Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dole ya karta mata warning.

"Kee!!" Ya faɗa fuskar nan ba annuri. Sam ba ma ta ji shi ba ita gaba ɗaya a tsorace take da yanda ta ga jini na cigaba da zubowa daga ƙafarta.

"Keee!" Ya sake maimaitawa a karo na biyu. Se a lokacin ma ta tuna a inda take. Se ta soma ƙoƙarin miƙewa dan ficewa daga ɗakin tun kafin ma ya fahimci abin da ya kawo ta wajen. Ba tare da ta kalle shi ba ta yi nasarar miƙewa a kan ɗayar ƙafar tata, ya yin da take riƙe da ɗayar. Fuskarta gaba ɗaya ta cika da hawaye caɓa caɓa. Cikin kula ta soma takawa dan ficewa daga ɗakin tana yarfe hannayenta a tsorace. Tsaki ya ja yana ɗan cije lips ɗinsa, duk da ya lura da jinin da ke a ƙasa hakan be sanya shi jin tausayinta har ya kai ga taimaka mata ba. Se dai a lokacin da ya ɗaga kai ze yi mata warning ɗin saboda fahimtar da ya yi ta gama ruɗewa se idanunsa suka yi tozali da yanda jinin ya cigaba da zuba a inda duk ta sanya ƙafarta. Iska ya fesar daga bakinsa kamar me tunani, se kuma can ya shiga takawa gaba.

"Kee!!" Ya faɗa yanzun cikin er ɗaga murya da kaurin murya. Ba ta san lokacin da ta tsaya ba tana runtse idanunta, shi kenan ita kam yau tata ta ƙare. Ga wannan uban ciwo da ta ji ga kuma ɓarnan da ta masa.

"Nemi waje ki zauna." Ya faɗa yana tsareta da idanunsa. Ita kanta ma a wani wajen yake dan haka har yanzun ba ta ɗaga ido ba balle ta kalle shi. Se dai kamar yanda yace mata ɗin se ta koma ƙasa kawai ta zube a wajen tana jin wasu hawaye na taho mata. Be sake cewa komai ba se komawa cikin ɗakin da ya yi. Bayan wajen minti 1 ya dawo inda take. Ita ta yi tunanin ma ko wani abun hukuncin ya tafi nemowa dan haka har ta gama saddaƙarwa, ta kuma rabu da zugin da ƙafarta ke yi mata. Ba tare da ya kalleta ba yana zuwa kawai ya sanya tattausan tafin hannunsa ya kama ƙafarta da ke da ciwon. A zabure ta ɗaga kai ta kalli ƙafar jikinta na ɗaukar wani rawa. Se ta soma ƙoƙarin janye ƙafar tata, shi kam ya haɗe face waje ɗaya babu alamun wasa. Babu ɓata lokaci ya shiga naɗe ƙafar da bandage duk da har lokacin Didi ba ta bar ƙoƙarin fuzge ƙafafunta ba. Hannu ta kai da niyyar ƙwace ƙafarta. Ya ɗago idanunsa ya watsa mata wani kallo da ya sanyata saurin janye hannunta lokaci ɗaya tana share hawayen da ke ta reto a kan kuncinta. Be saki ƙafar ba se da ya naɗeta tass sannan ya saketa. Ta sauke wata ƙatuwar ajiyar zuciya tana ƙoƙarin miƙewa, se ganinsa ta yi yana ƙoƙarin haɗe tazarar dake tsakaninsu. Ƙirjinta ya sake bugawa, wani irin tsoro ya ziyarceta. Er tazara kaɗan ya bari a tsakaninsu sannan yace lokacin da ya ɗora gaba ɗaya idanunsa a kan fuskarta.

