Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fice daga cikin ɗakin ba tare da tace komai ba. Ita kam Didi ko jin abin da ya faɗa ma ba ta yi ba saboda yanda hankalinta gaba ɗaya ke kan yanda za ta ƙwace jikinta daga nasa. Lura da hakan da ya yi ne ya sanya shi sakin Didi da ɗan ƙarfi. Har se da hakan ya sa ta yi taga taga kamar za ta faɗi se kuma ta dawo ta tsaya a kan ƙafafunta. Ya ɗan ja ƙaramin tsaki yana ɗan lumshe idanunsa na tsawon second 10 kafin ya buɗe. Ba tare da ya kalleta ba yace lokacin da ya fara takawa dan ficewa daga cikin ɗakin

"Kar ki ɓata min lokaci, ki fito.." Daga haka ba tare da ya jira amsar da za ta ba shi ba ba ya fice daga ɗakin. Hannu ta kai wajen allurar ta dafe tana jin yanda wajen ke mata zugi. Ta ja sheshsheƙa kamar wadda ta yi kuka sannan ta soma takawa dan bin bayansa. Se a lokacin abin da ya faru ya dawo mata. An ya kuwa lafiyarsa ƙalau? Me ye ya shiga kansa ɗazun be tashi sauka ba se yanzu? Har ta isa inda motarsa take ba ta dena jin zafin allurar ba kawai mazewa take yi. Lokacin da ta isa har ya shige cikin motar yana shirin tayarwa. Ta yi saurin buɗe murfin motar ta shige a inda ta zauna ɗazun. Shiru ya yi lokacin da ya ji zamanta a gidan bayan. Shi se yanzu ne ma ya tuna a inda ta zauna ɗazun, saboda yanda yake a fusace be ma lura ba.

"Kee!!" Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. Kamar ba za ta ɗaga kai ba dan ita ta ƙafarta take da inda aka mata allura. Se dai ta san tabbas da ita yake tunda babu kowa cikin motar daga shi se ita. Hakan ne ya sanyata ɗaga kai kawai.

"Waye sa'anki? Waye drivernki?" Tun kafin ya kai ƙarshen maganar ta buɗe murfin motar ta fito ta shige gaba. Kamar wancan karon haka ta kame kanta waje guda in case ma ka da ta yi wani abun yace ta yi.



... "Mami don Allah ki zauna.." Jadwa ta faɗa tana kallanta.

"Rabu da ni Jadwa.. ki bar ni. Na kasa mantawa da cin mutuncin da Lulu da wancan mijin nata suka min. Har ni Sadiya za a cewa na fita na bar waje?" Ta yi maganar tana jin zafin hakan har cikin ranta.

"Ki yi haƙuri ki manta kawai. Lokaci ya yi da za ki cire hannunki a kan al'amuran Lulu. Ni da ma tun da na ga kina ta shishshigewa na janye jikina saboda gudun yarfi."

"Uhmm ai ba a taɓa ci min mutunci irin wannan ba." In ji Mami tana girgiza kai.

"Mami wai kuma wannan ɗin nan da muka gani shi ne mijin Sister Lulu? Na ji kina kwatanta shi da wani banzan mutum. Ni wallahi ba dan abin da kike faɗa ba ba zan yadda ba daga gidan arziƙi ya fito ba. Saboda kalar shigarsa da kyawunsa wallahi da farko na ɗauka wani balaraben ne fa.. se da na ji ya yi magana.."

"Dallah can.. shashashar banza shashashar wofi.. ke dai kin shiga 3 idonki idon maza. Kowa kika gani se kin yaba shi. Me ye haka ne Jadwa? An ya kuwa?" Mami ta ƙare tana kallanta sosai. Hararar gefe Jadwa ta yi tana ɗauke kai lokaci ɗaya tana huhhura hanci ita a lallai dole maganar Mamin ta ɓata mata rai. Fahimtar hakan da Mami ta yi ne ya sanya ta faɗin

"Naa ji amma dai ba ki na nufin kin dawo daga rakiyar Kaseem ba ne koh?"

