Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jin muryar za ka ce yana cikin fushi ne, fushi ma na sosai kuwa.

"Tashi.." Har cikin kanta ta ji muryarsa, saboda yanda ba ta yi tsammanin jin muryar wani ba, ba ta kuma san da wanzuwar wata halitta ba bayan ita da Little tun bayan da ta tafi tunanin har yanzu da ta dawo. Don haka a zabure ta buɗe jajayen idanunta ta watsa su kan Gwanin dake tsaye shi ma yana kallanta. Yanayin yanda ta kalle shin ba tare da ta shirya ba ya sanya ƙwayar idanunsu sarƙewa cikin na juna a karon farko kenan. Cikin lokaci ƙanƙani zuciyoyi biyu suka harba, kowanne kuma da abin da yake saƙawa. Saurin ɗauke idanunsa Gwani ya yi yana sake gyara tsayuwarsa gami da riƙe wayarsa sosai. Karon farko a rayuwarta da ta ji ta kasa yiwa Gwanin musu ko da kuwa gwadawa ne, se ta ji gaba ɗaya wani irin tsoro ya zo ya bi ya mamayeta. Haka nan kawai ta ji ta kasa sukuni da zuwansa wajen, gani take kamar akwai abin da ya kawo shi. "Ko dai a kan abin da Mami ta faɗa mata ne?" Ta tambayi kanta tana tashi zaune gaba ɗayanta. Duk da yanda duk ta soma sire masa, mamaki da kuma tunanin idan da gaske ta aikata abin da ake zarginta da shi me ze biyo baya? Hakan be hana shi mamakin yanda ta tashi zaunen kamar yanda ya umarceta ba tare da gardama ko wani abin makamancinsa ba. Ƙirjinta wani irin bugawa yake yi, duk da bayan ta tashin tazarar dake tsakaninsu ta ragu, amma hakan be dameta ba sam, damuwarta ɗaya shi ne jin abin da ze fito daga bakinsa. Kamar kuwa ya san take tunani se ya soma faɗin

"Afaaf.." Ba ta san lokacin da ta sake kallansa da narkakkun idanunta ba waɗanda suke cike taff da ƙwalla kamar ba yanzu ta gama kuka ba. Tun zuwanta gidan be taɓa kiran sunanta ba, ko da a makaranta ne se da dalili yake kiran sunan. Dan haka shi kansa se da ya ji shi daban, yayin da ita Lulu duk da halin da take ciki, hakan be hanata ji kamar ba sunanta ya ambata ba, saboda yanda sunan ya fito daidai daga cikin bakinsa. Ba ta kai ga amsawa ba ta tsinto muryarsa yana faɗin

"Me ya sa kika zaɓi rayuwar nan? Me ya sa kika zaɓi zubarwa da kanki mutunci da na iyayenki? Me ya sa ba kya so ki zama 'ya ta gari wadda iyayenta za su yi alfahari da ita? Me ya sa kika so ɓata rayuwarki da ƙananun shekarunki? Shin ba kya tunanin sakayyar da zaki samu tun a nan gidan duniya ballantana kuma a can? Me ya sa kika zaɓi rayuwar da tafi kama da ta dabbobi? Me ya sa?" Ya yi maganar yana kallanta. Kallansa take yi sosai kamar me son gano wani abun daga cikin fuskarsa. Kenan dai da gaske Mami take abin da ta faɗa, shi kenan shi ma yana mata kallan er iska. Daidai lokacin da wasu hawaye masu ɗumi suka soma zubowa daga cikin idanunta, ta lumshe idanun nata tana jin yanda jikinta ya ɗauki rawa fiye da ɗazu.

