Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni da ke ba." Ya ƙare cikin barkwanci. Dariya ta yi ita ma tana tuna yanda auransu ya kasance se ka ce shirin film.

"Bayan duk wannan se ga shi yau ɗin kin haifa min kyakykyawan yaro me kama da ni."

"Wai da kai yake kama?" Ta faɗa tana tura baki. Murmushi ya yi yana cizar gefen laɓɓansa yace

"Ehh mana, kar ki ce min ba ki gani ba?"

"Ni dai ban yadda ba ka min wayo.. Ni na gama shan wahalar kuma ka ce yana kama da kai.."

"Iyeeee!!" Areef ya faɗa hadda riƙe haɓa.

"Yana so ne ya nuna miki ya fi ƙaunata.." Ya ƙare maganar cikin salo na tsokana. Dariya ta yi tana kallansa saboda jin yadda ya yi maganar. Ganin yana gyara zamansa kamar me shirin kwanciya ya sanya ta faɗin

"Babe wai kwanciya za ka yi?" Ta faɗa tana kallansa sosai.

"Aou kora ta kike yi?" Waro idanunta Didi ta yi kafin ta marairaice fuska tace

"Ni ɗin wa?" Ta faɗa a marairaice. Se da ya gyara zamansa sannan yace

"Toh a nan zan kwana." Ya faɗa kamar irin da gasken nan.

"Babe..!" Ta sake faɗa dan ita da gaske ta ɗauka da gasken yake. Be san sanda dariya ta ƙwace masa ba saboda yanda ta yi maganar. Ya kai hannu ya lakuci kumatunta yace

"Ke dai ko Babe..? Wannan tsoron naki.." Se ya girgiza kai har lokacin da murmushi a kan fuskarsa. Bayan shuɗewar wasu mintuna ya danna kiran number Gwani. A ɓangarensu Gwani kuwa yana riƙe da hannunta ya ƙarasa da ita har kan gadon a nutse. Ya taimaka mata cike da takatsantsan ta zauna a kan gadon, ya gyara mata zaman sosai yanda za ta ji daɗi kafin ya nemi gefenta ya zauna.

"Sannu.." Ya sake faɗa a karo na barkatai. Murmushi kawai ta yi tana zuba idanunta a kan fuskarsa. Ya lumshe idanu yana sake buɗewa a kanta.

"Sannu.. Allah Ya miki albarka."

"Ameen." Lulu ta amsa a hankali har lokacin da murmushi ita ma a kan fuskarta.

"Kin yi ƙoƙari sosai Ƙalb, na san halinki, kwata-kwata ban yi tunanin za ki iya haihuwa da kanki ba.." Shagwaɓe fuska ta yi tana faɗin

"Me ne halin nawa toh?" Ta tambaya tana kallansa. Se dai ya yi murmushi kafin ya kamo hannunta ya buɗe baki ze yi magana, daidai lokacin wayarsa ta soma ƙara. Se ya maida dubansa kan wayar, ya kalli me kiran kafin ya ɗaga ya kara a kunne.

"Wai a nan za ka kwana ne?" Areef ya faɗa bayan ya kara wayar shi ma a kunnensa. Se da ya kalli Lulu da idanunta yanzu ke kan Babies ɗin da ke kwance suna bacci hankalinsu kwance. Idan ba ka san mutane biyu ne suka haife su ba, se ka yi tunanin daga mahaifa ɗaya suka fito, saboda kamanceceniya da suke yi.

"Ba ni minti 1 yanzu zan fito." Gwani ya faɗa, be jira Areef ɗin ya sake cewa komai ba ya katse wayar. Ya maida dubansa kan Lulu yace

"Ya kike jin jikin naki?" Ya tambaya yana kallanta. Ƙura masa idanu ta yi tana kallansa kamar wadda ta soma ganinsa yau. Shi kansa se da ya yi mamakin irin wannan kallan, har se da yace

"Ƙalb.." Sannan ta lumshe idanunta ta buɗe su lokacin da suka ɗan sauya kala.

"Subhanallahi! Me ya faru? Wani abun na damunki ne?" Ya tambaya cike da kulawa. Girgiza kai ta yi kafin tace

"Don Allah ka yi haƙuri.." Cikin rashin fahimta yace

"In yi haƙuri? Me kika min?" Ya ƙare yana kafe ta da idanunsa cikin son jin amsar da za ta ba shi.

