Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shaƙo wuyanta. Hannunta na rawa ta sanya wajen karɓar yaron a hannun Maimuna, se kuwa ya biyo hannunta. Ta sake jin wata sabuwar faɗuwar gaban ta ziyarceta. Amma duk da haka ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen tattaɓa shi ko za ta ga ya yi motsi kamar yanda jarirai ke yi, se dai sam be yi ba. Hasalima kamar yanda Maimunan ta faɗa babu rai a tare da yaron. Rungume shi Mom ta yi tana faɗin

"Na shiga 3 ni Salma.. Na shiga 3 na lalace." Ta faɗa ilahirin jikinta na rawa saboda tsananin tashin hankali. Kamar kuma wadda aka kunna se ta ajje jaririn a gefenta tana saka hannu ta goge hawayen fuskarta. Ta kalli Maimuna da ke kallanta cike da tausayawa tace bayan ta yamutsa fuska saboda yanda take jin jikinta.

"Ɗauki mukullin can ki je sashen Sa'adah ki duba min halin da take ciki cikin dabara, ki gano min abin da ta haifa." Ta ƙare tana sake share hawaye zuciyarta na bugawa da ƙarfin gaske.

"Toh Hajiya." Maimuna ta faɗa tana ficewa daga ɗakin.

"Na shiga 3 ni en nan.." Mom ta sake faɗa tana fashewa da wani sabon kukan idanunta a kan mataccen jaririnta.

Bayan shuɗewar wasu mintuna har lokacin Mom ba ta motsa daga inda take ba, se ga Maimuna ta faɗo ɗakin kamar wadda aka jefo. Har wani haki take yi, ta ƙaraso kusa da gadon ta tsaya, a gaggauce kamar wadda aka biyo tace

"Hajiya en biyu ne ta haifa.. Wallahi na rantse da girman Allah Hajiya en biyu ne." Maimuna ta faɗa gaba ɗaya jikinta na wani irin karkarwa. Tashin da Mom ba ta shirya ba se ganinta na yi kawai ta miƙe zaune, idanun nan kamar za su faɗo ƙasa tace

"En biyu kuma? An ya lafiyarki ƙalau kuwa?"

"Wallahi da gaske nake Hajiya.. Na duba su kuma duk maza ne.." Suman zaune kawai Mom ta yi ba tare da tace uffan ba. Idan ban da jikinta da ya ɗauki rawa kai se ka ɗauka sanyi take ji. Har wani hazo_hazo ta ga yana giftawa ta wajen idanunta, bakinta kuwa wani karkarwa yake yi wanda hakan ya hanata iya furta kowacce kalma. Ban da kallan Maimuna babu abin da take yi. Ji take kamar Maimunan za ta buɗe baki ne tace mata da wasa take yi. Mommahn na can rai a hannun Allah, abin da ta haifa kuma ya koma. Se ga shi yanzu ta zo tana mata wani wasan kwaikwayo..


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO64*

___Ta ɗauki kusan mintuna 2 har lokacin ta kasa furta komai. A hankali kuma ta juya ta kalli mataccen jinjirinta da ke gefe a kwance. Kawai se ta fashe da kuka me sauti, ta shiga girgiza kai cikin rashin sanin abin yi.

"Ki yi haƙuri Hajiya.. Don Allah ki dena wannan kukan.." Shi ne abin da Maimuna ta faɗa tana kallan Mom ɗin cike da tausayawa. Hannu Mom ta kai fuskarta ta shiga ƙarar da hawayen da ke kan fuskarta da hannunta. Gaba ɗaya ita ta ma manta da yanda take jin jikinta, burinta ta nemowa kanta mafita kafin lokaci ya ƙure mata.

"A yaya kika samu Sa'adah?" Mom ta faɗa tana kallan Maimuna cikin idanunta. Se da ta ɗan yi shiru sannan tace bayan ta girgiza kai

"Duk da hankalina na kan abin da ta haifa.. Amma da ƙyar ne idan tana da rai fa. Dan wallahi ban ga alamar tana motsi ba. Idan kuwa tana yi to dab take da ƙarasawa.." Hannu Mom ta saka ta ɗauki jaririn da ta haifa, duk da yanda hannunta ke rawa hakan be hanata miƙawa Maimunatu shi ba tace lokacin da ƙirjinta ya buga kamar wadda ke jin tsoro.

