Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fa saboda ya ɗauka ita ma zama za ta yi, se ga shi ta fice ta bar shi. Toh me ze zauna yi kam. Se kawai ya fito shi ma daga cikin motar yana faɗin

"Mu je.." Tare suka shiga gidan. Se dai su Lulu na gaba ya yin da su suke baya. Sosai Ummeey ta ji daɗin zuwansu, nan take ta shiga nan nan da su. Ta ajje musu abinci da ruwa sannan ta dawo ta zauna suka sake gaisawa. Da ma har ga Allah ita dai Lulu abin da take jira kenan, dan haka babu ɓata lokaci ta zuba abincin da tun shaƙar ƙamshinsa na farko ta ji ya mata, aikuwa ta shiga cin abinta hankali kwance. Kallanta Didi da Gwani kawai suke yi cike da mamaki. Ita dai haka ta ci abincinta ta yi nakk sannan ta sha ruwa.

"Kin ƙoshi ɗiyata?" Ummeeey ta faɗa tana kallan Lulun. Se ta jinjina kai tana murmushi tace

"Eh Ummeey.." Cigaba da zama suka yi na en mintuna kafin suka yi sallama suka fice daga gidan suka bar Gwani da Ummeeyn.

"Bari na ɗauki wannan Ummeey ko za ta nema zuwa an jima.. Wai ta kasa cin na can gidan ne, na nan ɗin take so." Shiru Ummeey ta yi tana nazarin maganar Gwanin. Se dai tace

"Bari na tashi na zuba mata cikin flask ɗin can.. Idan ma tana buƙata ne ko zuwa gobe ma ka zo se ka tafar mata da shi." Ummeeey ta faɗa tana miƙewa. A cikin ranta tana fatan a ce abin da ya fara zuwar mata cikin rai shi ne. Bayan shuɗewar wasu mintuna se ga shi ya fito hannunsa ɗauke da leda. Daga haka Bad Man ya ja motar suka wuce gida.

.. Yana yin parking Gwani ya sauka daga motar, kusan lokaci ɗaya da Lulu. Suna fita kuwa ya datse ƙofar. Didi ta tura ta tura ta ƙi buɗuwa. Se ta juya ta kalle shi daidai lokacin da ya zuba mata waɗannan idanun nasa. Ya kashe mata ido guda ɗaya yana cije gefen lips ɗinsa na ƙasa. Kawai se ta juya tana bin Lulu da ta yi gaba da kallo, zuciyarta kamar za ta buga dan takaici. Sun fi minti 2 a haka ba tare da kowannensu yace komai ba. Jikinta a sanyaye ta juya ta kalle shi kamar za ta fashe da kuka tace

"Don Allah ka buɗe min.." Se a lokacin sannan ya ɗan yamutsa fuska yace

"Fita za ki yi?" Da sauri ta jinjina kai tana fatan ya buɗe matan ta fita. Numfashi ya sauke sannan ya soma faɗin

"Ohk.. Idan ki na so na buɗe miki se kin yadda daga nan babu inda inda za ki wuce se kitchen ki dafa min Coffee. Daga haka se ki tafi sashen Mommahn. Idan kuma ba haka ba mu kwana cikin motar nan." Ya ƙare yana ɗaga hannunsa. Shiru ta yi tana kallansa bayan ta gama jin bayaninsa. Fisabillahi kwana nawa ne ba ta kai masa Coffee ɗin ba? Ba se ya bari ta huta ba. Wai ma shi duk me ye ya chanja shi haka ne?

"Toh ai ba a sashen nake ba.." Ta faɗa kamar za ta yi kuka. Tsayawa ya yi yana kallanta yanda ta yi ɗin nan ba ƙaramin kyau ta masa ba. Karo na farko ya cigaba da biyewa zuciyarsa da ke tunzura shi ya yi ta shigewa yarinyar, se kuma daga baya ya zo yana tuhumar kansa. Kai a yanzu ma fa kwana 2n nan da suka yi ba ya ganinta sosai se yake jin wani abu ne kama da kewa na kama shi. Haka nan yake tsintar kansa da son ganinta, abu se ka ce asiri.

