Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta faɗa masa cewa ita ce. Kamar ba za ta yi magana ba se kuma cikin ƙarfin hali ta soma faɗin.. bayan ta yi iya ƙoƙarinta wajen janye idanunta daga cikin nasa.

"Ehh ni ce.." Ta faɗa a fili se ka ɗauka wata boss ta koma. Nan kuwa tsoro ne fall cikin ranta, se dai tana ƙoƙarin ɓoye shi ne dan kar ya fahimta.

"Ke ce..?" Ya tambaya cike da mamakin ƙarfin halinta. Se ta jinjina kai tana wani haɗiye yawu. Shiru ya yi yana cigaba da nazarinta. Kamar ba Bad Man ba yace

"Ko me ya sa?"

"Saboda babu kyau.. Ni kuma ba zan iya ganin ka na saɓon Allah kuma na bari ba. Shi ya sa nake kwashewa ko hakan ze sa ka dena. Amma wallahi ka ji tsoron Allah ka dena don Allah.." Ta ƙare a raunane. Tun da ta soma maganar yake kallanta kamar wani saƙago. Mugun ƙarfin gwiwar da ya shigeta wanda ya bata dama har ta iya tsayawa gabansa ta faɗa masa waɗannan maganganun shi ne ya fi komai ba shi mamaki.

"Ke ki ke kwashewa ashe..?" Ya sake tambaya dan sake tabbatarwa.

"Ehh.. Amma ka yi haƙuri." Murmushin gefen baki ya yi yana sake tuna maganganun da ta faɗa masa. Se dai kafin ya ida ɗin ma ya ji ta ɗora da faɗin

"Kai musulmi ne.. wanda ke zaune da iyayensa. Ba ka tunanin idan har wata rana zancen ya kai gare su wani irin hali za su shiga?" Ta ɗan dakata tana ƙoƙarin yin baya da fuskarta saboda yanda kusancinta da tasa ya ƙaru.

"Idan kuma zancen ya je wajen wasu shi kenan fa kowa ya san waye ka..." Ai be jira ma ta gama ci masa mutuncin ba, bakin da ke magana ya sanya bakinsa ya riƙo shi cikin nasa. Ba da niyyar sumbata ya kama bakin nata ba, se dan ya hora bakin da ke faɗa masa magana. Se dai cikin ƙanƙanin lokaci hakan ya nemi ya sauya, amma ya ƙi bada dama. Rashin tsammatar hakan ya sanya zancen nata katsewa lokacin da ta ji bakinta cikin nasa, ya kama lips ɗin yana sumbata, se dai yana sane ya shiga kissing nata a zafafe yanda ya san tilas za ta ji zafin hakan. Ya kuma san ba lallai ta sake buɗe baki tace za ta masa magana ba. A'ah daga mugunta se ga ɗan mutumunku har da lumshe idanunsa se dai har lokacin a zafafen ya cigaba da abin da yake yi, be kuma saketa ba. Saboda yanda take jin zafin kissing ɗin har tsakiyar kanta ya sanya tuni hawaye sun gama wanke fuskarta. Idanunta sun fito sosai saboda tsananin mamakin abin da ke faruwa. Zuciyarta na bugawa da ƙarfin gaske saboda tsoron da ya kama ilahirin jikinta. Ban da ƙoƙarin zame bakinta babu abin da take yi, amma ko bi ta kanta be yi ba. Ya kai wajen minti ɗaya da rabi kafin ya sakar mata bakin ya ma saketa gaba ɗaya. Hannu ta yarfar lokacin da ya saketa ɗin tana ji kamar ya tsinke mata baki gaba ɗaya saboda azaba. A daddafe ta nemi hanyar fita ko gani sosai ba ta yi ta fice daga ɗakin. Kai tsaye ɗakinta ta wuce. Se a lokacin ta iya kai hannunta ta goge hawayen fuskarta na wannan muguntar da ya mata. Hannunta a kan bakinta da ya yi mugun ja kamar wadda ta ji ciwo. Kawai se ta kifa kanta a kan gadon tana fashewa da kuka mara sauti. Ita kam yau ta yi danasanin da ba ta taɓa yi ba. Ta yi danasanin shiga ɗakin, ta kuma yi danasanin tanka masa bayan ya kulata. Ga shi nan garin hakan ya kusa cire mata baki.

