Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ajje kwalbar a gefensa yana buɗe lumsassun idanunsa da suka yi jajur kamar garwashi. Wani kalar lumshewa suke yi da kansu kamar wanda yake sane yake yi. Be tsammaci ganin Mommahn a irin wannan lokacin ba, dan haka da sauri ya gyara zamansa, ya tashi zaune daga kishingiɗen da yake ya sake sauke idanunsa a kan Mommah. Cikin dakushashshiyar muryarsa ya buɗe baki da ƙyar yace

"Mommah..." Ya ƙare yana lumshe idanunsa.

"Me kake yi haka Areef?" Ta yi ƙarfin halin tambayarsa idanunta a kansa cike da tsoro. Ya san Mommahn ta riga ta gan shi babu wani ɓoye_ɓoye. Ko da ma ba ta gan shi ba waɗannan kwalaben da ke zube sun isa su nuna abin da yake yi. Mommahn ta fahimci abin da yake yi ta tambaya ne kawai dan tabbatarwa. Se dai kuma a wanne hali za ta tsinci kanta bayan ta ji da gasken wani abun yake sha. Shin ya za ta ji ranar da ta gano ɗanta kuma ta same shi mashayin giya? An ya kuwa ya yi wa Mommahn adalci? Ya tambayi kansa. Kawai se ya girgiza kai, yana sake jin yanda ƙirjinsa ke masa zafin da har yanzun ya ƙi raguwa.

"Mommah na kasa jurewa.. na kasa jurewa, zuciyata zafi take min Mommah.. Idan ban sha wani abun ba zuciyata za ta iya tarwatsewa."

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.." Shi ne kaɗai abin da Mommah ke maimaitawa hawaye na cigaba da zuba a kan fuskarta, ƙirjinta na bugawar da ya zarce ƙa'ida fiye da tunani. Da gasken kenan giya yake sha? Tsawon wane lokaci ya ɗauka yana sha se yanzu ta sani? Wace irin rayuwa Areef ɗin yake? Shin tsawon wane lokaci ya ɗauka yana wannan ɗab'iar? Mom ta sani? Idan ta sani ya aka yi ba ta tsawatar masa ba? Idan kuma ba ta sani ba ya aka yi ta yi sake hakan ya faru, duk da yanda take nuna kamar ta fi kowa iya kula da ɗa? Shin wacce irin ɗab'ia Areef ɗin ke da ita saboda samun sakacin kulawar uwa? Shaye_shaye? Shaye_shaye a cikin gida ba tare da kowa ya sani ba? Shaye_shaye a matsayinsa na musulmi me ilimin addini? Shin me ya kamata ta yi a irin wannan lokaci. Se ta shiga girgiza kai tana jin wani jiri na kwasarta, wanda ke barazanar kayar da ita. Haka ta daure ta ja jikinta da ƙyar ta nemi waje ta zauna gefen gadon. Ta ɗaga jajayen idanunta ta kalle shi, muryarta na rawa tace

"Areef..." Se ta kasa furta komai dan tsananin tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki.

"Ki yi haƙuri Mommah.. Ba na shan me bugarwa.. ina sha ne kawai dan na saba da rayuwa da ita tun a U.S."

"U.S" Mom ta maimaita tana kafe shi da idanunta. Maganar da ya faɗa yanzun ita ce ta sake ɗaga mata hankali, yana sha ne dan ya saba rayuwa da ita. Kenan duk tsawon rayuwarsa yana sha ko kuwa me yake nufi? Kawai se ta kifa kanta a kan hannunta wasu hawaye masu ɗumi suka shiga zubowa a kan kuncinta. A kan laɓɓanta ta shiga maimaita

"Hasbunahallahu wa ni'imal wakeel.."



✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO68*

___ Runtse idanunsa ya yi yana sake kifa kansa jikin gadon zuciyarsa na zafi. Mommah sam ta kasa furta komai, ban da tsoro da kuma faɗuwar gaba da take ji ta kasa cewa komai saboda tsananin tashin hankali. A hankali ya buɗe idanunsa ya sake kallan Mommah, cikin shaƙaƙƙiyar muryarsa ya furta

"Mommah.. Ki dena kukan please.." Se a lokacin sannan ta iya ɗaga kanta ta kalle shi. Ita kaɗai ta san abin da take ji cikin zuciyarta a halin yanzu.

