Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haihuwa. Bayan wasu satika haka nan kawai Mom ta kasa sakewa da Maimuna tun bayan abin da ya faru. Duk da Maimunan ba ta taɓa nuna mata wani abu da ze sa ta tsargu ta ga cewar ko za ta iya tona mata asiri ba. Amma ita dai haka nan ta kasa sukuni. Dan haka rana ɗaya aka wayi gari za ta sallami Maimuna. A ranar ta gama aikinta, ta zo da niyyar fita daga ɗakin Mom ta kirata. Se ta dawo ta nemi waje ta zauna, ta kalli Areef da ke gefe yana bacci cikin kwanciyar hankali ta sakar masa murmushi tana kama kumatunsa ta ja kaɗan.

"Ga ni Hajiya." Ta faɗa tana kallan Mom. Se da Mom ta sauke ajiyar zuciya kamin ta ɗauko wata babbar leda ta ajje a gabanta tace

"Ki ɗauki wannan naki ne Maimuna.. kuɗi ne.. ki tafi garinku.. Na gode da kulawarki da kuma taimakonki gare ni.. Allah Ya saka da alkhairi." Da mugun mamaki Maimuna ke kallan Mom ƙirjinta na bugawa, kafin da ƙyar ta yi ƙarfin halin faɗin

"Hajiya me na miki? Me na aikata miki? Wani abun aka ce na miki?" Girgiza kai Mom ta yi da sauri tana faɗin

"A'ah fa Maimuna ba ki min komai ba wallahi.. Yanzun ne kawai ba na buƙatar er aiki, kin san ma ke ba a matsayin er aiki na ɗauke ki ba. Kawai dai na fi so ki koma garinku ki je ki ɗan huta ke ma. Wannan kuɗin ze ishe ki ki yi duk abubuwan da kike buƙata.. Amma don Allah ki yi haƙuri na sallameki, kuma wallahi ba dan komai ba, dan kuwa alkhairinki gare ni yawa gare shi."

"Ki taimaka min don girman Allah Hajiya.. kar ki kore ni.. Ki faɗa min idan wani abu na miki in gyara amma ni dai kar ki kore ni don Allah." Ajiyar zuciya Mom ta sauke sannan tace

"Wallahi babu abin da kika min Maimuna. Idan ma kin min na yafe miki. Ki yi haƙuri dai ki ɗauki kuɗin nan ki koma garinku, Zan neme ki zuwa nan gaba. Sannan ki tabbatar kin riƙe min sirri, kamar yanda muka bar shi a wajen ke ma ki bar shi a wajen. Hakan ne kaɗai kuma ze sa ki din ga ganin aikena duk sanda na ga dama ba se ƙarshen wata ba." Da dai Maimuna ta ga Mom ta dage, haka tana ji tana gani ta shirya kayanta ta bar gidan har da kuka. Dan babu ƙarya gidan ya mata, tana yanda ta ga dama a cikin gidan, ga wadata, ga uwa uba kuɗin da take samu duk ƙarshen wata. Se dai ta wani ɓangaren tana jin ɗan sanyi idan ta tuna da kuɗin da Mom ɗin ta bata kafin ta fito. Se a lokacin sannan hankalin Mom ya kwanta da ta buɗe idanunta ta ga babu Maimuna cikin gidan.