A ɓangarensa kuwa ɗora hannunsa ya yi a kan sumar kansa. Ba tare da ya shirya ba wani murmushin gefen baki ya suɓuce masa. A hankali ya cigaba da shafa sumar kan nasa yana tuna abin da ya faru. Se kuma ya ɗan yi gyaran murya kamar shi da wani ne a wajen, ya gyara tsayuwarsa yana haɗe face ya koma kan gado ya zauna. Ya ɗauki mintuna masu ɗan dama a wajen kafin ya kalli gefensa da ya ji motsi. Se a lokacin ma ya tuna da Little da ke cigaba da baccinsa hankali kwance. Se ya miƙe a hankali ya saka hannu ya ɗauke shi. Kai tsaye ɗakin Didi ya wuce. Zuwa lokacin ta haƙura, se dai ta shafawa bakinta man zafi kar ta je ya kumbure mata kafin gobe. (Lolz) Ta juya da niyyar kwantawa dan kuwa ta sanya a ranta babu abin da ze sake kaita ɗakin ɗauko Little. Ya daɗe be kwana a can ba, ita ɗaya za ta kwanta babu komai. Daidai lokacin ya turo ƙofar ɗakin ya shigo hannunsa ɗauke da Little. Kawai se ta tsaya ta kasa ko da jan bargo ne ta lulluɓe jikinta. Se ka ce wadda aka ƙamar kawai ta ƙame tana jira ta ga abin da ze yi. Idanuwan da ya ji a kansa ne ya sanya shi kallanta, ta yi saurin ɗauke kai tana jan bargo ta lulluɓa gaba ɗayanta. Kawai se ya ƙarasa har kan gadon ba tare da yace mata komai ba ya ajje Little. Daga haka ya juya ya fice daga ɗakin. Ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya lokacin da ta ji fitarsa daga ɗakin.


... A ɗaya ɓangaren kuwa kwanaki 5 ciff aka kwashe ana bawa Maimuna kulawa ta musamman duk da taimakon Ammi da ke biyan kuɗin komai. Cikin ikon Allah se ga shi a kwana na biyar ɗin zancen farin ciki ya ziyarci Talatuwa. Shi ne na buɗewar bakin Maimuna. Farin ciki kamar za ta yi me. Haka ta shiga wajenta cikin matuƙar jin daɗi. Sun daɗe suna magana da Maimunan, duk da maganar tata a hankali take yinta kamar er koyo. Amma a haka suka yi maganganunsu.

Bayan wajen minti 10 Talatuwa ta fito tana murmushi, ta kalli Ammi tace

"Hajiya wai ki je tace tana son magana da ke."

"Ikon Allah! Ni ɗin?" Ammi ta faɗa tana mamakin wannan abu da ke faruwa. Ko me take ta so ta faɗa mata duk tsawon kwanakin nan? Kawai dai se ta miƙe ta kalli Gwaggo tace

"Gwaggo bari na je."

"Toh Allah ya jishshe mu alkhairi." Ba ta iya amsawa a fili ba se cikin zuciya. Haka ta kama jiki zuwa cikin ɗakin. Tun daga nesa Maimuna ta hangeta kasancewar idanunta na kan ƙofa ne. Ba ta san lokacin da ta yi dariya ba tana ji kamar ta tashi ta ƙaraso da Ammin. Da sauri Ammi ta ƙarasa dan kar Maimunan tace za ta tashi zaune. Kujera ta ja ta matsar da ita dab da gadon ta zauna. Hannunta riƙe da na Maimuna tace

"Ba se kin tashi ba ai gani nan." Jinjina kai Maimuna ta yi har lokacin fuskarta da murmushi a kai.

