Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zata ba, be yi tsammani ba ko kaɗan. Dalili kenan da ya sa be san lokacin da wani ƙawataccen murmushi ya suɓuce a kan fuskarsa ba. A hankali ya shiga takawa zuwa inda take zaune. Kamar yace mata wani abu, se dai be ce ba. A nutse fuskarsa ɗauke da annurin da ya kasa barin fuskarsa yace

"Mu wuce koh?" Ba tare da ta kalle shi ba ta miƙe a hankali ta shiga takawa. Ji ya yi kamar ya saka hannu ya ɗagata gaba ɗaya ya fitar da ita daga ɗakin. Se dai kawai ya bita a baya har suka fice daga asibitin.


Sun fi minti 5 da soma tafiya babu wanda yacewa da wani uffan. Zuwa can dai ya kaasa haƙuri, farin cikin da yake ciki yana da yawa. Yanda yake jin Lulun a zuciyarsa kullum ƙara haɓɓaka yake fiye da zaton me zato. Kawai se ya saka hannunsa ya kamo nata ya riƙe sosai, ta yadda ko da ta yi tunanin ƙwacewa ma ba za ta iya ba. Da sauri ta juyo ta kalle shi. Ya zuba mata idanunsa ba tare da niyyar janyewa ba. Tare ta yi amfani wajen ƙoƙarin janye idanunta da kuma hannunta amma ta kasa. Se ta narkar da fuska kafin ta buɗe baki tace

"Don Allah ka sake ni." Idonsa ya ɗaga mata guda ɗaya yana murza hannunta. Hakan ya bata damar janye nata idanun tana maida shi kan hannunta. A hankali kamar me raɗa ya shiga furta

"Allah Ya yi miki albarka Afaaf.. Allah Ya saka miki da alkhairi, Ya albarkaci abin da ke cikinki.. A karo na farko zan yi amfani da wannan damar wajen sanar da ke ina sonki. Ina ƙaunarki.." Ya ƙare yana sake zuba mata duk wani nauyi da idanunsa. Ba ta san lokacin da ta ɗaga kai ta sake kallansa ba. Se dai duk da yanda jikinta ya yi sanyi hakan be hanata janye hannunta ba. A sukwane ta koma gefe ta zauna tana jin yanda zuciyarta ta shiga harbawa da ƙarfi. Kamar wani maraya, kamar kuma ba Gwani ba cikin sanyi ya furta

"Ki taimaka ki amsa min Afaaf.. Ko da ba ki ce ki na sona ba dan na san da ma ba sona ake yi ba koh?" Ya ƙare kamar wani maraya..

"Ehh." Ta faɗa tana ɗauke kai. Be san dalilin da ya sa sam be ji zafin amsar da ta ba shi ba. Ko kuma mamakin hakan ya sanya shi ka sa furta komai, se hakan ba ta faru ba. Hasalima be san dalilin da ya sa be ɗauki amsar tata a matsayin wadda ta fito daga can cikin zuciyarta ba. Duk da dai abu ne a bayyane, ya san ba son na shi take ba. Amma kuma In Sha Allah cikin kwana kaɗan ze yi amfani da wannan cikin da Allah Ya azurtasu da shi ya koya mata son shi.

Tun kafin su ƙarasa cikin gidan kaɗe-kaɗe da bushe-bushe irin na gidan sarauta yake ziyartar kunnuwansu. Dakatawar da drivern ya yi ne ya sanya Gwani ɗaga ido ya kalle shi daidai lokacin da yake faɗin

"Da alama Yallaɓai ya yi baƙi daga gidan sarauta.." Ya faɗa yana sake leƙawa ko ze iya gano yawan motocin da yake hange.

