Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan saboda tsabar mamaki ta kasa ko da motsawa ne ballantana ta fita daga ɗakin..


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO29*

___Ta kai wajen minti ɗaya a tsayen cikin rashin sanin abin yi. Da dai ta ga babu abin da za ta sake yi cikin gidan, babu kuma wanda ya fito, se ta ja tsummar ƙafafunta ta fice daga ɗakin. Tun kafin ta ƙarasa su Hero suka hangota. Gaba ɗaya idanunsu na kanta, musamman Ladi da ta ƙagu kawai ta ji abin da ke faruwa. Daidai sanda ta iso inda suke ta sauke ajiyar zuciya. Cikin ƙaguwa da son jin wani abu daga bakin Abidan Ladi tace

"Me ya faru? Ki yi sauri ki faɗa mana.."

"An yi aurenta wai.." ta faɗa a sare.

"An yi aurenta kuma? Kamar yaya?" Ladi ta faɗa tana kallanta cike da mamaki.

"Wallahi haka aka ce min." Tsayawa Hero ya yi yana kallan Abidar kamar me son gano gaskiyar abin da take faɗa.

"Ko dai abin da muke tunani ya faru shi ya sa aka yi saurin ɗaura musu aure?" Hero ya faɗa yana haɗe babban ɗan yatsansa da na uku ya murza. Kallansa Ladi da Abida suka yi jin abin da ya faɗa. Kamar kuma wanda ya tuna wani abu, se ya girgiza kai yana faɗin

"Kai.. anya kuwa?"

"Ƙwarai kuwa.. ko dai hakan ne ya faru? Ina tunanin hakan ni ma.." Ladi ta faɗa. Sake girgiza kai Hero ya yi yace

"Toh ba haka ɗin ba ne kenan.."

"Kamar ya ya? Ban gane nufinka ba.." ta tambaya tana kallansa.

"Tunda dai har zan iya hasashen abu, ke ma kuma ki yi, toh mutane da dama ma abin da ze zo kansu kenan.. Kin ga kenan cikin lokaci ƙanƙani za a ramfosu, a gano abin da ya faru. Ba haka ba ne. Abin da kuma ya sa nace ba haka ne ba, idan da hakan ne ya faru ba za a yi saurin ɗaura musu aure ba, dan kuwa kowa ze gano dalilin yin auren.." Shiru Ladi ta yi tana sake jinjina kaifin ƙwaƙwalwa irin na Hero. Tabbas ta yadda da zancensa ɗari bisa ɗari. Hakan ne ya sanyata faɗin

"Uhmm, lallai wannan maganar taka abar dubawa ce.."


... "Jadwa! Jadwa!!" Mami ke ta ƙwalawa kira tun shigowarta gidan. Da sauri Jadwa ta fito, cike da mamakin kiran Mamin.

"Maza ke ki shiryo ki zo na aike ki gidan Lulu.."

"Lulu kuma? Me zan yi mata?" Ta tambaya har lokacin dai cike da mamaki.

"Cewa na yi ki je ki shiryo.. Yaya yace ka da wanda ya je gidan cikinmu.. ina dai ke yarinya ce ai koh? Dan haka je ki shirya zan baki saƙo zuwa wajenta.." Neman waje Jadwa ta yi ta zauna tana taɓe baki da fuska. Tace

"A'ah ni wallahi, babu inda zan je Mami. Tunda dai an samu Kaseem be auri Didi ba ai shi kenan, mu zo mu nemo mafitar yanda ze yi ya so ni.. Ina ruwanmu da wata Lulu kuma don Allah..?"

"Kee Jadwa.. Lulu fa nake miki magana ko ba ki gane ba ne? Shin ba ki ga gidan da aka kaita ba ne? Ki na nufin na yi shiru ta zauna a wannan gidan kamar wadda ba ta da dangi? Toh wallahi ba za ta zauna ba, ko ta halin ƙaƙa se ya saketa ta baro gidan nan in dai ina raye.. Ai Lulu ba kalar gidan nan ba ce, ba matar talakawa ba ce. Ni nan zan tsaya mata.."