"Je ki ajje mata wannan.. ki ɗauko min nata yaran da ta haifa." Kallan yaron Maimuna ta yi da sauri tana jin yanda cikin ƙanƙanin lokaci zuciyarta ta soma harbawa fiye da ƙa'ida. Muryarta har rawa take yi wajen furta

"Ha..jiya.." Wani banzan kallo Mom ta watsawa Maimuna tana ji kamar ta miƙe ta je ta aiwatar da abin da zuciyarta ta raya mata, ta kuma yi na'am da hakan ba tare da wani dogon tunani ba.

"Ba za ki yi ba ne in tashi da kaina in je in yi?" Da sauri Maimuna ta girgiza kai tana faɗin

"Ba haka ba ne Hajiya.. Kawai dai ina jin tsoro ne wallahi.. Kar in je a kama ni."

"Waye ze kama ki? Babu kowa cikin gidan nan.. Kin kuma san duk mazan da ke cikin gidan suna can suna harkokinsu. Faɗa min wanda ze ganki?" Ajiyar zuciya Maimuna ta sauke kafin tace komai Mom ta ɗora da faɗin

"Ki yi min wannan taimakon Maimuna. Jikina babu daɗi, ba ni da ƙarfin da zan tashi na je na ɗauko jarirai har biyu.. ina ganin kafin na zo nan an kama ni.. Ki taimaka ki min wannan taimakon Maimuna, ko kuwa da ma ba zaman amana muke yi da ke ba?" Hannunta Maimuna ta kamo ta riƙe tace

"A'ah Hajiya.. Zan iya miki ko wanne irin taimako ne.. Kin fi ƙarfin haka a wajena. Wannan ɗin ma kawai dan ina jin tsoro ne, amma kuma yanzu kin ƙarfafa min gwuiwa, dan haka ki jira dawowata yanzun nan." Wani irin sanyi Mom ta ji ya ratsata har cikin ranta. Ta ji tamkar ta miƙe ta rungume Maimunan, se dai ba ta da wannan ƙarfin. Hasali ma jikinta duk babu kyau, amma ta fi burin ganin samun yaran kafin ta dawo ta yi ta kanta.

"Na gode sosai Maimuna.." Mom ta faɗa daidai lokacin da Maimunan ke dab da ficewa daga ɗakin. Kamar wadda aka tsayar se ta dakata, ta juyo ta kalli Mom tace

"Hajiya ga shawara.. Ki ɗauki ɗaya ki bar mata ɗaya, tun da kin ga kowa ya san abin da za ki haifa ba biyu ba ne." Wata harara da ba ta shirya zuwanta ba ita ta makawa Maimuna, tace a fusace

"Ashe ma ba ni da hankali.. toh me kenan na yi? Da in yi hakan ba gwara na bar mata gaba ɗaya 'ya'yan ba. Ba na so ne ya zamana tana da ɗa ko ɗaya cikin gidan nan.. Maza ki je ki kwaso min su, kafin wani ya shigo gidan nan."

"Shi kenan.." Se a lokacin sannan Maimuna ta saka hannunta ta karɓi mataccen jaririn Mom ɗin. Ba tare da ta sake cewa komai ba ta fice daga cikin ɗakin, Mom ta runtse idanunta cike da fatan Maimunan ta je lafiya ta dawo lafiya tare da jira_jiran nan. Ba kuma tare da kowa ya ganta ba.

