Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nuna su ba taimako suke so ba kai suke son gani. Da suka ga dai mun hana da gaske, se suka ba ni wannan takardar wai a taimaka a baka." Kallan takardar Daddy ya yi cike da mamaki. Se ya saka hannunsa ya karɓa ya karanta abin da ke ciki. Cigaba ya yi da kallan takardar na tsawon wasu sakanni kafin ya ɗaga kai ya kalli saurayin yace

"Ka shaida musu su shigo nan.."

"An gama Rankayadaɗe." Ya faɗa cikin girmamawa. Kallansa Bad Man ya yi cike da mamakin abin da ya faɗa ɗin.

"Daddy.."

"Babu komai Areef.. Idan magana ce me muhimmanci bari na gama da saurarar waɗannan." Ajiyar zuciya Bad ya sauke yana miƙewa tsaye.

"Tohm." Daidai lokacin da yake ƙoƙarin fita, Ammi, Talatuwa da kuma Maimuna dake a kan kujerar masu matsala irin tata suka saka kansu cikin ɗakin, da taimakon wani daga cikin yaran Daddy. Ya ɗaga kafaɗa yana sake mamakin dalilin Daddyn na cewa a barsu su shigo nan ɗin.


.. Mota ɗaya ce se dai haɗaɗɗiya ta shigo cikin gidan. Cikin rawar jiki wasu mutane 2 suka bi bayan motar har zuwa inda ta tsaya.

"Daga ƙarshe dai mun dawo." Aunty Makiyy ta faɗa tana murmushi. Ita ma Mom murmushi ta yi kafin tace

"Ke bari kawai.. Duk da dai na san ze yi faɗa a kan abin da na yi. Amma buƙatata kawai nake so ta biya."

"Ai Yaya ke ɗin nan koh?" Ta ƙare tana girgiza kai.

"Kya dai ji da shi." Mom ta faɗa tana sanya ƙafarta waje ta sauka daga cikin motar. Ita ma Aunt Makiyy sauka ta yi suka soma takawa zuwa ciki. Daidai za su gifta sashen mommah Aunty Makiyy tace

"Ni kam ban ga juyarki ba Mom." Ta ƙare tana riƙe dariyarta. Dariya ita ma Mom ta yi tana faɗin

"Au tawa ce ma? Lallai ma Makiyya ba ki da kirki.." Kafin Aunty Makiyya ta sake cewa komai Bad ya fito daga cikin ɗakin Daddy. Duk da be yi tsammanin dawowar Mom ɗin a wannan lokaci ba, amma hakan be saka shi sakar mata murmushi ba ya ƙarasa ya bata side hug yana faɗin

"Welcome Mom.." Rungume shi ta yi sosai tana murmushi. Don ba shakka ta yi kewar ɗan nata. Se da ta sake shi sannan tace tana kallansa

"Ka na lafiya Son?"

"Ehh.. Kun dawo lafiya?" Ya faɗa bayan ya bawa Aunty Makiyy nata hug ɗin da ya fi kama da gaisuwa kusa kusa.

"Lafiya ƙalau." Suka amsa kusan a tare.

"Zan ɗan fita Mom.. Se zuwa anjima."

"A'ah ka san wani abu Areef?" Aunt Makiyy ta faɗa bayan ta riƙo hannunsa lokacin da yake ƙoƙarin barin wajen. Se ya dakata ya kalleta lokacin da take faɗin

"Mom fa ta yi laifi. Saboda haka ka tsaya mu shiga tare, idan ma haƙuri ne mu ba shi tare." Ɗan shiru ya yi se kuma yace

"Yana da baƙi fa."

"Baƙi kuma?" Cewar Mom cike da mamaki. Ba ta jira ya amsa mata ba ta ɗora da faɗin

"Baƙi a cikin ɗakin nan? Wane irin baƙi ne wannan? Ko kuwa Abbun Kaseem ne?" Girgiza kai ya yi ya ɗan ɗaga kafaɗa sannan yace

"Ban sani ba gaskiya.. Ni ma abin da ya fito da ni kenan." Hannun Aunt Makiyy Mom ta kamo tace

"Kin ga ku wuce mu je. Ko su waye su fito su tafi kowanne palour ne amma dai ban da wannan. Wannan ma ai rashin daraja ne da sakawa a zubarwa da mutum mutuncinsa. Na kuma san ba aikin kowa ba ne se waccan uwar iyayin."

