Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tsananta. Abeey ba lafiya? Ba ɗazun nan ya baro gidan ya same shi ƙalau ba? Ko da ma ba shi da lafiya ne be sanar da shi ba? Me ye ke damun Abeeyn? Dukka waɗannan tambayoyin suke yawo cikin ƙwaƙwalwarsa. Ya yi ƙoƙarin saita nutsuwarsa, muryarsa har ɗan rawa take yi lokacin da ya furta

"Me ke damunsa Ummeey?" Tun lokacin da ta shigo take kallansa, kai tsaye wajensa ta nufa. Ta kalle shi yanda ta ga cikin ƙanƙanin lokaci yanayinsa ya chanja. Ita kanta se da ta ji faɗuwar gaba ta zo mata. Se kawai ta cigaba da kallansa a ranta tana fatan Allah Ya sa lafiya.



✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO81*


___ A sukwane ya sauke wayar daga kunnensa. Ta sake kallansa tana jin ƙirjinta na bugawa da ɗan ƙarfi. Jira take ta ji me ze ce, se dai da alama ba shi da niyyar cewa komai. Dalili kenan da ya sanyata faɗin

"Me ya faru?" Ta tambaya cike da fargaba tana sake jin faɗuwar gaba na zo mata. Se da ya sauke numfashi kafin yace a hankali.

"Abeey ne ba lafiya."

"Subhanallahi.. me ke damunsa?" Girgiza kai ya yi lokaci ɗaya yana jefa wayarsa cikin aljihu kafin yace

"Ba na ce ba.. Bari dai kawai na tafi.." Ya ƙare yana duba gefe ko da akwai abin da ze ɗauka. A gaggauce ya miƙe kuma ba tare da ya sake cewa komai ba ya zo ze fice. Ba ta san lokacin da ta riƙo hannunsa ba. Ya dakata yana juyawa ya kalleta. Duk ta yi wani sanyi, se ka ce mara lafiya. Yanda ya gantan duk a dame, ya kuma san hakan na da nasaba da yanayin da ta gan shi ne ya tilasta masa kai hannunsa kan nata hannun ya kalmashe su waje ɗaya. Ya yi ƙoƙarin wanzar da murmushi a kan fuskarsa kafin yace

"Kar ki damu Uhmmm?" Maƙe kafaɗa ta yi tana kwaɓe fuska kamar me shirin yin kuka. Dan ita dai har ga Allah ba ta san irin wannan yanayin da ta gan shi ciki. Be san lokacin da ya lumshe idanunsa ba, lokaci ɗaya sanyi da kuma fargabar halin da ze je ya samu Abeey suka dirar masa. Lallai se yanzu ne ya san ya yi aure, se yanzu ne ya san yana da mata.

"Ɗauko hijab ɗinki mu wuce.." Ya faɗa dan yana ganin wannan ce kaɗai hanyar da ta dace. Se kuwa ta sake shi da sauri. Ta ƙarasa wardrobe ta buɗe ta ɗauki wani dogon jalbab kala me kyau ta saka. Tsayawa ya yi kawai yana kallanta gaba ɗaya hankalinsa na gida. Dan da hankalinsa na nan da kansa ze zaɓa mata, har ma ya saka mata duk da ya san ƙilan ta yi ta zillewa.


... Se da ta bari ya idar da karatun da yake yi, ya ajje Alqur'anin a inda ya dace kafin ta kalle shi ta yi murmushi a nutse tace

"Yallaɓai.."

"Yallaɓiya uwar en biyu." Ya ƙare yana murmushi. Ita ma murmushin ta yi kafin tace

"Ya karatun?"

"Alhamdulillah.." Ya faɗa yana gyara zamansa ya koma yana kallanta, kamar ya san dama muhimmiyar magana ce ta kawota.

"Wato Yallaɓai da ma wata magana ce ta kawo ni."

"Toh ina jinki." Se da Mommah ta sauke ajiyar zuciya kafin tace

"Waɗanda suka zauna tare da Areef a U.S da kuma waɗanda ke kula da sauran al'amuransa na gida nake so a sallama idan babu damuwa." Da mamaki sosai Daddy ke kallan Mommahn, dan ba su taɓa ko makamanciyar wannan maganar ce da ita ba.