"Saka idanunki cikin nawa.." Ya yi maganar cikin bayar da umarni. Sam ba ta da niyyar yin hakan, se ma ƙoƙarin tashi da take son yi ta gudu, se dai a yadda ya matso dab da ita idan dai har ba ta ɗaga idanu ta kalle shi ba toh se dai ta kalli gangar jikinsa da har yanzun take a buɗe. Mafita ɗaya ta rage mata shi ne ta saka hannu ta riƙe ƙafar tata me ciwo sosai sannan ta soma ƙoƙarin tashi da sauri. Hannunsa ya saka ya riƙo hannunta da ƙarfi har se da ta runtse idanunta. Ya sake watsa mata wani kallo sannan yace

"Taurin kai koh?" Yanda ya riƙe mata hannun ba ƙaramin zafi ta ji ba. Ta kuma fahimci ba ta da wata mafita illah ta yi abin da ya faɗa ɗin, dan haka se kawai ta ɗaga idanunta ta sanya a kan fuskarsa. Gaba ɗaya idanunsa ya ɗauka ya ɗora a kan tata fuskar. Se ma ya shigar da idanunsa cikin nata dan saƙon da ze faɗa mata ya fi shigarta. Karo na farko kenan da irin wannan kallon ya taɓa haɗa su. Har ta numfashinsu se ya shiga haɗewa da na juna. Ruwan da har yanzu ke jikin gargasar dake ƙirjinsa har sakkowa yake a kan hijab ɗin jikinta. Duk wani sauka da ruwan ze yi ji take kamar da zuciyarta yake sauka, saboda yanda yake sauka tare da bugun zuciyarta. So take ta ɗauke idanun nata amma ya ƙi ba ta ko da ƙaramar dama ce.

"Tsoronki wannan jinin da ke ta zuba koh? Toh yanzu babu shi.. Saboda haka ki buɗe kunnanki da kyau ki ji ni.. Idan kika sake na ji wata magana a kan abin da kika gani, ko a wajen waye.. ko ke ce kika faɗa ko ba ke ba ce ba damuwata ba ce..hukuncin da zan yi a kan ki ne.. Kin ji koh?" Ya yi maganar yana jan kunnensa guda ɗaya. Jinjina kai ta yi dan har ga Allah ta gaji da kallan cikin ƙwayar idanunsa haka nan. Cigaba ya yi da kallanta ba kamar kallan ɗazu ba, haka nan kawai ta fahimci abin da yake nufi, dan haka ta buɗe baki da ƙyar tace

"Ehh.." Da ƙarfi ya sake ta yana miƙewa ya bar wajen. Ta saki ajiyar zuciya har lokacin bugun zuciyarta be saitu ba ta miƙe da ƙyar ta fice daga ɗakin hannunta riƙe da ƙafarta me ciwon.

Ajiyar zuciya ta sake saukewa a karo na barkatai lokacin da ta ganta a cikin ɗakinta. Da ƙyar ta ja ƙafafunta ta nemi waje ta zauna. Duk da yanda ƙafarta ke zugi amma farin cikinta ɗaya da ta fito daga ɗakin. Ta kai wajen minti 10 a haka tana cigaba da kokawa da saita numfashinta kafin ya dawo daidai.



.... "Kin shigo kenan?" Daddy ya faɗa lokacin da yake neman waje ze zauna kan kujera.

"Ehh 'Yallaɓai na dawo."

"Toh Madallah.. ya batun duba lafiyarki kuwa?"

"Yana nan.."

"Amma dai ba ki manta lokacin ba koh? Anya ma kuwa kina lissafi.." Murmushi Mom ta yi tace

"Haba dai Daddyn Areef ta ya ya za a yi na manta? Ina sane fa." Shi ma murmushin Daddy ya yi yana girgiza kai sannan yace

"Yanda na faɗa kuwa haka ne. Domin da ki na sane da lokacin zuwanki da tuni yanzu haka kin fara shirye shirye."

"Haba 'Yallaɓai se ka ce me yin tafiya cikin satin nan?"

"Toh kin gani ba? Cikin satin nan ne tafiyar taki, na ga ba ki fara shiri ba shi ya sa na tambaya." Cike da mamaki tace

"Wannan satin kuma? Ya aka yi na ɓace a lissafi.."

"Tsufa mana.." Ya ba ta amsa cikin barkwanci. Yaƙe kawai ta yi dan ita tuni hankalinta ya tafi wani wajen. Se ta miƙe a sanyaye tace

"Bari na je toh 'Yallaɓai. Godiya da tunasarwa." Ba ta jira amsarsa ba ta fice daga cikin ɗakin. Binta ya yi da kallo yana mamakin yanda yanayinta ya chanja kamar ba maganar neman lafiyarta ake yi ba. Ya girgiza kai kawai.