"Me ya sa bayan duk abubuwan da na maka a baya, ka kuma ga hoton nan ba ka yi ko da yunƙurin rabuwa da ni ba?"

"Ni ba lusarin namiji ba ne.. Ke! Mu bar maganar nan, ba na so ki kuma tunata har abada. Ni na manta ta a gaba ɗaya rayuwarmu, ina so ke ma ki manta ta.. Abu ne wanda Allah Ya rubuta dole se ya faru, ya kuma faru.. mun kuma karɓi hakan matsayin ƙaddararmu.. Don haka kar in sake jin kin tuna wannan maganar.." Jinjina kai ta yi tana cigaba da kallansa. Tana jin yadda wutar ƙaunarsa ke sake ruruwa a cikin zuciyarta. Tabbas Gwani Affan mutum ne har da rabin mutum. Miji ne kuma da kowacce mace za ta yi fatan samun irinsa.

"Maza goge ƙwallar ki yi murmushi in gani.." Ya faɗa a nutse. Babu musu ta yi ƙasa da kai ta ɗauke ƙwallar tana jin murmushi na suɓuce mata. Dan ya sake kautar da maganar ma gaba ɗaya ya sanya shi faɗin

"Yanzu haka ina ji ina gani zan barku har na tsawon kwana 40?" Ya yi maganar a marairaice. Kallansa Lulu ta yi kafin ta sake yin murmushi, kafin ta kai ga cewa komai yace

"Don Allah a rage kwanakin su dawo 10.." Waro idanunta ta yi tana saka hannu a kan bakinta tace

"Kai Habibi kwana 10 fa?" Ɗage girarsa ɗaya ya yi kana yace

"Eh mana.. Ni zan cigaba da kula da ke ai.." Dariya Lulu ta yi kafin tace

"Kamar.." Kafin ta sake cewa komai wayarsa ta ƙara yin ƙara. Ya kalla ya ga Areef ɗin ne dai. Ya miƙe yana faɗin

"Bari ki ga na je, idan ba haka ba mutumin nan ba ze ƙyale ni ba.." Ƙarasawa ya yi ya ba ta side hug a nutse saboda sanin yanayinta a halin yanzu. Ya ƙarasa ya buɗe inda yaran ke ciki, a hankali ya sumbaci goshin kowannensu kana ya ɗaga kai ya sake kallan Lulu. Suka sakarwa junansu sanyayyen murmushi kafin ya miƙe ya fice daga cikin ɗakin.

Suna haɗa ido Gwani ya watsa masa wani kallo. Ya ɗauke kai yana murmushi, oho dai shi ko a jikinsa. Tun da dai ya rabo shi da matarsa kamar yadda shi ma ya haƙura ai shi kenan. Haka yana ji yana gani ya baro jariran nan, dan haka shi ma kawai ya haƙura haka nan. Haka duk suka tafi gida jiki a sanyaye, kowanne na tunanin kwana 40 ɗin da ze yi ba tare da matarsa ba.

Sosai masu jegon ke samun kulawa ta ɓangare da dama. Bayan ɓangaren Ammi da kullum ke tare da su, Ummeey kanta ba a barta a baya ba, haka Mommah ma da Yaya Amina. In taƙaice muku labari dai har da Mami (Mamin Jadwa) wadda yanzu ta yi laushi sosai, kai ba zaka ce ita ba ce. Kafin kuma Abba ya yadda ta cigaba da mu'amalantar iyalinsa se da ya tabbatar da gasken ta gyaru kamar yadda ta faɗa masa. Se dai ita kanta Lulu da a da suke ɗasawa, se ya zamana ma yanzu sun fi zama tamkar baƙi idan suka haɗu. Dan yanzu ta kama kanta, tun da ta gane Mamin ba ƙaunarta take ba. Ta ɓangaren Masoyiya kanta ta taka rawar gani, babbar ƙawa ta haihu. Haka ta din ga zuwa gidan tun washegarin ranar da aka yi haihuwar. Duk lokacin da ta zo kuwa haka za ta wuni yaron nan a hannunta suna hira da Lulu da jiki ya yi kyau sosai Alhamdulillah.

