Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata kwanciyar ko da za ta samu ta yi baccin.

"A'ah ni dai ka.."

"Shhh..!!" Ya katseta da faɗin hakan, kafin ta sake cewa komai yace

"Na ce ki yi baccin ki koh?" Ya ƙare maganar daidai lokacin da ruwan hawaye suka zubo a kan hannunsa. Ya girgiza kansa yana sake mamakin yanda ta chanja gaba ɗayanta kamar ba ita ba. Da dai ta gaji, ta kuma ga ba shi da niyyar sakin nata se kawai ta haƙura, dan har ta gaji da yunƙurin da ta san shi kaɗai ɗin za ta iya.
Shiru ya yi yana saurarar bugun zuciyarsu dake fita kusan a tare, ya ɗan lumshe idanunsa a ransa yana tsara yanda ze cigaba da nemo daga inda hoton ma kansa ya zo wajen Abbati. Tunda abin nan ya faru gaba ɗaya zuciyarsa ba ta hutawa, kullum burinsa ya gano gaskiyar lamarin, wanda hakan ne ze wanke Lulu 100 bisa 100 daga duk wani zargi da ya so shiga tsakaninsu. Tun dai tana ta ƙoƙarin kufcewa har dai ta haƙura saboda yanda jikinta yake babu ƙwari, se komawa ta yi ta yi shiru kawai. Ba ta taɓa kawowa kanta za ta iya yin bacci ba dan har lokacin ta kasa dena kukan, se dai ba tare da ta shirya ba bacci ya zo ya yi awon gaba da ita. Kallan fuskarta ya yi lokacin da ta soma sauke numfashi a nutse, fuskarta ta sake yin fayau kamar ba ita ba. Ya ji wani abu ya tsirga masa tun daga saman kansa har ƙasan ƙafarsa, wanda hakan ya tilasta masa sauke ajiyar zuciya. Bayan shuɗewar wasu mintuna ya soma ƙoƙarin miƙewa tunda dai ta samu baccin. Se dai me? Yanda jikinta yake da zafi, yayin da na shi kuma yake da sanyi, hakan ya yi mata daɗi sosai, yana ƙoƙarin sauketa daga jikinsa ta yi saurin riƙo shi ba tare da ta sani ba. Hannunsa da ta rungumo ya bi da kallo, da alama ba ta san me ta yi ba. Ya ɗan sake ƙoƙarin zamewa se ta sake riƙo shi. Ajiyar zuciya ya sauke yana ɗan lumshe idanunsa sannan ya buɗe su lokaci ɗaya. Har lokacin jikinta da zafin, wanda cikin ƙanƙanin lokaci ya soma wasar jikinsa saboda yanda ta cukwuikuye shi tana baccinta hankali kwance. Duk da fuskarta kaɗai za ka kalla ka fahimci ba daɗin baccin take ji ba. Haka yana ji yana gani ya cigaba da zama don ta yi baccin. Har kusan bayan mintuna da dama ta ƙi sakinsa, da dai ya ga ba ta da niyyar sakinsa se kawai ya gyara zamansa kan gadon ya barta idan ta gama baccin se ya tashi. Ɗan lumshe idanunsa ya yi tunani barkatai na zuwar masa ƙwaƙwalwa..



.... Kwana biyu ta jera tana kai masa Coffee ɗin kamar yanda ya buƙata safe da daren. Kodayaushe idan ta je kaiwa ɗin kuma babu fashi za ta gaida shi.