Tun kafin ta ƙarasa cikin ɗakinta ta soma kiran number ƙanwarta Makiyya. Babu daɗewa kuwa ta ɗaga.

"Hajiya Yaya ikon Allah.. kafin Allah ba na mutum ba."

"Kin ga riƙe kirarinki na san dalilinki na hakan."

"Haka za mu yi da ke?" Aunt Makiyy ta faɗa.

"Kin ga ba wannan ba.. Ashe wai cikin satin nan ne zan koma ganin likita.."

"Toh fa! Har lokacin ya yi?"

"Wallahi kuwa.. yanzun nan Daddyn Areef ke tuna min." Mom ta bata amsa.

"Toh yanzu me ye abin yi?" Aunt Makiyy ta tambaya. Shiru Mom ta yi na en wasu mintuna kafin ta sauke ajiyar zuciya tace

"So nake na kora yarinyar nan gida kafin na bar ƙasar nan. Dan matuƙar ban yi hakan ba hankalina ba ze taɓa kwanciya ba."

"Ehh toh da gaskiyarki Yaya.. se dai ni a ganina ba haka ya kamata ki yi ba. Me ze hana shi kansa Areef ɗin ki tura shi wata ƙasar ya yi adadin kwanakin da za ki yi a can? Idan ya so se ku dawo tare. Kin ga ku na dawowa se a san abin da za a yi dan zuwa lokacin ni ma na dawo." Shiru Mom ta yi na en wasu sakanni. Se kuma can ta shiga jinjina kai cike da gamsuwa da abin da Aunt Makiyyn ta faɗa.

"Hakan ya yi. Zan jarraba na gani. Duk yanda ake ciki zan kira ki ki ji.." Murmushi Aunt Makiyy ta yi tace

"Yawwah.. Allah ya taimaka.."

"Ameen." Mom ta amsa da hakan sannan suka yi sallama.



... Ƙarasawa Baba Atine ta yi cikin ɗakin hango Didi da ta yi zaune a kan gado riƙe da ƙafarta da ke nannaɗe da bandage tana kalla.

"Subhanallahi me ya same ki Afrah?" Ta yi maganar lokacin da ta isa inda Didin take. Da sauri ta sauke ƙafarta dan ko jin shigowar Baba Atinen ba ta yi ba.

"Me ya same ki 'yata?" Baba Atine ta sake faɗa a karo na biyu. Idanunta da suka yi rau rau ta ɗan lumshe kafin ta buɗe, ba dan ta so ba tace

"Bigewa na yi.."

"Bigewa kuma? A ina?" Baba Atine ta faɗa cike da kulawa, dan har ga Allah ta tsorata da ganin bandage ɗin a ƙafar Didin. Shiru Didin ta yi tana tunanin me za tace wa Baba Atinen, dan ba ta so ta faɗa mata a inda ta taka saboda tuna gargaɗin da Bad Man ya mata. Gefe guda kuma ba ta so ta yi ƙarya. Kafin ta gama tsara abin da za ta faɗa ɗin Baba Atine ta miƙe ta fice daga ɗakin. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya Didi ta sauke ganin Baba Atinen ta fita daga ɗakin. Ko babu komai kafin su sake haɗuwa ta san me za ta ce mata. Lumshe idanunta ta yi tana jinginar da bayanta a jikin gadon da take kai har lokacin hannunta na kan ƙafarta da take ji tana mata zugi.

Tana nan zaune bayan wajen minti 10 har baccin wahala ya fara ɗaukarta ta ji an turo ƙofar ɗakin. Da yake baccin be yi nisa ba ya sa ta buɗe manyan brown eyes ɗinta da suka ɗan yi ja saboda baccin da ya fara ɗaukarta. Baba Atine na baya yayin da Mommah ke gaba kamar kodayaushe sanye cikin hamshaƙiyar shiga da kodayaushe take matuƙar karɓar madaidaicin jikinta. Da sallama suka shiga ɗakin kamar yanda Mommah ke gaba, yanzun ma ita ce ta fara isa inda Didin take. Ganin Mommahn da ta yi ba tare da ta tsammata ba ya sanyata miƙewa zaune da sauri ta zauna a kan gadon. Gefen gadon Mommah ta samu ta zauna cikin kulawa tace

"Daughter me ya same ki?" Ta yi maganar tana sanya hannunta ta ɗago ƙafar da idanunta suka sauka a kai.