"A'ah ni kam ba haka nake nufi ba. Ai ke ce ba ki tsaya kin ji ƙarshen maganar tawa ba." Ta ƙare tana tura baki.

"Toh shi kenan ya wuce.. Mu koma kan abin da ze fishshe mu."



... A ɗaya ɓangaren kuwa tana zaune a kan gadon jingine jikin bango tana tunanin yanda rayuwarsu ita da er uwatta ta sauya cikin lokaci ƙanƙani. Ba ta ji shigowarsa ba dan ko sallamarsa ma ba ta ji ba saboda yanda ta yi zurfi cikin tunani. Se gyaran murya kawai ta ji, hakan ne ya sanya ta buɗe ido da sauri. Idanunta da suka sauka cikin nasa ta yi saurin janyewa.

"Wace ce ita?" Ya tambaya still yana kallanta. Kamar ta yi shiru se kuma ta ji ba za ta iya hakan ba, dan haka ta buɗe baki a hankali tace

"Ƙanwar Abba ce.."

"Ƙanwar Abba?" Ya ƙare da alamar tambaya. Se dai be jira ta ba shi amsa ba ya ɗora da wata tambayar

"Amma me ya sa kika mata haka?"

"Ba komai.." ta faɗa tana taɓe fuska dan har lokacin ranta babu daɗi. Girgiza kai ya yi yana ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗe baki yace

"Ba haka ba ne.. akwai dai wani abun.."

"Babu.." ta ba shi amsa a gajarce

"Toh kuwa zan barta ta cigaba da zuwa wajenki.." Daga haka ya juya dan barin wajen. Da sauri ta kalle shi, ganin ba shi da niyyar tsayawa ya sanyata faɗin

"Da ta ga hoton nan ne fa ta nuna jin daɗinta.." Abin da ya ji ta faɗa ne ya sanya shi dakatawa cike da mamaki. An ya kuwa da gaske take yi? Ko dai ta faɗi hakan ne dan kare kanta? Ƙanwar mahaifinta fa? Toh idan kuma haka ɗin ne me ye dalilin da ze sa ta ji daɗin gani hoton? Akwai wani dalili kuwa? Toh ko dai duk dan hakan ya zama sanadiyyar rabuwar aurensu ne? Dan ya lura tun farkon ganinta ba son shi take yi ba. Shi haka nan ma kawai ya ji ba ta kwanta masa a rai ba ko kaɗan. Duk shi kaɗai yake tsara hakan cikin ransa har kuma lokacin be juyo ba. Se da ya gama saƙe saƙen sannan ya juyo ya kalleta.

"An ya kuwa?" Ya tambaya dan sake tabbatarwa. Se kawai ta jinjina kai tana sake tuna lokacin da suke magana da Mamin a kan hoton. Se ya jinjina kai yana sauke numfashi har lokacin ya kasa dena mamakin abin da ta faɗa ɗin.

A ranar aka sallami Lulu daga asibitin. Bayan dawowar Ummeey suka suka shirya komai se gida..


.. A ɗaya ɓangaren kuwa babu daɗewa suka isa gida. Yana gama parking ɗin motar ba ta jira komai ba ta fice daga ciki. Daidai lokacin da take sauka daga cikin motar idanun Mom suka sauka a kanta. Se ta buɗe idanu sosai tana kallan wanda ze fito daga cikin motar. Bayan wasu sakanni se ga Bad Man ya fito daga cikin motar hannunsa saye cikin aljihunsa da ya jefa key ɗin motar a ciki.

"Na shiga 3.." Mom ta faɗa tana maida dubanta kan Didi da ta kusa ƙarasowa inda take. Tun da Didi ta hangota ta ji faɗuwar gaba ta ziyarceta, ita ta rasa dalilin da ya sa take shakkar matar. Idan ta ganta kamar wadda ta ga sheɗan, ta dinga janyo duk wata addu'a da ta zo bakinta kenan. Haka dai ta daure ta cije lokacin da ta iso wajen Mom ɗin, ta tsugunna a nutse tace

"Barka da wannan lokaci.."

