Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kusa da ita ne ya sanya ta ɗaga kai ta kalle shi. Wani kallo da yafi kama da na gargaɗi shi ya jefa mata, da sauri ta ɗauke kai tana murguɗa baki gami da huhhura dogon siririn hancinta.

"Ina ruwanka da ni?" Ta faɗa ƙasa ƙasa tana miƙewa tsaye ta koma gefe ta cigaba da tsayuwa.

"Ki..."

"Wai me ye haɗinka da ni ne? Ina ruwanka da inda zan kwanta? Ka rabu da ni mana a'ah.." ta yi saurin katse shi da faɗin hakan, duk da yanda wannan kallan kawai da ya mata ya hautsina mata 'ya'yan hanji. Amma duk da haka, kwaɓar zuciyarta kawai take yi ka da tun yanzu ta masa abin da ta san in dai ta yi dole ya saketa. Shi yasa jira kawai take yi gobe ta yi Mami ta dawo ta ji abin da za ta faɗa mata. Be ce komai ba ya koma kan gadon, ya ɗauki bargonsa da yake lulluɓa da shi me taushi, da pillow ya taho daidai bakin ƙofar ya ajje su. Sannan yace

"Wuce ki je.." ya faɗa yana tsareta da waɗannan idanun nasa masu shegen kwarjini da kyau. Gaba ɗaya se ta dibibice. Amma duk da haka ƙoƙarin sake bijirewa take yi, se dai har ga Allah ta ji tsoron yanda ta ji sautin muryarsa. Se dai duk da haka ba ta bar da kai bori ya hau ba, se ta ɗauki ƙoƙarin bin abin da ya faɗa ɗin da take yi a matsayin kawai dan tana jiran gobe ta yi ne. Ba dan haka ba kome ze mata se dai ya yi amma ba za ta ko da ɗaga ido ne ta kalle shi ba. Cike da sassarfa ta soma takawa zuwa cikin ɗakin, fuskar nan a ɗinke tsaff, ita a lallai dole kar ya rainata ballantana yace umarninsa ta bi. Hakan ne ya sanyata ɗan buɗe baki tace ƙasa ƙasa

"Dan dai dama ina da niyyar kwanciya ne. Ban da haka ba wanda ya isa ya min dole se na kwanta.. Ai dai na ga jikina ne.." ta ƙare tana hararar gefe. Sarai ya jita amma ko bi ta kanta be yi ba, ya shimfiɗa daddumar dake ajje a wajen kana ya hau kai ya zauna idanunsa a lumshe. Zuwa can ya buɗe bayan ya furzar da iska me ɗan ɗumi ba can ba. Yana kallan lokaci da take gyara zaman labulen da ya kare gadon ɗakin, ya ɗauke kai yana sakin ƙaramin tsaki zuciyarsa na masa wani zafi.



... Kallan ɗakin Mom ta cigaba da yi, duk da yanda Mommah ke da muguwar tsafta hakan be hana sashen nata nuna baƙi basu daɗe da watsewa ba. Mom ta jinjina kai tana yamutse fuska ta cigaba da takawa zuwa cikin ɗakin.

"Ohk.. yanzu dai kina nufin ki ce min da gaske har an kawo amaryar?" Mom ta faɗa tana kallan Didi da har lokacin take zaune kan kujerar kanta a ƙasa. Murmushi Mommah ta yi kana tace

"Wallahi kuwa.." Lallae kam se yau ta tabbatar da abin da Daddyn ke faɗa gaskiya ne. Babu shakka ya shammacesu, ya kuma wulaƙantata, ya wulaƙanta ɗansu ɗaya tilo. Yaro me ji da jini a jika, kyakkyawa ɗan ƙwalisa, wanda ke ji da ƙuruciya da kuma kuɗi, shi ne za a yiwa auren cushe, auren haɗi, auren dole, da yarinyar da be sani ba? Yarinyar da be san wace ce ita ba? Yarinyar da karon farko hatsaniya ce ta soma haɗasu, kafin kuma komai ya saitu har Daddyn ya ɗaura musu aure? Lallai akwai sake a wannan al'amari. Maida dubanta kan Didi Mom ta yi tace

"Toh ke se ki tashi mu yi gaba koh?" Kafin Didi ta kai ga ɗago kanta se ta ji Mommah na faɗin