Ranar suna ta zagayo dukka jariran suka ci suna ABUBAKAR, ɗan gidan Didi da Areef sunan Daddy ya ci. Ya yin da ɗan gidan Lulu da Gwani ya ci sunan Abeey har ma da Daddyn. Duk da ba taron suna aka yi ba, amma en uwa da abokanan arziƙi nata zuwa ganin jarirai. Tun daga kan en uwansu Ammi, na su Abba har zuwa kan na su Mommah da Daddy. Haka zalika ma daga ɓangarensu Abeey da Ummeey gaba ɗaya en uwansu se zuwa suke yi barka. Abokan Daddy kansu se da suka je suka ga jikokin nasu. Kowa kuma da kalar abin da yake kaiwa. Daddy kam kowanne jariri manyan akwati ya cika masa shaƙe da kaya masu tsada, da shegen kyau. Ita kanta Mommah ba a barta a baya ba wajen gwangwaje jikokin nata. Abeey da Ummeey na kansu sun taka muhimmiyar rawa a kan yaran, dan yanzu komai se dai su ce Alhamdulillah, dan Ummeey yanzu haka sana'a take yi. Abeey kuma tuni shagon da Daddy ya buɗe masa yake cigaba da albarka, kullum cigaba ake samu. Don haka su ma kansu se da suka gwangwaje jikokin nasu da kaya masu kyau. Se da suka yi kwanaki 40 ɗin kuwa ciff kafin kowacce ta koma gidanta. Zuwa lokacin sun sake yin kyau, sun sake murjewa. ARYAAN da AYAAN kyawunsu ya ƙara fitowa sosai. Sun yi ɓulɓul abinsu. Zuwa lokacin ma hatta girman Ayaan (Ɗan Didi) ya yi daidai da na Aryan (Ɗan Lulu). Idan ma ba ka sani ba ba za ka ce be kai watannin haihuwarsa aka haife shi ba. Ranar da suka koma ɗin se ta zamana wata rana ta musamman a wajensu gaba ɗaya.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, cikin farin ciki da ƙaunar junansu. Cikin ikon Allah kullum cigaba ake samu a rayuwarsu. Aryan da Ayaan na ta ƙara girma da wayo. Suna kuma ƙara girma kyawunsu na ƙara fitowa. Kamanninsu da iyayensu kuma na ƙara bayyana. Zuwa lokacin Didi da Lulu sun koma makaranta. Suka soma karatunsu cike da ɗumbin nasara, musamman da abun ya zo da duk mazajen nasu sun ba su goyon baya ɗari bisa ɗari. Ta ɓangaren Aryan da Ayaan kuwa kullum shaƙuwarsu ƙaruwa take, sun zama tamkar en biyu musamman da ya kasance suna kama. Komai nasu iri ɗaya ne, komai za su yi tare suke yi. Ba a bambanta musu komai, dan kuwa a cikin iyayen ko me ɗaya ya tashi siya ba ya taɓa siyar ɗaya se dai biyu. Yadda suke ƙaunar junansu ya sa masu musu kallan en biyu kullum ƙaruwa suke yi. Tsayinsu ɗaya, haka zalika girmansu ɗaya. Hatta da halayensu kaɗan ne suka bambanta.


_BAYAN WASU SHEKARU_


.. A cikin shekarun abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa hadda auren da Kaseem ya yi. Wanda ya auri Masoyiya (Fatima Kabeer), bayan haɗuwar da suka yi ya je wajen Areef, ita kuma ta je wajen Lulu, ta zo tafiya ta biya ta yi wa Didi sallama a nan suka haɗu. Daga nan dai soyayya ta ƙullu har ta kai ga aure. Jadwa ma ta yi aure, se dai duk burinsu na auran me kuɗin be cika ba, ta dai samu wani me rufin asiri ta aura. Ita ma kuma dama Mami burinta ya yo ƙasa tuntubi. Ladi (Jakadiya) ta rasu a cikin shekarun bayan wani hatsari da suka yi a kan hanyarsu ta zuwa Kaduna. Hatsarin ne Abban ya yi sanadiyyar rasuwar mutane har 5, ciki kuma har da Ladi. Ɓangaren Lulu da Didi kuwa karatunsu ya yi nisa sosai. A ɓangaren zamantakewarsu kuwa kullum shaƙuwa, zaman lafiya da ƙaunar juna ke ƙaruwa a tsakaninsu.