"Yi haƙuri.. mu je ɗin." Aunt Makiyy ta faɗa tana bin bayan Mommah zuwa cikin ɗakin..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO61*


___ Ba Lulu ce ta koma ɗaki ba se da suka gama aikin tsaff. Ta kuma taimakawa Ummeey sosai, taimakawar da ta matuƙar yi wa Ummeey daɗi. Ta kuma sake jin ƙaunar Lulun na ƙaruwa a ranta.

Buɗe plate ɗin ta yi a fili tana faɗin

"Da na taɓa ci ai da se na ci yasin." Ta faɗa tana kallan kwaɗon yaɗiyar da Ummeey ta haɗa ya ji kayan haɗi, ban da ƙamshi babu abin da yake yi. Tun ɗazu ya bata sha'awa, se dai kuma ba ta taɓa ci ba. Hakan ne ya sa take tunanin soma ci. Se kawai ta saka wankakken hannunta cikin plate ɗin ta ɗiba ta kai baki. Lumshe idanunta ta yi lokacin da ta tauna ta ji daɗi. Se ta jinjina kai har lokacin idanunta a rufe. Se da ta taune na bakinta tsaff kafin ta buɗe idanunta a kan yaɗiyar tana faɗin

"Allah kuwa Ummeey ƙwararriya ce." Ta faɗa tana sake ɗibar wata lomar. Babu daɗewa kuwa se ga shi ta tashi yaɗiyar tass, har da suɗe hannu. Dariya ta yi lokacin da ta tuna furucinta na farko

"Da na taɓa ci ai da se na ci." Se gata ta cinye tsaff. Da ma wani abun idan ba ka taɓa ci ba ka da ka ce ba ka ci, dan ba ka san yanda ɗanɗanonsa yake ba. Banɗaki ta wuce ta wanko hannunta sannan ta fito daidai lokacin da yake shigowa cikin ɗakin. Se ta ƙarasa ta ɗauki plate ɗin ta wuce da shi ɗakin nan kafin ta dawo ta nemi waje ta zauna. Ƙarasa ware naɗin kansa ya yi yana sauke idanunsa a kanta. Kamar ba ze ce da ita komai ba se kuma yace

"Ya dai kamata ki dinga barin jikinki na shan iska haka nan.. Bacci hijabi, karatu hijabi, sallah hijabi, cin abinci hijabi, komai ma hijabi.. A dinga haƙura da shi wani lokacin tun da ki na gida." Shiru ta yi tana murza yatsan hannunta da ɗayan hannunta. Kai ba za ka ɗauka za ta ce wani abu ba. Se a hankali tace

"Ai dai jikina ne, kuma ɗakina." Ta faɗa tana ɗauke kai bakinta kamar ze faɗo. Be san lokacin da murmushi ya ƙwace masa. Wato kalmar "Ɗakina" ta ba shi dariya ainun. Yau ita ce da kanta take faɗin ai ɗakinta ne? Se ya girgiza kai kawai yana cigaba da abin da yake yi, a ransa yana saƙa yanda ze rabata da wannan zama da hijab ɗin kullum kamar me.



...Ajiyar zuciya Bad ya sauke yana soma takawa ya bi bayansu Mom ɗin zuwa ɗakin Daddy.

"Assalamu Alaikum.." Aunty Makiyy da kuma Mom suka haɗa baki wajen faɗin hakan. Ba su jira amsar kowa ba suka dirfafi cikin ɗakin. Kallan waɗanda Bad Man ya kira da baƙin Daddy Mom ta yi ɗaya bayan ɗaya. Sannan ta ɗauke kai da shirin zuwa ta zauna. Se kuma da sauri kamar wadda ta tuna wani abu ta maida dubanta kan Maimuna. Ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske. Se ta kai hannunta ta murza idanunta dan sake tabbatar da abin da take gani, har kuma lokacin ba ta janye idanunta daga kan Maimuna ba.

