta gimbiya Bahijja na godiya Allah yasaka maku da alkhairi."
"Ameen suka amsa."

Fita tayi bada jimawa ba, ta kirawo hadimai guda hudu suka ɗauki kayan, suka tafi har sashen waziri Dammur nan suka iske gimbiya Zahra'u da gimbiya Mulaika sai maman Huzaifa gimbiya Salsabila haka aka nuna masu shaidin Bahijja, Mulaika sai murna takeyi itako Zahara'u kamar ta mutu dan baƙin ciki, da kyal gimbiya Salsabila ta yunkura taje ta dauko kudi a dakile ta daura bisa kyautukan Bahijja, taga tashin hankali ganin uwar dukiyar da aka jibgama Bahijja, na gani na faɗa, aranta ko cewa tayi inama Zahara'u ce tasami gata irin na Bahijja, yau ga baiwa ita shugaba a garesu.
Haka suka dinga shiga gidan dangi duk wanda yakama ta akaimawa ankai mashi kuma sun bada tukwici daga nan suka wuce sashen Sarauniya Zulaiƙa, akan hanyar su suka iske Sarkin shela yanata shelar shaidin mutuncin gimbiya Bahijja, bayi sai murna sukeyi, snnan ya sanar da walimar da za'a gudanar bayan sallar la'asar kai kace wani biki za'a sakeyi, itako Zahara'u tanajin shelar ta faɗa bisa gadon ɗakin ta ta rushe da kuka, itako Binta sakon nan zuwa kunnen ta sujudur shukur tayi tana godema Allah, ta ɗago da rinannun idanun ta ta kalli yar uwar ta Saude tace.




_Yar Mutan Kankia ce ❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️



*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 115&116




"Alhmdullh yau fargaba na yakare Saude Bahijja ta wayanye lafiya yanzun tazama cikakkar 'ya a idon mutane masu kima da daraja, naji tsoro da fargaba musamman inna tuna da 'yata ba gareni ta girmaba, tun tana kankanuwar ta ta rabu dani taje aikin bauta, godiya ta tabbata ga Allah, Allah ya azurtaki da zuriya ɗayyiba Bahijja."

"Ameen ya rabbil izzati, wannan abin alfahari ne ta wuce wannan gorin da takaici dan Masarautar nan tanaba lamarin mahimmanci Allah yasa albarka."

Shiko Abdulmajid murmushin jin dadi yayi, ya shiga dakin shi yana kara godema Allah.

A wajen Sarauniya Zulaiƙa kuwa kayayyaki Jakadiya Hajara ta dinga nuna mata itako baki har kunne sai murna takeyi tana ajewa, har akazo wajen na Saifulislam wanda yafi kowane kyauta sata jin dadin ganin irin daraja da kimar kyautar musamman a wajen su, jinjina kai tayi ganin kyautar Baffan ta data Matawalle, murmushi tayi ganin kyautar Sarkin Raifasu, haka aka gama nuna mata kyautuka dan tayi mamaki har kyautar tayi yawa, itama batai kasa a guiwa ba, haka ta shiga cikin dakin ta, ta dauko wani kwanon tasa mai girma ta dawo falo ta zauna gefen kawarta Hajia Kubra da kanwar ta Rukayya fiddo da wata sarka tayi ta a salin narkakken gold din Barri sai yan kunnen ta da yan hannu da zobe ta mikama Jakadiya Hajara tace.

"Kinga wadan nan sarkar basai na yimaki bayani akan taba, saidai inkara kicema 'yata ba mai saka wannan sarkar sai Sarauniyar Daborah, zanbata itane dan a wajena itace magajiya ta mai gadona, duk da take gimbiya amman ni Zulaiƙa na sadaukar mata da wannan sarkar ta kakata Sarauniya Yahanasu abin kauna ta, ta kula da ita da kyau, kayan Barri ba kananan abu bane agremu tunda ga kan Takobin Barri har zuwa sarkar ta, da ace Yarima Malik macene da da wannan sarkar za'a naɗa shi Sarauta, amman dayake namiji shiyasa aka rataya mashi Takobin Barri, dan haka ki kara nuna mata kima da daraja irin ta wannan sarkar itace abin tunkaho ga gadon gidan mu gadon gidan Sarki Abduljabbar."

Cikeda gamsuwa ta jinjina kai tace. "Kwarai kuwa ya shugaba ta Bahijja tayi goshi, tana godiya."

Rausayar dakai tayi ta kuma dauko wasu irin alqabba guda ukku masu masifar kyau tace.
"Waɗan nan alqabba a cikin alqabbobi masu daraja da kima a wajena, sunfi kowane aminci da nagarta ki kaima 'yata kyauta ce daga tsantsar zuriyar Saifulislam."