"Ina jin ki ga ni." In ji Ammi. Se da Maimuna ta sauke ajiyar zuciya sannan tace da muryarta da ba ta gama fita duka ba. Se dai ana iya fahimtar duk wani abu da zata faɗa

"Ki yi haƙuri na zaunar da ke da muka yi. Hajiya taimako nake buƙata don Allah bayan wannan uban taimakon da kika yi mana.. Kae ji gaji don Allah.. Wato na daɗe da damuwa cikin raina. Ban tashi soma son zuwa Kano ba saboda wani dalili se da na soma rashin lafiya. Hakan ne ya sa hakan ya ƙi yiwuwa saboda ciwon nan da ya same ni. Ga shi ni ba iya rubutu na yi ba ballantana na rubuta abin da ke cikin raina har ya je inda nake so ya isa ba. Ban kuma san yanda zan faɗawa Talatuwa Kano nake so na je ba. Se da zuwanki na ji an ce a Kano kike shi ya sa duk na ruɗe. Na ji tamkar a lokacin na warke ne saboda tsananin farin ciki. Na ɗauka Talatuwa za ta fahimci wani abun, se dai ban ga hakan ba. Se dai yanzu da bakina yake a buɗe ina me neman alfarmarki.. ina me neman amincewarki da ki zo ki taya ni duban wani gida da nake da tabbacin In Sha Allah za ki iya sanin shi. Ina so na je wajen masu gidan.. shi ne kaɗai burina. Ban da shi babu komai." Daga haka ta yi shiru tana amfani da hannunta lafiyayye wajen goge fuskarta da ta jiƙe sharkaff da gumi da kuma hawaye. Tun da ta fara magana Ammi ke kallanta har ta ƙarasa. Ganin irin kallan da Ammin ke mata ne ya sanyata cigaba da faɗin

"Ban san da wane irin baki zan buɗe na miki bayani ba, dan ban san yanda za ki ɗauki zancen ba. Ni dai fatana ki taimaka min ki kai ni Kano se mu nemi gidan tun da ke kin san garin. Don Allah ki taimake ni kar ki ce a'ah. Kamar yanda kika taimaka min a kan wannan ciwon nawa ki taimaka ki kai ni Kano. Ban taɓa zaton bakina ze kuma buɗewa ba. Ban taɓa tunanin zan kuma zama na yi magana kamar yanda mutane ke yi ba. Ba na so na butulcewa Allah, haƙiƙa Allah na sona, shi ya sa ya sake ara min baki a lokacin da ban yi tsammani ba. Ban sani ba ko dan ya ba ni damar gyara kuskurena ne."

Se a lokacin sannan Ammi tace

"A haka za ki je har wani garin?" Ammi ta faɗa cike da mamakin maganganun Maimunan da suka matuƙar jefata cikin tunani. Lokaci ɗaya kuma tana kallan Maimunan da ke kwance kan gado ko tashi ba ta iya yi, take zancen tana so ta je Kano. Hawaye ne suka zubo daga cikin idanun Maimuna tace

"Ai shi ya sa nake cewa ki taimaka min don girman Allah. Ko da wannan ɗin ita ce alfarma ta ƙarshe da za ki iya min ki yi min ita." Shiru Ammi ta sake yi na tsawon sakanni kafin ta sauke ajiyar zuciya tace

"A kan wane gida kike magana? Gidan na da wani suna ne da za a iya gane shi da shi?" Jinjina kai Maimuna ta yi tana ji kamar ta tashi zaune ta ƙarasa maganar. Se dai kasancewar ta san hakan ba me yiwuwa ba ne ya sanyata faɗin

"Na sani.. Sunan me gidan Alhaji Matawalle.."

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO60*


___ "Alhaji Matawalle.." Ammi ta maimaita sunan tana jinjina kai.

"Ehh haka sunan yake." Talatuwa ta sake faɗa.

"Shi kenan.. zan taimaka miki." Hawaye sosai Maimunatu ta shiga yi tana godewa Ammi, tana ji tamkar ta tashi ta ɗauketa ta yi ta juyi da ita a bayanta. Kai tsaye Ammi na fitowa number Abba ta nema ta sanar da shi abin da ya faru.

"Alhaji Matawalle..?" Shi ma ya maimaita sunan cike da mamaki.