Cike da takatsantsan ta sake tura ƙofar a hankali. Kamar yanda ta bar Mommahn yanzun ma tana kwance kan gadon kai ba za ka taɓa cewa akwai rai a tattare da ita ba. Amma saboda shegiyar zuciya irinta Maimuna ko kaɗan hakan be dameta ba, ita burinta ɗaya shi ne ta cika umarnin uwar ɗakinta. Ƙarasawa ta yi inda jinjirayen suke cikin zanin gado. Ta ƙarasa tana kallansu. Se ta yi maza ta ajje jaririn Mom a gefensu bayan ta gyara su ta haɗe su waje ɗaya, dan kuwa tun ɗazu da ta zo ta same su kowanne yana inda yake. Duk da yanda take sauri ta fice daga ɗakin, hakan be hanata ƙare musu kallo ba. Ɗaya idanunsa a rufe yake da alama ya yi kuka har ya gaji bacci ya ɗauke shi. Ya yin da ɗayan idanunsa biyu yana kukan da ba ya fita sosai. Dan ko sautinsa ba a iya ji sosai se ka matso kusa da shi. Ta jinjina kai lokacin da ta ga wani tsantar kyau a tattare da jariran, duk da ko a yanzun za ka fahimci babu kama ko kaɗan a tare da su amma kowanne Allah ya zuba kyau a tare da shi. Kuma ba za ka iya tantance wanda ya fi kyau ba, dan kuwa kowanne kyawunsa daban yake. Duk da a lokacin aka haife su hakan be hana komai fitowa ba tarr tarr ba, kamar misalin siririn dogon hanci, mitsitin baki da kuma manyan idanu. Ta kalli ɗan gidan Mom a fili ta furta

"Ikon Allah!!" Dan kuwa yaron ba dai hanci ba. Hancinsa irin na en gidansu Mom ne kamar an saka guduma an maida shi ciki. Duk da ko kaɗan be ɗauko kamar Mom ba amma a fizge yana kama da en gidansu Mom ɗin, har warɓeɓen bakin. (Astagfirullah)

Tuna kasassaɓar da take ƙoƙarin aikatawa ne ya sanyata juyawa ta kalli ƙofar ɗakin, kafin ta dawo da dubanta cikin ɗakin. Hannunta na wani irin karkarwa ta saka ta ɗauke su. Ta sanya su cikin hijab duk da yanda ƙafarta ta yi sanyi hakan be hanata ficewa daga ɗakin ba ƙirjinta na bugawa. Amma haka ta daure, ba tare da ta juya ba ta shige sashen Mom. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta ganta cikin ɗakin Mom ɗin. Da sauri da sauri ta ƙarasa tana cigaba da sauke numfashi ta buɗe hijab ɗinta ta fito da su. Kawai miƙawa Mom da tun da ta shigo take kallanta ta yi ba tare da tace komai ba. Mom ta saka hannu ta karɓe su tana wata irin dariya saboda tsananin farin cikin da ta ji. Ta kalli yaran, irin kyawun da Allah ya basu kaɗai ya isa ya sa ta ji abin da ta aikata shi ne daidai. Kawai se ta rungumesu a ƙirjinta a fili tana furta

"Uwar biyu.." Ta ƙare tana murmushi.

"Kar ki yi haka Hajiya. Kar ki bar wata kafa da za ta kawo zargi a kan wannan haihuwar. Ki maida mata da yaro ɗaya, ko kuma ki san yanda za ki yi da shi. Amma dai kar ki riƙe su duka a matsayin kin haifi 'ya'ya biyu." Shiru Mom ta yi tanaa nazarin maganar Maimunan. Ta wani ɓangaren kamar ta faɗi gaskiya ne. Kar ta je hakan ya janyo zargi, ko kuma dai can wata matsalar daban. Ta sauke ajiyar zuciya tana juyawa ta kalli Maimuna

"Ya za a yi yanzu?" Shiru Maimuna ta yi tana tunanin abin da za tace. Kafin ta gama tunanin Mom ta sauko da jinjirayen tana kallansu. Ɗayan wanda yanzun ya yi shiru har kuma lokacin idanunsa a buɗe suke, se dai yana ta mutsu mutsu alamar ze iya cigaba da kukan da ya yi shiru yanzun shi Mom ta sake riƙewa. Ta kalli ɗayan da har lokacin yake bacci abinsa. Se ta miƙawa Maimuna shi tana faɗin

"Riƙe shi ki ga.." Babu musu ta saka hannu ta karɓe shi.

