Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa ɗakin da take zaune a ciki. Kai tsaye kan gado ta nufa ta haye. Babu ɓata lokaci ta ja bargo ta lulluɓe jikinta cike da fatan bacci ya zo ya ɗauketa, dan ba ta so Baba Atine ta dawo ta tambayeta yanda aka yi. Ba za ta iya mata ƙarya ba idan ta tambayeta, ba ta so kuma ta ga kamar ba ta isa da ita ba ne shi yasa taƙi shiga ɗakin. Runtse idanunta ta yi tana karanto addu'oi. Babu daɗewa kuwa bacci ya kwasheta me cike da mafarkin en gidansu da ta matuƙar yin kewarsu.

... Baccin da ya yi yau me yawa ne, dan shi kansa se da ya yi mamaki lokacin da ya farka ya ga tsawon awannin da ya kwashe yana baccin. Ya ɗan lumshe lumsassun idanunsa da suka ɗan ƙanƙance suka ƙara kyau, sanda ya gama shiryawa ya haɗe cikin wasu haɗaɗɗun tsadadddun kaya. Fitowa ya yi daga cikin ɗakin hannunsa ɗauke da wayarsa yana dannawa, da alama wani abun yake dubawa cikin wayar. Ko tsakiyar parlourn be kai ba Mommah ta shigo cikin sashen kamar ko yaushe ta yi kyau cikin wata tsadaddiyar atamfa da aka mata ɗinki me kyau. Be damu da motsin mutum ɗin da ya ji ba, se cigaba da takawa da ya yi, daidai ze giftata tace

"Areef.." Dakatawa ya yi saboda muryar da ya ji, ya kalleta da mamaki a kan fuskarsa. Be amsa kiran da ta masa ba se cewa ya yi

"Wani abu?" Girgiza kai Mommah ta yi tana murmushi tace

"A'ah kawai dai na zo wajen ɗiyata ne.."

"Ɗiyarki?" Ya tambaya yana kallanta. Se da ta gyara tsayuwarta sannan tace

"Wace ce ɗiyata kuma banda matarka Areef?" A kan laɓɓansa ya maimaita kalmar "Matata." Se kuma ya yi yaƙe yace bayan shi ma ya gyara tsayuwarsa

"Ina ganin mutuncinki Mommah.. So pls stay away from this matter.. Har yanzu am single, ba ni da wani abu me makamancin wannan sunan.." ya ƙare a fusace cike da jin haushin Mommahn. Girgiza kai Mommah ta yi tana sake mamakin halin Areef ɗin, da ba kowa ce sanadin lalacewarsa ba face mahaifiyarsa, wadda idan da za a kwana ana faɗar hakan ba za ta taɓa yarda ba.

"Banda abinka Areef me ye na.."

"Plss!!" Ya faɗa yana ɗaga hannunsa idanunsa a ƙanƙance. Be kuma ƙarasa faɗar abin da ya yi niyya ba ya fice daga ɗakin. Binsa da kallo Mommah ta yi tana sauke ajiyar zuciya. Ba ta yi tunanin hakan daga gare shi ba sam. Haƙiƙa ta san tana ƙaunar yaron, amma kuma tunda har ya yi mata warning kamar ya manta ita ɗin wace ce, ta san idan har ta cigaba da abin da ta ƙudurta zumuncinsu ka iya lalacewa a yanda ta ga Areef ɗin, tunda har ya iya buɗe baki ya faɗa mata magana ba tare da jin komai ba. Se dai koma mene ne za ta yi ƙoƙari wajen ganin ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen saita wannan ma'auratan. Ta sake girgiza kai a karo na barkatai tana sake mamakin wannan bauɗaɗɗen hali na Areef ɗin. Idan banda abinsa ma ai yarinyar da aka aura masa ita ce abar tausayi, ita ya kamata a lallaɓa, a kuma tausayawa saboda auren Areef ɗin da ta yi, wanda ba shi da alƙibla ko kaɗan.

Tura ƙofar ɗakin ta yi a hankali ta shiga da sallama a bakinta. Didi dake zaune gefen gado ta amsa mata sallamar, tana faɗaɗa fuskarta da murmushi sanda ta fahimci wace ce.