Nan ma godiya Jakadiya ta kuma yi sannan Sarauniya Zulaiƙa tace.
"Kuje kukaima ƴar tawa sannan aci gaba dabata kulawa sosai."

"Angama ranki shidade."
Hajia Kubra ce tabada foam dari, tace gatata kyautar.

Namsa sake godiya Jakadiya Hajara tayi nan tasa hadimai suka jidar mata kayan suka nufi sashen gimbiya Bahijja..


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️


Jakadiya Aisha ce da Mairo suka gama gyara Bahijja sannan suka hada mata kayan gyaran da Sarauniya Zulaiƙa ta basu, suka sa ta zauna cikin ruwan sosai takejin dadin ruwan inda tagama gasa jikin ta sai ta ɗaura zani ta fito tace tagama, sai kuma su sake sauya mata wani, ita kanta taji sauyi sosai na kamar dazun ba kafin suzo, tunda yanzun tana iya ƴar tafiya ba laifi saidai bata yin sauri sosai, kuma zuwa yanzun zazzabin dayai mata ringis ya dan saketa, tanajin jikin nata yai sauki, tana gama shiga ruwan zafin aka hada mata ruwan wanka na turaruka iri iri tayi wanka dasu sannan aka bata wani jiko tasha duk sa ba dadi, saida aka takurata ta shanye shi tas, alwalla ta dauro jin anfara kiran sallar la'asar a masallaci Daborah.

Tana fitowa ta dauko wani mint green na material ta saka doguwar riga amman tai mata das a jikin ta shafa mai tayi ta saka lipstick mai sheki da santsi a leben ta, saka sarkar azurfa tayi marar nauyi sannan ta tada sallah tana gamawa ta fito falo Mairo ta gama kimtsa mata dakin, itako Jakadiya Aisha zuba mata naman kan da Binta ta hada mata tayi tafara ci tana santi, tana cikin ci, Ya Malik dinta ya fado mata arai dan tunda su inna Mairo suka shigo yabar gidan har yanzun bai kara shigowa ba, ko a sashen shi bataji alamun yana ciki ba, a ranta ko tana mamakin inda ya tafi haka taci gaba dacin abincin ta, sallamar Jakadiya Hajara da hadimai dauke da kaya sukaji da ido suka bita suna amsa sallamar kayan suka aje a cikin tamfatsetsen falon Bahijja, sannan suka juya suka tafi abinsu, Jakadiya Hajara ce tace.

"Lantana ki wuce sashen Yarima Huzaifa, kice ma Sarki MalikusSaif, ina sashen shi zanbashi sako kinji,kiyi sauri."
"Toh ranki shidade."

Haka suka fita har sashen Huzaifa, dogarawa ne tsaye bakin shiga cikin side din dakatar da ita wani dogari yayi yace.

"Ke baiwa ina zuwa bakisan Sarkin Daborah yana ciki ba."

Sunkuyar da kanta tayi tace. "Eh ranka shidade nasani Jakadiya ce kesan magana dashi tana sashen gimbiya Bahijja."

Mai kula da zirgazirgar Sarki MalikusSaif ne ya shiga cikin falon dasu Huzaifa ke ciki ya iske shi da aminan nashi dukawa yayi kanshi kasa cikin girmamawa yace.

"Angaishe da uban masarayu Sarki mai adalci, sako daga Jakadiya tana sashen gimbiya Bahijja tace zata baka sako."

Rausayar dakan shi yayi, yana kallan dogarin nashi, ganin haka yasa shi yace.

"Jakadiya nagodiya Allah yakara maka yawan nasara."

Fita yayi inda yabar lantana nan ya isketa kallan ta yayu yace.
"Kice yana zuwa."

Shiko Sarki MalikusSaif cewa yayi.
"Kasan wani abu, Allah Yazid kadaina daka ta, Huzaifa zai kaika yabaro ka."

"Allah yakara girma ai nadawo rakiyar Huzaifa nima gaskia."

Murmushi yayi yace.
"Ka kyauta dan duk randa Huzaifa yai aure zaiga abinda baiso saina hana shi motsin kwarai."

Dariya Huzaifa yayi yace.
"Wato yaudai kun hade mani kai daga fadar gaskia yanzun kawu Dawud kaji iyakar gaskia ta nafada fa amman abin yazama ciwon kai."

"Ai kaine baka daga kafa, ka fiya bin kokonto ne da yawa."

