Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min Coffee ne.. So na ji shiru shi ne na biyo baya.. Ban da haka babu komai wallahi."

"Wai me kake nufi da yarinyar nan ne? Na ɗauka ka ce ba ka sonta koh? Toh mun ji kuma mun amince, me ye kuma ya yi saura? Me ye na duk wannan shishshige matan?" Mommah ta faɗa fuskarta a haɗe, dan so take da gasken ta koya masa hankali. Runtse idanunsa ya yi kafin ya buɗe, ya ɗauki wajen second 30 kafin yace

"Mommah.. Don Allah ki dena tuna abin da ya wuce.. Wallahi ina sonta yanzu.. Don Allah ki bar ni ko da ganinta ne na yi." Ya ƙare a marairaice kai ba kace Bad Man ne ba. Shi sam ya ma manta akwai kunya a irin wannan maganar da ya faɗawa Mommahn. Shi dai kawai so yake Mommah ta yadda ya tuba, yana kuma son matarsa yanzun. Ɗauke kanta Mommah ta yi lokacin da murmushi ya suɓuce mata. Se kuma ta juyo bayan ta maida fuskarta kamar ɗazun tace bayan ta yi murmushi kamar na yaƙe

"Ka dena yaudarar kanka Areef.. Ka riga ka yi sake, dan haka ka shirya rubuta mata takardar saki dan kuwa daga nan se gidansu. Yarinya da gatanta ba aura maka ita aka yi dan ba a sonta ba." Be san lokacin da ya ɗaga idanunsa ya kalli Mommahn da sauri ba. Kallanta kawai yake yi yana ji kamar ta yi wani saɓo ne. Da gaske take tana nufin abin da ta faɗa? Wai an ya kuwa yanzu Mommah na ƙaunarsa? Ya tambayi kansa lokacin da idanunsa suka kaɗa, zuciyarsa na wani irin harbawa. Se dai ya kaasa furta komai. Shi kansa wannan lamari ya shammace shi, be taɓa tunanin watarana ze tsinci kansa cikin ƙaunar yarinyar ba. Shin mene ne mafita? Ze iya sakin nata ko kuwa?

"Mommah.." Ya sake faɗa murya a sanyaye. Ɗaga masa hannu Mommah ta yi tace

"Na gama magana Areef.. Ka je zan nemeka" Daga haka ta miƙe ta wuce cikin ainahin palournta. Dafa kujerar gefensa ya yi yana runtse idanunsa. A fili numfashinsa ya shiga fita da sauri da sauri har kuma lokacin be buɗe idanunsa ba. Me ye mafita? Ya tambayi kansa. Ya kai wajen minti 2 a haka kafin ya buɗe idanunsa lokacin da suka rine suka yi jajir. Se a lokacin ya bi inda Mommah ta yi da kallo sannan ya ɗaga ƙafafunsa cike da sassarfa ya fice daga ɗakin.


.. Kai tsaye ɗakin da su Didi ke ciki Mommah ta wuce, da ma Didi take son magana da ita. Se kuwa ta sameta zaune a kan kujerar ɗakin ta yi shiru kamar me tunani. Ƙarasawa Mommah ta yi ta zauna, Didi ta yi murmushi tana gaidata. Ta amsa cikin kulawa kafin tace

"Afrah.."

"Na'am Mommah.." Didi ta amsa da hakan tana tattaro duk wani hankalinta ta bawa Mommahn. Saboda jin yanda ta kira sunanta ta san muhimmiyar magana ce za ta mata.

