Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba shi amsa ita ma ba tare da ta kalle shi ba, saboda yanda ta ga yau ɗin yana ta wani mammazewa, yana ƙin kallanta idan ze yi magana kamar ba shi ba. Ita dariya ma yake bata. Se dai kawai ta riƙe abarta. Be sake cewa komai ba ya fice daga gidan.


... Ƙarasowa Baba Atine ta yi cikin ɗakin hannunta ɗauke da waya. Ta zauna a kan wani ƙaramin tuntu dake ƙasan gadon tace

"Barka da wannan lokaci Rankiyadaɗe.."

"Kai Baba.. na ce miki ba na so." Didi ta faɗa tana tura baki.

"To ya za a yi.. Se dai ki yi haƙuri 'yata.. ko ban faɗa ba wani lokacin ki bar ni na faɗa wani lokacin ko dan kar na dinga manta matsayinki.." Ita dai sam Didi ba ta san irin wannan zancen. Dan haka dan ta kawar da zancen ya sanyata faɗin

"Ina Mommah?"

"Kin ga ma yanzu ita ce ta aiko ni.. Tace ki kira Ummanki ku gaisa." Wani irin farin ciki ne ya ziyarci Didi jin abin da Baba Atinen ta faɗa. Cikin farin cikin da ya bayyana har cikin muryarta tace

"Toh Baba.." Miƙa mata wayar Baba Atine ta yi tana jin daɗin yanda ta ga tana murmushi. Dan babu ƙarya tana so ta ga Didin ta yi farin ciki ta sanadiyyarta. Karɓar wayar ta yi ta loda number Ammi. Cikin ƙanƙanin lokaci se ga number ta fito an yi saving nata da 'Ammin Afrah' Babu ɓata lokaci ta kira number tana karawa a kunnenta. Cike da kewar juna kamar ko yaushe suka shiga gaisawa bayan Ammi ta ɗaga wayar. Kamar ko yaushe se suka shiga hirar yaushe gamo. Cikin haka ne Didi tace

"Ammi makaranta fa?" ta faɗa a sanyaye dan tabbas tana kewar makarantar. Dan za ta iya cewa bayan kewar er uwatta ɗan uwanta da kuma iyayenta kewar makarantar ce za ta biyo baya.

"Ki kwantar da hankalinki.. yanzu kam dai babu zancen makaranta Didi.. Zuwa gaba dai idan Allah ya yi za ku cigaba se ki ga da kansu su mazajen naku sun sama muku makarantar kun cigaba." A sanyaye tace

"To Ammi.."

"Ina Little..?" Didi ta tambaya cike da kewarsa.

"Sun fita da Abbanku. Ina so ma a kawo shi wajenki ya ganki kafin mu je ganin Gwaggo.."

"Kai Ammi barin garin za ki yi?"

"Ki ji min ja'ira.. Aou kar na je ganin Gwaggon?" Tura baki Didi ta yi tace

"A'ah Ammi.. Amma don Allah kar ki tafi da Little.. A kawo min shi nan ya kwana har zuwa lokacin da za ki dawo. Don Allah Ammi kar ki ce a'ah.." Shiru Ammi ta yi bayan ta gama jin abin da Didin ta faɗa. Tabbas ta san daga Didin har Little sun yi kewar junansu. Dan kuwa tun bikin ba su sake ganin junansu ba. Ga shi kuma ya je wajen Lulu ya kwana, ko babu komai ita ma idan ya je wajenta ya kwana za ta ji daɗi. Dan haka Ammi ta amsa da

"Shi kenan.. In Sha Allah ze zo.."


MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO54*

Not edited..

