Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ta yi tambayar cike da mamaki. Wanda hakan ba ƙaramin kaɗa 'ya'yan cikin Didi ya yi ba.

"Aeho.. Aff.. Ai na manta ɗazun sun fita da Yallaɓai Areef." Duk da yanda ta ji abin wani banbarakwai amma hakan be hanata sauke numfashi ba. Ba tare da ta san a fili ba ne ta furta

"Yallaɓai Areef kuma?"

"Ƙwarai kuwa sun fita tare.. Kar ki damu." Cikin wata nutsuwar da ta sake samu ta lumshe idanunta kafin tace

"Toh Baba na gode." Se da ta miƙa mata saƙon da Mommah ta aiko mata da shi sannan ta mata se da safe ta fice daga ɗakin. Cigaba da tsayuwa ta yi kamar wadda aka dasa. Fisabilillahi ya fita da yaro amma har yanzu be dawo ba? Ta raya hakan a ranta tana turo baki. Da dai ta ga tsayuwar ba za ta yi mata ba se ta nemi waje ta zauna tana cigaba da jiran nasu. Dan kuwa hankalinta ba ze taɓa kwanciya ba idan ba ta ga Little ɗin ba..


.... A ɓangaren Ammi kuwa tun ranar da ta sauka a garin da ta je se ta tarar jikin Gwaggon na buƙatar ganin Likita. Don haka da kanta ta ɗauketa zuwa asibiti. Abinka da jikin tsufa nan take aka basu kwanciya. Cikin ikon Allah kamar yanda jikin Gwaggon ya saba a kwana 2 se ga shi jiki ya yi kyau kamar ba ita ce mara lafiya ba.

Gwaggon na kishingiɗe a kan gadon, ya yin da Ammi ke zaune a kan kujera. Wadda ke jinyar ta kusa da gadonsu ma tana kan kujera tana kallan Gwaggo wadda ta su ta zo ɗaya. Suna ta hirarsu kamar sun saba. Se dai lokaci zuwa lokaci ta kan juya ta kalli wadda take jinyar saboda tsaro. Mata ce wadda a kallan farko idan ka mata za ka ɗauka ta baiwa 50 baya. Se dai kuma ko 45 ba ta rufa ba. A kishingiɗe take, kallan farko ka mata se ka ɗauka lafiyayyiya ce. Se dai a zahiri gaba ɗaya jikinta ba ya aiki idan ka cire hannunta na dama wanda shi kaɗai ne ke iya motsi a jikinta. Se kam idanunta da take ƙiftasu lokaci zuwa lokaci. Idan ka kalleta za ka san tabbas tana tare da hirarsu Gwaggon. Dan kuwa ka na kallan ƙwayar idanunta za ka san da tana da baki za ta buɗe ne ta taya su hirar. Se dai da yake babu bakin, se ya kasance kawai jinsu take yi babu damar amsawa. Ita dai Ammi na gefe se dai ta yi murmushi kawai idan kuma an sakota ciki ta ɗan tofa albarkacin bakinta.

"Kuma wai wannan ɗin ma ɗiyarki ce ta cikinki Gwaggo?" Matar ta tambaya tana murmushi. Kallan Ammi Gwaggo ta yi se ta yi murmushi sannan ta maida dubanta kan matar tace

"'Yata ce.. Ita kuma a Kano take aure.." Ta ƙare tana murmushi.

"Allah sarki kuma tun farkon aurenta a Kanon take zaune?"

"Eh tun ranar da aka ɗaura mata aure."

