Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO23*


.. Cakk Abba ya ɗauketa a hannunsa, ya soma takawa zuwa cikin ɗakin Ammi. Be ajjeta ba, se da ya ƙarasa kan gadon ya ajjeta. Juyawa ya yi zuwa side fridge ɗin Ammin dake gefe, ya saka hannu ya buɗe ya ɗauko ruwa me ɗan sanyi sannan ya matsa kusa da Lulun. Ɗan zubawa ya yi a hannunsa kafin ya kai kan fuskarta a hankali ya shafa, ba ta motsa ba, kamar wadda ba a shafawa komai ba. Ƙirjin Ammi ya sake bugawa, se ta ƙarasa hawa kan gadon, ta ɗauki kan Lulu ta ɗora a kan cinyarta, daidai lokacin da Abba ya sake kai ruwan fuskarta a karo na biyu. Ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta soma buɗe jiƙaƙƙun idanunta. A kan Abba idanunta suka fara sauka, Abba ya lumshe idanu yana sauke ajiyar zuciya lokaci ɗaya yana furta

"Alhamdulillah.." Daga haka se kawai ya miƙe ya fice daga ɗakin, dan tun yanzu zuciyarsa na neman karyewa a kan 'ya'yan nasa, ba kuma ya so ya cigaba da zama anan ɗin har hakan ya janyo ya fara tunanin ya aikata ba daidai ba. Tsam Ammi ta rungumeta cikin jikinta cikin matuƙar farin ciki mara misaltuwa. Didi ma kasa sukuni ta yi se da ta ƙarasa ta rungume su. Ammi ta haɗa 'ya'yan nata waje ɗaya ta rungume. Se a lokacin Lulu ta sake tuna abin da ya faru ɗazun, zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske, se ta ɗago da sauri muryarta na sake yin rawa fiye da yadda take, wata ƙwalla kwance a cikin kyakykyawar ƙwayar idanunta. Hannunta na wani irin rawa tace bayan ta tashi daga jikin Ammi

"Ammi mafarki na yi koh? Ammi wani mummunan mafarki na yi koh? Ammi don Allah ki ce min mafarki ne wannan ɗin ba gaske ba. Don Allah Ammi kin ji.." ta ƙarashe tana girgiza kai, gami da fashewa da wani sabon kuka. Janta Ammi ta sake yi cikin jikinta, itama tana jin wata sabuwar ƙwalla na taho mata.

"Ki yi haƙuri Afaaf.. ki dena wannan kukan, babu abin da ze ja miki se ciwon kai.."

"Ammi ba ki ce min ehh ba. Ammi ba ki faɗa min ba gaskiya bane. Wannan wane irin mafarki ne? Wannan wane irin mummunan mafarki ne? Ta yaya ma wannan abin ze yiwu? Ammi sake ni na je wajen Abba ya tabbatar min da wasa yake mana. Ammi wallahi har abada ba zan sake wani laifi a makaranta ba. Ammi na dena wallahi. Na dena bazan sake ba. Na san abin da Abba ke buƙatar ji kenan daga bakina, kuma gashi na faɗa. Don Allah Ammi ki sanar da shi na dena, wallahi na tuba na bi Allah.." yanzun ma ƙarasawa ta yi tana sakin kuka. Gaba ɗaya Didi se ta ji kamar ita ba a faɗa mata an ɗaura mata aure da wani ba, gaba ɗaya se ta ji kamar bata da wata damuwa idan banda ta er uwarta. Yanayin da take ganinta a ciki a yanzun ya danne komai. Wannan kukan da take ta yi ita kanta shi ke ɗaga mata hankali, gashi se magana take kamar wadda bata a hayyacinta.

"Ya isa haka.. Ki yi shiru nace koh?" Ammi ta faɗa tana goge idanunta. Ba dan taso ba haka ta haƙura ta cigaba da zama a jikin Ammin. Tun tana kukan a fili har tazo ta gaji ta koma sheshsheƙa har daga ƙarshe baccin wahala ya kwasheta. Se a lokacin Ammi ta sauke ajiyar zuciya, ta ɗaga kai ta kalli Didi dake zaune kusa da ita. Idanunta duk sun yi face_face da hawaye, gaba ɗaya kamar ba Didin ba, se ta miƙa mata hannu, babu ɓata lokaci ta ƙarasa Ammin ta haɗasu ta rungume. Se a lokacin ta samu damar fashewa da kuka gwanin ban tausayi.