"Wai Mami kin manta ni ce ɗiyarki ba Lulu ba?" Jadwa ta faɗa tana kallan Mami, jin wannan magana da take faɗa.

"Ke na sani mana. Duk da dai na san ba zan so ta auri wanda ya fi wanda za ki aura kuɗi ba, amma ai ba zan so ta zauna a wannan gidan ba, gwara ya saketa ta samu wani ta aura.."

"Toh idan kuma ta auri wanda yafi Kaseem ɗin kuɗi fa?" Jadwa ta faɗa tana gyara zama. Girgiza kai Mami ta yi tace

"A'ah hakan ba ze faru ba. Za dai ta samu wani me rufin asiri ne ta aura, amma ba wanda ya fi Kaseem ba.." Matsawa kusa da ita Jadwa ta yi tace

"Ai Mami so nake ki ƙaddara idan hakan ta faru ya za ki yi?" Shiru Mami ta yi na tsawon sakanni kamar ba za tace komai ba, se kuma can tace

"Se na san abin yi mana.." ta faɗa tana miƙewa ta ɗauki jakar da ta ajje a gefenta.

"Ah toh ai Mami abin da nake tsoro kenan. Dan wallahi a kyau dai irin nasu Lulu, babu wanda ze gansu ya ji basu masa ba.." Tsaki Mami ta ja cike da jin haushin abin da Jadwan ke faɗa. Tace bayan ta juya ya kalleta

"Ki min shiru haka nan.. Se abu ya faru sannan ake nemo mafita.. saboda haka ki bar ni yanzu na san yanda zan kuɓutar da ɗiyata daga wannan gidan.." Daga haka ta shige ɗaki. Binta da kallo Jadwa ta yi kawai, ta ma rasa abin da za tace, se kawai ta koma kan kujera ta zauna ta cigaba da danna wayarta.


.. A hankali ya tura ƙofar ɗakin, ga mamakinsa yanzu ma tana bakin ƙofar, se dai yanzu kanta ba ɗore yake a kan cinyarta ba. Idanunta gaba ɗaya suna kan ƙofar ne, jira kawai take ta ji sallamar Mami. Tana ji ya turo ƙofar ɗakin, ta ɗaga kai da sauri ta kalli ƙofar. A kan fuskarsa idanunta suka fara sauka. Cike da takaici ta ɗauke kai, tana sake jin haushin ganinsa da take ta yi tun jiya. Dab da ze giftata ba tare da yace komai ba. Se kuma ya dakata, ya ɗan lumshe idanunsa sannan yace ba tare da ya kalleta ba

"Ki je ku gaisa da Ummeey.."

"Wace Ummeey?" Ta tambaya da sauri, dan a tunaninta ko mantawa ya yi ze ce Mami yace Ummeey. Kamar ba ze tanka ba, se kuma ya ga rashin dacewar hakan, hakan ne ya sanya shi faɗin

"Mahaifiyata.." Daga haka ya yi cikin ɗakin. Ya ɗauki abin da ze ɗauka kana ya taho da niyyar fita. Be ɗauka ze ganta a zaune kamar yanda ya barta ba, se dai be san tunda ta ji ya ambaci sunan wata ba Mami ba ta ji kamar ta tashi ta rufe shi da duka. Me ye haɗinta da babarsa da za ta je ta gaesheta, bayan kawai ta zauna a gidan ne kafin Mami ta zo su tafi? Ita har ga Allah ma ta gaji da jiran Mamin, haƙurinta na dab da ƙarewa a kan rashin ganinta da ba ta yi ba tun da gari ya fara haske. Kwantacciyar sumar dake shimfiɗe a kan fuskarsa ya ɗan shafa kaɗan, kafin a hankali ya sake kallan inda take. Se kace wata me aljanu idan tana wani abu.