"Ya salaam garin yaya haka ta faru? Me ya samu ƙafarki?" Mommah ta faɗa yanayin fuskarta na nuna yanda tashin hankalin da ta shiga lokacin da ta yi tozali da ƙafar Didin. Lumshe idanunta Didi ta yi tana jin lokacin faɗin gaskiyar ya yi, dan Mommahn ta fi ƙarfin ta yi mata ƙarya. Dan haka cikin sanyi tace

"Kwalba na taka.."

"Subhanallahi kwalba kuma?" Mommah ta faɗa tana kallan Didin cike da mamaki. Jinjina kai ta yi kafin tace komai Mommahn ta sake faɗin

"A ina kika taka? Kwalbar me ye ne?" Ta tambaya cikin tsare Didin da idanunta. A yanzu kam ba ta ji za ta iya faɗa mata kwalbar giyar Bad Man ta taka cikin ɗakinsa. Komai lalacewarsa komai kuma rashin kirkinsa a gareta mijinta ne, idan ya zamana ta faɗa gaskiyar abin da ta taka hakan na nufin ta tona masa asiri kenan? Bayan ta san illar hakan.

"Kwalbar turare ce.." Ba tare da ta kammala harhaɗa zancen ba ta yi ƙarfin halin faɗa.

"Ya ilahy.. shi ne ba ki faɗa min ba Daughter? Kin kyauta kenan? Wannan bandage ɗin kuma a ina kika samo shi?" Dukka Mommah ta haɗa tambayar ta yi ta lokaci ɗaya. Ba ta san lokacin da murmushi ya ƙwace mata ba duk da jin jerin gwanon tambayoyin da Mommahn ta jero mata. A kullum a kodayaushe mutuncin Mommahn ƙaruwa yake yi a wajenta, ƙaunarta kuma daɗuwa take yi a cikin ranta.

"Ki yi haƙuri Mommah.." Ta faɗa a sanyaye.

"Naa ji.. shi ne kuma har da ɗaura bandage a ƙafarki. Wato ba dan Atine ta gani ba da shi kenan se dai ki yi shiru ba tare da sanin illar hakan ba? Kwalba fa kika taka Daughter."

"Ki yi haƙuri Mommah.. ba ni na saka bandage ɗin ba.. shi ne ya saka min." Ta faɗa lokacin da muryarta ta raunana saboda fahimtar da ta yi Mommahn ba ta ji daɗin ɓoye matan da ta yi ba.

"Waye?" Mommah ta tambaya dan kwata kwata ba ta kawo Bad Man ba saboda sanin hali. Rasa sunan da za ta faɗa ta yi, se ta shiga kame kame kawai.

"Wai Areef kike nufi?" Baba Atine ta faɗa lokacin da ta ƙaraso kusa da su. Se ta jinjina kai kafin a hankali ta buɗe bakinta da ƙyar tace

"Ehh.." Wani ƙayataccen murmushi Mommah ta yi tana jin wani irin sanyi har cikin ranta.

"Ma Sha Allah, Alhamdulillah.. Allah ya ƙara ƙara haɗa kan ku." Baba Atine ta faɗa.

"Ameen Ameen.." Mommah ta faɗa da murmushi a kan fuskarta.

"Toh Alhamdulillah.. Amma duk da haka tashi mu je asibiti.."

"Mommah ba.."

"Tashi na ce.." Mommah ta katse Didi da faɗin haka. Ba ta sake cewa komai ba se miƙewar da ta yi da ƙyar, dan ta kasa taka ƙafarta. Cike da tausayawa Mommah ke binta da kallo a ranta tana sake addu'ar Allah ya daidaita tsakanin Didin da Areef.

Da taimakon Baba Atine suka fita daga ɗakin tana riƙe da Didi. dauriya kawai take yi dan ita kaɗai ta san yanda take ji a ƙafar tata.

"Ki koma ki kula da gidan kafin mu dawo" Mommah ta faɗa tana kallan Atine

"Toh Hajiya se kun dawo, Allah ya tsare."

