Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuce zuwa inda ɗakin nasa yake. A nutse ta shiga knocking na ƙofar, kamar yanda take yi da, tana jin motsi ta soma ƙoƙarin ajjewa dan barin wajen. Se dai kafin ta kai ga aiwatar da hakan ya gama buɗe ƙofar. Ya maka mata wani kallo yana kallan abin da take ƙoƙarin yi

"Wace irin er qauye ce ke ne? A ko ina se kin nuna shi?" Ya ja tsaki yana yin baya kaɗan.

"Wuce.. ki ajje shi a wajensa.." ya yi maganar yana nuna mata wani keɓantaccen waje dake cikin ɗakin nasa, wanda da alama dama an tanadi wajen ne dan shan Coffee ɗin. Ko kallansa ba ta yi ba ta soma tafiya, duk da jikinta na rawa. Haka ta ƙarasa ta ajje Coffee ɗin duk a tsorace kamar wadda za a ce kett ta gudu. Ko bi ta kansa ba ta yi ba, duk da ma tun lokacin da ya mata maganar ba ta sake ganinsa ba. Ita dai hakan ba damuwarta ba ce, dan haka ta ɗaga en matan ƙafafunta ta fice daga ɗakin. Se da ya gama abin da ze yi sannan ya ƙaraso ya nemi waje ya zauna yana kallan Coffee ɗin. Babu ɓata lokaci ya ja shi ya shiga kaiwa bakinsa a nutse. Har wani lumshe idanu yake yi ba tare da ya sani ba. Har ya gama sha ji ya yi shi ya ma yi masa kaɗan, da so samu ne ya dinga samun ko da 2cups ne, se dai kuma ba ya buƙatar wata maganar ta sake shiga tsakaninsa da ita. Hakan ne ya sanya shi ɗaukar abin da ze ɗauka ya fice daga ɗakin.


.. Har wajen ƙarfe 9 na safe babu Didi babu dalilinta, ya yi tsammanin zuwanta tun ɗazu amma har yanzu shiru. Ya ja tsaki a karo na barkatai yana tunanin kalan rashin darajar da ze mata. Kenan iskanci ne ya hanata zuwa tunda dai har ya bada saƙo a bata, ita wace ce da ze sakata yin wani abu ta ƙi yi? Jinjina kai ya yi yana kama lips ɗinsa na ƙasa ya shigar da shi cikin bakinsa ya ɗan tauna yana neman waje ya zauna. A karo na babu adadi ya sake jan tsaki yana miƙewa a fusace ya fice daga ɗakin. Bin inda yake da tabbacin nan ne da mutum a ciki ya yi yana yatsine fuska. A nutse se dai cike da kuzari, mazantaka da kuma wani irin kyawu ko a tafiyar tasa ya shiga takawa zuwa ƙofar ɗakin. Babu jira ya saka hannunsa ya tura ƙofar ɗakin idanunsa a cikin ɗakin yana tunanin ta inda ze ganta. Tana kwance a kan gado ta ji motsin buɗe ƙofar ba kuma irin na Baba Atine ko Mommah ba. Hakan ne ya sanyata ɗagowa dan ganin wanda ya yi hakan. Tozali da shi da ta yi se da ya wani irin kaɗa mata 'ya'yan hanji, ta tashi zaune a zabure tana kallan yanda yake watsa mata wani irin kallo da ta gaza gane inda za ta ajje shi. Cigaba da takawa ya yi zuwa cikin ɗakin, ya yin da ta ji wani irin rauni ya ziyarceta. Se ta soma ƙoƙarin tashi a miliyan dan barin ɗakin, ya katseta da faɗin

"Hey young lady.. Me ke a cikin kanki? Kina da motsi ne?" Ya faɗa without minding yanda maganar za ta mata. Ita ba ma ta wani fahimci abin da ya faɗa ba saboda ruɗewa da ganinsa cikin ɗakin, abin da ba ta taɓa gani ba.