.. Wasu kyawawan yara na hango sanye cikin Uniform iri ɗaya, takalmi iri ɗaya maƙale da jaka a bayansu kala ɗaya, haka basket ɗin ma da ke a hannun kowannensu iri ɗaya ne. Farare tass kyawawa kamar yaran larabawa.

"Laa!! Aryan Abbu yace za mu je gidan Granny yau.." Ɗaya daga cikin yaran ya faɗa yana kallan ɗan uwan nasa. Buɗe idanunsa Aryan ya yi kamar wani babba. Yace bayan ya ajje basket ɗin hannunsa.

"Toh mu zaɓi wace za ta shirya mu." Shiru duk suka yi. Dukkansu suka ɗaga kai suna kallan sama kamar masu nazari. Shi Aryan hadda ɗaga kai hannunsa na kan kumatunsa yana faɗin

"Uhmmm!!" Irin ya zurfafa tunanin nan. Can Ayaan yace

"Ko a yi er rige-rige."

"Ehh kuwa." Aryan ya faɗa yana jinjina kai fuskarsa ɗauke da murmushi. Se da ya ɗauki basket ɗinsa sannan yace

"Kuma se na riga ka.." Yana gama faɗa ya yi sashensu a guje. Da gudu shi ma Ayaan ya tafi yana faɗin

"Na rantse se na riga ka." Ya faɗa shi ma yana wucewa sashensu.


Tun kafin ya ida shiga cikin ɗakin ya soma jefar da basket da jakar bayansa. Da ƙarfi yake kiran

"Maami.. Maami.."

"Toh Babana ya dawo kenan.." Gwani da ke zaune cikin ƙananan kaya ya faɗa yana kallan Lulu. Ya yi matuƙar kyau, ya sake zama babban mutum. Kwanciyar hankali kuwa da kanta ta ke bayyana kanta a jikinsa. Lulun na tsaye bakin mirror tana buɗe drawer jikinsa alamar abu take nema. Gwani na kai ƙarshen maganarsa Aryan ya shigo ɗakin a guje.

"Mami ki sauri ki shirya ni, Mami ki shirya ni kin ji?" Abin da yake faɗa kenan har wani numfashi yake saukewa. Da sauri ta rufe drawer tana juyowa. Cikin sauri ya ƙaraso ya rungumeta yana faɗin

"Mamina.."

"Na'am yaron Maminsa." Ta faɗa tana rungume shi gam.

"Mami ki shirya ni." Ya sake faɗa.

"A'ah, wai ina za ka je ne?" Lulu ta faɗa tana kallansa. Turo ƙaramin bakinsa ya yi kafin yace

"Unguwar da Abbu yace za mu je." Ya ƙare a shagwaɓe

"Toh da alama dai ba ka ga Abbun ba koh?" Lulu ta faɗa tana kallansa kafin ta maida dubanta inda Gwani yake. Da gaske sam be lura da shi ba sabosa hankalinsa gaba ɗaya na kan ya zo Mami ta shirya shi kar Ayaan ya riga shi shiryawa. Se kuwa ya tafi a guje yana faɗin

"Abbu.."

"Na'am yarona.." Ya faɗa yana rungume shi fuskarsa ɗauke da murmushi.

"Abbu ai ka ce za mu je unguwa koh?" Ya faɗa yana kallan Gwani. Murmushi Gwani ya yi dan ya san da ma a wayon yaron nan ba ze manta da zancen unguwar nan ba.

"Ehh na ce.."

"Toh ka ce Mami ta shirya ni." Ya ƙare yana kallan Lulu. Miƙewa ta yi tana faɗin

"Se an jima toh.." Take fuskarsa ta sauya, kamar ze fashe da kuka yace

"Abbu Ayaan fa ze riga ni shiryawa."

"In ji wa?" In ji Gwani. Se da ya sake turo baki yana ƙiƙƙifta ido kafin yace

"Shi! Abbu ka ce Mami ta shirya ni."

"Ohh Ya Allah!" Gwani ya faɗa yana miƙewa. Ya san halin Aryan ɗin, idan dai har ba a yi hakan ba toh ba ze taɓa barinsu su samu sukuni ba. Hakan ne ya sanya shi faɗawa toilet ɗin da kansa ya cuɗe shi tass kafin suka fito. Kaya ya saka masa Lulu na zaune tana kallansu gwanin burgewa. Ana shirin yana ta hirarsa yana bawa baban labarin abubuwan da suka faru a makaranta, shi kam yana ta biye masa. Lulun ce ta ƙarasa shirya shi, se ga shi ya fito tass da shi ya yi matuƙar kyau.