"Maimunatu.." Ta yi ƙarfin halin faɗa muryarta na rawa.

"Na'am.." Maimuna da idanunta suka yi jajir ta amsawa Mom kiran sunanta da ta yi. I zuwa lokacin suman tsaye ta yi. Cikin lokaci ƙanƙani jikinta ya ɗauki rawa na tashin hankali. Ta kasa ko da motsawa daga nan ne zuwa can. "Maimunatu! Maimuna!!" Shi ne kaɗai abin da take iya maimaitawa.

"Yallaɓiya ki zo ki zauna koh?" Daddy ya faɗa yana kallan Mom. Se kawai hawaye suka shiga zarya a kan fuskar Mom. Kafin kowa ya lura da hakan ta yi amfani da hannunta wajen gogewa, sannan ta taka har wani tangaɗi take kamar er maye ta yi inda Aunt Makiyy ta zauna ita ma ta zauna. Ji take kamar tace ba za ta zauna ba, ko kuma akwai inda za ta je, se dai ta kasa yin hakan. Tunaninta gaba ɗaya ya tsaya cakk. So kawai take ta farka daga wannan mummunan mafarkin da take yi. Dan kuwa a wajenta da ganin Maimunatu gwara a ce wata masifar ce ta same su. Kan hannun wata side chair Bad Man ya ɗosana jikinsa, shi dai yau ya ga yanda Mom za ta yi da waɗannan mutanen. Idan kuma a gabansu za ta yi magana da Daddy se ya gani.

"Wai me ye haka ne?" Aunt Makiyy da ta kasa fahimtar yanayin da Mom ke ciki ta faɗa tana kallanta. Shiru kawai Mom ta yi gaba ɗaya hankalinta da idanunta na kan Maimunatu ne.

"Uhmm.. babu damuwa ki faɗa min me ke tafe da ku." Daddy ya faɗa yana kallan Maimuna kamar yanda aka sanar da shi ita ce ta zo wajensa. Se da ta saka hannu ta share fuskarta sannan tace

"A yi min afuwa Rankayadaɗe.. Amma zan so a ce Hajiya Sa'adah na cikin ɗakin nan zan sanar da komai." Jinjina kai Daddy ya yi, kafin daga bisani ya sauke ajiyar zuciya. Be ce komai ba ya ɗauki wayarsa ya yi waya ta tsawon mintina 2 sannan ya sauke. Shiru ya wanzu cikin palourn. Har Bad Man ya miƙe da niyyar ficewa Mommah ta yi sallama cikin ɗakin. Sanye cikin wani lace me shegen kyau, ɗinkin riga da skirt. Kamar ko da yaushe ta yi ɗaurin ture ka ga tsiya, ta kuma yafa mayafinta madaidaici. Ta mugun yin kyau, kamar wadda ke shirin zuwa gasar sarauniyar kyau. Da mamaki take kallan cikin ɗakin, musamman da ta ga baƙin fuska. Se dai kawai ta isa kan kujera ta nemi waje ta zauna bayan ta yi jam'u wajen gaida su.

"Bismillah.." Daddy ya sake bata umarni a karo na biyu. Se ta haɗiyi yawu sannan tace

"Ka yi min afuwa da duk abin da ze fito daga bakina.. Haƙiƙa na san ni me laifi ce.. Na kuma san ze yi wuya ka yafe min.. Amma duk da haka ba zan iya ƙasa a gwuiwa ba wajen faɗa muku gaskiyar al'amari." Shiru ɗakin ya ɗauka kowa da abin da yake tunani. Ita Mommah sam ba ta shaida fuskar Maimuna ba, hakan ne ya sanyata kallanta kawai. Ya yin da Aunt Makiyy ke taɓe fuska tana mamakin ko wace Maimunan? Dan ita ma ba ta shaida fuskar ba. Ta ɓangaren Mom kuwa babu irin tunzuratar da zuciya ba ta yi ba a kan ta tashi ta fatattaki Maimunan tun kafin ta kwance musu zani a kasuwa. Se dai kuma daga lokacin da ta yi hakan ta gama kashe kanta. Hakan ne ya sa ta yi shiru, ta jira jin abin da Maimunan za ta faɗa kafin ta ɗauki mataki, duk kuwa da yanda ilahirin jikinta ke wani irin rawa kamar me jin sanyi.