Haka rayuwa ta cigaba da garawa, Areef kullum girma da wayo yake ƙara yi. Har kuma lokacin madara yake sha. Dan kuwa tun ranar da aka haife shi Mom ta gwada shayar da shi amma sam yaron nan ya ƙi karɓa. Idan ma aka tilasta shi se ya fashe da kuka. Haka ya din ga musu kuka, ga yunwa yake ji, ga shi ita kuma babu ruwan mama ko kaɗan, ga shi ma yaron ya ƙi kamawa ko hakan ze sa ya zo. Da dai ta ga da gasken ba karɓa ze yi ba ga shi kuma yunwar yake ji, se ta sanarwa da Daddy aka siyar masa madara. Aikuwa sosai ya sha madarar, ya shanye wadda aka haɗa masa tass. Daga nan kuwa se ya hau bacci. Tun daga ranar se ya kasance madara ita ce abincinsa, dan kuwa har lokacin tana cigaba da gwada shayar da shi amma ba ya karɓa se madarar. Tun tana gwadawa har ta zo ta haƙura ta cigaba da ba shi madarar kawai. Zuwa lokacin da Areef ya soma tasawa se ya kasance yaron na da wani mugun farin jini, ga wani shahararren kyau da kullum ƙaruwa yake yi. Har wasu en uwan Mom kan mata gori wataran da faɗin

"Daɗin auren miji kyakkyawa kenan.. Yanzu dai kalli ɗanki Salma.." Ita kuma a lokuta da dama amsarta ba ta wuce.

"Kwa ci kanku.." Soyayya Mom ke nuna masa kamar za ta maida shi ciki, haka Daddy ma jinsa yake har ƙasan ransa, sosai yake ƙaunar yaron. Dan tun da ya same shi se ya zamana komai Areef ɗin, ba shi da wani zance idan ba na Areef ɗin ba. Hakan ba ƙaramin yi wa Mom daɗi yake ba, musamman idan a gaban Mommah ne, se ta ji kanta ya ƙara girma, ta yi ta buɗe hanci kenan tana jijjiga kai ita a lallai dole me ɗa. Se dai me?? Tun da Areef ɗin ya soma wayo se wata matsala kuma ta tunkaro mata, matsalar da ta so bata tsoro har ta ɗaga mata lissafi. Ƙalubale na farko da Mom ta soma fuskanta shi ne yanda wata irin soyayya da shaƙuwa ta ƙullu tsakanin Mommah da Areef. Kai se ka ce iyayensa biyu ne cikin gidan nan. Yanda yakewa Mommah abubuwa idan ba ka san uwarsa ba se ka ɗauka ita ta haife shi. Ai tuni Mom ta tashi tsaye a kansa, ta shiga hana shi abubuwan da yake yi. Daga ƙarshe ma se ta dena barinsa duk inda ta san ze haɗu da Mommah. Se dai ƙalubale na biyu da ya fi kowanne ɗaga mata hankali shi ne wayar gari da aka yi Areef na kiran Hajiya Sa'adah da suna Mommah. Lokacin kam har duka ta so yi masa amma ta kasa, ta kama kunnansa ta ja ranta a ɓace tace

"Kar na sake ji ka kira waccan matar da Mommah ka ji koh?" Shiru ya yi kawai yana kallan Mom ba tare da yace komai ba. Dan kuwa tun yana ƙarami yake da shegen taurin kai da wata iriyar zuciya. Wadda duk sangartawar da Mom ta masa ne ya janyo hakan. Wai a hakan ma dan Daddy na kwaɓarsa ne yana tsawatar masa. Da dai ta ga idan ta yi faɗa har ta gama ba lallai ya tanka mata ba, se ta janyo shi tana murmushi tace

"My boy.. Kar ka sake kiranta da Mommah ka ji? Ka ga ai ba ita ce Mom ɗinka ba?" Ta ƙare tana murmushi.

"Toh." Ya amsa da hakan kawai.

"Dats my boy.." Ta faɗa tana kama kumatunsa.