"Oh.. ya yi. Da ma ban miki dole ba ai.. Gyara zama ki shirya kwana cikin motar nan." Ya ƙarasa maganar yana kwantar da kujerar da yake kai. Da sauri tace

"A'ah zan kawo maka." Buɗe idanunsa da ya fara rufewa ya yi yace yana ƙunshe dariyarsa.

"Oh kin amince?" Se ta jinjina kai tana ɗauke kai. Ɗaga kafaɗa ya yi kamar irin be damun nan ba, ya yin da yana saka hannu ya buɗe ƙofar ya saki wani miskilin murmushi yana sake cije lips ɗinsa. Kamar ta fasa ihu haka take ji, haka ta bi bayansa zuwa sashen nasu da yanzu ba a ciki suke zaune shi da Gwani ba. Sun koma ainahin sashen Bad Man. Kai tsaye hanyar kitchen ta yi dan yin sauri ta gama abin da za ta yi. Ya yi saurin riƙo hannunta yana faɗin

"Saurin na meye ne? Mu je na nuna miki wani abu." Ya yi maganar ba tare da ya bata damar musu ko ƙwace hannunta ba. A haka suka ƙarasa ɗakin.

"Mu je mana.." Ya yi maganar irin ransa a ɗan haɗe ɗin nan dan kar ma ta kawo wani abun a ranta.

"Yau da rashin kirki ya tashi kenan." Ta faɗa ƙasa ƙasa tana shiga cikin ɗakin. Kusan a tare suka shiga, se dai shi ya dakata yana shiga ya saka key a jikin ƙofar sannan ya jefa cikin aljihun wandonsa. Da sauri ta juyo ta kalle shi, kamar za ta yi kuka tace

"Ka ce fa Coffee zan kawo maka.. Kar Mommah ta neme ni."

"Se me? Ki na wajen mijinki." Ya yi maganar cikin basarwa yana ƙarasawa cikin ɗakin. Binsa ta yi da kallo ta girgiza kai tace

"Ni dai don Allah.."

"Shhhh...." Ya faɗa bayan ya ɗora hannunsa a kan bakinsa. Ya juya ya ƙarasa cikin ɗakin. Kai tsaye soma rage kayan jikinsa ya yi kamar wanda ke shirin yin wanka. Lura da ko damuwa da wanzuwarta a wajen be yi ba, dan kuwa cigaba ya yi da ƙoƙarin cire kayan shi ya sanyata saurin juyawa ƙirjinta na dukan uku uku. Ya sake yin wata miskilar dariya ƙasa ƙasa yana ƙarasa abin da yake yi. Toilet ya faɗa ya watsa ruwa, ya fito. Rigar bacci ya saka, irin me buɗaɗɗen gaban nan. Se ya saka igiyar rigar ya ɗaureta kafin ya feshe jikinsa da turarukansa masu mugun daɗin shaƙa. Har lokacin tana tsaye ta rasa abin yi. Tun bayan shigarsa wankan da ta duba mukullin ba ta gani ba. Se ta sake tsayawa tana jiran fitowarsa dan ta sake roƙarsa. Ta buɗe baki da niyyar yin magana yace

"Ki kwantar da hankalinki.. Ki zo ki kwanta kawai.. Yau a nan za ki kwana." Ya faɗa lokacin da ya soma takowa zuwa inda take. Girgiza kai ta yi daidai lokacin da ƙwalla ta taru a idanunta tace

"Don Allah kar ka min haka.. ka bar ni na tafi ka ji?"

"Na ƙi." Ya yi maganar lokacin da ya iso dab da ita. Hannu ya ɗora a kan hijab ɗinta daidai lokacin da ta soma ja baya lokaci ɗaya kuma tana danne hijab ɗin jikinta.

"Ki yi shirin kwanciya.. Ko ki cire wannan hijabin ko ni na cire." Ya yi maganar yana kafeta da idanunsa.

"Don Allah.." Ta faɗa tana girgiza kai.