"Am i ur mate?" Ya tambaya yana kallanta. Da sauri ta jinjina kai tana jiran jin abin da ze sake fitowa daga cikin bakinsa.

"Me ya hana ki kawo min Coffee?" Inda inda ta soma yi dan ba ta da amsar bayarwa, dan kuwa tana sane ta ƙi yi ba tare da wani dalili ba. Kafin tace komai yace

"Kafin lokacin zamanki ya ƙare a gidan nan zan faɗa miki abin da za ki dinga yi.." ya ɗan dakata a nan, lumsassun idanunsa sun ɗan sake lumshewa kamar me jin bacci

"Ƙarfe 8 ki tabbatar kin kawo na safe.. And na dare ma hakan take.. Idan kika kuma yin tsallake ba ki yi ba wallahi zan fito miki na nuna miki waye ni.. Kin ji?" Ya ƙare da sigar tambaya. Da sauri Didi ta jinjina kai dan kasancewarsa a wajen duk shi ne ya ruɗata. Ga yanda yake magana kamar ze kai mata duka. Ita ta kasa gane dalilin da yasa har yanzu idan ta ji muryarsa se ta ji tana mata kama da wata muryar, amma har yanzu ta kasa ganewa. Bata ankara ba se nemarsa ta yi cikin ɗakin ta rasa har ya fice.

"Wayyo Allah na.." ta faɗa tana dafe ƙirjinta. A fili ta cigaba da faɗin

"Da kana jin daɗinsa amma girman kai ya hanaka faɗa? Yacin da ba ka faɗa ba se dai ka bushe ba zan kuma yi ba." Ta ƙare tana murguɗa baki.


... "Ka yi haƙuri Hero ina ganin kawai mu ƙare wannan harkar yanzun nan, na gaji wallahi. Na gaji da saka kuɗina da amfani da jikina duk dan ganin na samu yarinyar nan, amma kullum sake yin wani abun da ze nisantani da ita ne ke faruwa."

"Kin ga ki fito min a mutum kawai.. me kike nufi?" Ya tambaya yana kallanta da wani irin kallo.

"Na haƙura. Ba zan iya cigaba da wannan harkar ba. Ka yi haƙuri kawai.." Dariyar yaƙe Hero ya yi yana kallanta hannunsa a kan gemunsa yana shafawa.

"Kike cewa me? Kwantar da hankalinki.. ko da kin rabu da wannan maganar tana nan tare dake, don wallahi ba ki isa ki bar ni a ruwa ni kaɗai ba. Se da na gama yin burgima na yi nashe_nashe cikin wannan harƙallar sannan za ki ce kin haƙura? Yanda aka farata dake har kika janyo ni cikinta, haka za a cigaba da tafiya. Kin saka na rungume yarinya babu gaira babu dalili, na ɓata da abokina duk a kan ki, kin saka na yadda an haɗa baki da ni wajen ɓatawa yarinyar nan suna. Sannan kuma yanzu ki zo ki ce min kin haƙura? Ba ki isa ba wallahi, idan kuma ba haka ba uban kowa ma ya mutu.. wallahi ki tabbatar duk lokacin da lamarin nan ya caɓe ki shirya karɓar gaba ɗaya laifukan da na aikata, dan kuwa wallahi babu abin da ya dame ni tona miki asiri zan yi, kar ki wani duba muna mutunci, babu ruwana.."


A yi manage da wannan pls ☹️ wallahi bacci nake ji.☹️


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO40*


__Tsayawa Ladi ta yi tana kallan Hero jin abin da ya faɗa. Kafin ta kai ga cewa komai ya sake faɗin

"Tabbatar min da da gasken kike kin haƙura?" Ya yi maganar yana kallanta. Gyara zamanta ta yi tace bayan ta sauke ajiyar zuciya

"Ya zan yi Hero? Wallahi da gaske na haƙura.. Idan kuma za ka sama min damar da zan je har cikin gidan nata toh hakan ya min. Tunda dai na ga ba fitowa za ta yi ba. Bar wannan ma idan ta fito ɗin abin da nake tsarawa be yiwu ba fa?" Ta ƙare da sigar tambaya. Dariyar gefen baki ya yi duk da a fusace yake yace

