Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abin da yake yi. Ta yunƙura za ta miƙe daga kan gadon ta jiyo muryarsa ya yi sallama cikin ɗakin. Shiru ta yi ba tare da ta amsa ba, se Little da ya amsa yana ƙarasawa ya rungume shi.

"Areef.." ya faɗa yana murmushi, se kuma ya ɗora da

"Ina Auntynka?"

"Tana kan gado. Ba ta da lafiya.."

"Je ka ce mata ta shirya mu tafi asibiti.." Gwani ya faɗa yana kallan Little. Dan tabbatar da ya ji abin da ya faɗa ya sanya shi faɗin

"Me za ka ce?" Se kuwa ya maimaita masa tiryan tiryan. Se a lokacin ya saki hannunsa, shi kuma ya tafi da sauri yana kiran sunan Lulu.

"Ya sayyadi yace ki zo ya kai ki asibiti.." ya faɗa yana yaye hijab ɗin da ta lulluɓa da shi.

"Je ka ce ba za ni ba.."

"A'ah.. ni dai ki taso mu je.." Galla masa harara ta yi tana miƙewa a kan gadon tace

"Wallahi zan ɓallaka idan ba ka bar wajen nan ba.." Hannu ya ɗaga ya kai kan idanunsa da suka fara yin rau rau. Ganin da gasken kuka ze yi ya sanyata saurin riƙo hannunsa tana faɗin

"Toh yi haƙuri na dena maka faɗa ka ji?" Ta tambaya tana narkar da fuskarta ita ma. Turo baki ya yi kawai be ce komai ba. Lulu tace

"Kaa ji sweetienah?" Ta faɗa tana jan kumatunsa. Se a lokacin ya yi murmushi sannan ya fice a guje ya koma wajen Gwani. Kamar yadda ta faɗa ɗin haka ya faɗa. Ya ɗan cije lips ɗinsa yana sauke ajiyar zuciya. Se kuma ya jinjina kai kawai be ce komai ba, ya kama hannun Little yace

"Je ka duba min me Ummeey take yi.." Babu musu Little ya fice daga ɗakin. Shi kuma ya wuce zuwa inda gadon yake.

"Na baki minti 10 ki shirya.. Idan ba haka ba in zo in shiryaki da kaina.." ya faɗa dan yanzu ya riga ya gane lagonta, idan kuwa har haka ne ze dinga amfani da hakan wajen sakata yin wasu abubuwan ko da kuwa ba ta yi niyya ba. Ɗaga ido ta yi ta maka masa harara a ɗan tsorace dan kar ya ganta. Se dai ba ta san sarai ya ganta ba, amma sam be nuna ya ganta ba. Ita yanzu ma idan ta yi abu dariya take ba shi musamman da ya lura duk wannan rashin kunyar ashe matsoraciyar banza ce.

"Kin zaɓi ɗayan kenan? Ya yi.." ya yi maganar yana soma takawa zuwa wajen gadon. Durowa ta yi daga kan gadon rai a ɓace duk da yanda ƙirjinta ke bugawa be hanata cewa

"Ai dai na ga jikina ne, kuma cikina ke ciwo. Ka ƙyale ni mana ai dama so nake na mutu a zo a ɗauki gawata a fitar da ita daga cikin gidan nan. Saboda haka ka fita a harkata ka ƙyale ni.." ta yi maganar cikin ƙarfin hali wanda a fuska ba za ka taɓa fahimtar hakan ba, se dai a zuciya ita kaɗai ta san tsoron da take ji. Ɗan luu Gwani ya yi da idanunsa kamar ze lumshesu se kuma ya buɗe su ya sauke su a kan Lulu. Yana mamakin jin furucin bakinta. Kenan tsanar da ta masa har ta kai ta dinga yi wa kanta fatan mutuwa. Ba ma iya nan ba, har ta yi abin da ta san ze janyo mata rashin lafiya may be ma daga nan ta rasa ranta? Kautad da idanunta ta yi saboda yanda ta ji bugun zuciyarta ya ƙaru tun lokacin da ya zuba mata idanun nan nasa.