"Ba ki yadda ba kenan?" Ya yi maganar yana sake matsawa kusa da ita da niyyar saka hannu ya cire mata hijabin. Se ta yi saurin saka nata hannun ta soma yaye hijabin. Ya yi dariya ƙasa ƙasa, tabbas wannan tsoron nata na ɗaya daga cikin abubuwan da ke burge shi a tattare da ita. Kamar ba za ta cire ba, se dai ta runtse idanunta kawai ta cire. Ya karɓa yana jefa shi gefe.

"Je ki kwanta.." Ya yi maganar yana nuna mata kan gado. Ganin alamar za ta sake yin magana ne ya sanya shi katseta da faɗin

"Kar ki min musu." Se ta haɗiye maganar ta ƙarasa kan gadon kawai ta kwanta. Ta runtse idanunta tana curewa waje ɗaya kamar kayan wanki. Ji take kamar ta fashe da kuka, ko kuma ta yi ihu ko ze fahimceta tun da dai ya ƙi jin roƙon da take masa. Ya ɗan shafa sumar kansa yana sauke ajiyar zuciya. Bayan shuɗewar wasu mintuna se ya ƙarasa kan gadon ya zauna. Yana lura da yanda take sake jan bargo tana rufe jikinta. Ya yi ƙwafa yana murmushi. Ya kai wajen minti 5 da zama ba tare da ya yi yunƙurin yin komai ba kafin a hankali ya kai hannunsa ya yaye bargon gaba ɗaya. Abin da ya ba shi mamaki shi ne har ta fara baccinta cikin kwanciyar hankali. Ya yi murmushi lokaci ɗaya yana lumshe idanunsa sanda zuciyarsa ta ɗan buga kaɗan. Be ɓata lokaci ba wajen maidata cikin jikinsa ya kwantar a kan ƙirjinsa da ke a buɗe. Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da bugun zuciyarsa ya ƙaru. A hankali ya kai hannunsa kan hular da ke kanta ya zameta. Nan take dogon baƙin gashinta da ke tufke da ribbom ta bayyana, babu abin da take se sheƙi da wani daddaɗan ƙamshi. Ƙamshin da ya tilasta masa lumshe idanunsa. Se ya shagala da son cigaba da shaƙar ƙamshin, dan haka ya ɗora hancinsa kan gashin nata yana shaƙar ƙamshin da ke fitowa daga jikinsa. Sake rungumeta ya yi sosai tamkar wanda za a ƙwacewa ita. Cikin bacci ta ji ta kamar ba a kwance ba, hakan ne ya sanyata soma ƙoƙarin buɗe idanunta da sauri. Se ta ji ta ƙam ƙam a jikinsa, yana kuma cigaba da shaƙar ƙamshin da ke fita daga kanta. Ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske, ba ta san lokacin da ta buɗe baki a tsorace ta saki ƙara ba, dan ba ma ta fahimci a inda take ba. Cikin sakannin da ba su wuce 3 ba, ya yi amfani da bakinsa wajen lalubo nata ya haɗe su waje guda. Se a lokacin ta fahimci lallai shi ne, shi ɗin ne dai yau ma ya maimaita abin da ya yi rannan. Cikin lokaci ƙanƙani wata irin kasala ta rufe shi, bugun zuciyarsa ya ƙaru fiye da na ɗazu. Be san yanda aka yi ba, ba kuma ta tsammata ba, bayan ƙoƙarin ƙwace bakinta da ta yi daga cikin nasa, se salon nasa ya chanja ma gaba ɗaya. Cikin ƙanƙanin lokaci wani irin tsoro ya ziyarci Didi. Da dai ta ga duk ƙoƙarin da take a banza kawai se ta cigaba da kukanta cike da tsoro. Ƙarar da wayar Bad Man ta yi ita ce ta dawo da shi hayyacinsa. Ya ja Didin ya rungume cikin jikinsa yana komawa gefe har lokacin bugun zuciyarsa be saitu ba. Ya lumshe idanunsa kafin ya buɗe yana mamakin wanda ya kira shi a wannan lokacin. Hannunsa ya kai ya ɗauki wayar ya duba me kiran.