"Kin ɗauka ni yaron ki ne ko Ladi? Wallahi daga yau na gama yi miki aiki.. A je a kin haƙuran, se anjima." Daga haka ya juya ya fice daga cikin ɗakin. Binsa ta yi da kallo kamar za ta bi shi ta masa magana se kuma ta fasa, dan idan ita ze nunawa duniyanci ita ma gwana ce a wajen, dan za ta iya cewa ita degree ne ma da ita a wannan fannin. Hakan ne ya sanyata jan tsaki a fili ta furta

"Ka daɗe ba ka yi fushin ba.. Haba.." ta ƙare tana tauna chewing gum ɗin bakinta yana ba da sautin "ƙaras"


... Ko da ta idar da Sallah kai tsaye banɗakin ta faɗa ta yi wanka da ruwan da ta jona a heater. Har zuwa lokacin ta kasa dena tunanin abin da ya faru, ta kasa dena tunanin wanda ya aikata mata haka, ta kuma kasa dena kuka, wanda shi ne musabbabin saka mata ciwon kan da ta tashi da shi. Har zuwa lokacin da ta gama shiryawa be shigo ɗakin ba, karon farko ta ji ya kamata ta fita ta je ta gaida Ummeey ba se ya sakata ta yi hakan ba. Dan haka se ta fice zuwa ɗakin Ummeeyn tana ɗan lumshe idanunta saboda ciwon da kanta yake mata, ga shi kuma har lokacin cikinta be dena mata ciwo ba. Cikin siririyar dashashshiyar muryarta ta yi sallama cikin ɗakin, Ummeey da Gwani suka amsa sallamar tata. Ƙarasawa ta yi ta nemi waje ta zauna a hankali tace kanta a ƙasa

"Barka da wannan lokaci.."

"Barka dai ɗiyata.. ya jikin naki?" Ummeey ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi.

"Alhamdulillah.." Lulu ta amsa da hakan. Haka kawai ya tsinci kansa da mamakinta, wanda har se da ya kalleta kamar me son gane da gasken ita ce? Se dai be ƙare mamakin ba, ya tsinto muryarta tana faɗin

"Ina kwana?" Ta faɗa a raunane cike da matsananciyar kunya. Dan tunda ta zo gidan ba ta taɓa ko da kuskuren gaishe da shi ba. Se dai yau ɗin se ta kasa yin shiru, ta kasa ɗauke kai ba tare da ta gaishe shi ba. Cigaba ya yi da kallanta da mamaki kwance a kan fuskarsa. Se dai tuna a inda suke ya sanya shi amsa gaisuwar tata lokaci ɗaya yana miƙewa.

"Ka tashi kenan?" Ummeey ta tambaya tana kallansa.

"Ehh.. bari na je" ya bata amsa.

"Toh ba damuwa.." Ummeey ta faɗa, shi kuma ya fice daga ɗakin.

Yau ɗin kawai se ta ji tana son cigaba da zama a ɗakin Ummeeyn, hakan ne ya sanyata cigaba da zama har kusan azahar. Se dai har zuwa lokacin ta kasa saka komai a bakinta. Hankalinta gaba ɗaya ya ƙi kwanciya har lokacin, so take ta ji Gwani yace mata ya binciko gaskiyar al'amarin nan. Ba ta jin idan dai har hakan be faru ba hankalinta ze iya kwanciya.

Wajen ƙarfe 3 Ummeey ta shigo ɗakin, ta ƙarasa ta buɗe kwanan da ta zubo mata shinkafa da miya. Kamar yanda ta tsammata kuwa yana nan yanda yake ba a taɓa komai ba.

"Afaaf.." Ummeey ta kira sunanta tana kallanta. Idanunta dake a lumshe ta buɗe lokacin da suka chanja kala.