"Da ma rayuwar da ka ɗaukarwa kanka kenan?" Ta yi maganar a sanyaye tana goge hawayen fuskarta. Se ya girgiza kai yana sake buɗe idanunsa da ke lumshewa da kansu.

"Mommah na kasa jurewa ne wallahi. Na kasa jure yanda na zauna tsawon shekaru ina matsayin ɗan macuciya, azzaluma kuma mara imani.. Na kasa jure yanda na shafe tsayin shekaru tare da ke ina miki kallan kishiyar uwata.. Duk yanda na so mantawa da hakan na kasa, duk yanda na so in kawo walwala ta maye gurbin ɓacin ran hakan ya citira. Damuwa na neman yi min yawa Mommah.." Ya ƙare muryarsa a raunane kamar ba ta shi ba.

"Shin ba ka san Alqur'ani shi ne kaɗai maganin damuwa ba? Irin wannan damuwar da kake magana a kai ba ka san ka ɗauki Qur'ani ka karanta ba Areef? Wace irin rayuwa ce wannan ka ɗaukarwa kanka? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un..." Ta ƙarasa faɗa tana riƙo kanta da ke sara mata. Kawai ta kasa yadda ba mafarki take yi ba. Wai Areef, ɗanta ke shaye shaye. Wannan wace irin baƙar rana ce?

"Ki yi haƙuri Mommah.. Kar ya zamana ranar farin ciki kuma ta koma ta baƙin ciki.." Ya yi maganar kamar ba shi ba. Se ka ce chanja shi a ka yi gaba ɗaya.

"Ba ka so hakan ta faru amma kake shan wani abu Areef?" Mommah ta yi ƙarfin halin faɗin hakan. Se ya girgiza kai kawai yana sake lumshe ido saboda yanda wani bacci me daɗi ya soma fuzgar shi wanda hakan da ya tilastawa idanunsa sake ƙanƙancewa.
Ga kuma tausayin Mommahn da ya kama shi. Yanda duk ta ruɗe lokaci guda, yanayinta gaba ɗaya ya chanja, muryarta ta sauya, haka zalika komai nata ma ya chanja. Abubuwa da dama sun haɗar mata a yau ɗin. Ga wannan labarin da ya zo mata a bazata, ga kuma kama Areef ɗin da ta yi yana shan wani abun. Sun kai wajen minti 3 babu wanda ya sake cewa uffan, kowa da abin da ke saƙawa cikin ransa. Can Mommah ta miƙe jikinta a matuƙar sanyaye. Ta kwashi kwalaben tana jin wani irin ɗaci har a cikin bakinta, ta wuce da su toilet. Babu jimawa ta fito, da alama kuma ta kasa daurewa se da hawaye suka tarar mata. Ta yi saurin kawar da su tana kallansa a kaikaice tace

"Ka shiga ka watsa ruwa yanzun nan ka fito ina jiranka." Mommah ta faɗa tana ƙoƙarin juyawa. Lura da wani siririn hawaye da ya yi a kan fuskarta shi ne ya sanya shi sake buɗe baki a sanyaye yace