"Kema karya min zuciyar za ki yi Afrah?" Ammi ta faɗa a sanyaye. Girgiza kai Didi ta yi se dai ta kasa tsaida hawayen, da ƙyar ta iya buɗe baki tace

"Ammi Abba...!" Se kuma ta yi shiru, sannan ta ɗora da

"Ammi ban san wanda Abba ya aura min ba.. Abba be faɗa min ba Ammi.." Ɗan runtse idanunta Ammi ta yi, kafin a hankali ta ɗora hannunta a kan Didi tace

"Ina saka ran samun sassauci daga gare ki Didi. Don Allah ko wane ne Abbanku ya aura miki ki yi haƙuri, ba ze taɓa zaɓa muku abin da ze ce cuceku ba. Idan har kika damu, toh shi kenan Afaaf kuma ta samu dama. Kin ga kenan ta duka ɓangarori biyun Abba ze yi nadamar abin da ya yi, bayan kuma hakan ba laifi bane. Idan kuwa kika haƙura, ke zaki ɗora er uwakki a kan hanya, kamar yanda kika saba. Dan haka ki dena kukan nan, kin san dai yanzun nan kanki ze soma ciwo.." Ammi ta ƙarasa maganar cikin rarrashi. Ba ta iya cewa komai ba, illa zuciyarta da ta cigaba da bugawa. Ta yi shiru tana tunanin yadda rayuwarsu ta gaba zata fara. Aure a ƙananun shekaru irin nasu, da kuma mijin da basu sani ba, baya sonsu basa son shi.

"Allah ze kawo mana mafita.." Ammi ta faɗa kamar ta san abin da Didin ke tunani.


... "Ina ɗana yake Yallaɓai? Me ya same shi haka? Ya ka yi aka kawo shi wannan asibitin?" Mom ta yi duka waɗannan tambayoyin a lokaci guda. Ajiyar zuciya Daddy ya sauke kafin yace

"Duka waɗannan tambayoyin a lokaci ɗaya?" Daddy ya faɗa yana kallanta.

"Don Allah so nake na ga ɗana, yana ina?"

"Mu je.." Daddy ya faɗa yana yin gaba. Babu ɓata lokaci Mom ta bi bayansa hankali tashe, burinta kawai ta ga shalelenta ta kuma san abin da ke damunsa.

"My boy.." ta faɗa tana kai hannunta kan fuskar Bad ɗin dake kwance har lokacin kamar matacce. Ganin da ta yi be motsa ba ya sanyata kallan Daddy tace

"Bacci yake yi ne? Wai me ya same shi?"

"Ki kwantar da hankalinki. Ze farka zuwa anjima In Sha Allah."

"Har yanzu ba ka faɗa min abin da ya same shi ba Yallaɓai.." Kafin Daddyn yace komai, likita ya shigo cikin ɗakin. Bayan sun gaisa da Daddy cikin girmamawa sannan ya ƙarasa inda Bad ke kwance, ya duba shi sosai sannan ya kalli Daddy har lau dai cike da girmamawa yace

"Har yanzu be motsa ba?"

"Ehh.." in ji Daddy.

"Ohk a cigaba da addu'a. Kamar dai yadda muka faɗa zuwa anjima In Sha Allah ze farka.."

"Allah ya yadda.."

"Likita me ke damun ɗana?" Mom ta faɗa tana kallan Doctor ɗin. Kallanta Daddy ya yi, kafin ya maida dubansa kan Doctor ɗin yace

"Za ka iya wucewa.."

"Ohk Sir.." Daga haka ya fice daga ɗakin.

"Abin da yafi dacewa ki zauna ki masa addu'a ya samu ya farka, ba tambaye tambaye ba.." Daddy ya faɗa yana kallan Mom.

"Wai abun har ya kai haka?" Mom ta faɗa a sanyaye.

"Kar ki ɗaga hankalinki.." Se ta sauke ajiyar zuciya tunda dai ta ga ba faɗa mata za a yi ba, se ta nemi waje ta zauna kawai tana kallan ɗan nata cike da tausayawa.


... "Sannu da zuwa.." Ummeey ta faɗa tana kallan Abeey.

"Yawwah.." ya yi maganar yana neman waje ya zauna. Murmushi Abeey ya yi kafin yace

"Na san kin ƙagu ne ki ji abin da zan faɗa.." Ɗan yaƙe ta yi tace

"Ƙwarai kuwa Malam.. Ka fita kai ba cikakkiyar lafiya ba.. ga kuma wannan zancen da yafi kama da almara.."