"Babu yanda za a yi mu wuce kenan?" Gwani ya tambaya shi ma yana kallan yawan motocin, lokaci ɗaya kuma kaɗe-kaɗen na cigaba da tashi a nutse, cikin kuma ƙwarewa da sanin ya kamata. Sun ɗauki wajen minti 2 a haka kafin drivern ya samu ya shige cikin gidan. Daidai lokacin da Gwani ya maida dubansa kan Lulu. Duk da Hijab ne a jikinta hakan be hanata yin amfani da hannunta ba wajen ɗora shi a kan cikin nata. Jin abun take kamar a mafarki, ji kuma take kamar hakan ma ba ze taɓa zama gaskiya ba. Ita dai Lulun ita ce ke ɗauke da ciki. Ciki wanda ake haihuwa. Kenan ita ma dab take da ɗaukar jariri ko jaririya, ba ma na mutane da suke ɗauka ba, nata mallakinta na kanta, wanda za ta haifa da kanta. A daidai nan ne wani murmushi ya suɓuce mata. Ta kai hannunta guda ɗaya ta kare fuskarta. Kasa haƙuri ya yi. Har ga Allah idan tana tsiwa kyau take yi masa. Ga shi kuma da ma yana so ya ji muryarta amma se basarwa take yi. Hakan ne ya sanya shi gyara zama yana faɗin

"Ya kuma naga ki na murmushi? Kar dai ki ce min ki na son abun cikin naki." Ɗaga kai ta yi ta kalle shi kamar irin kallan lallai ya ma raina mata hankali. Se kuma ta tura baki tana ɗauke kanta, ciki ciki tace

"Ai dai na ga a cikina yake ba na wani ba."

"Iyeeee me ye kike cewa? Lallai kin girma.. Amma kuma ko kin manta ajiyata ce?" Ya ƙare yana kafeta da idanunsa bayan ya ɗage girarsa guda ɗaya lokaci ɗaya yana cijar gefen lips ɗinsa na ƙasa. Yanzu ma kallansa ta yi da sauri kamar ɗazu. Se dai yanzu da sauri ta janye idanunta dan wallahi ita idan ya yi wani abun yanzu mamaki yake bata. Se ta ga kamar ba shi ba. Bayan surutu har da rashin kunya duka ya koyo. Se ta sake zunkuɗa baki gaba tana haɗe rai, ita a lallai dole kar ma ya ga fuska bare ya sake kawo mata irin wannan maganar da ta ji kamar ƙasa ta tsage ta shige dan kunya. Hannu ta kai da sauri ta buɗe ƙofar tana ƙoƙarin ficewa. Ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar riƙo hannunta da kuma faɗin

"Yi a hankali.. saboda ajiyata.." Ya ƙare cikin basarwa ba kuma tare da ya kalleta ba. Dakatawar ta yi amma ba tace komai ba dan kamar ta fahimce shi so yake ya kunnota. Da kansa ya fita ya buɗe mata ƙofar, a hankali ta sauko. Daidai lokacin da ta ida saukowa ɗin idanun Gwani suka sauka a kan masu fitowa daga cikin ɗaya daga cikin motocin da suka riga su shigowa cikin gidan. Da mamaki ya ɗan ƙanƙance idanunsa dan tabbatar da ita ɗin ce. Cikin sakanni kaɗan idanunsa suka tabbatar masa da ita ɗin ce, lokacin da ta fi kusa da shi.. Kenan ya aka yi ya ganta a nan? Ya tambayi kansa..


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO74*


___A hankali kamar me yin magana da wanin da ba ya so a ji yace

"Maama.." Shi dai a sanin da ya mata tun zuwansa gidan nan er uwa ce ga Mommah. Se ga shi kuma yanzu ya ganta tare da wasu mutane da ke nuni da daga gidan sarauta suke. Ganin hakan ba lallai yana da wani amfani a wajensa ba ya sanya shi maida dubansa kan Lulu.

"Mu je na raka ki.." Ya yi maganar yana soma tafiya tun kafin tace komai. Da ma ba ta yi niyyar cewa komai ɗin ba. Se kawai ta bi bayan nasa zuwa sashen Mommahn.