"Ki chanja wata hanyar ba dai wannan ba, dan ba za ta ɓille miki ba. And magana ta ƙarshe.. ki wuce ki shirya, ko kuma wallahi ki ga abin da zan yi.." ya ƙare a ɗan fusace duk da yanda yake tausar zuciyarsa a kan Lulun. Banda haka da ƙyaleta ze yi ta yi abin da ta ga dama tunda har yanzu ba ta da hankali. Se dai koma mene ne tana ƙarƙashin kulawarsa ne, kuma daga lokacin da ya yi fatali da wannan nauyin dake kansa ya san shi ɗin me laifi ne. Jin yanda ya yi magana da kallan da yake jefa mata ya sanya yana ficewa daga ɗakin ta ɗauki hijab ta saka tana jin wani kuka na taho mata. Allah ma ya gani yanzu tsoron Gwanin take ji, ko da rashin kunyar za ta yi a tsorace take yinta. Ga shi yanzu ma ta ga kamar ba ya jin rashin kunyar, dan idan ma yana ji ita dai ba ta lura da hakan ba. Dan ko da za ta masa ɗin hakan ba ze hana shi yin abin da ya yi niyya ba. Se da ta ɗauki wajen minti 12 sannan ta fito tana ta ciccin magani. A tsakar gida ta taddasu shi da Ummeey har ma da Little. Ummeey na ganinta tace

"Sannu kin ji ɗiyata.. Wallahi ga shi kuwa har kin faɗa.. Sannu kin ji?" Ta faɗa tana kallanta.

"Yawwah.." shi ne kawai abin da Lulu ta faɗa tana riƙe hannun Little da ya je wajenta.

"Ummeey bari mu je.." Gwani ya faɗa cikin nutsuwa.

"Toh Allah ya tsare.. ya kuma ba da lafiya.." Ai tunda Little ya gansu cikin shirin fita ya ƙi yadda ya je wajen Ummeey, haka Ummeeyn ta haƙura tace su je tare. Hannun Little cikin na Lulu suka fito zuwa ƙofar gidan. Gwani na gaba yayin da su suke baya, Lulu se raka shi da wata uwar harara take yi, ga haushinsa dama da take ji ga kuma wata tafiya da yake yi kamar ɗan gidan sarakai ko wani me muƙami. Daidai lokacin da suka fito Abbati ma ya iso ƙofar gidan. Hango shi da Gwani ya yi ne ya sanya shi datakawa, yayin da Lulu da Little suka cigaba da tafiya. Tun daga nesa kuma se kallan Abbati ya koma kan Little da kuma Lulu, har wani ƙanƙance idanunsa yake yi dan yafi ganin daidai. Kallan Little Abbati ya sake yi, ya sake satar kallan Lulu da fuskarta ke a cunkushe kamar za ta kai wa duk wanda ya mata magana duka. Ɗaga idanunsa da Gwani ze yi se ya tsinci idanun Abbati a kan Lulun. Ya juya ya kalli Lulun dan tabbatarwa da gasken ita yake kalla? Se kuwa ya kama shi dumu_dumu yana kallan nata. Duk da ba sonta yake yi ba, amma ko babu komai matarsa ce a yanzun. Ko babu komai ba ze so ganin wani ɗa namiji na kallanta ba tunda dai matar aure ce. Shi ya sa tun ɗazu kafin su fito yake tunanin samo mata niƙab dan ta saka. Se dai kuma be san wata fassara za ta masa ba. Se dai koma mene ne daga yau ɗin ko wacce fassara za ta masa, kome kuma za tace ba za ta sake fita daga cikin gidan nan ba se da niƙab, dan ko babu komai yanzun mallakinsa ce. Shi kuma yana da wani abu, duk wani abu da ya kasance nasa, toh burinsa kawai ya kasance a killace a koyaushe. Kallan Little da ke ta kallan cikin layin nasu ya yi, ya kamo hannunsa da murmushin yaƙe yace

"Ku jira ni a can.." ya faɗa yana nuna masa wajen.