"Kwantar da hankalinki.. Ni kam garau nake jina musamman ma da yau ɗaya daga cikin burina ya cika. Wato na aurar da Affan.." Cike da mamakin dai Ummeey tace

"Wai Malam dama da gasken ne?" Girgiza kai Abeey ya yi kafin yace

"Ban da abinki, wannan ɗin ai ba maganar da za a yi wasa a kanta bace. Da gaske a yau ɗin na aurar da shi. Kin ga kema burinki ya cika, ko dama ba abin da kike so ba kenan?" Ya tambaya yana kallanta.

"Ikon Allah.." Ummeey ta faɗa cike da mamaki. Se kuma ta ɗora da

"Toh Alhamdulillah.. Allah ya sanya alkhairi.. ya basu zaman lafiya.. ya haɗa kansu. Ni kuma ina nan ina jiran zuwan sirikata.." ta ƙarashe tana murmushi. Murmushi Abeey ya yi yace

"Ameen Ameen.."

"Amma Malam.. kana ganin Affan ze iya riƙe mata kuwa? Duk uban hidindimun nan na aure da ake yi.. abubuwan kamar da yawa, kuma na san dai mutane ba zasu ɗauki ɗiyarsu su bamu ba tare da an gabatar da abubuwa na al'ada ba.."

"Haka ne.." Abeey ya faɗa bayan ya sauke ajiyar zuciya. Se kuma ya ɗora da

"Allah ze hore yadda za a yi In Sha Allah.."

"Toh Allah ya yadda.."

"Ameen.." Abeey ya amsa kafin yace

"Har yanzu be shigo ba?"

"Wallahi kuwa.. dama yace ze daɗe.." Ummeey ta bashi amsa.

"Ko yaushe ya dawo, ki faɗa masa ina son ganinsa ko da bana nan.."

"Toh Malam.."




... Kamar a mafarki ta ji tarinsa ƙasa_ƙasa. Da sauri ta miƙe ta ƙarasa inda yake tana faɗin

"Areef.." Cigaba da tarin ya yi se dai har lokacin a hankali.

"Na gode maka Allah.." Mom ta faɗa cikin matuƙar farin ciki tana kai hannunta ta riƙo Bad ɗin. Fara miƙewa ya yi cike da kasala yana cigaba da yamutse fuska. Mom ta taimaka masa ya tashi zaune. Jin kansa yake gaba ɗaya wani gingirin kamar wani sabo aka ɗora masa bayan na shi. Hannu ya kai ya ɗan dafe kansa daidai lokacin da ya ɗan saki ƙaramin tsaki.

"Sannu ka ji yarona..?" Mom ta faɗa tana kallansa. Kamar be ji ta ba, dan kuwa bece komai ba. Se da ya ɗan lumshe idanunsa sannan ya soma ƙoƙarin sauka daga kan gadon.

"Ina zaka je?" Mom ta tambaya.

"Pls Mom.." ya faɗa da dashashshiyar muryarsa.

"Don Allah ka koma ka zauna. Ba ka da lafiya fa.."

"Mom.." ya sake faɗa cikin kaushi. Girgiza kai ta yi tana faɗin

"A'ah Son pls ka koma ka kwanta.. kana buƙatar hutu plssss.." ta faɗa cikin rarrashi har lokacin tana riƙe da hannunsa. Haka kawai tunda ya farka yake jinsa a fusace, gaba ɗaya jikinsa ya masa wani irin nauyi, komai na jikinsa jinsa yake kamar ba na shi ba. Hakan ne ya sanya a yanzu burinsa kawai ya fita yaje ya sha wani abun ko ze samu ya dawo daidai. Dan gaba ɗaya ya kasa gane me ke damunsa. Se a lokacin ma ya lura da inda yake, ya lura da ba a cikin gidansu yake ba. Hakan ne ya sa ya sake kallan Mom ɗin yace

"Ina ne nan?" Ya faɗa yana sake kallan ɗakin sosai. Kafin tace komai ya sake faɗin

"What brought me here? Asibiti?" Ya faɗa a mamakance.. Da sauri Mom ta girgiza kai tace

"I don't even know my Son.. But bari na kira Daddynka shi ya san dalilin kawoka nan ɗin.." Ta yi maganar tana ɗakko wayarta, ta shiga kiran Daddy. Se dai cikin rashin sa'a ake faɗa mata wayar ba zata shiga a lokacin ba.