Ta ɗauka ba za ta sake ji ya kira Hajiya Sa'adah da Mommah ba, se dai kamar ma tura shi ta yi dan kuwa cigaba ya yi da kiranta da hakan yana kuma cigaba da zuwa wajenta, dan kuwa haka nan kawai yake son zuwa wajen matar kuma tun yarinta. Ita kanta Mommahn ba ta san dalilin da ya sa ta tashi da matsananciyar ƙaunar Areef ɗin ba. Idan a rana be zo sashenta ba kuma ba su haɗu a sashen Daddy ba, se ta ji kamar ta bi shi sashensu ta gan shi. Jinsa take kamar ɗanta da ya rasu. Daga nan se rayuwar gidan ta soma chanjawa. Dan kuwa a lokacin ne Mom ta shiga fito da sinƙi_sinƙin rashin mutunci. Da ta ga babu haza, Mommahn ta ƙi ƙyale mata ɗa se ta shiga yada habaici da maganganu marasa daɗi game da Mommah. Waɗanda ta san ko da a da ba su taɓata ba yanzun dole su taɓata. Da Mom za ta gane ƙaunarsu daga Allah ce da ta ƙyale su ta rabu da su. Se dai ina, ita sam ba ta so ta ga wani abu da ze kawo kusanci tsakanin Mommahn da Areef ɗin. Ita da a so samunta ne ma sun tashi da matsananciyar ƙiyayyar junansu, da se tafi kowa farin ciki. Amma tun da hakan ta faru se ta tsiro da tura shi makarantar kwana tun a primary. A nan ne Daddy ya nuna mata ba ta isa ba. Da dai ta ga da gasken Daddy ba ze amince a kai shi makarantar da take so ba se ta huce haushinta a kan Mommah da ke cikin ɗakin lokacin da suka sake yin maganar da Daddy. Areef na gefen Mom yana danna wayar Mommah da ya je ta buɗe masa yake game. Ta saka hannu ta fuzge wayar daga hannun Areef tace cikin ɗaga murya

"Dallah can ba ni wayar nan kafin na yi rashin kirki.." Ta ƙare tana ajje wayar a kan centre table ɗin gabanta. Sannan ta ɗora da

"A ƙyale min ɗa mana.. A ƙyale min ɗa haka nan.. Idan mutum ya haifa ya din ga shishshigewa al'amuransa.. Haba.." Ta kai ƙarshe tana sakin tsaki gami da miƙewa tsaye dan ficewa daga ɗakin.

"Salma.." Daddy ya faɗa a kausashe dan ya fahimci abin da take nufi. Se ta koma ta zauna ba tare da ta kalli Daddyn ba. Ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin

"Kar ki ƙara maimaita wannan kuskuren.. Idan ba haka ba zan ɗauki mataki a kai. Ɗa kuma ke kika haife shi mun san wannan.. Amma kuma idan da kaara ai ɗan Sa'adah ne."

"A'ah wallahi ba nata ba ne tun da ba ita ta haifa min shi ba.."

"Ya isa haka.. Je ki." Daddy ya katseta da faɗin hakan. Se kuwa ta ja hannun Areef suka fice daga ɗakin fuuu kamar za ta tashi sama.

"Ki yi haƙuri.. Allah ze kawo miki masu albarka.. Rayayyu kuma lafiyayyu." Daddy ya faɗa a tausashe yana kallan Mommah. Se ta yi murmushin nan na yaƙe da ake cewa ya fi kuma ciwo sannan tace

"Babu komai Rankayadaɗe.. Allah Ya amsa addu'arka." Tun daga ranar Mommah ta yi ƙoƙarin fita daga sabgar Areef duk da yanda zuciyarta ba ta son hakan, amma dan son a samu zaman lafiya ya sanyata janye jikinta daga al'amuransa. Shi kam ko a jikinsa haka idan yana so ze zo sashenta ya yi wasansa, idan ya gaji ya tafi nasu sashen. A yanzu dai haka Mommah ta din ga janye jikinta daga gare shi, se dai idan ya zo se su yi ta abinsu da Baba Atine. Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa Mom ba, duk da dai ita da a so samu ne ma su dena magana kwata kwata. Amma har zuwa lokacin ya ƙi dena ce mata Mommah, haka dai ta haƙura ta rabu da shi dan ta ga alama ba ze dena ba.