"Toh ai gidan surukan Afrah ne take nufi kenan." Numfashi Ammi ta sauke tana faɗin

"Tabbas.. Dan kaf Kano babu wani me irin sunan bayan shi."

"Ikon Allah.. Toh Allah ya sa lafiya. Yanzu ke me kika yanke?"

"Duk abin da ka ce Yallaɓai." Murmushi Abba ya yi yace

"Toh shi kenan.. Idan ze yiwu ku samu ku taho Kano ɗin zuwa gobe, idan likitocin za su baku ita mara lafiyar. Allah ya bada lada."

"Ameen Ameen Abbansu. Amma ka na ganin babu komai idan na je gidan?" Girgiza kai Abba ya yi kamar Ammin na gabansa yace

"A'ah babu komai.."

"Tohm." Daga haka suka yi sallama.

.. Cikin ƙanƙanin lokaci Ammi ta soma haɗa kaya. Ta bar Aunty Maryam ta cigaba da kula da lafiyar Gwaggo kafin ta samu sauƙi sosai a nemo mata sabuwar er aiki. Da yake jikin Maimunan ya yi sauƙi shi ne dalilin da ya sa suka barta bayan an bata ɗaya daga cikin kujerar da wani bawan Allah ke bayarwa a raba saboda guragu da masu irin lalurarta.


... Sanye cikin doguwar rigar atamfa ɗinkin rapper. Se wani hijab madaidaici da ta saka a kai. Ta yi wani shahararren kyau kamar ba ita ba. Kitchen ta nufa ta shiga duba abubuwan da take da su. Se ta fito a nutse ta nemi gefen gadon ta zauna. So take ta yi girki tun da dai ta warke, se dai kuma babu kayan miya. Ga dai kayan abincin da ya siyo mata en daidai kamar na me ƙarfinsa. Ta ɗan tura baki da alama wani abin ta tuna cikin zuciyarta. Kawai se ta miƙe ta fice zuwa tsakar gida. Abeey na zaune a kan dadduma yana saurarar wani shiri daga gidan Radio. Gefe guda kuma Ummeey na zaune tana tsince wake a cikin faranti. Daidai lokacin Lulu ta fito daga cikin ɗakin se ta ƙarasa gefen Ummeeyn ta zauna a nutse tace

"Sannu da hutawa Abeey."

"Yawwah sannu dai ɗiyata. Ki na lafiya?"

"Ehh.." ta amsa da hakan tana maida dubanta kan Ummeey.

"Ummeey Barka da wannan lokacin."

"Barkanki dai.." Ummeey ta amsa da murmushi kan fuskarta. Se ta saka hannu ta karɓi farantin hannun Ummeeyn tana faɗin

"Kawo na tsince."

"Daga fitowarki kuma?" Ummeey ta faɗa. Se kawai ta yi murmushi tana soma tsince waken. Girgiza kai Ummeey ta yi har cikin ranta tana sake jin daɗin chanjawar Lulun. Miƙewa ta yi ta je ta zubawa Abeey da ze fita ruwa a buta. Se da ya miƙe sannan Lulu tace

"A dawo lafiya."

"Allah ya sa." Abeey ya amsa shi ma da murmushin kan fuskarsa. Daga haka ya ƙarasa ya ɗauki butar ya yi alwala kafin ya yi sallama da Ummeey ya fice daga gidan. Komawa Ummeey ta yi ta zauna tana ɗan soma jan Lulun da ta yi shiru da hira ko za ta samu ta sake. A daidai lokacin ne kuma Gwani ya yi sallama cikin gidan. Duka suka amsa masa sallamar, se dai ita Lulu ƙasa ƙasa ta yi tata ta cigaba da abin da take yi. Ƙarasawa ya yi ya nemi waje ya zauna Ummeey na masa sannu da zuwa. Ya amsa yana maida dubansa kan Lulu da tun ɗazun yake jin zuciyarsa na azalzalarsa a kan ya kalleta.

"Sannu da zuwa." Ta faɗa kamar wadda aka tilastawa se dai har lokacin ba ta kalle shi ba.