"Barka da lokacin uwarwa? Ke.. ni za ki asircewa ɗa? Toh wuce ki je sashena ki jira ni gani nan zuwa za ki gane kurenki.." Mom ta faɗa a fusace. Sauke numfashi Didi ta yi kawai se ta miƙe cikin nutsuwar nan tata, ta shiga karanto duk addu'ar da ta zo cikin bakinta kamar kodayaushe ta yi gaba jiki a sanyaye.

Murmushi ya sakarwa Mom ɗin tasa lokacin da ya ƙaraso inda take, yana shirin yi mata magana tace

"Kar ka ce min komai Boy.. Ba na buƙatar jin komai daga bakinka.. Abin da nake son ji kawai shi ne me ya kai yarinyar can cikin motarka?" Tsayawa ya yi yana kallan Mom ɗin cike da mamakin tambayar da ta fito daga bakinta. Ya ɗauka ko wata ce ze iya ɗaukarta cikin mota ba tare da wani abun ba. Ballantana wadda Daddy da kansa ya masa umarni da ya ɗauketa dan tana matsayin matar da ya aura masa? Ko tana zarginsa ne?

"Mom.." ya faɗa muryarsa a ɗan kaurare.

"Ka ba ni amsa kawai.. ka fara biyewa waccan munafukar matar ne ka na so ka bijire min? Areef ko ka manta wace ce ni? Ka manta abin da na faɗa maka? Ba na son auren kuma ba na son matar? Ba ka tsoron Allah ya kamaka? Me ya kai ka ɗaukarta cikin motarka? An ya kuwa Areef?"

"Wai Mom hakan na da zunubi ne?" Ya katse Mom da faɗin hakan a ƙage fuskarsa na nuna hakan. Saboda yanda ya ƙagu ta kai ƙarshen maganar tata amma ta ƙi katseta se ma nunawa da take yi kamar ya aikata wani babban saɓo ne..



A yi manage da wannan..


MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO47*


___Tsayawa Mom ta yi tana kallan Bad Man sosai kamar me nazarin abin da ya gama faɗa ɗin. Anya kuwa shi ne a gabanta? Me yake shirin faruwa ne? Se da ta ɗan ja numfashi kaɗan kamin tace

"Areef.." Kamar ba ze amsa ba, se kuma ya buɗe baki a daƙile yace

"Yes Mom.." Iska ta sake fesarwa daga bakinta sannan tace

"Shi kenan.. mu je ciki mu yi magana.." Girgiza kai ya yi dan har ga Allah be ji daɗin yanda Mom ɗin ta titsiye shi haka tana ta masa tambayoyi ba.

"Mom ina so na wuce.."

"Plss.. mu je dai." Gaba ya yi ya wuce zuwa sashen Mom ɗin hannunsa riƙe da wayarsa yana dannawa. Ɗan dakatawa ya yi kafin ya kai ga ƙarasawa sashen Mom ɗin yana sake kallan cikin wayar tasa.

"Oh god.." ya faɗa yana kai hannunsa ya ɗan dafe goshinsa. Sam ya manta da maganar Hero se yanzun yake tunawa. Ya ja ƙaramin tsaki yana ɗan furzar da iska daga bakinsa. Se ya ƙara saurin tafiyarsa zuwa sashen Mom ɗin cike da fatan ta gama faɗa masa abin da za ta faɗa masa ya wuce inda yake da tabbacin ze sami Hero wanda tunda abin nan ya faru be sake bi ta kansa ba.

Kafin ya shiga palourn ya dakata, ya ja kujera ya zauna yana ɗan karkaɗa ƙafarsa. Daidai lokacin Mom ta iso. Se a lokacin sannan ya sauke ƙafar tasa yana kallanta. Neman waje ta yi ta zauna tana fuskantar shi. Cikin kwantar da murya tace

"Wai ka fara son yarinyar can ne?" Ta tambaya tana kafe shi da idanunta. Dan so take yau ɗin ta gano komai a wuce wajen, shi ya sa take bugar cikinsa. Kallan Mom ɗin kawai ya tsaya yana yi kamar wanda ya ji ta yi saɓo. Se can ya yi wani murmushi wanda ke matuƙar ƙawata fuskarsa.