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, wasu abubuwan sun chanja ya yin da wasu ba su chanja ba, ciki kuwa hadda halayyar Mom. Arziƙin Alhaji Matawalle kuwa ban da haɓaka kullum babu abin da yake yi. A cikin tsukun ne kuma Hajiya mahaifiyar Alhaji Matawalle ta rasu bayan gajeriyar rashin lafiya. Ba ƙaramin taɓasu mutuwar ta yi ba musanman da babu wanda ya taɓa kawo mata mutuwar a irin wannan lokacin. Haka dai suka haƙura suka cigaba da yi mata addu'a. Cikin ikon Allah kuma har zuwa yanzun babu wadda ta sake samun ciki a cikinsu. Duk da haka Mommah ba ta gaji ba, wajen addu'a Allah Ya bata ko ta samu ta ga jininta a duniya, ta kuma huta da gorin da Mom ke mata, wanda ba ta gajiya da shi sam kamar ita ma wayonta ko dabararta ne ya bata Areef. A haka rayuwa ta cigaba da tafiya, har zuwa lokacin da Areef ya shiga University, bayan tataɓurzar da aka sha tsakanin Mom da Daddy a kan fitarsa ƙasar waje. Mom ta kai wajen sati tana bibiyar Daddy a kan fitar tasa, amma kullum amsa ɗaya take samu, ta je kawai. Yau ma kamar kullum ta shigo ɗakin ta nemi waje ta zauna.

"Yallaɓai magana na zo mu yi da kai." Se da ya ɗaga kai ya kalleta sannan yace

"Ina jin ki.."

"Da ma a kan maganar Areef ne na zo in ji ko ka yanke shawarar barinsa ya fita ƙasar wajen. Ka ga dai haka na so ya fita tun a secondary amma ba ka amince ba. Toh a wannan karon ina roƙonka da Allah da ka amince ya fita.." Ajiyar zuciya Daddy ya sauke, shi kam sam ya rasa dalilin Mom ɗin na dagewa a kan fitar Areef ɗin waje karatu. Ko da yake ya san hakan na da nasaba da ganin da take 'ya'yan abokansa duk a wajen suke karatu.

"Shi kenan.. Amma ki sani duk wani tsari da na fito da shi za ki bi shi matuƙar ki na so na yadda Areef ya bar ƙasar nan."

"Babu damuwa.. Na amince ma." Ta faɗa tana murmushi cike da farin ciki da jin daɗi. Abu na farko da ya fara faɗo mata shi ne nisa da Areef ɗin ze yi da Mommah, ta san tabbas ze mantata kafin ya dawo. Abu na biyu kuma da ma burinta kenan kar ya yi karatu a ƙasar nan dan tana ganin a matsayinsa na ɗan gidan hamshaƙin me kuɗi kamar Alhaji Matawalle be dace a ce ya yi karatu a ƙasar nan ba. Haka dai bayan gama shirye shirye aka tura Areef U.S bayan dogon gargaɗin da Daddy ya gindaya masa. Be kuma bar shi ya tafi ba se da ya haɗa shi da waɗanda za su din ga kula da shi. A lokacin Mommah ji ta yi ina ma tana da ƙarfin faɗa a jin da za ta iya hana Areef tafiya ƙasar waje. Sanin da ta yi ba ta da shi ne ya sanyata kama bakinta. Ta bi shi da addu'a lokacin da ze tafi ɗin.

Duk da yanda Daddy ya tsaya tsayin daka wajen tarbiyyar Areef ɗin duk da ba ya ƙasar nan, amma hakan be yi wa Mom ba, ita se take gani ma kamar wannan ɗin ai takura ce. A bar yaro mana ya wataya ko dan kasancewarsa ɗan me kuɗi mana. Amma kullum yana tare da masu ba shi kariya da tsaro ai wannan ma takura ce da rashin yadda da shi. Shi kam Daddy ko a jikinsa, idan ma tana irin waɗannan maganganun ko kallanta ba ya yi. Dan kuwa be taɓa yadda da abin da take faɗa ba. Abin da ya sani kawai shi ne tun da Areef ɗin ya bar gabansu ya bar gabansu kenan, babu wani me kwaɓarsa a can ɗin. Dan haka tura masa masu kula da shi shi ne kaɗai mafita. Duk da ya san Allah ne kaɗai me karewa, amma ko babu komai hakan ze taimaka ainun.