Yau ma kamar ko da yaushe ta gama haɗa komai cikin ƙaramin cup, ta wuce ɗakin ta yi knocking. Ta saba jin shiru ko da yana ciki kuwa, hakan ne ya sanyata cigaba da tsayuwa har bayan shuɗewar wasu sakanni. Lura da ta yi ƙofar ɗakin a buɗe take ya sanyata saka hannu ta turata. Kai tsaye ta wuce inda ta saba ajjewa ba tare da ta kalli ainahin cikin ɗakin ba. Ta je ta ajje sannan ta soma takawa dan ficewa daga ɗakin. Tozali da wasu kwalabe zube a kan kujera ta yi, wata murfinta yashe a ƙasa yayin da wata take rufe da murfinta. Shi kuma yana kwance a kan gadon, ƙafafunsa ne kaɗai zube a ƙasa yayin da duka gangar jikinsa na kan gado ne. Lokaci ɗaya ta ji ƙirjinta ya buga, ta ɗan sake satar kallan kwalaben. Haka kawai zuciyarta ta bata waɗannan ɗin kwalaben giya ne, kenan ya sha su ne ya bugu shi ya sa yake bacci? Cikin ƙanƙanin lokaci jikinta ya ɗauki rawa, se ta ji komai na son sire mata. Kenan ɗan giya ne dama?

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.." ta faɗa a kan laɓɓanta tana cigaba da kallan kwalaben. Hawaye ta ji suna son taho mata, ta yunƙura da niyyar ficewa, kamar kuma wadda aka riƙo se ta dakata, ta juya ta sake kallan kwalaben. Kawai se ta ƙarasa inda suke, ta sanya hannunta ta ɗauke su, ta ɗan sake kallan inda yake kwance tana jin wani irin yanayi da ta kasa fassara shi. Duk da yanda jikinta ke rawa, zuciyarta ke a ƙuntace, tsoro na mamaye ƙarfin gwiwarta, hakan be hanata ɓoye kwalaben cikin hijab ɗinta ba sannan ta fito daga cikin ɗakin. A hankali ta cigaba da takawa dan ficewa daga sashen gaba ɗaya, karo na farko kenan tun zuwanta gidan. Daidai tana shirin fita Daddy da tun ɗazu yake kiran number Bad Man be ɗaga ba, hankalinsa ya kasa kwanciya se da ya zo da kansa dan duba shi, suka yi kaciɓus. Zuciyarta ta wani irin tsinkewa lokaci ɗaya tana dakatawa.

"A'ah Afrah.." Daddy ya faɗa. Se a lokacin ta sauke ajiyar zuciya sannan ta buɗe idanunta ta kalli Daddyn tace

"Barka da wannan lokaci.." ta yi maganar tana sake ɓoye kwalaben hannunta.

"Barka dai.. lafiya dai koh?" Daddy ya tambaya ganin yanda take a birkice kamar wadda aka biyo. Murmushin yaƙe kawai ta yi tana faɗin

"Ehh.. ehh.."

"Toh madallah.." Shi ne abin da Daddy ya faɗa kawai. Se da ya shige ciki sannan ta iya ficewa duk ta gama ruɗewa kamar wata korarriya. Kai tsaye ɗakin Bad Man ɗin Daddy ya wuce. Ya tura ƙofar ɗakin yana kallan cikinsa. A kan gadon ya hangi Bad Man, cike da mamaki yake kallansa yana tunanin baccin na meye haka? daidai lokacin da hancinsa ya shiga shaƙo masa wani ƙamshi ƙamshi na daban da ya kasa bambance na meye? Se ya ɗauke kansa daga kan Bad Man ɗin ya maida cikin ɗakin dan ganin abin da ke wannan ƙamshin mara daɗi..


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO41*


___A iya hangensa be hango abin da ze iya cewa shi ke wannan ƙamshin ba, wanda zuwa yanzu ƙamshin turaren dake tashi tun ɗazun ya yi tasiri wajen danne shi. Numfashi Daddy ya sauke yana ƙarasawa inda Bad Man ɗin yake, ya saka hannunsa ya ɗan yi tapping na kafaɗarsa. Ko motsawa be yi ba saboda yanda baccin ya masa daɗi.

"Areef.." Daddy ya faɗa yana sake mamakin wannan baccin haka. Se a lokacin sannan ya soma ɗan buɗe idanunsa da suka masa nauyi. Be yi tsammanin akwai wanda ze shigo har cikin ɗakin tashinsa ba, hakan ne ya sa ransa ya mugun ɓaci tun kafin ya ida buɗe idanunsa. Da ƙyar ya ƙarasa buɗe idanun nasa ya zube su a kan Daddy dake tsaye yana kallansa. Mamaki ya kama shi ganin Daddyn da be taɓa zata ba. Da sauri ba tare da ya shirya ba ya tashi zaune a kan gadon ya soma jefa idanunsa cikin ɗakin cike da fatan Daddyn be ga abubuwan dake ajje ba.