"Subhanallahi.. jikin ne dai?" Ummeey ta faɗa tana matsowa kusa da ita. Jinjina kai kawai ta yi saboda yanda kanta ke wani irin juyawa. Taɓa jikinta Ummeey ta yi ta ji zafi zau, ta girgiza kai tana faɗin

"Ya salaam.. Sannu kin ji. Tashi mu je ɗakin naki ai akwai maganin da kuka siyo jiya." Ummeey ta yi maganar kamar tambaya se dai ba jiran amsar Lulun take yi ba. Kwata kwata jikinta babu ƙwari, hakan ne ya sa se da Ummeey ta kamata sannan ta miƙar da ita. Kai tsaye ɗakin Gwanin ta nufa har lokacin riƙe take da hannunta. A kan gadon ta zaunar da ita tana ta jera mata uban sannu, ita kam Lulu babu baki, gaba ɗaya ya mutu. Zamewa ta yi ta kwanta a kan gadon saboda duk da yanda take a zaune amma jiri take ji. Duba maganin Ummeey ta yi ta ɗakko shi, ta fito da shi. Ta fita ta ɗebo ruwa sannan ta dawo dan ɓallo mata ta sha. Se dai tana duba fuskar Lulun se ta ga har bacci ya ɗauketa. Tausayinta ya kamata, ta girgiza kai tana faɗin

"Allah sarki.." Se kawai ta ajje maganin ta ja mata zanin gadon ta lulluɓeta da shi sannan ta fice daga ɗakin.


.. "Yarinyar nan ba ta da lafiya Affan. Ka tabbatar ta ci abinci sannan ta sha magani.. Zazzaɓi ne ya kamata da sauri haka, idan akwai maganinsa cikin na jiyan da ka siyo se ka ba ta. Idan kuma babu zuwa safiya se a maidata asibitin.."

"Toh Ummeey." Ya faɗa yana soma takawa.

"Amm ba ka ji ba?" Ummeey ta faɗa tana kallansa. Se ya dawo yana faɗin

"Na'am.."

"Ya kamata idan ta samu sauƙi ka kaita ta leƙa ko da er uwarta ne, za ta ji daɗi."

"In Sha Allah.."

"Allah ya ba da lafiya.. Ameen." Daga haka ya wuce ɗakin nasa.

A nutse ya saka hannu ya yaye labulen idanunsa a kan gadon. Tana kwance tana baccin da be daɗe da ɗaukarta ba tun bayan da ta farka ta yi Sallah. Ya ƙarasa ya nemi gefen gadon ya zauna, kansa a ƙasa ya faɗa duniyar tunanin da yanzun ta zama abokiyarsa. Ya kai wajen minti 2 zaune a hakan kafin ya soma jin tarinta. Da sauri ya juya yana kallanta lokacin da take ƙoƙarin tashi hannunta a kanta da har lokacin yake juya mata. Miƙewa ya yi se dai be yi yunƙurin yin wani abu ba ganin da ya yi ta ma tashi zaunen da kanta. Yamutsa fuska take yi se dai ba za ka gane kuka take yi ba se ka kalli fuskarta ka ga hawayen da ke zuba a kan fuskarta. Kwata kwata baccin ya ƙi ɗaukarta yanzu, ta rasa yanda za ta yi. Gaba ɗaya ji take kamar an sauyata. Sam ba ta san da shigowarsa ba se lokacin da ta ji muryarsa yana faɗin

"Ya kike jin jikin naki?" Ya tambaya yana kallanta. Da sauri ta kalle shi ba tare da ta shirya ba. Se kuma ta yi saurin ɗauke kan nata tana faɗin

"Ba sauƙi.." Ta faɗa tana cigaba da yamutsa fuska. Murmushi ya suɓuce masa ba tare da ya shirya ba. Ya ɗan girgiza kansa yana faɗin

"Kukan fa?" Ba ta ba shi amsa ba se shirin komawa kwanciyar da ta yi. Ya yi saurin faɗin