"Kora? Da kanki?" Ya yi tambayar still yana kallanta. Se ta jinjina kai kafin ta ɗan sauke numfashi

"Ehh.."

"Allah Ya sa lafiya.. Duk da dai kin kai ki yi abin da kike so cikin gidan nan, se dai wannan ɗin abu ne me muhimmanci, dan haka zan so in ji dalilinki na faɗin hakan.. Wani abu ya faru ne?" Ya faɗa cike da fatan ba wani abu ne babba ba. Se da Mommah ta gyara zama tana tunanin ta inda za ta fara. Se da ta ɗauki wajen minti 1 ba tare da tace komai ba kafin ta soma faɗin

"Babu amfanin cigaba da zama da su.. sun ci amanarka Rankayadaɗe.." Daga nan ta shiga sanar da shi abubuwan da suka faru, da irin gwagwarmayar da suka sha wajen ganin sun ƙwato Areef ɗin daga halayyar da ya jefa kansa ciki. Da taimakon Ubangiji kuwa se ga shi ya dena ɗin. Hannu Daddy ya kai ya sauke hular kansa ya ajjeta a gefe.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel.." Abin da ya din ga maimaitawa kenan yana jin yanda ilahirin jikinsa ya yi mugun sanyi.

"Kar ka ɗaga hankalinka Yallaɓai.. Komai ya daidaita da izinin Ubangiji. Ban ma so bari ka sani ba saboda sanin halinka, dan dai ka nemi da ka sani ɗin ne ya sa na sanar da kai. Don Allah kar ka saka damuwa a ranka." Girgiza kai Daddy ya yi kafin ya sauke dogon numfashi. Ya yi murmushin yaƙe sannan yace

"Allah Ya kyauta.." Ya yi maganar yana ƙoƙarin miƙewa. Da sauri Mommah ta katse shi, ta hanyar faɗin

"A'ah don Allah.. Da na san haka ne ai da ban faɗa maka ba." Mommah ta faɗa yanayin fuskarta na sauyawa. Se ya koma ya zauna yana faɗin

"Ina tunanin abin da ya kamata na yi ne. Ashe yanzu duk yaddar da na ba su se da suka ci amanata? Me ye amfanin zuwansu kenan? Duk zaman nan da suka yi babu wanda ya taɓa buɗar baki yace ga abin da Areef ke yi. Se ga shi yanzu abin da nake ji.. Kaii!!" Ya ƙare yana dafe kansa.

"Ka yi haƙuri.. In Sha Allah komai ya wuce Uhmmm?" Ɗaga kansa ya yi kafin yace

"Allah Ya yadda.. Ya ƙara shirya mana su dukansu. Su kuma duk za su haɗu da ni ne." Ya ƙare maganar a ransa yana tunanin abin da ya kamata ya yi musu.


.. Lokacin da Gwani da Lulu suka isa gidan a kwance sosai suka tarar da Abeey, wanda har hakan ya so baiwa Gwani tsoro. Dan haka cikin ƙanƙanin lokaci ya ɗauki Abeeyn se asibiti. Babu ɓata lokaci aka ba shi taimakon gaggawa, aka kuma yi masa duk abin da ya dace. Kiran Daddy da ya gani cikin wayarsa shi ne abin da ya sanya shi komawa ya zauna. Ya ɗaga wayar yana karawa a kunnensa.

"Barka da wannan lokaci Daddy."

"Barka dai Son.. Ka na cikin gida ne?" Se da ya kalli Ummeey da Lulu ke kusa da ita kafin ya girgiza kai

"A'ah muna asibiti."

"Subhanallahi.. waye ba lafiya?" Daddy ya tambaya cike da mamaki.

"Abeey ne.." Ya bayar da amsar kansa na kallan ƙasan tiles ɗin asibitin.

"Ya ilahy! Da ma ba shi da lafiya ne?" Se da Gwani ya sauke ajiyar zuciya kafin yace

"Eh toh.. Daddy da ma dai yana fama da rashin lafiyar ne, ga kuma ciwon ƙoda.. Wani lokacin jikin kan motsa ba ma tare da kowa ya sani ba. Se dai a wannan karon abin ya kai shi ƙasa ne, se da ya kayar da shi."