"Bacci na meye haka?" Daddy ya faɗa yana kallansa. Sake wurga lumsassun idanunsa ya yi yana ɗan shafa sumar kansa sannan murya a cunkushe ya buɗe baki da ƙyar yace

"Hu..tawa.." ya ƙare yana yamutsa fuska saboda yanda yake ji ma kamar yanzu ya fara yin baccin, idanunsa har wani cigaba da lumshewa suke, se dai se basarwa yake yi kada Daddyn ya fahimci wani abun. Cigaba da kallansa Daddy ya yi, haka kawai wani zargi ya so ya ɗarsu a ransa, se dai har abada ba ya fatan hakan, hakan ne ya sanya shi kauda wannan tunanin yace

"Ka tashi haka nan.. Idan ka shirya ka same ni a parlourna ina jiranka.."

"Toh.." ya faɗa yana sake kauda kansa gudun haɗa ido da Daddyn. Ɗan tsayawa Daddy ya sake yi na tsawon sakanni kafin ya taka ya fice daga ɗakin. Se da Daddyn ya fita sannan ya miƙe da sauri ya ƙarasa ya kulle ƙofar ɗakin kafin ya dawo cikin ɗakin ya soma duba kan kujerar da yana da tabbacin a nan ya barsu kafin bacci ya kwashe shi. Se dai me? Sam babu ko da bottle 1 ne a wajen. Jefar da kujerar ya yi gefe da hannunsa, cike da fatan ganinsu a ƙasan kujerar. Se dai nan ɗin ma babu su babu alamarsu. Hannunsa ya cusa a cikin sumar kansa yana fesar da iska daga cikin bakinsa.

"Kenan Daddy ya gani?" Ya tambayi kansa cikin sarewa. Yamutsa sumar kansa ya yi yana neman waje ya zauna cikin rashin sanin abin yi. Numfashi ya sake ajjewa yana sake tuna idan dai har Daddyn ya gani me ze faru? Ko shi ya sa yace ya zo yana son ganinsa? Ya aka yi ya yi wannan saken? Miƙewa ya sake yi ya shiga zagaye ɗakin, se kuma ya sake komawa ya zauna har lokacin hannunsa ɗaya na cikin sumar kansa. Gaba ɗaya ransa a ɓace yake, ya rasa ma abin da ya kamata ya yi. Sam ba ze wani iya zuwa wajen Daddyn ba anjima, dan be san da wane ido ze kalle shi ba, and idan ya titse shi kuma ya gano ya daɗe yana kwalɓewa ba tare da saninsa ba, wane hali Daddyn ze shiga? Ya san Daddyn da saka abu a ransa, ya kuma san shi da fushi da zafin zuciya, sam be san yanda za ta kaya tsakaninsu ba. Ya ja tsaki a karo na babu adadi cike da haushin kansa da ya kasa tsayawa ya kulle ɗakin ko kuma ya kwashe kwalaben kafin Daddyn ya gani. Miƙewa ya yi ya shige toilet dan watsa ruwa, saboda baccin da ya fice masa a rai gaba ɗaya. Kamar yadda ya saba ɗaukar mintuna masu yawa idan ya shiga wankan, yanzun ma haka ya ɗauka, ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya har lokacin ransa be koma da daɗi ba. Kai tsaye inda ta saba ajje masa Coffee ɗin ya nufa, kamar yanda ya tsammata ta riga ta ajje, dan haka ɗauka kawai ya yi ya soma sha a tsayen da yake, dan yanzu ba shi da sukunin zama. A hankali yake sha yana cigaba da tunanin yanda za su ƙare da Daddy. Har ya gama sha be gama yanke yanda za su yi ba, ya ajje cup ɗin yana girgiza kai lokaci ɗaya yana ɗan lumshe idanunsa, se kawai ya koma kan gadon ya kwanta ba tare da ya fita daga ɗakin ba.