Waro idanunta wannan mara lafiyar ta yi. Se dai da yake babu baki, ba kuma za ta iya motsa jikinta ba ya sanya duk ba su lura da hakan ba. Tsananin tashin hankalin da na gani cikin idanunta shi ne ya sanya ni sake kafe idanu ina kallanta. Daidai lokacin da ta ɗaga lafiyayyen hannunta ta soma yafito Ammi wadda sam ba ta lura da ita ba. Hatta Gwaggo da ita me jinyar tata babu wanda ya lura da ita. Ta runtse idanunta tana jin zuciyarta na karyewa. Se ta sake yin amfani da hannun nata ta daki wata roba da ke kan gadon. Se kuwa ta faɗi a ƙasa, wanda hakan ya janyo hankalinsu Gwaggo gaba ɗaya suka kalleta. Da sauri me jinyar tata ta miƙe ta ƙarasa inda take tana faɗin

"Lafiya..?" Inaa.. ita sam ba ta ta take ba. Ta rasa yanda za ta yi a fahimci abin da take nufi. Se dai yanzu da yake duk hankalinsu na kanta ne ya sanyata sake yin amfani da hannunta ta yi wa Ammi alama da ta zo. Babu ɓata lokaci Ammi ta miƙe ta ƙaraso har inda take. Still dai ba ta dena miƙa mata hannun ba. Hakan ne ya sanya Ammi saka hannunta ta riƙo na mara lafiyar tana maida dubanta kan fuskarta. So take ta yi magana se dai ta kasa. Ta yi iya bakin ƙoƙarinta ko yau ɗin Allah ze buɗe mata baki ta samu ta yi magana, ta samu ko da saƙo ne ta bayar kafin ta bar duniyar nan. Se dai duk iya ƙoƙarinta ta kasa ko da motsa bakin ne. Idanunta da suka yi jajir kamar gauta har sun soma zubar da hawaye. Da za ta iya magana da idanunta da ta yi hakan a yanzu. Se dai hakan ba me yiwuwa ba ne. Amma kuma ko da idanunta ka kalla se ka tausaya mata. Saboda yanda take cigaba da bin Ammin da kallo kamar me mata magana da idanu. Cikin tausayawa Ammi ke kallanta cike da mamakin abin da ke faruwa. Me ya faru? Wace ce wannan ɗin? Me take so tace mata?..

🤔🤐g


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO58*


___Cigaba ta yi da iya ƙoƙarinta ko za ta iya yin maganar, se dai duk yanda ta yi hakan ya citira. Dalili kenan da ya sanya wasu hawaye masu ɗumi suka zubo a kan kuncinta har kuma lokacin idanunta na kan Ammi, haka hannunta na cikin na Ammi. Daga Ammi, Gwaggo har me jinyar tata me suna Talatuwa mamaki da tausayinta ya gama cikasu. Se dai abin da ya ɗaga hankulan gaba ɗayansu shi ne yanda jikin Maimuna ya rikice cikin lokaci ƙanƙani. Dan kuwa idanunta ne suka soma ƙaƙƙafewa kamar wadda ke shirin barin duniyar. Cikin matuƙar tashin hankali Talatuwa ta fashe da kuka tana faɗin

"Na shiga 3.. Me yake faruwa da ke Maimuna." Ta faɗa tana kai hannunta jikin Maimunan ba tare da ta yi yunƙurin zuwa kiran likita ba. Ganin da Ammi ta yi ita kanta Talatun ba ta a hayyacin da za ta iya zuwa kiran likita ya sanya Ammin fita daga ɗakin da sauri. Se dai tun a ƙofar ɗakin ma suka haɗu da likitan kasancewar lokacin da ze duba marasa lafiya ya yi. Se ta faɗa masa abin da ya faru. Nan da nan kuwa ya ƙarasa cikin ɗakin.

"Ki ɗan ba ni waje." Ya faɗawa Talatuwa da ta yi kane kane ta kasa matsawa ko ina daga jikin Maimunan. Ban da kuka babu abin da take yi tamkar ƙaramar yarinyar goye. Se a lokacin ta iya miƙewa ta matsa gefe tana share hawayen fuskar tata. Ya yin da shi kuma likitan kai tsaye ya shiga dubata cikin ƙwarewa.

.. "Ki yi haƙuri In Sha Allah komai ze daidaita. Za kuma ta samu sauƙi da yaddar me sama." Gwaggo ta faɗa tana kallan Talatuwa. Jinjina kai Ammi ta yi kafin a nutse ta ɗora da

"In Sha Allah.." Hannu Talatuwa ta kai ta goge fuskarta kafin tace

"Ina fatan haka ni ma. Amma yanda suka fita da ita ne ya ba ni tsoro."