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!" Daddy ya faɗa muryarsa na bayyana damuwar da ya tsinci kansa ciki bayan jin abin da ya faru.

"Amma kuma shi ne ba ka sanar da ni ba tuntuni?"

"Daddy ban ɗauka.."

"Idan dai har ba kare kanka za ka yi ba, ba na buƙatar jin wani abu daga bakinka." Daddy ya katse Gwani da faɗin hakan. Se ya kama bakinsa ya tsuke har se da Daddyn ya kai ƙarshe kafin ya amsa da

"A yi haƙuri Daddy." Ajiyar zuciya Daddy ya sauke kana yace

"Shi kenan, zan shigo an jima za mu yi magana."

"Allah Ya kai mu, Ya kawoka lafiya."

"Ameen." Daddy ya amsa da hakan yana ajje wayar.


.. A ɗaya ɓangaren kuwa yana ganin fitowar Lulun ya miƙe ya shige ɗakin. A kan kujera ya hangi Didin zaune. Ya fesar da iska daga bakinsa kafin yace bayan ya sauke ajiyar zuciya

"Thank God." Ya faɗa yana ƙarasawa cikin ɗakin.

"Awwwn, that's my baby gurl.." Ya ƙare yana neman waje ya zauna inda ya zamana yana kallanta ne tana kallansa. Ba ta san da shigowarsa ba se maganarsa kawai da ta ji. Abin da ya bata tsoro kenan, ta ɗaga kai ta kalle shi da sauri, se kuma ta sauke ajiyar zuciya dan har ga Allah ta tsorata.

"Kaina bisa wuyana." Ya faɗa yana ɗan marairaice fuska kamar ƙaramin yaron da ya yi laifi ya tuba. A hankali ya miƙe ya ƙarasa ƙasan kujerar da take kai ya ɗan leƙa fuskarta, cikin basarwa yace

"Kin ji sauƙi ne Babe? Ko dai in duba ki..?" Se kuma yanzun ya ƙare maganar yana ɗan kwaɓe fuska. Haɗa idanun da suka yi ne ya sanyata saurin ɗora kanta a kan kafaɗarsa da ta fi kusa da ita tana rufe idanunta cikin kunyar da ta ƙi sakinta. Fara alamun kukan shagwaɓar da ya ji ta soma yi ne still kuma kanta na kan kafaɗarsa ya sanya shi saurin faɗin

"Yi haƙuri na dena.. Uhmmm?" Ya faɗa yana ƙunshe dariyarsa. Gefe guda kuma yana jin daɗin yanda ya ganta, da alama ta ji daɗin jikinta. Hannu ya saka ya ɗago kan nata. Ya miƙe ya koma kan kujerar kusa da ita ya zauna. A hankali ya jata da niyyar kwantar da ita a jikinsa, ta zille tana maƙe kanta a kan kafaɗarta gami da ja baya. Dariya ta so ba shi, dan ya gane abin da take nufi. Dan kuwa da gaske tsoro take ji kar daga haka a sake maimaita abin da ya faru. Hannu ya sake miƙa mata yana motsa kansa alamar ta taho. Se ta sake kauda kai tana ma ƙoƙarin tashi gaba ɗaya. Da sauri ya riƙo hannunta yana faɗin

"Afuwan Sweerie.. Na yi alƙawarin babu abin da zan miki.. Runguma ce fa kawai." Ya ƙare maganar a marairaice yana langaɓar da kai. Ita dai har ga Allah ta gaji, so take ta sake jinta a kwance, da ma ta zauna ne saboda zuwan Lulu.