"Ki fitar da shi daga gidan nan. Duk inda za ki je ki je da shi. Yanzu ban san abin da zan ce a masa ba, zuwa anjima idan hankalina ya dawo jikina za ki ji kirana."

"Hakan mafita ce kuwa Hajiya?"

"Sosai kuwa.. Ke dai ɗauke shi kawai ki je." Se da ta sake sauke ajiyar zuciya sannan ta saka hannu ta ɗauke shi ta fice daga ɗakin duk da har lokacin tsoro ne fall a cikin ranta. Ba ta fita daga cikin gidan ba se da ta tabbatar babu wanda ya lura da jinjirin da ta ɓoye cikin hijab, kafin ta fice daga cikin gidan. Fitarta ke da wuya Baba Atine ta shigo cikin gidan, kai tsaye ɗakin Mommah ta wuce dan ta sanar da ita saƙon matar da ta aiketa wajenta. Se dai ta ji shiru cikin ɗakin. Hakan nan kawai ta ji hankalinta be kwanta ba, dan kuwa idan dai har sashen Mommahn a buɗe yake toh idanunta biyu, tana sallama za ta amsa ta fito, se kuma yau ta ji shiru Mommahn ba ta amsa ba, ga kuma ƙofar bedroom ɗin kusan a buɗe. Se ta ji tamkar ta shiga cikin ɗakin. Amma kuma hakan ba huruminta ba ne. Se kawai ta nemi waje ta zauna bayan ta sake yin sallama ba a amsa ba. Ta ɗauki wajen minti 10 zaune a palourn kafin daga bisani ta miƙe saboda yanda zuciyarta ta ƙi na'am da shirun Mommahn. A hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga. Se kuwa ta hangi Mommahn kwance, ga wani abu da take hanga kamar jinjiri cikin jini. Da sauri ta ƙarasa tana kiran sunan Allah. Kamar yanda idanunta suka nuna mata haka ɗin ne kuwa. Tsoro ya kamata ganin daga jinjirin har Mommahn babu wanda ke da alamar rai a tattare da shi. Jikinta na wani irin rawa ta fice daga ɗakin, sam ta ma manta akwai wasu halittun cikin gidan bayan su, kawai ta faɗa wani gida dake kusa da su. Bayan wajen minti 2 se ga ta sun dawo tare da maƙociyar tasu. Babu ɓata lokaci driver ya ɗauki Mommahn da Baba Atine se asibiti. Tun a mota Baba Atine ta karɓi wayar drivern babu ɓata lokaci ta kira Daddy ta sanar da shi abin da ke faruwa. Cikin tashin hankali ya baro inda yake, ko neman wani be yi ba da kansa ya hau mota dan wucewa asibitin. A kan hanya ya kira wayar Mom. Se dai ita ɗin ma se take sanar da shi babu lafiya. Tsoro ya kama shi, kawai se ya chanja akalarsa zuwa gidan, tun da ko babu komai ita yanzu Mommah za ta samu kulawar likitoci. Ita kuma Mom ta shaida masa babu kowa cikin gidan. Hakan ne ya sa ya wuce can ɗin. Da kukan jariri ya soma cin karo, be san lokacin da murmushi ya ƙwace masa ba. Ya ƙarasa yana karɓarsa daga hannun Mom ɗin. Se kuwa ta koma ta kwanta tana sauke numfashi a wahalce. Duk da dai da gasken jikinta babu daɗi, amma tana sane take ƙarawa dan Daddyn ya tausaya mata.

"Sannu Yallaɓiya.." Daddy ya faɗa yana kallanta. Se ta jinjina kai kawai ba tare da tace komai ba. Daddy ya rungume jinjirin duk da jikinsa babu kaya kuma ba a gyara shi ba, yana jin wata irin ƙaunarsa na ratsa shi. Be ɓata lokaci ba ya taimakawa Mom ɗin ya sanyata cikin mota se asibiti.


