Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗin.

... Cikin gidan Alhaji Matawallen babu wanda ya san abin da ke faruwa. Se dai wasu daga ciki sun ɗan fara tsarguwa, musamman da suka ga shigar en sanda gidan, daga baya kuma gaba ɗaya en gidan suka zo suka fice. Daddy na parking motarsa, tuni aka zo aka fara bubbuɗe musu ƙofa. Didi farin ciki kamar ze sheƙeta dan daɗi, yau ga ta ga er uwarta. Ita ma Lulu na kusa da er uwatta, kan cinyarta kuma Little ya ɗora kansa ya soma baccin da ya fara fuzgarsa. Kallan gidan Lulu ta yi lokacin da suka sauka daga motar, a ranta tana mamakin nan ɗin ne gidan da aka kawo Didi kenan? A nan Didinta ke rayuwa? Ta tambayi kanta.

"Dukka ku je ku yi bacci ku huta.. Zuwa gobe za mu samu mu yi magana."

"Toh Yallaɓai.. Allah Ya tashe mu lafiya." Mommah ta amsa da hakan.

"Ameen." Ya amsa da hakan yana maida dubansa kan Bad Man yace

"Ka tafi da ɗan uwanka sashenka.. Ku samu ku samu bacci yau ɗin nan.."

"Ohk.." Bad ya amsa da hakan. Daga haka Daddy ya wuce, masu tsaron lafiyarsa na bin bayansa zuwa sashensa.

"Daughter ku wuce mu je sashena.. Areef ku je tare da Affan ku yi bacci cikin nutsuwa, ba na son dogon tunani. A bar komai se zuwa gobe kamar yanda Daddynku ya faɗa. Uhmm?"

"Toh Mommah.." Bad Man ya amsa da hakan, yana fata a ce ta manta da abin da ya faru ɗazu. Be dai fahimci hakan ba, dan kuwa maida dubanta ta yi kan Gwani daidai lokacin da ya furta

"In Sha Allah.." Daga haka matan suka wuce part ɗin Mommah, ya yin da mazan suka wuce ɗakin Bad Man.

Tuni Mommah ta shiga haba haba da sirikanta. Bayan kowaccensu ta yi wanka ta shirya tsaff cikin dogayen rigunan Didi. Se suka nemi waje suka zauna suka shiga hira sama sama. Shigowar Mommah ce ya sanya su katse hirar da suke. Ta ƙaraso da murmushi kan fuskarta tace

"Me za a dafa muku?"

"Mommah ni dai a ƙoshe nake.." Didi ta faɗa tana kallan Mommahn.

"Couscous.." Lulu ta faɗa dan ta tsaya ta yi tunani kawai shi ta ji tana sha'awar ci.

"Toh shi kenan Daughter.." Mommah ta faɗa, daga haka ta fice daga ɗakin. Ji take yau ɗin rana ta daban ce, dan haka ko me sirikanta ko 'ya'yanta ke so za ta tsaya ne ta musu ita da kanta.

"Wai ni kam Lulu yaushe kika zama acici ne?" Didi ta faɗa da mamaki tana kallan Lulu. Turo baki Lulu ta yi kamin tace

"Ni ɗin?"

"Eh fa.."

"Ba wani nan ni kam kawai yunwa nake ji." Jinjina kai Didi ta yi tace

"Toh ya miki kyau ai."

Mommah da kanta ta shiga kitchen, tare da taimakon Baba Atine cikin ƙanƙanin lokaci suka gama dambun couscous da ya ji kayan haɗi. Cikin ƙankanin lokaci sashen Mommahn ya ɗauki ƙamshin girkin Mommahn me daɗin shaƙa. Kwashe shi Mommah ta yi a duk inda ya dace, ta bawa Baba Atine ta fitar mata da waɗanda ta zuba cikin wasu ƙananan warmers. Se ta fito daga cikin kitchen ɗin, kai tsaye ta wuce ɗakinta inda a nan ne su Lulu ke zaune. Lulu na zaune kusa da Little da ke ta baccinsa. Mommah ta ƙarasa ta nemi waje ta zauna.