"Kar ki kwanta.." ya yi maganar yana ƙarasawa inda ya ga ledar magangunanta ya ɗauko. Sannan ya ja abincin da Ummeey ta kawo ya matso da shi gabanta. Neman waje ya yi ya zauna a kan bedside drawer bayan ya matso da ita kusa da gadon. Ba tare da ya kalleta ba ya soma fito da maganin. Ita kam Lulu da ko ƙamshin maganin ta tsana har idanunta sun sake tara sabuwar ƙwalla. Ɗagowar da ze yi ya kalleta ya ga tana girgiza kai tana kallansa fuskar nan a narke kamar ba Lulu ba. Ɗaga mata kai ya yi alamar "Lafiya?" Da sauri kuwa ta buɗe baki tace

"Wallahi ba na son magani.. Ba na so wallahi.." Ta faɗa daidai lokacin da wasu hawaye suka zubo a kan fuskarta. Ɗan lumshe idanunsa ya yi yana miƙewa yace bayan ya sake matsar da abincin kusa da ita.

"Ni ma ba magani na ce ki sha ba. Maza ki ci abinci.." Ya yi maganar yana nuna mata abincin. Girgiza kai nan ma ta yi tace

"A ƙoshe nake.." ta faɗa da sauri. Shi ma girgiza kan ya yi sannan yace

"Ba ki ƙoshi ba. Ko ki ci abincin nan ko kuma ki sha maganin."

"Don Allah ka yi haƙuri wallahi duka ba na so. Bakina babu daɗi, kuma so nake na kwanta." Ta yi maganar tana lumshe idanunta da suka janye saboda ciwon kan.

"Maganin kike so kenan?" Ya tambaya yana kallanta, be jira amsarta ba yace

"Well.." Se ya yi maganar yana soma ɓallo maganin daga cikin gidansa. Kamar za ta saka ihu haka ta ji, ji take kamar ta ƙyale shi ta yi kwanciyarta, se dai ba ta jin za ta iya aikata hakan. Dan haka se janyo abincin kawai ta yi ta shiga kaiwa bakinta ba tare da tana bari ta tauna ba, ita dai kawai dan ya ga ta ci abincin ya ƙyaleta, ya dena mata zancen maganin da tun kafin ta kai shi bakinta take jin kamar ta yi amai. Babu laifi ta ci abincin duk da kawai turawa take yi dan ba za ta iya cewa ga ɗanɗanonsa ba. Se dai tun kafin ta kai ga shan ruwa ta ji gaba ɗaya abincin na neman dawo mata. Hakan ne ya sanyata ƙoƙarin miƙewa. Se dai tana yin ƙoƙarin miƙewar se kuwa ta yi luuu ta koma tana shirin zubewa, ya yi saurin saka hannunsa ya riƙota. Idanunta gaba ɗaya a rufe suke saboda yanda take jin gaba ɗaya garin na juya mata kamar ze faɗo mata a kai, ga kuma Jikinta dake rawa bayan wani mummunan zafi da ya ɗauka. Yanda ya riƙota ɗin ya sanya suka ɗan samu kusanci, wanda hakan ya janyo har hucin zazzafan numfashin da take fitarwa yana iya ji. Tunda ta yi ƙoƙarin faɗuwar nan se ta kasa miƙewa duk da yanda har lokacin take jin aman na taho mata amma ta kasa wani yunƙuri. Se cigaba da kakarin da ta yi, sam be fahimci abin da take ƙoƙarin yi ba, se ƙoƙarin ajjeta da ya fara yi a kan gadon, ba tare da ta shirya ba gaba ɗaya abincin da ta ci ya dawo, cikin rashin sa'a kuma rabinsa duka ya sauka ne a jikin Gwani.

"Ya ilahy.." ya furta a kan laɓɓansa yana kallan yanda ta ɓata shi da kuma ƙasan gadon. Se kuma ta koma sauke numfashi tana girgiza kai saboda yanda take jin jikinta kamar ana sassara mata shi. Se kuma ta ɗan buɗe idanunta da ƙyar ta kalle shi daidai lokacin da yace

"Tashi ki je ki gyara jikin ki.." ya faɗa ba tare da ya sake kallan jikinsa ba. Ya kuma faɗa ne kawae duk da a yanda take ya san ba za ta iya wani tashi ta je ta gyara jikin nata ba. Cigaba ta yi da kallansa ta yi tunanin ze rufeta da faɗa ne ko kuma wani abun makamancin hakan, se dai ga mamakinta se ta ji be damu da abin da ta masa ɗin ba face faɗa mata da yake yi ta je ta gyara jikinta.