"Toh.." Little ya faɗa yana yin gaba. Kai tsaye wajen Lulu ya koma, da tun daga fara tafiya har ta gaji.

"Lulu wai mu jira shi a can.." ya yi maganar yana nuna mata wajen shi ma kamar yanda Gwanin ya nuna masa. Tsaki ta ja tana murguɗa baki kamar ba za ta motsa daga inda take ba, se kuma ta soma takawa zuwa wajen, ƙasa_ƙasa tana faɗin

"Ko ina ruwan mutum da ciwona.. Na tsani shishshigi.. Mutum se nuna shi wani ne yake yi bayan ba haka ɗin ba ne.." ta yi maganar duka a lokaci ɗaya .

Harɗe hannayensa Gwani ya yi a ƙirjinsa yana kallan Abbati fuskarsa a haɗe. Se da jikinsa ya yi sanyi a ransa yana tunanin ko ya kama shi ne yana kallan yarinyar can? Kuma ko dai ita ce matar tasa? Se da ya sosa ƙeyarsa sannan ya ƙaraso inda Gwani yake yace

"Afuwa Gwani.. A yi min aikin gafara.. Wallahi na kalleta ne dan tabbatar da wani abu da nake zargi.." Sam be yi niyyar saurarar abin da Abbatin ke faɗa ba, se dai jin abin da ya ambata daga ƙarshe ya sanya shi kallansa har lokacin be saki fuskarsa ba

"Zargi?" Ya faɗa cike da mamaki. Jinjina kai Abbati ya yi yace

"Ƙwarai kuwa.. Amma ka yi min haƙuri don Allah.. maganar a kan matarka ne.." ya faɗa ba dan yana da tabbacin hakan ba, se dan gane gaskiyar hakan. Kamar Gwani ba ze ce komai ba, se dai kuma ya ji yana son jin maganar, amma kuma maganganu irin wannan ɗin ba kasafai suka saba haɗa shi da Abbatin ba. Kallan inda Lulu take Gwani ya yi, kafin ya dawo da dubansa kan Abbati yace

"Me kake so ka ce?" Gyara tsayuwa ya yi, yana tunanin ta inda ze fara. Abubuwa kala kala ke tare da shi, se kuma ya fahimci dalilin tsayar da shi da aka yi aka ba shi wani saƙo, ashe duk dan ya yi amfani da su ne wajen ganar da Gwani gaskiyar al'amari. Be so hakan ta kasance a kan Gwani ɗin ba, mutum me matuƙar kirki da sanin ya kamata. Se dai kuma koma mene ne ba ze iya zuba ido a cuci Gwanin yana kallo ba tare da ya taɓuka wani abun ba..


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO36*

___ "Amma na ga kamar sauri kake yi.. Idan babu damuwa zan jiraka ku je ku dawo.." Abbati ya faɗa. Sauke numfashi kaɗan Gwani ya yi kafin yace

"Shi kenan.."

"Dama zamu yi magana da Malam, kafin ka dawo mun gama.." Abbati ya faɗa ba dan ya so hakan ba, se dan ba ya so ya yi maganar kuma a gaban Lulun. Ko babu komai ba ze so ta dinga masa kallan wanda ya tona mata asiri ba. Duk da ma shi be yi hakan da nufin tozar tata ba, kawai dai ze yi hakan ne saboda mutuncin dake tsakaninsa da Gwani. Dan idan ya yi shiru ba tare da ya faɗawa Gwani ba, bayan sanin ainahin wace ce Lulun kamar be kyauta masa ba. Yin gaba ya yi, har ya zo ya wuce su Lulu, ta yi kamar ba ta gan shi ba, se da Little yace mata

"Lulu ya tafi fa.."

"Ina ruwanka toh? Ya daɗe be tafi ɗin ba mana.."

"Kaiii!!" Ya faɗa kamar wani babba yana kallanta. Ɗauke kai ta yi tana harara sannan ta kama hannunsa suka soma tafiya. Wani ƙaramin asibiti dake bakin titinsu suka nufa wanda za a iya kiransa da chemist, se dai saboda faɗaɗashin da mamallakinsa ya yi ne ya sanya ya zama clinic.