"Ameen.." Mommah ta faɗa sannan ta juya dan zuwa sashen Daddy. Dakatawa ta yi tana kallan lokacin da Daddyn yake ƙarasowa inda take masu tsaron lafiyarsa na bayansa. Daga nesa suka tsaya lokacin da ya kusa isowa inda Mommah take. Se ta saki nurmushi me ƙayatarwa lokacin da ya iso inda take.

"Barka da wannan lokaci Rankayadaɗe.."

"Barka dai Rankiyadaɗe"

"Wajenka nake son zuwa se kuma ga ka a nan."

"Ehh zan ɗan fita ne."

"Toh madallah.. Allah Ya taimaka, Ya kuma tsare." Ta yi maganar cikin kulawa.

"Ameen.. akwai wani abun ne?"

"Ehh Afrah ce ta taaka kwalba shi ne zan kaita asibiti a duba ta."

"Subhanallahi.. kwalba kuma?"

"Wallahi kuwa Rankayadaɗe."

"Tana ina?" Daddy ya tambaya. Nuna motar da Didi ke ciki Mommah ta yi tace

"Tana ciki.."

"Mu je na ganta." Daddy ya faɗa lokacin da ya soma takawa zuwa wajen motar. Babu musu Mommah ta bi bayansa har zuwa wajen motar. Cikin kulawa ya dube ta yace

"Sannu koh Daughter?" Bata lura da tahowarsu ba se maganarsa da ta ji. Aikuwa tana ganinsa se ta soma ƙoƙarin buɗe motar dan fitowa daga ciki.

"A'ah yi zamanki ba se kin fito ba.. ya ƙafar taki?"

"Da sauƙi Daddy.. Barka da wannan lokaci.." ta yi maganar lokaci ɗaya.

"Barka dai.. Allah ya ƙara sauƙi." Daddy ya amsa da hakan. Daga haka ya matsa inda Mommah take yace

"Shi Areef ɗin baya nan ne?" Girgiza kai Mommah ta yi tace

"A'ah ban sani ba dai ko yana ciki.." Daddy be ce komai ba se ɗauko wayarsa da ya yi ya kira number Bad Man. Yana tsaye bakin mirror yana feshe jikinsa da turaren nan nasa me daɗin ƙamshi ya ga kiran Daddyn. Be kawo komai ba ya ɗaga wayar. Bayan sun gaisa Daddy yace

"Ka na cikin gida ne?"

"Ehh.."

"Ina parking space ina jiranka.."

"Ohk.." ya amsa da hakan yana ajje wayar. Ƙarasa shiryawa ya yi sannan ya fito daga ɗakin. Kai tsaye can ɗin ya nufa. Tun kafin ya ƙarasa ya hangi Daddy da Mommah a tsaye. Da farko be kawo komai ba, se kuma daga baya zuciyarsa ta soma raya masa ko dai yarinyar nan ta je ta faɗa musu abin da ta gani a ɗakinsa? Anya kuwa hakan ze faru bayan duk gargaɗin da ya mata? Ƙwafa ya ja yana ɗan cijar leɓensa gami da lumshe sexy eyes ɗinsa kafin ya buɗe su lokaci guda. Duk da abin da zuciyarsa ke raya masa hakan be hana shi sakarwa Mommah da ya fara tozali da fuskarta murmushi ba. Ita ma maida masa ta yi tana faɗin

"Areef.."

"Yes Mommah.. Good evening.."

"Ka na lafiya?" Ta faɗa har lokacin da murmushi a kan fuskarta. Jinjina kai kawai ya yi yana maida dubansa kan Daddy yace

"Daddy.."

"Areef.." Daddy ya faɗa yana kallansa. Ɗaga idanunsa ya yi ya kalli Daddyn dan jin abin da ze faɗa. Se kuwa Daddy ya soma faɗin

"Yanzu ku na gida ɗaya, sashe ɗaya amma a ce matarka ta taka kwalba ba ka sani ba?"

"Kwalba?" Ya maimaita kamar yanzu ya taɓa jin sunan.

"Ta tabbata ba ka sani ɗin ba kenan?" In ji Daddy. Ɗan yin shiru ya yi kamar yace ehh be sani ba, se kuma ya ga rashin dacewar hakan, musamman yanda ya san ran Daddyn ze sake ɓaci ne idan ya ji haka. Hakan ne ya sanya shi faɗin.