.. Kai tsaye lokacin da su Baba Atine suka isa asibitin ɗaki na musamman aka wuce da Mommah. Cikin lokaci ƙanƙani aka shiga bata taimakon gaggawa. Ya yin da tun gwadawar farko da likita ta yi wa jaririn ta tabbatar babu rai a tare da shi. Babu daɗewa su Daddy suka isa asibitin. Ita ma Mom ɗin karɓarta aka yi daga ita har jaririn dan duba lafiyarsa shi ma.


... "Ya jikin wife ɗin tawa?" Daddy ya faɗa yana kallan Likitar.

"Alhamdulillah jikinta da sauƙi.. Kuma In Sha Allah nan ba da jimawa ba za ta warke ma gaba ɗaya. Abin ne ya zo mata a juye.. Ga shi haihuwar fari, ga shi kuma a gida babu kowa. Hakan ya taka muhimmiyar rawa. Gaskiya dai Yallaɓai ba zan ɓoye maka ba ta ji jiki.. Se dai muna mata fatan samun lafiya ingantacciya nan ba da jimawa ba." Likitar ta ƙare tana jinjina kai. Fesar da iska Daddy ya yi daga bakinsa kafin ya sauke ajiyar zuciya yace

"Allah Ya amince.. Zan iya ganinta?"

"Ehh babu damuwa Yallaɓai za ka iya ganinta.." ta ba shi amsa tana murmushi.

"Toh godiya nake.. Abin da ta haifa fa?" Daddy ya yi tambayar. Se ta ɗan yi shiru kamar ba za tace komai ba, se kuma ta ɗaga kai ta kalli Daddyn tace

"A yi haƙuri Alhaji.. Amma Allah ya yi masa rasuwa gaskiya tun da daɗewa kafin zuwansu asibiti."

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un..!" Shi ne abin da Daddy ya faɗa har cikin ransa yana jin babu daɗi. Ya ɗan zame hularsa yana shafa kansa a hankali. Duk da yanda ya so ganin ɗan Mommahn da rai da lafiya, yanzu kuma ake faɗa masa ya rasu, hakan be kai yanda ya ji tausayin Mommahn ya kama shi ba.

"Allah Ya sa me ceto ne." Likitar ta faɗa tana kallan Daddy lokacin da ya miƙe.

"Ameen." Ya amsa da hakan yana ficewa daga Office ɗin.

A hankali ya ƙarasa cikin ɗakin yana kallan Mommahn da ke kwance idanunta a rufe tana bacci, kai da ka ganta ka san babu ƙarya ta sha wahala. Dan kuwa hatta a baccin da take za ka iya ganin yanda idanunta suka yi ciki, baccin kuma da ka gani za ka fahimci kawai tana yinsa ne ba dan tana jin daɗinsa ba. Wani sabon tausayinta ya kama shi, ya ƙarasa ya nemi waje ya zauna yana cigaba da kallanta cike da tausayawa. Ya kai wajen minti 5 cikin ɗakin kafin ya tashi ya fita daga ɗakin. Se a lokacin da ya ga gawar yaron ma sannan ya sake tausayawa Mommah. Ya sumbaci goshin yaron a fili ya furta

"Allah Ya bata wani me albarka.. Ya kuma ba ta lafiya.. Kai kuma Allah Ya sa me ceto ne."

.. Tun da ta ga Daddyn cikin ɗakin se ta sake wani narkewa ita a lallai dole dan ya san ta ji jiki fa. Ya kalli yaron da ba a daɗe da dawo da shi ba bayan duba shi da aka yi aka tabbatar lafiyarsa ƙalau.

"Bacci yake yi ne?" Ya ƙare yana kallanta.

"Ehh.. Ai gwara ya huta bawan Allah.. Ya wahalar da kansa ya wahalar da ni.." Ta ƙare tana yaƙe haƙora. Kallan cute fuskar yaron Daddy ya yi kamin yace

"Bawan Allah.. Sannu.. Yaron da Sa'adah ta haifa ya koma." Ya ƙarasa maganar yana kallanta. Kamar da gaske ta ɗaga kai da sauri tana faɗin

"Inna lillahi.. Ita ma ta haihu ne?" Daddy ya jinjina kai yana neman waje ya zauna.