"Toh a zauna a ci abinci." Lulu ta ƙare maganar tana murmushi. Girgiza kai ya yi kafin yace bayan ya maƙe kafaɗarsa

"Uhmm uhmm.." Harara Lulu ta jefa masa kafin tace

"Toh na ga inda za ka fita a haka." Ta ƙare maganar tana gyara zamanta. Take hawaye suka taru a idanun Aryan, ya koma wajen Gwani yace muryarsa kamar wanda ya gama yin kuka

"Abbu.." Abin da ya faɗa kenan. Gwani ya kalli Lulu da ta haɗe rai ita a lallai dole tana nufin abin da ta faɗa. Wato su ba sa gajiya kullum se sun yi faɗa.

"Kamar yadda Mami ta faɗa zauna ka ci abinci."

"Abbu zan ci a gidan Maama." Ya faɗa yana ɗaga kai ya kalli Gwani, haka nan kawai yake ji ya samu mafita. Ganin Gwanin ya girgiza kai ne ya sanya shi sake faɗin

"Allah da gaske Abbu."

"Shi kenan.. Amma fa kar na zo a ce min ba ka ci ba, zamu ɓata."

"Ehh, na yadda." Aryan ya faɗa yana buga tsalle kamar wani babba. Tilas Lulu ta yi dariya. Shi ma Gwani dariyar ya yi yana sakinsa ya tafi. Dab da ze fita Lulu ta jawo shi ta sumbaci goshinsa kafin ta ɗaga masa hannu. Shi ma sumbatarta ya yi a hannunta kana ya fice daga ɗakin a guje. Sauke ajiyar zuciya ta yi tana miƙewa dan ita ma ta samu ta shirya. Gwani ya saka hannu ya maidota ta koma inda take.

"Maza ba ni sumba ɗaya.." Ya faɗa yana juya mata gefen kumatunsa. Ta kalli gefe da gefe kamar me neman wani abu, maimakon ya ji saukar bakin nata a kan kumatunsa se jin saukar shi ya yi a kan laɓɓansa. Ya buɗe ido yana kallanta, ta kanne masa ido ɗaya tana soma kissing lips ɗin nasa. Hannu ya saka ya ɗan jawo ƙugunta, hakan ya sa suka sake samun kusanci sosai. Ya lumshe idanunsa shi ma ya shiga kissing ɗin nata. Ai se ta yi nadama, dan kuwa se ga Gwani na neman zarmewa. Fahimtar hakan ya sanya ta faɗin

"Habibi!!" Ta faɗa da muryarta da ta ɗan sauya. Kansa ya ɗora a kan wuyanta yace yana kallanta.

"Tun da an sallami Aryan ya kamata a sallami babansa." Turo baki ta yi kafin tace

"Habibi.." Ta ƙare a marairaice. Murmushi ya yi be ce komai ba, haka ita ma kafin ta sake cewa komai ya ɗauke ta gaba ɗaya se toilet. Bayan wasu mintuna suka fito, tare suka shirya. Shi ya shiryata ya yin da ita ma ta shirya shi. Cikin ƙanƙanin lokaci suka fito suka yi wani shahararren kyau. Shi cikin manyan kaya ya yin da Lulu ke cikin wani ɗinkin lace da ya gama fita a cikin fitattu.

A ɗaya ɓangaren kuwa da gudu Aryan ya ƙarasa shiga ɗakin. Duk suna zaune a palour. Didi ta cake ita ma cikin lace da mayafinsa, ɗaurin nan ya zauna ya yi mata mugun kyau. Ita kanta ta sake yin kyau, ta murje ta kuma yi ƙiba daidai misali.

"Maama." Aryan ya faɗa bayan ya shigo cikin ɗakin.

"Oyoyo my boy." Didi ta faɗa tana buɗe masa hannayenta. Babu musu ya faɗa ciki, ta rufe gam.