"Babu damuwa hakan ma. Ke dai kawai ki fawwalawa Allah." Ba ta iya amsawa ba se ɗaga kai da ta yi. Shiru ne ya wanzu a wajen na en mintuna kowa da abin da yake tunani. Kafin daga bisani Gwaggo ta kalli Ammi tace

"Goben za ki wuce Fatima?" Kallan Gwaggo Ammi ta yi tana ji kamar tace a'ah, dan duk da Gwaggon ba ita ta haifeta ba amma tana ganinta ne kamar tata mahaifiyar da ba ta raye. Se dai kuma ta riga ta faɗawa Abba adadin kwanakin da za ta yi. Ba kuma ta so ta saɓa hakan. Don haka tace

"Ehh.. mun yi magana da Maryam tana nan tahowa a goben."

"Toh shi kenan babu matsala. Allah Ya kai mu." Tun da suka soma magana Talatuwa ke kallansu, har zuwa lokacin da suka gama. Se ta sauka daga kan kujerar da take ta ƙarasa zuwa wadda Ammi take. Hannu ta saka ta kamo hannun Ammin daidai lokacin da hawaye suka cika idanunta tace

"Don Allah.. ba don halinmu ba, ki taimaka ki bari kar ki tafi har se Maimuna ta farka. Duk wasu alamomi sun nuna tana son magana da ke ne. Ban sani ba ko ta sanki ne ko ke kin santa tuntuni. Don Allah ki mana wannan alfarmar Hajiya." Shiru Ammi ta yi tana kallanta dan ba ta san me za tace ba.

"Ki na ganin kin san fuskarta ne?" Gwaggo ta yi maganar tana kallan Ammi. Girgiza kai Ammi ta yi, tana tunanin ko ta santa ɗin ne. Se dai kuma duk wani tunaninta ita dai ba ta san Maimunan ba. Hasalima ba ta taɓa ganinta ba se zuwansu asibitin.

"Ikon Allah! Toh kuma ba ta taɓa faɗa miki wata magana da za ta saka yanzu ki kawo ko tana da alaƙa da abin da ya faru ɗazun." Gwaggo ta faɗa tana kallan Talatuwa.

"Wallahi ba ta taɓa ba. Abin da kawai zan ce cikin shekarun baya gaskiya ta haɗu da ciwon damuwa. Don haka kawai za ta zauna ta yi ta tunani kamar me iskokai. Komai tunani komai tunani. Shi ne dai daga ƙarshe aka ce mana ciwon damuwa ne. Kuma na yi na yi ta faɗa min abin da ke damunta ta ƙi. Wallahi daga haka dai ciwo ya din ga tafiya. Daga wannan lalurar se wannan. Har dai aka zo kan wannan na shanyewar jikin." Talatuwa ta ƙare a sanyaye. Ita dai Ammi har lokacin ba ta sake cewa komai ba tun bayan amsar da ta baiwa Gwaggo. Har zuwa lokacin da Gwaggon ta sake faɗin

"Ki yi haƙuri Fatima. Ki ba ni wayar da kaina zan masa bayanin abin da ya faru, wanda ze hanaki komawa. Duk da na san halin Muhammadu mutumin kirki ne." Murmushi Ammi ta yi kafin tace

"Toh Gwaggo."



.. A nutse ya tura ƙofar ɗakin da sallama ɗauke a bakinsa. Sanye yake cikin wata tattausar farar jallabiyya. Kansa babu komai yanzu haka. Se gyarararriyar sumar kan nan nasa da kuka sani a waje. Hakan ba ƙaramin kyau ya yi ba. A nutse ya ƙarasa ya nemi kan gadon ya zauna. Tana ganin haka ta ɗauke kai ta juya wani ɓangaren tana wasa da gefen hijab ɗinta. A nutse ya ɗaga idanunsa ya kalleta na tsawon second 10 kafin ya ɗauke idanunsa daga kanta.

