Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasa furta komai tun bayan shigowar Gwani. Se dai miƙewar Ummeey ke da wuya se ita ma ta miƙe tana sake riƙe Little a hannunta. Ba ta tsammata ba, se muryarsa ta jiyo a dake yace

"Ina za ki je?" Buɗe baki ta yi da niyyar faɗar duk abin da ya zo bakinta, se ta tuna da abin da ya faru. Se ta ɗan cije bakinta kafin tace

"Toh ina ruwanka..?" ta faɗa tana hararar gefe da gefe cike da takaici.

"Wannan abincin fa?" ya tambaya tana kallan kwanon da ya gani a gabanta. Ze iya cewa tun zuwanta gidan nan be ganta ta saka wani abun a bakinta ba, dan haka be jira amsarta ba yace

"Dawo ki zauna ki ci.."

"Ba na ci." ta faɗa da sauri. Miƙewa ya yi daga inda yake, ya soma takawa kamar ze nufo inda take, se kuma ya dakata yace, lokacin da muryarsa ta ɗan kaurara kamar wanda ke fushi.

"Se kin ci.. Je ki zauna" Ya yi maganar hatta fuskarsa babu alamun wasa ko kaɗan. Jin muryarsa da ta yi a kusa da ita ne ya sanyata ɗaga kai. Se kawai ganinsa ta yi dab da ita. Da sauri ta ja baya ƙirjinta na bugawa, se dai duk da haka ji take kamar ta buɗe baki ta faɗa masa wata maganar da ze daɗe tana masa zafi a zuciyarsa. Se dai tozali da fusatattun idanunsa, se suka sanya duk wani ƙwarin gwuiwarta ya tafi. Se ma ƙwalla da ta zo ta tarar mata a cikin idanu. Ita kam ta rasa mafita a rayuwarta, kowa ba ya sonta. Tunda aka aura mata Gwani dama ta sallamawa duniya, ta san ko ba daɗe ko ba jima mutuwa za ta yi saboda wannan auran. Se dai tun kafin hakan ma ta kasance, za ta sauƙaƙawa mutuwar yanda za ta ɗauketa salin alin. Hakan ne ya sa tun zuwanta gidan ba ta ɗauki ko ƙwayar shinkafa ce ta saka a cikinta ba. Komawa ta yi ta zauna bayan ta zaunar da Little. A hankali a kuma fusace tace

"Wallahi ba zan ci ba.." Ta faɗa ƙasa_ƙasa. Ba dan ta so ba, ta saka hannu ta ɗauki cokali ta shiga bawa Little. Se da ya ga hakan sannan ya miƙe yana ɗan sakin ƙaramin tsaki ya fice daga ɗakin. Cigaba ta yi da bawa Little abincin, duk da yanda cikinta ke kiran ciroma, hakan be sanyata kai ko da lomar abinci ɗaya ba ne. Se ma sake ɗaukar ruwa kawai da ta yi ta sha. Se da Little ya ƙoshi sannan ya fara hamma alamar bacci yake ji. Daidai lokacin da Ummeey ta shigo ɗakin. Ta kalle shi ta cikin er ƙaramar fitilarsu me haske yanda yake ta lumshe idanunsa tace

"A'ah baccin ne? Mu je na kai ka toh ka yi fitsari" ta faɗa tana riƙo shi. A yanzu kam be yi musu ba se ya bari Ummeeyn ta ɗauke shi zuwa banɗakin. Babu jimawa suka dawo, kai tsaye jikin Lulu ya ƙarasa ya kwanta. Ɗan lumshe idanunta ta yi tana jin yanda cikinta ke hautsinewa yana takurewa waje guda. Ta ɗan buɗe idanunta tana sake ɗaukar ruwa ta sake bankawa cikinta. A ranta tana ji lallai wannan hukuncin da ta yanke shi ne daidai. Ko banza idan suka ga gawarta za su ɗauketa daga gidan nan, su kuma gane da gasken ba ta ƙaunar Gwani ko kaɗan. Babu daɗewa kuwa bacci ya ɗauki Little. Se a lokacin sannan Ummeey ta ɗauke shi, bayan ta yi masa shimfiɗa ta shigar da shi cikin net. Kallan Lulu ta yi tace cikin kulawa

"Ya kamata ki je ki kwanta haka nan.." Kallan Little ta yi kamar ba za ta miƙe ba, se kuma ta miƙe tana riƙo cikinta ta cikin hijab.