"Wato duk da na kasance mahaifiya ga Areef amma har yanzu ba na goyon bayan halayensa. Wannan shi ne lokacin da ya dace, ina nufin wannan ce damar da kike da ita da za ki ƙwatowa kanki 'yanci. Yana sonki yanzun dan haka ina neman alfarma a wajenki don Allah ki yi amfani da wannan soyayyar da yake miki wajen taya ni ƙwato shi daga ɗabi'ar nan ta.." Se ta yi shiru ba tare da ta ƙarasa ba, dan yanda ma ta ƙarasa maganar kaɗai ya isa ya nuna maka yanda zuciyarta ta karye. Narkakkun idanunta Didi ta ɗaga ta kalli Mommah. Ta fahimci abin da take nufi dan haka babu amfanin ma se ta ƙarasa. Ita kanta da take amsa sunan matarsa ita kaɗai ta san takaicin hakan da take ji. Ballantana mahaifiyar da ta haife shi. Wadda ta ɗauki tsayin shekaru ba tare da shi a matsayin ɗanta ba. Ga shi kuma yanzun ya bayyana se dai da wata ɗabi'ar da babu wanda ze so ko waye na sa ya kasance da ita.

"Ki dena damuwa Mommah.. In Sha Allah zan yi duk abin da kika ce.. Kuma In Sha Allah Allah ze shirye shi.." Didi ta faɗa ita ma cikin karyayyiyar murya. Murmushi Mommah ta yi kafin ta kamo hannun Didin tace

"Allah Ya yi miki albarka. Ya daidaita tsakaninku nan ba da daɗewa ba. Ya saka miki da alkhairi, Ameen." Ba ta daɗe ba Mommahn ta fice daga ɗakin. Didi ta jinginar da kanta jikin kujera tana ji zuciyarta na sake karyewa.

"Allah Ka taimake ni, Ka shiryi bawan nan naka Ya Allah.." Ta ƙare tana runtse idanunta. Ba ta tsammata ba, se jin zaunawar Lulun kawai ta yi a gabanta da ƙarfi tana dariya hannunta a kan cinyarta. Buɗe ido ta yi da sauri ta kalleta tace a tsorace

"Me ye haka Lulu? Ba ki san yanzu ba ke kaɗai ba ce? Shi ne kike irin wannan abun.. me ye haka?" Ta ƙare tana riƙo hannunta ta ɗagata ta koma kusa da ita. Turo baki Lulu ta yi, ita fa sun fara takura mata, ko me ta yi se su ce wai ba ita kaɗai ba ce yanzu. Toh ashe ma ba sa ta kanta se ta abin cikin nata.

"Da ma Didi ba ta ni kike ba koh?" Ta yi maganar da iya gaskiyarta. Girgiza kai Didi ta yi dan ta lura ita har cikin ranta da gaske take.

"Ke ba fa haka ba ne.. Kin ga shi ai yanzu dole se an kula da shi saboda ingantarsa. Se kin dinga kula sosai Lulu don Allah, ko kuma ki na so mu rasa shi ne?" A hankali kuma se ta kai hannunta kan cikinta kamar wadda za ta jiyo motsin yaron tun yanzun. A sukwane ta girgiza kai tana kallan Didin. Murmushi Didi ta yi kafin tace

"Yawwah.."

"Toh wai da ma ki na son Areef ɗin ne?" Lulu ta faɗi abin da ke ranta tun ɗazun. Da sauri Didi ta buɗe idanunta tana kallan Lulun cike da mamakin dalilinta na faɗin haka.

"Me ya sa kika ce haka?"

"Toh gani na yi ki na ta masa addu'a hadda su kuka." Riƙe haɓa Didi ta yi ta shiga jinjina kai tana faɗin

"Iyeeee.. haka kika shahara Lulu."

"Toh ki ce ƙarya ne mana." Lulu ta yi maganar tana ɗage gira. Ta san yanzu ko me za ta cewa Lulun ba yadda za ta yi ba. Ƙila ma ta maida abin na tsokana.