"Afaaf.." Ya kira sunanta kai tsaye yana maida dubansa kanta. Idan da ita wata ce a yanda ya yi magana kaɗai ya isa ya nuna mata magana me muhimmanci yake son yi da ita. Amma ita ba ma ta fahimci hakan ba. Se kawar da kai da ta sake yi tana turo baki gefe guda kuma zuciyarta na neman karyewa. Dan ita yanzu sam ba ta so ta gansu waje ɗaya. Da da dama ma tashi za ta yi ta bar masa wajen, se dai kuma yanzu ta san halinsa ƙaramin aikinsa ne ya kamota. Jin da ya yi ta yi shiru ne ya sanya shi lumshe idanunsa a kan laɓɓansa ya furta

"Se yaushe ne..?" A fili kuma se ya yi amfani da hannunsa wajen lalubo inda nata hannun yake ya sanya shi cikin nasa ya riƙe da duka biyun. Da sauri ta juyo da niyyar ƙwacewa. Se dai a yanda ya zuba mata narkakkun idanunsa, se ta ga kallan da yake mata a kwanakin nan ba irin wannan ba ne. Dan yanzun se ta ga yana neman rikiɗe mata ya koma Gwani na can baya. Gwani Affan Ya mu'allim ɗin Islamiyyarsu. Dalilin kenan da ya sanya ta yi maza ta janye idanunta da ke wani girgiɗi.

"Ki nutsu.. ki kalle ni da kyau.. ki kuma faɗa min gaskiya." Ya faɗa sanda ya lura ba ta haƙura ba tana cigaba da neman ƙwace hannayenta ne.

"Gaskiya?" Ta maimaita a kan laɓɓanta har ba ta san lokacin da ta kalle shi ba. Lura da maganar da ya faɗa ɗin ta sakata mamaki ne ya sanya shi sakin hannun nata a hankali kafin yace

"Mene ne haɗinku da wadda kika kira da ƙanwar Abba?" Ya tambaya yana kafeta da idanunsa. Shiru ta yi, kamar yanda ya kafeta da idanu haka ita ma ta kafe shi da su. A karo na farko da ko da da second ɗaya ne ba ta ji tsoron haɗa idanu da shi ba. Se dai wannan kwarjinin na nan. Amma duk da haka ba ta janye ba.

"Ki ba ni amsa." Ya sake faɗa. Kawai se ta sauke ajiyar zuciya. A yanda take ta uban fushin nan be yi tunanin da wuri haka za ta sakko har ta masa magana ba. Se kuwa ta fara faɗin

"Ƙanwar Abba ce wallahi.. Babansu ɗaya." Jinjina kai Gwani ya shiga yi yana sake yin mamakin Mamin.

"Kin san ta san da zaman hoton nan? Kar ki faɗa min ba gaskiya ba.." Ya yi tambayar da kuma maganar duka a haɗe. Shiru ta yi a ranta tana tunanin idan dai har ta faɗa masa to ta tonawa Mamin asiri. Idan kuma ba ta faɗa ba wani abu ya zo ya faru tabbas za ta zama me laifi. Kamar ba za tace komai ba se kuma tace

"Ita...." Se ta dakata a nan kamar wadda aka riƙe. Ya fesar da iska daga bakinsa kafin ya kai hannunsa ya sake riƙo hannunta ya sanya shi cikin nasa. Cikin nutsuwa kamar me raɗa yace

"Kar ki damu. Kar ki ji komai.. ki faɗa min abin da kika sani. Kar ki ɓoye min komai Uhmm?" Ya ƙare yana kallanta. Se ta zame hannun da sauri tana ɓata fuska. Babu musu ya sakar mata hannun. Se da ta sake ɗaukar wasu sakannin kafin ta cigaba da faɗin

"Ita ce ta nuna min hoton a wayarta.." Ta dakata a nan. Se kuma tace

"Don Allah kar ka faɗawa su Abba. Idan dai ka faɗa musu se sun ji abin da ya faru. Don Allah ka min alƙawari." Ta faɗa a sanyaye.