"Ka yi haƙuri don Allah.." ta yi ƙarfin halin faɗar hakan. Idanunsa ya sanya cikin nata, sannan ya lumshe su lokaci ɗaya yana jinjina kansa. Gane abin da yake nufi ya sanyata sauke ajiyar zuciya. Se ta fara ƙoƙarin tashi idanunta a rufe saboda tsoro take ji, dan idan a buɗe idanun suke ba za ta iya ko da ƙoƙarin ba ne. Ganin yanda take tangaɗi kamar wata er maye ya sanya shi kawai saka hannunsa ya riƙota. Taimaka mata ya yi zuwa banɗakin duk da yanda take ta noƙewa da nufin ya barta za ta iya kai kanta. Amma sanin da ya yi ba iyawar za ta yi ba ya sanya shi ƙyaleta har se da ya kaita banɗakin. Yana shirin juyawa dan ficewa ya tuna shi ma fa jikinsa a ɓace yake. Duk da haka dai se ya fice ɗin kawai. A bakin ƙofar ya tsaya yana tsumayin fitowarta. Se dai kafin lokacin ya saka hannunsa ya cire rigar jikinsa da ta ɓaci ya musanyata da wata kafin ta fito. Se da ya shafe wajen minti 5 a tsaye amma har zuwa lokacin ba ta fito ba. Ya ɗan gyara tsayuwarsa yana cigaba da jiran fitowar tata. Se dai har zuwa bayan wasu mintuna ba ta fito ba. A hankali ya matsa bakin toilet ɗin se dai ga mamakinsa tana zaune hannunta dafe da kanta.

"Ya Allah!" Ya faɗa yana ɗan cije gefen lips ɗinsa na ƙasa. Kamar ba wani abun ze yi ba ya ɗan ƙara tsayawa na tsawon sakanni sannan ya ƙarasa cikin toilet ɗin. Sam ba ta san da shigowarsa ba har se da ta ji hannunsa ɗore a kan hijab ɗinta lokaci ɗaya kuma yana faɗin

"Daure ki tashi.." Ya yi maganar babu yabo babu fallasa kuma a hankali. Se ta ɗaga kai da sauri a kuma tsorace. Se dai yanda kanta ya sara ya sanyata saurin runtse idanunta. Da hakan ya yi amfani da hannunsa wajen soma ƙoƙarin yaye hijab ɗin jikinta da shi ne ya ɓaci. A tsorace duk da yanda take jin jikinta ta yi ƙarfin halin danne hijab ɗin da hannunta tana girgiza kai, jajayen idanunta cike da hawaye. Iska ya ɗan fesar daga bakinsa sannan ya ɗan girgiza mata kai shi ma fuskarsa babu yabo babu fallasa. Ganin da ya yi ba ta da niyyar barinsa ya yi abin da ya soma, kuma ya gaji da jiran nata ya sanya shi saka hannunsa ya ɗauke nata hannun da ta danne hijab ɗin. Babu ɓata lokaci kuma ya yaye hijab ɗin gaba ɗaya. Kawai se ta fashe da kuka tana yin ƙasa da kanta. Shi ko bi ta kanta ma be yi ba se jefa hijab ɗin da ya yi cikin wani bokiti sannan ya ɗauki ruwa a buta ya sake matsawa kusa da ita. Duk da yanda take kukan, tana kuma jin tsoron yi masa rashin kunya saboda kirkinsa gareta da kansa ya gyara mata jikin nata. Sannan ya haɗa da hijab ɗin nata da rigarsa ya wanke su tass ba tare da jin wani ƙyashi ba. Se da ya gama wanke duka sannan ya fitar da su ya shanya kana ya dawo cikin ɗakin. Zuwa lokacin har ta kwanta ta lulluɓe jikinta, dan ko tashi ta je ta ɗauki wani hijab ɗin kasawa ta yi. Tsayawa ya yi yana kallanta ta cikin abin lulluɓar, ganin yanda ta takure waje ɗaya kamar munafuka. A nutse ya ƙarasa ya kalli fuskarta da ta yi mugun fayau kamar wadda ta yi wata da watanni tana ciwo. Ya ɗan lumshe idanunsa yana jin ya zama dole gobe ya kaita asibiti ko da allura ne su mata se tafi mata sauƙi a kan maganin. A hankali ya kai hannunsa kan wuyanta ya ɗan taɓa, fiye da ɗazu ma yanzu jikin ya sake yin zau kamar garwashi. Ya sauke ajiyar zuciya yana ɗakko wayarsa daga aljihu ya kalla sannan ya maidata, se kuma ya soma takawa ya bar wajen. Bayan wajen minti 2 ya dawo hannunsa ɗauke da wani ƙaramin towel. Kai tsaye kan bedside drawer ɗin nan ya sake zama, a hankali yace

