Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan dawo." Kafin ta sake cewa wani abun har ya bar wajen dan idan be yi da gaske ba ze iya ɗauketa da mari.

"Toh se kun dawo." Ta faɗa tana binsu da kallo lokacin da suka shige cikin motar Bad Man ɗin. Se ta sake jin kanta na wani irin tiriri. Se dai ganin yanda mutane ke kallanta ya sanyata haɗe ranta tana komawa cikin gidan.

"Ina matuƙar godiya. Allah ya saka da alkhairi." Gwani ya faɗa yana miƙawa Bad Man hannu. Shi ma nasa hannun ya miƙa sannan yace

"Babu damuwa. Gobe ba na da lokaci.. Zuwa jibi se mu ƙarasa abin da ya rage mana. Yanzu dai ka ji gaskiyar al'amari.."

"Ƙwarai kuwa.. Abin da ya rage kaɗai tarwatsa gidan nan kamar yanda na yi buri. Ita kanta wannan ɗin kuma ina son miƙata wajen hukuma dan a hukunta ta. Ba ma ita kaɗai ba.. ka yi haƙuri amma har da Abokinka.." Kamar ba shi ba Bad Man ya yi murmushi yace

"Babu komai.. Ni me taimaka maka ne ma."

"Ina godiya." Gwani ya sake faɗa. Dan babu ƙarya ya mugun jin daɗin taimakon nan da Bad Man ɗin ya yi masa. Daga haka ya tashi motar suka bar wajen. Ba su yi nisa ba Gwani ya sauka, dan ba ya son takura masa kuma. Bayan wannan taimakon da ya masa se ya sake kai shi gida kuma. Dan haka ya sauka ya tari mota ta kai shi gida.

Cike da mamaki yake kallan Lulu dake yanka albasa a zaune a tsakar gidan. Ummeey na zaune gefenta tana tsince zogale. Se ya kaasa ɗauke idanunsa daga kanta, wani abu me kama da shauƙin ganinta na kama shi. Uwa uba kuma da ya ganta tana taya mahaifiyarsa girki. Ga kuma waccan Ladin da ta gama wanketa tass a idanunsa ba tare da ta sani ba. Duk da shi ɗin da ma be taɓa zarginta ba amma dai yana buƙatar tabbatar da gaskiyar al'amari ko dan a yi wa tufkar hanci. Ba ƙaramin kyau ta yi ba daga inda take zaune. Duk da shigar dai kamar ta ko yaushe ce da take kindima uban hijabin nan. Se dai farar fuskarta ta yi matuƙar kyau cikin hijab ɗin da kalarsa da ɗauki fatar jikinta.

"A'ah Affan.. ka dawo?" Ummeey ta faɗa tana kallansa. Se a lokacin ya ƙarasa shigowa cikin gidan da murmushi kan fuskarsa yace

"Ehh Ummeey.. sannu da hutawa."

"Yawwah.." ya ƙare yana maida dubansa kan Lulu yana jira ya ji ko za tace wani abu ko dan ka da Ummeeyn ta saka ayar tambaya.

"Sannu da zuwa.." ya ji ta faɗa kamar wadda aka wa dole. Wani sanyi ya ji har cikin ransa. Bayan haka kuma ya san ita kanta Ummeey za ta ji daɗi.

"Yawwah kin wuni lafiya?" Da ma tana faɗa ta miƙe. Dan haka ba ta kula shi ba ta kalli Ummeey tace

"Ummeey ga albasar nan bari na je ɗaki."

"Toh sannu ɗiyata kin ji? Allah ya miki albarka.." Ummeey ta faɗa tana murmushi. Se da ta je ta ajje albasar sannan ta wuce ɗaki. Kai tsaye banɗaki ta wuce ta wanke hannunta kana ta koma ɗakinta. Ba ta daɗe da zama ba ta jiyo sallamarsa cikin ɗakin. Ba ta yi tunanin ze shigo ɗakin da take ba. Se dai cikin ƙanƙanin lokaci se ga shi cikin ɗakin da alama da ma kai tsaye nan ɗin ya taho. Da sauri ta kalle shi lokacin da ya ida shigowa cikin ɗakin. Se ta ɗauke kanta tana tura baki can ƙasa tace

"Ko me kuma ya kawo shi ɗakin mutane.." Jin yanda take wani ƙunƙuni ya sanya shi yin murmushi yana girgiza kai. Se da ya nemi waje ya zauna sannan yace

"Juyo ki kalle ni.." Shiru kawai ta yi kamar ba ta ji me yace ba.