"Ki yi haƙuri Hajiya.. Amma Yallaɓai be ce ta je ko ina ba.. Ya ce ta zauna anan har ya dawo, yana san ganinta ita da Areef ɗin.." Sheƙewa da dariya Mom ta yi tace

"Yau ni nake ganin ikon Allah.. Wato ke da baki haifa ba, ballantana ki aurar. An kuma haifa kina ƙoƙarin nuna iko da matar da ba ki da haɗi da ita. Me ye haka ne?" Mom ta ƙarasa a fusace. Se kuma ta ɗora da

"Ko kuma dai, idan ma ba za ki bamu yarinyar ba, ki cigaba da riƙeta anan ɗin. Ai ɗakin ki ba baƙon Areef bane. Ze shigo ne har nan ya bata takaddarta. Idan ya so in kin ji haushi a yau ki yi ciki ki haifi ɗa namiji ki aura masa yarinyar.." Runtse idanunta Mommah ta yi saboda yanda maganganun Mom ɗin ke saukar mata kamar mashi. Tabbas ta ji raɗaɗinsu matuƙa gaya, ta ji tamkar ta yi kuka ko za ta samu ta ji sauƙi a cikin ranta. Ina ma Allah ze azurtata da ciki duk da yanayin shekarunta da suka ja. Da tafi kowa farin ciki a rayuwarta. Se dai duk da hakan ma ko a yanzu tana godewa Allah a bisa ni'imomin da ya mata masu yawa.

Ita gaba ɗaya Didi ta gaza fahimtar abin da suke faɗa, ta kasa fahimtar inda zancen nasu ya dosa. Idan ma za tace ta gane, toh be wuce wasu abubuwa ƙalilan da ta gane a cikin maganganun nasu ba. Amma abin da ta kasa ganewa shi ne.. Ita wace ce a cikin gidan? Mene ne matsayinta? Wacce ce sirikarta a cikin waɗannan mata biyun? Waye ma shi kansa mijin nata da ake magana a kansa?. Wayarta Mom ta ɗaga ta soma kiran layin Bad Man ba tare da damuwa da yanayin da maganganun da ta faɗawa Mommah suka jefata ba. Se dai a karo na 2 ta sake gwada kiran nasa babu amsa. Se ta sauke ajiyar zuciya tana maida dubanta kan Didi tace

"K..." Kafin ta kai ga ƙarasa faɗar abin da ta yi niyya sallamar Daddy ta karaɗe cikin parlourn daidai lokacin da Mommah ke ƙoƙarin barin wajen, dan haƙiƙa maganganun Mom ɗin sun karceta da yawa.

"Sa'adatu.." Daddy ya faɗa yana kallan Mommah. Juyowa ta yi ta kalle shi daidai lokacin da ya sake faɗin

"Ka da ki je ko ina.. Dawo ki zauna.." Ba dan ta so ba, se dan bin umarnin Daddyn ta dawo. Ya nemi waje ya zauna. Ya kalli Mom ma yace mata ta zauna. Dukkansu zaunawa suka yi, ya kalli Didi dake zaune duk a takure yace

"Ɗiyata.." Zamowa ta yi daga kan kujerar cikin siririyar muryarta tace

"Barka da wannan lokaci.."

"Barkanki dai 'yata.." Daddy ya faɗa da murmushi a kan fuskarsa. Se kawai ta cigaba da zama a ƙasan, dan dama tafi jin daɗinsa, dan Mommah ta maidata kan kujerar ne ya sa ta zauna. Wayarsa ya ɗauko daga cikin aljihu ya danna kiran Bad Man. Dab da za ta tsinke ya ɗaga, cikin murya me kama da ta me bacci ya amsa kiran sunansa da Daddy ya yi.

"Ka zo parlourn Mommah.. Ina jiranka yanzu.."

"Bacci nake.." ya faɗa yana ɗan lumshe idanunsa saboda abin da ya gama sha yanzun nan.

"Ka zo dai na ce.." Daddy ya faɗa. Jin shiru ne ya sanya shi sake faɗin

"Ka ji?"