"Ban sani ba.. ban san a kan me kake magana ba.. Wallahi ban sani ba.." ta faɗa cikin raunanniyar murya kamar ba Lulu ba. Ɗan rufe idanunsa ya yi lokaci ɗaya yana buɗe su a lokaci ɗaya. Gaba ɗaya ma shi zancen ba ya so, ba kuma ya so a ja da nisa. Musamman yanda yake jin kansa na cigaba da sarawa tun lokacin da abin ya faru har zuwa yanzu. Wayarsa ya juyo da ita zuwa kan fuskar Lulun ba tare da ya kalli wayar ba. Da ƙyar ya iya buɗe baki yace

"Wace ce wannan?" Ya yi tambayar yana tsareta da idanunsa masu mugun kwarjini. Kamar wadda ta soma ganin waya a yau haka ta bita da kallo, daidai lokacin da idanunta suka sauka a kan hoton ta ji kanta ya shiga juyawa kamar an ɗagata ana juyi da ita. Ba tare da ta sani ba ta miƙe tsaye har lokacin idanunta da suka tsaya ƙyam a kan wayar suna kai ba tare da ko ƙiftawa ne ta yi ba. Ta kai hannunta dake wani irin rawa ta karɓi wayar tana cigaba da kallan hoton. Idan ka ganta se ka ɗauka wadda ba ta taɓa ganin waya ba ce. Se dai tsananin mamaki da ruɗewa sune suka sanyata hakan, suka kuma sanya ta kasa furta komai, ta kuma kasa aiwatar da komai bayan kallan wayar da take. Tunda take kallan hoton yake cigaba da kallan fuskarta yana nazarin yanayinta. Wani irin jiri da ta ji ya kwasheta yana shirin watsar da ita ƙasa, shi ne ya sanyata saurin zubewa a ƙasa kawai wayar hannunta na suɓucewa idanunta a lumshe. Gaba ɗaya ganinta se da ya ɗauke na wucin gadi, ƙwaƙwalwarta ta dena aiki na wucin gadi. Har tsawon minti 1 ba ta furta komai ba. Se da ta yi ƙarfin hali wajen ganin ta buɗe baki ta soma magana, maganar tata ma da gaba ɗaya ta dusashe, haka zalika fuskarta ita kanta ta koma kalar tausayi, kai ba zaka taɓa cewa Lulu ba ce. Girgiza kai take yi a sa'ilin da ta soma magana cikin wani irin kuka me tsuma zuciyar me sauraro

"Ba haka nake ba wallahi.. Ba haka nake ba.. Wallahi ba haka nake ba.." Shi ne abin da take maimaitawa kawai tana cigana da girgiza kai. Ɗan lumshe idanunsa Gwani ya yi kamin yace

"Wace ce a jikin hoton nan?"

"Ni ce.. Amma ban san waye ya ɗauka ba.. Ban sani ba wallahi.." Haka kawai ya ji bugun zuciyarsa ya ƙaru, kenan tana nufin da gasken ita ce rungume da wani? Kenan hakan ta faru, hoton ne kaɗai ba ta san an ɗauka ba?. Se ya ji gaba ɗaya ya sare da lamarin, jikinsa ya yi wani mugun sanyi, kamar yanda ɓacin ransa ya ƙaru. Ko bi ta kan wayarsa be yi ba ya fice daga ɗakin. Wani sabon kukan ta fashe da shi a fili tana faɗin

"Na shiga 3.." ta faɗa kanta a tantagaryar ƙasa hawayen na zuba a ƙasan.


... A bakin ƙofar sashen suka haɗu da Atine. Cikin girmamawa ta gaida shi, ya amsa kamar ba ze ce komai ba se kuma yace

"Ina me coffee..?" Ya tambaya a yatsine. Har ga Allah ba ta gane abin da yake nufi ba, hakan ne ya sanyata faɗin

"Yallaɓai ban fahimta ba.." ta faɗa tana murmushi dan kar ta je ya gwaɓa mata magana. Yatsine fuska ya yi kamin yace

"Yarinyar da ke dafa Coffee tana ajje min.."