"Ke.." ya faɗa yana kallanta. Daga inda take ta murguɗa baki tana hararar gefe, a fili se dai ƙasa ƙasa tace

"Ko ina ruwan mutum da ni oho masa. Shegen shishshigi kamar me.." Jin yana ƙoƙarin sake faɗin wani abun ya sanyata saurin miƙewa tace ba tare da ta kalle shi ba, dan ta san ba za ta iya kallansa ta faɗa masa abin da take da niyyar faɗa ba.

"Ni don Allah ka ƙyale ni. Wai ina ruwanka da ni ne? Me ye haɗina da kai da zan je gaishe da en gidanku? Don Allah ka ƙyale ni. Mami kawai nake jira ta zo mu bar muku gida." Da mamaki yake kallanta jin abin da take faɗa. Se kuma ya taɓe baki, yana girgiza kai har wani murmushi na suɓuce masa. Lallai Afaaf ɗin ba ta san waye shi ba. Yana ganin mutuncin mahaifinta ainun, se dai hakan ba shi ke nuna ze shanye duk wani rashin daraja da za ta yi ba. Ƙiris yake jira ya taka mata birki a kan duk wani hali nata. Duk da be san yaya zamansu ze kasance ba, amma tabbas ze taka mata birki, ze saita mata wannan rashin kunyar da take ji da shi. Dan ya ga alama ba za ta biyu ta daɗin rai ba, burin Abbanta kuma ba ze taɓa cika ba na gyara masa Afaaf ɗin matuƙar yace ze cigaba da binta a yadda take ɗin nan.

"Ka da na dawo na same ki a bakin ƙofar nan.. Gida kuma se an zo tafiya dake za ki tafi? Ba ki ga ƙofar ɗakin a buɗe take ba, ga hanya nan maza zo ki fice.. Ni kuma za ki dawo ki same ni.." Ya ƙare maganar a nutse, kai ba za ka taɓa cewa cikin fushi yake maganar ba, saboda tantagaryar nutsuwar dake cikin muryarsa. Daga haka ya soma takawa dan ficewa daga ɗakin.

"Ai dai nan ɗin ba gidanmu ba ne, muna da gidanmu kuma ba na buƙatar na kowa." Ta faɗa da ɗan ɗaga murya dan ya ji ta. Be bi ta kanta ba, se cigaba da takawa da ya yi. Har ya fita, se kuma ya dawo, ya watsa mata kyawawan idanunsa dake cikin fushi yace

"Na dai faɗa miki.. Kar ki bari na dawo na same ki a bakin ƙofar nan, idan ba haka ba zan baki mamaki.." Bin wajen ta yi da kallo ranta a ɓace. Shin wai me mutumin nan ke nufi da ita ne? Me yasa yake son takurawa rayuwarta dan kawai an ce an aura masa aurenta? Auren da a yau ɗin nan take da tabbacin ze ƙare. Ko ma hakan ne me ye haɗinsa da ita? Ya yi rayuwarsa ta yi tata mana. A yi mutum se neman magana da shishshigi? Ƙwalla ta ji ta taso mata a cikin idanunta. Se ta nemi waje ta zauna a wajen tana faɗin

"Kuma bakin ƙofa ne se na zauna. In ga me hana ni.." Ko minti ɗaya ba ta yi da zaman ba, se jin motsin ƙofa ta yi kamar za a buɗe, ai ba ta san sanda ta miƙe da gudu ba ta yi cikin ɗakin, lokaci ɗaya tana faɗin

"Kuma ba dan kai na dawo ɗakin ba.." ta faɗa tana hararar ƙofar ɗakin. Ga mamakinta ma se ta ji shiru, ashe ba shi ba ne, duk da haka se ba ta koma bakin ƙofar ba. Ta cigaba da zama a ɗakin tana jiran zuwan Mamin. Se dai lokaci na cigaba da ja babu Mami babu alamarta. Anya kuwa ba ta yi kuskuren zama jiran Mami ba? Me yasa har yanzu Mamin ba ta zo ba? Ta sakata ta haƙura ta kwana a gidan, ba tare da fitowa fili ta nuna tsanarta ga Gwani ba, amma har yanzu babu wani sauyi? Ita ga shi ba waya ba ballantana ta kira Mamin ta ji lafiya? Komawa ta yi ta zauna tana ƙiyasta adadin mintunan da ta ƙarawa Mamin, waɗanda idan dai har suka cika Mamin ba ta zo ba toh za ta aikata abin da zuciya ke raya mata.