"Ku ɗan fito ku yi wani aikin lada mana.." Didi ce ta fara miƙewa kafin Lulu ma ta miƙe. Se suka bi bayan Mommah suka fice daga ɗakin. Ba tare da wata kunya ba Mommah ta ba su umarnin ɗaukar abincin kowacce ta kaiwa mijinta. Tura baki Lulu ta yi dan ita kam bacci ya soma fizgarta. Ya yin da ita dai Didi ba ta yi komai ba, ba kuma tace komai ba duk da sanin hali. Abin da kawai ta sani tun da har Mommah tace su yi kawai za su yi ne. Hannu Didi ta saka ta ɗauka, ganin da ta yi Lulu ba ta ɗauka ne ba ya sanyata watsa mata wata harara. Babu shiri ta saka hannu ta ɗauka tana cuno baki. Murmushi Mommah ta yi lokacin da suka fice daga ɗakin, wai yau ita ke da 'ya'ya biyu. Bayan su kuma har da sirikai biyu.

"Allah abun godiya.." Ta faɗa a fili tana sauke ajiyar zuciya.

... Fitowarsa daga wanka kenan, se a lokacin ya tuna da be taho da kowanne kaya ba, toh kenan me ze saka? Ya tambayi kansa. Daidai lokacin Bad Man ya shigo cikin ɗakin, ya saka hannu ya ɗauki wasu kaya da ke a ajje ya matsar da su kusa da Gwani yace

"Ka yi manage da waɗannan kafin gobe.." Kallan kayan Gwani ya yi, kafin ya saka hannu ya ɗauka. Wandon ya bi da kallo, irin wannan crazy ɗin ne mara kirki. Ya kalli Bad yace

"Wannan ɗin zan saka?" Bin wandon Bad Man ya yi da kallo. Shi sam be ma kula da wanda ya ɗauko ba se yanzu. Cikin basarwa yace

"Toh mene ne? Dan dai rana ɗaya? Na ga dai ba wani ne ze ganka ba." Jefar da wandon Gwani ya yi a kan gado ya nemi waje ya zauna a kan gadon lokaci ɗaya yana faɗin

"Ba zan saka ba wallahi." Ya yi maganar ya yi kici kicin da fuskarsa. Tilas hakan ya bawa Bad Man dariya. Ya saka hannu ya ɗaga wandon yana sake kalla.

"Yanzu me ye aibun wannan wandon Iyee?"

"Ka ba ni wandon mutunci Malam." Be ce komai ba Bad Man, se komawa da ya yi ya buɗe wardrobe ɗinsa ya shiga dubawa. Shi dai ya san kwata kwata ba shi da manyan kaya, dan ko Daddy ya ɗinka da shi bayarwa yake yi. Gaba ɗaya kayansa na kanti ne. Shi ya sa nau'in wandunansa duka ba su wuce crazy ko kuma normal jeans irin matsatstsen nan ba. A cikin jeans ɗin dai ya samu ya ɗakko wani me dama dama. Ya ƙarasa ya miƙawa Gwani yace

"Ga shi Malamin Addini.." Ya ƙare yana er dariya ƙasa ƙasa. Harara Gwani ya watsa masa ba tare da yace komai ba.

"Ohh duk ƙoƙarin da na yi ba ka gani ba koh? Ya yi.." Bad ya faɗa yana jinjina kai. Kai idan ka gansu se ka ɗauka sun fi shekara a tare. Ba za ka taɓa cewa da ma ba tare suka rayu ba, saboda kowannensu yana ji da miskilanci, amma kuma ga shi sun saki jiki suna ta maganarsu kamar ba su ba.

"Kawo.." Gwani ya faɗa yana miƙa masa hannu. Miƙa masa ya yi yana komawa gefe ya kwanta yana faɗin

"Bari na ga Malamin Addini cikin matsu.." Ya faɗa ƙasa ƙasa. Shi dai Gwani be kula shi ba ya shirya abinsa. Sosai fa Gwani ya fito ya yi wani mugun kyau abinsa. Yau ɗin se ya fita daban kamar ba shi ba. Shi dai ta ɓangarensa har ga Allah ya saka wandon ne a bisa lalura, dan kuwa haka nan kawai be ga abin da ze saka shi saka irin wandon nan ba.