"E.." ya amsa a taƙaice yana kashe wayar. Sanye cikin ƙananan kaya riga da wando, dogon wando ne wanda ya ɗan tattare shi zuwa ƙasan gwuiwarsa, se riga me gajeren hannu wadda ta bayyana ƙaƙƙarfan damtsen hannunsa. Kansa babu hula se kwantacciyar sumar kansa dake a gyare kamar ta mace. Fuskarsa a cunkushe take sosai, sexy eyes ɗinsa sun sake lumshewa, wanda hakan ya ƙara musu kyau, da armashi, suka kuma ɗan ƙanƙance, sannan suka sake bayyanar da zallar kwarjinin dake tattare da shi.

"Zo ka zauna.." Daddy ya faɗa yana kallansa. Ƙarasawa kawai ya yi ya je ya zauna dan shi sam be ma lura da wata sabuwar halitta da ke zaune cikin ɗakin ba.

"Afrah.."

"Na'am.." ta faɗa a sanyaye.

"Areef.." Daddy ya faɗa yana kallan Bad Man da ya ɗan kifa kansa a kan kujera.

"Bacci kake ji ne?" Jinjina kai ya yi kamin yace yana ɗan dafe kan nasa.

"Yeah.. Na sha magani ne, ban san yana saka bacci ba.." ya yi maganar muryarsa a ɗan cunkushe. Da sauri Didi ta ɗaga kanta ta kalli me maganar, saboda yanda ta ji kamar ta san me muryar. Se dai tun a kallan farko, kafin ta ida kallansa ma ta sauke kanta tana girgiza kai. Saboda yanda ta ga halittar da bata taɓa gani ba, ballantana ta kai ga sanin muryarsa.

"Ohk.. Bari mu gama maganar ka je ka yi baccin... Afrah wannan ne mijinki.. Areef wannan ce matarka Afrah.." Daddy ya yi maganar a lokaci ɗaya. Ɗaga kai Bad ya yi ya kalli Didi da ta kasa ɗaga idanunta ta kalli wanda Daddyn ke cewa shi ne mijinta. Wani irin harbawa zuciyar Didi ke yi tun bayan jin abin da Daddyn ya faɗa, se ta sake maida kanta ƙasa har lokacin bugun zuciyarta be gama saituwa ba. Jin ba wani fuskantar abubuwa yake yi ba in banda wani jahilin bacci da yake ji ya sanya shi faɗin

"Ohk.." Kawai. Kallansa Daddy ya yi yana mamakin yanda ya yi reacting kamar komai normal, wanda hakan ba ƙaramin faranta masa rai ya yi ba. Se ya yi murmushi dan shi ya ɗauka ya karɓi auren ne hannu biyu yace

"Ohk je ka yi baccin. Za mu yi magana gobe In Sha Allah.." Be ce komai ba se miƙewa da ya yi ya soma takawa dan ficewa daga ɗakin. Hankali a tashe Mom ta miƙe tana faɗin

"Ina za ka je? Aou tafiya za ka yi ba tare da ka sawwaƙewa yarinyar nan ba? Kai ko dai asiri aka maka ne ban sani ba? Dawo nan ka saketa a gaban kowa da kowa, magana ta ƙare a yanzun nan ba se wata rana ba.." Mom ta faɗa cikin ɗaga murya. Ko bi ta kan Mom be yi ba ya fice daga ɗakin. Cikin sauri Mom ta juya da niyyar sake yin magana ta ga Daddy na binta da wani irin kallo. Tun kuma kafin tace komai ɗin ya soma faɗin

"Ashe dama ke kike ƙoƙarin ɗora yaron nan a kan hanyar da ba ta dace ba? Ashe ke kike tunzura yaron nan har yake ƙoƙarin bijire min? Ashe ke kike zuga shi a kan ya bijirewa umarnina? Toh ki buɗe kunnenki da kyau ki ki ni. wallahi duk ranar da kika saka yaron nan ya saki wannan yarinyar, ki tabbatar ke ma a ranar za ki karɓi takaddarki.."


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO28*


___Daddy ya faɗa fuskarsa a haɗe. Da matuƙar mamaki Mom ke kallan Daddy, dan bata taɓa tunanin abin da ze fito daga bakinsa ba kenan.