"Hala ba ki ji abin da Mommah ta faɗa ba?.." Ƙwanƙwasa ƙofar da aka yi shi ne ya dakatar da ita daga maganar da ta soma. Baba Atine ta shigo ta sanar da su saƙon Mommah a kan su fito za a yi dinner. Amsawa suka yi da "toh" Didi ba ta sake cewa komai ba ta miƙe cike da fatan Lulun ta ƙyaleta. Se kuwa ba tace mata komai ba, se ɗaukar mayafin abayar jikinsu da suka yi suka yafa sannan suka fice daga ɗakin. Daidai lokacin da suka fito daga ɗakin ya yi daidai da lokacin da Gwani da Bad Man suka shigo cikin ɗakin. Haka kuma ya yi daidai da lokacin da Iftihal ta fito daga cikin ɗakin da yanzu ita kaɗai ce a ciki, saboda en uwanta da suka tafi saura ita ɗaya da za ta koma ranar da su Mommah za su je gidan. Cikin jin daɗin ganinsu ta tafi da sauri cikin iyayi tace

"Sannunku da zuwa en uwa." Ta faɗa tana murmushi.

"Yawwah." Suka amsa kusan a tare.

"Mu je koh?" Ta faɗa kamar ita ce me gidan. Suna fara takawa ta yi yanda ta yi ta jera da Gwani. Kallan juna Lulu da Didi suka yi kafin suka maida dubansu gaba ba tare da sun ce komai ba. Se suka cigaba da takawa daidai lokacin da Iftihal ta ja kujerar kusa da wadda ta ga Gwani ya riƙe da alama a ita ze zauna. Se dai shi ba abin da yake nufi kenan ba, ya janyota ne dan Lulu ta zauna, se dai kuma har yanzu yana jin kunyar Mommah, wasu abubuwan dole ya dinga haƙura har su bar gabanta. Kafin ma ya gama tunanin da yake ya lura da Iftihal da ke ƙoƙarin zama a kusa da kujerar da ya riƙe ɗin. Kawai se ya zauna a kan kujerar yana ɗaga kansa ya kalli su Lulu da suka kusa ƙarasowa. Daidai lokacin da ya kalleta ya yi daidai da lokacin da ita ma ta kalle shi, ya sakar mata murmushi yana lumshe idanunsa cikin nata. Janye idanunta ta yi tana ɗan rufe idanunta kafin ta buɗe suka cigaba da tafiya. Tun tahowarsu ya kafeta da idanun nan nasa. Tun daga nesa ta tabbatar da lallai yana cikin ɗakin kuma kallanta yake yi. Dan kuwa idanunsa na da matuƙar tasirin da in dai ze kalleta se ta ji hakan, duk kuma se ya saka ta rasa sukuni. Sake gaisar da Mommah Gwani da Bad Man suka yi, ta amsa cikin kulawa. Ita da kanta ta shiga serving na kowa.

"Mommah kawo na.." Tun kafin Didi ta ƙarasa Mommah ta katseta da faɗin

"Yi zamanki Daughter.. babu damuwa." Se ta koma ta zauna. Se da Mommah ta gama da kowa sannan ta koma ta zauna. Se a lokacin sannan kowa ya ja abincin ya fara ci. Se dai ban da Bad Man, da ko kallan abincin be yi ba, se zubawa Didi ido da ya yi. Abin da Mommah ta faɗa ɗazu kawai shi yake tunawa. Maganganun da suka hana shi sukuni kenan, har ya kasa nutsuwa. Yanzu ma kiran nan ma Mommah yq ɗauka wani abun ne, se da suka zo sannan ya ji hankalinsa ya kwanta, da ya fahimci maganar ba a kan Didi ba ce. Gyara zama ya yi yana ɗora hannayensa a kan dinning ɗin kafin ya ɗora tafin hannunsa a haɓarsa. So yake Mommah ta haƙura, ta yadda da shi ta kuma ba shi matarsa dan wallahi ya yi nadama. Kwata kwata ta kasa sukuni, se gyara zama kawai da take yi. Ita kam ta ga ta kanta. Wai yaushe ya yi wannan muguwar chanjawar? Se kace wanda aka chanja? Gaba ɗaya ya zama wani iri. A hankali kuma se abin da Mommah ta faɗa mata ɗazun a ɗaki suka shiga dawo mata. Kenan da gaske yanzun yana sonta? Yana sonta sosai? Irin son da har za ta iya amfani da shi wajen sauya shi?