... "Ni fa Yallaɓai har yanzu mamaki nake.." Mommah ta faɗa maɗaukakin mamaki na bayyana a kan fuskarta. Jinjina kai Daddy ya yi kafin yace

"Ni kaina.. Kawai na bari ne su shigo ɗin. Allah Ya kawo su lafiya." Mommah ba ta iya sake furta komai ba saboda tsananin mamaki. Dan ita dai tun da ta ji alamar mutanen da suka zo daga gidan sarki suke jikinta ya yi sanyi, haka kawai ta kuma shiga tsintar kanta cikin bugun zuciya. Kawai se ta yi shiru ta baza ido dan ganin su waye za su shigo. A nutse, cikin kuma dattako da kuma sarautar da ke yawo a cikin jininsa ya shigo cikin ɗakin tare da fadawa. Se da ya nemi waje ya zauna kafin ya bawa fadawan umarni da su fice daga ɗakin. Tun da suka shigo Mommah ke kallansu. Da sauri Daddy ya miƙe cike da mamaki ya furta

"Yallaɓai.." Ya yi maganar cike da maɗaukakin mamakin ganin Sarkin a cikin palournsa ba tare da wani dalili ba. Kafin ya ida tunani se ga Yaya Amina ta shigo cikin ɗakin, bayanta wasu mata ne guda 5. A'ah mamaki fa na neman kashe Mommah. Ta kuma kasa gane me ke faruwa. Me ye haɗin Yaya Aminar da waɗannan mutanen.

"Duk ku zauna.." Sarki ya yi umarni da hakan da muryarsa me kauri da kuma wani irin kwarjini a cikinta. Babu musu duk suka nemi waje suka zauna. Idanun Mommah gaba ɗaya yana kan Yaya Amina ne, dan ƙarin bayani kawai take jira. Kamar kuma ta san me take nufi, se ta kalli Mommah tace

"Sa'adah Baba Abdullahi ne.." Shiru ta yi na en wasu sakanni kafin can tace

"Wanne Baba Abdullahin?" Ta faɗa cike da maɗaukakin mamaki, kasancewar Baba Abdullahi dai ɗaya ta sani a rayuwarta. Ita kuma yanzu wanda take gani zaune a nan ba ta shaida fuskarsa ba ballantana har ta kawo cewar shi ne Baba Abdullahi. Se dai ko dan kaɗe-kaɗen da ta ji ya sa ta yi tunanin yana da alaƙa da sarauta.

"Baba Abdullahi dai namu Sa'adah.." Maida dubanta kansa Sa'adah ta yi cike da mamaki tana kallansa. Idan dai har ba ta yi kuskure ba se yanzu ta fahimci wannan ɗin Sarki ne wanda suka sani, se dai ba su taɓa ganinsa a zahiri ba se yanzu da yake zaune ga shi ga su. Shi ne kuma Yaya Amina ke faɗa mata Baba Abdullahi ne? A hankali Mommah ta ƙarasa ta zube a gaban Sarkin tana faɗin

"Baba Abdullahi."

"Na'am Sa'adatu.." Kawai se Mommah ta fashe da kuka. Kamar wadda aka wankewa ƙwaƙwalwa, ko kuma wadda aka zuba mata sabon tunani haka ta ji. Baba Abdullahi? Baba Abdullahi shi ne Sarkin garin nan, sun san shi suna kuma ganinsa amma ba su taɓa tunanin komai ba. Wannan wane irin abu ne?