"Ni dai.." Ta faɗa tana fakar idanunsa da niyyar miƙewa. Ya yi saurin sanya hannunsa ya jawota, gaba ɗaya se gata ta dawo jikinsa babu tsammani. Ta yi kane-kane a kan faffaɗan ƙirjinsa. Hakan ne kuma ya ba shi damar gyara mata kwanciyar yanda za ta ji daɗi, ya rungumeta gam gam yanda ma ba za ta yi ko da yunƙurin tashi ba ne. Haka tana ji tana gani ta haƙura. Se kawai ta yi shiru tana sauraran bugun zuciyarsu dake fita kusan a tare. Ganin yanda ta ke ta ɗan gyara kwanciyar ne ya sanya shi faɗin

"Wani abu na miki ciwo ne?" Ya tambaya cike da kulawa. Runtse idanunta ta yi kamar yana kallanta. Ta girgiza kai ba tare da tace komai ba. Lura da abin da ta yi ne ya sanya shi faɗin

"Kin tabbatar? Idan akwai don Allah ki sanar da ni." Ya ƙare yana kallan tsakiyar kanta da ke kwance a ƙirjinsa. Nan ma jinjina kai kawai ta yi, ya cije lips ɗinsa kafin yace

"Idan fa ba ki buɗe baki ba zan duba ne in tabbatar.. Ni ban fahimci abin da kike nufi ba, lafiyarki kuma na da matuƙar muhimmanci a wajena." Jin ya ƙarasa maganar yana sassauta riƙon da ya mata ne ya sanyata saurin faɗin ba tare da ta shirya ba, dan ta san ba ƙaramin aikinsa ba ne ya aikata abin da ya yi niyya.

"Eh, na warke fa.." Ta ƙare tana turo baki kamar za ta fashe. Wata miskilar dariya ce ta ƙwace masa. Be ce komai ba se shafa sumar kansa da ya yi har lokacin murmushi ya ƙi barin fuskarsa. Tana jinsa lokacin da ya ɗauki hannayenta ya zagaya da su bayansa. Se kawai ta sake su, ta dai cigaba da kwanciya a jikin nasa.

"Idan fa ba ki yi abin da nake so ba toh ni zan.." Ya ƙare yana ƙoƙarin birkitota. Babu shiri ta yi saurin rungume shi. Ya lumshe idanunsa yana komawa ya baje a kan kujerar har lokacin idanunsa a lumshe. Cikin lokaci ƙanƙani wani daddaɗan bacci ya yi awon gaba da kowannensu.



.. A ranar kuwa kamar yanda Daddy ya alƙawarta se ga shi cikin asibitin. Se da ya je ya duba Abeey kafin suka dawo suka zauna dan yin magana da Gwani. Sake tattaunawa suka yi a kan rashin lafiyar Abeeyn kafin daga bisani Daddy yace

"Yanda na yanke, ina ganin tun da har da ma za su je Saudiyya, na kuma amince da ƙwarewar likitocin asibitin da na taɓa zuwa shekarun baya, se ku je a duba lafiyar Malam sosai. In Sha Allah za a dace.." Cikin na'am da maganar Daddyn Gwani ya amsa da

"Allah Ya saka da alkhairi Abeey, Ya ƙara arziƙi me amfani." Murmushi kawai Daddy ya yi. Shi kam idan be yi wa su Abeey abu ba su wa ya kamata ya yi wa? Mutanen da suka renar masa ɗa tun yana jinjiri har girma. Lokacin da ya je wa da Ummeey da maganar Daddyn ba ƙaramin farin ciki ta yi ba. Ta shiga kwararowa Daddyn addu'o'i cike kuma da fatan Allah Ya sa a dace. Cikin ƙanƙanin lokaci Daddy ya shiga shirya musu tafiyar. Cikin haka ne kuma Mommah ta bayar da shawarar tafiya tare da Didi da Areef su ma su je su ziyarci ɗakin Allah, su kuma roƙawa Abeeyn lafiya. Gefe guda kuma kafin su dawo ginin gidan da ake musu duka ya kammala, an gama komai a tsanake. Idan ya so suna dawowa se su yi can ɗin. Su ma kuma su Ummeey su shige nasu gidan. Da ma tafiyar za a yita ne tare da Lulu tun da sai mijinta ma ze je. Shi kenan yanzu se su tafi gaba ɗaya. Sosai Daddy ya yi na'am da shawarar Mommahn, dan haka babu ɓata lokaci aka fara duk wasu shirye shiryen tafiyar har da su gaba ɗaya.