"Matarka ce?" Shi ne abin da Likitan ya faɗa yana kallan Gwani sanda ta faɗa masa abin da ke damunta kamar za ta kai masa duka shi ma, saboda yanda take ta ciccin magani. Dama tunda suka taho Gwanin kansa ransa ba ya jinsa da daɗi ballantana har ya biye mata, hakan ne ya sa daga ita har shi ɗin fuskarsu babu annuri. Se dai fuskar Gwani kana kalla za ka gane a haka yanayinsa yake, yayin da oganniyar kuwa haushi da takaici su ne suka sanyata tsuke kyakkyawar fuskarta waje ɗaya.

"Cikinta ke ciwo, saboda abincin da ba ta son ci. Ya ɗan kumbura kuma.. Ina fatan yanzu ka fahimci abin da ke damunta?" Gwani ya faɗa dan ya ga yana nema ya yi wa ciwon nata wata fassara, saboda yanda ta yi bayanin a cunkushe. Sake haɗe face ta yi ita a lallai dole wata boss ce, wadda ba ta son raini. Ta saci kallansa ta maka wasa wata harara cike da haushinsa, da takaicin yanda ya kallan mata ciki saboda iskanci. Murmushi Likitan ya yi yana faɗin

"Ohk.." Basu daɗe cikin asibitin ba suka baro shi, bayan ya siya magangunan da aka rubuta mata, sannan suka dawo gida. Ita dai kawai daurewa take yi, ji take kamar ta tari adaidaita ta koma gidansu. Se dai idan ta koma ɗin bata san me za tace musu ba, hakan ne ya sa ta ɗan runtse idanunta ta buɗe daidai lokacin da ta shige cikin gidan hannunta na riƙe da na Little dake ɗauke da ledar magangunan.


A ƙofar gidan ya samu Abbati, zuwa lokacin har sun gama magana da Abeey, jiran Gwani kawai yake yi. Da mamaki Gwani ya ƙarasa wajen nasa yana faɗin

"Ashe kana nan?"

"Wallahi kuwa.. Kun dawo kenan? Sannunku da dawowa.." ya yi maganar duka a lokaci ɗaya.

"Yawwah.." Gwani ya faɗa. Gyara tsayuwarsa Abbati ya yi kafin ya soma faɗin

"Ban san ta yaya zan fara maka magana ba Gwani.. Ba munafunci zan maka ba, ba kuma so nake na tozarta wani ba. A'ah na ga hakan yana da kyau ka sani ne, saboda takanas aka zo aka faɗa min wata magana da ta hana ni sukuni a kan matar da ka aura." Cikin matuƙar mamaki Gwani yace

"Matata?" Ya tambaya a makakance.

"Ehh.." Cikin ƙankanin lokaci ya shiga zayyane masa yanda suka yi da mutanen nan ɗazu, sannan ya ƙare da fito da madaidaiciyar wayarsa ya shiga kamo hoton lokaci ɗaya yana faɗin

"Idan kuma har ban yi kuskure ba, toh wallahi yarinyar nan ita na gani ranar nan za ta shiga gidan nan da mutane ke kuka da shi, har na maka ƙorafi a kan yara ƙanana dake shiga gidan, toh ashe ma wannan ɗin ce. Na shaida na kuma tabbatar da hakan ne saboda a ranar ma tana tare da yaron nan.. Sannan kuma na sake gasgata hakan ne sanadiyyar wannan hoton da aka nuna min.." ya ƙare yana miƙawa Gwani wayar. Tunda ya soma maganar Gwani ke rarrabe kowacce kalma da ya faɗa yana haɗata da ma'anarta, saboda ya fi fahimtar abin da ya faɗa ɗin. Se dai zuwa lokacin da ya gama maganarsa ya kuma miƙo masa wayar hannunsa, se kawai ya ji wani bugun zuciya. Haka kawai ya ji kamar tsoro na shigarsa, har ya ji tamkar ma ka da ya duba wayar. Se dai kawai ya karɓa ɗin ya ɗora idanunsa da suka ɗan sauya tun lokacin da Abbati ya fara faɗa masa wace ce Lulu kamar yanda aka faɗa masa. A take, a kuma lokaci ƙanƙanci idanunsa suka sauka a kan hoton, kamar yanda aka faɗa ɗin hakan ne kuwa, Lulun ce tsaye wani ya rungumeta, wani wanda ba a iya ganin fuskarsa se tata, saboda daga ɓangarenta aka ɗauki hoton. Ɗan runtse idanunsa ya yi cikin rashin sanin abin yi. Bayan wajen second 30 ya buɗe idanun nasa lokacin da suka yi ja kamar ba na shi ba, se dai ba a kan hoton ba, dan ba ya tunanin ze iya cigaba da kallan hoton, ko da kuwa ba maganar wadda take a matsayin matarsa ake yi ba, ballantana kuma wadda ke a matsayin matar tasa. Cikin matuƙar dakiya yace