___ Lokacin da ya shigo cikin gidan Ummeey ba ta tsakar gidan, dan haka kai tsaye kawai se ya wuce ɗakin nasa. A hankali ya kalli kan gadon cike da fatan ganin fuskarta. Se dai kamar ɗazun yanzun ma har kanta a lulluɓe yake se dai baccin take yi. Sauke ajiyar zuciya ya yi lokacin da yake ajje ledar hannunsa a kan side drawer. Ficewa ya yi daga ɗakin dan ya ƙara mata lokaci ya barta ta yi baccin sosai. Ba shi ya dawo ba se bayan wajen awa 2 duk da lokaci zuwa lokaci ya kan dawo ya duba ya ganta sannan ya koma. Dan duk da be fita gaba ɗaya ba kuma ya san idan ta tashin ba lallai kirki ya haɗa su ba, ji yake kamar idan ya tafi ya ƙyaleta be yi mata adalci ba.

Daidai lokacin da ya shigo ya yi daidai da lokacin da take ƙoƙarin komawa baccin da ta tashi daga shi. Da sauri ya ƙarasa inda take a hankali kuma a tausashe yace

"Kar ki kwanta.. ki tashi ki samu ki ci wani abun.." Shiru ta yi tana cigaba da ƙoƙarin kwantawar. Hannu ya saka da niyyar riƙota, ta kuwa tattaro duk wani kuzarinta ta buɗe baki tace

"A'ah...!!! Ba na ci.." ta faɗa da ɗan ƙarfi.

"Ya Allah!.." ya faɗa hannunsa dafe da goshinsa. Sam ba ya son ta sake takurawa kanta. Ba ya son ya sake jawa kansa sabon haushinsa da take ji. Se dai koma mene tana buƙatar taimako, amma kuma ya ga duk da haka ba ta so. Duk da yanayinta kaɗai ya isa ya nuna halin da take ciki. Ya sauke ajiyar zuciya yana duba agogon wayarsa. Lokaci ya ja babu laifi, har kuma zuwa lokacin ba ta saka komai a bakinta ba. Shi wallahi tausayi ma take ba shi. Shi ya sa ma yake cigaba da lallaɓata, dan kome za ta yi ba kowa ne ya ka fa face shi. Ya kuma san ya riga ya tarowa kansa match. Ba tare da ya sake cewa komai ba ya fice daga ɗakin. Ita kuma tana kwance cikin ɗakin duk da ta gaji da kwanciyar saboda ba ma ta daɗe da farkawa ba. Kawai dai ta fi jin daɗin kwanciyar ne shi ya sa ta kwanta. Sam ba ta yi tsammani ba se jin sallamar Ummeey ta yi cikin ɗakin. Kalar kunyar da ta ji ɗazun ta sake yi mata dirar mikiya. Wai ita kam da wane ido za ta cigaba da kallan Ummeey ne bayan fahimtar abin da ya faru?

"Afaaf.." Ummeey ta kira sunanta a hankali. Yanzu kam babu musu ta miƙe zaune tana amsa kiran da

"Na'am.." Se dai sam ta ƙi kallan Ummeeyn.

"Gyara zamanki ki ci abinci kin ji 'yata? Ai ba kya zauna babu abinci ba.. Ban da galabaita babu abin da za ki yi.." jinjina kai kawai ta yi dan ta kasa buɗe baki ta yi magana, ta kuma kasa yi wa Ummeeyn musu. Mamakinta ɗaya kuma yanda rashin kunyar Gwanin ta kai haka.. Wato shi ko a jikinsa dan Ummeey ta sani. Har da wani zuwa ya kirata dan ta ƙi cin abinci, ko ina ruwansa? Se ta kai hannu ta share idanunta da ƙwalla ta taru. Daidai lokacin da Ummeey ta miƙa mata abinci cikin plate tace

"Ki samu ki ci ko yaya ne Uhmm?" Babu yanda ta iya dan ko doguwar magana ma ba ta so ta haɗata da Ummeeyn. Haka ta ja plate ɗin ta shiga tsakurar abincin da take jinsa tamkar magani take taunawa. Cigaba ta yi da turawa kawai ko da za ta dawo da shi. Da dai ta ga da gasken idan ba ta yi wasa ba za ta iya dawo da shi ta kuma san ba ƙaramin galabaita za ta yi ba ya sanyata ɗaukar ruwan da Ummeyn ta ajje mata ta kafa kanta, se da ta shanye shi tass sannan ta ajje tana ajje numfashi a gurguje.