"Shi ne maganar da ma?" Ya tambaya a nutse.

"A'ah.. so nake na ji dalilin da ya sa ka ɗauketa cikin motarka.." Numfashi ya sauke daidai lokacin da yake lumshe idanunsa, ya buɗe su kana yace

"Bari dai na faɗa miki yanda aka yi.. Daddy ne ya saka ni.. Daga nan babu wani abu" ya ƙare yana kallanta.

"Toh madallah.. Amma ka san wani abu?" Ta ɗan dakata a nan tana tunanin an ya kuwa ta fara yi masa maganar ya bar ƙasar kamar yanda ita ma za ta bari har ta dawo yanzu?

"Shi kenan ma kawai je ka.. Ina za ka je?" Ta fasa yin maganar bayan ta gama tsarawa a ranta ba yanzu ya kamata ta yi masa ba. Shafa sumar kansa ya yi kamar yanda marasa gaskiya ke yi yace lokacin da ya miƙe

"Babu.."

"Toh shi kenan.. duk lokacin da kake free dai ka zo mu yi hira ka san ba na son shigowa sashen nan.." ta ƙare tana ɗan yamutsa fuska.

"Ohk.." ya faɗa yana matsowa kusa da ita ya yi hugging nata sannan ya fice.

"Allah ya maka albarka.." ta faɗa tana binsa da kallo murmushi fall fuskarta. Har yau har gobe ta kalli Areef ɗin se ta ji farin cikin kasancewarsa ɗanta..

Bayan wajen minti 1 da fitarsa Mom ta sauke ajiyar zuciya sannan ta cigaba da takawa zuwa palournta. Tana zaune a ƙasan carpet a mugun takure kamar wadda wani abun ze kama. Se babbaza idanu kawai take yi cikin rashin sanin abin yi. Wani kallo Mom ta watsa mata tana sake ji har cikin ranta wannan yarinyar ba za ta taɓa zama sirikarta ba. Dan kuwa tun kallon farko ta ji ba ta mata ba, ban da ma tsanarta babu abin da take ji cikin zuciyarta. Ballantana kuma a kai ga ba ita ce ta yi wa Areef ɗin zaɓi ba, zaɓin mahaifinsa ce. Ita kuma ba ta ga abin da ze sanya ta amshi zaɓin Daddyn a matsayin zaɓinta ba, ko da kuwa yarinyar ta mata ne ballantana kuma ba ta mata ba. Wani banzan kallo Mom ɗin ke binta da shi lokacin da ta ida shiga cikin ɗakin. Se a lokacin sannan Didi ta san da zuwanta cikin ɗakin. Ta yi saurin yin ƙasa da kanta saboda yanda ƙirjinta ya buga lokacin da suka haɗa idanu.

"Tashi maza ki ji ni shashasha.." Mom ta faɗa a tsawace. Babu musu Didi ta tashi se dai har lokacin ba ta sake gangancin kallan Mom ba.

"Ki buɗe kunnanki da kyau ki ji ni.. Daga yau se yau, kar da wata ƙatuwa ko kuma wani yace miki ki shiga motar ɗana ki shigeta. Wannan motar ba an yi ta ne dan irinki ba a'ah.. ki kama kanki, idan ba haka ba zan ɗauki mummunan mataki a kanki. Zan kuma ƙarasa nuna miki wace ce ni, dan na ga har yanzu kin kasa fahimtar wace ce ni.. kin ji ni??" Jinjina kai Didi ta yi a hankali.

"Ki buɗe baki ki min magana shashasha.." Mom ta sake faɗa har wani huci take fiddawa.

"Eh na ji.." Didi ta faɗa a sanyaye.

"Toh ga hanya nan ɓace min da gani." Ta yi maganar tana nuna mata hanyar fita. Babu musu, da ma abin da take buƙata kenan, Didi ta ɗaga ƙafafunta ta fice daga ɗakin.