"No Dad.. na sani."

"Yah Allah!!" Daddy ya faɗa yana ɗan fesar da iska daga bakinsa kafin ya ɗora da

"Shin ba ka san illar kwalba ba ne ko kuwa rashin kirki ne irin naka da ya hana ka ɗaukarta ka kai ta asibiti a duba ta?" Shiru kawai ya yi dan ba shi da amsar bayarwa.

"Toh ga ta nan cikin mota ka shiga ka kaita a duba mata ƙafa. Wai Areef ba ka tunanin Allah ya kama ka a kan haƙƙin yarinyar nan ne?" Daddy ya faɗa cike da mamakin taurin kai irin na Areef ɗin.

"But Dad akwai.."

"Ban son jin komai idan ba toh ba." Daddy ya katse shi ta hanyar faɗin hakan da kuma amfani da hannunsa wajen dakatar da shi.

Mommah ji take kamar ta cewa Daddyn ya bar Areef ɗin ita za ta kai Didin asibiti. Se dai ta yi shiru ta bar shi. Ta san halin Areef ɗin dama ba me iyawa da shi se Daddyn. Duk taurin kansa idan aka ce Daddy ne ya yi magana toh fa ko ba ya so ze yi shi. Shiru na en wasu sakanni kamar ba ze tanka ba se kuma can ciki ya furta

"Ohk.." fuskar nan ba yabo babu fallasa. Key ɗin motar Mommah ta miƙa masa, be ce komai ba ya karɓa ya wuce zuwa inda motar take. Kai tsaye ya shiga cikin motar ba tare da ya kalli ko da inda take zaune ba ne. Gaba ɗaya ta ɗauka da Mommah za su je asibitin, se dai ganin mutum cikin motar ya sanya ta tunanin ko Mommahn ta fasa ne shi ya sa ta aiko wani ya kaita asibitin. Se dai me? Tun kafin ya tayar da motar wannan mayen turaren nasa me shegen ƙamshi ya ziyarci cikin hancinta. Ƙamshin nan me daɗi da ke sanya wanda ya shaƙe shi lumshe idanu. Hakan ce ta faru da Didi, dan kuwa ba ta san lokacin da ta lumshe idanunta ba lokaci guda kuma tana jin bugun zuciyarta ya ƙaru. Har ga Allah tsoronsa take ji, musamman idan ta tuna shi ɗazun nan lokacin da yake shata mata uban gargaɗi. Se ta kame kanta gefe ɗaya tana Allah Allah su isa asibitin ya sauke ta ya juya. Sosai yake gudu kamae wanda ze tashi sama a kan titin. Har suka isa cikin asibitin be ce komai ba. Sauka ya yi daga motar ba tare da yace da ita komai ba. Ta sauke ajiyar zuciya tana saka hannu ta buɗe murfin ƙofar. Sam ta ma manta da ciwon ƙafarta saboda yanda ta tsorata da irin gudun da yake yi. Se da ta saukar da gaba ki ɗaya ƙafafun nata ƙasa ta ji wani azabtar zafi sannan ta tuna, ta ɗage ƙafar da sauri tana faɗin

"Ahhh.." Ya juya ya maka mata wani kallo sannan ya soma takawa. Bin bayansa ta yi a hankali a hankali cike da lura take tafiyar tana ɗan runtse idanunta saboda zafi. A haka har suka isa cikin ainahin asibitin inda za su ga likita.


.. "'Yallaɓai za ka iya shigowa ai." Shi ne abin da wata nurse ta faɗa tana kallan Bad Man, dan sarai ta gane fuskar shi, barinsa kuma a waje tamkar rashin daraja ne. Siririn tsaki ya ja lokacin da ya fahimci zaman be ƙare ba. Kamar yace a'ah se kuma kawai ya shiga cikin ɗakin. Tana zaune a kan wani gado tana kallan ƙafarta da aka sabuntawa bandage. Ba tare da ya kalleta ba ya nemi waje ya zauna yana cigaba da danna wayarsa. Murmushi nurse ɗin ta sakarwa Didi lokacin da ta ƙarasa inda take tace

"Bismillah Madam.." Tsilli_tsilli da idanu Didi ta yi tana kallan nurse ɗin dan sake fahimtar abin da take nufi. Se ta ga tana haɗa allura. Kafin daga bisani ta sake kallanta tace

"Allura zan miki. Kar ki ji komai ba ni da zafin hannu.. ki cire hijab ɗin" Girgiza kai Didi ta yi, ta buɗe baki tace

"Don Allah kar ki min wallahi na dena jin zafi.." ta faɗa cikin sanyin muryarta.