... Gaba ɗaya se da Daddy ya miƙa musu hannu suka gaisa. Daga Abeey har Abba suna sake mamakin hali irin na Alhaji Matawallen.

"Barkanku da wannan lokaci.." Daddy ya faɗa..

"Barka dai.." Abeey da Abba suka haɗa baki wajen faɗar hakan. Bayan sun sake gaisawa sosai Daddy ya soma faɗin

"Toh wannan dai aure an yi shi ne ba tare da sanin kowanne ɓangare ba. Saboda haka na san iyaye mata kan iya yin taro duk ranar da yaran nan zasu tare. Saboda haka ina ganin mu saka ranar da ya kamata a ɗauki yaran nan a kaisu gidajensu. Ina ganin hakan shi ne mafita.." Jinjina kai dukansu suka yi cikin na'am da zancen Daddyn. Abeey ya ɗan yi gyaran murya sannan yace

"Toh se dai wani hanzari ba gudu ba.. Akwai abubuwa da ake irin na al'ada, wanda idan akace a cikin kwanaki kaɗan za a yi su Yallaɓai kamar ya yi kusa. Dan haka nake neman alfarmar bamu lokaci ko da kaɗan ne a fara kai kayan sannan a bamu matar.." Murmushi Abba ya yi yana kallan Abeey yace

"Ayyah.. Malam.. in dai dan wannan ne babu matsala.. Kowannensu ka iya yi wa matarsa duk abin da ya ga dama bayan zuwanta gidansa. Wannan ɗin tunda ba addini bane ina ganin kawai mu bar shi.."

"A'ah barinsu kam be taso ba. Gwara dai da kace idan sun je can ɗin se a musu.." Abeey ya katse Abba da faɗin hakan. Dukansu se suka yi murmushi daidai lokacin da Daddy yace

"Hakan ma ya yi.. Muma kuma ta ɓangaren mu bama buƙatar komai.. yarinya kawai muke buƙata.."

"A yi min wannan alfarmar Yallaɓai. Ko daga baya ne zan yi wa yarinyar nan kaya a aiko mata dasu.." Abba ya faɗa yana murmushi.

"Shi kenan.. Malam ka amince da hakan?" Daddy ya faɗa yana kallan Abeey

"Shi kenan.. Allah ya sanya alkhairi, ya haɗa kan yaran nan. Ya kuma kaɗe fitina.." Abeey ya amsa da hakan. Gyara zama Daddy ya yi kafin yace

"Toh Alhamdulillah.. Tunda dai an gama da kowacce matsala. Ina ganin kawai nan da sati ɗaya idan Allah ya kai mu kowaccensu ta tare a ɗakinta. Allah ya bada zaman lafiya.."




Toh Alhamdulillah. Bayan hutun en kwanaki da na ɗauka, yau ga ni na dawo. In Sha Allah zamu cigaba da fafatawa babu kama hannun yaro. 😍💃


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO24*



___"Toh madallah, Allah ya kaimu ya kuma sa ayi komai a sa'a, ya kaɗe fitina." Abeey ya faɗa. Abba da Daddy suka amsa da "Ameen."



... "Barka da wannan lokaci Abeey.." Gwani ya faɗa yana neman waje ya zauna. Murmushi Abeey ya yi kana ya amsa da

"Barka dai Affan.. Zauna sosai magana zamu yi.." Abeey ya yi maganar lokaci ɗaya yana kallansa. Gyara zaman ya yi shima yana murmushin. Abeey ya ɗan sauke ajiyar zuciya sannan yace

"Wato Affan kamar yanda na sanar da kai, zan ɗaura maka aure.. toh na cika. Na ɗaura maka aure kuma In Sha Allah ina fatan zaka karɓi matar hannu bibbiyu.." Shiru Gwani ya yi yana ɗan so ya tunano abin da ya sa Abeeyn ya ɗaura auren nasa haka kamar a gaggauce. Se dai kome ya yi hakan ba laifi bane. Dan haka ya yi shiru yana cigaba da saurarar abin da yake faɗa ɗin.