.. "Ke ashe dama en biyu ne yaran nan amma ba ki faɗa min ba?" Hero ya faɗa yana kallan Abida a fusace. Zaro ido ta yi kafin tace

"Inna lillahi.. Wallahi na manta, wallahi sam na manta da kamarsu ɗaya za ka iya kasa gane wace ce Afaaf.. Inna lillahi.. wallahi mantawa na yi.." ta faɗa kamar za ta fashe da kuka. A fusace Ladi ta kalleta jin ashe tun farko ita ta so ta kwafsa musu, se dai kafin ta kai ga cewa komai Hero yace

"Ba su da bambanci koh?" Jinjina kai Abida ta yi tace duk a muzance

"Basu da shi, kamar su ɗaya sakk. Ni ma ina gane su ne kawai ta hanyar niqab da ɗayar take sakawa. Sannan ita shiru shiru ce tana da haƙuri yayin da ita Afaaf ba ta da haƙuri ko kaɗan, se dai ita ma miskila ce kamar er uwar.."

"Idan haka ne kenan ba ki da tabbacin da wadda na haɗu a restaurant..?" Hero ya tambaya yana kallanta. Se da ta saci kallan Ladi dake cigaba da auna mata da harara sannan tace

"Ehh.." Ajiyar zuciya Hero ya sauke a ransa yana tuna haɗuwarsu da Lulu. Duk wata hanya da ze bi wajen gane wadda ya haɗu da ita ya ma kasa ganewa. Toh ita kanta Abidar ma da ta sansu ba ta gane ba ballantana shi?

"Yanzu wace hanya ta rage mana?" Ladi ta yi ƙoƙarin faɗin haka. Buɗe baki Abida ta yi da niyyar yin magana Ladi ta katseta da

"Dallah yi mana shiru. Ina ke kika janyo duk wani abu da ya faru? Fice min da gani tun kafin na kai miki duka.." ta faɗa tana watsa mata wata banzar harara.

"Ki yi haƙuri, wallahi mantuwa na yi.."

"Kin ga ki fice min a ɗaki nace koh?" Ganin Abidar na ƙoƙarin sake cewa wani abu, ya sanya Ladi sake faɗin

"Ki fice min nace dallah.." ta faɗa cikin ɗaga murya. Sum_sum ta ja ƙafafunta ta fice daga ɗakin cike da haushin kanta da kuma takaicin abin da Ladin ta mata. Maida dubansa Hero ya yi kan Ladi yace

"Toh wai ki haƙura da yarinyar nan mana.. Ga mata nan kala kala a cikin garin nan, ba ma garin nan ba, ko a wajen garin nan ne za ki samu duk kalar macen da kike so za ki iya samu, ki haƙura da wannan, ban da wahala babu abin da muke sha."

"Haba Hero.. Kai ɗin ne kuwa? Anya kai ne kuwa? Ina dukka ƙwarin gwuiwarka? Ya kake so na yi idan ka juya min baya? Ni kawai ina son yarinyar, kuma ba zan iya haƙura da ita ba. Don da zan iya haƙura da ita da tuntuni na haƙura tun lokacin da ta suɓuce min.." Ajiyar zuciya Hero ya sauke, a ransa yana jin haushin irin wannan nacin na Ladi.

"Shi kenan.. Yanzu ya kike so a yi?"

"Ina hoton nan da ka ɗauka?" Ladi ta tambaya.

"Wane amfani ze mana?" Ya yi maganar cikin halin ko in kula.

"Ina dai yanzu neman Afaaf muke yi? Waye ya aureta? Ya za a yi na san inda take, su ne abin da muke nema koh?" Ta ƙare da sigar tambaya. Se dai ba ta jira yace komai ba ta ɗora da faɗin

"Wannan hoton ze matuƙar taimaka mana.. Ta inda za mu gane da gasken ma ta yi auren ko kuwa? Idan ta yi auren tana ina? Idan mun gano inda take wa ta aura? Ina kuma abokinka yake?"