"Ohk ba za ki juyo ba?"

"Ai na ga dai ba ka ba ni wayarka ba.." ta faɗa a kan laɓɓanta. Sarai ya ji abin da ta faɗa, hakan ne ya sanya shi sake yin murmushi.

"Ni ma ba batun wayar ne ya kawo ni ba.. Juyo ki ji.."

"Ina ji." Ta faɗa ba tare da ta juyo ba. Se ya sauke numfashi sannan yace

"Amm anjima zan fita za mu je wata musabaƙa da za a gabatar In Sha Allah.. se zuwa gobe kuma da dare nake saka ran zamu dawo In Sha Allah saboda wajen ba kusa ba ne." Da sauri ta juyo ta kalle shi kamar wadda ta yi mamakin abin da ya faɗa. Se dai a zahiri ita tunani take kenan yau ɗin ze bar mata ɗakin ne ita ɗaya? Ita kaɗai za ta kwana ba ta jin motsin kowa? Tana shirin jin ta sare da lamaein se kuma cikin ƙanƙanin lokaci ta tuna gadon nan da ya hanata kwana tun da aka kawo mata shi idan ba ya gidan za ta iya hawa ta yi kwanciyarta ba tare da wata takura ba.

"Toh.." shi ne kawai abin da ta faɗa.

"Babu fatan alkhairi?" Ya ƙare yana aza mata kyawawan idanunsa. Se ta ɗauke kai kawai. Da ya bari sun cigaba da mutunci tun bayan wannan hoton. Amma ya zo ya ɓata hakan ta hanyar sumbatarta kamar ba Malamin Addini ba.

"Ka gaida gida toh." Yanzu kam se da ya yi dariyar wannan sakarcin na Lulu. Wai ya gaida gida? Wanne gida kuma bayan wanda yake ciki? Jin da ya yi dai da alama daga haka ba za ta sake cewa komai ba ya sanya shi miƙewa a nutse dab da ze fice ya juyo cikin kwantar da murya yace

"Ki kula da kanki.." Daga haka ya fice daga ɗakin. Se ta bi shi da kallo lokacin da ya gama ficewa daga ɗakin. Ga shi har ze je ya kwana a wani wajen amma har yanzu be bata wayar ta kira Didinta ba. Ta murguɗa baki kamar yana gabanta.



... Se bayan la'asar sannan Gwani ya gama shiryawa tsaff. Kamar ko yaushe cikin favourite shigar nan tasa ya shirya, ya yi matuƙar kyau kamar ko yaushe. Daidai lokacin da ta fito daga cikin ɗakin shi kuma yake da niyyar shiga. Se ta yi maza ta koma ciki. Se dai kafin ta gama komawa ya sanya hannunsa ya riƙota. Se gata ta dawo kusa da shi sosai.

"Ni ka sake ni.." ta faɗa tana ƙoƙarin fuzge hannunta. Riƙo hannun ya sake yi sosai kafin ya yi amfani da ɗayan hannun nasa ya riƙo ƙugunta. Se da ya sanya idanunsa cikin nata idanun sannan yace

"Zan tafi.." Kamar ba za tace komai ba. Se dai kuma burinta ya saketa, hakan ne ya sanyata faɗin

"Ai dai na ce ka gaida gida koh?" Ta faɗa tana ɗauke kai.