"Kuma fa ka yi kyau.." Bad Man ya faɗa yana kallansa.

"Ka ji da shi.." Gwani ya ba shi amsa da hakan yana sake kwantar da sumar kansa.

"Wai ba a maka abun kirki ne?"

"Yi haƙuri, na gode." Gwani ya faɗi hakan. Murmushi kawai Bad Man ya yi yana komawa kan gadon ya sake kwantawa.

"Bari na ɗan fita.. zan shigo zuwa an jima." Gwani ya yi maganar yana kallan Bad Man.

"Ohk.." Ya amsa da hakan. Daga haka Gwani ya fice daga ɗakin zuwa palour, ko ze samu ya yi tunani a cikin nutsuwa. Dan ya ga alama idan suna tare da Bad Man ɗin ba ze samu ya yi tunani da kyau ba. Sosai hakan ya bawa Bad Man ma dama wajen zama ya yi tunanin da ya aure su a yau ɗin.

Yana zaune a kan kujerar ɗakin ya yi shiru.. Har yanzu jin abun yake kamar a mafarki, wai su Ummeey ba su ne suka haife shi ba. Amma suka riƙe shi tsayin shekaru ba tare da sun taɓa faɗa masa ba, ko kuma su yi wani abu da ze nuna ba su suka haife shi ba. Kullum soyayyarsu a gare shi ƙaruwa take yi. Kullum burinsu be wuce a kansa ba. Duk wani fatansu na kansa. Se ga shi yau an wayi gari ashe ma ba su ne iyayensa ba. Kenan ya soyayyar iyaye take? Shi dai tun da yake be san wani abu ba ban da soyayya. Dan kuwa Ummeey da Abeey sun nuna masa so, wanda har abada ba ze taɓa mantawa ba. Rayuwarsa da su irin abun nan ne da ake kira wanda ba za a iya mantawa ba. A ko da yaushe abubuwa da dama za su zama waɗanda ze din ga tunawa a matsayin lokuta mafiya tsada kuma masu daraja a cikin rayuwarsa. Gefe guda kuma tunanin yanda aka raba shi da mahaifiyarsa da ɗan uwansa shi ma ya kasa barinsa. Dan haka se ya zamana ya yi shiru ne kawai a fili, amma cikin zuciyarsa cunkushe take da tunanuka kala kala. A daidai wannan lokacin Lulu da Didi suka yi sallama cikin ɗakin. Ya riga ya saba, duk nisan tunanin da yake da wuya a yi magana be ji ba. Dan haka suna yin sallamar ya ji, ya amsa sallamar ba tare da ya kalle su ba.

"Barka da wannan lokacin Ya mu'allim.." Didi ta faɗa cike da girmamawa. Se a lokacin sannan ya kalleta. Ya yakice tunanin ya ƙaƙalo murmushi yace

"Barka dai Afrah.. Ki na lafiya?" Se da suka gaisa sannan ta miƙe a sukwane, duk da yanda take jin kunya na kamata haka dai ta daure ta durfafi ɗakin nasa. Da ta kwantar da hankalinta ma shi Gwani hankalinsa ma ba ya nan. Dan tun shigowarsu hankalinsa ya koma kan matarsa. Zuwa lokacin da suke gaisawa da Didi a lokacin ne kuma Lulu ta samu kanta da tsayawa tana kallansa. Tun da take ba ta taɓa ganinsa da irin wannan shigar ba, se ya fita daban, ya zama kamar ba shi ba. Ita kam ta yi mamakin ganinsa da wannan shigar. Se dai ko mahassadi ya gan shi ya san ya yi kyau. Kansa a buɗe ba kamar ko yaushe ba. Kyakkyawar baƙar sumar kansa a kwance luff luff. Damatsan fararan hannunsa a waje, wanda suka bayyanar da murɗaɗɗen hannunsa me jan hankali. Fahimtar da ta yi yana shirin dawo da dubansa kanta ne ya sanyata saurin ɗauke nata idanun tana maidawa kan abincin.