"Toh se da safe 'yata.." Ummeey ta faɗa da murmushi kan fuskarta

"Toh" shi ne kawai abin da Lulu ta faɗa tana wucewa, dan so take kawai ta kwanta, ta san kafin ta tashi rai ya yi halinsa. Se dai duk da haka za ta so ta sake ganin Didinta ko da sau ɗaya ne kafin ta bar duniya, ta ga Amminta ita ma ko sau ɗaya ne, haka Abbanta ma. Se dai babu wannan damar. Uwa uba kuma daga Abban har Ammin sun dena sonta. Da wannan tunane_tunanen ta ƙarasa ɗakin, kai tsaye kan gadon ta nufa. Babu ɓata lokaci ta haye, bargon dake kai ta yaɓa a kanta ta rufe idanunta. Duk da ta san dama hakan za ta faru, amma kuma tana tsoron ciwo matuƙa. Dan haka burinta a yanzu be wuce ta ji bacci ya ɗauketa ba.


.. Juyawa ta sake yi a karo na barkatai saboda yanda ta ji kamar ana ɗaukarta ana juyi da ita. Ta buɗe idanunta da sauri a tsorace. Se dai kamar yanda ta buɗe shi da sauri, haka ta kulle shi da sauri, saboda yanda wani jiri ke kwasarta duk da a kwance take, hannunta dafe da cikinta da yanzun yanda yake curewa waje ɗaya ya ninka ɗazun sau nawa. Tun tana juyi cikin bargo har se da hawaye suka taru a cikin idanunta. Ta kasa jurewa se da ta buɗe baki ta saki ƙara tana sake juyawa.

Yana zaune kan dadduma, ya idar da sallah kenan yana addu'a, se ƙarar da ta yi ta sauka a cikin kunnensa. Da ma ba tun yanzu ba yake ɗan jin kamar sauke numfashi. Se dai be ɗauka da gasken ba ne se yanzu da ya jiyo ƙararta. Se ya miƙe a nutse ya ƙarasa inda gadon yake, bayan ya yaye labulen dake zagaye da wajen. Tana cikin bargon dai har lokacin tana juyin kamar wata macijiya. Se ƙaramin kukan da take yi a duk lokacin da cikin ze juya. Haka kawai ya ɗan ji fargaba ta shige shi, ya sake kallan gadon ganin har lokacin ba ta fito daga cikin bargon ba. Se kawai ya kai hannunsa a nutse ya yaye bargon idanunsa a kanta, dan gane abin da ya sanyata kukan. Ita sam ba ma ta lura da yaye bargon ba, saboda zuwa lokacin cikin nata yafi ɗazu yi mata ciwon. Inda hannunta ke kai ya bi da kallo bayan ya ajje bargon a gefe. Ganin tana tattare cikinta ya sanya shi kallan kyakykyawar fuskarta da ta yi jazur ta cikin jan ƙwan fitila.

"Wayyo Allahna" ta faɗa wasu hawaye na zubo mata. Ita a ranta ta gama saɗɗaƙarwa mutuwa za ta yi, dan haka mala'ika kawai take jira a zare ran ta huta da ciwon cikin nan. Ɗan lumshe idanunsa ya yi dan daga tsayen nan dai da yake ya san babu abin da ze iya yi, dan haka kawai se ya nemi gefen gadon ya zauna. Ganin har lokacin dai akwai tazara a tsakaninsu ne ya sanya shi ƙarasa hawa kan gadon. A nutse ya kai hannunsa zuwa kan nata hannun da ke kan cikinta sannan cikin nutsuwa ya furta