_SHEKARUN BAYA_

Alhaji Abubakar Matawalle ya kasance matashin me kuɗi tun a wancan lokacin. Matashin da ke ji da kyau, ilimi da kuma kuɗi. Hakan ne ya sa mata da yawa suka din ga kawo masa tayi a kan ko ze aure su. Se dai shi duk ba sa gabansa. Mace ɗaya ce a gabansa, wato Sa'adah (Mommah) wadda ya haɗu da ita gidan wani Abokinsa da ta kasance ƙanwar matarsa. Tun daga wannan lokaci ya ji duk duniya babu wadda yake so se ita. Nan take ya je wa da mahaifiyarsa zancen. Se dai abin da ta faɗa masa ne ya sanya ya ji duk wani ƙwarin gwuiwarsa ya kau. Wato sanar da shi da ta yi tana so ya auri er ƙawarta Salma (Mom). Gyara zama ya yi kansa a ƙasa yace

"Ki yi haƙuri Hajiya.. Tun da na ga yarinyar nan wallahi na ji ina ƙaunarta. Ban san yanda zan ji ba idan kika ce min ba zan aureta ba." Girgiza kai Hajiya ta yi tace

"A'ah fa Abubakar.. Ni ba zan hanaka auren wadda kake so ba, matuƙar dai za ka haɗa da Salma. Saboda wannan ɗin alƙawari ne na ɗaukarwa mahaifiyarta, kuma ina son cika shi.
Se dai ka sani ba na goyon bayan rashin adalci. Idan har ka san ba za ka yi adalci ba, ka sanar da ni in san abin yi." Hajiya uwa ce a wajensa, wadda ta amsa sunan uwa har ma da mahaifi. Ba ya jin akwai wani abu da za ta saka shi kuma ya ƙi yi. Musamman a kan wannan abun da tace ta yi alƙawari. Idan har be karɓa ba kenan se tace ta fasa saboda ɗan nata ya ƙi amincewa? Ya girgiza kai yana faɗin

"Na amince Hajiya.. In Sha Allah kuma ba za ki same ni da rashin adalci ba." Murmushi Hajiya ta yi tana faɗin

"Toh Allah ya yi maka albarka."

"Ameen." Ya amsa da hakan yana miƙewa. Daga nan Hajiya da kanta ta je ta samu ƙanin mahaifinsa da maganar. Babu ɓata lokaci aka je aka yi magana a ko ina. Be samu tsaiko wajen Mommah ba, dan kuwa ita ma ta yaba da hankalinsa. Hakan ne ya sa suka soma zuba soyayyarsu babu kama hannun yaro. Ta ɓangaren Mom ma hakan take, dan kuwa ita tuntuni tana ƙaunar shi da ma. Shi ɗin ne dai a hankali yake ƙoƙarin ganin ya koyawa kansa. Kowaccensu ta san da zaman ɗaya. Haka kuma be ɓoyewa kowa gaskiyar al'amari ba. Duk da Mommah ta ji babu daɗi amma haka ta daure ta haƙura musamman saboda tana son shi. Ya yin da ta ɓangaren Mom kuwa hauka ne kawai ba ta yi ba lokacin da ta ji wai idan an tashi aurensu ba ita kaɗai ze aura ba. Da tausasawar mahaifiyarta ta samu ta haƙura ta dena ɗaga hankali. Se dai gefe guda kuma tuni ta soma shiryawa yanda zamanta da Mommahn ze kasance. A haka dai har aka ɗaura aure. Mom ita ce uwar gida ya yin da Mommah ta kasance Amarya. Hakan ba ƙaramin bawa Mom damar zuba rashin kirkinta ya yi ba. Ita a nata ganin ai ita ce uwar gida. Tun a satin farko Mommah ta soma fahimtar wace ce Mom. Hakan ne ya sanyata kama kanta. Ta fito mata a ainahin Sa'adahnta. Ita kam Mom babu abin da ke damunta irin kyawun Sa'adahn. Wadda wani lokacin take mata kama da en india. Ga wata shegiyar izza kamar er gidan sarauta. Ke idan ta yi shiga, ta saka kaya haɗaɗɗu tana takun nan nata ba Daddy kaɗai ba, ita kanta Mom ɗin ji take kamar kar ta dena kallanta. Hakan ba ƙaramin sosa mata rai yake yi ba, daurewa kawai take yi. Ta rasa wane irin abu ne wannan, wace irin yarinya ce Sa'adahn. Me za ta mata ta bar mata Alhaji Matawalle ita ɗaya? Da dai ta ga duk wannan ba mafita ba ce, se kawai ita ma ta shiga kamanta shiga irinta Mommahn ko za ta samu ta din ga fitowa kamar Mommahn. Se dai sam sam zaren ba kalar yadin ba ne.