"Ki yi haƙuri Mommah.." Kawai se ta fice da sauri ba tare da tace komai ba. A iya yau ɗin abubuwa sun faru da dama. Ita ba fushi take da Bad Man ba, dan ta san rashin kulawar uwa ya yi matuƙar taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwarsa. Dan haka ba za ta yi wannan kuskuren a yanzu haka ba. Tun farko Mom ce ta jawo, dagewa da ta yi se an tura shi ƙasar waje ya taimaka ƙwarai, tun da ga shi nan be fara shan komai ba se da ya bar ƙasar. Shi ya sa ashe tun lokacin da za a tura shi wata ƙasar ta ji hankalinta be kwanta ba, ta ji ina ma za ta iya faɗawa Mom ɗin gaskiya, da ta ce mata kar ta bar Areef ɗin ya bar gabanta. Ta gefe guda kuma har yanzu ta kasa gane duk ina tulin masu tsaro da Daddy ya tura masa? Ba su san yana sha ba ne ko kuwa ya ya? Su da aka tura kula da shi, da duk wani abu da yake yi, ya aka yi har ya fara shan wani abu ba su sani ba? An ya kuwa hakan za ta faru? Amma kuma idan sun sani ɗin ya aka yi ba su sanarwa da Daddy ba? Ire_iren wannan tunanin ke ta mata yawo a kwanya. "Ya zama dole na bincika abin da ya faru." Ta tsara hakan cikin zuciyarta. Hannu Mommah ta saka ta kamo na Didi ba tare da tace komai ba ta jata zuwa kan kujera ta zaunar. Babu musu Didi ta zauna, ya yin da Little ya ɗora hannunsa a kan cinyarta.

"Kalle ni nan Afrah.." Mommah ta faɗa tana kallanta. Babu musu ta kalli Mommahn cike da mamakin abin da za ta faɗa mata. Se dai tambayar da Mommahn ta mata ita ce ta sanyata ƙamewa a wajen ta rasa abin da za tace

"Faɗa min halayen Areef da kika sani kin ji?" Ita ce tambayar da Mommahn ta mata. Ta ɗauki kusan minti 1 ba tare da tace komai ba. Se kame_kame kawai da take, daga zarar ta kamo can se ta kamo nan. Amma takamaimai ta rasa abin da za ta faɗa.

"Kin ga kwantar da hankalinki Afrah.. Kin san dai yanzu ni mahaifiyar Areef ce.. Ke kuma na ɗauke ki ne tamkar 'yata.. toh idan dai har kin ɗauke ni a matsayin uwa ki buɗe baki ki faɗa min gaskiya.." Haba, komai rashin kirkinta ai ta yi wa Mommahn kara, tun da komai lalacewar Bad Man ai dai ɗanta ne. Ba kuma za ta so ta buɗe abin da yake a rufe ba. Dan haka a sanyaye tace

"Yana da kirki.." Tun kafin ta kai ƙarshe Mommah ta shiga girgiza kai. Ta ɗan yi murmushi duk da har lokacin ba ta gama komawa daidai ba tun shigarta ɗakin Bad Man.

"Ki faɗa min gaskiya Daughter.. Amma tabbas ba haka ne a ranki ba.." Kawai se ta yi ƙasa da kanta ta rasa abin da za ta ce. Dan ba ƙarya Mommahn ta kasheta da jijiyoyin jikinta. Ajiyar zuciya Mommah ta sauke jin da ta yi Didin ta kasa cewa komai. Ta ɗan lumshe idanunta kafin ta buɗe. Cikin ƙarfin hali, da kokawa da zuciyarta da ke bugawa tace

"Kin san Areef na shan wani abu ne?" Babu shiri Didi ta ɗaga kai ta kalli Mommah cike da mamaki. Ya aka yi ta sani? Waye ya faɗa mata? Ta tambayi kanta.

"Uhmm?? Kar ki ɓoye min komai.." Mommah ta sake faɗa. Runtse idanunta ta yi tana jin yanda jikinta ke rawa kamar wata mara gaskiya. Se kawai ta jinjina kai kafin cikin ƙarfin hali ta soma faɗin

"Ehh Mommah.. Na yi ƙoƙarin barin abun a zuciyata ne ba tare da na faɗawa kowa ba, in yi maganin abun kuma ni kaɗai da yaddar Allah. Ba zan iya tunkarar Mom in faɗa mata abin da ke faruwa ba, ba kuma zan iya faɗa miki ba saboda kamar na tona masa asiri ne bayan babu wanda ya sani. Shi ya sa na cigaba da ƙoƙarin ganin ya dena, amma hakan ya citira. " Shiru Mommah ta yi tana kallanta, lokaci ɗaya tana jin wata ƙaunarta har cikin ranta. Lallai Didin ita ce matar da ya kamata a zauna da ita. Didin ita ce matar nan da ake kira da matar rufin asiri. Yanzu da wata ce aka mata auren haɗi ta fahimci mijin na shaye shaye, ai da tuni mutanen duniya sun ji. Amma ita ta zaɓi ta yi shiru, ba tare da ta sanarwa da kowa ba. Lallai ta cancanci yabo na musamman.