"Da kin ƙara ko kaɗan ne ai.." Ummeey ta faɗa tana kallanta. A karon farko ta buɗe baki da ƙyar tana sauke numfashi tace

"Ummeey Allah ya ishe ni.." ta ƙare fuskarta kamar za ta yi kuka.

"Toh shi kenan.. Anjima se ki ƙara.."

"Tohm." Ta amsa da hakan tun kafin Ummeey ta dire maganarta. Se a lokacin sannan Ummeey ta fita daga ɗakin. Ya yin da ita kuma ta jinginar da kanta jikin gadon tana sauke numfashi a kai a kai.



.. Ba tare da ya kalleta ba ya shiga shimfiɗa bargon da ya shigo da shi. Ai ba ta san lokacin da ta miƙe zaune dandagarya ba. Nufinsa cikin ɗakin ze kwana? Bayan tana ciki? Ai ko karen hauka ne ya cijeta ba za ta kwana cikin ɗakin da yake ba. Haka kurum? Zamowa ta ƙarasa yi daga kan gadon hannunta dafe da kan gadon ta soma takawa dan ficewa daga ɗakin. Ita ta gwammace ta kwana ko ma a ina ne da dai ta kwana ɗaki ɗaya da shi.

"Ina za ki je?" Ta ɗauke kai duk da yanda zuciyarta ke harbawa dan kuwa yanzun wani shahararren tsoronsa take ji.

"Ni ka matsa min na fita.. Ba zan kwana a nan ɗakin ba.. Allah ba zan kwana ba.." ta ƙare ba tare da ta kalle shi ba. Hawayen kuma da yanzun kamar arharsu take ji har sun wanke mata fuska saboda yanda ta ga ya kare mata hanya kamar ma ba ze barta ta wuce ba.

"Ohh shi kam yau ya ga ta kansa.. wannan yarinya wannan yarinya.." ya raya hakan a cikin ransa. A fili kuma se cewa ya yi

"Shi kenan.. Ni ne koh? Maza ke ki yi kwanciyarki fita zan yi ma daga ɗakin gaba ɗaya kin gani..?" Ya yi maganar yana ɗaukar pillow da bargo. Be jira ta amsa masa ba ya juyo gareta a hankali duk da ta ƙi kallansa yace

"Ki kula da kan ki... idan ba ki ki daɗin jikin naki ba ki sake shiga cikin ruwan zafi.." Ya faɗi kamar yanda ya ga Ummeey ta mata ɗazun. Daga haka ya fice daga ɗakin da sauri. Kawai se ta fashe da sabon kuka fahimtar abin da yake nufi. Ai shi kenan ita kam tata ta ƙare. Duniya ta juya mata baya. Ajiyar zuciya ta cigaba da saukewa lokacin da ta koma kan gadon ta kwanta. Duk da har lokacin jikinta be gama komawa daidai ba amma tun da ya yi magana ba za ta yi komai ba. Se kawai ta ja blanket ta lulluɓe jikinta da shi ta kwantar da kanta a kan pillow tana kallan waje ɗaya cike da tausayin kanta da ya rufeta. Gefe ɗaya kuma haushin Gwani wanda ba ta taɓa jin irinsa ba.


... Knocking ɗin ƙofar da ya ji an yi ne ya sanya shi ɗaga kai ya kalli ƙofar. Da ma daidai lokacin yake da niyyar fita couz ya duba agogon wayarsa ya kai sau nawa amma shiru ba ta kawo Coffee kamar yanda ta saba kawowa ba. Ya ɗauka ma ko ta sake aro taurin kai ne ta sena yi, se kuma ya ji knocking ɗin. K
Ɗan tsayawa ya yi yana kallan ƙofar dan kuwa ya saba idan ta yi knocking ɗin ta ji shiru hakan na nufin ta shiga ne se dai kuma yau be ga ta shigo ba.