"Yallaɓai..?" Ta faɗa har lokacin cike da mamakin dai. Ɗaga mata hannu ya yi tun kafin ta ƙarasa faɗar abin da ta yi niyyar faɗa kana yace

"Abin da kika ji na faɗa shi nake nufi.." Daga haka ya fice daga ɗakin. Binsa ta yi da kallo kamar wata doluwa tana jin yanda ilahirin jikinta ya yi sanyi, kunya da haushin abin da ya faru a gaban Mommah na kamata. Me yasa ta kasa controlling kanta har hakan ya faru a gaban Mommahn? Ba tare da ta sake kallan kowa ba ta ja tsummar ƙafafunta ta bi bayan Daddy da ya fice daga ɗakin a fusace. Se a lokacin Mommah dake zaune gefe ta yi shiru hannunta a kanta kamar me tunani ta miƙe, ta ƙarasa inda Didi ke zaune kamar wadda aka dasa a wajen. Ita kanta da bata san ainahin abin da ya faru ba jikinta wani irin rawa yake yi, kuka ke shirin taho mata musamman yanda ta ji ana zancen saki kuma kamar a kanta ake maganar. Kenan idan haka ne wane ne mijin nata? Kenan ba shi ke sonta ba? Toh idan dai haka ne ya aka yi aka yi auren? Ita gaba ɗaya kanta ya kulle da wannan lamarin. Kamar daga sama ta jiyo muryar Mommah na faɗin

"Daughter.." Se ta ɗago da sauri, dan babu ƙarya ta tsorata, dan ba ta yi tsammanin akwai mutum a kusa da ita ba. Kafin tace komai Mommah tace

"Tashi mu je na raka ki ɗakinki, dare na yi.." Miƙewa ta soma yi jikinta a matuƙar sanyaye, kyawawan brown eyes ɗinta sun cika taff da ƙwalla, wadda ke jiran ƙiris ta zubo. Har cikin part ɗin dake kusa da na Mommah ta kaita, bata barta iya nan ba se da ta kaita har cikin bedroom. Sannan ta kalleta bayan ta yi murmushi tace

"Ki yi duk abin da za ki yi anan.. Zan aiko a kawo miki abinci, zuwa da safe idan Allah ya kai mu zan shigo.." Da sauri Didi ta kalleta jin tana ambatar da safe za ta shigo. Kenan anan za ta barta ita kaɗai? Jin Didin ba tace komai bane ya sanya Mommah faɗin

"Ya sunanki ne?"

"Afrah.." Ta faɗa cikin sanyayyiyar muryarta tana iya ƙoƙarinta wajen maida hawayen dake ƙoƙarin zubowa. Karo na farko kenan da ta yi magana tun zuwanta cikin gidan.

"Suna me daɗi.." Mommah ta faɗa tana murmushi. Se ta ɗora da

"Se da safe..?" Ta ƙarasa maganar cikin sigar tambaya. Da sauri Didi ta girgiza kai, sannan tace a sanyaye

"Don Allah.." ta yi maganar tana riƙo hannun Mommahn. Murmushi Mommah ta yi kana tace

"Shi kenan.. Zan turo miki Atine za ta zo ta tayaki kwana ko da na kwana biyu ne, kafin komai ya daidaita.." Cikin jin daɗi tace

"Tohm.." Se a lokacin ta saki hannun Mommah, ita kuma ta miƙe ta fice daga cikin ɗakin tana mamakin yanda ta ji lokaci ɗaya Didin ta kwanta mata. Tana nan zaune cikin ɗakin kamar marainiya, ta kaasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne se baza idanu kawai da take yi, dan kuwa ita bata saba zama a ɗaki ita ɗaya a irin wannan lokaci ba. Ta riga ta saba ganin Lulunta kodayaushe a gefenta. Se kawai ta shiga bin haɗaɗɗen ɗakin da ya ginu bisa tsari da kallo. Can se ga sallamar Atine cikin ɗakin, cikin farin ciki ta amsa sallamar se dai murya a sanyaye. Ƙarasowa Atine ta yi tana kallanta da murmushi kan fuskarta tace

"Barka da wannan lokaci Rankiyadaɗe.."

"Ina yini?" Didi ta katseta da faɗin hakan. Se ta sake yin murmushi tana amsa gaisuwar tata.

"Ga abinci nan, Hajiya tace a kawo miki.." ta faɗa tana nuna mata wasu warmers masu kyau da ta shigo dasu.

"Na gode.." Didi ta faɗa dai. Murmushi Atine ta yi, se kuma tace

"Kina buƙatar wani abun ne Rankiyadaɗe?" Ita duk idan tana mata abubuwa kamar wata ƙanwarta duk kunya ke kamata wallahi. Dan haka se ta girgiza kai kawai.