"Lah kaima harda kai kana bayan su kenan."
Dariya kawai sukayi shiko Sarki MalikusSaif yanasan ya tashi ya tafi kiran Jakadiya yana shakkar iskancin su Huzaifa, dan sun maida shi tamkar kakan su, satar kallan su yayi yai gyaran murya yayi, zaiyi magana kenan, Huzaifa yace.

"Angaishe da Sarkin Daborah angon gimbiya Bahijja Allah yakara lfy, karka manta da kiran Jakadiya nasan dai tukwicin gimbiyar Daborah ne zaka karba."



tsuke fuska MalikusSaif yayi ya harari Huzaifa ta gefen ido, bai kuma magana ba, Dawud ne yace

"Allah ya shirye ka, Huzaifa."

Dariyar shakiyanci yayi yace. "Ameen ya rabbi."
Shiko MalikusSaif tashi yayi ya fita, abakin kofar ya tarar da dogarawan shi yai tunanin kowa ya kama gaban shi, da yasan sunanan da baijima a ciki ba, baki dayan su, sukai mashi rumfa suka take mashi baya, amintaccen dogarin sane yafara cewa. "Takawarka lafiya, Sarki mai adalci Allah yakare gaban ka da bayan ka, Allah yakara girma da daukaka, daidai nan kuwa sun iso bakin side din shi, tsaywa sukayi a hankali ya juyo yace.
"Kutafi kowa yai hidimar gaban shi."
Godiya sukayi mashi suka tafi, yana shiga cikin sashen ya nufi bangaren Bahijja ta wani corridor yabi ya shiga cikin kayataccen falon ta, da sallama a bakin shi ya shiga, cikin sakin fuska suka amsa mashi, samun wata kayatacciyar kujera yayi ya zauna wadda ke facing din shi, a mutunce ya gaishe dasu Jakadiya da Mairo, amsawa sukayi cikin jin dadi.

ta gefen ido yake satar kallan Bahijja dan jimawar da yayi bai gantaba ji yake kamar yai watanni bai gantaba, itama din satar kallan nashi takeyi cikin rashin sa'a idon su ya sarke wani narkakken murmushi ya sakar mata, tai saurin sauke nata idon itama murmushin yayi, ya shagala da kalan gimbiyar tashi, maganar Jakadiya Hajara ce ta dawo dashi duniyar soyayya da begen matar tashi, maida hankalin shi yayi kanta yace.

"Naam Anni."
Gyara zaman ta tayi saman kafat ta janyo kayan gaban ta ta dinga gwadawa MalikusSaif, shiko ga nauyin su yanaji amman ya dake sai murmushi yakeyi, saida tagama kaf sannan tabar kyautar Sarki Abu-Jalal dana Saifulislam saita Sarauniya Zulaiƙa daban ta fiddo su ta riko hannun Bahijja tace.

"Yata kinga wannan kyautar daga mai girma Kangiwa take ki kula da kyau tanata matukar anfani a gareki dama ziriyar da Allah zai albarkace ki da ita, kikara kulawa itace gadon gidan su."

Rausayar dakai tayi a kunyace, tace. "Nagode Allah yasaka da alkhairy."

Ameen suka amsa, shiko MalikusSaif lumshe idon shi yayi yanajin amon muryar ta kamar me dadin ta ya dira cikin kunnuwan shi da zuciyar shi baki ɗaya, jin maganar Jakadiya tasa shi bude idon nashi tace.

"Wannan kuma kyau tace da Masarautar Runo daga Sarkin musulmai Sarki Abu-Jalal shida zuriyar shi, ki rike wannan kyautar da girma 'yata."

"Tom Ummi nagode."
Fiddo sarkar da Sarauniya Zulaiƙa ta bada abata tayi tace.

"Wannan kuma Ummun kuce ta baki sarkar Barri kenan, tanada mahimmanci da girma, Sarauniya kawai ya kamata ta malleketa idan za'ayi nadin Sarauta, amman yanzun kin jama jigo ga ahalin Daborah baki ɗaya kinfi kowa cancantar ya saka wannan sarkar itama ki kula da ita, Allah yaimaki albarka."

A kunyace ta sadda kanta tace. "Ameen Ummi nagode Allah yakara girma."

"Ameen ya rabbi."

Yawwa kinga kuwa na manta wannan alqabbar kyauta ce ga zuriyar maigirma Kangiwa."

Kife kanta tayi jikin inna Mairo cikin sanyin murya tace. "Allah yasaka da alkhairy."

Cikin jin dadi sukace amin, haka Jakadiya tagama hada kayan ta aje gaban Sarki MalikusSaif tace.
"Ranka shidade ga kayan shaidin gimbiya Bahijja nan."