Sam sam Daddy ba ya nuna banbanci tsakanin Mommahn da kuma Mom. Komai ze musu babu bambanci, haka zalika yana ƙoƙarin kwatanta adalci a komai musamman yanda cikin zuciyarsa yafi son Mommah. Se dai ba ya taɓa nuna hakan, ko dan ka da hakan ya janyo matsala a tsakaninsu. Duk da hakan ba ya isar Mom, se ta nemi wata hanyar da za ta takali Mommah faɗa da ita. Ita kam Mommah sam ba ta biye mata. Wanda hakan ba ƙaramin sake ingiza Mom yake ba. Gaba ɗaya burinta be wuce a ce Sa'adah kar ta haihu da Alhaji Matawalle ba. Ta fi so koma mene ne ita ta yi ta haihuwa da shi ya yin da Sa'adah za ta mutu a juya ba tare da ta ajje komai cikin gidan ba. Cikin wannan tsukun ne kuwa ta soma wani zazzaɓi me naci, da kasala. Da yake Daddy ba ya wasa da zuwa asibiti, ya sa kai tsaye asibiti ya ɗauketa ya kaita aka dubata. Binciken farko aka tabbatar da Mom ɗin na ɗauke da juna biyu. Farin ciki kamar ze kashe Mom dan daɗi. Ko babu komai alamar cikar burinta ya bayyana. Da alama dai Sa'adahn juya ce kamar yanda take fatan hakan a ranta kullum ko ta samu dama ta farko da za ta samu ta soma muzguna mata. Ta saki wani murmushi lokacin da Daddy ya yi parking motarsa cikin harabar gidan. Cikin ranta tana tsara irin rashin kirkin da za ta soma zubawa tun daga yau ɗin..


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO62*


___Tun da ta hango Mommah ta fito daga sashenta, se ta tsiri wani yamutse fuska tana riƙe ƙugu, irin yanda wasu masu tsohon ciki suke yi. Kamar za ta wuce ba tare da ta nuna ta gansu ba, se kuma ta ga rashin dacewar hakan. Tun da ko babu komai tare suke da Daddy. Hakan ne ya sanyata juyawa ta ƙarasa inda suke tana faɗin

"Sannu da zuwa.."

"Yawwah sannu ka dai." Daddy ya faɗa da murmushi kan fuskarsa. Lura da hakan da Mom ta yi ne ya sanyata tamke fuska, ta faki idanunsu Dad ta saka ƙafa tana sane ta bigi wani ƙaramin gini da ke ƙasa a gefenta. Se kuwa ta saka ƙara tana yin baya kamar za ta faɗi, cike da fatan Daddy ya lura da ita ya riƙota. Cikin sa'a kuwa ya lura da itan, se ya yi saurin riƙota yana faɗin

"Subhanallahi.." Se da ta koma ta tsaya a kan ƙafafunta sannan tace tana sake yamutsa fuska

"Ka ga tun yanzu wai har yaron nan ya fara wahalar da ni." Ta faɗa tana sake riƙe ƙugu lokaci ɗaya tana satar kallan Mommah dan tabbatar da ta ji abin da ta faɗa, dan kuwa ta yi hakan ne dan Mommahn ta fahimci abin da take ɗauke da shi, ko za ta kama kanta, ta san ita ɗin ba sa'arta ba ce yanzu, ta fita ta kowanne ɓangare. Dan ta san ba lallai ne Daddy ya sanar da ita tana ɗauke da juna biyu ba. Kallanta Daddy ya yi jin ta ambaci jinsi a maganar tata tun yanzun. Se ya yi murmushi kawai yana faɗin

"Ya kamata ki dinga kula dai kam."