"Ba haka nake so ba.. Ki ce Allah ya tsare hanya.." ya yi maganar yana sake kawo kusanci a tsakaninsu har lokacin idanunsa a kan fuskarta. Ita dai ba wani addu'a da za ta masa. Ko ya manta wulaƙantatan da ya yi. A hankali ta ji yana sake matsar da fuskarta kusa da tashi. Idanunsa kuma na kallan jajayen laɓɓanta. Ba ta san lokacin da ta yi saurin cusa leɓenta na ƙasa cikin bakinta ba. Jikinta na soma rawa ta buɗe bakin da ƙyar tace

"Allah Ya kiyaye hanya, Ya tsare, Ya dawo da kai lafiya." Be san lokacin da wata dariya ta ƙwace masa ba. Se kawai ya saketa saboda yanda tsoro ya gama bayyana a tattare da ita. Duk kuma uban addu'oin nan da take jerowa ya san saboda yanda ta ruɗe ne, tana tsoron kar a sake maimaita abin da ya faru. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauke wadda har se da ya jiyo sautinta. Ya sake kallanta yana kuma mamakin wannan tsoro nata.

"Ameen Ameen.." ya amsa da hakan yana ficewa daga ɗakin. Ta sake sauke wata ajiyar zuciyar tana sake mamakin halin Gwanin. Ashe da ma haka yake. Yanzu duk ya wani chanja kamar ba Gwani Affan na makarantarsu ba.

A tsakar gida ya tarar da Ummeey da Abeey dake shirin fita. A nutse ya ƙarasa cikin girmamawa yace

"Abeey ya jikin naka?" Murmushi Abeey ya yi sannan yace

"Ni fa na faɗa maka na riga da na warke.. babu abin da ke damuna, ka da ma ka kawo min maganar asibiti."

"Abeey ba dai ka san asibitin nan kawai." Gwani ya faɗa yana sake karantar yanayin Abeey. Shi ma dai a yanda ya gani kam kamar babu abin da ke damun Abeeyn. Saboda yanda jikinsa ya yi kyau sosai babu wata alama da ke nuna akwai abin da ke masa ciwo.

"Akwai haka ɗin ma.. Amma dai na warke."

"Toh Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana." Gwani ya faɗa har cikin ransa yana jin daɗin yanda ya ga Abeeyn.

"Ameen." Ummeey da ke gefe ta amsa da hakan.

"Za ka wuce ne?" Abeey ya tambaya.

"Ehh zan wuce Abeey.."

"Toh Affan Allah Ya tsare, Ya kiyaye hanya.. Se ka dawo. Bari na fita yara na jirana."

"Ameen Abeey.."

"A dawo lafiya." Ummeey ta faɗa tana kallan Abeeyn. Amsa mata ya yi da "Allah ya sa." Sannan ya fice daga gidan.



.. Tana idar da Sallahr isha'i ta koma kan gadon ta sake gyara shi tsaff. Ta karkaɗe shi tass sannan ta koma cikin wardrobe ɗinta. Yau ɗin wani daɗi take ji babu takura cikin ɗakin, ga shi kuma za ta kwana ba a ƙasa ba. Kasancewar babu Nepa ga kuma yanayin gari ya sanya ɗakin da zafi. Dan haka cikin jin daɗin rashin kasancewarsa cikin ɗakin ta shiga haska er ƙaramar fitilar cikin wardrobe ɗin. Wata ƙaramar riga mara hannu irin me zamammen wuyan nan da underwear ta ɗauko ta saka. Kasancewar duka ba su da nauyi ya sanya ta ji daɗinsu, dan ba su da takura ko kaɗan. Haka suke sakayau. Ko bi ta kan wani ɗan kwali ba ta yi ba ta koma kan gadon ta yi kwanciyarta da mifici a hannunta tana fifita. Duk da zafin da ake yi hakan be hana bacci soma ɗaukarta ba. Babu daɗewa kuwa wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.

A hankali ya tura ƙofar ɗakin gaba ɗaya jikinsa a gajiye yake jinsa. Babu haske ko kaɗan cikin ɗakin kasancewar har lokacin babu Nepa. Se ya wuce toilet kawai, se da ya je bakin ƙofar sannan ya kunna fitilar wayarsa ya yi amfani da ita wajen shiga toilet ɗin ya yi wanka ko ze ji daɗin jikinsa. Kaya marasa nauyi ya saka riga mara hannu da kuma gajeren wando. Ko bi ta kan ɗakin da Lulu take be yi ba, dan yana da tabbacin yanzun ta yi bacci ne. Kuma ba ya son takura mata. Hakan ne ya sanya kai tsaye ya wuce kan gadon. Cikin drawer gadon ya buɗe dan ɗaukar maganin sauro ya kunna. Cikin ikon Allah kafin ya ɗago se ga hasken Nepa.