"Wawiyar yarinya.." Mom ta faɗi hakan bayan ta bi ta da wata harara..



... A ranar da aka sallami Lulu ranar Abba ya wakilta wasu suka je suka kai mata haɗaɗɗun kayanta na gani na faɗa wanda suka kasance sakk irin na Didi ne babu bambancin komai. Ba wani daɗewa suka yi a gidan ba, bayan sun gama shirya komai da taimakon Ummeey suka wuce gidan Alhaji Matawalle inda a can ɗin waje daban aka basu suka ajje kayan da niyyar duk lokacin da su Didin za su koma gidansu na su su kaɗai se a tafi mata da su. Saboda nan ɗin ko ina akwai furniture, akwai komai na buƙata. Se bayan da masu jeran suka tafi sannan Ummeey ta wuce asibiti suka taho tare da su Gwani da Lulun gida.

.. A ɗakin Ummeey suka sauka duk da kasancewar dare ne hakan be hana Ummeeyn saurin hura wuta ta ɗorawa Lulu ruwa dan ta samu ta yi wanka ba.

"Ki tashi ki je ki yi wanka za ki sake jin daɗin jikinki.." Ummeey ta faɗa da murmushi a kan fuskarta tana kallan Lulu.

"Toh.." Lulu ta faɗa tana miƙewa. Kai tsaye banɗakin tsakar gidan ta wuce bayan an kai mata kayanta. Ta yi wankan kuwa sosai ta shiryo sannan ta fito. A ɗakin Ummeeyn dai ta sake zama kamar yanda Ummeeyn ta mata umarni. Ba ta daɗe da zama ba Gwani ya shigo cikin ɗakin. Ta amsa sallamar da ya yi ƙasa_ƙasa sannan ta cigaba da zama kawai. Neman waje ya yi ya zauna yana danna wayarsa da alama wani abun yake dubawa me matuƙar amfani. Babu daɗewa Ummeey ta shigo cikin ɗakin ta nemi waje ta zauna.

"Afaaf ya kamata kuwa ki tashi ki je ɗaki ki ga kayan da aka kawo miki daga gidan.. Ɗazun nan aka zo aka miki jere cikin ɗakinki.." Ummeey ta ƙare tana murmushi cike da fatan Lulun ta saki jiki da ita kar ta ɗauketa a matsayin suruka. Kallanta Lulu ta yi duk da ta fahimci abin da Ummeeyn ke nufi amma kuma se hankalinta ya tafi wajen tunanin makomarta. Ta tabbata dai ba za bar gidan ba kenan, tun da ga shi har da yi mata jere cikin ɗakin Gwanin. Se kawai ta yi murmushin yaƙe tana faɗin

"Toh.." Daga haka ta miƙe.

"Toh se da safe kenan?" Ummeey ta tambaya.

"Ehh Ummeey.." ta yi ƙarfin halin faɗin sunan Ummeeyn. Wanda hakan ba ƙaramin farantawa Ummeeyn ya yi ba. Har se da ta yi murmushi sannan ta amsa da

"Toh Allah ya tashe mu lafiya.." da "Ameen" ta amsa tana ficewa daga ɗakin. Ummeey ta bita da kallo ganin daga Gwanin har ita Lulun babu wanda yace da ɗan uwansa uffan. Kar dai har yanzun a haka rayuwar tasu take babu wani cigaba? Ta tambayi kanta.

"Affan.."

"Na'am Ummeey." Ya amsa yana ɗaga kansa daga kan wayar ya kalleta.

"Ba ka jin bacci ne?"

"A'ah, akwai wani aiki ne da zan ƙarasa.."

"Toh Allah ya taimaka.." Ummeey ta faɗa tana sauke numfashi. Cikin zuciyarta tana addu'a a kan Gwanin da kuma Lulun.