"Afrah lafiya kuwa?" Mommah da ta lura da ita ta faɗi haka. Kamar za ta yi kuka tace

"Mommah.." Se kuma ta yi shiru ba tace komai ba. Ganin Mommah na shirin kallansa ne ya sanya shi gyara zamansa ya basar. Se a lokacin Didi ta sauke numfashi. Ita kam har yanzu ba ta san ta ina za ta fara ba. Se take jin tsoron yin abin da Mommahn tace mata ta yi saboda gudun ɓacin rana. Kar ta je ba yanda Mommahn ke tunani ba ne ita kuma ta zo ta zaƙe. Se dai ko ma mene ne za ta yi ƙoƙarin yin hakan ko ma me ze biyo baya. A hankali ya kai hannunsa ze ɗauki ruwan da ke ajje kusa da plate nasa. Iftihal ta yi saurin riƙewa tana faɗin

"Haba.. bari na taimaka maka.." Ta yi maganar cikin muryarta da tafi kama da tsantsar iyayi a cikinta. Cokalin da Lulu ke amfani da shi cikin abincin da ke gabanta tana caccakawa kawai ba tare da ta kai ko loma ɗaya ba ne ta dakatar lokacin da ta ji abin da Iftihal ɗin ta faɗa. Haka nan kawai ta ji tana son ganin da wanda take. Ba ma ita kaɗai ba hatta Mommah da Didi se da suka ɗaga kai suka kalleta. Daidai lokacin da ta ɗaga idanun nata se suka sauka a kan Iftihal lokacin da take tsiyaya ruwa cikin wani glass cup. Se ta kasa ɗauke idanunta daga kanta. Har zuwa lokacin da Iftihal ta miƙawa Gwani kofin tana faɗin

"Ga shi.." Ta ƙare tana binsa da wani kallo lokaci ɗaya kuma tana sakar masa wani tattausan murmushi..


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO76*

____ Kaasa ɗauke idanunta Lulu ta yi, se ta ji tana son gani ze karɓa ne ko kuwa ya ya? Hannu Gwani ya miƙa ya karɓa bayan ya ɗan yi wani yaƙe saboda murmushin da ya ga tana sakar masa kar ya yarfata.

"Na gode.." Ya yi maganar a nutse. Wani sabon murmushin ta sake saki tana wani buɗe baki tace

"Ahh me ye na godiya kuma Yayana?" Ta ƙarasa maganar tana ɗaukar cokali ta soma cin abincin, murmushi ya ƙi barin fuskarta. Da alama za ta yi nasara a wannan wasan. Yanzu dai duk wani burinta shi ne ta samu numbersa ta ƙarasa ragowar aikin ko da a gida ne. Ba ta san lokacin da ta sauke idanunta da sauri ba tana jin yanda zuciyarta ta shiga harbawa. A hankali kuma bugun zuciyarta ya soma saituwa, mamaki na kamata. Me ye musabbabin hakan? Tun da ta sauke idanunta ƙasa har suka gama dinner ba ta sake ɗagowa ba. Duk kuwa da tana jin magana sama sama amma ta kasa ɗaga idanunta. Duk yana lura da ita, hatta abincin da ba ta ci ba duk yana lura da ita. Be kawo komai a ransa ba, ya ɗauka ko abincin ne be mata ba.

"Afaaf me za a dafa miki?" Mommah ta tambaya tana kallanta. Se a lokacin sannan ta ɗaga kai ta kalleta ta girgiza kai kafin tace

"Na ƙoshi."

"Ya za ki ce kin ƙoshi? Me kika ci?"

"Ba komai amma na ƙoshi."

"Ba ki isa ba.. Je ki ɗaki zuwa an jima zan aiko kiranki." Kamar jira take, ta tura kujerar da take kai baya ta miƙe ta wuce ɗaki ba tare da ta kalli kowa ba. Binta da kallo Gwani ya yi yana mamakin abin da ya chanjata haka cikin ƙanƙanin lokaci.


.. Washegari tun safe Mommah ta ɗauki Lulu da Didi suka fice daga gidan, ba su suka dawo ba se wajen ƙarfe 3. Daidai lokacin da suke ƙoƙarin shiga sashen Mommah Gwani da Bad suka ƙaraso.