"Wayyo.. Allah sarki.. Allah Ya ji ƙansa, Ya sa me ceto ne."

"Ameen Ya rabbi." Daddy ya faɗa. Cikin zuciyarsa yana mamakin yanda Mom ɗin ta nuna damuwa sosai, duk wannan uban kishin nata. Ko da yake ai magana ake ta mutuwa, ya san dole ta saduda, komai abinka kuma ka tausayawa Mommahn musamman idan ka ga halin da take ciki.

Duk da yanda ta ga yanayin da Daddyn ke ciki hakan be hanata tambayarsa inda wayarta take ba wai za ta kira Aunt Makiyy. Ba tare da yace komai ba ya miƙa mata wayar yana ficewa daga ɗakin. Se da ta tabbatar ya fita sannan ta danno number Maimunan ta kira. Tun da ta soma ringing se ta shiga dube_dube saboda tsaro kar ta je a shigo ba tare da ta lura ba.

"Yawwah Hajiya ga mu tare da Muttaƙa." Maimuna ta faɗa daga can ɓangaren.

"Ba shi wayar.." Mom ta faɗa tana kallan cikin ɗakin da take. Babu musu Maimuna ta miƙa masa wayar.

"Hello.." Ya faɗa da muryarsa da tafi kama da ta en shaye_shaye. Ba tare da Mom ta amsa ba ta soma faɗin

"Ku san yanda za ku yi da wannan jaririn.. Ban iyakance muku abin da za ku masa ba.. ni dai kun gama min nawa aikin idan kuka salwantar da rayuwarsa, ba na son sake ganinsa har ƙarshen rayuwata. Ka tura min Account number ɗinka da zarar kun gama aikin za ka ji ni.."


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO65*

___"An gama Hajjaju." Ya faɗa yana jinjina kai. Ba ta sake cewa komai ba ta katse wayar. Maimuna ta kalli Muttaƙa tace.

"Ya za mu yi yanzun?" Shiru ya yi na tsawon sakanni kamar me nazari, har se da Maimuna tace

"Ko dai kawai mu je mu jefar da shi salin alin tun kafin ya tona mana asiri, dan ka ga fa yanzu ya soma kuka." Ɗaga idanunsa Muttaƙa ya yi ya watsa mata wani kallo da ya fi kama da harara.

"Kee!! Duk fa tantirancina ina tsoron Allah.. Wallahi ba zan iya jefar da wannan ɗan tahalikin ba, wa ya san me ze same shi idan mun watsar da shi.?" Ya ƙare da wannan muryar tasa. Buɗe baki Maimuna ta yi tana kallan Muttaƙa, cike da mamakin furucinsa.

"Amma ka san ba za ka iya ba ka karɓi wannan aikin?" Ta tambaya still dai tana kallansa.

"Ke kin san tun da na karɓa zan yi ne.. Kawai dai abin da kika ce ne ba zan iya ba. Tun da dai ba ta ce ga abin da za a masa ba, toh ni dai yanda na yanke kawai mu kai shi gidan marayu.. Duk abin da ya faru da shi laifinsu ne ba nawa ba.." Ya ƙare yana ɗaga hannayensa sama.

"Gidan marayu kuma? Me kenan?" Maimuna ta tambaya.

"Ke kar ki ɗaga min murya mana. Waye ze san gidan marayu aka kai shi? A rana sau nawa ake kawo yara? Daga zarar mun kai shi fa shi kenan an manta da babinsa."

"Ina jin tsoro gaskiya."

"Ke dallah can.. Tsoro kuma?" Muttaƙa ya faɗa yana harararta.