Cikin nutsuwa da nuna jin dadi yace.
"Allah yabiya yasaka da alkhairy, Anni Allah ya huta gajiya, karkatawa yayi ya fiddo kudi cikin aljihu ɗauri ukku ya mikama Hajara yace.

"Ga tukuici nan Anni, Allah yakara lafiya da nisan kwana."

Murmushi tayi mai yalwa a saman fuskar ta tace.
"Da kabar wannan tukwicin mudai fatan mu Allah yabaku zaman lafiya da zuriya dayyiba."

Sake mika mata yayi ba tareda yace komai ba, saidai fuskar shi ba yabo ba fallasa, amsa tayi tayi godiya, baki ɗayan su suka mike, zasu tafi Bahijja tace.

"Inna ina zakuje tun yanzun?"

"Eh anjima da marece zamu dawo ki zauna ki huta."

Zatayi magana kenan, Jakadiya Aisha taimata alamun tai shiru da kanta, shirun tayi ta koma ta zauna a darare.

Suko tafiyar su sukayi suna farin ciki, ta gefen ido ya kalleta sai kuma ya tashi kayan ya dauka ya shigar mata dasu gudan dakin ta ya aje mata, a zahiri ko cewa yayi saura nawa gimbiya ta, na musamman zan baki tawan yar aljanna.

Fitowa yayi ya nufi hanyar shiga sashen shi cikin zazzakar muryar ta mai saka shi nutsuwa tace.


"Ya Malik tsayawa yayi bai juyoba kuma bai fita ba, murya na rawa tace.

"tafiya zakayi kabarni inajin tsoro."

ta ida maganar cikin sigar shagwaɓa, a hankali ya juyo da lumsassun idon sa mai dauke da feelings ya tako cikin takon kasaita da kamala ya iso gaban ta, dukowa yayi ya rike hannayen ta a hankali ya buso mata isakar bakin shi zuwa bisa idanun ta da kuma kyakyawar fuskar ta, da sauri ta lumshe idanun ta, sannan ta bude su a hankali ta sauke su bisa fuskar shi mai yawan kwarjini, a batazata taji yace.

"Hayatiiih!"
Yanda yaja sunan saida yasa tsikar jikinta mimmikewa taji wani yar yarr, kamar mai tsoron magana ta motsa labbanta masu sheki tace.
"Naam."

"Muje inbaki kayan dadi zaki dainajin tsoron kinji tawan."
A shakkance take kallan shi dan gano manufarsa saidai hakan yaci tura yanda ya nuna mata ba abinda zai mata, hakan yasa ta bishi, shiko rikeda hannun saidai tana dan dingisawa a hankali a hankali a ranshi ko cewa yayi.

"Uhmmm Nurul hayat dina har yanzun baki worke, gaskia a matsenike fa."

A zahiri ko cewa yayi. "Tawan ya jikin naki muje inbu ingani ko?"

Make kafada tayi tace. "Uhmm na kusa worke wa Anni tace, indai zan dinga wonka d ruwan dumi zan warke da wuri."


Ya gane tana tsoro karyai mata wani abu haka yasa bai kuma cewa komai ba, har suka shigo cikin kayataccen falon shi, ta wani corridor sukabi suka shiga cikin wani hadddan daki daya kayatu da kayan more rayuwa saidai komai na dakin white sai labulayen windows da dor din dakin suke sky blue ba kadn dakin ya burge Bahijja dan tasan ba a wannan dakin bane suka kwana ba a daren jiya ba, cikin nutsuwa tace.

"Ya Malik mizakayi da dakuna har biyu.?"
"Saboda ke matata kiji dadin ki duk wanda yaimaki a nan zaki kwana."

Murmushi fal a fuskar ya ida maganar yana murza tafin hannun ta, da haka suka dinga yan wasanni na masoya suna cikin wasan ne yasa lips dinshi a kunnen ta yasa hakori yadan ciza kadan aiko abinka da maijira tafara kuka saita rama, cikin danne dariyar shi yace.

"Haba kanwar Malik, karfa kimanta yayan Bahijja ne afuwan kinji tawan."

Sake make kafada tayi tace. "Uhmm saina rama ko insanarwa Ummu."
Tashi yayi itako binshi tayi sai zagaye gadon suke dauke da pillow a hannun ta saida dukeshi, cikin rashin sa'a ta daga kafarta da karfi da sauri tace. "Waaaashhhh! zafi Ya Malik tana yar fa hannu, da saurin shi yazo ya rungume ta a kirjin shi yafara lallashin ta kamar jaririya itako sai kara narkewa takeyi tana kara shagwaɓa iya son ranta haka yai ta

Please Login or Register in order to submit comment