"Barka.." ta faɗa har lokacin ba ta ɗago ba.

"Barkanki dai.. Ina fata ki na lafiya?" Ya tambaya cike da kulawa. Ita wallahi idan yana wani abun mamaki yake bata. Kawai se ta jinjina kai tace

"Eh.." Daga haka ta miƙe dan ficewa daga ɗakin.

"Tafiya za ki yi?" Ya yi maganar a hankali. Kafin tace komai ya ɗora da faɗin

"Yanzu tafiya za ki yi? Ba za ki tsaya in din ga ganinki ba ko da hakan ze rage abin da nake ji cikin zuciyata ba?" Ba ta san lokacin da ta ɗaga idanunta ta kalle shi ba. Ya lumshe mata idanu yana buɗewa a cikin nata idanun. Ta kautar da idanunta da sauri tana zumɓuro baki gaba.

"Toh ni bacci zan yi.." Ta faɗa kamar a shagwaɓe, se dai sam ba ta san haka maganar ta fito ba. Dan ita ta yi ne kawai ba da wata manufa ba. Kawai tsayawa ya yi yana kallanta ba tare da yace komai ba. Da ƙyar dai ya sake kokawa da zuciyarsa yace

"Ba kya buƙatar komai?" Ɗan jim ta yi kafin ta jinjina kai tana ji kamar ta yi ficewarta. Se ta kasa yin hakan, kawai ta cigaba da zama. Idan ta tuhumi kanta dalilinta na yin hakan, se ta kawo uzurin yau ɗin Gwanin abun tausayi ne sosai, shi ya sa ta zauna saboda kuma yace mata ta zauna. Sosai kuma hakan ya taimaka masa, dan babu ƙarya Lulun ta zame masa sanyin idaniya, musamman a yau ɗin da ya sake gasgata hakan. Abu ɗaya ne ya rage, shi ne sauyawar halin Lulun gaba ɗaya, duk da cikin ikon Allah a hankali a hankali take chanjawa, dan yanzu an samu kaso me yawa ya ragu daga cikin halayenta.

A ɗaya ɓangaren kuwa da sallama ta shiga ɗakin ɗauke a bakinta. A Zuciyarta tana fatan Allah ya sa ya yi bacci, ko kuma dai ma kar ta same shi cikin ɗakin gaba ɗaya. Se dai addu'arta ba ta karɓu ba, dan kuwa samunsa ta yi kishingiɗe a kan gadon, ya ɗora kansa a kan hannunsa idanunsa a lumshe kamar me bacci. Se dai ba baccin yake ba, tunanin abubuwan da suka dinga faruwa kamar a mafarki ɗazun yake yi. Ya kasa dena tunanin, duk kuwa da abin da ya sha ɗazun amma har yanzu be manta abin da ya faru ba. Sallamar da ta sake yi ne ya sanya shi buɗe idanunsa da suka fi kama da na wanda ya tashi daga bacci. A hankali ta cigaba da takawa zuwa cikin ɗakin, kai tsaye ta ƙarasa inda ta saba ajewa ta ajiye sannan ta juyo. Kamar ta fice daga ɗakin ba tare da tace masa komai ba, se kuma ta ga rashin dacewar hakan, dan haka cikin siririyar muryarta tace

"Barka da wannan lokaci.." Se a lokacin sannan ya miƙe zaune. Maimakon ya ji kamar a da yana son shareta ko kuma sake mata gargaɗin kar ta sake shigo masa ɗaki, se ya ji yau ɗin ba haka ba ne. Ta wani ɓangaren ma kamar jin daɗin zuwanta ya yi. Ya ɗan sauke numfashi a gajiye sannan yace

"Barka." Ko a iya sautin muyarsa ya isa a fahimci yanayin da yake ciki a halin yanzu. Dan ita kanta Didi se da ta ɗaga kai ta kalle shi saboda yanda ta ji muryarsa ta sauya. Abin da dai ba ta sani shi ne, ko baccin da ya yi ne ya sanya muryarsa sauyawa ko kuma har yanzu a kan al'amarin da ya faru ɗazu ne?.