_CIGABAN LABARI_


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO66*


___ Shiru ɗakin ya ɗauka na fiye da tsawon minti 5, babu wanda yace komai tun bayan da Maimuna ta gama faɗar abin da suka aikata ita da Mom. Bad Man dake zaune a gefen side chair yanzun haka yana zaune ne a kanta gaba ɗaya, hannunsa na kan goshinsa idanunsa a lumshe, ba za ka iya fahimtar yanayin da yake ciki ba. Se dai za ka iya ganin yanda jijiyoyin kansa suka tashi, suka fito raɗa raɗa har a kan goshinsa. Zuciyarsa babu abin da take yi se wani irin harbawa da ya wuce na misali. Ya ma rasa abin da ya kamata ya yi. Tunanin me ze yi? Me ya kamata yace? Me ya kamata ya aikata? Gaba ɗaya kansa ya kulle, ƙwaƙwalwarsa ta toshe, ta yadda ya kasa ko da yunƙurin yin wani tunanin ne. Daddy kam hular da ke kansa ɗazun yanzun tana gefensa, kansa yana kallan ƙasa lokaci zuwa lokaci yana bubbuga ƙafarsa a ƙasa, se dai shi ma har zuwa shuɗewar waɗannan mintunan be ce komai ba. Ammi da Talatuwa da basu san da zaman labarin ba su kansu sun jijjiga bayan da suka ji abin da Maimunan da Mom suka aikata. Kuka kawai Talatuwa ta fashe da shi, dan ba ta taɓa tunanin rashin imanin Maimunan ya kai har ta yadda a haɗa baki da ita su aikata wannan mummunan aikin ba. Mom da tun ɗazu take yunƙurin magana Daddy na hanata, a karo na barkatai ta sake buɗe baki jikinta na wani mugun karkarwa, ba ma ta taɓa tunanin idan ta buɗe baki za ta iya magana ba. Se dai cikin ƙarfin hali ta buɗe bakin da ƙyar ta soma faɗin

"Wallahi ƙarya take yi, ƙarya take yi. Sharrin Sa'adatu ne kawai. Duk yadda aka yi nauyinta ta ɗauka dan ta zo ta ƙala min wannan sharrin. Da ma tun da na sallameta a aiki na lura ta ƙullace ni ashe abin da suka shirya kenan. Kar ka yadda da ita, kar ka yadda da ita.. ƙarya take min.." Ta ƙare muryarta na karkarwa. Se a lokacin sannan Daddy ya ɗaga idanunsa da shi kansa suka sauya kala ya sauke su a kan Mom, wata irin tsanarta na zuwa ta mamaye zuciyarsa. Haushi, takaici da kuma tsananin mamaki sun ƙi barinsa. A karo na farko tun bayan gama bayar da labarin da Maimuna ta yi yace

"Kin gama?" Ya faɗa muryarsa a wani irin kaurare. Se ta yi maza ta jijjjiga kai a tunaninta ko ya yadda da abin da ta faɗa ne, tace

"Ehh wallahi ƙarya take min.." Ta sake wallacewa ba tare da damuwa ba, a cewaeta ai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba. Se da Maimuna ta goge hawayen da ya ƙi tsayawa a kan fuskarta saboda danasani da nadama sannan tace