"Ko ba ita ba ce?" Zuciyarsa ta raya masa hakan. Se ya sauke ajiyar zuciya kawai yana soma takawa zuwa wajen ƙofar. Daidai lokacin da ta yi maza ta ajje Coffee ɗin ta bar wajen a million. Tsayawa ya yi yana kallan Coffeen dake ajjiye kamar yanda ta fara yi a farko kafin ya taka mata birki. Ba ƙaramin mamaki ya yi ba. Wato hakan na nufin ta yi fatali da unarninsa kenan? Me take taƙama da shi da har ze ce ga abin da za ta yi ta yi wanda ta ga ya fi mata? Ƙwafa ya ja yana cije laɓɓansa har lokacin kuma idanunsa na kan Coffee ɗin. Ba dan ya riga ya saba da ɗanɗanon Coffee ɗin nata ba da ko kula shi ba ze yi ba. Se dai ya kasa hakan, dan haka ya sanya hannunsa ya ɗauka se dai a fuskarsa a haɗe kamar wanda akawa dole ya sha. Komawa cikin ɗakin ya yi ya nemi waje ya zauna. A nutse ya shiga shan Coffee ɗin gaba ɗaya idanunsa a kan ƙofa kamar me neman wani abu. Be san me ya sa abin da ta yi ɗin ya ɓata masa rai ba. Se dai ya alaƙanta hakan da rainashin da ta nuna ta yi bayan ita ɗin ba kowa ba ce. Se da ya shanye tsaff sannan ya tashi ya fice daga ɗakin.


... "Sauri kake yi ne?" Daddy ya faɗa yana kallan Bad Man. Se ya girgiza kai lokaci ɗaya yana amsawa da

"No Dad.. Kamar ka na wani aiki ne?" Girgiza kai Daddy ya yi yana amsawa da

"A'ah zauna.." Babu musu Bad Man ya zauna yana shirin harɗe ƙafarsa ɗaya kan ɗaya Daddy sa ya lura da hakan, ya watsa masa wani kallo, babu shiri ya sauke ƙafar yana ɗan shafa sumar kansa. Daddy ya girgiza kai yana sauke ajiyar zuciya.

"Shirye shiryen me kake yi ne?" Daddy ya katse shi da faɗin hakan.

"Ina so na ɗan je na huta ne ko da na 3 weeks ne.."

"3 weeks for what? Kawai saboda hutu ka tafi wata ƙasar bayan ka na da abubuwa da yawa da ya kamata a ce ka yi? Ko ka manta yanzu ku na da abin yi ne kai da Kaseem? Ko so kake ka bar shi shi ɗaya ya din ga yi komai? Ko kuwa wani hutu ka shiryawa kanka da matarka?" Daddy ya tambaya yana kafe shi da idanunsa. Shi ma kallan Daddyn yake yi kamar wanda ya ga sabon halitta. Se kawai ya yi wani yaƙe jin abin da Daddyn ya faɗa. Wai hutu? Shi da matarsa? Wace matarsa kuma? Ko Daddyn ya manta kawai tana zaune da su ne ba a matsayin matarsa ba?

"Daddy.. Ba wannan gaskiya a tsarina.. Ni kaɗai nake son zuwa, ba na buƙatar kowa.."

"Har matar taka Areef?" Daddy ya faɗa a sukwane. Sauke numfashi ya yi kafin yace

"Daddyyy.." ya ja ƙarshen sunan kamar me shirin faɗar abu me amfani.

"Ka ga Areef idan har za ka ɗauki matarka ne ku je wata ƙasar ina maraba da hakan. Dan na ze taɓa yiwuwa ka tafi wata ƙasar ka bar er mutane a cikin gidan nan ba. Idan kuwa har wannan ne kawai dalilinka toh ban amince ba. Se dai kuma idan har za ka tafi ne ba tare da izinina ba tun da yanzu ka girma." Shiru Bad Man ya yi ba tare da yace komai ba. Duk ya fahimci Daddyn ba ya son zuwa ko ina ne shi ɗaya. Shi ya sa yake ta kawo waɗannan ƙorafe ƙorafen. Shi kuma sa ya tafi da ita gwara gaba ɗaya ya haƙura da zuwa ko ma ina ne. Musamman ma kuma sa dama shi kansa ba son zuwa yake ba. Kawai dai yana ƙoƙarin bin umarnin Mom ne. Yanzu kuma da Daddy ya yi magana dole ya haƙura gaba ɗaya.