.. A ɓangaren Didi kuwa babu ɓata lokaci ta je ta zubar da bottles ɗin a bayan part ɗin nasu. Duk da yanda tsoro ke ƙoƙarin mamayeta amma hakan be hanata jefar da su ba sannan ta koma cikin ɗakin. Kai tsaye kan gado ta nufa ta zauna ta cure waje ɗaya tana jin wani kuka na taho mata. Tausayin kanta da rayuwarta na kamata. Anya kuwa Abba ya san wanda ya aura mata? Shi ne tambayar da ta tsaya mata a cikin kwanyarta. Ta cigaba da kukanta kawai ko zata samu ta ji sauƙin abin da take ji cikin zuciyarta. Se dai memakon ta ji haushin Bad Man ɗin ya kamata, se ta ji wani irin tausayinsa ya mamaye zuciyarta. Me ya sa yake shaye_shaye? Me ya sa ya fara tun farko? Shin ba yana da iyaye uwa da uba ba? Amma ya aka yi yake shaye_shaye? Shin basu sani ba ne ko kuma sun sani, saboda wasarere da kuma dukiyar da Allah ya basu shi ya sa suka ƙyale shi ya yi abin da ya ga dama? Tambayoyi rututu su ne suke ta yawo a cikin kwanyarta, se dai ta rasa wanda ze bata amsa. Hakan ne ya sanya ta samawa kwanyarta hutu ta haƙura da jerowa kanta tambayoyin da babu me amsa mata. Kwanciya kawai ta yi cikin rashin sanin abin yi. Se dai duk wani motsi da za ta yi se ta tuna da abin da ta gani, haka nan kawai ta ji tana so ta san dalilin da ya sanya yake shaye_shaye. Ta kuma ji tana so ta yi wani abun da ze sanya ya dena yi ko da kuwa hakan na nufin barinta gidan ne. Gaba ɗaya ranar wuni ta yi ba ta da sukuni, hankalinta gaba ɗaya ya ƙi kwanciya, se bugun zuciya da take ta ji, da kuma hawayen da yau ɗin kamar arharsu take yi. Dan kuwa motsi kaɗan se ta ji ƙwalla kawai ta cika mata idanu.


.. Fitowarta kenan daga cikin ɗakin Baba Atine ta shigo cikin sashen. Da murmushi a kan fuskarta ta kalleta tace

"Afrah.." Maida mata da murmushin ita ma ta yi tana gaisheta cike da ladabi. Amsawa ta yi cikin kulawa sannan ta ɗora da

"Ba dai yanzu kika tashi ba?" Se da ta ɗan cuno baki sannan tace

"Bacci ne ya ɗauke ni fa.."

"Toh ya yi kyau.. Hajiya Sa'adah tace gobe idan Allah ya kai mu ki shirya za a aiko a raka ki sashen Hajiya Salma." Rashin gane wace ce Hajiya Salman shi ne ya sanyata amsawa da

"Toh Allah ya kai mu." Ba tare da ta ji komai ba. Baba Atine tace

"Je ki zauna bari na zo na ɗora miki abin da za ki ci." Buɗe idanu Didi ta yi tace

"Kaiii. a'ah Baba Atine ki bar shi zan ɗora da kaina." Girgiza kai Baba Atine ta yi tace

"A'ah wallahi 'yata ki je ki zauna ki huta.." Sake girgiza kai ta yi ta sake nuna mata ta gode. Da dai ta fahimci ba barin nata za ta yi ba, se ta yi murmushi tana sake yabawa da hankalin Didin ta mata sallama ta fice daga ɗakin. Se a lokacin sannan Didin ta wuce kitchen kai tsaye ta ɗora tukunya. Tana tsaye tana ɓare maggi tana cigaba da tunani kamar yanda ta saba. Sam ba ta ji shigowar mutum ba se lokacin da ta ji muryarsa a shaƙe yace