.. Mommah da Yaya Amina sun kasance 'ya'ya ne ga yayan Baba Abdullahi, wato tsohon Sarki Abdulrazaq kafin Allah Ya karɓi rayuwarsa. Lokacin da yana raye shi ne Sarki. Ya kasance yana da mata biyu. Mahaifiyarsu Mommah 'ya'yanta biyu Sa'adah da kuma Amina. Ya yin da ɗayar ke da 'ya ɗaya Ramla. Lokacin da suke a matan Sarki ba ƙaramin kishi ake bugawa ba, dan ita Samira wani kalar jahilin kishi take da Mahaifiyarsu Mommah, musamman lokacin da take da 'ya'ya biyu ita kuma tana da ɗaya. Se dai ashe tsananin kishin da ze kaita ga saɓawa mahalicci yana nan zuwa, shi ne lokacin da Mahaifiyarsu Mommah ta haifi maza en biyu waɗanda suka ci suna Hassan da kuma Hussaini. A lokacin ne Samira ta kusa ƙaramin hauka, daga lokacin ne kuma tunaninta ya chanja, dan ba ƙarya hankalinta ya tashi saboda ganin magadan Sarki Abdulrazaq sun zo. Dan haka se ta fara shiga bokaye. Ta din ga bin bokaye dan su mata maganin damuwarta. (Wa iya zubillah) Abu na farko da suka fara fuskanta shi ne wata matsananciyar rashin lafiya da babarsu Mommah ta soma yinta, wadda kwata kwata aka rasa gane kanta. Babu kuma daɗewa Allah Ya karɓi ranta. Mutuwar da ta girgiza gidan sarautar gaba ɗaya, ban da mutum ɗaya da tafi kowa farin ciki da hakan. Ko banza ta gama da matar, hankalinta ze kwanta tun da dai yanzu babu fargabar kar ta je ta sake haifar namiji. Daga nan kuma se hankalinta ya koma kan En biyun. Sati 1 da mutuwar Mahaifiyarsu Mommah Hussaini ma ya rasu. Nan take gidan Sarkin ya sake rikicewa. Haka dai suka haƙura. Tun daga wannan lokacin se hankalin Samira ya koma kansu Mommah da kuma Hassan. Dan ita ta ɗauka ma har Hassan ɗin za a gama mata da shi. Se dai a nan bokan nata ke faɗa mata dole se dai su fara gamawa da mutum ɗaya kafin su koma kan ɗayan. Ita gaba ɗaya kishin nata ma ba a kan namiji ne kaɗai ba, dan duk da ta san namiji ne kaɗai ze iya yin sarauta, amma kishi ya rufe mata idanu, dan sam ta ƙi jinin ta buɗe idanunta ta ga su Mommahn. Hakan ne ya sa ta je aka mata aikin da za a raba su Mommahn da ɗan uwan nasu daga dangin mahaifinsu gaba ɗaya. Dan tun da an kasa gamawa da Hassan ɗin gwara kawai a kaɗa su can wani wajen su je su ƙarata. Dan tana tsoro ka da ta barsu su rayu cikin gidan kuma nan gaba Sarki ya bar duniyar a zo a ce shi ze gaje shi. Ana cikin hakan ne kuma Sarki suka yi hatsari a kan hanyarsu ta dawowa daga wata gaisuwar Abokin Sarkin. Kuma a hatsarin ne Abban nasu ya rasu. Mutuwar da ta fi kowacce mutuwa girgiza kafatanin gidan. Bayan mutuwarsa ne kuma babu daɗewa aikin Samira ya fara aiki. Sam su Mommah se suka kasa zaman gidan, musamman da ya kasance kowa na gidan ya juya musu baya. Babu be raga musu, daga ƙarshe ma se ya kasance babu me bi ta kansu gaba ɗaya. Su kansu ji suke kamar ana kaɗa su. Kamar kaɗa su ake da su bar gidan. Ga shi ko Baba Abdullahi wajen sati kenan be neme su ba. Ko ya manta da suna gidan ne? Ba su sani ba. Se dai su ma cikin ƙanƙanin lokaci wata irin tsanar gidan ta addabe su. Ana cikin haka ne kawai suka saɓi jiki suka bar gidan, kasancewar ta saka an ɗauke hankalin kowa daga kansu ya sa babu wanda ya neme su. Se dai inda Allah Ya taimake su se suka yi dangin mahaifiyarsu. Gwaggo ita ce ta riƙe su su ukun. Dan da ma tun mutuwar er uwatta ta so ɗaukarsu. Tun daga lokacin se ya kasance sun manta da wasu en uwan Babansu kwata kwata. Yanda ka san an goge musu wani abun haka suka manta da su kwata kwata. Gwaggo ce ta riƙe Hassan ta cigaba da kula da shi. Se dai da yake shi ma ba me tsawon rai ba ne ba a daɗe ba ya rasu. Haka dai Gwaggo ta cigaba da riƙe su kamar ita ce ta haife su. Tun tana musu zancen dangin mahaifinsu har ta gaji ta watsar, musamman da ta ga ko lokacin da za su dawo wajenta da zama babu wanda ya kawo su, su kaɗai suka zo. Daga nan dai rayuwarsu ta cigaba da tafiya.