"Mommah!" Ya faɗa da kasalalliyar muryarsa. Dab da za ta tsinke ya ɗaga yana maida dubansa kan Didi da jikinta ke rawa tana kuma so ta miƙe daga jikinsa. Se dai duk da yanda jikinta ke rawa hakan be hanata sake ƙoƙarin miƙewa ba, dan gani take kamar idan ya ajje wayar ze dawo ne ya ƙarasa abin da ya yi niyya.

"Ka na ina?" Mommah ta tambaya muryarta babu wasa, dan tabbas so take ta tabbatar da Areef ɗin yana son Didin sosai kafin ta ba shi ita gaba ɗaya. Kamar yanda ya garasu a farkon auren haka take so shi ma ta wana shi, ta saita shi, ta yanda ze fahimci ba komai kake samu a lokacin da kake so ba. Duk da yanda ta lura yanzun akwai soyayyar Didi cikin idanun Areef ɗin amma so take bayan wannan kuma su yi amfani da hakan wajen ceto shi daga mummunar ɗabi'ar shaye shaye da yake. Har yanzu kuma ba ta yi wa Daddy magana a kan masu tsaron Areef lokacin da yana ƙasar waje ba. Dan so take idan Allah Ya yadda komai ya daidaita se ta sanar da shi dan ka da hankalinsa ya tashi. Se da ya ɗan lumshe idanunsa sannan ya buɗe yace muryarsa a cunkushe

"Ina gida.."

"Ina Afrah?" Ta tambaya kai tsaye. Se da ya fara kallan Didi da ya sake rungumowa sannan yace kamar me magana shi ɗaya.

"Tana nan.." Daga yanda ya yi maganar kaɗai ya isa ta fahimci kamar be so ya faɗi hakan ba. Se dai ba ya so ya sake yin wani laifin da ze sa Mommahn ta ji haushinsa bayan rannan. Ba tare da ta bi ta kan yanda ya yi maganar ba tace

"Toh ka yi maza ka dawo min da ɗiyata yanzun nan ba se an jima ba. Idan kuma ba haka ba ranka ze ɓaci Areef." Daga haka Mommah ta katse wayar tana lumshe idanunta.

"Allah Ka ƙara daidaita tsakaninsu gaba ɗaya.." Ta faɗi hakan har cikin ranta tana jin daɗin yanda wannan ranar da suke ta jira ta zo..


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO73*


____An ɗauki wajen minti 1 bayan kashe wayar Mommah amma be sauketa daga kunnensa ba. Se can kuma ya sauke a hankali yana sake maida dubansa kan Didi da har lokacin jikinta be dena rawa ba. Ya ɗan lumshe idanunsa a hankali zuciyarsa na hasaso masa abubuwa da dama. Musamman kwanaki kaɗan da suka wuce cikin gidan nan. A karo na barkatai ya sake sauke ajiyar zuciya kafin a hankali ya saka hannunsa ya zame Didin daga jikinsa, tun kafin ya saketa ta yi ƙoƙarin tashi gaba ɗaya. Ya yi amfani da hannunsa wajen sake riƙeta sosai ya zuba mata lumsassun idanunsa. Haka nan kawai yau ɗin ya ji wani tausayinta na kama shi, abin da be taɓa ba ji ba kenan tun zuwanta gidan.