"Na yi miki." Ya ba ta amsar a taƙaice yana lumshe ido, saboda yanda ta yi maganar ba ƙaramin dukan zuciyarsa hakan ya yi ba. Kasancewarsa Malami ya sanyata amincewa, dan ta san ba ze faɗi abu kuma ya zo ya ƙi yi ba musamman ma dai a yanda ta san Gwanin.

"Me ya saka ta samo hoton toh? Ko ita ce ta saka a ɗauka?" Girgiza kai Lulu ta yi tace

"A'ah ba ta faɗa min ba. Ce min ta yi wai.. ze taimaka idan ka gani hakan ya sa ka..." Se kuma ta ƙi ƙarasawa. Ta saci kallansa ta ƙasan idanunta. Murmushi ya yi yana girgiza kai

"In sake ki ba..?" Se yanzu ya fahimci kan labarin. Wato ashe ita ta nemi Hero ya ba ta hoto ne dan ta ba wa Abbati. Shi kuma Abbati ya nuna masa daga haka ya saketa. Saboda ga lusarin namiji, wanda be san abin da yake yi ba. Ko da yake ko babu komai hakan ya yi sanadiyyar gyaruwar abubuwa da dama a zamantakewarsu. Daga ƙarshe kuma ga shi ta rufta da su Mami a ciki.

"Ba zan sanar da Abba abin da ya faru ba, ko dan ka da zumuncinsu ya lalace. Se dai ki sani daga yau na datse duk wata alaƙa da ke tsakaninku. Ba na so na sake ganin ku na alaƙa kamar ta da. Se dai kasancewarki musulma ita ma haka, kuma er uwar mahaifinki ya sa na sahalce miki gaisuwa da kuma sallama. Daga nan babu wani abu.. Kin fahimta?" Kawai se ta samu kanta da gyaɗa kai kamar wata ƙadangaruwa. Ya yi murmushi har cikin ransa yana jin daɗin hakan.




.. Daga cikin ɗakin ta fito hannunta ɗauke da wayar. Ta nemi waje ta zauna tana kara wayar a kunnenta.

"Ashe ki na kusa.."

"Ehh Abbansu ina kusa.." Ta amsa tana murmushi. Kafin yace komai ta ɗora da faɗin

"Barka da wannan lokaci.."

"Barka dai.. Ki na lafiya?" Shi ma ya amsa mata da murmushin kan fuskarsa.

"Alhamdulillah."

"Madallah.. ya masu jikin?"

"Gwaggo kam ta warware. Toh ka san yanayin jikin nata har yanzu dai ba su sallame mu ba. Ita ma kuma waccan ɗin an ce ana samun cigaba. Su na saka ran farfaɗowarta ma nan da kwanaki kaɗan."

"Toh Ma Sha Allah.. Allah Ya ƙara lafiya. Ki samu idan ana buƙatar wani abu ne ko dan a ceto lafiyarta ki bayar. Kin san irin waɗannan ciwukan su na da cin kuɗi."

"Sosai kuwa Yallaɓai.. Kuma da ma In Sha Allah ni ma na yi ƙoƙarin hakan." Murmushi Abba ya yi dan ya fahimci abin da Ammin ke nufi yace

"Allah Ya saka da alkhairi, Ya ƙara buɗi." Dariya Ammi ta yi jin abin da ya faɗa ɗin. Bayan duk kuɗin da take amfani da su na shi ne. Amma duk da haka se ta amsa da

"Ameen Ameen." Daga haka suka yi sallama.


... Se da ta shirya shi tsaff cikin kayansa masu kyau sannan ta shiga tattare inda ya ɓata. Tana cikin yi ta tsaya ta jefa masa harara

"Haka kurum ka yi ta ɓata waje kamar me.." Turo ƙaramin bakinsa ya yi yace

"Kai Didi Allah kin ƙaro faɗa."

"Aou da ma ina da faɗa kenan koh?" Ta faɗa tana waro ido.

"Ehh." Ya faɗa yana gyaɗa kai kamar wanda ke shirin tsinka shi. Dariya Didi ta yi tana faɗin

"Little.. Little.." tana girgiza kai. Ranar a ɗaki suka wuni abinsu. Ba ta bari Little ɗin ya je ko ina ba ballantana ma Bad Man ya gan shi.