"Afaaf.." Duk da ta ji shi saboda ba bacci take ba, amma ba ta da ƙarfin amsa masa. Jin da ya yi shiru ne ya sanya shi sake maimaita sunan nata da a bakinsa yake fita na daban. Motsawa kaɗan ta yi se dai har lokacin idanunta a rufe suke. Miƙewa ya yi a hankali ya nemi gefen gadon ya zauna ya yaye abun da ta lulluɓa da shi ɗin. Yanda take cure a waje ɗaya ne ya sanya shi se da ya ɗagota sannan ya soma saka mata towel ɗin da ya jiƙa shi da ruwa me ɗan sanyin hankali. Bugun da zuciyarta ke yi ne ya ƙaru, ta yi ƙoƙarin tashi se dai ta san yaudarar kanta take yi ba iyawa za ta yi ba. Gaba ɗaya jikinta zafi, har wani huci ke fita idan ta yi nishi. A wuyanta ya soma dandala mata towel ɗin, daidai lokacin da ta yi ƙarfin halin komawa baya ko da faɗawa ne kan gadon ta yi, ita dai ta dena jinta a jikinsa. Ɗan ƙaramin tsaki ya yi yana sake riƙeta sosai. Ya cigaba da abin da yake yi. Da dai ta ga ta kasa yin komai se kawai ta haƙura ta cigaba da kukan da shi ne mafita kawai. Har kuma lokacin zuciyarta ba ta dena bugawa da sauri ba. Shi da yake dab da ita har iya jiyo bugun zuciyarta yake yi. Gaba ɗaya a rikice take, a kuma tsorace take. Zazzafan numfashinta dake sauka a jikinsa ya nemi saukar masa da kasala, se dai be bi ta kan hakan ba ya cigaba da abin da yake yi yana ɗan ɓata ransa. Se da ya tabbatar jikin nata ya ɗan lafa daga ɗaukar zafin da ya yi sannan ya ajje towel ɗin. Ya san idan dai har ya ƙyaleta sake lulluɓar za ta yi ba tare da ta damu da zafin da jikinta ya yi ba. Kamar ya rabu da ita, se kuma ya kasa tafiya. Se yake ji kamar idan ya tafi ɗin be yi adalci ba.

"Don Allah ka ƙyale ni.. ka sake ni.." ta faɗa da dashashshiyar muryarta hawaye na zuba daga gefen idanunta dake a lumshe. Kallan fuskar tata ya yi se ya ji wani abu na son ɗarsuwa a cikin ransa, ya yi saurin kawar da shi yana fidda iska daga bakinsa. Kamar ba ze ce komai ba se kuma ya buɗe baki kamar ba ya son yin maganar yace

"Ki yi baccin ki.." ya faɗa yana gyara

Please Login or Register in order to submit comment