"Me ya faru?" Duk da ba ta san da wanzuwarsa ba, amma jin an janye mata hannu ya sanyata fizgewa da ƙarfi tana mayarwa kan cikinta. Se ta maida kanta kan katifar ta kifa shi tana cigaba da kukanta gami da rirriƙe ciki kamar me wanke kaya. Iska ya fesar yana ɗan lumshe idanunsa. Dan har cikin kansa yake jin wannan kukan. Hakan ne ya sanya shi kai hannunsa saman kanta ya juyo da fuskarta, kafin a hankali ya ɗora kan nata a kan ƙafarsa. Se ya ɗauki idanunsa ya ɗora a kan fuskar tata, yana shirin cewa wani abu ta fara ƙoƙarin miƙewa duk da har lokacin ba ta fahimci a inda take ba. Ɗan haɗe face ɗinsa ya yi kafin ya sake maimaita tambayar da ya mata ɗazun. Se dai har yanzun ma babu amsa, se cigaba da kukan nata dai ta yi. Kansa ya matsar dab da fuskarta, ya shiga hura mata iska a kan idanunta. Se ta yi saurin lumshe su lokaci ɗaya kukan na tsayawa cakk. Kafin ta cigaba kuma se jin muryarsa ta yi yana faɗin

"Keee!! Ki nutsu.. Me yake damunki?" ya yi maganar a saitin kunnenta kamar me raɗa, se dai har lokacin fuskarsa na nan a yanda take. Jin muryarsa da ta yi ne ya sanyata soma fahimtar a inda take, a ina kuma ta ji muryarsa. Hakan ne ya sanyata yunƙurawa dan miƙewa, daidai lokacin da cikinta ya yi wata muguwar murɗawa, ba ta san sanda ta koma kan ƙafar tasa ba cikin kuka tace muryarta na sarƙewa

"Cikina.. Cikina ze cire.." Ta yi maganar tana rirriƙe shi da ƙarfi lokaci ɗaya tana fashewa da wani marayan kuka..


Pls kar a tambaye ni dalilin da ya sa jiya aka ji ni shiru, ni kaɗae na san abin da nake ji.😭 Na yi rabin typing na ajje shi a email, ina ta saurin na je na ɗauko shi na haɗa na muku posting. Na duba na neme shi na rasa, ban san yanda aka yi hakan ta faru ba. Se da na taushi kaina na sake maimaitawa.


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO33*


___ Se kuma murɗawar ta tsaya, hakan ne ya sanyata sakinsa a hargitse ta miƙe da sauri ƙirjinta na bugawa. Kawai se ta fashe da kuka tana zubewa a wajen tunawa da ta yi yanda ta riƙe shi, shi kuma har da riƙota.

"Ɗan iska kawai.." ta faɗa a kan laɓɓanta tana cigaba da kukan durƙushe a ƙasa. Binta ya yi da kallo a ransa yana tunanin ko dai tana da wasu nau'i ne na iskokai? Se dai kafin ma ya ida tunanin da yake cikin nata ya sake murɗawa, da ta sake sakin wata ƙara tana bajewa a wajen tana kuka kamar ranta ze fita. Yanzu kam fargabar da ya ji har tafi ta ɗazu. Se kawai ya miƙe ya sakko daga kan gadon ya sake komawa inda take. Ya tattare girar sama da ta ƙasa sannan ya saka hannu ya ɗagota gaba ɗayanta. Gudun ka da ma ta masa gardama ya sanya shi shigar da ita cikin jikinsa. Jin abin da ya mata ne ya sanyata soma fiffizgewa, tana ƙara sautin kukanta, amma be bi ta kanta ba, se ma saka hannu da ya yi ya ɗage hijab ɗinta da yake har wajen gwuiwarta, ya maida shi saman cikinta. Duk da yanda take cigaba da fizgewa tana wani marayan kuka saboda yanda muryarta ta soma dashewa hakan be dame shi ba. Se saka hannunsa da ya yi ya ɗage rigar daga kan cikinta zuwa sama. A hankali kuma ya kai tattausan hannunsa kan farin cikinta. Kamar wata wutar lantarki me ja haka dukansu suka ji lokacin da hannunsa ya sauka a kan fatar cikinta. Ita Lulu suma ne kawai ba ta yi ba saboda tsoron da ta ji ya shigeta, yayin da Gwani se da bugun zuciyarsa ya ƙaru, ya koma fita da sauri da sauri, idanunsa a ɗan lumshe kamar me jin bacci. Wani yunƙurawa ta yi dan miƙewa daga jikinsa amma ina ya mata tsatstsauran riƙo. Se kawai ta shiga kai masa cizo ko za ta samu ya saketa. Shi kam ko kulata be yi ba, se matsa cikinta da ya yi da hannunsa. Ya ɗan taɓa gefe shi ma sannan ya yi saurin janye hannunsa yana janyo rigar da ya ɗage ya maidata yanda take. Sakinta ya yi ya miƙe a nutse yana ɗan sake buɗe idanunsa sosai, ya ƙarasa drawer ɗin mirror. Fashewa ta yi da kuka sanda ya saketa, se ta ja hijab ɗinta ta lulluɓe ilahirin jikinta dake wata irin karkarwa kamar ana kaɗa ganga. Ta cure waje ɗaya kanta kife a kan cinyarta tana kuka me cin rai. Duk da yanda cikinta ke juyawa hakan be dameta ba yanzu, wani tsoron gwanin ne ya kamata. Ba ta ankara ba se jin muryarsa ta yi dab da ita yace