"Yawwah.." Ya amsa a hankali yana ƙoƙarin nemo ƙwayar idanunta dake kallan ƙasa. Sam ya manta ma Ummeey na wajen. Ita dai Ummeey ba tare da tace komai ba ta miƙe ta shige kitchen. A karon farko ta ɗaga kanta saboda tasirin idanunsa da suka mata nauyi a ka. Se kuwa suka haɗa ido. Ya lumshe ido yana ƙoƙarin basarwa. Se dai ya kasa, be san dalili ba. Yau ɗin se yake ganinta kamar wata ta daban, ta yi kyau. Uwa uba ramar nan da ta yi babu ita, ta koma ainahin Afaaf ɗinta. Duk da ya ga sarai ta gan shi yana kallan nata amma hakan be sanya shi fasawa ba. Allah ma ya gani ba ƙaramin farin ciki yake samun kansa a ciki ba duk lokacin da yake kallanta. Shi kansa har mamakin kansa yake yi idan yana wani abun. Abubuwa da dama kuma suna ɗaure masa kai. Musamman yanda yake ji tabbas a cikin ransa ƙaunar Afaaf ɗin yake. Abin da be taɓa zata ba, be kuma tsammani ba. Ya sauke ajiyar zuciya yana ɗauke kansa daga fuskarta lokacin da ya tabbatarwa kansa da ya gamsu da ganinta. Miƙewa ya yi ya wuce ɗakinsu. Se a lokacin ta iya ɗaga kai ta kalli inda ya tashi. Se kuma ta maida kanta kan waken tana faɗin

"Kawai ya yi ta wani kallan mutane.." Ta faɗa tana sake turo baki.



.. Se da ta tabbatar hankalinsa na kan wasan da yake yi. Wanda yana yi yana karatu hankalinsa kwance kuma yana wasansa. Se ta ƙarasa ta shimfiɗa dadduma ta tayar da sallah. Ba ta ankara ba kuwa ya faki idanunta ya fice daga ɗakin a guje.

"Wannan yaro." Ta faɗa tana dafe goshinta lokacin da ta idar da Sallah ta kuma fahimci ya fice daga ɗakin. Ba ta takurawa kanta ba dan ta san wajen waye ze tafi, wato Areef. Mutumin da cikin lokaci ƙanƙani ya shiga ran Little ɗin. Ita har mamaki abin yake bata musamman ita da ta san halin Little. Ga shi ma kuma Bad ɗin dake da bauɗaɗɗen hali. Se ga shi kuma tasu ta zo ɗaya. Cigaba da zama ta yi a kan daddumar dan kuwa ta saka a ranta ko kwana Little ze yi a wajensa ba za ta je ɗaukarsa ba. Se da ta yi karatun Qur'an me yawa sannan ta miƙe daga kan daddumar. Har zuwa dare Little na tare da Bad Man da yau be fita ko ina ba musamman saboda saɓanin da suka samu da Kaseem. Kowa fushi yake da kowa, hakan ne ya sanya shi ba shi space kafin ya waiwaye shi.

Fitowarta daga wanka kenan ta gama shiryawa. Se ta ƙarasa ta nemi wata doguwar riga mara nauyi, wadda iyakacin tsayinta gwuiwarta. Se da ta ɗauki ƙaramin mayafi ma tukunna kafin ta koma gaban mudubin. Saka rigar ta yi, hakan ne ya sanya ta janye towel ɗin jikinta ta ƙasa ta maida shi inda ya kamata. Kafin ta dawo ta ɗauki mayafi da niyyar ɗaure kanta ta samu ta kwanta. Daidai lokacin ya turo ɗakin ba tare da ya nemi izini ba. Da sauri ta ɗaga kai dan ganin ko waye? Se dai tun kafin ya shigo ɗin tuni ƙamshin turarensa me daɗi ya riga shi shigowa cikin ɗakin. Se kuma daga baya ya shigo hannunsa ɗauke da Little. Kai tsaye yanzun ma kan gadon ya nufa ya sauke shi, ya ja masa blanket ya lulluɓe shi kafin ya miƙe. A hankali ya saci kallan inda take hannunta ɗauke da hijab ɗin da ta yi nasarar ɗaukar shi. Duk da ba ta kallansa amma ta san ita yake kalla. Ba ta ɗago ba se ta soma ƙoƙarin kare ƙafafunta dake a buɗe da hannunta. Duk da ba ta so ya fahimci abin da take yi. Tun daga ƙasa ya maida dubansa kanta ya shiga kallanta har saman kanta. Ya ɗan ciji laɓɓansa kafin ya soma takawa. Ta ɗauka fita ze yi daga cikin ɗakin, har tana shirin sauke ajiyar zuciya se tsintar mutum ta yi a gabanta.