"Duk da hoton?" Hero ya tambaya irin a sheƙen nan. Se ta jinjina kai kafin tace

"Ƙwarai kuwa.. abu ɗaya kawai za mu yi, shi ne neman ta inda hoton ze isa wajen mijin nata. Daga nan zamu san ko shi waye, na kuma san dole ze sakota, idan da gaske ta yi auren kenan. Daga nan kuma kamar yanda na faɗa wasana ze soma.. Kai ni ko be ma sakota ba, idan dai har ya bayyana kansa na san waye shi, neman gidansa ba ze min wahala ba, dan haka har cikin gidan zan je, ni ba baƙuwar zafi ba ce, musamman ma kuma a kan abin da nake so.." ta ƙare tana murmushi, ji take kamar ta gama samun Lulun ta gama.

"Hakan ya yi.. Se dai wani hanzari ba gudu ba.."

"Me ya faru?" Ladi ta faɗa tana kallan Hero.

"Zan ɗan yi tafiya ne in dawo na en kwanaki kaɗan. Saboda haka ki jira dawowata, ni zan yi miki aikin komai. Kin ga kuma ga abokina ya shiga cikin case ɗin, dole zan fi bada himma wajen nemo gaskiyar lamarin." Da sauri Ladi ta girgiza kai, tace sanda ya kai ƙarshen maganarsa.

"A'ah.. Allah ya tsare hanya.. amma kafin ka dawo na gama aikata abin da na tsara.. Babu buƙatar se ka je ka dawo, kawai ka ba ni hoton, zan san yanda zan yi.."

"Ohk kina nufin ba kya buƙatar taimakona."

"No ba wai haka ba ne.. Kawai dai tun da tafiya za ka yi, ai gwara na yi komai da kaina koh?"

"Toh je ki yi.. Amma ki sani duk wata matsala da aka samu, kar ki tuhume ni. Ka da ma ki sake janyo ni cikin wannan harkar taki.." ya ƙare yana shirin juyawa. Da sauri Ladi tace

"A'ah kai fa daɗina da kai kenan, saurin fushi.. dawo ka ji.."

"Za ka kai kwana nawa kafin ka dawo..?"

"Kwana 5.." ya faɗa cikin basarwa.

"Shi kenan zan jiraka.. Dama akwai wasu en mata da nake jira, gobe goben nan za su iso.. Idan ya so kana dawowa se mu dira a kan wannan maganar.."

"Kar ki damu.." Hero ya faɗa yana juyawa dan barin ɗakin..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO30*


___A ɓangaren Bad Man kuwa, kwance yake a kan gadonsa, bayan sanda wannan nannauyan baccin ya yi awon gaba da shi. Idanunsa ya shiga buɗewa a hankali kamar wanda ya gama shan wasu kayan maye. Fuskarsa ya yamutse saboda yanda ya ji kansa ya wani irin sara masa. Se ya kai hannunsa kan nasa ya ɗan dafe shi, kafin ya miƙe zaune har lokacin be saki kan nasa ba. Har wani ɗan layi yake sanda ya miƙe ɗin, hakan ne ya sanya shi komawa ya sake zama na en sakanni. Sannan ya sake miƙewa kai tsaye ya wuce toilet ɗinsa. Ya shafe fiye da mintuna 30 a ciki sannan ya fito lokacin da duk wata sumar dake jikinsa take a jiƙe, ta kuma sake lafewa a jikinsa. Kai tsaye kaya ya saka, kamar ko yaushe ƙananan kaya. Wayarsa ya ɗauka ya jefata a aljihu kafin ya fice daga ɗakin, dan yau ɗin so yake ya ɗan fita ko yaya ne. A parlour suka yi kaciɓus da Daddy dake ƙoƙarin haurowa saman. Se ya dakata cike da mamakin ganinsa, dan abu ne da be saba gani ba. Daddyn a sashensa ba tare da wani ƙwaƙwƙwaran dalili ba.