"Sannu da zuwa.." Shi ne abin da Didi ta faɗa tana zamewa ƙasa daga kan gadon. Hannu Mommah ta saka ta kamota tana faɗin

"Yawwah daughter.." Se da ta zaunar da ita kan gadon sannan suka gaisa kafin Mommah tace

"Ya kuma haƙuri da zaman gidan nan?" Murmushin yaƙe Didi ta yi kawai ba tace komai ba. A kodayaushe hankalin Didi sake burge Mommah yake yi, komai nata yinsa take cikin sanyi.

"Ki cigaba da haƙuri kin ji? In Sha Allah komai ze wuce kamar be taɓa faruwa ba Uhmm?" Ta ƙare tana kallanta. Se ta jinjina kai sannan a hankali ta buɗe bakinta tace

"Tohm.."

"Yawwah.. Akwai wata matsalar ne kuma?" Mommah ta sake tambaya. Da sauri ta girgiza kai har cikin ranta tana jin daɗin kulawar mutanen nan biyu a cikin gidan nan. Har kuma yanzu ta kasa amincewa ba Mommah ce sirikarta ba.

"Tohm shi kenan bari na koma.." Mommah ta faɗa tana miƙewa. Ɗaga manyan kyawawan idanunta Didi ta yi tace a sanyaye

"Don Allah ina son in kira Ammina.." Murmushi Mommah ta yi ta koma ta zauna a kan gadon, ta miƙa mata tsadaddar wayar hannunta tace

"Saka number ki kira.. Idan kun gama ki ajje min Atine se ta taho min da ita.." Cikin jin daɗi Didi tace

"Toh na gode sosai.." Girgiza kai Mommah ta yi tace

"Babu wannan tsakaninmu.. Ki ɗauke ni a matsayin mahaifiyarki shi ne kawai.." Wani murmushin dai Didi ta sake yi daidai lokacin da Mommah tace

"Aff.. Idan an ɗan kwana biyu, wato abubuwa sun ɗan sake lafawa za ki soma shiga sashen Hajiya Salma kina gaidata." Haka kawai ta ji ƙirjinta ya buga, duk da ba ta san wace ce Hajiya Salman ba, amma se take ji kamar ita ce mahaifiyar mijin nata.

"Toh" kawai ta amsa da shi. Hakan ya bawa Mommah damar ficewa daga ɗakin dan bata waje ta samu ta yi wayar cikin nutsuwa.

Tun kafin wayar ta gama ringing take murmushi, burinta kawai ta ji Ammin ta ɗaga. Babu daɗewa kuwa Ammin ta ɗaga da sallama ɗauke a kan bakinta. Ai ko iya amsa sallamar Didi ba ta yi ba se miƙewa da ta yi tana jin wani irin sanyi na ratsata, ta buɗe bakinta da ƙyar tace

"Amminmu.."

"Didi.." Ammi ta faɗa ita ma cike da farin cikin jin muryar ɗiyar tata.

"Na'am Ammi ni ce.. Na yi kewarku sosai Ammi.. Ina jin gaba ɗaya babu daɗi Ammi.." Tsoro ne ya ziyarci Ammi jin abin da Didin ta faɗa, cikin sanyi tace

"Akwai matsala ne a nan gidan?" Ta san Ammin daga lokacin da ta ji akwai wani abun za ta tayar da hankalinta ne, hakan ne ya sanyata girgiza kai tace

"A'ah Ammi babu komai fa.."

"Kin tabbatar?" A hankali ta amsa da

"Ehh.." Se a lokacin Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta nemi waje ta zauna, suka sake gaisawa da Ammin sannan Didi tace

"Ammi ina ɗan uwa?" Murmushi Ammi ta yi tace

"Yana gidan Lulu.."

"Kai Ammi.. Ni fa?" Ta faɗa a shagwaɓe. Girgiza kai Ammi ta yi tace

"Ke baki san kin girma ba koh? Toh maza cigaba.. Za a kawo miki shi ki kwantar da hankalinki kin ji?" Turo baki ta yi sannan tace

"Toh.." Daga haka suka cigaba da hira, Ammi na yin amfani da wannan damar wajen yi wa ɗiyar tata faɗa sosai.