"Ban da kai se wa ya ga hoton?" Ya tambaya a sautin muryarsa kaɗai za ka fahimci yanda abin ya yi masa ɗaci.

"Ni kaɗai aka nunawa, ni ma ɗin wai dan ya je wajenka ne.." Fito da wayarsa Gwani ya yi, ya yi danne_danne a ciki. Bayan wajen minti 1 ya miƙawa Abbati wayar sannan yace

"Ba na son sake jin maganar a wani wajen. Zan yi maka magana duk lokacin da na gama bincike.." Daga haka kawai ya wuce cikin gidan saboda yanda yake jin wani irin zafi cikin ransa, ba kuma ya tunanin ze sake tsayawa su yi wata maganar bayan wannan. Binsa da kallo Abbati ya yi cike da tausayawa, se kuma ya girgiza kai yana faɗin

"Toh Allah ya kawo mafita.." Daga haka ya soma tafiya dan barin ƙofar gidan. Cike da fatan ƙin samun kowa a tsakar gidan ya shiga, cikin sa'a kuwa babu kowa. Kai tsaye ɗakin nasa ya wuce. Cikin sa'a Lulun na can ɗakin Ummeey. Neman waje ya yi ya zauna a kan gadon yana saka hannu ya ware abin da ke kansa ya ajje shi gefe. Ya ɗauki hannayensa duka biyun ya ɗora a kan baƙar sumar kansa idanunsa a lumshe. Farar fuskarsa har wani ja ta yi, haka zalika idanunsa. Sake runtse idanunsa ya yi saboda yanda idanunsa babu abin da suke hangowa se wannan hoton. Ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen cire hoton daga ƙwaƙwalwarsa amma ya kasa. Dama haka take? Ya tambayi kansa. Tambayar da ita kaɗai ke yawo a cikin ƙwaƙwalwarsa. Girgiza kai ya shiga yi kamar wanda aka ba shi amsar tambayar da ya yiwa kansa. Se ya cigaba da zama cikin ɗakin na tsawon mintuna 5 sannan ya miƙe tsaye, ya shiga zagaye inda yake ɗin gaba ɗaya ransa a cunkushe kamar yanda fuskarsa take. Iska ya ɗan fesar da ita daga cikin bakinsa, yana so hakan ya fice masa a rai, ya kuma dena damuwar sosai. Be san me ya sa ya ji ransa ya mugun ɓaci ba, wanda ko da shi ya zaɓeta a matsayin mata iya abin da ze yi kenan. Se dai ya rasa dalilin da ya sa ya ji sam ya kasa amincewa da abin da Abbatin ya faɗa. Ga dai sheda nan duka ya kawo masa, har da hoto kuwa, amma duk da haka neman wata hanya yake yi da ze sa ya yi fatali da hakan, hanyar da za ta danne duk wata sheda da aka nunawa Abbatin. Babban abin da ya sa ya sanya wa duk abin da Abbatin ya faɗa masa ayar tambaya, yanda har aka tare shi aka faɗa masa abin da matar Abokinsa ta yi. Idan dai har da gasken ba sa so a yaudare shi me ya sa kai tsaye ba a zo an same shi shi da kansa ba?. Lumshe idanunsa ya ɗan ƙara yi, daidai lokacin da hoton ya sake dawo masa. Se ya yi saurin buɗe idanun nasa yana fesar da wata zazzafar iska daga bakinsa.