"Wai kare jikinki ki ke dan kar na kalla?" Ta tsinci maganarsa, wadda ta sanyata saurin ɗaga idanunta ta kalle shi. Ya ɗaga kansa alamar "Uhmm.." Ya ƙare lokacin da ya zamana tazarar dake tsakaninsu ba ta da yawa ko kaɗan. Gaba ɗaya ta ruɗe. Kunya duk ta baibayeta. Har ga Allah ba ta san ya fahimci abin da take yi ba. Fahimtar yana cigaba da kallanta ne ya sanyata ƙoƙarin zamewa ko da ta ƙasa ne. Se ya sanya hannunsa ya riƙota ta kusa haɗewa da jikinsa.

"Kare jikinki kike dan kar na kalla?" Ya sake tambaya da niyyar ta ba shi amsa. Idan ma kallan ɗan iska take masa, ya gwada mata da gasken haka yake. Ya san hakan ne kaɗai ze sa ta dena masa haka. Se ta yi saurin girgiza kai tana runtse idanunta. Ba ta ankara ba se ta soma jin hucin numfashinsa a kan fuskarta, dalili kenan da ya sanyata buɗe idanunta ta yi saurin jan laɓɓanta ta taune cikin bakinta. So take ta yi magana amma tana tsoro kar ta buɗe bakin a sake maimaita abin da ya faru a karo na biyu. Hakan ne ya sanyata kama bakinta a tsorace. Daidai lokacin da wayar Bad Man ta yi ƙara kenan. Se ya saketa da sauri yana jin wani ɓacin rai na taso masa. Juyawa ya yi kawai ya fice daga ɗakin ba tare da ya sake kallan inda take ba.

"Bro ina son magana da kai." Kaseem ya faɗa muryarsa a cushe. Kamar ba ze ce komai ba dan se da ya ɗauki sakanni masu yawa, hannunsa na cikin tulin sumar kansa yana hautsinawa.

"Ina ji."

"Ka faɗa min ya aka yi ka auri Afrah?" Shiru Bad ɗin ya yi dan so yake ya fahimci maganar sosai kafin yace wani abu. Zuwa can ransa ya soma ɓaci. Wani irin ɓacin rai da ya haɗu da na yanzu.

"Kaseem.. ka kama kanka. Ka na nema fa ka wuce gona da iri. Na barka ranar nan ba tare da na illataka ba, hakan be isheka ba? So daga rana irin ta yau kar ka sake magana a kan matata, idan ba haka ba zan illataka.." Daga haka be jira Kaseem ɗin yace komai ba ya kashe wayar. Ya nemi waje ya zauna, har lokacin hannunsa na cikin sumar kansa.

"Wane irin mutum ne Kaseem?" Ya tambayi kansa. Be taɓa tunanin haka yake ba. Ya kuma saka a ransa duk ranar da ya sake yi masa magana a kan yarinyar nan ze ga abin da ze masa. Se kuma can ya yi shiru yana nazarin abubuwan da ya faɗawa Kaseem ɗin da kuma abubuwan da shi kansa yake yi. Me ya shiga kansa ne? Me yake damunsa? Ya ja tsaki yana miƙewa ya faɗa toilet dan watsa ruwa a jikinsa.