.. A ɓangarensu Mom kuwa ana can gidan yari an soma girbar abin da aka shuka, zuwa lokacin ta yi laushi matuƙa. Maimunatu kuwa da ma tuntuni ta tuba ta bi Allah. Wannan dalilin ne ma ya sa Daddy ya roƙa mata sassauci ko dan albarkacin tona wannan ɓoyayyan sirrin da ta yi, wanda idan ba dan Allah Ya sa ta tona ba, da tuni ba wannan zancen ake ba..


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO82*


___ Cikin ƙanƙanin lokaci suka cigaba da shirye-shiryen tafiya Saudiyyar. Ta gefe guda kuma har lokacin Abeey na asibiti ana cigaba da kula da lafiyarsa. Kwanakin da suka ɗauka na shirye shiryen cikin kuma kwanakin ne kowanne ya sake zage damtse wajen kula da matarsa. Hakan ne kuma dalili da ya sa shaƙuwa sosai ta shiga tsakaninsu. Musamman ta ɓangaren Gwani da Lulu, da yanzu ta gama bayar da kai bori ya hau. Ta saki jikinta ta maida hankali wajen kula da mijinta da yanzun take matuƙar ƙauna, shi ma kuma ta ɓangarensa hakan ne. Ɓangaren Bad Man da Didi ma sosai ake samun cigaba, musamman da ya kasance Bad Man ɗin ɗan soyayya ne. Kai idan yana wani abun se ka ɗauka ya taɓa samun wani horo ne na musamman a kan soyayya. Kulawa da kuma soyayyar da yake nuna mata ita ce silar da ta sa take iya ƙoƙarinta wajen ganin ta faranta masa, ta kuma saki jikinta gaba ɗaya da shi, tun da dai ta san tana ƙaunarsa. Musamman a kwanakin nan da ƙaunar tasa take ƙaruwa a cikin zuciyarta saboda tsananin kulawarsa gareta.


.. A compound ɗin gidan suka rabu da Kaseem, kai tsaye sashensu ya wuce. A gajiye yake liƙis, dan haka duk wani burinsa be wuce ya watsa ruwa a jikinsa ya zo ya baje ba. A nutse ya tura ƙofar ɗakin duk da baccin da yake ji amma idanunsa na cike da fatan ya ganta. Saboda tun safe ya fita daga gidan se yanzu ya shigo. A kishingiɗe ya sameta kan kujera tana bacci, hannunta ɗauke da littafi, da alama karatu take bacci ya ɗauketa. Ƙarasawa ya yi yana murmushi. A hankali ya saka hannunsa ya ɗagata gaba ɗaya ya maidata kan gado. A nutse ya kai bakinsa kan goshinta ya yi kissing. Kafin ya sauko da bakin nasa kan cute lips ɗinta da suka sake tsukewa saboda baccin da take. Sumbata me ɗan tsayi ya bawa bakin nata. Har se da hakan ya farkar da ita. Cikin kulawa da karyar da kai yace

"Tuba nake." Se ta tura red lips ɗin nata da ya sake yin ja saboda sumbatar da ya sha tana ɗan murza idanunta. Har ga Allah baccin ya mata daɗi. Ta ji daɗinsa, duk da ba tare da ta sani ba ya ɗauketa. Ganin da gasken bacci take ji, ya sanya shi miƙewa tsaye. Ya sake kallanta a nutse yace

"Baccin ne?" Jinjina kai ta yi tana sake lumshe idanunta kamar er maye. Kallanta ya yi sosai kafin yace

"Toh mu je ki samu ki watsa ruwa ke ma." Ya yi maganar ba tare da ya jira amsarta ba ya ɗauketa gaba ɗaya. Kai tsaye toilet ya wuce da ita, ya kulle ƙofar. Ganin da ya yi baccin da take ji ya fi nasa ya sanya shi sauƙaƙe mata wahala ya wanketa tass, kafin ya wanke kansa. Ai gaba ɗaya baccin ji ta yi ya tafi babu alamunsa. Dan kuwa ita dai har yanzu ta kasa sakin jikinta gaba ɗaya. Har yanzu wannan kunyar akwai ta. Dan haka yanzun ma ji ta yi kamar ta nutse dan kunya, musamman da ta ga yana abubuwansa ko a jikinsa shi kam. Se ita yake bari da kunya kullum. Ko da suka fito ma be ƙyaleta ba, duk da yanda take ta zillewa a kan za ta shirya da kanta, ya ƙi barinta se da ya shiryata tsaff cikin wata doguwar rigar bacci mara nauyi kamin yace yana kallanta

"Ni ba ki shirya ni ba." Ya ƙare maganar a marairaice se ka ce wani maraya. Ɗaga narkakkun idanunta ta yi ta kalle shi. Tilas murmushi ya suɓuce mata ta sunkuyar da kanta.