"Ma Sha Allah.." Ya faɗa lokacin da fankar ɗakin ta soma kaɗawa. Se ya rufe drawer ya ɗago dan kashe socket ya yi bacci, dan har wani lumshewa idanunsa ke yi saboda bacci da kuma gajiyar da ta tarar masa. Maganar da yake ƙoƙarin yi ce ta maƙale lokacin da idanunsa suka sauka a kan Lulu da ke baje kan gadon ta yi ɗaiɗai da alama baccin na mata daɗi. Kanta da babu ɗan kwali ya sa gashinta da ke a tsefe kuma ba a ɗaure ba ya warware a kan gadon. Fuskarta ta yi mugun kyau. Yayin da ɗan ƙaramin bakin nan nata ta wani cuno shi gaba kamar me shirin yin kuka. Gaba ɗaya fararen hannayenta a buɗe suke. Saboda rigar da ba ta da hannu, hatta farin wuyanta a buɗe yake har zuwa wajen da wuyan rigar ya fara. Underwear ɗin da ta saka kuwa gaba ɗaya ya tattare ya koma saman gwuiwarta, hakan ne ya sanya kyawawan madaidaitan fararan ƙafafunta suka fito. Ɗan runtse idanunsa ya yi yana jin yanda zuciyarsa ta harba da ƙarfin gaske. Wajen minti 1 idanunsa a rufe yana so ya kawar da abin da ya ɗarsu a cikin ransa. Se dai hakan ya citira. Ya ɗan buɗe idanun nasa da cikin ƙanƙanin lokaci suka ɗan sauya kala kamar ba na shi ba. Se ya sake sauke idanun nasa a kanta lokacin da yake sake jin wata kasala na rufe shi. Da ma ga gajiyar da ya yi, duk se ya ji kamar an masa wani mugun duka. A nutse bayan ya sake lumshe idanunsa ya buɗe ya ƙarasa kan gadon, ya nemi gefe ya zauna a kasalance. Hannunsa ya kai inda socket ɗin ɗakin yake ya kashe. Cikin ƙanƙanin lokaci ɗakin ya sake yin duhu kamar ɗazun. Ba ka jin komai se ƙarar fanka da ke ta aikinta.


MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO52*


___Duk da kuma duhun hakan be hana shi sauke lumsassun idanunsa a kan Lulun ba duk da yanzun ba ya iya ganinta sosai. A hankali sanyin da ke cigaba da ratsa cikin ɗakin ya shiga ratsa kowacce gaɓa ta jikinsa tamkar wanda zazzaɓi ke shirin rufewa. Cikin sakannin da basu fi a ƙirgasu ba ya ji da gasken sanyin na neman yi masa illah. Gefe ɗaya kuma kamar wani abu memakon gajiyar da ya shigo da ita ta tafi. Se ji ya yi tana ƙaruwa, ga kuma kasalar dake sake rufe shi. A hankali ya laluba hannunsa ya ɗauki wayarsa dake ajje ya kunna fitila ya sake ajjeta inda ya ɗauketa. Da wannan hasken ya yi amfani da shi ya ɗauki ƙaramin bargon dake ajje a ƙasa wanda be lura da shi ba ɗazun. Babu ɓata lokaci ya lulluɓe jikinsa da shi saboda ko ze dena jin sanyin dake ratsa shi. Wanda ko ba a faɗa masa ba ya san zazzaɓi ke neman rufe shi. Ya ɗan gyara zamansa ba tare da ya sake kallan inda Lulu take ba ya lumshe idanunsa ko bacci ze samu ya ɗauke shi. Se dai tamkar wanda ake ja se ya ji sam ya kasa barin idanun nasa a rufe. Ya ɗan sake buɗe idanun nasa ya saci kallan Lulu da zuwa yanzun ta sake bajewa saboda yanda iska ke kaɗata ta ko ina. Baccinta take hankali kwance da alama baccin na kai mata. Nutsatstsen numfashinta na sauka a nutse kamar wadda ke tsara fitarsa da kanta. Yanda zuciyarsa ta ɗan sake bugawa da ƙarfi ne ya sanya shi sake lumshe idanunsa sannan ya buɗe su a lokaci guda. A nutse ya kai hannunsa kan tattausan hannunta ya riƙe shi cikin nasa hannun. Kamar hakan kawai ze yi se kuma ya saka ɗaya hannun nasa ya ɗagota gaba ɗayanta se dai cikin takatsantsan be yi wata wata ba ya ɗorata a kan ƙirjinsa. Be kuma yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar bargon ya lulluɓe rabin jikinsu da shi. A nutse ya sake yin amfani da hannunsa wajen shigar da ita cikin jikinsa ya rungume ta da dukka hannayensa. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauke sanda ya jita cikin jikin nasa. Cikin lokaci ƙanƙani wasu sababbin al'amura da ya soma ji a kanta kwanakin nan suka cigaba da ta'azzara. Yanda take sauke numfashi a nutse a kuma kan ƙirjinsa ya sanya duk wani numfashi da za ta fitar se ya ji tamkar da zuciyarsa take ƙoƙarin tafiya. Sake ƙanƙameta ya yi jin da ya yi jikinta da sanyi ba kamar nashi ba da ke ɗauke da zafin zazzaɓi. Duk ba ta san abin da ke faruwa ba saboda nannauyan baccin nan da ya ɗauketa. Har kuma yanzun be saketa ba. A haka ya gyara musu kwanciya duk da yanda gaba ɗaya jikinsa ya sake yin sanyi. Wata sabuwar kasala ta rufe shi. Be kula da hakan ba se gyara mata kwanciyar da ya yi cikin takatsantsan. Dan ba ya so ta tashi ballantana ta hana kanta kwanciya a kan gadon. Duk da haka se ya kasa ko da lumshe idanu ne ballantana ya yi baccin. Be yi tunanin kasancewarta a jikinsa ze hana shi bacci ba. Ya ɗauka idan ya ji ta kusa da shi ze yi bacci ne cikin nutsuwa. Se kuma ga shi hakan ya citira. Cikin sarewa da lamarin ya dubi cute baby face ɗinta lokacin da take cigaba da sauke numfashi a kan dokin wuyansa. Ya ɗan ɗauke kai yana sake kokawa da zuciyarsa, se dai ita kam hankalinta kwance ta cigaba da sauke masa numfashi a kan wuyansa. Bugun da zuciyarsa ta shiga yi ne wanda ya wuce misali shi ne ya sanya shi jan wani dogon numfashi. Ya ɗauka ze iya cigaba da daurewa. Se dai ina ya kasa. Dan haka cikin ƙanƙanin lokaci ya birkitata gefe. Ba tare da ɓata lokaci ba ya haɗe bakinsu waje ɗaya. Ya shiga kissing nata a zafafe cike da shauƙi. Cikin nauyin bacci, ta ji wani sabon al'amari. Dan haka cikin sauri ta buɗe idanunta dan ganin abin da ke faruwa. Tun kafin ta ida buɗe idanun nata ta fahimci abin da ke faruwa. Dan haka a tsorace ta buɗe bakinta dan yin ihu ko dan a taimaka mata. Ko kuma shi ɗin ya taimaka ya saketa. Se dai ta ma manta bakin nata na cikin nasa ne. Ta yanda ko da me za ta yi kuwa babu wata wanda ze jita. Yanayin yanda yake kissing ɗin nata ne ya saka mata tsoro. Cikin zafin nama ta shiga jan jikinta dan ta fuzge bakinta amma ta kasa. Se kawai ta shiga zubar da hawaye kamar an kunna famfo. Ta shiga rera kukan da babu sauti lokaci ɗaya tana kai masa duka ko dan ya saketa. Se da ya gaji dan kansa sannan ya soma ƙoƙarin cika bakin nata bayan ya tabbatar ya riƙeta gam a cikin jikinsa. Tana jin ya cika mata bakin nata da take ji idan be yage ba toh ya tsinke. Se ta tashi a zabure dan dira daga kan gadon. Da sauri ya janyota se ga ta ya yi mata kyakkyawan masauki a cikin jikinsa. Kawai se ta fashe da kuka cikin muryarta dake rawa ta buɗe baki tace