... Zaune yake a kan kujera hannunsa ɗauke da remote yana kamo wata channel. Sanye cikin wata shegiyar dakakkiyar shadda da ta matuƙar karɓar jikinsa. A cikin wayoyinsa dake zube a gefensa ɗaya ta shiga ruri, kamar ba ze kula ba, se da ya kamo channel ɗin sannan ya dubi wayar. Da mamaki yake bin number da kallo, a ransa yana tunanin ko lafiya? Kawai dai se ya ɗaga wayar, ya kara a kunnensa. Daga can ɓangaren cike da girmamawa aka gaishe shi. Ya amsa yana gyara zamansa, dan ya san tunda ya ga wannan kiran akwai wata a ƙasa.

"Yallaɓai ka yi haƙuri na kira ka ba tare da sanin dalilin kiran ba.."

"Babu damuwa.." Dad ya amsa da hakan. Ajiyar zuciya na can ɓangaren ya sauke kafin ya soma faɗin

"Rankayadaɗe idan babu damuwa ko da na minti biyar ne ka ba mu dama mu yi wata magana. Kwanaki wata magana na ta yawo, amma ni ban bi ta kanta ba saboda na ɗauka ko irin ana yaɗawa ne haka kawai. Se kuma daga baya na fahimci lallai mutanen da gaske suke yi, abin da ya sanya ni yin bincike kenan. Se dai ban samu wani ƙwaƙwƙwaran dalili da zan iya kare Areef Matawalle ba. Hakan ne ya sa na yi wannan gangancin. Na yi wannan kasadar, na yi wannan tsaurin idon na kira ka dan ka bayyanawa mutane gaskiyar al'amari a kan abin da ya faru.." Daga haka ya kora masa bayani a kan kai Bad Man da Didi asibiti da aka yi. Shiru Daddy ya yi na en wasu sakanni. Shi dama ya san za a zo wajen, ya riga ya fahimci hakan za ta faru saboda munafukai da suka musu yawa. Murmushi ya yi me sauti sannan ya soma faɗin

"Ba na buƙatar wata hira da zan wanke ɗana ko ni kaina. Dama wannan ɗin halayyar ɗan adam ce. Zargi! Saboda haka abin da kawai zance mutane su dena zargi a kan abin da basu da tabbaci a kai, dan kuwa ita wannan ɗin matar Areef Matawalle ce.." Shi kansa da ya ji abin da Daddy ya faɗa se da mamaki ya kusa kashe shi. Ashe dama Areef ɗin yana da aure amma babu wanda ya taɓa sani? Lallai kam wannan rahoto ne babba. Bayan sanin gaskiyar al'amarin da ya faru, ga kuma ƙarin wani information ɗin da suka samu. Ba ya so ya fusata Alhaji Matawallen da tambayoyinsa, hakan ne ya sanya shi faɗin

"Godiya nake rankayadaɗe.. Allah ya ƙara girma.." Daga haka Daddy ya katse wayarsa yana girgiza kai yana sake mamakin al'amarin mutanen duniya. Kallan da be yi ba kenan, se miƙewa kawai da ya yi ya bar ɗakin ma gaba ɗaya.


.. A ɓangaren su Lulu kuwa tun lokacin da ta baje a ƙasan nan tana cigaba da kukanta, ba ta yi tunanin kuma ze sake dawowa ma cikin ɗakin ba. Se dai bayan wajen minti 15 se ga shi ya shigo ɗakin hannunsa ɗauke da plate dake ɗauke da shinkafa da taliya da miya. Ƙarasawa ya yi ya zauna a gefen gadon yana kallan yanda har lokacin take a wajen, zuwa lokacin ta gama kukan se wasu uban ajiyar zuciya da take saukewa kamar za ta haɗiyi zuciya. Shiru ya yi na tsawon sakanni yana tunanin ta inda ze fara kuma. Dan har ga Allah ya gaji da jin wannan kukan, banda ciwon kai babu abin da yake saka masa. A hankali ya buɗe bakinsa yace