"In haƙura koh? Ni ba wanda ke sona." Ya sake marairaice murya fiye da ɗazun. Yanzu kam da sauri ta ɗaga idanunta ta kalle shi.

"A'ah fa ni dai ba.." Se kuma ta ƙi ƙarasawa. Jinjina mata kai ya yi sau ɗaya alamar ta ƙarasa. Se ta turo baki kawai ba tace komai ba. Kawai se ya yi murmushi yana girgiza kai. Duk wani ƙoƙari da ze yi se ya yi shi wannan kunyar ta ajjiyeta. Se da ya shirya tsaff cikin rigar bacci kafin ya dawo inda ya barta kamar saƙaguwa. Surarta ya yi zuwa kan gadon, ya kwantar. Kafin shi ma ya kwanta yana ɗan lumshe idanunsa jin baccin ya dawo. Ya ja ta cikin jikinsa ya rungume yana gyara kwanciyarsa yanda za ta ji daɗin kwanciyar kafin ya ja musu bargon ya lulluɓe su. Ya kai wajen minti 5 yana jin yanda bugun zuciyarsu ke fita a tare. Ya buɗe baki da niyyar yi mata magana, se ya lura da yanda numfashinta ke sauka a kan wuyansa a hankali. Da sauri ya leƙa fuskarta cike da mamaki, dan be yi tunanin a ɗan wannan lokacin har ta yi bacci ba. Se dai da alama ba ma yanzu ta yi baccin ba, kawai dai se yanzu ya yi nisa. Ya sake gyara mata kwanciyar kafin ya lumshe idanunsa shi ma.



... Kai tsaye palourn Mommah suka wuce, suna sanye cikin wata atamfa me kyau, ɗinkin riga da skirt. Sun yi mugun kyau, kamaninsu sun sake fitowa sosai musamman da suke cikin kaya iri ɗaya. Se dai yanzu kam a kallan farko za ka fahimci yanda Lulu ta fi Didi murjewar jiki. Dab da za su shiga ɗakin Mommahn Didi tace

"Allah kuwa Lulu yanzu kin zama er lukuta." Didi ta faɗa tana ɓoye dariyarta. Harara Lulu ta ɓalla mata kafin tace

"Wallahi ba wani nan." Ta faɗa tana tura bakinta gaba.

"Kin ga fa yanda kayan nan suka miki.. Chaɓɓ..!"

"Allah Didi ba na so.." Lulu ta katseta da faɗin hakan tana bubbuga ƙafa kamar za ta saka ihu. Se da Didi ta yi dariyarta kafin ta tsuke bakinta ta yi shiru. Kafin kuma tace

"Shi kenan, yi haƙuri." Didi ta faɗa. Maƙe kafaɗa Lulu ta yi ba tace komai ba. Didi ta langaɓar da kanta tana kama kunnenta, tace a marairaice

"Pls mana.." Se kuma Lulun ta yi murmushi kafin tace

"Na haƙura." A haka suka ƙarasa cikin ɗakin Mommahn. A palour suka sameta, tana magana da Baba Atine. Suka ƙarasa da sallama ɗauke a bakunansu. Da fara'a Mommah ta karɓe su, cike da jin daɗin zuwansu. Baba Atine ma miƙewa ta yi tana musu barka da zuwa. Suka amsa suna neman waje suka zauna. Se da suka gaisa da Baba Atine kafin ta yi sallama da uwar ɗakin nata ta fice daga ɗakin.

"Barkanku da zuwa.." Mommah ta sake faɗa da murmushi ɗauke a kan fuskarta. Kusan a tare suka amsa da

"Barka dai Mommah."

"Ya shirye shirye?" Ta tambaya tana kallansu.

"Alhamdulillah." Nan ma suka amsa a tare.