"Ina me rantsewa da girman Allah abin da na faɗa gaskiya ne. Ban ƙara ba kuma ban rage ba. Idan dai har ƙarya na yi mata Allah ya wulaƙanta ni tun kafin na bar gidan nan.. Za kuma ku iya zuwa ku yi gwaji dan tabbatar da abin da na faɗa.." Se a lokacin Mommah da tun da aka fara maganar ba ta iya ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ba ne. Illah kafe Maimuna da ta yi da ido tana jin abin da take faɗa ɗin kamar almara. Lokacin da ta kai ƙarshe kuwa tuni jikinta ya ɗauki rawa, har ta numfashinta se da ya soma yi mata barazanar ɗaukewa, dalili kenan da ya saka bugun zuciyarta ya ƙaru, ta shiga fuzgo shi da ƙyar idanunta a lumshe. Har lokacin babu abin da kunnuwanta ke jiye mata se maganar Maimunan. Kamar wadda kunnanta ya yi recording haka take ji. Cikin lokaci ƙanƙani ta ji wani jiri na ɗibarta duk da kasancewarta a zaune. Ba tare da ta shirya ba kuwa ta yi maza ta riƙe kanta da ya mugun sara mata, a take a gun kuma ta zube kan kujerar sumammiya.

"Sa'adah.." Daddy da ke lura da ita ya faɗa yana miƙewa da sauri. A karo na farko ya buɗe idanunsa da ƙyar kuma da sauri, sun yi wani irin ja kamar gauta. I zuwa lokacin ban da zafi babu abin da numfashinsa ke fitarwa. Be san lokacin da ya miƙe ba kai tsaye ya wuce kujerar da Mommah ke kai.

"Areef ɗorata kan waccan kujerar.." Daddy ya faɗa duk da yanda yake jin wani tsoro na kama shi. Se dai ta gefe ɗaya ya san dole ne Mommah ta shiga irin wannan yanayi, jin abin da ba ta taɓa tsammani ba. Shi kansa ya rasa a wanne yanayi ze saka wannan al'amari, ballantana kuma ita da ta haifa. Babu musu Bad Man ya saka hannunsa ya ɗauki Mommahn ya soma takawa dan kwantar da ita kan wata kujera da ke cikin palourn wadda ta yi shigen kama da gado, se dai ita ma irin yadin kujerun gareta.

"Ka sauketa Areef.. Ka da ka yadda da abin da suke faɗa.. Sharri ne.." Mom ta yi ƙarfin halin faɗin hakan, dan kuwa a lokacin ita kaɗai ta san tsoron da take ji. Kawai dai tana yin magana ne dan kar zargin ya yi yawa. Wani kallo da ya watsa mata da gigitattun idanunsa shi ne ya sanyata saurin sauke kanta ƙasa hantar cikinta na kaɗawa. Kaddai har ya amince da abin da aka faɗa? Yau kam ta shiga uku idan haka ɗin ne.

Kai tsaye kwantar da ita ya yi a nutse. Be jira Daddy ya ce komai ba ya ɗauko ruwa da kansa ya ƙaraso ya shiga shafawa Mommahn a fuskarta. Cikin ƙanƙanin lokaci ta ja wani gauron numfashi kafin ta sauke ajiyar zuciya, se ta shiga buɗe idanunta kamar me neman wani abu. Ba ta jira komai ba ta miƙe zaune da kanta a kan kujerar. Hawaye ne suka shiga zubowa a kan fuskar Mommahn, ranta babu daɗi sam, ta rasa me ya kamata ta yi. Cikin kulawa Daddy ya kamo hannunta idanunsa a kan fuskarta yace

"Ki na lafiya?" Jinjina kai ta yi daidai lokacin da wasu hawayen suka zubo a kan kuncinta. Da ƙyar ta buɗe baki tace

"Da gaske en biyu na haifa? Da gaske Areef ɗana ne? Da gaske ne Yallaɓai?" Mommah ta yi maganar gwanin ban tausayi. Rufe idanunsa Daddy ya yi yana jin wani mugun tausayin Mommahn na ratsa shi. Kaff cikin ɗakin cike da tausayawa suke kallan Mommah, idan ka cire Mom da Aunt Makiyy da suke tsoron kar asirinsu ya tonu. Juyawa Daddy ya yi ya kalli Mom da har lokacin su take kalla, ban da gumi babu abin da ke tsatstsafowa daga jikinta.