A can ɓangaren kuma Baba Abdullahi da ya hau kan kujerar Sarkin shi ne ya auri Samira bayan mutuwar Sarki Abdulrazaq. Daga nan ta cigaba da zuba rayuwarta. Gaba ɗaya dai ta mantar da su rayuwarsu Mommah. Babu kuma wanda ya sake tunawa da su har zuwa shuɗewar waɗannan shekarun. Se a cikin satin can da Allah Ya karɓi ranta, ba tare da ta nemi yafiyar ɗumbin laifukan da ta aikatawa en adam ba. Se dai kafin ta mutun se ta din ga tonawa kanta asiri a kan abubuwan da ta aikata. Babu wanda be yi mamaki ba a duk waɗanda suka ji lokacin da take waɗannan sumbatun. Haka dai ta tafi a banza, bayan wata irin mutuwar wulaƙanci da ta yi. A lokacin ne asirinta ya soma warwarewa a hankali, dan kuwa cikin ƙanƙanin lokaci mutane da dama suka fara tunawa da 'ya'yan Sarki Abdulrazaq. Musamman ma Baba Abdullahi da hankalinsa ya tashi a lokacin saboda buɗe ido da ya yi ya ga babu Sa'adatu, babu Amina kuma babu Hassan. Ga kuma maganganun da Samira ta din ga faɗa kafin ta mutu. Sosai hankalinsa ya sake tashi, ko bacci ba ya iya yi a cikin kwanakin. Ya kasa sukuni saboda tunanin kamar be riƙewa ɗan uwansa amana ba.

"Se da na saka aka min bincike na gano ashe ma kun bar wajen dangin mahaifiyar taku yanzu haka ku na cikin garin nan. Na yi mamaki ainun da ya kasance duk tsayin shekarun nan ashe muna cikin gari ɗaya, amma ba ku taɓa nemana ba ko ni ko ragowar en uwa. Se dai da na tuna ni kaina na manta da shafin rayuwarku ya sanya ni yi muku uzuri. Na san kuma ɗauke muku hankali aka yi daga kanmu, tun da ga shi ku kuna ganina ma a wasu lokutan amma ba ku taɓa kawo komai a ranku ba. Ashe ashe duk ba mu sani ba aikin Samira ne.." Baba Abdullahi ya ƙarasa yana girgiza kai. Mommah da Yaya Amina kuka kawai suka shiga yi, rayuwarsu ta baya na dawo musu. Sun ɗauki mintuna masu tsayi kafin suka samu suka yi shiru. Se suka koma suka shiga gaisawa da Baba Abdullahi. Kamar ba sarki ba haka ya saki jiki yana jan su da hira duk dan ya kawar musu da damuwar da ya ga sun shiga a yanzun. Babu laifi sun ɗan saki jiki duk da idan suka tuna da abin da Samira ta musu se su ji duk wata damuwa ta mamaye su. Tunanin mahaifiyarsu se ya dawo musu sabo.
Sosai Baba Abdullahi ya ji daɗi lokacin da ya ji yana da jikoki. Dan haka babu ɓata lokaci ya sa a kira masa su ya gansu. Baba Atine Mommah ta saka aka kira mata, da kanta ta je ta isarwa Twins ɗin saƙon Mommah na son ganinsu da ake yanzu. Babu ɓata lokaci kuma suka wuce kiran Mommahn. A daidai za su shiga sashen suka yi kaciɓus da su Lulu da su ma suke shirin shiga sashen. Dukkansu dakatawa suka yi. Didi ta yi wani saurin janye idanunta, dan ba ta tunanin bayan abin da ya faru kuma za ta iya cigaba da haɗa ido da Bad Man ɗin. Hannunta har rawa yake lokacin da ta yi amfani da shi wajen riƙo hannun Lulu.