"Idan kuma garin hakan aka kama mu fa? Ta ya ya zamu fidda kanmu?" Shiru ya yi hannunsa a gefen fuskarsa yana bubbugawa, kafin can yace

"Ɗauko shi mu tafi.." ya yi maganar yana yin gaba. Ba tace komai ba ta ƙarasa ta ɗauki jaririn da zuwa yanzun kuka yake yi. Se ta shiga rarrashinsa saboda ya samu ya yi shiru ko dan kar ya ɗaga musu hankali su kasa abin da suke niyyar aikatawa. A lokacin da suka fita daga gidan magrib ta yi, dan haka kafin su isa inda Muttaƙan ya ja su duhu ya sake yi sosai. Ajiye motar ya yi a can nesa da wani ƙaton gini da ya fi kama da gidan marayu. Hannu ya saka ya karɓi yaron da ke hannun Maimuna yace

"Bari ki ga abin da za a yi.." Be jira tace komai ba ya fice daga cikin motar. Cike da takatsantsan da kuma lura haka ya ƙarasa har ƙofar gidan marayun nan. Ya yi gefe inda ya san ba za a gan shi ba, duk da lokacin ma kowa hankalinsa na kan abin da yake yi ne. Se da ya duba gabas da yamma, kudu da arewa, ya tabbatar babu me kallansa sannan ya ajje jaririn. Ba tare da ya kalli inda ya ajje shi ba da sauri ya koma cikin motar. Babu ɓata lokaci ya figi motar suka bar wajen. Daga nan Maimuna ba ta wuce ko ina ba se asibiti, a nan take sanarwa da Mom an gama da jaririn nan. Ba ta damu da inda suka kai shi ba, dan ta san halin Muttaƙa ba raga masa ze yi ba duk kuwa da jariri ne. Ita dai kawai ta tura masa uban kuɗi cikin account ɗinsa. Aikuwa ya yi ta godiya. Ita kam ji take kamar ta haɗa duk abin da ta mallaka ta bawa Maimuna da Muttaƙa, dan ko babu komai sun sakata cikin farin cikin da har abada ba ta tunanin za ta fita daga cikinsa. A ranar Yaya da Aunt Makiyy suka iso asibitin. Kowacce wajen er uwatta ta nufa. Yaya se da ta yi ƙwalla da ta ga halin da er uwatta ke ciki, da kuma jin labarin abin da ta haifa ma ya koma. Aunt Makiyy kam farin ciki kamar ta yi mene, musamman da ta ga Babyn yayar tata kamar shi ya yi kansa dan kyau. Ta dinga koɗa shi kamar za ta cinye shi. Daga farko kamar Mom ba za ta faɗawa Aunt Makiyy yanda aka yi aka samu jaririn ba, se dai daga baya da ta yi tunanin wace ce Makiyyan, kuma da ma babu ɓoye ɓoye tsakaninsu, se ta sanar mata da abin da ya faru. Sosai mamaki da kuma tsoro suka kamata, waɗanda suka gaza ɓoyuwa a kan fuskarta. Tace a tsorace

"Ba kya tsoron a gano gaskiya?"

"Ki ji banza.. Ta ya ya za a gano? Waye ze gano? Kin ga ki kwantar da hankalinki.. Ka da ma ki sake ki saka wannan abun a ranki.. Ni ce na haifi yaron nan ba wata ba. Dan haka ki ma manta da mun yi maganar nan." Mom ta faɗa tana kallan Aunt Makiyy. Ita dai kam mamaki sun kasa barinta tace wani abun. Se kuma can daga baya sannan tace

"Wallahi Yaya tsoronki ya shige ni.. Haka kika iya shirya makirci ban sani ba?" Jin yanda ta koɗata ne ya sanyata yin murmushi tana wani kallan gefe da gefe tana hura hanci.

"Ki na wasa da ni."


A ranar aka sallami Mom, ya yin da Mommah se da ta yi sati sannan aka sallameta bayan ta sha kuka bayan farkawarta. Se dai daga ƙarshe ta fawwalawa Allah komai ta rungumi ƙaddararta hannu biyu. A ranar da aka sallameta ne ranar ya kama sunan ɗan gidan Mom. Yaron da ya ci sunan Areef. Ba ƙaramin hamshaƙin suna aka gabatar ba a ranar. Sunan ɗan gata. Mom ji take babu ya ita, ta yi shiga kala kala, ana wani babbasarwa, ita a lallai dole me

Please Login or Register in order to submit comment