... Cikin matuƙar farin ciki take kallan ko ina na cikin ɗakin lokacin da ta sake ƙyalƙyale shi, yanda ya yi matuƙar kyau kamar ba shi ba. Da ma kuma ga shi en Nepa sun bar wuta se ya kasance ɗakin ya haskaka ga wani ƙamshin furniture wanda ya haɗe da ƙamshin turare ɗan tsinke da Ummeey ta ba ta ta saka cikin ɗakin suke ta tashi gwanin daɗi. Murmushi kawai take saki saboda babu ƙarya ɗakin ya mata. Ta yi iya bakin ƙoƙarinta dan kar ta tuna da inda take. Se dai hakan ya citira. Dan kuwa cikin lokaci ƙanƙani zuciyarta ta soma kitsa mata gidan wanda take ciki har take farin ciki irin wannan. Cikin lokaci ƙanƙani gaba ɗaya annurin dake kan fuskarta ya ɗauke. Ta lumshe idanunta tana jin wata ƙwalla na taho mata. Se kawai ta sanya hannu ta ɗauketa tunawa da ta yi ba ta da wata mafita. Dan haka gwara ta bari kawai ta yi farin cikinta. Dan babu ƙarya kayan nan da Abba ya saka aka kawo mata ta mugun jin daɗinsu. Kuma za ta so ta samu damar yi masa godiya shi da Ammi. Kawai se ta sake yin murmushi lokacin da idanunta suka sake sauka kan gadon da ta gama gyarawa tass tass kamar ba hannu ne ya gyara ba. Ƙarasawa ta yi ta ɗauki zani da hijab ta shige banɗaki dan yin wanka. Ba ta wani ɗauki lokaci ba ta fito se ƙamshin sabulun Gwani me daɗi take yi. Kamar yanda ta saba yanzun ma a cikin banɗakin ta shirya duk da ba ya ɗakin sannan ta fito. Kai tsaye kan dadduma ta wuce ta yi sallahr isha'i da ba ta yi ba sannan ta yi addu'ointa kana ta miƙe dan komawa ta kwanta kan lafiyayyen gadonta da ta gama tamawa. Dan babu wai yau ɗin ta san za ta baje ta yi bacci cikin kwanciyar hankali. Se dai me?? Tana ida ninke daddumar ta juya da niyyar isa kan gadon ta kwanta se ganin shi ta yi zaune kan gadon yana buɗe Al_qur'an, da alama karatu ze yi. Wani irin ɓacin rai ta ji ya taso mata saboda sam ba ta yi tsammanin ganinsa a irin wannan lokacin ba. Se dai kuma se ta yi saurin kwaɓar kanta tuna kirkinsa gareta. Duk da haka dai ji take kamar ta buɗe baki tace ya tasar mata daga kan gado. Ba dan mutuncin da ya mata ba, ya ƙi sanar da Abba abin da ya faru, da kuma ɓoyewa kowa ma abin da ya faru ba da abin da ze fara fitowa daga bakinta shi ne ya tasar mata daga kan katifa tun da dai tata ce ba tasa ba. Se dai tun da ta san ba za ta iya faɗa ba a yanzu kam ya sanyata komawa gefen gadon ta nemi waje ta shimfiɗa daddumar ta zauna dan jiransa ya gama karatun ya koma inda yake kwana. Tun da dai tasa katifar ma yake bar mata ta kwana ballantana tata. Ba tare da ta kalle shi ba ta yi zamanta tana jiransa. Se dai jefi_jefi ta kan ɗaga kai ya kalle shi ko ya idar? Se ta ga ba haka ba. Sarai ya ganta, ya kuma fahimci abin da take jira amma ya basar ya cigaba da karatunsa. Shi da ya yi niyyar karanta izu ɗaya se ga shi har ya shiga izu na uku har kuma lokacin tana zaune. Zuwa lokacin har wani bacci bacci ya fara fuzgarta, amma har lokacin ba shi da niyyar tashi ya bata waje. Da dai ta fahimci be san zarau ba se kawai ta shiga ɓata rai tana wani ciccin magani gami hararar gefe, tun da dai ta san yanzu ba za ta iya masa tsiwar tata ba. Se da ya idar da karatun sannan ya buɗe wani littafi na addini ya