"Maama ni fa?" Ayaan ya faɗa yana turo baki. Dariya ta yi kafin tace

"Toh shi kenan, zo nan.." Ta faɗa tana buɗe hannun. Se kuwa ya ƙarasa ta haɗa su ta rungume. Baya ta matsar da su tana kallansu su duka yanda suka yi kyau sosai ya sanyata faɗin

"Allah Ya raya min ku." Ta faɗa ƙaunarsu da ba ta iya bambance su na sake mamaye zuciyarta.

"Na riga ka shiryawa." Ayaan ya faɗa yana yi wa Aryan gwalo.

"Maama kin gan shi koh?" Aryan ya faɗa yana kallan Didi. Girgiza kai Didi ta yi kafin tace

"A'ah Ayaan ba na son tsokana.. Ba ka ga tare kuka shirya ba?" Se da ya tura bakinsa kafin ya ɗaga kai kawai, dan shi dai so ya yi ya riga Aryan ɗin shiryawa. Gwalo Aryan ya yi masa jin da ya yi Maman ta bi bayansa. Daidai lokacin Areef ya shigo cikin ɗakin. Abun mamaki shi kansa cikin manyan kaya yake, abin da ya ba ni mamaki kenan. Rashin saba ganinsa da kayan da na yi ya sanya yau ɗin ya fita wani na daban, ya yi daƙiƙin kyau kamar ba shi ba. Ya zama wani babban mutum. Yau ɗin se ya yi yanayi da Gwani, kamar Gwani ne ya sauya kama.

"Dad.." Suka haɗa baki wajen faɗa suna tafiya da gudu wajensa. Ɗaukarsu ya yi gaba ɗaya kafin ya sauke su yana faɗin

"Na'am yaran Dad.." Ya saka hannu ya lakuce kumatun kowannensu.

"Bari na chanki wanda ya fi kyau.." Ya faɗa yana kallan nasu. Tsalle suka fara gaba ɗayansu, kowanne jira yake a ce ya fi kyau.

"Dukkanku kun yi kyau sosai." Ya ƙare yana kambaba kalmar ƙarshe.

"Yeehhh!!" Suka haɗa baki wajen faɗar hakan.

"Let's go.." Ya faɗa yana kama hannun yaran se dai idanunsa na kan Didi da ita ma take kallansa saboda yadda ya mata kyau sosai yau ɗin nan. Miƙewa Didi ta yi tana gyara zaman mayafin jikinta. Sakin hannun Aryan da Ayaan Areef ya yi yace

"Ku wuce mu je.." Babu musu suka fita da sauri.

"Madam." Areef ya faɗa bayan ya riƙo hannun Didi. Tuni har Aryan da Ayaan sun fice daga ɗakin. Ta juyo da niyyar jin abin da ya sa ya kirata ɗin, se kawai jin bakinsa ta yi a kan nata. Ya rungumeta sosai ya shiga bata zazzafan sumbata. Duk da ba ta shirya ba, amma hakan be hana ta sakin jiki itama tana kissing ɗin nasa ba. Wajen minti 1 duka ɗauka a haka, kafin ta zare bakinta daga cikin nasa bayan ya bata dama.

"Wannan lipgloss ɗin da kika saka shi ya tsone min ido." Ya ƙare yana shafa sumar kansa.

"Ai dai ga shi yanzu babu shi.."

"Ƙwarai kuwa, shi ya sa na lashe abuna tass kar ma wani ya kalla." Ya faɗa yana kallanta ɗauke da murmushi a kan fuskarsa. Ita ma murmushin ta yi kafin tace

"Shi kenan koh Babe?" Jinjina kai ya yi kafin ya kai hannunsa ya riƙo nata hannun, daga haka suka fice daga cikin ɗakin. Daidai lokacin da suka fito su ma su Gwani suka fito. Kai da na gansu a tare duk se na rasa gane waɗanne ma'aurata ne suka fi kyau. Dan kowannensu kyau ne iya kyau, haɗuwa iya haɗuwa, dacewa iya dacewa. Hakan ne ya sa duk suka fito suka yi kyau abinsu. Da gudu Aryan da Ayaan suka tafi wajensu Gwani. Kusan a tare suka tsuguna suka rungume yaran.

"Mami ai na fi Aryan kyau koh?" Ayaan ya faɗa yana kwantar da rigar jikinsa kamar wani me yin guga. Dariya ta yi kafin tace komai Aryan yace

"Abbu ai na fi Ayaan kyau koh?"