"Tashi ki ci abinci.." Idan gadon da yake kai ya kalle shi toh Lulu ta kalle shi. Ba ta ma nuna alamar ta san da wanzuwar wani a wajen ba, ballantana ta nuna ta ji abin da ya faɗa. A karo na biyu ya sake maimaita abin da ya faɗa ɗin. Nan ma dai shiru, izuwa lokacin ransa ya gama ɓaci, dan kuwa ya san rashin kirki ne kawai ya hanata amsawa. Ban da haka ya san tana jinsa. Ajiye plate ɗin ya yi, ya miƙe kyakkyawar fuskar nan tasa a haɗe kamar me shirin yin dambe, dan babu ƙarya zuwa yanzu ya gaji da wannan iskancin nata. Se ya shiga tattare hannun rigarsa dan ya ji daɗin yi mata ɗurar.

"Za ki ci ko na yi miki ɗura?" Ya sake faɗa yana kallanta. Nan ma dai ba ta amsa ba. Jin shiru be sake cewa komai ba ne, ya sanyata ɗan ɗaga idanunta a sace dan ganin abin da yake yi. Se ganinsa ta yi yana ƙoƙarin zuwa inda take. A miliyan ta zabura ta sake yin baya tana fashewa da sabon kuka da dashashshiyar muryarta.

"Wai ni ina ruwanka da ni? Ai dai cikina ne ba na wani ba.. ka rabu da ni mana na ce maka.." ta faɗa ɗin dai da dashashshiyar muryarta. Numfashi ya ɗan fitar daga cikin hancinsa sannan ya cigaba da takawa zuwa inda take.

"Ka dena taɓa ni ni ba er iska ba ce. Kar ka kuma taɓa ni wallahi.. Ni don Allah ka ƙyale ni ba na ci.." ta ƙarashe maganar a raunane. Dan izuwa yanzu a tsorace take da Gwanin matuƙa. Burinta kawai ta dena ganinsa a kusa da ita. Be san sanda wani murmushin gefen baki ya suɓuce masa a kan laɓɓansa ba. Ya kai hannunsa ya ɗan shafa sumar kansa dake a buɗe. Wato ita wannan taɓatan da ya yi duk shi ne ya tsoratar da ita. Ya sa ta yi laushi haka.

"Wallahi ko ki ci ko na saɓa miki.." ya yi maganar a kaurare kuma a ɗan zafafe bayan ya maida fuskarsa yanda take ɗazun.

"Kar ka matso nan. Kar ka taɓa ni na ce maka. Idan ba haka ba wallahi se na tona maka asiri a wajen duk waɗanda ke maka kallan Malamin Addini.." Ta faɗa a tsorace tana kallansa sanda ya rage saura tazara kaɗan ya cike wadda ke tsakaninsu. Yanzu kam se da ya yi dariya yana girgiza kai cike da mamakin wannan wautar ta yarinyar nan. Dan dai a samu lafiya se ya koma kan gadon ya zauna yace yana kallanta.

"Na ji ba zan taɓa ki ba. Kuma kar ki tona min asiri, amma ki ci abincin nan.." Ya faɗa kamar ba Gwanin da muka sani ba.

"Ba na ci.." ta sake faɗa tana kauda kai a zafafe. Zuwa yanzu kam yana ganin gwara ya san abin yi dan kar ta sake kai shi bango. Ga kansa dake ciwo, ga baccin da yake ji amma tana ƙoƙarin ɓata masa rai da lokaci. Se da ya daure sannan ya iya furta

"Ba ki yadda da abin da na faɗa ba kenan? Fyn.." ya yi maganar yana miƙewa. Hannu ta kai ta janyo plate ɗin da sauri wasu hawaye na kwarayowa daga cikin idanunta, ba ta san sanda ta fara kai abincin bakinta ba. Duk da cikin nata ya ɗan lafa, amma har yanzu da akwai ragowa. Tana yi kuma tana cigaba da kukanta da ƙananun maganganu a kan laɓɓanta. Se da ta ɗan ci ba laifi duk da yanda abincin ya yi daɗi har a bakinta amma taurin kai irin nata ba ze bari ta yi abin da ze sa ya ɗauka umarninsa take bi ba, ta ture plate ɗin gefe tace a kufule

"Ai dai se.."