"Allah Ya taimaka, Ya nuna mana lokacin, Ya kai ku lafiya Ya kuma dawo mana da ku lafiya."

"Ameen." Maida dubanta kan Lulu Mommah ta yi tace cikin kulawa

"Ya jikin naki Daughter? Fatan dai babu abin da ke damunki?" Ɗan murmushi Lulu ta yi tana murza hannunta da ɗayan hannunta kafin tace

"Eh."

"Kin tabbatar?"

"Ehh Mommah." Ta ba ta amsa har lokacin ba ta kalleta ba. Mommah ta yi murmushi tana maida dubanta kan Didi.

"Afrah ya wajen naki? Ina fata dai babu matsala?" Ta yi tambayar da kodayaushe ba ta gajiya da yinta, kullum kuma cikin fatan amsar da za ta fito daga bakin Didin ta kasance "Ehh" ne.

"Ehh Mommah." Didi ta faɗi hakan. Murmushi Mommah ta yi kafin tace

"Toh madallah.." Daga haka se suka ɗan taɓa hira, har zuwa lokacin da Mommah ta umarce su suka fice daga ɗakin. Kai tsaye compound suka wuce driver ya ɗauke su zuwa gida, bayan Mommah ta bayar da saƙo a kai wa Ammi har ma da Little.

Ammi sam ba ta san da zuwansu ba, dan haka tana zaune cikin ɗaki ita da Little tana koya masa hadda, sallamar en biyun nata ta ratsa kunnenta. Kusan a tare suka ɗaga kai ita da Little suka kalle su. A guje Little ya sauka daga kan kujerar har yana ƙoƙarin kifawa ya ƙarasa ya rungume en uwan nasa.

"Didi.. Lulu.. Didi.. Lulu." Shi ne abin da yake ta faɗa cikin tsananin farin cikin ganinsu. Rungume shi suka yi a tare cike da kewarsa. Ita kanta Ammi murmushi ya ƙi barin fuskarta. Kallan 'ya'yan nata kawai take yi. Allah ne kaɗai ya san irin farin cikin da ta ji na ganinsu da ta yi. Sanda suka ƙaraso inda Ammi take, basu ɓata lokaci ba suka rungumeta. Tuni ƙwalla har ta cika idanun Ammi. Ta dai saurin maidata dan kar su ma ta karya musu zuciya.

"Ammi mun yi kewarki sosai." Didi ta faɗa. Lulu ta jinjina kai fuska a narke.

"Ni kaina yarana. Kun zo lafiya?" Ta tambaya cikin kulawa. Gaisawa sosai suka yi, shi dai Little ya yi shiru daga ya je jikin wannan, se ya koma jikin waccan. Ji yake kamar mafarki yake yau ma en uwansa ya sake ganinsu. Ga shi ma har sun dawo gida. Sosai yau ɗin ta kasance rana ta musamman a wajensu. Sun yi hira da Ammi sosai. Ta basu shawara, ta musu faɗa, ta kuma fahimci abubuwa da dama. Ciki kuwa har da cikin da Lulu ke ɗauke da shi. Ba su suka buɗi baki suka sanar da ita ba, amma duk wata alama ta me ciki ta gama bayyana a tattare da Lulun. Ga shi kuma ba ta iya cin dambun da Ammin da kanta ta tashi ta shirya musu ba, se da aka dafa mata wani abincin daban kafin ta iya ci. Ammi ta lumshe idanunta har cikin ranta tana jin farin ciki, musamman da ta ga alamar komai ya daidaitu tsakanin 'ya'yan nata da mazajensu. Se dai fatan Allah Ya ƙara musu zaman lafiya, ƙaunar juna da kwanciyar hankali me ɗorewa. Se da yamma sannan Lulu ta je gidansu Fatima Kabeer (Masoyiya). Kamar sa haɗiye juna saboda farin cikin ganin junansu. Haka suka zauna suna ta hira ta yaushe gamo. Se magribh sannan Masoyiyar ta rakota har gida kafin ta koma gida jiki duk ba daɗi. Ita kanta Lulu ji ta yi kamar kar su rabu, dan babu ƙarya sun yi kewar junansu.

Kasancewar Gwani ba ya nan, tun safe

Please Login or Register in order to submit comment