"Don Allah.." ta faɗa tana girgiza kai tana sake yunƙurin tashi. Ya buɗe idanunsa sosai a kanta kamar me karantar wani abu daga cikin fuskar tata. A hankali kuma se ya saketa yana miƙewa ma gaba ɗaya daga kan gadon. Hijab ɗinta ya miƙa mata muryarsa can ciki yace

"Saka.." Da sauri ta ɗauka jikinta har rawa yake yi. Idanunta kuma sun yi ja. Sam ta kasa haɗa ido da shi, dan haka ko kallan fuskarsa ma ba ta yi ba. Yin gaba ya yi yana tafiya a hankali, se dai saboda yanda jikinsa yake babu ƙwari, ya sanya tafiyar tasa ta zama wata iri. Har wani ɗan layi yake kamar wanda ya sha wani abun. Ba tare da ya lura da hakan ba ya cigaba da tafiya. Binsa take yi a baya ƙirjinta na bugawa, tsoro take ji kar yace ɗaki ze maidata. Yanzu idan Mommah ta ganta da wane ido za ta kalleta? Me za tace mata? Dab da za su shiga sashen Mommahn ta dakata, lokacin da idanunta suka cika taff da ƙwalla. Har lokacin ta kasa kallansa tace muryarta na rawa.

"Don Allah ka juya.." Dakatawa ya yi jin abin da tace. A hankali ya ɗan cije laɓɓansa kafin ya saki. Kamar ba shi ba, dan hatta muryarsa a cunkushe take yace

"Ki yi haƙuri.." Wallahi ba ta san lokacin da ta ɗaga ido ta kalle shi ba. Haƙuri? Shi ɗin? Kuma ita yake bawa? Dukka ta jerawa kanta waɗannan tambayoyin. Ba ta taɓa zaton jin kalmar haƙuri daga bakinsa ba. Ba ma ita ba, duk wata tattausar kalma daga gare shi. Ban da ma a kwana biyun nan da ya chanja da abubuwa da dama ba ta yi tsammaninsu daga gare shi ba. Kawai se ta cigaba da binsa har ɗakin Mommahn. Fakar idanunsa ta yi tai wuff ta faɗa ɗakin da suke kwana ita da Lulu. Murmushin gefen baki ya yi kafin ya girgiza kai yana kai hannu ya shafa sumar kansa sannan ya juya dan ficewa daga ɗakin.

"Areef.." Mommah ta faɗa tana ƙarasowa cikin palourn. Sam be yi tsammanin Mommahn za ta fito a wannan lokacin ba. Abin da ya sa ya shigo har ciki kenan. A sukwane ya juyo yana ɗan cigaba da shafa kansa, kansa a ƙasa ba tare da ya kalleta ba. Tamke fuska Mommah ta yi dan ka da ma ya ɗauka abun da wasa.

"Ka ƙyale min 'ya na faɗa maka Areef.. Ban son rashin kunya.. Wallahi kar na sake ganin ka ɗaukar min 'ya zuwa wani wajen, idan ba haka ba zan saɓa maka."

"Mom..mah.." Ya faɗa a rarrabe. Ɗaga masa hannu ta yi kafin tace

"Na dai faɗa maka.. Wuce ka tafi." Kamar ya yi me, haka dai ya ja jiki ya fice daga ɗakin jiki a sanyaye.

"Kaii!! Didi yaushe kika shigo?" Lulu ta faɗa tana kallan Didi dake kwance kan gadon lulluɓe cikin bargo kamar me jin sanyi. Shiru ta yi ba tace komai ba, dan ba ta so Lulun ta fahimci komai. Neman waje Lulu ta yi ta zauna tana kai hannunta tace

"Didi.." ta yi maganar lokacin da ta yaye bargon. Riƙewa Didi ta yi da sauri ta sake rufe kanta.

"Ohh na gane.. Ai dole ki ji kunyata. Ni wallahi Didi ban san lokacin da kika zama haka ba. Shi ne ke ga me miji har da binsa ɗaki a gidan surukai." Ba ta san lokacin da ta yi saurin yaye bargon gaba ɗaya ba, ta ɗaga kai tana kallan Lulu cike da mamakin abin da ke fitowa daga bakinta. Kallan juna suka shiga yi. Kafin can Didi tace

"Ke ma haka kike tunani?"

"Aou se waye na biyu me irin tunanin nan?" Hannu Didi ta kai duk da a sanyaye jikinta yake ta buge hannun Lulu tace

"Da gaske fa nake don Allah."

"Da gaske nake fa Didi." Lulu ta faɗa tana ɓata fuska.