"Allah Ya yi miki albarka Daughter.." Mommah ta faɗa bayan ta rungumeta cike da farin cikin samun sirika kamar Didi. Sanye cikin ƙananan kaya ya fito kamar kodayaushe. Tafiyarsa ta sake zama nutsattstsiya me burgewa. A haka ya ƙaraso inda su Mommahn suke. Sam ya kasa haɗa ido da Mommahn, dan haka ba tare da ya kalleta ba yace

"Mommah na fito.."

"Je ka, ga mu nan zuwa.." Mommah ta ba shi amsa tana miƙewa ita ma ba ta kalle shi ba. Be sake cewa uffan ba ya fice daga ɗakin.


... Har cikin gidan marayun Daddy da kansa ya yi parking na motarsa. Ya juya ya kalli Mommah da tun ɗazun ya lura da idanunta da suka yi ja yace

"Kukan kuma na mene ne?" Se ta girgiza kai da sauri, dan ba ta so Daddyn ya gano abin da ke faruwa. So take ta yi amfani da wasu dabarorin nata ta yi maganin Bad Man ɗin. Sam kuma ya dena shan komai gaba ɗaya da yaddar Allah.

"Babu komai Yallaɓai.." Se da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ɗauki waya ya kira wata number. Tsawon minti 1 suna magana kafin ya ajje wayar. Cikin ƙanƙanin lokaci se ga wasu mutane 2 sun zo. Ɗaya ya saka hannu ya buɗewa Daddy ƙofar motar. Babu musu ya fito. Se a lokacin Mommah, Bad Man da kuma Didi, se kuma Little da ke hannun Bad Man suka sauko daga cikin motar. Babu ɓata lokaci aka ɗauke su zuwa cikin wani ɗaki. Babu wanda ke cewa da ɗan uwansa uffan, dan kuwa kowa da abin da yake saƙawa a ransa.


"Barka da zuwa Yallaɓai.." Wani babban mutum ya faɗa yana kallan Daddy. Murmushi Daddy ya yi yana faɗin

"Barka dai." Ya yi maganar hawa kan kujera ya zauna. Se da ya zauna sannan aka baiwa su Mommah kujeru su ma suka zauna.

"Ina jinka Yallaɓai.." Wanda ke zaune kan kujera ya faɗa yana kallan Daddy. Se da Daddy ya gyara zama sannan ya soma faɗin

"Wani taimako nake so ka mana.. duk da na san an fara maka bayani.. Amma idan ka ji daga bakina se yafi.. A ranar 1 ga watan june..." Daga nan Daddy ya sanar da shi kwanan watan da su Mommah suka haihu, da kuma duk wani abu da ya kamata su ji wanda ze ba su haske a kan neman jaririn da aka yar a ranar. Jinjina kai dattijon mutumin ya shiga yi bayan da ya gama jin bayanin Daddy. Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace

"Wato ze iya zama a ga yaron har a ɗauke shi a kawo shi cikin gidan nan.. Se dai ba ni da tabbas, amma zan saka a dubo files ɗin ranar. Dan kuwa duk yaron da aka kawo yana da file, idan da rabon an kawo shi ɗin za ku iya samunsa cikin gidan nan ko kuma wajen masu karɓar yara idan suna buƙata.."

"Toh godiya nake.."

"Babu damuwa.. Ai ka fi ƙarfin haka Alhaji.. Kawai dai se kun ɗan yi haƙuri saboda abun ne da yawa.. Ka ga shekarun suna da yawa."

"Babu damuwa.. Idan dai har za a gani za mu iya jira.." In ji Daddy. Se a lokacin Mommah ta sauke ajiyar zuciya dan ita ma abin da za ta faɗa kenan Daddy ya rigata. Se suka cigaba da zama jiran wanda ya tafi binciko files ɗin.