"Kee!!" Ya faɗa a kaurare. Ba ta san lokacin da ta jefar da maggin ba tana juyawa ta kalli inda ta ji maganar. Yana tsaye jikin locker hannayensa duka biyun harɗe a ƙirjinsa. Fuskar nan kamar ko yaushe babu annuri. Ganinsa da ta yi babu shiri ya sanya ta ƙoƙarin ficewa daga kitchen ɗin da sauri. Taku ɗaya ya yi ya saka hannunsa ya riƙo tsintsiyar hannunta dake cikin hijab ya dawo da ita baya jikin locker. Idanunsa ya zuba mata a kan fuskarta ganin yanda ta yi saurin rufe idanunta a matuƙar tsorace

"Buɗe idanun ki." Ya yi maganar cikin bayar da umarni. Girgiza kai ta yi daidai lokacin da kuka ya taho mata ta buɗe baki da ƙyar tace

"Don Allah ka yi haƙuri.."

"Ohh ashe kina sane.. Buɗe idanun ki nace.." ya yi maganar a tsawace se dai ba cikin ɗaga murya ba. Babu shiri ta buɗe idanun nata da suka gama cika taff da ƙwalla. Lumsassun idanunsa suka shiga cikin brown oily eyes ɗinta dake wani sheƙi musamman yanda ƙwalla ta cika su. Ji take kamar ta janye idanunta saboda yanda ta ji bugun zuciyarta na daɗuwa, waɗannan idanun nasa masu kama da na en iska sun mata mugun nauyi cikin nata. Se dai yanda ya tsatstsareta da nasa idanun ya sa ta kasa yin hakan, se barin hawayen ta yi suka soma saukowa zuwa kan kuncinta.

"Me ya hana ki kawo Coffee yau?" Ya yi maganar yana sake riƙe hannunta sosai dan mugunta. Ƙara ta saki saboda yanda ta ji kamar hannunta ze tsinke. Ita wallahi gaba ɗaya ma ta manta yau ɗin nan, wani irin bacci ne ya kwasheta, kuma kafin ta tashi ta manta. Da ta tashi kuma yunwa ce ta tasota ya sa ta sake mantawa gaba ɗaya.

"Open ur mouth and talk.." Ya faɗa a fusace dan ya fahimci kamar iskanci take ji da shi.

"Wallahi mantawa na yi." Ta faɗa muryarta na rawa. Jinjina kai ya yi yana faɗin

"Ohhh.." Ya ɗan yi shiru se kuma ya saki hannun nata da ya riƙe. Gaba ɗaya ta yi ƙasa ta zube a wajen, duk da yanda ya ji ta faɗi ƙasa hakan be sanya shi ƙoƙarin riƙota ba. Se ma watsa mata kallo da ya yi yace yana murza yatsun hannunsa

"Ki sake mantawa kin ji?" Ya ƙare yana wani murmushi da yafi kama da na mugunta. Be sake cewa komai ba ya fice daga kitchen ɗin a ransa yana jinjina taurin kai irin na yarinyar nan. Amma ze koya mata hankalin da ba za ta so ta sake cewa ta manta ba ta masa abin da ya sakata ba.
Riƙe ƙugunta ta yi bayan ya fita daga kitchen ɗin tana fashewa da kuka. Duk da ta ji abin da yace ba tace komai ba saboda haushin abin da ya mata. Se da ya fita sannan ta bishi da kallo tana faɗin a kan laɓɓanta

"Mugu kawai.." ta yi maganar tana miƙewa tsaye saboda motsin girkin dake kan wuta da ta ji.
Ta yadda za ta cigaba da kai masa Coffee ɗin, se dai wallahi ze ga ɓarna a kan kayansa. Se ta yi amfani da wannan damar ta hana shi sakat dan kuwa ta ci alwashin ko sau nawa za ta ga wani abun da ya danganci shaye_shaye a cikin ɗakin nasa se ta ɗauka ta zubar se dai ko me ze yi ya yi.