"Toh se da safe.." Atine ta faɗa. Kallanta Didi ta yi da mamaki tace

"Ba anan za ki kwana ba dama?" Ta tambaya cike da sarewa.

"Anan zan kwana amma a parlour.."

"Don Allah ki kwana anan kin ji?" Didi ta faɗa tana kallanta fuska a raunane.

"A'ah Rankiyadaɗe ki dai bari na kwana a can ɗin.. Idan kina buƙatar wani abu se na zo.."

"Don Allah Baba, wallahi tsoro nake ji.." Didi ta sake katseta da faɗin hakan. Se da Atine ta sauke ajiyar zuciya sannan tace

"Toh shi kenan.." Cikin farin ciki Didi tace

"Yawwah.." har murmushin da bata shirya masa ba na fitowa. Haka ba dan Atine ta so ba ta zauna cikin ɗakin duk a takure, tana ganin kamar ta zaƙe ne ta kwana ɗaki ɗaya da matar masu gidan. Ita kuwa Didi ko a jikinta, daɗi ma ta ji na zuwan Atinen, se a lokacin kuwa ta saki jiki ta samu ta ɗan yi wanka, kana ta fito ta tayar da Sallah.


... A ɗaya ɓangaren kuwa shimfiɗa bargon ya yi, ya jefar da pillow, kana ya ɗan kishingiɗa a kai. Idanunsa ya ɗan lumshe kaɗan, duk da ya san shima ya yaudari kansa in dai bacci ne ba zuwar masa ze yi ba. Haka dai ya cigaba da zaman, hannunsa ɗore a kansa. Ya daɗe zaune a wajen, babu abin da kwanyarsa ke yi se tunani. Be ankara ba se ji ya yi ana kiran Assalatu. Buɗe idanunsa da suka ɗan lumshe ya yi. A hankali ya miƙe zaune, se kawai ya miƙe kai tsaye ya nufi toilet. Ko kallan inda gadon yake be yi ba. Kai tsaye wanka ya yi, ya ɗauro alwala sannan ya fito. Shiryawa ya yi kamar yanda shigarsa take ta koyaushe. Cikin ƙanƙanin lokaci ya fito a Gwaninsa sakk, ya yi matuƙar kyau kamar wanda ya shafe tsawon awanni yana shiryawa. Se a lokacin ya ɗan dakata, ya kalli kan gadon. Tana kanannaɗe cikin zanin gadon, kwata kwata ba a iya ganinta saboda yanda ta cukwuikuye zanin gadon. A hankali ya ɗan danna wayarsa, ya kalli ƙarfe nawa. Se ya maidata aljihu kawai ya fice daga ɗakin. Be daɗe da fita ba ɓarawon baccin da ya saceta ya soma sakinta. Se ta shiga buɗe idanunta a hankali. Firgigit! Ta zabura gami da miƙewa zaune tana kallan inda take. Ya aka yi ta yi bacci a cikin gidan nan? Me yasa ba ta cigaba da jiran safiya ta yi har Mami ta zo ba? Ture zanin gadon ta yi a fusace, kamar shi ne ya mata laifi. Ta ja dogon tsaki tana jin ɓacin rai na taso mata. Hijabin da ta lalubo shi ta sake gyara zamansa, ta sake kallan ɗakin tana cigaba da yamutse fuska. Ƙofar da ta fi mata kama da banɗaki nan ta nufa. Tana zuwa ta tura ƙofar banɗakin da hannu ɗaya, ita a lallai dole ƙyanƙyami take ji. Bin toilet ɗin ta yi da kallo, yanda yake a wanke tass kamar ka lashe. Babu abin da ke tashi se ƙamshin sabulun da ya yi wanka da shi yanzun. Sam sam babu alamar datti ko na wani abun makamancinsa a cikin banɗakin, dan kuwa mamallakinsa me tsafta ne, kuma mara son ƙazanta. Duk kuwa da yanda toilet ɗin yake ƙal ƙal hakan be hanata sake taɓe fuska ba. Ta shiga ciki duk a ɗarare kamar wadda ke kan tutu. Wanka ta yi da sabulu kawai, shi ma ba dan ta so ba, se dan kawai ba ta so ne Mami ta zo ta sameta yaɓe_yaɓe. Kuma har su koma gida ma babu wanka, shi yasa ta gwammace ta yi anan ɗin. Ko da ta fito babu abin da ta shafa a jikinta, se maida kayanta da ta yi, ta sake saka hijab ɗinta, kana ta tayar da Sallah. Se wajen ƙarfe 7 ya dawo gidan. Kai tsaye ɗakin ya nufa dan tabbatar da tashinta. Se ya yi tozali da ita a bakin ƙofa kamar yanda ya sameta jiya. Be bi ta kanta ba kawai ya rufe ƙofar, ya koma ɗakin Ummeey kamar yanda ya saba. Se da suka gaisa sannan Ummeey tace