"Barkanku da wannan lokaci.." Ta faɗa tana jan hannun Lulun. Kamar wata doluwa se ita ma ta maimaita abin da Didin ta faɗa kafin suka shige da sauri. Kamar waɗanda ake ja se duka suka bi su da kallo. Shi Gwani ma se yanzu ya lura da chanjawar da Lulu ta yi. Dan idan da a yanzu ka sansu toh tabbas za ka bambance su, saboda yanda yanzu Lulun ta ƙara haske, ga kuma jikinta da yafi na Didi a yanzu. A tare suka ɗaga kai suka kalli juna kamar wanda suka ga wani abu. Se kuma cikin basarwa duk suka janye idanunsu. Murmushi Gwani ya yi a kan laɓɓansa ya furta.

"Ya Allah!!" Ya ƙare yana ɗan rufe idanunsa. Se kuma daga baya ya buɗe, kai tsaye suka faɗa cikin ɗakin.

Da sallama suka shiga cikin ɗakin, suka gaisa da kowa sannan su Lulu suka nemi waje suka zauna. Kafin su Gwani su zauna Baba Abdullahi yace

"Kar dai waɗan ne Abokan nawa?" Baba Abdullahi ya faɗa yana kallansu Bad Man. Jinjina kai Yaya Amina ta yi tace

"Ƙwarai kuwa su ne.."

"Ikon Allah.. Ku zo in ganku.. Yau ga yaran Sa'adatu a gabana.." Ya yi maganar yana miƙa musu hannu. Sam ɗaukar sarautar ya yi yanzun ya ajjeta a gefe, dan ganin 'ya'yansa da jikokinsa da ya yi ya saka shi cikin matukar farin ciki mara misaltuwa.

"Wannan shi ne Kakanku.. Ƙani ne a wajen mahaifinmu ni da Yaya Amina.." Mommah ta faɗa dan haska musu waye shi. Se kuwa suka ƙarasa suka zube suka shiga gaisawa. Sosai ya sakar musu fuska yana ƙoƙarin kawo wasa a gaisawar tasu. Kallansu ta yi lokacin da suke duƙe gaban Baba Abdullahin. Ta lumshe idanunta tana jin wata ƙwalla na tarar mata cikin idanu. Ita kam ba ta san da wane baki za ta godewa Allah ba. Irin waɗannan ni'imomin da ke kewaye da ita. Abubuwan alkhairi se faruwa suke da ita ba tare da ta yi tsammani ba. Se ta buɗe idanunta a kan nasu dai, daidai lokacin da Bad Man kalli Didi se kuwa ta kama shi dumu dumu yana kallan Didin. Ta maaze tana watsa masa wani kallo tana ɗauke kai. Da sauri shi ma ya ɗauke kansa a sukwane. Shi kam be san me Mommahn ke nufi da shi ba. An aura masa mata ana so ya zauna da ita, da farko ya nuna ba ya so, yanzu kuma yana so ba shi kenan ba? Se dai da alama ya ga ba haka ba ne. Dan a yanda ya lura da take-taken Mommah tamkar wani yaƙi ne a gabansa.