... A hankali ya maida idanunsa kan fuskarta dake kan ƙirjinsa, yanda take ɗan yamutsa baby face ɗinta se ta matuƙar yin kyau. Sauke numfashi ya yi yana jin sanyi a ransa, dan dama tun ɗazun yake ƙoƙarin zameta daga jikinsa amma ta ƙi ba shi haɗin kai, yanzu kuma daga yanda take yamutsa fuska ya fahimci tashi za ta yi daga baccin. A hankali ta ida buɗe idanun nata, se kuma ta yi saurin rufe su sannan ta sake buɗewa. Still dai a kan fuskar Gwani ta sauke idanun nata, sake buɗe idanun ta yi dan tabbatar da abin da idanun nata ke gani. Se dai me? Jinta da ta yi kane_kane a jikin nasa ya sanya ta ji ƙirjinta ya buga lokaci ɗaya kanta na sarawa. Da wani irin sauri da kuzarin da ba ta san tana da shi ba a yanzun ta wani hantsila cikin sakannin da basu wuce 3 ba se ga ta a ƙasa. Duk da faɗuwar da ta yi da kuma yanda wani jiri ya ɗebeta hakan be sanyata haƙura ba se da ta koma gefe ta takure tana jin wani irin kuka na taho mata. Kallanta ya yi a nutse, se kuma ya sauka daga kan gadon jikinsa a sanyaye ya wuce toilet dan ɗaura alwala, zuciyarsa cike fall da tunani barkatai.
Babu jimawa ya fito ya ƙaraso inda take a hankali ya furta

"Ya jikin naki?" Shiru ta yi tana ji kamar ta yi masa shiru, se dai kawai ta buɗe baki ba tare da ta kalle shi ba tace

"Da sauƙi.."

"Allah ya ƙara sauƙi.. Ki tashi ki yi sallah, ki yi wanka za mu je asibiti." Jinjina kai kawai ta yi har lokacin ba ta kalle shi ba, kanta na kan cinyarta duk da yanda take jin gaba ɗaya jikinta na ƙamshin Gwanin nan da suka san shi da shi. Se sauke numfashi take yi tana ɗan mammazewa dan kar ta cigaba da shaƙar ƙamshin nasa, dan har lokacin numfashinta ya ƙi saituwa, ji take kamar har yanzun tana cikin jikinsa ne. Ficewa ya yi daga ɗakin kai tsaye ya wuce masallaci. Tafi minti 2 zaune a wajen bayan fitarsa ba tare da ta motsa ko nan da can ba ne. Se da ta gaji dan kanta duk da har lokacin zazzaɓin jikinta na nan, haka ciwon kan ma na nan, se dai sam ba ta son abin da ze janyo ya sake taɓata, hakan ne ya sanya ta yin iya bakin ƙoƙarinta wajen miƙewa ta wuce toilet ɗin.

... Kallansu Ummeey ta yi lokacin da suka shigo cikin ɗakin tace tana kallan Lulu cike da tausayawa, ganin tun zuwanta gidan har lokacin jikinta ya ƙi daɗi.

"Sannu kin ji en nan.. Allah ya ƙara sauƙi."

"Ameen" Gwani ya amsa da hakan yana miƙewa.

"Ummeey bari mu wuce, kar rana ta yi."

"Ya kamata kam, gwara ku je da wuwwurin, kwa samu ku dawo kafin rana ta ƙwalle." Ummeey ta amsa masa da hakan. Se a lokacin Lulu ta fara ƙoƙarin tashi idanunta a rufe saboda jirin da har yanzun ba ta dena jinsa ba. Ta ɗan yi luu za ta faɗi, lura da hakan da ya yi ne ya sanya shi kai hannu dan tarota se kuma cikin ikon Allah ta tsaya a kan ƙafafunta.

"Sannu.." Ummeey ta sake faɗa cike da tausayawa. Gaba ta yi yana biye da ita har suka fice daga gidan. Duk iya ƙoƙarinta da jarumtarta ta aro take takawa sanda suka fito ɗin. Shi kam tausaya mata yake yi, ganin lokaci ɗaya ta zabge, ta rame. Se yanzu ya fahimci ita ɗin wace irin yarinya ce, ta cika saka abu a ranta. Yanzu tunda wannan abun ya faru take ta kukan da ya ƙi ƙarewa har ya ja mata ciwon kai, daga nan kuma se zazzaɓi. Ko da yake dole ne ta damu, shi kansa da ba a kansa abin ya faru ba hankalinsa ya ƙi kwanciya, bare kuma ita.