"Shi kenan.." ya ƙare daidai lokacin da ya miƙe yana kuma tura hannayensa cikin aljihun wandonsa.

"Ka da ka fita.. Akwai inda za ka raka ni anjima.."

"Tohm." Ya amsa a taƙaice yana ficewa daga ɗakin.


... Washegari kamar yanda suka yi da Bad Man ya shirya cikin shigar nan tasa. Zuwa lokacin tana zaune a kan gadon saboda Ummeey da ta hanata yawan kwanciyar. Sai dai ta kwantar da kanta ne a kan bangon gadon da alama tunani take yi. A nutse ya saci kallanta daga inda take zaune. Yanda ta sake zama wata shiru shiru hakan na matuƙar ba shi mamaki. Yana kuma sakawa duk ya ji jikinsa ya yi sanyi. Ya kuma dinga tunanin ko akwai wani abun da ke damunta? Da za ta iya ba shi dama da ya tambayeta ko wani abun na damunta ne ko kuma ta ba shi dama ya shiga rayuwarta sosai ko babu komai da yaddar Allah ze yi ƙoƙari wajen rage ko da kaso mara yawa ne daga yanayin da take ciki. Se dai kuma ya san ba ma za ta saurare shi ba musamman a yanzun da ko son ganinsa ba ta yi. Har a karon kansa kuma ba ya son yin nisa da ita bayan abin da ya faru. Duk da idan ya zauna ɗin ma ba wani abun za ta yarda ya yi mata ba. A nutse ya soma takawa zuwa wajen gadon. Ya ja side drawer ya zauna a kai yana cigaba da kallanta, duk da ba ya iya ganin fuskarta. Daidai lokacin da ta ɗago idanunta saboda motsin da ta ji se idanunta suka sauka a kansa. Ta sunkwui da kanta tana saka hannu ta ɗauke wata ƙwalla da ta sauka a gefen kumatunta.

"Ya ilahy.. Kuka ki ke? Me aka miki? Me yake damunki?" Duka ya jera tambayar ysvyi ts lokaci guda, duk da ya san ba lallai ta amsa masa ba. Jin shirun da ta yi kamar yanda ya tsammata ɗin kuwa ya sanya shi faɗin

"Ko Ammi ki ke so ki yi waya da ita? Ko kuma Afrah?" Ya tambaya yana kafeta da idanunsa. A yanda yake magana cike da rarrashi kai ba za ka taɓa cewa Gwani ba ne. Ba ta san lokacin da ta ɗaga kai ta kalle shi ba. Tana shirin cewa "Ehh" se kuma ta tuna abin da ya mata. Dan haka ta yi saurin maida kanta tana cuno baki daidai lokacin da idanunta suka tara ƙwalla. Ga samu ga rashi. Sauke numfashi ya yi yana kai hannunsa kan goshinsa ya ɗan murza sannan ya miƙe.

"Za ki kira su?" Karo na farko ts buɗe baki ba tare da ta kalle shi ba tace

"Ba na so.." Murmushi ya yi ko ba komai maganar ma da take masa ta fi shirun. Fiddo wayarsa ya yi daga cikin aljihu. Ya ajjeta kan gadon yace

"Ga shi nan ni zan fita.. Kar ma ki yi zaton ina cikin gidan nan ki ƙi ɗaukar wayar ki yi kira da ita.." ya ƙare yana soma takawa. Se kuma ya dakata ya yi shiru na en wasu mintuna kafin yace