"Duk da dai ka ce na dena shiga harkarka amma da ka ɗauki Qur'an ka karanta.." Be san dalilin da ya sa yanzu idan ta yi makamanciyar maganar nan yake jin haushin hakan ba. Ya ɗan ja ƙaramin tsaki yana miƙewa tsaye a hankali. Ba ta yi tunanin ma ze tanka mata ba, se jin cunkushashshiyar muryarsa ta yi yace

"Kamar na ce ki bar min wannan maganar koh?" Ya yi maganar yana kafeta da idanunsa. Se ta yi saurin kauda kai tana ɓata fuska. Ƙasa-ƙasa ta furta

"Ai dai gwara na kama kaina.. kafin ka shuka min rashin kirkinka.." Sarai ya ji abin da ta faɗa, dan tun da ta fara maganar yake kallan bakinta dan fahimtar abin da ta faɗa. Ya ja ƙwafa yana cigaba da kallanta, ba tare da ya bari ta ankara ba ya ɗan soma rage tazarar da ke tsakaninsu. Ita dai tun da ta kawo abincin ta kuma gaida shi babu abin da ya rage mata. Dan haka ta ɗaga ƙafa da niyyar takawa dan ficewa daga ɗakin, ba tare da ta lura ba se jin hannunsa ta yi a kan hannunta, kafin ta yi ƙoƙarin yin komai ya jata gaba ɗaya zuwa jikinsa.

"Me kika ce?" Ya faɗa yana kafeta da lumsassun idanunsa. Ba ta san lokacin da jikinta ya kama rawa ba, musamman yanda ba ta yi tsammani ba. Se ta rasa ma abin da za ta ce. Ita burinta ɗaya ya ɗauke waɗannan idanun nasa daga kanta, idanun da suke sakawa ta ji tsoronsa ya kamata.

"Me kika ce..?" Ya faɗa yana riƙe hannunta sosai.

"Ni ba abin da na ce.."

"Kin faɗa.." Ya katseta da faɗin hakan yana sake janta cikin jikinsa. Da sauri ta girgiza kai tuna abin da ya faru rannan. Tsoron kar a sake maimaita abin da ya faru ya sanyata faɗin

"Allah ba da kai nake ba.. Don Allah ka yi haƙuri." Har ga Allah ta ba shi dariya, amma be yi ba ya maaze, ya sake tamke fuska. Yanayin yanda tsoro ya bayyana a kan fuskarta ba ƙaramin kyau ta yi ba. Se ya ji tamkar kar ya saketa, su cigaba da kasancewa a haka.

"Ashe mara kunyar ƙarya ce.." Ya faɗa yana sakinta, dan yau ɗin kusan duk hankalinsa na kan abin da ya faru ne ɗazun. Ba ta jira ta sake cewa komai ba, ko ya ce wani abu ba ta fice daga ɗakin kamar za ta yi tuntuɓe. Sam ba ma ta lura da waye a palour ba, Lulu ta koma ko ba ta koma ba duk ba ta lura ba. Ita dai burinta kawai ta ganta a sashen Mommah.

Komawa ya yi ya zauna a kan gadon, ya lumshe idanunsa tunani barkatai na zuwa masa cikin ƙwaƙwalwa. Se dai waɗanda suka fi tasiri su ne tambayar da ke ta masa yawo cikin kwanya.
"Shin me ke damunsa ne? Me ye ya sa yanzu yake kasa controlling kansa ne idan yarinyar na gabansa? Duk me ye hakan?" Ya tambayi kansa hannunsa cikin kwantacciyar sumar kansa.



✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO71*


___Ba ta daɗe da shiga ɗakin ba Lulu ta shigo ɗakin ita ma. Ta bi Didi da kallo tana mamakin yanda ta ganta.

"Ya na ganki kamar a zabure?"

"A zabure kuma?" Didi ta faɗa tana harararta. Se ta yi dariya tana faɗin

"Ehh yasin. Kamar wadda ta wa sarki ƙarya." Dariya ita ma Didin ta yi. Ta saka hannu ta janyo hannun Lulu tace

"Wai ni kam ki na kallan kanki a mudubi kuwa Lulu?"