Sake gaisawa Baba Abdullahi ya yi da matan jikokin nasa kafin ya maida dubansa kan en biyun da ke gabansa zaune. Abin da ya san dole za su kawo a ransu shi ne duk lokacin da ya wuce me ya sa basu san shi ba? Ina yake? Dalili kenan da ya sa cikin nutsuwa ya shiga haska musu abubuwan da suka faru a taƙaice. Shiru dukkanninsu suka yi cike da mamakin jin wannan abu da ya fi kama da almara. Lallai Mommah ta ga rayuwa. Ƙaddarori kala-kala ta gansu. Didi ma kanta kallan mutanen cikin palourn take, cike da tausayin Mommah da kuma Yaya Amina. Lallai a kowanne irin yanayi ka tsinci kanka kar ka cire ran samun sauƙi. Wato gaba ɗaya dai rayuwar Mommah ishara ce a wajen mutane. Tun daga kan iyayenta, danginta ta soma fuskantar ƙalubale. Haka kuma a kan 'ya'yanta ma. Se ga shi da ta yi haƙuri a cikin kwanaki kurkusa duka matsalolinta sun warware. Dangin nata sun bayyana, haka kuma 'ya'yan nata ma sun bayyana cikin ƙoshin lafiya. Ko wannan ya isa ya zamarwa bawa ishara. Kamar wata doluwa, kamar kuma wata mara lafiya ita kanta haka take jinta. Ba ta san dalilin da ya sa tun da ta ji su Gwanin jikokin Sarki ne ta ji wata irin kunya, sanyin jiki da kuma mamaki sun rufeta ba. Runtse idanunta ta yi ƙirjinta na bugawa. Kenan da gaske Gwanin ya kasance jikan Sarki ne? Kenan wannan ne dalilin da ya sa duk da be yi rayuwa tare da Mommah ba ya kwaso halayen gidan sarautar? Kenan shi ya sa take ganin halayensa gaba ɗaya sun bambanta da irin gidan da yake ciki? Ashe shi ya sa idan yana wani abun se ka ɗauka ɗan wani ne, ko kuma ɗan gidan wani me sarautar ne? Ko kuma shi kansa ma yana da sarautar ne? Ashe jini ba ƙarya ba ne.. Ashe da gasken shi ɗin ɗan gidan wani ne, jika kuma ga Sarki. Wanda ya yi gadon Izza tun daga kan kakansa, har kuma daga wajen mahaifiyarsa. Wasu halayen kuma ya kwaso su daga wajen mahaifinsa. Ashe ba siya ya yi ba, ba girman kai ba ne, ba kuma ɗaukar kansa wani ba ne, kawai izzar ce ke yawo cikin jininsa. Ba ta taɓa zata ba, ba ta taɓa kawo haka ba. Ita a duk lokacin da za ta gan shi, ko kuma ta ga ya yi wani abun, ba ta kawo komai se tsantsar girman kai da ɗaukar kansa wani. Ashe IZZARSA A JINI TAKE. Ba girman kai ba ne, ba kuma duk wani abu da take ɗauka ba ne. Duk da mutane da dama, ko kuma tace duk wanda ta sani kowa ba ya goyon bayanta a kan kallan da takewa Gwani, ciki kuwa har da Didinta. Dan kuwa da za ta kwana tana faɗin abin da ta saba faɗa a kan Gwani babu wanda ze yadda. Ita a duk mutanen da ta sani ma babu wanda ke ƙinsa, se sonsa da ganin mutuncinsa fiye da kima. Hakan kuma be taɓa damunta ba, a ganinta sun kaasa fahimtarsa ne kwata kwata. Se dai soyayyar da mutanen ke masa na ɗaya daga cikin dalilin da ya sa tsanarsa ta nunku cikin zuciyarta. A ganinta kowa ya kasa fahimtarta. Kowa ya ƙi bin bayanta se shi shafaffe da mai. Ba ta taɓa tunanin da gaske yanda take ɗaukarsa ba haka yake ba se lokacin da ta haƙura, ta yadda za ta zauna da shi. Wato lokacin da suka yi rayuwa a gidan Ummeey. Ba ta san dalilin da ya sa ta kasa fahimtar gaskiya suke faɗa mata ba se a lokacin, duk da a lokacin ɗin ma se ta yi ta ƙaryata zuciyarta duk sa'ilin da ta raya mata haka. Se ga shi yau an sake tabbatar mata. Bayan tabbacin da ta ƙara samu tun bayan zuwansu gidan Mommah.

"Umma ki faɗawa Baba a nan zan kwana.." Wata budurwa ta faɗa tana kallan wata babbar mace da take zaune kusa da ita. Murmushi ta yi tace

"Ba ma se na faɗa ba.. Da ma hakan za a yi."

"Yawwah Umma." Ta faɗa tana murmushi. Su uku ne za su kwana cikin gidan, ba ƙaramin farin ciki

Please Login or Register in order to submit comment