"Ai dole na ma.. Duk da dai ka san yanzu ba zan iya aiki ni ɗaya ba saboda yaron nan.. Dole se dai a samar min yarinyar da za ta dinga taya ni."

"Yallaɓai se ka shigo." Mommah ta faɗa tana murmushi dan sarai ta fahimci maganganun da Mom ɗin take tana sane take ta yinsu duk dan ta ɗarsawa Mommahn wani abun cikin zuciyarta.

"Olright.." Daddy ya faɗa. Wata banzar harara Mom ta bita da ita a kan laɓɓanta tana furta

"Se dai baƙin ciki ya kashe ki.. Haihuwa kuwa se dai ki ga ina ta yi In Allah Ya yarda."

"Magana kike ne?" Daddy ya tambaya yana kallanta. Se ta yi saurin girgiza kai tana faɗin

"A'ah.." Daga haka suka wuce.

Daga wannan rana Mom ta shiga zuba rashin kirki kala kala, taɓara kuwa ba a magana. Kuma ba ta tashi yi se ta gansu a gaban Mommah. Ita kuwa Mommah ba ta taɓa nuna ta ga wani abun. Rayuwarta take cigaba da yi babu takura, babu ɗorawa kai damuwa wai dan kishiyarta ta samu ciki ita ba ta samu ba. Musamman kuma a lokacin da dududu ba su wuce watanni ba. A cikin wannan tsukun ne wata mata me samarwa da gidajen masu kuɗi en aiki ta samowa Mom Maimunatu, wadda aiki ne ya kawota Kano. Ta fara aikin gidan wani me kuɗi ya nemi ya lalata mata rayuwa. Daga nan ba ta sake zama ba, ta gudu. Shi ne aka samarwa Mom ita. A lokacin tana budurwa, da ma kuma Mom ba son babbar mace take yi ba, dan kuwa so take ta mallaka mata komai na aiki da ke cikin gidan. Ita kuma ba za ta bawa wata babba ta mata girki ba. A karon farko da ta soma ganin Maimunatu ta kwanta mata a rai. Dan haka babu ɓata lokaci ta karɓeta. Daga wannan lokaci Maimuna ta fara aiki a cikin gidan. Mom na cigaba da lura da take_takenta. Komai sakar mata shi ta yi, kama daga girki ne, wanke_wanke ne, shara, gyaran ɗaki, kai ba na Mom kaɗai ba. Hatta na Daddy idan ranar girkinta ce ita take turawa ta je ta gyara. Se daga baya da Daddy ya lura da hakan ya taka mata birki, yace idan ba za ta gyara da kanta ba ya bari Mommah ta gyara. Haushi ya cikata, se dai ta san tun da Daddyn ya faɗi hakan yana nufin haka ɗin. Hakan ne ya sanyata haƙura ta dena saka Maimunan gyaran ɗakin. Idan ranarta ce haka take haƙura ta yi da kanta gudun fushin Daddyn.

Cikin ƙankanin lokaci Mom da Maimuna suka yi mugun sabo. Har ta kai ga Mom ɗin kan zama su yi wata maganar ta sirri da ita, idan ta gaza samun Aunt Makiyya da lokacin take en matanci. Wani abu da ya ƙara saka alaƙarsu ta yi ƙarko shi ne yanda Maimunan ta kasance guntsi fetsi ce, wato ma'ana dai er gurmi ce. Da gangan ta tsiri cusa kanta wajen Mommah ko dan ta samu wani abun ta je ta faɗawa Mom. Se dai da yake Mommahn akwai tsare gida, da kuma kama kai, ya sanya ba ta samu wannan damar ba. Daga ƙarshe ma se kama kanta ta yi ta dena zuwa sashen.