"Na shiga 3 me na yi?" Lulu ta faɗa tana waro ido waje.

"Dillah kyau kika yi fa.. Kin ga har da ƙiba ma fa duk kin yi wallahi, kamar ba ke ba. Ke idan Ammi ta ganki ma ba za ta gane ki ba." Dariya Lulu ta yi jin ta ƙare zancen nata da barkwanci ya sa ta fahimci da wasa take. Tace

"Didina."

"Lulun Gwani." Buɗe baki Lulu ta yi tana kallan Didin. Se ta fuzge hannunta tana faɗin

"Allah ba na son kalar haka Didi.. Ni ba na so."

"Iyee.." Didi ta faɗa tana kallanta. Ita dai ba ta ga alamar har yanzu Lulun na cigaba da takun saƙa da Gwani ba, ba kuma ta ga alamun tsanar nan tasa da ta yi ba. Se dai abin da ba ta sani ba yanzun ta fara son shi ne ko kuwa a'ah? Se dai ba ta so ta gwada tambayarta kuma ta zo ta ɓaro wani aikin. Shi ya sa ta yi maganar nan ko za ta fahimci wani abun. Ba ta ankara ba se ganin Lulun ta yi ta fice daga ɗakin. Ta bita da kallo tana murmushi.

"A dai juri zuwa rafi.." Daga haka ita ma ta miƙe ta fice daga ɗakin zuwa palour. A nan suka sami Mommah, suka sake gaisawa. Ta kalli Baba Atine da shigowarta kenan tace

"Kin gama komai?"

"Ehh Hajiya.." Maida dubanta kansu Mommah ta yi tace

"Ya kamata ku je ku huta haka nan.. Ta kai muku abinci ku tabbatar kun ci sannan ku kwanta se da safe." A tare suka miƙe, Baba Atine ma ta miƙe dan musu rakiya zuwa ɗakin duk da a cikin palourn Mommahn yake.

"Se da safe Mommah.." Didi ta faɗa.

"Se da safe." Ita ma Lulu ta faɗa a hankali saboda rashin sabo a tsakaninta da Mommahn.

"Allah Ya tashe mu lafiya Yarana.." Ta yi maganar tana murmushi. Kai tsaye bin bayan Baba Atinen suka yi zuwa cikin ɗakin, ya yin da Mommah kuma ta miƙe ta faɗa ɗakinta.


.. Washegari da safe, fitowar Mommah daga cikin ɗakinta kenan suka yi sallama cikin ɗakin. Ta amsa sallamar tana kallan en biyunta da ta kwana tana musu addu'a a kan Allah Ya kare mata su. Se ta ƙaraso cikin ɗakin daidai lokacin da su ma suka ƙaraso. Dukkansu zamewa suka yi suka zauna a ƙasa. Mommah ta yi murmushi daidai lokacin da take amsa barka da safiyar da suka mata.

"Kun tashi lafiya?" Ta tambaya cikin kulawa.

"Alhamdulillah.." Gwani ya amsa da hakan, ya yin da Bad Man ya amsa da

"Ehh Mommah."

"Bari na ɗan amsa waya." Bad Ya faɗa yana miƙewa. Se duk suka bi shi da kallo, Gwani har yanzu ganin abin yake kamar a mafarki. Se kawai ya jinjina kai yana sake kaɗaita Allah a cikin zuciyarsa. Maganar Mommah ita ce ta katse masa tunani lokacin da take faɗin

"Don Allah ka din ga saka min ido sosai a kan Areef.. Ban san waye babba cikinku ba, amma haka nan zuciyata ke ba ni kai ne babba.. Dan haka ga ɗan uwanka nan ina fata za ka taya ni kula da tarbiyyarsa, duk wani abu da za ka gani be dace ba a wajensa ka yi ƙoƙarin hana shi ko tunasar da shi. Kai ne za ku din ga kasancewa tare shi ya sa nake faɗa maka haka." Jinjina kai Gwani ya yi kafin yace

"In Sha Allah Mommah.."