Tabbatarwa da ta yi idanun Little ba sa kanta ya sanyata nufar ƙasan gado ta sanya hannu ta ɗakko wata ƙaramar bottle da ta yi nasarar ɗaukowa daga ɗakinsa ɗazu da ta je kai masa coffee ɗin safiya.

"Kar ka je ko ina ka ji ɗan ƙanina.. Yanzu zan dawo." Ta faɗa tana murmushi. Jijjiga kai ya yi yana cigaba da wasansa. Se kuwa ta fice daga ɗakin. Kamar yanda ta yi ranar nan haka yau ma ta haƙe rami ta fasa ciki ta kuma binne kwalbar. Se a lokacin sannan ta sauke ajiyar zuciya. Kamar kullum da yanzu ya shiga cikin duk wasu addu'o'inta haka yanzun ma a fili ta furta

"Allah Ya shiryeka.. Ya yaye maka wannan masifar." Ta yi maganar tana miƙewa. Karkaɗe jikinta ta soma yi wajen da ƙasa ta ɓata. Ba ta ankara da tahowar mutum ba se ji ta yi an ce

"Daughter!" A zabure ta ɗaga kai ta kalli Mommah da ta ƙaraso wajen. Me ya kawota nan? Ya aka yi ta zo? Yaushe ta zo? Tambayoyin da suke lugude a kanta kenan. Waɗanda suka sakata kasa amsa kiran da Mommah ta mata. Tsoronta ɗaya kar ta je ta ganta shi kenan komai ya ƙare ba tare da ta samu nasara ba.

"Lafiya? Me ya faru? Me kike yi a nan?" Ta yi tambayar duka a jere. Ba ta san lokacin da wani yaƙe ya ƙwace mata ba

"Ehh.. ehhh.. Mommah lafiya.. Kawai dai kin ga na zo dubawa ne ko na yi mantuwa a wajen." Ta yi ƙoƙarin ƙarasa maganar cikin dakiya dan kar ta fahimceta. Kallanta Mommah ta yi, ita tsoronta ɗaya ka da ta je akwai wani abun amma Didin ba ta gaya mata ba. Se dai kuma tun da har tace babu komai bari ta bar shi a haka ɗin.

"Toh shi kenan yanzu kin duba?"

"Ehh na duba babu komai." Didi ta faɗa a ranta tana jin babu daɗi na ƙaryar da ta yi wa Mommahn.


Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta zauna a kan gado, har se da Little ya kalleta. Ba ta sake fita daga ɗakin ba har se da dare da za ta fita kai masa coffee sannan ta ja hannun Little suka fita. Suna fitowa ya yi daidai da lokacin da Bad Man ke ƙoƙarin shiga ɗakinsa. Se kuwa Little ya zame hannunsa daga na Didi ya tafi da gudu yana faɗin

"Uncle.."

"Aww baby boy.." Bad ya faɗa yana ɗaga shi sama ya jefa sannan ya sauke shi ƙasa yana ta dariya. Kawai se ta tsaya tana kallansu kamar waɗansu da suka yi shekara a tare. Ga kuma mamakinsa da ya kamata na ganin ya yi murmushi har da sakin fuska kamar ba shi ba. Ashe da ma shi ma yana sakewa ya yi rayuwa kamar ya mutane? Ta tambayi kanta. Gefe guda kuma haushin Little ɗin ya kamata, kamar ta je ta ja shi ta mammamgare shi. Se dai se ta yi shiru tana jira ta ji ko ze sake shi ya taho shi kuma ya wuce ɗakinsa. Se ta ga ya ja hannunsa sun wuce ɗakin.

"Wai toh ko dama shi aka kawo wa Little ɗin ne?" Ta tambaya a shagwaɓe tana binsu da kallo, kamar akwai wanda ze amsa mata. Ta kai wajen minti 2 a tsaye kafin ta wuce kitchen.