"Na shiga 3." Didi ta faɗa tana ji kamar ta fasa ihu. Gefe guda kuma tana ji tamkar ƙasa ta tsage kawai ta shige, ko kuma wani abun makamancin hakan. Kamar wadda ke a gaban alƙali tace

"Wallahi Lulu ba kai kaina na yi ba, shi ne ya ja ni.. Don Allah kar ki min irin wannan fassarar. Idan ke kin ce haka saura kuma me za su ce?" Didi ta faɗa kamar za ta yi kuka.

"Toh shi kenan, na yadda da ke. Amma me ye kike kuka?" Kawai se ta rungumeta ba tare da tace komai ba tana jin wata ƙwalla na taho mata tuna abin da ya faru. Murmushi Lulu ta yi ita ma tana rungume Didin da har lokacin jikinta be dena rawa ba. Ranar dai haka ta kwana duk a kunyace. Ba kuma ta fita ko nan da can ba saboda kar ta haɗu da Mommah. Har washegari kaasa fita ta yi gaida Mommah, dan gani take kamar tana zuwa Mommahn za ta fahimci abin da ya faru. Hakan ne ya sanyata cigaba da zama cikin ɗakin. Ita ma kuma Mommah ba ta takura ba, har cikin ɗakin ta saka aka kai musu hamshaƙin breakfast nasu.

... Kallanta Didi ta cigaba da yi cike da mamaki da kuma tausayin yanda take ajje numfashi kamar wadda ta yi tsere.

"Mene ne?" Ta sake tambaya a karo na barkatai. Lulu ba ta iya amsawa ba, se tashi da ta yi da gudu ta faɗa toilet ta shiga kwara amai. Da ma tun da ta ji ƙamshin abincin be mata ba. Dan dai Didi ta dage se ta ci ne, shi ne dalilin da ya sanyata ci. Se ga shi yanzu gaba ɗaya ya dawo duk da da ma kaɗan ne ta ci.

"Sannu.." Shi ne abin da Didi ke ta sauke mata kamar ba ta gajiya. Tausayin er uwar tata na sake rufeta. Ita da ma idan ta fara rashin lafiya ba sarki sai Allah. Daidai lokacin Mommah ta shigo cikin ɗakin. Ta kalli Didi da ke sake jerawa Lulu sannu kamar ba gobe. Tana kuma yi amfani da towel ɗin hannunta wajen saka mata wajen wuyanta.

"Subhanallahi me ya faru ne?" Mommah ta faɗa tana kallansu su duka. Sam mantawa ma ta yi da abin da ya faru jiya saboda halin da er uwatta ke ciki tace da muryarta da tafi kama da ta masu shirin yin kuka.

"Lulu ce ba ta da lafiya Mommah.. Yanzu ma Amai ta gama."

"Ya salaam.." Mommah ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin. Hakan ne ya sanya Didi neman waje ta zauna a gefen Lulu.

"Da ma tuntuni ki na aman ne?" Ta tambaya tana kallan Lulu. Se ta girgiza kai tana jin wata kasala na rufeta.

"Ni dai tun da muka zo gidan nan ban ga ta yi ba. Tana dai cewa tana jin tashin zuciya, ina ga ko zazzaɓi ne.." Didi ta faɗa tana kallan Lulu cike da tausayawa. Cigaba da kallanta Mommah ta yi na en wasu sakanni kafin ta miƙe.

"Maza ki shirya ku je asibiti.. Abun ya yi yawa." Jinjina kai Lulu ta yi a sanyaye ta amsa da

"Toh." Kai tsaye Mommah Gwani ta kira ta sanar da shi abin da ke faruwa. Babu jimawa ya zo cikin palourn. Zuwa lokacin Lulun ma ta shirya. Kai tsaye suka hau mota driver ya ɗauke su zuwa asibitin da en gidan ke zuwa.