"Za ki buɗe baki ki faɗi gaskiya ko kuma se na yi miki abin da har ki mutu ba za ki manta da shi ba?" Ya yi maganar a kaurare yana kafeta da idanunsa. Shiru Mom ta yi a ranta tana ji kamar ta buɗe baki ta sake maimaita ƙarya Maimunan take yi. Se dai gefe guda kuma tana tsoro kar ya gano ƙarya take ya yi mata abin da yake iqrari, dan ta san tabbas ba ze wuce saki yake nufi ba. Kai amma duk da haka ba za ta bari asirinta ya tonu ba, dan haka ta buɗe baki da niyyar sake ƙaryata Maimuna a karo na barkatai se jin muryar Aunt Makiyy dake gefenta ta yi tace

"Haka ne abin da Maimuna ta faɗa.. Se dai wallahi ba mun yi hakan ba ne dan wani abu.. se dan soyayyar da muke masa.. Kuma tun da muke ba mu taɓa cutar da shi ba, dan ba ƙiyayya ce ta saka mu ɗaukarsa ba tsantar soyayya ce.. da.." Wata wawuyar tsawa da Bad Man ya dakawa Aunt Makiyy ita ce ta dakatar da ita ƙarasa abin da ta soma faɗa. Take jikinta ya ɗauki rawa cike da tsoro. Shi kansa saboda tsabar yanda ɓacin rai ke tare da shi har rawa jikinsa yake yi. Idanunsa sun sake rinewa sun yi jajur, fuskar nan ta haɗe irin haɗewar da ban taɓa ganinta ba. Kallo ɗaya za ka masa ka tabbatar da tsananin ɓacin ran da yake ciki. Kamar ba ze ce komai ba se kuma ya ɗaga yatsansa ya nuna Aunt Makiyy muryarsa na fidda wani irin amo ya soma faɗin

"Kuuulll!! Kar na sake jin kin ambaci soyayya a wajen nan, idan ba haka ba daga ke har yayar taki zan lahantaku.." Ya ƙare yana sauke numfashi. Wanda hakan kaɗai ya isa ya nuna maka abin da yake faɗa tun daga ƙasan zuciyarsa yake fitowa. Tun kuwa da ya buga mata wannan tsawar ba ta sake ko da yunƙurin cewa wani abun ba ne. Se ƙasa ma da ta yi da kanta tana ji kamar ta tashi ta fice daga ɗakin. Ita kam Mom suman zaune ta yi, kukan da take yi ya tsaya cakk, jikinta ya sake ɗaukar rawa. Tana ji a jikinta tabbas yau ƙarshenta ne ya zo. Ban da haka ya ya za a yi Makiyya da kanta ta tona mata asiri? Se dai ba ta san ita Aunt Makiyy ta yi hakan ne dan nemawa Mom ɗin mafita ba saboda jin abin da Daddy ya faɗa. Dan ta riga ta san halin er uwatta na taurin kai da ƙeƙashashshiyar zuciya, ko me ze yi ba za ta amsa laifinta ba. Shi ya sa ta ga kamar hakan ne kaɗai ze sanya a fahimce su, musamman idan ta yi amfani da kalmar soyayya. Se dai kamar ba haka ba ne. Neman waje kawai Daddy ya yi ya zauna cike da tsananin mamaki da kuma takaici. Duk da tun ɗazun zuciyarsa ta yadda da abin da Maimunan ta faɗa, amma ko babu komai yana da kyau ya ji ta bakinsu. Shi ya sa yanzu da ya ji maganar daga bakin Aunt Makiyy abin ya fi taɓa shi da yawa. Ashe be sani ba yana zaune ne da mara imani. Muguwa mara tausayi, wadda za ta iya yin komai saboda

Please Login or Register in order to submit comment