Tana tafe tana saƙa ai dai yanzu idan ta je ze bata Little ɗin ta tafi da shi tunda dai dare ya yi. Da sallama ta shiga ɗakin kanta a ƙasa. Tana shirin wucewa ta ji yace

"Malama kin bar mana ƙofa a buɗe.." Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. Kai idan ma ba sanin muryarsa ka yi ba se ka ɗauka ba shi ya yi maganar ba. Sauke numfashi ta yi se ta juya a sukwane ta rufo ƙofar kafin ta juya har lokacin ba ta kalli inda suke ba. Kai tsaye wajen ta ƙarasa ta je ta ajje. Se ta saci kallansa yana kan gado yana danna system. Ya yin da Little ma ke kan gadon yana game, wanda da ka gan shi ka san bacci yake ji, saboda yanda yake lumshe ido. Se kawai ta yi shahada ta soma takawa dan ficewa daga ɗakin. Har ta kusa kaiwa ƙofar ta jiyo muryarsa.

"Heyy!!" Se ta dakata a inda take. Kafin ta juyo ya ɗora da faɗin

"Nemi waje ki zauna yaron nan ya yi bacci ki ɗauke shi.. ko kuwa ni zan kawo miki shi ne?" Ya ƙare a karo na farko tun shigowarta ɗakin yana watsa mata idanunsa..



✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO59*


___Shiru ta yi a ranta tana maimaita abin da ya faɗa ɗin. Se take ji kamar kawai ta yi tafiyarta. Amma kuma idan ta tuna da cewar komai fa lalacewarsa mijinta ne, kuma umarni yake bata se ta ji jikinta ya yi sanyi. Hakan ne ya sanyata juyawa ta nemi waje ta zauna. A matuƙar takure take jinta burinta Little ya yi bacci, yace mata ta zo ta ɗauke shi. A karo na barkatai ta sake kallan Little wanda zuwa lokacin har baccin nasa ya yi nisa. Ta sauke ajiyar zuciya tana ƙoƙarin fara miƙewa. Se kuma ta koma kamar wadda aka dakatar. Ta ɗaga kai da niyyar satar kallansa, se idanunta suka faɗa cikin nasa. Sam ba ta yi tsammanin ganin idanunsa a kanta ba shi ya sa ma ta kalle shi, ban da haka da babu abin da ze sa ta kalli inda yake. Se da ya jefa mata wani kallo da ya fi kama da harara sannan ya ɗauke kansa yana wani ciccin magani.

"In zo in ɗauke shi?" Ta faɗa a sanyaye ba tare da ta kalle shi ba.

"Baccin be yi nisa ba." Ya bata amsar cikin basarwa. Ba ta sake cewa komai ba ta cigaba da zaman, dan ta fahimci kamar hadda son wahalar da ita da yake ne ya sa yake mata haka. Bayan shuɗewar wasu mintuna Bad Man ya miƙe kai tsaye kan mudubi ya nufa. Idanunsa ya shiga jefawa da alama wani abun yake nema. Zuwa can ya saka hannunsa ya buɗe drawer, nan ma dai rufeta ya yi a fili yana furta

"A'ah.." Cike da mamaki. Tun da ya soma dube duben nan ta ji hantar cikinta ta kaɗa. Ka da fa a ce abar nan tasa yake nema. Tuna hakan ne ya sanyata cigaba da sussuskuy da kai kamar munafuka tana kuma murza hannunta lokaci ɗaya. A hankali ya sake kallanta yana ganin yanda take kallan inda yake a fuzge. "Ko dai ita ta ɗauka?" Ya tambayi kansa. Ɗan cije lips ɗinsa ya yi na ƙasa yana soma takawa zuwa inda take. Hannu ya saka ya ɗagota daga zaunen da take. Ya zamana tana kallansa ne fuska da fuska. Ƙirjinta ne ya cigaba da harbawa tana ji kamar ta fashe da kuka.

"Ke kike ɗauke min bottles ɗina koh?" Ya yi maganar yana kafeta da waɗannan idanun nasa. Runtse idanunta ta yi ta rasa me za tace. Ji take kamar tace ba ita ba ce. Ji take kamar kuma ta fito fili

Please Login or Register in order to submit comment