"Me ya samu wayarka ina ta kiranka ba amsa?" Daddy ya tambaya cikin kulawa, dan ba kaɗan ba hankalinsa ya tashi, saboda kiransa da ya dinga yi babu amsa. Ɗan yamutse fuska ya yi bayan ya shafi gefen kansa yace

"Tana silent ne."

"Ohk toh me ya samu idanunka haka?" Daddy ya faɗa yana karantar yanayinsa. Cikin basarwa ya gyara tsayuwarsa yana faɗin

"Babu.. Ciwon kan nan ne dai kawai.."

"Ohk.. ya kamata ka je ka ga likita.."

"Tohm.." ya amsa da hakan yana shirin wucewa.

"Areef.." Daddy ya faɗa. Se ya juya ya kalli Daddyn ba tare da yace komai ba.

"Me kake yi cikin part ɗin nan?" Da mamaki yake kallan Daddyn jin abin da ya faɗa. Kafin kuma yace komai Daddy yace

"Ka manta yanzu ka yi aure? Wancan sashen za ka koma kafin komai ya daidaita.." Shiru ya yi na tsawon sakanni har lokacin yana kallan Daddy. Shi gaba ɗaya ma ya manta da wannan wasan yaran. Toh abu ne da ba ya tunanin yiwuwarsa dan haka ta yaya ma ze yiwu? Kamar ba ze ce komai ba se kuma ya buɗe baki da ƙyar yace

"Daddy.." se kuma ya dakata kamar wanda ya manta abin da ya soma faɗa. Jin shirun da ya yi ne ya sanya Daddy faɗin

"Kaa fahimta koh?"

"Za mu fita da Kaseem ne, na san yana jirana.." shi ne abin da Bad Man ya faɗa cikin basar da zancen Daddyn da sam ba ya son jin shi. Zuciyarsa zafi take masa sosai, gani yake yi kamar ya gama zubewa ƙasa warwass, har kamar shi za a ɗaurawa aure ba tare da saninsa ba? Da yarinyar da be santa ba? Kuma a ɗauketa a kawota gidansu, har ake faɗa masa ya koma inda aka kaita. Wace ce ita? Wace ce ita da har ze iya haɗa wajen zama ɗaya da ita? Lallai kuwa yau ɗin idan dai har ya shiga part ɗin, toh fa ba ze fito ba har se ya rubuta mata takaddar saki.

"Ka dai ji abin da na faɗa maka ai. Za ka iya tafiya.." Daddy ya faɗa yana riga shi yin gaban ma. Bin Daddyn ya yi da kallo sanda ya fice daga ɗakin. Ya ɗan ciji gefen lips ɗinsa na ƙasa yana fidda numfashi da ɗan sauri.


... Da sauri Mom ta ƙarasa inda yake, ta yi saurin riƙo hannunsa tana faɗin

"Ina za ka je?" Juyawa ya yi ya kalli Mom ɗin yace muryarsa a ɗan zafafe se dai ba cikin ɗaga murya ba

"Zan je na aikata abin da na yi niyya ne.." ya faɗa ransa a ɓace.

"Me kenan? Kar ka ce min sakin yarinyar can?"

"Yeah shi.." ya faɗa yana tsare Mom ɗin da ido, cikin rashin fahimtar abin da take nufi da dakatar da shi da ta yi. Girgiza kai ta yi da sauri tace kamar za ta yi kuka.

"Rabu da ita tukunna Boy.. Kar ka sake ka saketa.. Daddynka yace duk ranar da ka saketa ni ma ze sake ni.. dan haka ka bar komai a hannuna, zan nemo hanyar da za ka saketa cikin kwanciyar hankali ba tare da kowa ya zargi wani abu ba." Hannunsa dake cikin nata ya cire a hankali yana kallanta. Ya ma rasa abin da ya kamata ya yi. Da gaske Mom ɗin ke faɗin haka? Kar ya saketa fa take faɗa, toh ta zauna ta masa uwar me? Shin duk abin da Daddyn ya masa ba ta ji babu daɗinsa ba? Ko kuwa me yake faruwa.