"Aiyo Afrah kenan.." Wayar hannunsa ya ɗan danna sannan yace

"Saƙo zan ba ki.." ya ɗan dakata a nan kafin ya ɗora da

"Ta cigaba da kawowa morning nd night.." Jin abin da ya faɗa ne ya sanya Atine jin wani irin daɗi, ko babu komai wannan ɗin matakin nasara ne. Wannan ɗin kuma nasara ce babba. Gyara tsayuwarta ta yi tace cike da fatan ya amince da abin da za ta faɗa ɗin

"A min aikin gafara Yallaɓai.. Ka da Hajiya Salma ta ɓata min idan ta ji na shiga harkar ka da yarinyar nan.." Kallan Atine ya yi kamar wata sa'arsa sannan yace

"Uhmm.. Ki faɗa mata ni na saka ki.. Maza je ki.." Har ranta ba ta ji daɗi ba, ta so da kan shi ze yi wa Didin magana ko babu komai sa ɗan soma magana. Se dai kuma tunda har aka zo nan ɗin ta san In Sha Allah za a zo inda suke fata.

"Toh.." ta faɗa tana juyawa zuwa ciki. A cikin ɗakin ta tarar da Didin tana kwance idanunta a buɗe, da alama tunani take yi. Da murmushi Atine ta ƙarasa tana faɗin

"Tashi ɗiyata.." Babu musu ta miƙe ɗin tana kallan Baba Atinen.

"Kin san me ya faru? Ina tunanin Allah ya karɓi addu'o'inmu.. Yanzun nan Areef ke ce min na faɗa miki ki dinga kai masa Coffee safe da dare.. Kin ga wannan ɗin ai matakin nasara ne.." Tura ɗan ƙaramin bakinta ta yi tana tuna rashin kirkin da ya yi mata, shi ne kuma yanzu ze wani aiko a faɗa mata ta dinga kai masa Coffee. Lallai ma wannan mutumin.

"Baba Atine Amma fa shi ne ya koro ni shi ya sa na dena.." ta ƙare dai cikin tura bakin. Murmushi Atine ta yi tace bayan ta riƙo hannun Didi

"Ki yi haƙuri ɗiyata.. In Sha Allah komai ze wuce, na san abun da ciwo amma ki daure wataran ze zama tarihi kin ji?" Jinjina kai kawai Didi har ranta tana jin babu daɗi, dan wukaƙancin da ya mata har yanzu ba ta manta ba. Hango angry fuskar nan tasa ta yi lokacin da yana faɗa mata magana, ta murguɗa baki a kan laɓɓanta ta furta

"Mutum se baƙin hali da son wukaƙanta wani.."

.. Kafin ya ƙarasa parking space wayarsa ta shiga ruri, be damu da hakan ba ya cigaba da takawa ya shige cikin wata hamshaƙiyar mota. Se a lokacin ya fito da wayar tasa yana shirin ajjewa wani kiran ya shigo. Ganin me kiran ne ya sanya shi jinginar da kansa jikin kujera ya kara a kunnensa.

"Ka na ina?"

"Ina gida.."

"Ka zo ina parlourna.." Daddy ya faɗa. Kamar yace fita ze yi se dai kawai ya amsa da

"Toh" yana katse wayar.

Daddy na zaune a kan kujera yayin da Mom ma ke zaune kan kujera suna ɗan taɓa hira. Ta saki murmushi lokacin da ta ga Bad Man ɗin ya shigo. Ya nemi waje ya zauna, bayan sun gaisa Daddy ya kalli Mom yace

"Za ki iya ba mu waje.."

"Haba Rankayadaɗe.. Yanzu magana ma da ɗana a ce se ba na wajen za a yita?" Ta faɗa tana buɗe idanu cike da iyayi kamar ƙaramar yarinya. Girgiza kai Daddy ya yi yana faɗin

"Kaiii.." Se kuma ya ɗora da

"Toh ba se kin saka mana baki ba"

"Ba zan saka ba." Ta faɗa tana gyara zama. Maida dubansa kan Bad Man Daddy ya yi yace

"Ya aikin? Ya kuma matar taka?" Jin tambayar ya yi kamar wani saɓo, hakan ne ya sanya shi ɗan taɓe baki yace cikin basarwa

"Aiki Alhamdulillah.."