Cikin sa'a lokacin da suka je asibitin ba su tarar da layi ba. Dan haka kai tsaye wajen ganin likita suka shiga. Se aka yi sa'a suka sami mace. Cikin ƙanƙanin lokaci Lulu ta mata bayanin abin da ke faruwa. Abu na farko da likitar ta soma faɗa shi ne gwajin ciki Lulun za ta yi. Daga ita har shi kallan juna suka yi kamar waɗanda suka ji an yi saɓo. Lulu ce ta soma janye idanunta lokacin da ilahirin jikinta ya ɗauki rawa. Ya yin da Gwani ya lumshe idanunsa yana fatan tabbatuwar hakan. Ya san ko babu komai idan cikin ne ze taimaka masa ainun wajen shawo kan matsalarsu da Lulu. Gefe guda kuma idan haka ɗin ne dab yake da zama uba kenan? Ya sake lumshe idanunsa, ji yake yi kamar ma an riga an tabbatar da haka ɗin ne.

Gwajin farko da aka yi wa Lulu aka tabbatar musu da cewa tana ɗauke da juna biyu ne.. Kwantar da kansa ya yi a kan kujerar da yake kai wani irin farin ciki mara misaltuwa na mamaye shi. Gaba ɗaya ya ma rasa a wanne fanni ze iya kwatanta farin cikin da ya tsinci kansa a ciki. Abin da dai ya sani kawai shi ne wannan ranar na ɗaya daga cikin ranaku mafiya daraja da kuma muhimmanci a rayuwarsa. Da gasken dai ya kusa zama uba. Lallai ikon Allah ya wuce gaban wasa. Be taɓa tsammanin hakan ba wallahi. Se ga shi Allah Ya ba shi a lokacin da dukkansu ba su yi tsammani ba. Kawai se ya zube a wajen ya yi sujudush-shukr. Ya miƙe yana sake jin farin cikin da ke sake mamaye shi. Ji yake kamar ya fi kowanne ɗa namiji dace da kuma farin ciki a yau ɗin nan. A ɓangaren Lulu kuwa shiru ta yi na tsawon minti 1 ba tare da tace komai ba se kallan waje ɗaya kawai da take yi kamar wadda ta zare. Ciki? Ita? Cikin ma na Gwani kenan? Shin me ya kamata ta yi? A tunaninta baƙin ciki, ƙunci da kuma takaici na har abada shi ne ze zo mata a yanzun da aka sanar da ita tana ɗauke da cikin Gwani. Se dai ga mamakinta maimakon ta ji wannan tsanar da ta yi masa tuntuni ta yi tasiri a kan cikinsa da ake maganar tana ɗauke da shi, se ta ji saɓanin haka. Dan kuwa wani irin farin ciki ne ta ji ya ziyarceta. Cikin lokaci ƙanƙani ta soma jin wata irin ƙaunar abin da ke cikin nata. Ba ta taɓa tunanin haka ba, ba ta taɓa kawo haka cikin ranta ba. Duk kuma da tunanin nan da take, hakan be chanja yanayin da zuciyarta ke ciki ba. A hankali ta kai hannunta kan cikinta ta shafa, kawai se murmushi ya suɓuce a kan fuskarta. Tun daga nesa yake kallanta tsayin lokaci ba tare da ta sani ba. Addu'a yake yi cikin zuciyarsa Allah ya kawo masa komai cikin sauƙi. Ya san yanzu Lulun ta chanja ba kamar da ba. Se dai har yanzu be sani ba, tana son shi ko ba ta son shi? Za ta iya zama da wani abu da ya dangance shi a jikinta ko kuwa a'ah? Mene ne ze biyo baya bayan shirun nan da ta yi? Tunanukan da ke sanya shi faɗuwar gaba kenan. Sam ya kasa ƙarasawa ya tunkareta ballantana ya ji wani abu daga gareta. Dalili kenan da ya saka shi tsayawa yana kallanta cike da tunanin ta ina za su fara. Se dai ga shi abin da be taɓa tsammani ba shi ne yanda ya ga farin cikin da ake yawan samu daga wajen kowacce uwa a lokacin da aka shaida mata tana ɗauke da juna biyu musamman a karon farko. Be

Please Login or Register in order to submit comment