"Ku wuce sashen Daddy.. Za mu taho yanzun." Da "toh" ya amsa yana miƙewa ya fice daga ɗakin. Ta bi shi da kallo wannan farin cikin da ya kasa barinta na cigaba da ratsata. Kafin ta fita se da ta sake tura Baba Atine ta duba mata su Lulu. Nan take shaida mata bacci suke yi, se ta umarceta da ta ƙyale su kawai. Ita kuma ta wuce zuwa sashen Daddyn.


.. A kan dinning ɗin da ke sashen Daddy Mommah ta jere duk wani abu da ta girka musu. A nan suka haɗu bayan sun gaisa da Daddy suka soma karyawa. Duk sun yi tsammanin za su ga matayensu a wajen, se dai sam ba ma su ga ɓurɓushinsu ba. Mommah na lura da yanda suke ta jefa idanu da alama wani abun suke nema. Tabbas za ta yi amfani da wannan damar wajen koyawa Areef hankali bayan wahalar da su da ya yi tuntuni. Ta ɓangaren Gwani dai ta lura da wasu abubuwa, se dai duk da haka za ta haɗa duka ta san abin da za ta musu. Shi ya sa baccin Twins ɗin ma ya mata daɗi. Dan ba ta so su bar gidan nan ba tare da kowanne ɓangare yana son ɗaya ɓangaren ba. Ba kuma tare da ta gyarasu ba, dan jinsu take kamar 'ya'yanta.

"Ina 'ya'yan nawa ne?" Daddy ya faɗa yana kallan Mommah.

"Wallahi Yallaɓai bacci suke yi.. Shi ya sa na ce a barsu su yi ɗin duk sanda suka tashi se su yi nasu."

"Toh babu laifi.." Daddy ya faɗi hakan. Se kuma ya ɗora da faɗin

"Se ku shirya, dan kuwa gobe muna da baƙi da yawa cikin gidan nan.. Affan se ka yi haƙuri da mutanen da za su buƙaci ganinka." Murmushi Gwani ya yi be ce komai ba.

"Babu dai wata matsala koh?" Ya tambaya cike da kulawa.

"Daddy idan ma akwai ze faɗa min na faɗa maka.." Bad Man ya faɗa yana gyara zamansa.

"Iyeeee saboda kai ne bakinsa koh?" Daddy ya faɗa yana murmushi. Dukkansu murmushin suka yi. Kafin Daddy ya sake faɗin

"Kar ka ji komai, duk abin da kake buƙata ka sanar da ni ko mahaifiyarka.. Ba na son ka ji kunyar tambayarmu komai Uhmm?"

"In Sha Allah.." Gwani ya amsa da hakan yana murmushi.


... Tun kafin ta gama loda number sunan da ta yi saving number Ammi da shi ya fito. Ta kalla da mamaki tace

"Ikon Allah! Yallaɓai na ɗauka number wadda ta rako waɗancan mutanen ne koh?" Kallanta Daddy ya yi kafin ya amsa da

"Ehh ita ce.." Jin abin da Daddy ya faɗa ne ya sanyata kawai danna number ta kira. Babu daɗewa Ammi ta ɗaga. Suka gaisa kamar yanda suka saba, kafin can Mommah tace

"Wai da ma ke ce kika rako mutane cikin gidan nan jiya?" Murmushi Ammi ta yi dan ta san da ma Mommahn ba ta shaidata ba ne.

"Ƙwarai kuwa ni ce."

"Ikon Allah! Kin ga wallahi ban ganki ba. Hankalina duk ba ya wajen. Ki yi haƙuri."

"Haba babu komai.. Da ma ai ba za ki gane ni ba tun da ba sanin juna muka yi ba." Murmushi Mommah ta yi tana faɗin

"Haka ne.. Da ma na kira ne na miki godiya a kan hakan.. Allah Ya saka da alkhairi.. Amma da ma kin san su ne?" Ba tare da ta amsa addu'ar ba kawai ta share tace

"Eh toh.. Ba zan ce na sansu ba gaskiya.. Amma dai mun haɗu da su ne na je wajen Gwaggota. So a can muka haɗu, ita Maimunan ba ta da lafiya." Daga nan dai ta faɗa mata yanda suka haɗu har zuwansu

Please Login or Register in order to submit comment