"Dukka kun yi kyau kamar wasu Actors." Dariya duka suka saka suna jin daɗin yadda Abbun ya yabe su. Hannun Gwani duk suka kama lokacin da suka fara takawa.

"Kai da yaran naka ne?" Areef ya faɗa yana kallan Gwani. Jinjina kai Gwani ya yi yace

"Ai fa.. So ake a ƙure kowa yau." Dariya duka suka saka suna maida dubansu kan Aryan da Ayaan da ke ta wasansu duk da hannunsu har lokacin na cikin na Gwani ne.

"Mu wuce koh?" Gwani ya faɗa. Babu ɓata lokaci suka soma takawa dan isa inda motar take. Se a lokacin Didi da Lulu suka haɗe waje ɗaya. Sosai suka fito suka zama manyan mata. Kana ganinsu ka san kwanciyar hankali ya zauna musu.

"Wai na ga ki na yin ƙiba Didi.. Ko dai ko dai?"

"Ko dai me?" Didi ta faɗa tana buɗe ido.

"Aryan da Ayaan sun kusa samun ƙani mana." Lulu ta faɗa cikin basarwa. Duka Didi ta kai mata kafin tace

"Lulu haka kika zama koh? Ke ban ce ta wajenki muka kusa zama iyaye a karo na biyu ba se ni koh?"

"Ni ba ni da komai." Lulu ta faɗa tana tura bakinta.

"Kya dai ji da shi, ni fa gani ma na yi kamar har cikin naki ya soma fitowa." Didi ta faɗa cikin basarwa.

"Kin ji Didi daga magana kina neman ki juya abun kaina.. toh wallahi na janye da wasa nake.." Dariya Didi ta saka a fili tace

"Aou har kin janye?" Ita ma Lulun dariya ta yi tana faɗin

"Wallahi na janye, ai ban manta wahalar nan ba." Ta ƙare maganar ita ma tana dariya.

"Toh Allah Ya bamu masu albarka." Didi ta faɗa a hankali.

"Ameen Didi."

Haka suka ɗunguma cikin motar, Areef na driving ya yin da Didi ke gefensa. Gwani da Lulu na baya, Aryan da Ayaan na ta dabdalarsu a bayan su ma. Suna tafe suna hira gwanin ban sha'awa, cike da sabo, ƙauna da kuma farin ciki. A haka suka cigaba da tafiya se gidan Alhaji Matawalle..


Haka rayuwarsu ta cigaba da kasancewa a kodayaushe se dai a ce Alhamdulillah..

GAME OVER!!! 🔥


ALHAMDULILLAH!
ALHAMDULILLAH!!
ALHAMDULILLAH!!!

Da sukuwa da zamiya, a nan na kawo ƙarshen wannan littafi nawa me suna *A JINI TAKE (IZZATA)* Ina me roƙon Allah ya ba mu damar ɗaukar abubuwa masu kyau cikin labarin, sannan mu watsar da akasin su. Abin da na rubuta daidai Allah Ya haɗa mu a ladan, abin da na yi ba daidai ba kuma Allah Ka yafe min.

Ina neman afuwar duk wanda na ɓatawa rai tun fara littafin nan har zuwa ƙarshensa. Ina kuma me matuƙar godiya a gare ku en amana. Your willingness to join me on this journey and trust me with your time and emotions means so much to me. Thank you for reading and caring. Allah Ya bar zumunci.
A JINI TAKE (IZZATA) comment section, and A JINI TAKE PAID GROUP, ina gaishe ku cikin buhu. Allah Ya ƙara mana haƙuri da juna, Ya kuma bar mana zumunci har abada. Kamar yadda na saba kodayaushe yau ma In Sha Allah gaisuwa ta musamman za ta je ne zuwa ga en amanata na Paid group

1. A'isha Sabo
2. Khulsum
3. A'ishahumairaazare
4. A'ishatu Muhammad
5. Amina
6. Auterr Mamy
7. Azizaty
8. Jidda Galadima
9. Maman Faruk
10. Maman Ikram
11. Mrs Hypan
12. Ummi Ja'afar
13. Zainab Umar Aliyu
14. Khadija Abubakar Oum Ashraf
15. Zainab Abubakar Yakubu
16. MAMAN IKRAM
17. Mrs Majeed
18. Ummu

Please Login or Register in order to submit comment