"Babban abin da ya min daɗi shi ne yadda mahaifin yarinyar da kansa ya nemi yana so ka auri ɗiyarsa. Kuma abin da ya sake min daɗi shi ne yanda yarinyar tasa ta kasance ɗalibarka." Tunda Abeeyn ya fara magana be ɗago ba se yanzun. Be san sanda ya furta

"Ɗalibata..?" Cike da tabbatarwa Abeey ya jinjina kai

"Ƙwarai kuwa ɗalibarka.. Er gidan Muhammadu Aji ce fa.." Ɗan shiru Gwani ya yi, se ya ji kamar yau ne ya fara jin sunan. Zuwa can kuma se ya tuna wane ne Muhammad Aji, su waye kuma 'ya'yansa. Kenan Afrah Abban nasu ya nemi ya aura? Har ma an ɗaura auren?

"Kaa ji sunan nata.. ɗan tuna min ya ɗan kwanta min.."

"Afrah...?" Ya faɗa cikin sigar tambaya da sauri yana kallan Abeey. Girgiza kai Abeey ya yi yace

"A'ah.. ina tunanin sunan er uwar tagwaitakarta ne wannan.." Cikin son sake tabbatar da abin da Abeeyn ke nufi. Da kuma son ya ƙaryata abin da yake hasashe yace

"Afaaf..?" Murmushi Abeey ya yi yace

"Ƙwarai kuwa Afaaf.." Runtse idanunsa Gwani ya yi yana jin yanda kansa ya ɗan juya masa. Be san ta yadda Abeey ze yi wani abu yace be masa ba. Amma wannan karon abin ya shammace shi. Afaaf fa? Ta yaya wannan yarinyar dake ganin tafi ƙarfin kowa zata zauna a matsayin matarsa? Bama wannan ba, ta yaya shi kansa ze iya zama da ita a matsayin matarsa? Wane alfahari ze yi idan an kira wannan da matarsa? Mutuniyar da bata ragawa kowa ba? Kallan kowa take a ƙasanta. Kallan kowa take a tafi ƙarfinsa. Yarinyar da tun zuwansa ajin basu taɓa shiri ba daidai da rana ɗaya kuwa? Yau ita ake kira da matarsa?

"Ya Salam.." ya faɗa cikin zuciyarsa yana dafe kansa, zuciyarsa na masa wani irin zafi.

"Affan.." Abeey ya faɗa yana kallansa. Da sauri ya ɗaga kai, yana ɗan wanzar da murmushi a kan fuskarsa yace

"Na'am Abeey.."

"Lafiya dai koh?"

"Ehh.. kaina ke ɗan sara min.." ya faɗa a nutse.

"Dama ba tun yanzu bane?" Abeey ya tambaya cike da kulawa.

"Yanzu ne. Amma babu damuwa Abeey, na ji wadda ka aura min.. Allah ya saka da alkhairi.."

"Ameen Ameen.. Ka daure ka sha magani, sannan ka kama kan naka. Allah ya ba da lafiya.. ya kuma saka albarka a rayuwar aurenku.. zuwa gobe se mu ƙarasa maganar kafin nan kan ya yi sauƙi."

"Ameen.." Gwani ya amsa da hakan yana ficewa daga ɗakin. Gaba ɗaya kansa ya kulle, ya ma rasa tunanin da ze yi. Ji yake kamar wani shirin film ne yake kalla, ko kuma wani abu da yafi kama da almara. Jin kansa na cigaba da sarawa lokaci ɗaya ransa na cigaba da ɓaci idan ya tuna wace ce Afaaf se ya nemi waje kawai ya kwanta, cike da fatan ya manta da komai a yanzun, ko ze samu bacci ya ɗauke shi. Ko kuma ma dai kawai ya ga ya farka daga wani baccin ya ga ashe duk mafarki yake yi. Idan kuwa gaske ne lallai ikon Allah ya wuce gaban wasa. Ko me kuma ya tsara ze faru, toh fa babu makawa se ya faru ɗin. A nutse ya ɗan lumshe kyawawan idanunsa har lokacin hannunsa na riƙe da kansa.


... Cikin matuƙar farin ciki yake driving, murmushi yaƙi barin fuskarsa. Tunda Abba ya kira shi a kan yana son ganinsa ya kasa sukuni, gaba ɗaya hankalinsa ya tafi can wajen Abban. Burinsa kawai ya isa ya ji dalilin kiran Abban. Duk da dai ya san kiran na da nasaba ne da maganar aurensa da Didi. Har ya isa gidan ya kasa dena zumuɗi. Aka yi masa jagora zuwa ɗakin baƙi, ya nemi waje ya zauna yana jiran zuwan Abban. Babu daɗewa kuwa se ga Abba ya shigo ɗakin da sallama. Yana ganinsa ya miƙe cike da girmamawa, se da Abban ya zauna sannan shima ya zauna bayan ya gaishe da shi cikin girmamawa.