"Haba Madam kar ki ba ni kunya mana.. babu fa zafi.."

"Eh ai na sani.. ni dai Allah kuwa ba na so.." ta sake faɗa tana girgiza kai. Maida dubanta Nurse ɗin ta yi kan Bad Man da har lokacin be kalle su ba tace

"'Yallaɓai ko za ka taimaka mini.. Madam tsoro take ji, ta manta akwai haihuwa a gabanta." Ta yi maganar cikin iyayi tana murmushi. Kallanta ya yi yana jin yanda ta soma ba shi haushi da maganganunta. Yau ɗin kawai ba ya son hayaniya ne shi ya sa be ce mata komai ba. Se kallan Didi da ya yi wadda ta yi tsilli tsilli da ido kamar shege a rabon a gado. Agogon wayarsa ya kalla ya ga yawan mintunan da suka kwasa cikin asibitin, ya sake jan ƙaramin tsaki yana miƙewa ya soma takawa zuwa cikin ɗakin.

"Yawwah.. toh godiya nake.." Nurse ɗin ta faɗa tana murmushi. Da niyyar yi mata magana ya yi a kausashe dan ta nutsu a yi mata. Se dai kuma ya tuna a inda suke, yanda ya ga tun da suka zo wannan Nurse ɗin ke masa ya sa ya fahimci sun san waye shi. Ya kuma san duk abin da ze yi idanunta na kansa ne. Hakan ne ya sanya shi ƙarasawa dab da Didi ya saka hannunsa ya kamo hannunta a nutse. Da sauri ta ɗaga kai ta kalle shi, se ya sakar mata wani murmushi wanda ba ta taɓa ganinsa a kan fuskarsa ba.

"Tsoron me kuma kike ji bayan ga ni?" Ya yi maganar a hankali kamar wanda ba ya so a ji me ya faɗa. I zuwa lokacin kam Didi se ta kaasa ɗauke idanunta daga kansa. A ranta tana tunanin ko dai ya manta wace ce ita? Ko kuwa dai Nurse ɗin yake so ya faɗawa hakan ya manta yake faɗa mata? Tana shirin ƙwace hannunta ta ji ya sake matsowa kusa da ita ya sanya hannayensa duka biyun ya ɗagota daga zaunen da take ya miƙar da ita tsaye. Share yanda take ta ƙoƙarin ƙwace jikinta ya yi ya saka hannu ya ɗage hijab ɗin zuwa kan wuyanta. Jin da ya yi da gasken ƙwace jikinta za ta yi ya sanya shi yi mata masauki cikin jikinsa, ya kuma riƙeta gam ransa na ɓaci. Se dai ya yi ƙoƙarin haɗiyewa kawai. Ƙasa ya yi da kansa se da ya tabbatar ya kai bakinsa saitin kunnenta sannan yace

"Ki nutsu ko na saɓa miki.." Ya ƙare yana murmushi a fili.
I zuwa lokacin kam Nurse ɗin ba ta sake cewa komai ba dan ita ta ɗauka wani abun soyayyar ya faɗa mata. Se ta ɗauke kai tana ƙarasa haɗa allurar jikinta a matuƙar sanyaye. Tana daga jikinsa ita kuma Nurse ɗin ta ƙaraso ta yi mata allurar har lokacin ba ta sake cewa komai ba. Ƙanƙame shi ta yi ba tare da ta sani ba lokacin da ta ji shigar tsinin allurar cikin jikinta. Kamar gaske ya zagayo da hannunsa ta bayanta yana faɗin

"Oh sorry babe.." Ya yi maganar irin kamar cikin tausayawar nan..



MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO46*

___Cikin sakannin da ba su wuce 60 ba Nurse ɗin ta

Please Login or Register in order to submit comment