"Shhhh!!" Ya faɗa yana ɗora hannunsa a kan laɓɓansa idanunsa a kanta yana maka mata wani kallo. Duk da ba ta kalle shi ba amma ta fahimci kallan gargaɗin da yake mata, hakan ne ya sanyata haɗiye maganar da ta yi niyyar faɗa. Ya tura mata ruwa kaɗan cikin kofi ba tare da yace komai ba. Se da ta gallawa ruwan harara sannan ta ɗauka ta sha kaɗan ɗin. Se a lokacin ya sauke ajiyar zuciya ya miƙe daga kan gadon ya fice daga wajen ma gaba ɗaya zuwa inda ya saka bargonsa yana sake jin yanda kansa ke wani irin sara masa. Binsa ta yi da harara tana faɗin

"Mugu kawai.." ta murguɗa baki tana miƙewa tana leƙen inda ya fita ɗin. Se ta miƙe duk da tana jin jiri na ɗan kwasarta amma ta ƙudurcewa kanta ba za ta sake kwana a ɗakin ba koma me za a yi mata. Dan haka wannan ƙaramin ɗakin dake cikin ɗakin ta shiga leƙawa. Da yake akwai nepa a lokacin ya sanya tana iya ganin cikin ɗakin. Komawa ta yi kan gadon, ta yayo zanin gadon da Pillow ta shiga cikin ɗakin da ƙarar kukan ƙwari ta cika shi. Jefar da zanin gadon kawai ta yi dan ba ta da ƙarfin tsayawa ta saita shi, ta yada pillown hannunta. Tana shirin kwanciya aka ɗauke nepa. Take wani uban duhu ya mamaye gaba ɗaya ɗakin, kukan ƙwarin kuma kamar an daɗa shi ya ƙaru. Cikin matuƙar tsoro da kiɗimewa ta buga wani uban tsalle ganin da ta yi gaba ɗaya idanunta ya mamaye da duhu kawai. Se dai ba ma ta san inda ta nufa ɗin ba ƙofa ba ne. Jin da ta yi ta taɓa gini ne ya sanyata kawai ta saki ƙara a matuƙar tsorace ta shiga lalube da hannayenta dan gano inda ƙofar take. Daidai lokacin da ta zo inda ƙofar take, shi kuma ya shigo cikin ɗakin saboda ihun da ya ji ta saki wanda ya tsorata shi yana fatan ba wani abun ne kuma ya sameta cikin ɗakin ba. Se hannunta ya sauka a kan ƙirjinsa, da yake ba ta tsammata ba se kawai ta yo gaba kamar za ta kifa. Be yi ƙoƙarin tareta ba saboda duhun da ya mamaye ɗakin, se da ya ji tace

"Wayyyyo.." Sannan ya yi saurin saka tattausan hannunsa ya riƙo tsintsiyar hannunta. A tsorace jin hannunta cikin wani hannun ta buɗe baki cike da sarewa da saddaƙarwa cewar yau ta haɗu da aljanu ta fashe da kuka tana kuma ƙwace hannunta lokaci ɗaya tana faɗin

"Na shiga uku.." Jin yanda hannun nata ke rawa ne da yanda take magana alamar gaba ɗaya a tsorace take ya sanya shi ɗan lumshe idanunsa ya buɗesu a lokaci ɗaya, kawai se ya janyo hannun nata se gata ta faɗo cikin jikinsa. Daidai lokacin da ilahirin jikinta ya sake ɗaukar rawa fiye da yadda be tsammata ba. Gaba ɗaya a birkice take, a matuƙar tsorace take, kamar ma wadda ba a hayyacinta take ba, ga muryarta da ta dena fita, haka zalika ba ta da wani ƙarfi. Amma duk da haka ba ta dena magana ba tana kuma ƙoƙarin ƙwace kanta. Hannunsa ya ɗauka duka biyun ya zagayeta da su cikin jikinsa sannan a hankali ya kai bakinsa saitin kunnenta yace

"Kee!! Ki yi shiru.. ki samu nutsuwa babu abin da ze faru.." ya faɗa a nutse, a ransa yana mamakin dama haka take?..