"Idan kuma haka ɗin ne fa? Idan da gaske duk abin da aka faɗa tana aikatawa fa?" Zuciyarsa ta raya masa hakan. A fili ya furta

"Hasbunahallahu wa ni'imal wakeel.." ya faɗa yana neman waje ya zauna. Cikin kuma ƙanƙanin lokaci ɓacin ransa ya daɗu, se ya ji kamar ana masa bita ne a kan abubuwan da Abbati ya faɗa masa.

"Me ya sa na amince da auranta?" Ya tuhumi kansa yana tunanin idan har wannan al'amari ya je kunnen wasu mutanen me ze faru? Se dai kuma har abada ba ze taɓa yin hukunci ba tare da bincike ba, dan haka abu mafi muhimmanci shi ne sanin gaskiyar lamarin.


... Ya yi mamakin ganin kiran Mami ɗin cikin wayarsa, se dai kawai ya ɗaga da sallama a bakinsa. Se da suka gaisa sannan Mami tace

"Na kira ne na yi maka jaje a kan abin da ya faru.." Se ta ɗan dakata a nan sannan ta ɗora da

"Na kuma sake baka haƙuri a kan wannan rashin da ka yi. Allah ya zaɓa maka wadda ta fita zama alkhairi.." Sosai ya ji daɗin addu'ar Mamin dan haka ya yi murmushi sannan yace

"Godiya nake sosai Madam. Allah ya bar zumunci.."

"Ameen Kaseem. Ai babu komai.." Mami ta faɗa tana murmushi sosai.

"Amma wani hanzari ba gudu ba.. ka na ji na?"

"Ehh.." cewar Kaseem. Se da Mami ta nemi waje ta zauna tana tunanin ta inda za ta fara wannan zancen, se dai kawai ta maaze tace

"Me ze hana tunda ka rasa Afrah ka yi tawakkali ka nemi wata? Da ba a yi wa Afaaf aure ba ni da kaina zan haɗaku. Se dai kowaccensu yanzu haka tana ɗakin mijinta, dan haka ni na yanke shawarar yi maka tayin er wajena Jadwa. Idan dai har ka amince zan san yanda zan yi na shawo kanta ta amince maka.." ta ƙare tana dariyar yaƙe, cike da fatan abin fa ze fito daga bakinsa ya zama amincewa ne da tayin da ta masa. Se dai addu'ar tata ba ta karɓu ba, dan kuwa buɗar bakinsa se cewa ya yi.

"Allah sarki.. Na gode sosai.. Allah ya saka da alkhairi, na kuma ji daɗin wannan tayin da kika mini, ko babu komai hakan ya nuna kin aminta da ni ne. Se dai kuma tare da dukkan wata girmamawa nake ce miki ki yi haƙuri.. amma na gode da wannan tayin. Ina nufin ba na buƙatar haɗin, ba kuma dan komai ba se dan yanzun babu batun soyayya a tare da ni, ba na buƙatarta sam. Ko da zan yi ma ba yanzu ba.."

"Ai babu matsala, in dai Jadwa ce za ta iya jiranka. Kai na san ma da kanta za ta chanjaka, ta cire maka wannan ƙudurin a ranka.." Murmushi ya yi kawai sannan yace

"Ki yi haƙuri Madam.. Yanda na faɗa ɗin dai shi ne.. Na gode sosai.." Cikin ɓacin rai Mami ta katse kiran tana jin wani irin takaici na mamayeta. Haushin Kaseem ɗin na kamata, ta zubar da mutuncinta ta tallata masa ɗiyarta amma ya watsa mata ƙasa a ido? Ta yi wata ƙwafa a fili tana furta

"Shashasha.."

"Mami.." Jadwa ta faɗa tana turo baki.