.. Washegari su Ammi suka ɗaga zuwa Kano. Saboda gidan Alhaji Matawallen ba ɓoyayye ba ne kai tsaye nan suka tari mota, Ammi ta masa bayanin inda ze kai su. Se aka yi sa'a me napep ɗin irin wayayyen nan ne, ya ɗauke su, se gidan Alhaji Matawalle. A can baya ya yi parking na motarsa yace

"Toh mu nan ne bodarmu fa Hajiya. Se dai ku sauka ku ƙarasa."

"Toh mun gode." Ammi ce ta fara sauka, ta haɗa keken Maimuna kafin ita da Talatuwa suka ɗora Maimunan a kai. Ammi ta saita duk wani abu da ya kamata jikin keken sannan ta kalli mutumin dake nuna mata gidan.

"Mun gode sosai.." Ammi ta faɗa tana murmushi. Bin gidan da ya nuna Maimuna ta yi da kallo, tun da suka shigo layin jikinta ya yi wani bahagon sanyi. Duk da ba a iya ganin ya yanayin jikinta yake amma ko a fuskarta se ka fahimci hakan. Abubuwa da dama ne suke dawowa cikin kwanyarta a wannan lokacin. Se yanzu take tunanin ƙalubalen da za ta fuskanta duk lokacin da ta faɗi dalilinta na zuwa gidan. A take jikinta ya ɗauki rawa, se take ji kamar tace su koma. Ji take kamar ta juya saboda tsananin yanda take jin bugun zuciya. Idanunta da ke kallan ƙasa ta bari suka cigaba da kallan ƙasan lokacin da Talatuwa ke turata suna cigaba da tafiya.

"Wa kuke nema?"

"Alhaji Matawalle.." Talatuwa ta faɗa tana kallan ƙaton mutumin da ke kallanta fuskarsa babu annuri.

"Ya san da zuwanku ne?" Se ta girgiza kai tana duban Ammi cikin neman ƙarin bayani.

"Amm bawan Allah da yake ba mu san ya tsarin yake ba ne shi ya sa ka ji mun ce haka. Mun san ta yanda muka biyo ɗin be yi ba, amma kuma saboda abin da ke tattare da mu shi ya sa ba mu ji komai ba wajen faɗin muna son ganin Alhaji Matawalle."

"Lallai fa.." Mutumin ya faɗa yana jinjina kai. Be sake cewa komai ba ya juya. Talatuwa ta kalli Ammi tace

"Hajiya da ma haka abun yake?"

"Kar ki damu.. In Sha Allah za mu samu ganinsa." Se ta karkaɗa kai tana faɗin

"Toh Allah ya sa." Zuwan wasu matasa su biyu ne ya sanya Talatuwa kallansu daidai lokacin da wani dogo a cikinsu ke faɗin

"Se dai gobe ku dawo. Yau ba ya buƙatar ganin kowa." Shiru ne ya wanzu a wajen. Maimuna dake kan kujera ba ta iya ganinsu ta ji ina ma za ta iya ɗaga kai ta kalli mutumin dan ta masa magana. Se dai kuma hakan ba ze yiwu ba. Ga shi kuma gaba ɗaya ma ba ta da wannan ƙwarin gwuiwar, dan ta daɗe da rasa ƙwarin gwuiwar tun bayan shigowarsu Kano.

... Har ƙasa ya tsuguna cike da ladabi yace

"Rankayadaɗe wasu mutane sun takura suna son ganinka ne. Mun yi niyyar korarsu ne ma da, toh kuma mun san ba ka so, shi ya sa muka fasa. Duk da ka ce yau ba ka san ganin kowa amma yanda na ga mutanen ya sa na ce bari na zo na faɗa maka Sir."

"Kamar dai yanda na faɗa ɗin ne. Ba na son ganin kowa a yau ɗin nan. Ku ji da duk mabuƙatan kawai" Se da ya ɗan yi shiru yana tunanin ta inda ze soma. Har Bad Man dake gefe na ƙoƙarin ba shi umarnin tashi ya fita se ya ji yace

"Haka muka sanar da su Rankayadaɗe.. Mun kuma yi ƙoƙarin taimaka musu suka

Please Login or Register in order to submit comment