"Don Allah ka sake ni.. Ka sake ni ni.." Numfashi ya ajje. Shi se yake ji ma kamar maganar da ta yi ƙara masa ƙaimi ta yi.

"Zan haƙura Afaaf.. Amma ke ma ki yi haƙuri.." ya ba ta amsar kamar me raɗa. Ba ta fahimci abin da yake nufi ba dan ita dai burinta ya saketa. Hakan ne ya sanyata saurin faɗin

"Na haƙura don Allah ka sake ni.." Ta faɗa tana girgiza kanta gwanin ban tausayi. Ilahirin jikinta har ya ɗauki rawa kamar mazari. Da ƙyar ya iya buɗe baki yace

"Ki yi baccinki.." Da sauri ta sake girgiza kai tana niyyar soma magana yace

"Shhhh... Kar ki ce komai ki yi bacci nace." Gaba ɗaya ta gama ruɗewa, dan ita se ta ji ma muryar kamar ba tasa ba. Burinta kawai ya saketa. Se dai shi kam sam ba shi da alamar yin hakan. Hannunta na kan bakinta da ta kasa saki tun ɗazun. Wanda take jinsa ya mata wani iri kamar ba nata ba. Se ta yi shirun kawai. Se dai daga zarar ta tuna abin da ya mata yanzun se ta ji wasu hawaye sun zubo a kan kuncinta. A tsorace take yanzun matuƙa, hakan ne ya sanya memakon numfashinta dake fita a hankali, yanzun da sauri yake fita kamar wadda ta yi tsere. Duk ta kasa kwanciya haka kawai, se mutsu mutsu take yi, ko za ta iya samun dama ta kufce daga jikinsa. Se dai ba ta san hakan sake kunno shi take yi ba. Ya yi niyyar ya barta ko baccin ne ta ɗan sake yi se dai hakan ma ya gagara. Be san lokacin da ya gyarata ba ya shiga aika mata da wasu zafafan saƙonni waɗanda suka kusan sanya ƙwaƙwalwar Lulu fashewa. Tsoro, fargaba, bugun zuciyar da ya zarce na ƙa'ida fiye da zaton me zato. Gaba ɗaya Gwanin ya chanja mata, ya koma kamar ba shi ba, se ta koma ganinsa kamar wani mayunwacin zaki, ko kuma wani mugun abu dake neman hallakata. Tun tana ƙoƙarin ƙwace kanta ko kuma ta zame kanta, har dai ta lura hakan ba me yiwuwa ba ne. Karo na babu adadi ta fashe da wani marayan kuka me tsuma zuciyar me sauraro. Tana girgiza kanta idanunta a rufe waɗanda suka kasa buɗuwa saboda kukan da ta sha. Fuskarta gaba ɗaya ta yi caɓa caɓa da hawaye. Da ƙyar ta buɗe bakinta muryarta na wani irin karkarwa, a cunkushe gwanin ban tausayi tace

"Ka yi haƙuri don Allah ka ƙyale ni.. wallahi zan mutu.. don girman Allah ka ƙyale ni." Ta ƙare tana sake fashewa da wani sabon kukan. Lumsassun idanunsa ya buɗe da ƙyar ya zuba su a kan fuskar Lulun. Duk da yanda yake jinsa amma hakan be hana shi jin tausayinta ya kama shi ba. Ko ma mene ne ya san ita ɗin yarinya ce, dole ne ta tsorata. So ya zama dole ya bita a hankali cikin rarrashi. Dan shi kan shi tausayinta yake ji. Musamman idan ya ji yanda jikinta ke cigaba da rawa. Har wani zafi jikinta ya ɗauka. Ga farar fuskarta da ta cakuɗe ta yi wani irin jaajir. Se ya girgiza kai a nutse yace