.."Kina ina?" Abeey ya faɗa sanda ya shiga cikin ɗakin. Ummeey ta amsa da

"Gani nan Malam.." ta faɗa tana ƙarasowa inda yake.

"Ai zama be ganki ba, maza ki shirya ki tafi asibitin da yaran nan suka je, kin ji sun riƙe yarinyar se ta kwana."

"Subhanallahi.." Ummeey ta faɗa tana ɗora bayan hannunta a kan haɓarta. Se kuma ta ɗora da

"Toh Allah ya bawa baiwarsa lafiya. Ya kira can gidan nasu ne?" Ta tambaya tana kallan Abeeyn.

"Yana ƙoƙarin kiransu dai yanzu."

"Yawwah toh.. bari na shirya." Ummeey ta faɗa tana komawa cikin ɗakinta dan shiryawa.


.. A nutse ya gaishe da Ammin cike da girmamawa.

"Ya Ummeyn taka? Ya haƙuri da Afaaf?" Ammi ta tambaya saboda sanin halin ɗiyar tata. Se ya yi murmushi kawai ba tare da ya amsa ba. Hakan ne ya sanya Ammi faɗin

"Ka cigaba da haƙuri da ita kaa ji?" Se a lokacin ya buɗe baki yace

"Babu wani abu da take fa.. yanzun ma ba ta jin daɗi ne muna asibiti shi ya sa nace bari na sanar.."

"Subhanallahi.. ya salaam. Wanne asibitin ne?" Ammi ta faɗa a ɗan ruɗe. Be ajje wayar ba se da ya sanar da ita asibitin sannan suka yi sallama ya ajje wayar. Cigaba da zama ya yi natsawon mintuna cikin asibitin, duk yanda ya so haɗuwa da Abbati a yau ɗin hakan ba ze yiwu ba dole se dai ya haƙura. Babu daɗewa Ummeey ta iso asibitin, lokacin Lulun ta yi bacci a kan gadon asibitin. Waje ta nema ta zauna bayan ta je ta duba jikin Lulun. Ta kalli Gwani a nutse tace

"Affan.."

"Na'am Ummeey." Ya amsa da hakan yana kallanta.

"Anya yarinyar nan ba ciki gareta ba kuwa Affan?" Ummeey ta faɗa a sanyaye dan ta gaji da barin tunanin da take yi cikin ranta. Ta san shi ɗin ba sanin laulayin ciki ya yi ba, ita ma kuma Afaaf ɗin ta san ba sani ta yi ba. Dan haka ita dai tana ganin gwara a jarraba tunanin nata. Be san lokacin da dariya ta ƙwace masa ba, kamar ba Gwani ba, se dai ita kanta dariyar cikin natsuwa yake yinta.

"Ka ga mun ja'iri.. Hala kakarka ce ni da za ka zauna ka na min dariya dan na yi magana." Ɗan lumshe idanunsa ya yi kafin yace

"Ummeey ba fa haka ba ne.."

"Likita ne kai Affan? A jarraba gwadata, ka san wasu yaran haka suke fama idan suna da ciki. Sun dinga yin rashin lafiya kenan.. Gwara idan aka gane se a san matakin da za a ɗauka." Ummeey ta ƙare maganar da za ka fahimci da iya gaskiyarta take yinta kuma babu wasa. Ɗan shiru ya yi yana tunanin abin da ze cewa Ummeeyn ta bar wannan maganar, tunda dai shi ya riga ya san babu wani ciki, wata matsalar daban ta janyo mata ciwon. Se dai hatta Ummeeyn ba ya son faɗa mata abin da ya faru ɗin nan, duk da ya san Ummeeyn me fahimta ce a ko da yaushe, amma a irin wannan abun be san da wanne ido za ta kalla ba, shi ya sa ko da wasa ma be yi mata maganar ba..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO42*

Not edited ☹️

___"Ummeey.." Gwani ya faɗa yana kallanta. itama kallan nasa ta yi daidai lokacin da

Please Login or Register in order to submit comment