... A karo na barkatai ta sake danna number, yanzu kam babu wani tunani ta danna number ta kira. Ringing ɗaya biyu aka ɗaga. Daga can ɓangaren aka ce

"Sa'adah.."

"Na'am Yaya ina kwana?.." Mommah ta amsa tana ɗorawa da tambaya.

"Lafiya ƙalau nake.. Ke fa?"

"Ni ma haka." Mommah ta faɗa tana dakatawa. Shiru na tsawon sakanni ba ta sake cewa komai ba. So take ta san ta ina za ta fara yi wa yayar tata magana. Duk da kasancewarta Yayarta da suke uwa ɗaya uba ɗaya. Yayar da ta zame mata tamkar mahaifiya tun bayan mutuwar mahaifiyarsu.

"Me ya faru ne Sa'adah?" Yaya Amina ta tambaya jin Mommahn ta yi shiru. Se a lokacin sannan Mommah tace

"Kin ga Yaya da ma so nake na faɗa miki, yau kwana 4 kenan ina amai. Duk abin da na ci se ya dawo, ga kuma kasala ina fama da ita. Tashin zuciya kuma shi ke sa in kaasa cin abinci. Kuma.." Se kuma ta yi shiru. Murmushi Yaya ta yi har tana miƙewa daga zaunen da take tace

"Ina Abubakar ɗin?"

"Ba ya nan.. Kwanansa 3 ba ya ƙasar." Sauke ajiyar zuciya Yaya Amina ta yi kafin tace

"Zuwa yaushe ze dawo?"

"Sati 1 ze yi." Mommah ta bata amsa.

"Toh shi kenan.. yana dawowa ki sanar da shi abin da ke faruwa. Ko kuma ma dai ki kira shi kawai ki sanar da shi zan zo in ɗauke ki mu je asibiti a duba ki."

"Yaya.." Mommah ta faɗa.

"Ehh haka na ce." Yaya Amina ta katseta da faɗin hakan.

"Tohm." Ta amsa da hakan. Daga haka suka yi sallama.

A ranar kuwa Yaya Amina ta zo ta ɗauketa suka tafi asibiti, a ranta tana fatan Allah Ya sa abin da take tunani ne. Aikuwa cikin yardar Allah suna zuwa aka tabbatar musu da Mommahn na ɗauke da juna biyu. Farin ciki a wajen Yaya Amina abin ba a cewa komai. Ita kam Mommah lumshe idanunta ta yi tana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa. Se ta rasa da wanne baki za ta yi amfani wajen godewa Allah da wannan ni'ima da ya mata.

"Bari na zama ta farko wajen yi wa Abubakar albishir." Hannunta Mommah ta kai ta dafe na Yaya Amina jin abin da tace

"A'ah Yaya Amina ni kam kar ki faɗa masa don Allah." Dakatawa Yaya Amina ta yi tana kallanta cike da mamakin jin furucinta. Se ta jinjina kai tana ɗorawa da faɗin

"Ni ba na so Salma ta sani ne Yaya. Ba ki ga rashin kirkin fa da take min ba. Na san da wuya idan ya ji be sanar da ita ba. Ni kuma na fi so kawai ta gan shi da idonta." Ta ƙare tana murmushi.

"Allah koh?" Yaya Amina ta tambaya tana kallanta. Se ta jinjina kai jin ta amince da abin da ta faɗa. Girgiza kai Yaya Amina ta yi tace

"Ba ki da wayo Sa'adah.. Yanzu saboda shiritita irin taki Sa'adah ta yaya dan kar kishiyarki ta san da zaman ciki a jikinki za a ƙi sanarwa da me shi? Idan na yi hakan ma ai ban kyauta ba."

"Kai Yaya.." Mommah ta faɗa tana kallanta.

"Ki bari na kira na sanar da shi. Ina ma da tabbacin ba ze faɗa mata ba, tun da dai shi ba mutum ne me surutu ba. Ke nata cikin a bakinsa kika ji?" Girgiza kai Mommah ta yi. Yaya Amina tace

"Toh kin gani." Yaya Amina ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kiran Daddy ta sanar da shi abin da ke faruwa. A

Please Login or Register in order to submit comment