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO35*

___Runtse idanunta ta yi zuciyarta na cigaba da harbawa dan tabbas ta matuƙar tsorata. Har hakan ya sa ta kasa taɓuka komai kawai ta shiga sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri, har kuma lokacin ta kasa buɗe idanunta. Maganarsa da ta ji ita ce ta sanar da ita inda take. Hakanne ya sanyata buɗe ido da sauri ta ture hannunsa dake bayanta sannan ta fice daga jikinsa daidai lokacin da bugun zuciyarta ya ƙaru. Kamar haɗin baki se ga nepa sun dawo da ita. Wasu zafafan hawaye suka zubo mata a kan fuskarta har kuma lokacin bata dena jin tsoro ba, ga kuma buɗe ido da ta yi ta ganta a jikin Gwanin. Ita ta rasa abin da ke damunsa, dama tun can ɗan iska ne? Shi ne ba ta sani ba. Shi burinsa kawai ya taɓata? Ina ruwansa da duk abin da ya sameta? Ai dama haka take so, daga nan kuma kawai ta wuce a zo a fiddata daga gidan nan. Sauri ta yi ta koma kan gadon ta haye, ko bi ta kan zanin gadon ba ta yi ba, ta kwanta kawai tana jan hijab ɗinta ta lulluɓe jikinta da shi. Har lokacin jikinta be bar rawa ba, haushin Gwanin na sake cikata. Ji take kamar ta fasa ihu ko za ta ji sanyi a ranta. Se dai kuma ta san tana yin ihun ze sake shigowa ne ƙila ma ya sake taɓata. Hakan ne ya sa ta kama bakinta ta dinga jan sheshsheƙar kuka a hankali. Se a lokacin ya sauke ajiyar zuciya lokacin da ya lura da ta kwanta kuma babu kukan, ko babu komai ze samu ya ɗan runtsa ko yaya ne.


... "Ni kina ba ni mamaki Yaya wallahi. Gaggawar ta meye ne? Se kace baki san wane ne Areef ba? Kin riga dai kin san halinsa ballantana ki ce kina tsoron wani abun.."

"Uhmm Makiyy ba za ki gane ba ne. Wallahi bana son auren nan kwata_kwata. Ban san dalilin da ya sa ba na so ba. Ke ko da ba Daddynsa da kansa ya samo masa matar nan ba, shi ya kawota da kansa, ba na tunanin zan bari ya auri yarinyar. Haka nan kawai na ji na tsaneta wallahi.." Girgiza kai Aunt Makiyy ta yi kamar Mom ɗin na kusa da ita tace

"Duk wannan ba wata damuwa ba ce. Za a raba auren dama ai, ko ta miki ko ba ta miki ba kuwa. Dan ba ze taɓa yiwuwa a yi wa Areef auren cushe ba, ba tare kuma da garin nan gaba ɗaya ya jijjiga ba.. Yanzu dai kin san abin da nake so dake?" Girgiza kai Mom ta yi tace

"A'ah ina jin ki.."

"Kar ki sake komawa sashen nan.. Ki kuma yi duk yanda za ki yi Daddyn Areef ya san da hakan.. Watan nan na cika komai ze baje.. Ki bar komai a hannuna, na miki alƙawarin gyara komai sannan in wargaza abin da ba ma so.." Dariya Mom ta yi cike da yabawa da wannan ƙoƙarin na ƙanwar tata tace

"Toh shi kenan Makiyy. Na san ba za ki ba ni kunya ba. Zan kuma yi iya bakin ƙoƙarina na ga ban sake zuwa sashen ba.."

"Haka nake so.." Aunt Makiyy ta faɗa tana murmushi.