"Sannunku da zuwa Mommah.." Suka haɗa baki wajen faɗar hakan.

"Yawwah sannunku dai.." Ta amsa da murmushi tana kallansu. Tuni Didi da Lulu sun yi gaba dan sun gaisa da safe. Ita ma Mommah bin bayan nasu ta yi, kafin su Gwani ma suka rufa mata baya. Shi dai Bad a ɗarare yake kar ya je Mommahn tace ya juya, be sani ba damar da aka ba shi ko iya ta jiya ce kawai. Se be ji Mommahn tace komai ba har suka isa palournta.

"Afaaf tsaya ki gaisa da mijinki.. Ke kuma Afrah wuce mu tafi.." Mommah ta yi maganar tana kama hannun Didi suka wuce ɗaki. Kamar wani dolo haka ya bisu da kallo. Ya ɗan runtse idanunsa yana buɗewa a lokaci guda. Shi kam jikinsa gaba ɗaya ya yi sanyi da lamarin. Be san girman laifin da ya aikata babba ba ne se Mommah ta masa abu. Duk soyayyar da take masa ajeta gefe take ta masa abin da ta ga dama. A nutse ya juya ya kalli Gwani yace muryarsa kamar wanda ya ƙware

"Se ka fito." Be jira yace komai ba ya fice daga ɗakin, be kuma nufi ko ina ba se wajen motarsa, ya hau ya fice daga gidan.

"Mu je ki zauna koh?" Gwani ya faɗa yana kallan Lulu. Se a lokacin sannan ta ɗaga ƙafafunta kamar me jin tsoron ƙasa ta shiga takawa. Kan kujera ta zauna har lokacin ba tace komai ba. Shi ma neman waje ya yi ya zauna a gefenta, se dai in da ya san ze din ga ganinta.

"Ki na lafiya?" Tambayar da ya soma mata kenan. A hankali ta ɗan ɗaga kanta ta kalle shi, daidai lokacin da yake kallanta, se idanunsu suka shige cikin na juna. Maimakon a da da daga zarar sun haɗa ido za ta ɗauke nata, yanzu se ta kasa janyewa. Se kace wadda take son karanto wani abun cikin idanunsa. Sun kai wajen minti 1 a haka kafin Lulu ta sauke kai da sauri. Ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe idanunsa, ya daɗe be mata irin wannan kallon ba. Yau ɗin da ya mata shi se yake jinsa zam zam. A hankali ya ɗan matsa kusa da ita, ya ɗan rage tazarar dake tsakaninsu. Ya saka hannunsa ya ɗan janye rigar jikinta kafin ya ɗora hannunsa a kan cikinta yace

"Ya Babyna? Fatan dai ba ya wahalar min da ke?" Yanda ta ji wani yamm da tattausan hannunsa ya taɓa fatar cikinta shi ne dalilin da ya sanyata saurin ɗora hannunta kan nasa. Tuni bugun zuciyarta ya ƙaru, burinta kawai ya janye hannunsa, musamman da suke cikin ɗakin da wani ze iya shigowa ya gansu.

"Kar wani ya shigo.." Ta yi ƙarfin halin faɗa tana sake riƙo hannunsa. Cikin basarwa yace

"Babu wanda ze shigo.. Ba ni amsata." Sake waiwayawa ta yi kamar me neman wani. Se dai da ta ga alamar ba shi da niyyar janyewa ya sanyata saurin faɗin

"Lafiya ƙalau." Se a lokacin sannan ya sauke hannunsa. Se gani ta yi ya zame a kan ƙafafunsa, ba ta yi tunanin komai ba, se binsa da kallo da ta yi dan ganin abin da ze yi, duk da yanda take ta ƙoƙarin basarwa amma kamar hakan na neman bijirewa. Soma matso da kansa ya yi a hankali har ya ƙaraso da shi kusa da ita. Maimakon ɗazu yanzu a kan rigar kawai daidai inda ya riƙe ɗazu ya sumbata yana jin wani shauƙi a cikin zuciyarsa. Ji yake tamkar yau ne yaron ze fito. Abin da ba ta tsammata ba kenan hakan ne ya sanyata kawai ta saki baki tana kallansa. Ita wallahi har yanzu idan ya yi wani abun ta kasa dena mamakin Gwani ne. Se kuma ta tura baki tana ƙoƙarin miƙewa ya yi saurin riƙo hannunta yana faɗin