"Karɓi ki sha.." ya yi maganar fuskar nan babu annuri ko kaɗan. Sauke kanta ta yi ƙasa tana sake matsawa baya. Ganin yana ƙoƙarin miƙewa ne ya sanyata buɗe bakinta da ƙyar cikin raunanniyar murya kamar ba Lulu ba ta soma faɗin

"Kar ka matso kusa da ni don Allah.. ka rabu da ni.. ka rabu da ni don Allah.." Da mamaki ya ɗan kalleta, se ya ji kamar ba Lulun ba. Ashe dai rashin lafiya na chanja mara kunyar mutum? Se da ya lumshe idanunsa sannan ya sake takawa ya ƙara rage tazarar dake tsakaninsu.

"Ki karɓa ki sha ko kuma na ba ki da kaina.."

"Ni ka ƙyale ni.. Allah ka ƙyale ni.." yanzun ma ta faɗa tana sake fashewa da sabon kuka. Ajiyar zuciya ya sauke, ganin za ta ɓata masa lokaci, ga shi so yake ya fita ya sama mata abin da za ta ci, ya sanya shi yin shahada ya sake riƙeta cikin jikinsa duk da yanda take fizgewa ya ba ta ruwan. Haka tana kukan tana komai se da ya tabbatar ta shanye tass duk da dama kaɗan ne sannan ya saketa. Ya miƙe ya bar wajen ma gaba ɗaya. Kawai bajewa ta yi a wajen cikin rashin sanin abin yi tana juya kanta wani dogon kuka na taho mata. Ta ɗauki tsawon sakanni, kafin kukan ya fito fili, ta kuwa shiga rera shi tana ji kamar ta mutu dan baƙin ciki. Farar fuskar nan ta haɗe ta yi jajur.


... A karo na biyu kiran ya sake shigowa cikin wayar, ya juya daga inda yake zaune yana saka haɗɗaɗen takalminsa. Iska ya fesar daga bakinsa a ransa yana tunanin wanda ya masa kira har 2 a jere haka. Daga inda yake zaune ya miƙa hannunsa zuwa inda wayar take, ya ɗaukota yana kallan wata hargitsatstsiyar number dake yawo a saman wayar tasa. Dogon tsaki ya ja yana jefar da wayar a gefensa ransa a ɓace saboda ganin da ya yi sabuwar number ce ma ke kiransa. Shi kuma da ma ba ya ɗaukar number da be sani ba. Se da ya gama shiryawarsa sannan ya miƙe lokacin da ya gama fitowa a Bad Man ɗinsa, ya yi matuƙar kyau, cikin shigar ƙananan kayan da a kodayaushe suke ɗaukar jikinsa. Sam be taɓa kawowa cewar Hero ke kiransa a wannan lokacin ba, dan kuwa ya daɗe da goge numbersa daga wayarsa kamar yanda ya goge shi daga cikin rayuwarsa. Daidai lokacin da yake ƙoƙarin saka wayar cikin aljihu ta ɗauki ruri, ya yi tunanin ko number ɗazu ke kira, dan haka a matuƙar fusace ya juyo da wayar, se ganin sunan Kaseem na yawo a kan wayar tasa ya yi. Ya ɗan ja ƙaramin tsaki yana ɗaga wayar ya kara a kunnensa.