... Sanye cikin doguwar rigar atamfa da ta matuƙar amsar ƙaramin jikinta. Ta saka wani baby hijab shi ma da ya karɓi zagayayyiyar doguwar farar fuskarta. Qur'an ne a hannunta tana karanta suratul baƙara. Baba Atine ta turo ƙofar ɗakin ta shigo da sallama. Da yake dab take da ƙarasa karanta ayar ƙarshe, ya sanyata ƙarasawa ta yi addu'a kana ta ajje Qur'an ɗin a kan bedside drawer ta juya ta amsa sallamar Baba Atinen. Murmushi suka sakarwa junansu, kafin Baba Atine tace

"Karatun ne?" Ta tambaya tana murmushi. Ita ma murmushin ta yi kamin ta jinjina kai kawai.

"Toh Allah ya taimaka.." In ji Baba Atine. Se da ta amsa da "Ameen" sannan tace

"Kin kai coffee ɗin kuwa?" Da sauri ta ɗaga kai ta kalli Baba Atinen ba ta san sanda a furta

"Yau ma se an kai?" Murmushi Baba Atine ta sake yi tace

"Ki daure dai 'yata.. ki cigaba da kaiwa ɗin.." Miƙewa kawai ta yi, dan dama ba ta san maganar tata ta fito fili ba.

"Ai kam kin yi kyau a hakan nan. Ki je a haka kin ji?" Ta faɗa tana murmushi. Murmushin yaƙe Didi ta yi kafin ta amsa da

"Toh.." Daga haka ta fice daga ɗakin. Kai tsaye kitchen ta nufa. Yau ma cikin ƙanƙanin lokaci ta gama. Ta juyo shi cikin cup ɗin sannan ta fito. Tunani ta shiga yi ko yau ma ta yi abin da ta yi rannan? Se dai kuma tana tsoro ka da rana ɗaya ya ganota ba ta san abin da ze mata ba, dan ba ta ga alamar mutunci a tattare da shi ba. Se dai koma mene ne da dai ta shiga ɗakin gwara ta tsaya a nan ɗin, idan ya so koma mene ne ze biyo baya ta san se daga baya. Hakan ne ya sanyata ƙarasawa ta shiga knocking ƙofar. Daidai lokacin da ma yana shirin fitowa ne. Tana kuwa jin alamar za a buɗe ta yi sauri ta ajje a ƙasa, har tana shirin yin tuntuɓe garin neman wajen ɓuya. Ko kuma meye ne ya manta se kuma ya koma cikin ɗakin. Bayan wajen minti 1 ya dawo ya buɗe ƙofar. Da mamaki yake kallan cup ɗin dake ɗauke da coffee kamar wancan karon. Kenan Mom ce yau ɗin ma ta yi ta ajje masa a nan? Amma me yasa ba za ta bari ya tashi ba? Ya tambayi kansa. Cikin lokaci ƙanƙani ya nemo amsar hakan, wato.. ba ta san takura masa ne. Taɓe baki ya yi, kamar ze yi ficewarsa daga ɗakin, se kuma ya saka hannu ya ɗauka ya koma cikin ɗakin. Neman waje ya yi ya zauna, ya ɗauki wayarsa ya shiga dannawa yana ɗan shan coffee ɗin lokaci zuwa lokaci. Be san yanda aka yi yanzu Mom ta fi iya coffee ba, se dai be sani ba ko ta sake neman yanda za ta ƙware ne dan faranta masa. Ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yake shan coffee ɗin a ransa yana sake yaba daɗinsa, wanda idan a fuska kake kallansa ba zaka taɓa tunanin ya masa daɗi ba. Dan kuwa babu wata alama da ta nuna yana jin daɗin abin da yake sha ɗin.


... Little se wasansa yake a ɗakin hankalinsa kwance babu wata damuwa. Dan tunda ya tashi yake kuka, amma yana ganin Lulu kukan ya ɗauke gaba ɗaya. Tana nannaɗe cikin hijab ɗinta tana kallansa, lokaci lokaci ta kan yi murmushi, idan ya yi wani abun kuma ta yi dariya.

"Ba ki da lafiya?" Ya tambaya yana kallanta sanda ya tsaya da wasan da yake yi. Jinjina kai ta yi fuskarta a narke tace

"Ehh.."

"Toh ki sha magani.." ya faɗa a sakarce ba tare da bawa zancen nasa muhimmanci ba ya cigaba da

Please Login or Register in order to submit comment