"Amm Kaseem na san zaka yi mamakin kiran nan da na maka da gaggawa haka.." Se ya yi murmushi sannan yace

"Babu damuwa Abba.." Gyara zama Abba ya yi kafin ya ɗan sauke ajiyar zuciya ya soma faɗin

"Wato kiranka na yi na sanar da kai wata magana, wadda na san ba lallai ne ta maka daɗi ba. Sannan kuma na nemi afuwarka, na baka haƙuri duka dai a kan wannan maganar. Se dai ka san dama ance kana naka ne Allah na nasa. Duk kuma abin da ze faru dama can rubutacce ne. Wani kuma ba ya taɓa aurar matar da ba tasa ba." Abba ya ɗan dakata anan. Har ga Allah tunda Abba ya soma maganar nan ya ji jikinsa ya yi mugun sanyi, tsoro ya shige shi, fatansa da burinsa Abba ya ida faɗar abin da ya soma faɗa. Kamar ya san abin da Kaseem ɗin ke tunani se ya cigaba da faɗin

"Ka yi haƙuri Kaseem.. Na aurar da Afrah ga wani daban ba kai ba. Na aurar da ita saboda wani dalili me ƙarfi. Na kuma ji daɗi da maganarka da ita ba ta yi nisa ba, ma'ana ba ta kai wajen iyaye ba har wannan abu ya faru. Dan da ban san da wane ido zan kalleku ba. Se dai duk da haka kai kanka ina me daɗa baka haƙuri a kan abin da ya faru.. Ina fatan Allah ya musanya maka ita da wadda ta fita. Amma ka sani, na yaba da hankalinka sosai, na kuma so haɗa zuri'a da kai, se dai hakan be yi ba. Da kuma ina da wata yarinyar bayan Afrah da Afaaf, da wallahi zan baka aurenta ne. Dan kuwa itama Afaaf na aurar da ita.. Se dai bani da ita, hakan ne yasa nake maka fatan alkhairi da kuma fatan samun wadda ta fita.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.." Shi ne abin da Kaseem yake maimaitawa. Zuciyarsa na masa wani irin zafi. Be taɓa tunanin abin da ze zo ya ji daga bakin Abban ba kenan. Da ya san wannan zancen kunnuwansa zasu ji masa da ya yi fatan Allah ya kawo dalilin da zesa be zo ba. Ashe ba ze taɓa samun Afrah ba? Ashe Afrah matar wani zata zama? Ashe duk saurin da yake a bashi ita a banza. Lallai kuwa kamar yanda Abban ya faɗa ne kana naka Allah na na shi. Da ƙyar ya iya buɗe baki, bayan shuɗewar wasu mintuna tun bayan da Abba ya gama magana yace

"Babu komai Abba.. Allah yasa haka ne mafi alkhairi.. Na kuma gode da wannan shedar da na samu. Ni kaina da kana da wata ɗiyar Abba da kaina zan nemi ka bani ita, se dai tunda babu, dole zan haƙura. Allah ya riga ya tsara dama ba matata bace.. Allah ya basu zaman lafiya.." ya ƙare muryarsa a raunane. Cike da tausayawa Abba yace

"Ameen.." Miƙewa Kaseem ya yi yace

"Bari na tafi Abba.." Binsa da kallo Abba ya yi yana sake jin tausayinsa na ratsa shi yace

"Toh.. Allah ya yi maka albarka.." Da ƙyar ya iya amsawa da

"Ameen.." ya fice daga ɗakin. Abba ya bi shi da kallo har ya fice ɗin. Ko da ya hau motarsa kasa taɓuka komai ya yi. Ji ya yi inama shi mace ne ya dirza kukansa har da ihu, ko da mutane zasu fahimci irin raɗaɗin da zuciyarsa take. Duk da haka kuwa se da wata ƙwalla ta tarar masa cikin idanunsa, jikinsa har wani ɗumi ya ɗauka. Wannan maganar na ɗaya daga cikin munanan maganganun da ya ya taɓa ji. Za kuma ta cigaba da zama a mummunarta har zuwa lokacin da be san ƙarshensa

Please Login or Register in order to submit comment