"Wajen matar taka fa?" Daddy ya tambaya yana kallansa, jin da ya yi ya basar da tambayar. Da sauri Mom tace

"Amma ai se da soyayya ake sanin wannan koh?" Wani kallo Daddy ya watsa mata irin na gargaɗi, wanda shi ne ya tunasar da ita ɓaran ɓaramar da take shirin yi. Duk da irin gargaɗin da Aunt Makiyy ta yi mata amma tana ƙoƙarin ta basu matsala da shegen bakin nan nata.

"Tashi ka je.. Zan neme ka." Daddy ya faɗa yana kallan Bad Man.

"A huta lafiya.." ya faɗa yana maida dubansa kan Mom dake zaune kamar an dasata ta kasa kallan kowa yace

"Bye Mom.." Daga haka ya fice daga ɗakin. Miƙewa kawai Daddy ya yi ya bar parlourn ba tare da yace da ita komai ba. Duk se ta sha jinin jikinta, lallai idan ba ta yi a hankali ba za ta janyo wannan matsalar ta jima musu ba tare da sun yi maganinta ba.


... "Ki fito Abba na jiranki.." Wannan kalmar se da ta kusa tafiya da numfashinta. Ta juya da niyyar yi wa Gwanin magana se dai tuni ya fice daga ɗakin. Ta juya ta kalli gefe, ta sake kallan gefe kamar me neman wani abun. Shi kenan ita kam yau tata ta ƙare, ta shiga uku ta lalace. Mami ta gama da ita, Mami ta cuceta ta taƙaici rayuwarta. Duk soyayyar da take mata amma ta rasa da abin da za ta saka mata se wannan. Me ya sa Mamin ta mata haka? Miƙewa ta yi duk da yanda jiri ke ɗan ɗibarta, hakan be hanata miƙewa ba tana hana kanta fitowar kukan da ya tsaya mata. A hankali ta shiga takawa, dama ba wani jiki ke gareta ba, ga kuma jirin dake kwasarta, se take ji kamar iska za ta kwasheta saboda yanda take kaɗata kamar wata bishiya. A ƙofar ɗakin ta tarar da Gwani. Fitowarta da ya gani ya sanya shi yin gaba. Ganin haka ne ya sanyata bin bayansa tana sauke numfashi da sauri da sauri kamar me shirin fashewa da kuka. Da sallama ya shiga cikin ɗakin, tana biye a bayansa, ba ta san lokacin da ta zube a ƙasa ba tana runtse idanunta. Fita Gwani ya yi daga ɗakin ya rage daga Abba se Little a cikin ɗakin. Little ya kalli Abba yace

"Abba Lulu se kuka take yi.." Da mamaki Abba ya kalli Lulu, daidai lokacin da ta yi ƙarfin halin faɗin

"Abba sannu da zuwa.." ta faɗa tana jira ta ji ta inda Abban ze fara. Se dai ga mamakinta se ji ta yi yace

"Ashe har yanzu ba ki kwantar da hankalinki a kan auren nan ba Afaaf? So kike ki ɗorawa kanki damuwa koh? Ashe ban isa na yanke hukunci a kan ki ba? Har yanzu kin kasa haƙuri ki karɓi zaɓin da na miki? Shi ne kika zauna ki na ta kuka kenan har yanzu ba ki haƙura ba? Afaaf ashe ban isa dake ba.." Da mamaki ta ɗaga jajayen idanunta ta kalli Abba, se ta shiga girgiza kai, sannan ta soma faɗin

"Abba wallahi na haƙura.. na haƙura wallahi.. Abba ka isa da ni don Allah ka yi haƙuri ka min afuwa. Na haƙura wallahi Abba, ba zan sake kukan ba." Ta faɗa tana kai hannunta kan fuskarta ta shiga goge hawayen fuskar tata.