"Yi haƙuri.. na tuba na bi Allah." Ya faɗa lokacin da ya gama miƙewa ya sake zama gefenta. Kamar ba za tace komai ba se kuma can tace

"Toh ina zuwa."

"A'ah kar ki min haka.." Ya faɗa a marairaice wai duk dan ta tausaya masa har da wani langaɓar da kai ya yi.

"Ai dai zan dawo."

"Kin yi alƙawari?" Ya katseta da faɗin hakan. Se ta jinjina kai tana ƙoƙarin miƙewa ya yi saurin saka hannu ya riƙo nata hannun.

"Rufa min asiri.. Yi a hankali." Ya yi maganar bayan ya ɗagota daga kan kujerar da kansa. Kawai se ta cigaba da kallansa kamar wadda ta soma ganinsa yau. Se ta cigaba da takawa zuwa ɗakin, ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba. Maganarsa ta ƙarshe ita ce ta sanyata murmushin hadda girgiza kai. Iska kaɗan ya fesar daga cikin bakinsa kafin ya gyara zama bayan ya sauke ajiyar zuciya.

"Ko dai na zo na tayaka hira ne?" Sam be lura da zuwanta wajen ba se muryarta da ya ji. Tana sanye cikin wata riga da wando masu kyau, duk babu wanda ya kamata a ciki. Ta yi kyau abinta, ta saka earpiece a kunnenta ɗaya, waya kuma ta riƙe da hannunta.

"A'ah babu buƙata." Ya faɗa yana ɗan wanzar da annuri a kan fuskarsa idanunsa na kan ɗakin da Lulu ta shiga.

"Ahh haba dai ai ko ya ya ne dai zama mutum biyu ya fi." Ta ƙare tana neman gefen kujerar ta zauna.

"Barka da wannan lokacin.." Ta yi amfani da faɗin hakan dan kawar da hankalinsa daga wani tunanin.

"Barka.. Akwai abin da za ki yi cikin ɗakin ne?" Ya tambaya, dan ba ya so ko kaɗan ya wulaƙanta wani ɗan adam. Musamman ma ita da take er uwa. Girgiza kai ta yi tana sauke earpiece ɗin kunnenta tace

"A'ah fa.. Wajenka na zo fa kawai." Ta ƙare tana murmushi. Daidai lokacin Lulu ta fito daga cikin ɗakin. Cikin sa'a se idanunta suka sauka a kan Iftihal dake zaune kusa da Gwani. Dakatawa ta yi daga inda take se dai har lokacin nan ɗin take kalla. Kamar wadda ake ja se ta cigaba da takawa zuwa cikin ɗakin. Murmushi Gwani ya saki yana kallan Lulu a nutse kuma cikin kulawa yace

"Sannu da dawowa.. Kin dawo kenan.." Ba tace komai ba Lulu se kallansa da ta cigaba da yi. Iftihal yi ta yi kamar ba ta ji me yace ba, ba kuma ta lura da wanzuwar Lulu a wajen ba, cikin basarwa tace