"Amma ki sake min haƙuri.. Sannan ko ba dan komai ba ki min alƙawarin ba za ki faɗawa kowaccensu abin da ya faru ba." A karo na biyu yanzun ba ba shiri ta ɗaga ido ta kalle shi. Se ga idanunsu cikin na juna. Ya cije lips ɗinsa na ƙasa daidai lokacin da ya kashe mata ido ɗaya. Se ta yi saurin kawar da kanta tana maida kanta ta kwantar kamar wata munafuka. Au dama ya san ba ya so kowa ya ji me ya sa ya aikata? Se yanzu ze wani zo yace mata kar ta faɗa. Ehh tunda ma ga er iska ai dole ta je ta faɗa salon ita ma a koma yi mata kallan hakan.
A ranta tana sake mamakin halin Gwanin da ba su gano shi tun a makaranta ba se yanzu. Ta san kuma ko za ta kwana tana faɗawa wasu halin Gwanin na yanzu ba yadda za su yi ba. Burinta kawai ta neme shi cikin ɗakin ta rasa, dan har ga Allah tun da abin nan ya faru ita yanzu kallansa take kamar wani dodo. Sam ba ta ƙaunar ganinsa kusa da ita. Kamar kuwa ya san me take saƙawa se ya fice daga ɗakin yana murmushi. Se bayan wajen minti 3 da fitarsa sannan ta juya ta kalli kan gadon. Da gasken wayar tasa na ajjiye alamar ya barta ta yi kiranta. Ba ta san lokacin da murmushi ya ƙwace mata ba. Se ta yaye bargon da take lulluɓe ciki ta sauka a hankali dan har yanzu jikinta be gama warwarewa duka ba. Ƙaramin ɗakin nan ta shiga, wajen minti 2 ta dawo ta nemi waje ta zauna a kan gadon. Number Mommah da ke cikin takarda ta shigar cikin wayar tasa. Ta kara a kunnenta lokacin da ta soma ringing. Fatanta kawai a ɗaga ta ji muryar Didinta.


.. A ɗaya ɓangaren Mommah na zaune a ɗakinta kan kujera. Ya yin da Didi ke zaune a kan wata kujerar.

"Me kika shiryawa Abban naki?" Se da ta turo baki sannan tace

"Mommah yace wai Little kawai ze kawo.. Ze zo mana zuwa na musamman.."

"Toh madallah.. Allah Ya kawo su lafiya. Kin kira Ummeeyn kin mata ban gajiya?" Ɗaga ido Didi ta yi ta kalli Mommah, se kuma ta sauke su ƙasa.

"Mommah.." ta faɗa kamar me shirin faɗar wani abu, se kuma ta yi shiru.

"Babu damuwa.. in Sha Allah komai ze zo ƙarshe Uhmm? Kar ki damu.. ki cigaba da addu'a.. ki kuma cigaba da abin da kike yi ka da ki ce kin gaji. Areef na da wuyar sha'ani ne shi ya sa.." Murmushi kawai Didi ta yi. Har kullum mutuncin Mommahn ƙaruwa yake a idanunta. Musamman yanda ta iya amfani da kalaman rarrashi ko da ba ta da tabbaci a kan abun, duk dan ta kwantar mata da hankali.

"Ai se ki samu kirata ko a wayar Baba Atine ne.. Ba na so ne ki kirata a wayata saboda gudun tashin hankali, shi ya sa na ce ki karɓi tasa ki kirata. Se dai kuma tun da hakan be yiwuwa ba ki karɓi ta Baba Atinen se ki kirata.."

"Tohm shi kenan Mommah In Sha Allah.." Didi ta faɗa a sanyaye. Dan kuwa ita duk wani abu da ze haɗata da Mom ba son shi take yi ba. Se dai kuma a matsayinta na sirikarta yana da kyau duk abin da Mommahn ta sakata yi ta yi ko dan a zauna lafiya. Daidia lokacin kira ya shigo wayar Mommahn. Da yake tana kusa da ita se ta kalli me kiran. Jerin numbers ɗin da ta ga suna yawo a kan wayar su suka sanyata tsayawa tana kallan allon wayar. Dab da za ta tsinke ta ɗauka ta kara a kunnenta da sallama ɗauke a kan bakinta. Daga can ɓangaren Lulu da ta gama sarewa ta amsa sallamar. Da ƙyar ta iya tsayawa ta gaida Mommahn sannan ta ɗan yi shiru kafin tace kamar ba ita ba

"Don Allah ina neman Didina Afrah." Kallan Didi Mommah ta yi daidai lokacin da ta yi murmushi saboda jin muryar da ta yi sakk irin ta Didin.