"Bro ka shirya ne?"

"Zuwa ina fa?" Ya tambaya yana ɗan ƙanƙance idanunsa.

"Ka na nufin ka ce har ka manta? Amma dai ai ka san za mu fita koh?" Kaseem ya tambaya yana mamakin yanda Bad Man ɗin ba ya ɗaukar komai serious. Kafin yace komai ya ɗora da faɗin

"Plss ina jiranka.. Ka yi ƙoƙari ka fito ko don farin cikin Daddy.."

"Ok.." ya faɗa a taƙaice yana datse kiran. Ya sake lumshe idanunsa kafin ya buɗe su. Sam be so bin Kaseem ɗin wani waje ba, shiryawar nan da ya yi ze ɗan fita ne ya samowa kansa wasu abubuwan charge. Se dai da ma yana tunanin yanda ze shigo da su, ko kuma yanda ze fita ba tare da samun wani tsaiko ba bayan Daddy na nan. Kai tsaye compound ɗin ya wuce hannunsa ɗaya na cikin aljihun wandonsa ya ƙarasa inda motar Kaseem take. Tun kafin ya ƙaraso dama ya riga ya buɗe masa ƙofar, dan haka yana zuwa kawai shiga ya yi ya nemi waje ya zauna.

"Mu tafi?" Kaseem ya tambaya yana kallan Bad Man.

"Yeap.." ya amsa yana fito da wayarsa. Babu ɓata lokaci Kaseem ya soma driving. Kaseem ɗin gwani ne wajen hira, se dai a wannan karon se ya kasance tafiyar tasu ta zama wata lami, musamman da ya kasance har yanzu Kaseem ɗin be koma ainahin Kaseem ɗinsa ba, tun lokacin da ya rasa Didi. Mutane da dama sun sha tambayarsa dalilin chanjawar tasa amma se dai yace babu komai. Areef da shi kansa wani na arziƙi ne me kula da wasu, da ze yi noticing chanjawar Kaseem ɗin. Amma da yake be iya damuwa da damuwar wasu ba ya sanya tun kallo ɗaya da ya yi wa Kaseem ɗin be sake ba, ballantana a kai ga tambayar abin da ke damunsa. Haka suka cigaba da tafiya babu me cewa da wani uffan. Se da Kaseem ya gaji sannan ya ɗan shiga jan shi da hira sama sama. Da yake akwai sabo a tsakaninsu ya sanya ya ɗan saki jiki suka taɓa hira babu laifi.

Da wannan damar ya yi amfani ya siyi kayan mayensa da na shaƙa, ya san yanda ya yi ya shigar dasu gida ba tare da kowa ya gani ba.


... Idar da sallahrta kenan, ta miƙe tana ninke dadduma Baba Atine ta shigo da sallama. Amsawa ta yi da murmushi a kan fuskarta. Baba Atine ta ƙaraso tana faɗin

"Sannu ɗiyata.. Kin idar da sallahr?" Ta tambaya ita ma tana murmushi.

"Ehh na idar.."

"Toh madallah.." Baba Atine ta faɗa tana neman waje ta zauna. Se ta kamo hannun Didi ta zaunar da ita kan gadon sannan tace

"Maganar da muka yi.. Ki tashi ki je kitchen ki haɗa coffee ɗin ki kai masa." Ita da ma tunda Baban ta shigo ta ji jikinta ya yi sanyi. Har ga Allah ba ta son zancen nan, ba ta son sake shiga harkar mutumin. Se dai ta riga ta yi wa kanta alƙawarin yin biyayya a wannan auren da Abba ya ɗaura mata, dan haka ta buɗe baki da ƙyar tace

"Toh.."