"Allah ya yi miki albarka. Allah ya ba ku zaman lafiya.. Allah ya miki albarka.." ya faɗa cikin matuƙar jin daɗin abin da ya fito daga bakin Lulun. Ita kam ba ta kuma san me za tace bayan wannan ba, ta riga ta san tsana ce a tsakaninta da Gwani, se dai daga ɗazu zuwa yanzu ta ji tsanar tasa ta ragu a cikin zuciyarta. Ta riga ta san har abada ba za ta so shi ba se dai tunda har ya iya ɓoye abin da ya faru ba tare da ya faɗawa Abba ba ita me iya cigaba da zama cikin gidan ne, ko babu komai ta bi umarnin Abbanta ta kuma cigaba da zama da Gwanin har lokacin da ze gano gaskiyar abin da ya faru. Ya gane ita ɗin ba yadda yake tunani ba ce. Da ƙyar ta iya amsawa da "Ameen" da dashashshiyar muryarta. Babu laifi sun ɗan taɓa hira, duk da hirar duk amfani da hakan Abba ya yi wajen sake yi mata faɗa sosai a kan zaman auren. Ita kuwa ba wani sosai take fahimta ba saboda har lokacin hankalinta a tashe yake, zuciyarta kuma ta kasa hutawa da tunanin yanda za ta fahimtar da Gwani gaskiyar al'amari.

"Toh bari mu tashi mu tafi.. Zan kuma tafi da Little kin san gobe za a koma makaranta.. Idan kuma aka yi hutun da za a yi nan da en kwanaki ze je wajen Didi.." Kallan Little ta yi tana jin sam babu daɗi, se dai dama ta san dole ze tafi. Don haka tace

"Toh Abba.. a gaida min da Ammina.. Sannan kuma ina so na yi waya da Didi don Allah.." ta faɗa da muryarta dake rawa.

"Babu damuwa.. ki faɗawa mijin naki idan ya amince ranar da za a kawo muku kayan ɗakin ku se a haɗo miki da wayar.. Ko kuma ma dai za mu yi magana da shi kawai, zan ba shi number da za a sameta se ku yi magana." Har ranta ta ji wani irin sanyi, ko babu komai za ta samu su tattauna da er uwarta a kan wannan abun.


... Tana takure a kan gadon dan ta kaasa sake gwada shiga ɗakin nan. Tana jin lokacin da ya shigo ɗakin, ta ɗauka ko ze sake mata maganar ne ta masa bayani amma ta ji shiru, dan shi tunda ya shigo ɗakin ya nemi waje ya zauna ba tare da ya kalli inda take ba.

"Kenan ya yadda hakan nake?" Ta tambayi kanta cikin karyewar zuciya. Hakan da ta raya a cikin zuciyarta shi ne ya sanya zuciyarta saurin karyewa, se ta shiga sauke ajiyar zuciya alamar kuka take shirin yi. Kukan da yanzu ba ya yi mata wuya.

Daga inda yake zaune yana jin yanda take jan sheshsheƙa a hankali, kamar ya share se kuma ya ga rashin dacewar hakan. Bayan kusan minti 1 ya miƙe a nutse ya soma takawa. Hannu ya saka ya yaye labulen idanunsa a kan gadon, jin motsinsa ne ya sanyata saurin tashi zaune a kan gadon ta kalle shi da fuskarta da ta zama kalar tausayi. Ita burinta ɗaya kawai ya fuskanceta, ya fahimci abin da take nufi, ya fahimci abin da ya gani ba shi ne gaskiya ba, wani ne yake son ɓata masa suna, wanda ba ta san waye shi ba. Kuma saboda tsabar ruɗewa ma ba ta taɓa kawowa kanta idan aka nemo Mami za a ji daga ainahin inda komai ya fito ba. Ƙarasawa ya yi cikin nutsuwar dai ya nemi gefen gadon ya zauna yana kallanta yace

"Kukan fa?" Ya faɗa a nutse kamar babu abin da ke faruwa. Kai ta girgiza lokacin da wasu sabbin hawayen suka zubo a kan kuncinta tace

"Ka ƙi ka saurare ni.. Zuciyata na dab da tarwatsewa wallahi" ta faɗa da iya gaskiyarta saboda ita kaɗai ta san abin da take ji a gaba ɗaya jikinta. Ɗan lumshe idanunsa ya yi yana ji a karo na farko tausayinta ya kama shi. Duk wannan rashin kunyar babu ita, duk wannan ji ji da kan babu shi, ta koma wata abar tausayi, gaba ɗaya ta zama kamar ba ita ba, se kace an chanjata.