... Fitowarta daga wanka kenan, ta ƙarasa ta buɗe wardrobe ta ɗauki wani riga da skirt na wani material me kyau ta saka. Se da ta gama shiryawa tsaff sannan ta nufi ɗakin nan. Se ta shiga duddubawa kamar me neman wani abun. Se dai tunanin abin da za ta ɗora take yi. Dan har cikin ranta take jin rashin dacewar barin Ummeey ta cigaba da yin girki cikin gidan, duk da dai ita ke zuwa ta tayata. Amma yau ɗin haka nan ta tashi da niyyar ɗora wani abun da za su ci. Kai tsaye gas ta kunna ta ɗora girkin. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa wani irin ƙamshi me daɗi ya baɗaɗe ɗakin. Ba ta san dalilin da ya sa ta ji sam ƙamshin be mata ba. Duk se ranta ya ɓaci tana ganin ga shi ta yi girki amma kuma da alama ba ze yi daɗi ba, dan kuwa ƙamshin da girkin ke yi irin me ɗaga zuciyar nan ne. Ta ɗan ja numfashi tana sake dubawa ko dai ba ta kula ba ta saka wani abun da be kamata ba? Jin da gaske dai sam ƙamshin be mata ba ya sanyata ficewa daga ɗakin tana ɓata rai. Neman waje ta yi ta zauna a gefen gado har lokacin ji take kamar ta yi kuka. Ta cigaba da sauke ajiyar zuciya a hankali. Daidai lokacin Gwani ya yi sallama cikin ɗakin, ƙamshin da ya fara dakar masa hanci shi ne ya tilasta masa lumshe idanunsa. A hankali ya ƙarasa cikin ɗakin idanunsa a kanta. Ba ƙaramin kyau ta yi masa ba. Musamman da ya kasance yau babu wannan hijab ɗin, se ɗan kwalin material ɗin da ta sake shi ba ta ɗaura ba. Ya ɗan lumshe idanunsa yana murmushi, daidai lokacin da ta ɗago kanta ta kalle shi saboda jin alamar ido da ta yi a kanta, dan sam ba ta ji sallamarsa ba, ta faɗa can wata duniyar.

"Sannu da gida.." Ya yi maganar yana kallanta dai. Be yi tunanin amsarta ba, ko kuma dai be yi tunanin za ta amsa da

"Sannu da zuwa.." ba. Ta faɗa tana miƙewa. Se ya saka hannunsa ya riƙo hannunta ya juyo da ita tana kallansa.

"Ina za ki je?"

"Wajen Ummeey zan je fa.." Ta ba shi amsa da sauri tana yamutsa fuska.

"Yanzu duk wannan ƙamshin da nake ji haka za ki tafi ki bar ni ba tare da kin sammun ba? Toh a taimaka a sammun na ɗanɗana.." Ya yi maganar a narke kamar wani maraya, kai ba za ka ce Gwani ba ne. Ba ta san lokacin da ta ɗaga kai ta kalle shi ba. Ya langaɓar da kansa gefe kamar me neman taimako. Wallahi ba ta san lokacin da dariya ta suɓuce mata ba saboda da gasken gaske ya bata dariya sosai. Ya lumshe idanunsa yana jin wani irin sanyi na ratsa shi. Wannan murmushin nata kaɗai abun farin ciki ne a wajensa, ya kuma ƙawatar, ya kuma ƙarawa kyakkyawar fuskarta kyau. Se a lokacin da ya buɗe idanunsa sannan ta tuna abin da ta yi. Ta yi saurin maida fuskarta yanda take tana yin baya saboda ya cika mata hannu.