"Yawwah ɗiyar albarka mu je na raka ki.." Baba Atine ta faɗa tana miƙewa. Babu musu Didi ta bita, se dai dukkan wata gaɓa ta jikinta a sanyaye take. Haka dai take ta giggimtsewa ka da ta bari zuciyarta ta karye tun yanzun. Har kitchen Baba Atinen ta rakata, sannan ta kalleta tace

"Wanne iri za ki yi?" Shiru Didi ta yi na en sakanni, kafin ta buɗe baki a sanyaye tace

"Cuppocino.." Jinjina kai Baba Atine ta yi tace

"Toh ya yi. Bari na je na dawo.."

"Toh.." Didi ta faɗa tana binta da kallo sanda take ficewa daga kitchen ɗin. Se a lokacin ta lumshe idanunta ƙirjinta na ɗan bugawa. Numfashi ta ja da ƙarfi ko za ta samu ta dena jin karyewar zuciyar, se dai har lokacin ba ta dena ji ba. Hakan ne ya sanyata juyawa ta shiga kallan cikin kitchen ɗin kamar me son gane abubuwan dake cikinsa.

A daidai bakin ƙofar sashen Baba Atine suka yi kaciɓus da Mom dake ƙoƙarin shigowa sashen. Tsayawa Mom ta yi tana kallanta da mamaki a kan fuskarta.

"Barka da wannan lokacin Hajiya.." Baba Atine ta faɗa cike da girmamawa. Kamar jira take yi, se a lokacin ta buɗe baki tace

"Me ya kawo ki nan?" Ta ƙare maganar tana buɗe hannunta alamar "mene ne"

"Amm Hajiya da ma.. da..ma.."

"Ke yi min shiru dallah.. munafunci ne ya kawo ki koh? Ko kuma ke ce er leƙen asirin da aka turo sashen nan? Munafuka?" Mom ta ƙare a zafafe. Girgiza kai Baba Atine ta yi kafin ta buɗe baki tace

"A'ah Hajiya, ba haka ba ne. Amma ki yi haƙuri.."

"Ɓace min da gani malama. An girma ba a dena munafunci ba." Ta ƙare tana sakin wani dogon tsaki kamar za ta tsinke harshenta. Jan ƙafafunta ta yi ta fice daga ɗakin, tana sake jin zafin maganganun da Mom ɗin ta faɗa mata. Ko babu komai ai ta girmeta. Ko da tana aiki ƙarƙashinsu be kamata ta dinga yi mata haka ba. Da wani banzan kallo Mom ta bi Baba Atine da shi, se da ta fice sannan ta dawo da dubanta cikin ɗakin tana sake sakin tsaki. Soma takawa ta yi, har zuwa inda ɗakin da Bad Man ya shiga yake. Knocking ta fara yi cike da fatan ba bacci yake ba. A daidai lokacin kuwa yana zaune kan bowl chair, gabansa kuma wata haɗaɗɗiyar kwalba ce da har wani sheƙi take yi kamar ba kwalba ba. Cups ne a gefen kwalbar har guda 3 duka ƙanana. Ɗaya na hannunsa ya watsa a cikin bakinsa idanunsa a lumshe. Kamar daga sama ya ji ana knocking ƙofar tasa. Kamar ba ze kula me knocking ɗin ba se kuma a hankali ya ɗaga kansa ya kalli ƙofar. Sake bugawar da aka yi ne ya sanya shi ɗan cije gefen lips ɗinsa sannan ya buɗe bakinsa yace

"Waye ne?" Ya faɗa da muryarsa da ta ɗan yi ƙasa.

"Ur Mom.. ka buɗe min ƙofar mana Boy.." Sake lumshe idanunsa ya yi, sannan ya dawo da dubansa kan abubuwan dake gabansa, kana ya ɗaga kansa ya sake maidawa kan ƙofar yace

"Bacci.."

"Ohhh sorry my dear.. Sleep well.. I will be back later.." ta faɗa cike da kulawa dan ba ta son abin da ze hana ɗan nata jin daɗi. Daga haka ta bar ƙofar ɗakin ta wuce part ɗinta.