"Shi kenan, ya isa haka.. Faɗa min waye a cikin hoton nan?" Ganin tana ƙoƙarin fara magana duk da kukan take yi ya sanya shi girgiza kai yace

"Kukan ya isa haka. Idan kuma cigaba za ki yi in tashi in tafi." Ya yi maganar yana ƙoƙarin miƙewa. Da sauri tace

"Na dena don Allah.." ta faɗa tana kai hannunta fuskarta ta shiga share hawayen fuskar tata. Se da ta gama gogewa sannan ta shiga sauke ajiyar zuciya kafin da kukan ya tsaya ta soma faɗin

"Ban san waye shi ba, mun zo wucewa kawai ya rungume ni.. A lokacin kuma se da na mare shi saboda ganewar da na yi ba mutumin arziƙi ba ne.. Wallahi ban taɓa ganinsa ba, ban taɓa sanin waye shi ba.. ba kuma ni da masaniya a kan hoton da aka ɗauka. Ni ba haka nake ba wallahi, ko waye za ka tambaya.." Shiru ya yi yana nazarin maganganun nata, yana kuma cigaba da kallanta kamar me son gano gaskiyar abin da ta faɗa daga cikin fuskarta. Yanayinta kaɗai ya isa ya nuna masa abin da take faɗa gaskiya ne, musamman yanda ta gama ruɗewa cikin mintuna kaɗan. Gaba ɗaya kuma ta fita a hayyacinta kamar ba ita ba. Har kuma ta zauna tana neman da ya saurareta, shi ɗin da ko magana ba ƙauna take ta haɗa su ba. Kenan idan dai har ya fahimci zancenta da kyau akwai wani abun a ƙasa. Se dai duk da haka akwai wani abun shi ma da yake so ya ji amsar daga bakinta ba a bakin wani ba. Se dai kafin nan se ya fara da

"Za ki iya shaida fuskarsa?" Tun kafin ya dire tambayar ta shiga jinjina kai, tana jin wani sanyi na ratsata. Ko babu komai ta samu ya fahimceta ko da ba duka ba ne..

.✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO39*


__Shi kenan.." ya faɗa yana miƙewa. Se ta bi shi da kallo kamar wata sokuwa, daidai lokacin da ya sake komawa ya zauna yace yana kallanta

"An taɓa ganinki za ki shiga wani gida, gidan da mutane da dama sun san na su waye. Wanda mutane kaɗan me ba su sani ba saboda rufesun da ake yi.. Me ya kai ki gidan?" Ya tambaya yana kafeta da idanunsa. Kallan nasa dai take yi ta kasa furta komai. Se da ya kai ƙarshen maganar tasa sannan tace

"Wanne gida?" Ta tambaya da muryarta dake a dusashe. Shiru ya yi still dai yana kallanta. Kamar wanda ke bata haske da kallan da yake mata haka ta ji, tabbas idan dai har ta fahimci inda tambayarsa ta dosa wannan gidan da Abida ta kaita yake nufi. Ta riga ta san ba ta taɓa sanin wani gida makamancinsa ba ballantana ta tsaya dogon tunani wajen bambance wanda yake nufi. Dan haka tunda ta tsaya ta yi nazari se ta fuskanci abin da yake nufi. Se ta ɗaga kai da sauri ta kalle shi tace

"Wallahi ja na ta yi tace in rakata, bani da masaniya a kan gidan, na ɗauka gidan en uwansu ne.." ta faɗa tana jin wani sabon kukan na taho mata.