"Zan samu abincin?" Ya sake katseta da faɗin hakan. Se kawai ta kafe shi da idanu kamar ba ita ba. Ita mamaki abun ya bata, ta ya ya ma ze ce wannan ƙamshin ne ya masa daɗi? Ƙamshin da ke neman sakata kasa zama cikin ɗakin? Ko dai ya faɗa ne kawai dan ta ji daɗi? Ita dai har ga Allah ba ta so yace ba ta iya girki ba dan yau an samu tangarɗa. Yanda kuma ya yi mata maganar se ta kasa bijirewa. Kamar tace masa ta cinye se kawai ta yi shahada ta ƙarasa ɗakin. Zuwa lokacin ƙamshin ya ɗan yi ƙasa ba kamar ɗazu ba. Amma duk da haka ita tashin zuciya ma take ji. Haka dai ta daure da sauri da sauri ta zuba abincin cikin flask. Ta ɗauko plate da spoon ta fito daga ciki. A karo na barkatai wani murmushi ya ƙara suɓuce masa. A kan laɓɓansa ya furta

"Ubangiji Ya ƙara gyara tsakaninmu. Ya kuma ƙara shirya min ke." Ya faɗa dan har ga Allah yana jin daɗin chanjawar Lulun fiye da zaton me zato. Kuma da alama kamar abun kullum gaba yake yi. Har gabansa ta ƙaraso ta ajje abin da ta ɗakko ɗin sannan ta juya ta fice daga ɗakin, dan tabbas idan ta cigaba da zama wannan ƙamshin ze sanyata amayar da abin da ke cikinta. Kuma ko babu komai gwara ya faɗi ko ma meye a kan abincin ba a gabanta ba. Da dai ya kushe girkinta a gabanta, gwara a bayan idanunta. Kai tsaye ɗakin Ummeey ta wuce. Da sallama ta shiga. Amsa sallamarta Ummeey ta yi tana kallan ƙofar ɗakin. Fuskarta ɗauke da murmushi take faɗin

"'Yata ke ce?" Se da Lulu ta yi murmushi sannan tace

"Ehh Ummeey.."

"Toh maraba.." Ta yi maganar tana gyara tabarmar da take kai. Neman waje Lulu ta yi ta zauna, suka sake gaisawa da Ummeeyn. Daga haka ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba. Se Ummeey ke ɗan jefo hira kaɗan kaɗan. Zuwa can dai da Lulu ta gaji, ga yunwa da take ji ya sanyata gyara zama. Ta ɗan ja numfashi kafin tace

"Ummeey babu yaɗiya?" Ta faɗa har a cikin idanunta tana tuna yaɗiyar nan ta Ummeey me ɗan karen daɗi. Murmushi Ummeey ta yi sannan tace

"Yaɗiya kike so Afaaf?" Da sauri ta jinjina kai hadda wani haɗiye yawu kafin ta amsa da

"Ehh Ummeeey.."

"Toh yi zamanki a nan.. Yanzun nan Malam ya shigo da ita, kin san da yake gwaninta ne, bari na kwaɗa muku.." Murmushi ta yi har haƙoranta na bayyana sannan ta amsa da

"Toh Ummeey.." Daga haka Ummeey ta fice daga ɗakin.

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO69*


___ A ɗaya ɓangaren kuwa bayan shuɗewar mintuna masu yawa se ga mutumin da ya fita daga ɗakin ɗazun ya sake shigowa hannunsa ɗauke da wasu files da yawa. Kai tsaye zuwa ya yi ya ajje su a gaban dattijon mutumin nan sannan ya fita daga ɗakin.

"Toh bari na duba.. Allah Ya sa a dace.."

"Ameen.." Dukkansu suka amsa da hakan. Se a lokacin Bad Man ya nemi waje ya zauna, ya lumshe idanunsa ya buɗe a lokaci guda. Hannunsa duka biyun ya haɗe waje ɗaya ya shiga jijjigasu. Shi kansa a yanzu haka ba shi da buri da ya wuce ya ga twin brother ɗin na shi. Ya gan shi a raye cikin ƙoshin lafiya idan ya so sa yi farin cikin gaba ɗaya. Dan kuwa har yanzu be gama komawa daidai ba. Daga zarar ya yi shiru se ya tuna abin da ya faru. Shi kaɗai ya san irin adadin tsanar Mom da duk wani da ya shafeta da yake ji a yanzu haka. A hankali ya shiga duba files ɗin. Kowanne cikinsu kallansa yake yi yana addu'a cikin zuciyarsa. Ya kai wajen minti 10 yana dubawa kafin ya ɗaga kai yana kallansu cike da tausayawa. Se da ya koma ya zauna a inda ya tashi sannan yace

"Ku yi haƙuri Yallaɓai.. Amma na duba files ɗin nan babu wani da ke nuni da ko da makamancin abin da ya faru ne a ranar.. Duka nan kawo su aka yi daga wani wajen, mutum biyu kuma tsintarsu aka yi.. Amma babu wanda aka tsinta a ƙofar gidan nan.."