Ba ta ɗauki mintuna masu yawa ba, ta fito daga cikin kitchen ɗin hannunta ɗauke da ƙaramin cup ɗin dake ɗauke da coffee ɗin dake ta tururi. Kallan ƙofar ɗakin ta yi, tana tunanin mafita. Dan ba ta san zuwa ɗakin bare ta gan shi. Se can wata dabara ta faɗo mata, dan haka ta cigaba da takawa zuwa ɗakin nasa. Ta kai wajen minti ɗaya tsaye ba tare da ta yi ƙoƙarin yin komai ba. Se kuma daga baya ta ɗaga hannunta ta shiga knocking ɗin ƙofar. Sake kallan ƙofar ya yi cike da mamakin abin da ya hana Mom ɗin tafiya. Ya ɗan fesar da iska daga bakinsa hannunsa cikin sumar kansa yana ɗan yamutsata. Kamar ba ze miƙe ba, kamar ba ze yi wani abu ba se kawai ya miƙe ya soma takawa zuwa bakin ƙofar, ya saka hannunsa dan buɗe ƙofar bayan ya yi blocking ko ina. Tunda ta ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar se ta yi saurin ajje coffee ɗin ta koma gefe a guje ta ɓoye dan kar ya ganta. Da mamaki yake kallan cikin ɗakin sanda ya gama buɗe ƙofar ya ga babu kowa. Toh ina Mom ɗin take kenan? Kawai se ya taɓe baki yana ɗaga kafaɗarsa. Yana ƙoƙarin juyawa idanunsa suka sauka a kan coffee ɗin. Kamar me nazari ya zubawa coffee ɗin ido, se dai shi abin da ya ba shi mamaki, ashe duk wannan bugun tana yi ne kawai dan ta ba shi coffee? Lallai ma Mom.

"Oh god.." ya faɗa yana dafe goshinsa. Har ze tafi ya bar coffee ɗin se kuma ya juyo ya ɗauka ya koma cikin ɗakin. Ya ajje shi a gefe guda sannan ya cigaba da abin da yake yi. Se da ya sha ya yi tatil har se da kansa ya soma sara masa kamar yanda yake masa a kwanakin nan sannan ya ajje gefe. Ya koma ya kwantar da bayansa a kan kujera idanunsa a lumshe. Chewing gum ya fito da shi daga cikin wata er ƙaramar jaka me kyau. Yana shirin jefawa cikin bakinsa idanunsa suka sauka a kan wannan coffee ɗin. Kamar ya share, se kuma ya ji yana da buƙatarsa, musamman ma da Mom ɗin za ta ji daɗi idan ta ga ya sha. Hakan ne ya sanya shi ɗauka ya buɗe, take tururin da be gama fita ba ya soma tashi. Se da ya ɗan lumshe idanunsa sannan ya kai bakinsa ya soma sha. Ɗan yamutse fuska ya shiga yi jin ɗanɗanon ya fita daban da wanda Mom ɗin ke masa. Hakan ne ya sanya shi sauko da shi ya shiga kalla, kamar anan ze ga ainahin wadda ta yi shi. Se dai kuma da ya tuna ɗanɗano kan iya chanjawa, bugu da ƙari kuma ɗanɗanon ya masa daɗi se kawai ya kafa shi a bakinsa ya shanye tass..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO34*


___Wata ƙatuwar ajiyar zuciya Didi ta sauke sanda ta ji motsin rufe ƙofar. A hankali ta fito daga inda ta ɓoye tana kallan ƙofar, a tunaninta za ta ga kofin a inda ta ajje shi. Se dai ga mamakinta se ta ga babu komai a wajen. Sake dubawa ta yi ko dai ba ta gani da kyau ba, ta ga dai ba ta gan shi ba.

"Kenan ya ɗauka?" Ta tambayi kanta kamar tana jira wani ya ba ta amsa. Da dai ta ga babu me bata amsar se ta ɗauki ƙafarta ta soma takawa

Please Login or Register in order to submit comment