"Ki yi haƙuri Afaaf.. Ki taimaka min kin ji?" Ya ƙare muryarsa da ƙyar take fita. Ita sam ba ma ta san me yake cewa ba, burinta kawai ya saketa. Se dai kwata kwata ta kasa ko da ƙwace hannunta ne daga jikinsa. Kamar wanda ba mutum ba ne ya riƙeta. Duk da yanda gaba ɗaya tausayinta ya rufe shi cikin ƙanƙanin lokaci, hakan ne ya sanya shi cigaba da rarrashinta duk da ya fahimci ba fahimta take yi ba. Se dai a daren Gwani be haƙura ba se da ya maida Lulu ta zama tashi gaba ɗayanta.


Rungume yake da ita cikin ƙirjinsa kamar wanda ze maidata ciki. Wata kalar soyayya da tarin tausayinta yake ji. Se a yanzun yake jin haushin kansa da ya gaza haƙuri ya ƙyaleta bayan yanda tarin tsoro da kuma firgici suka gama bayyana kansu tattare da Lulun. Hawaye kawai ke zubowa daga cikin idanunta, babu sauti ko kaɗan. Hatta numfashi da ƙyar take ajjewa. Jikinta kuwa ko hannunta ba ta iya motsawa saboda yanda take ji kamar an tsatstsaga mata ilahirin jikinta ne. Kawai se ya ƙurawa fuskar tata ido yana cigaba da kallanta. Gaba ɗaya ya ma rasa da wanne irin baki ze yi amfani wajen ba ta haƙuri da kuma kwantar mata da hankali. Dan ko ba a faɗa ba ya san ita kaɗai ta san me take ji a jikinta. Dan kuwa ko daga yanayin yanda take sauke numfashi ya isa ya nuna maka yanda ta galabaita. Wajen minti 10 a haka be yi ƙoƙarin yin komai ba dan shi kansa ya gaza aikata komai. Duk da yanda yake jin wani irin farin ciki na mamaye shi, amma tausayinta da yake ji ya danne komai. Hakan ne ya sa shi kansa jikinsa a matuƙar sanyaye yake. Hannu ya kai kan fuskarta ya share mata hawayen da suka ƙi tsayawa da zubowa. Karo na farko ya buɗe baki a nutse yace

"Ki yi haƙuri.." Idanunta a rufe suke gam, se dai ba bacci take yi ba. Tsananin azaba ne kawai ya sanya hakan. A nutse ya ɗaga kanta ya ajje kan pillow har lokacin ya kasa janye idanunsa daga kanta. Kai tsaye banɗaki ya faɗa duk da har lokacin be dena jin zazzaɓin ba amma a haka ya yi wanka da ruwan sanyi. Bayan shuɗewar wasu mintuna ya fito. Ya ɗauki wata jallabiyya mara nauyi ya saka sannan ya dawo kan gadon. Abin da ya ba shi mamaki har lokacin hawayen be tsaya ba, ba kuma ta buɗe idanunta ba. Ba kuma ta motsa daga inda ya barta ba. Wani sabon tausayinta ya sake kama shi. Ya runtse idanunsa yana sake jin haushin kansa. Kai tsaye inda flask ɗin da suke ajje ruwan zafi yake ya nufa. Cikin sa'a kuwa akwai ruwa, ya ɗauka ya wuce da shi banɗakin ya sirka shi daidai misali sannan ya sake fitowa. A hankali ya ƙarasa kan gadon idanunsa na kanta. Ya saka hannunsa da niyyar ɗagata gaba ɗayanta se ta miƙa hannunta da shi kansa take ji ya mata nauyi ta ɗaga shi alamar kar ya matso inda take. Ya ɗan lumshe idanunsa yana buɗewa still a kanta. Se ya sake matsawa ɗin se dai ya sauke hannunsa. Ya sunkuyar da

Please Login or Register in order to submit comment