"Ko dai na haɗo maka tea ne? Na san za ka ji daɗinsa." Wani kallo Gwani ya watsa mata, dan kamar ya soma fahimtar da wata manufar take wasu abubuwan. Ƙirjinta ya buga saboda yanda kallan ya hautsina mata 'ya'yan hanji. Se dai ta sake basarwa ta miƙe kawai dan wucewa kitchen, dan ita babban burinta be wuce ta ƙonawa Lulu rai ba. Duk yanda Lulu ke kai zuciyarta nesa, da kuma yanda take ƙaryata kanta a kan ɓacin ran da take ji ba shi da alaƙa da Iftihal dake tare da Gwani amma hakan ya citira. Ta yi ta yi ta jure ta kaasa. Har wani tafasa zuciyarta ke yi. Yau ɗin tabbas Iftihal ɗin ta kaita bango ainun. Hannu ta saka ta riƙo mayafin Iftihal ɗin ta dawo da ita baya. Saboda Iftihal ɗin ba ta tsammata ba se gata ta dawo baya kamar za ta kifa. Se dai da Allah Ya tsare se ta tsaya a kan ƙafafunta. A fusace ta juya ta kalli Lulu, daidai lokacin da fusatattun kyawawan idanun Lulu ke kanta tana binta da wani banzon kallo. Har ba ta san lokacin da ta buɗe baki tana jin zuciyarta na cigaba da harbawa kamar wadda ta yi mugun gudu ta gaji, ta soma faɗin

"Ke wace irin mace ce mara aji? Wane irin abu ne kike yi haka babu kyan gani? Wani yace miki ana buƙatar wani abu ne daga gare ki? Za ki wani ɗauki tsumman ƙafafunki kin tafi aikin neman suna. Toh ki kama kanki, ki riƙe mutuncinki tun kafin kallan rashin ajin da nake miki ya ƙarasa rushewa gaba ɗaya." Da wani irin kallo Iftihal ke bin Lulu da shi, ba ta taɓa tunanin za ta iya tsayawa tana faɗa mata irin waɗannan maganganun a gaban Gwanin ba. Duk da dai tun kallan farko da ta mata ta san yarinyar ba kanwar lasa ba ce. Amma yanda ta ga ta iya shariya a kan abubuwa, yanda take nuna tamkar ba ta gani ba ko da ta gani kuwa, ya sa ba ta taɓa kawowa a wannan karon ma za ta nuna ta gani ba ballantana har ta tanka. Kunya da haushi suka taru suka haɗarwa Iftihal. Ji take kamar ta saka ihu ko za ta ji daɗi, dan ba shakka wannan yarfin ya shigeta.

"Ni kike faɗawa haka? Ni kike faɗawa haka?" Shi ne abin da Iftihal ta faɗa tana huci, ji take kamar ta kama Lulu ta yi wa shegen duka ko za ta ji daɗi. Se da Lulu ta sake bata wani kallan da ya fi na ɗazu muni kafin ta ja tsaki ta juya ta bar wajen. Dan tsabar takaici da baƙin ciki ita kam Iftihal ba ta sake cewa komai ba se ɗaukar ƙafafunta da ta yi a kunyace, ba tare da ta sake kallan inda Gwani yake ba ta wuce ɗakinta. Tun da ta soma magana yake kallanta har ta kai aya. Kai har ta juya ta shige ɗaki kallanta yake yi. Kawai ya kasa cewa komai, abubuwan da suka faru yanzu su kaɗai ke sake maimaita kansu cikin ƙwaƙwalwarsa. Idan dai har ya lura da kyau kamar kishi ne yake gani a cikin idanun Lulu fa? Kishi dai me suna kishi. Kishin ma kuma a kansa? Kenan hakan na nufin tana sonsa? Tun da dai ba a kishi se a kan abin da ake so. Toh kenan daga wanne lokaci hakan ta faru? Yaushe ta fara son shi amma be ankare ba? Shin abin da yake hasashe yake kuma gani a idanunta haka ɗin ne? Shi kam me ya kamata ya yi idan ba godewa Allah ba?.



... Ya kai fiye da rabin awa a tsaye ba tare da yana komai ba se kallan kwalabe guda biyun da gabansa, kamar wanda ke tunani ko kuma wani abun. Se can dai ya koma ya zauna yana cigaba da kallansu ban da harbawa babu abin da zuciyarsa ke yi, idanunsa sun sake ƙanƙancewa. Wane irin abu ne wannan? Sam ya kasa komai cikin lumana? Shin Mommah me take jira

Please Login or Register in order to submit comment