"Me ya faru?" Mami ta faɗa tana kallanta a fusace.

"Yanzu ya zamu yi kenan?"

"Ya kuwa za mu yi, banda mu sauya zani.." Mami ta faɗa tana miƙewa.

"Kawai ki ba ni numbersa, zan san yanda zan yi na shawo kansa Mami.." Jadwa ta faɗa tana kallan Mamin.

"Aou wai ba ki ji haushi ba?" Mami ta faɗa cike da mamaki tana kallan Jadwan saboda ta riga ta san halin zuciya irin ta Jadwan. Se dai kuma ta ga kamar ba ta ji haushi ba bayan ita a wajenta kamar cin mutunci ne Kaseem ɗin ya musu.

"Ban ji ba.." ta faɗa tana ɗauke kai gami da yamutse fuska. Da dai ta fuskanci da gasken Jadwa take se ta haƙura ta ɗauki wayarta dan ba ta number Kaseem ɗin. Ba ta kai ga gama karanto mata number ba, wani kiran ya shigo cikin wayarta. Da sauri ta ɗaga wayar tana neman waje ta zauna.

"Hello Hajiya komai ya kammalu.." Daga can ɓangaren aka faɗa. Murmushi Mami ta yi tace

"Babu wata matsala kenan?"

"Ƙwarai kuwa. Se jiran sakamako kuma.."

"Na gode ƙwarai da gaske.. Ka sake tura min account ɗinka za ka ji ni.."

"Dena godiya Hajiya.. Aiki ne na yi a kan aiki, so duk ƙaruwarmu ce wannan ɗin.." daga can ɓangaren aka faɗa.


... A yatsine take bin ko ina na gidan da kallo fuskarta kamar tana kallan kashi ko wani abun makamancinsa. Da ƙyar ta buɗe baki tace

"Babu kowa a gidan ne?" Ta tambaya sanda ta baro soron gidan. Fitowar Ummeey kenan daga cikin ɗaki hannunta ɗauke da dadduma za ta gogewa Abeey kayansa ta ji maganar Mamin. Se ta juya ta kalleta, ta ɗauka za ta ji sallama daga bakinta se dai ba ta sake cewa komai ba se kallan Ummeeyn da take yi.

"Maraba.. shigo.." Ummeey ta faɗa fuskarta babu yabo ba fallasa.

"A'ah babu buƙata. Na zo wajen 'yata ne." Se a lokacin Ummeey ta fahimci wajen wadda ta zo ɗin, dan haka tace

"Tana ciki.." Daga haka ta yi gaba zuwa wajen da ta ajje dutsen guga dan ɗauka ta soma gugar. Tsaki Mami ta ja wani irin takaici na sake kamata. Wai a ce Lulu ke zaune cikin gidan nan a matsayin gidan aurenta. Ba ta taɓa tunani ba, ba kuma ta taɓa zato ba. Ita da Didi ce ma se ta haƙura tace dama haka ƙaddararta take, amma Lulu fa? Se kuma kawai ta yi murmushi tana tunanin ai kuma duk wata matsala ta zo ƙarshe tunda ta gama samun mafita. Tura ƙofar ɗakin Gwanin ta yi tana wurga idanunta dan ganin inda za ta hango Lulun tata. Se dai ba ta hangota ba, se da ta ida shiga ɗakin sannan ta hangeta a zaune kan gadon, Little na kan cinyarta yana bacci. Da sauri Mami ta ƙarasa tana faɗin

"Lulu.." Kamar a mafarki ta jiyo muryar Mamin, se dai ta san yaudarar kanta ne kawai take yi, amma duk da haka se ta ɗaga kanta dan tabbatarwa kanta da muryar da kunnuwanta suka jiye mata. Cikin sakannin da basu wuce 3 ba idanunta suka sauka a kan Mami. Ba ta san lokacin da ta yi wani uban tsalle ba, ta diro daga kan gadon, har ba ta san yanda aka yi Little ya sauka daga kan cinyarta ba. Rungume Mamin ta yi lokaci ɗaya tana

Please Login or Register in order to submit comment