shiga karantawa. Shi ne daidai lokacin da ya saci kallanta lokacin da take ta ciccin magani tana wani tura baki ita a lallai dole ya ɗaga mata katifa. Murmushi kawai ya yi dan shi dariya ma ta ba shi. Hakan kuma da take yi shi ke sanya shi ƙin tashi ya bata wajen. Ba ta ƙara minti 20 a haka ba wani nannauyan bacci ya saceta a inda take zaune. Se da ya gama muraja'ar inda ze yi sannan ya sake dubanta. Kanta na jingine da bangon bayanta tana bacci kamar ba ta da wata damuwa a rayuwarta. Numfashi take saukewa a hankali wanda hakan ze alamta maka yanda baccin nata ya yi nisa yake kuma mata daɗi. Ya ɗan furzar da iska yana ɗauke kansa daga kallanta. Har ya buɗe wani littafin da niyyar cigaba da karantawa se idanunsa suka sake kaiwa inda take zaune tana baccin. Ajje littafin ya yi a kan gadon ya miƙe a nutse zuwa inda take ɗin. Tsayawa ya yi na tsawon minti 2 yana kallan wani wajen kamar me tunani. Se kuma ya dawo da dubansa kanta still dai kamar me tunanin. Ranƙwafawa ya yi daidai lokacin da ya kai dukka hannayensa biyu inda take. Se kuma ya dakatar da hannun yana maida idanunsa kansu kamar me son ganin wani abu. Se kawai ya sake fesar da iska daga bakinsa kafin ya sake maida fuskarsa kanta. Babu ɓata lokaci ya saka hannayen nasa duka biyun ya ɗagata a hankali cike da fatan ka da ta farka. Dan ya san idan ta farka ɗin rigima ce za ta biyo baya. Shi kuma ya ji daɗin yanda ta koma a kwanakin nan kamar ba ita ba, kamar wadda aka chanjata. Cikin takatsantsan ya kwantar da ita a kan gadon bayan shi ma ya zauna inda ya tashi. Fahimtar da ya yi baccin nata ya yi nisa ne ya sanya shi saka hannu ya maido da kanta kan cinyarsa a nutse kuma cikin kula ya zame hijab ɗin dake jikinta har ƙasa kamar wadda za ta fita. Tana sanye cikin wata doguwar riga mara nauyi. Hannunta ba shi da tsayi, hakan ne ya baiwa fararen maidaidaitan hannayenta damar fitowa tun daga sama har ƙasa. Gashin kanta dake a tsefe yana ɗaure cikin wani ƙaramin ribbon. Se dai saboda yawansa da kuma tsayinsa kuma kasancewar babu ɗan kwali a kanta ya sanya yana ida cire mata hijab ɗin kwantaccen gashin kan nata ya samu masauki a kan cinyarsa. Be lura da hakan ba se shirin zameta da ya soma yi zuwa kan gadon. Cikin magagin bacci ta sanya tattausan hannunta ta gyarawa nasa hannun zama a kan cinyarsa gami da ɗora kanta a kai ta cigaba da baccinta. Binta ya yi da kallo kamar ba shi ba. Yanda take baccin ba ƙaramin wani shahararren kyau ta yi ba. Kamar wanda ake umarta se ya ji ya kaasa ɗauke idanunsa daga kan fuskar tata. Tsawon minti 1 yana kallan fuskar tata kafin zuciyarsa ta tunasar da shi abin da yake yi. Ya ɗan ja ƙaramin tsaki yana ɗauke kansa lokaci ɗaya kuma yana sauke wata ajiyar zuciya lokacin da bugun zuciyarsa ya sauya. Ɗayan hannun nasa ya kai saitin zuciyarsa cike da mamakin abin da ya sauya shi haka, har lokacin idanunsa a lumshe. Se da ya ji numfashin nasa ya saitu kamin ya buɗe idanun nasa. Ba tare da ya kalleta ba ya ja littafin ya soma karantawa. Se dai yanda take yawan gyara kwanciyarta tana kuma sake riƙe hannunsa ba tare da sanin abin

Please Login or Register in order to submit comment