"Mom.." ya faɗa da ɗan kaushi cikin muryarsa. Ajiyar zuciya Mom ta sauke, tana ganin kallan da Bad ɗin ke binta da shi tace

"Dalili ne ya sanya ni hakan. Shin ba ka ji me nace ba? Ba ka ji abin da Daddynka ya faɗa ba?"

"Whatever he said ba problem ɗina ba ne Mom. Ina so ne kawai na yi abin da ya dace. Ku kuma sake fahimtar ba a min abu se lokacin da nake so.." ya ƙare yana furzar da iska daga bakinsa me zafi, fuskarsa ta wani cakuɗe da ɓacin rai, haka zalika ko cikin muryarsa ma tana nuna ɓacin ran da yake ciki.

"Na sani Son. Daddy be kyauta mana ba, but za mu magance matsalar nan a hankali ba cikin gaggawa ba. Ni dai so nake ka tuna abin da ya faɗa, idan dai har ka saketa toh ni ma ze sake ni.."

"Daddy..?" Ya faɗa cike da mamaki. Se ta jinjina kai tace

"Ƙwarai kuwa.. Amma fa ka sani ba faɗin hakan da ya yi ne ze sanyaka zama da yarinyar ba, a'ah nan da en kwanaki ƙalilan zan fito da wata dabarar da ze sa ka saketa ba tare da kowa ya zargi wani ba." Shiru kawai ya yi mata, duk da ya ji abin da ta faɗa ɗin. Se lumshe lumsassun idanunsa kawai da ya yi yana jin yanda Daddyn ke ƙoƙarin sake manna masa ciwon kai da wannan aika_aikar da ya masa. Jin ya yi shiru ne ta fahimci ya ji abin da ta faɗa, ya kuma gamsu da hakan, dan haka tace

"Toh ka tashi ka je sashen kamar yanda yace maka saboda tsaro.." Se a lokacin ya buɗe idanun nasa, ya kalli Mom. Ya buɗe bakinsa da ƙyar yace

"Sashe..?"

"Ehh fa, duk dan ka da ya fahimci wani abun ne fa.."

"No.. ba zan je ba." Ya faɗa yana gyara zamansa. Cikin lallashi Mom ta nemi gefensa ta zauna, se da ta yi ƙasa da murya sannan ta soma faɗin

"Ka san.."

"Pls Mom ba zan je ba.." ya sake faɗa a karo na biyu yana ƙoƙarin miƙewa.

"Na fita se na dawo.." ya faɗa dan ya fahimci ita ma Mom ɗin so take ta fusata shi, bayan na Daddy.

"Pls Boy.. idan ka yi hakan fa za ka cire ni ne daga zargi.. Kuma ba ina nufin ku zauna ɗaki ɗaya ba, a'ah.. Allah ma ya kiyaye.. Kawai dai za ka nemi ɗaki ne cikin part ɗin ka zauna, saboda ko da maganar sakin ce ta tashi babu wanda ze yi wani zargi, ko a ce ni ce na zugaka." Ta ƙare cikin rarrashi cike da fatan ya amincewa maganar tata. Can ƙasan maƙoshi ya furta

"Naa.. ji" yana ficewa daga ɗakin.


... Ya ƙara wajen awa ɗaya a wajen suna cigaba da hira da Ummeey. Ita kuma tana cigaba da aikinta, har zuwa lokacin da ta gama ƙosai da kunu, se ta sami flask ɗinsu me kyau da kuma wani silver cup ta zuba kunu da ƙosan. Ta kalli Gwani dake kusa da ita tace

"Maza je ka kaiwa ɗiyata ta karya. Allah ya sa dai ban barta da yunwa ba.." Murmushi kawai ya yi a ransa yana mamakin hali irin na Lulu, tabbas da ita wata mutuniyar arziƙi ce se yace ta yi dacen sirika ainun. Ko a yanzu kaɗai se Ummeeyn ta birge

Please Login or Register in order to submit comment