"Gaskiya za ki faɗa min, kar ki ɓoye min komai.." ya katseta da fadin hakan. Jinjina kai ta yi babu musu ta shiga ba shi labarin yanda komai ya faru tiryan_tiryan. Tsananin mamaki ya kama shi, ya ma kasa furta komai tun bayan da ta ƙare bayar da labarin ta yi shiru. Ashe har yanzu akwai irin waɗannan mutanen? ya zama dole ya ɗauki mataki a karo na biyu ko da hakan ba ze yi aiki ba a wannan karon ma ze jarraba. Abin da kuma ya sake kashe shi a zaune shi ne ambatar sunan Abida da ta yi a matsayin wadda ta jata zuwa gidan. Duk da ita ɗin sabuwar ɗaliba ce, amma ya shaida sunan nata. Be kuma taɓa tsammatar wannan ɗin halinta ba ne.

"Ya salaam.." ya faɗa yana ɗan dafe kansa idanunsa a lumshe. Ya shafe wajen minti 2 a haka ba tare da yace komai ba, se zuwa can yace a nutse

"Ki kwanta ki yi bacci.. Za mu yi maganar gobe" Daga haka ya miƙe be jira cewarta ba ya fice daga wajen zuwa inda shimfiɗarsa take. A ranar dai daga shi har ita babu wanda ya rintsa, kowa da abin da yake tunani.

Juyawa ya yi ya kalli gadon da take kai, ga mamakinsa se ya hangi idanunta masu sheƙi a buɗe, alamar ba bacci take yi ba. Ya ɗan lumshe idanunsa sannan ya ɗan matsa kusa da gadon yace

"Ki tashi.." ya faɗa a nutse kuma a hankali. Abin da ya sake tabbatar masa da ba ta yi bacci ba shi ne yanda da ya yi mata maganar tafarar ɗaya ta miƙe zaune a kan gadon. Ya ɗan fesar da iska daga bakinsa yana shigewa cikin toilet ɗin dan ɗauro alwala.

Wajen ƙarfe 6 ne suka shigo gidan daga masallaci, kai tsaye ɗakin Ummeey ya wuce, ya yin da Abeey ya wuce nasa ɗakin dan ya samu ya ga ko ze iya baccin da be yi ba saboda kwana biyu da yake fama da matsanancin bugun zuciya, wanda ya ƙi faɗawa Gwani har yanzu, duk da ya san ba shi da lafiya amma ba ya son ɗagawa kowa hankali shi ya sa ya ƙi faɗawa ko da Ummeey ce.

Ummeyn na zaune a kan dadduma tana lazumi tun bayan idar da Sallahr da ta yi. Ya shiga ya nemi waje ya zauna, se da ta ida addu'ar da take sannan suka gaisa.

"Ya kasuwar?"

"Alhamdulillah.."

"Toh Allah ya daɗa dafawa" Ummeey ta faɗa

"Ameen Ameen.."

"Ni kam Affan Allah yasa dai lafiya. Tun jiya ban ga ɗiyata ba, ko jikin ne?" Ɗan lumshe idanunsa Gwani ya yi, ya gyara zamansa kafin yace

"Jikin da sauƙi kam Ummeey, zan faɗa mata kin tambayeta.. zuwa anjima za ki ganta."

"Toh Alhamdulillah.. Allah ya ƙara lafiya. Don Allah Affan ka cigaba da kulawa da yarinyar nan, sam ba ta da saurin sabo ballantana mu saba. Har yanzu ta kasa sakin jiki da ni. Ka yi ƙoƙarin janta a jiki sosai In Sha Allah komai ze yi daidai.. Har wannan rashin son cin abincin, ka yi ƙoƙarin ganin ko da ci ne ku dinga yi tare duk dai dan a samu ta dinga ci ɗin." Ya lumshe idanunsa yana sake yabawa da ƙoƙarin da Ummeey take yi, yana kuma sake godewa Allah da ya ba shi uwa kamar Ummeey.

"Toh Ummeey.. An gode, Allah ya saka da alkhairi.." Murmushi kawai Ummeey ta yi a ranta tana cigaba da musu addu'ar daidautawarsu cikin ƙanƙanin lokaci.



... Babu daɗewa ta ida, ta juye shi cikin wani hamshaƙin cup da ya matuƙar haɗuwa. Kai tsaye ɗaukar cup ɗin ta yi ta

Please Login or Register in order to submit comment