"Bari a bata.." Daga haka ta miƙawa Didi wayar. Hannu Didi ta saka ta karɓa duk da bata san waye ba. Se dai haka nan kawai take ji a jikinta kamar er uwarta ce. Aikuwa tana kara wayar a kunnenta ta jiyo muryar Lulu.

"Luluna."

"Uhmm Didina.." Lulu ta faɗa a narke. Cikin lokaci ƙanƙani ƙwalla ta ciko idanun Didi. Ya yin da ita waccan uwar shagwaɓan ta kasa haƙura se da ta fashe da kuka.

"Me ya faru Lulu? Me ye kike kuka? Don Allah ki dena kin ji?" Ta tambayar tana bin bayan Mommah da ta miƙe ta bar wajen da kallo.

"Didi.."

"Na'am."

"Na yi kewarki sosai.. Ina ji kamar na yi tsintsuwa na zo na ganki." Murmushi me haɗe da hawaye Didi ta yi se kuma dan ta kawarwa da er uwar tata damuwa ya sanyata faɗin

"Ni ma haka Lulu.. Na ma fi yin kewarki fiye da yanda kika yi tawa. Amma kuma ma fa kullum ki na ganina.."

"Kaii.. yaushe ɗin?"

"Duk lokacin da kika kalli mudubi mana.." ta ƙare tana murmushi. Dariya Lulu ta yi sosai.

"Kai Didi. Ni fa Allah Didina ta gaske nake son gani" Ta faɗa tana cuno baki. Sun kwashe fiye da awa 2 suna wayar. Sun yi hirar yaushe gamo, sun kuma taɓo Bad Man. Inda Lulu ke bawa Didi labarin abin da ya faru a Restaurant ɗin nan. Da kuma gaskiyar da ta bayyana. Ta kuma sanar da ita yanda a da take zargin Bad Man se daga baya ta gane ashe ba shi ba ne. Ba ƙaramin tashin hankali Didi ta shiga ba jin labarin da Lulun ta bata. Se dai ta gefe guda kuma ta ji wani sanyi jin da ta yi ba Bad Man ɗin ba ne ya yi wa Lulun hakan. Se kuma a lokacin ne ta iya fahimtar abin da ya kawo Bad Man gidansu. Wato ya ɗauka ita ce Lulu. Ashe ƙaddarar aurensu ke kiransa. Se ta sauke ajiyar zuciya lokacin da Lulu ta gama bata haƙuri a kan ɓoye matan da ta yi tun ranar da suka je Restaurant ɗin saboda ta ga Ɗidin ta ji haushi.

"Don Allah ki yi haƙuri Didina.. Ba na son ɗaga miki hankali ne.. Kuma ban san ma haka ne ze biyo baya ba shi yasa.. Amma ki yi haƙuri kin ji Masoyiyatah.."

"Ki je can ki nemi Masoyiyarki ba dai ni ba.." Didi ta sake faɗa.

"Haba mana Didi na baki haƙuri fa don Allah.." ta faɗa a shagwaɓe. Da ƙyar ta samu ta shawo kan Didin ta haƙura.

"Wai ya na ji kamar muryarki ta sauya ta koma ta masu hankali.."

"Kai Didi da ba ni da shi.?" Ta ƙare tana waro idanunta. Se kuma ta yi shiru ta yi jin abin da Didin ta faɗa. Toh ko dai ta gane abin da ya faru tsakaninta da Gwani duk da ba ta faɗa mata ba? Idan kuwa haka ne daga yanzu ba za ta sake kiran kowa ba balle ma a ganeta.

"Ni dai ban ce

Please Login or Register in order to submit comment