"Ya ilahy.." Daddy shi kaɗai ya iya ƙarfin halin faɗar hakan. Se da ya sauke ajiyar zuciya sannan yace

"Kuma ka duba sosai?" Jinjina kai ya yi dan tabbatarwa da Daddyn abin da ze faɗa kafin yace

"Ƙwarai kuwa Yallaɓai... Amma kuma ina tunanin ko ba nan aka ce muku ba?" Girgiza kai Daddy ya yi kamin yace

"A'ah dan waje kam tabbas nan ne.. Se dai..." Sallamar mutumin nan da ya kawo files ɗazu ita ta dakatar da Daddy daga maganar da ya soma. Ya ƙaraso ɗauke da wani file guda ɗaya a hannunsa, ya miƙa masa yace

"Ga wani ma na ranar ne.." Karɓa ya yi yana faɗin

"Sannu da ƙoƙari." Daga haka ya fice daga ɗakin. Gaba ɗaya hankalinsu se ya koma kan file ɗin. Kusan dukansu ji suke kamar su ce ya basu su duba da kansu. Se dai suka cigaba da zuba na mujiya cike da fatan jin alkhairi.

"Yess!! Yallaɓai tabbas wannan ya yi daidai da abin da kuka faɗa.. Ƙwarai ma kuwa.." Ya faɗa har lokacin kansa na kan file ɗin se dai da murmushi kan fuskarsa.

"Alhamdulillah.." Suka haɗa baki wajen faɗin hakan. Mommah ji take kamar ta yi magana ta tambayi inda ɗanta yake tun da an gano file ɗin, dan har yanzu hankalinta a tashe yake. Se dai ta bari ta yi shiru ta cigaba da saurarar abin da ze faru.

"Kar ku damu, In Sha Allah kun samu ɗanku kun gama.. Amma dai gaskiya ina tunanin..." Se kuma ya yi shiru be ƙarasa ba, ya miƙe ya fita daga ɗakin. Runtse idanunta Mommah ta yi tana jin faɗuwar gaba, kawai se ta bar idanunta a rufe, ta shiga karanto duk addu'ar da ta zo bakinta tana kuma roƙon Allah a kan ya bayyana mata ɗanta, dan haka kawai ta ji jikinta ya yi sanyi da maganar mutumin. Gyarawa Little da ke bacci kwanciya Bad Man ya yi yana furzar da iska daga bakinsa. Me yake nufi da maganarsa ta ƙarshe?.

Bayan kusan minti 20 se ga mutumin ya dawo, har lokacin suna zaune suna jiransa. Dukansu suka ɗaga kai suka kalle shi. Ya ƙaraso ya zauna, ya kalli Alhaji Matawalle yace

"Yallaɓai Alhamdulillah Alhamdulillah..." Tun kafin su ji me ze ce Bad Man da Mommah suka sauke ajiyar zuciya kusan a tare.

"Wato cikin yaddar Ubangiji yaronka yana nan a raye har yanzun.. Tun ranar da aka tsince shi, wani bawan Allah ya zo nan da matarsa da nufin suna neman ɗa, kasancewar matarsa ba ta haihuwa.. Toh da yake dai Allah Ya ƙaddara ɗanku ze rena se aka ba su shi.. Kuma cikin yaddar Allah har yanzu yana can tare da su.."

"Allah na gode maka.. Allah Ka ƙarawa Annabi daraja." Mommah ta faɗa sanda ta runtse idanunta tsananin farin ciki na ratsata.

"Lallai

Please Login or Register in order to submit comment