"Ina ɗiyar tawa? Ban ganta ba.. Ina fata dai ta tashi lafiya.." Murmushin yaƙe kawai ya yi kafin ya amsa da

"Alhamdulillah.."

"Madallah.. So nake yau na ɗora abun kari da wuri, saboda yarinyar nan. Ka san wasu sun saba da karyawa da wuri, ka da na je itama wajen ɗiyar tawa haka ne, a zo kuma a yi abin kunya.." Cike da tausayin Ummeeyn, da kuma tuna hali irin na Lulu ya girgiza kai. Da Ummeey ta san wace ce Lulun da ta rabu da ita. Ta watsar da ita a gefe tun kafin ta nuna mata wace ce ita. Da ta manta da zancenta ma kwata kwata duk da suna zaune cikin gida ɗaya.

"Bari na duba miki ita Ummeey.."

"Aikam dai duba min.. Idan kuma bacci take yi ka ƙyaleta.. Na san idan ta tashi za ta fito.." Da "toh" ya amsa yana wucewa ɗakin nasa.



... "Wallahi na yi iya bakin ƙoƙarina amma sun hana ni shiga cikin gidan nan. Wai tsaya! Ko a fuska ma na yi kama da ɗan iska ne?" Hero ya faɗa yana kallan Ladi. Dariya Abida dake gefe ta sheƙe da ita jin maganar Hero ɗin. Ita kuwa Ladi ba wannan ne a gabanta ba, dan haka tace

"Duk wata dabara ka gwada?" Ta tambaya fuska a dame.

"Wallahi na gwada.. Ke kaina gaba ɗaya fa ya kulle, ban san me mutanen ke nufi da mu ba.."

"Duk kai ne ka ja wallahi Hero.."

"Daga yau wallahi duk lokacin da kika sake cewa ni na ja, toh na cire hannuna a kan komai, se ki ƙarasa da kanki.." Hero ya faɗa a fusace.

"Ka yi haƙuri. Raina ne a ɓace.." Ladi ta faɗa. Se ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ɗora da

"Abin da ya rage kawai mu tura Abida gidansu yarinyar, na san za ta samo mana labari a kan abin da ke faruwa. Wallahi Hero ba zaka gane bane, kullum kwanan duniya ji nake ana ƙaramin ƙaunar jikin yarinyar nan.." Ladi ta faɗa tana lumshe ƙananan idanunta.

"Shi kenan, mu gwada hakan.." Hero ya faɗa, dan gaba ɗaya kansa ya kulle, ya ma rasa abin da ya kamata ya yi.



... "Toh mu dai Yaya za mu yi gaba.. Allah ya sa an yi komai a sa'a.." Mami ta faɗa sanda ta ga Abban na ƙoƙarin fita daga gidan. Juyawa ya yi ya kalleta yace

"Har za ki tafi..?"

"Ehh, amma dai zan biya ta gidan Afaaf ne, dan tun jiya na barta tana ta kuka, ina so ne na je na rarrasheta, ka san yarinyar nan fa dama Yaya se da rarrashi.." Mami ta ƙare tana murmushi, ita a lallai dole so take Abba ya yarda da abin da ta faɗa. Jinjina kai Abba ya yi sannan yace

"Ehh hakan ma na da kyau. Se dai yana da kyau duk yarinyar da ta yi aure ta san fa auren ta yi. Dan haka ya kamata itama Afaaf ta san yanzu ta girma ta yi aure, gwara ta fara sabawa tun yanzu. Dan haka ina ganin ba se kin je ba. A barta idan ta kwana biyu se a je a duba lafiyarta, amma banda yanzu.." Tunda Abban ya fara magana se ta tsaya sororo tana kallansa kamar wanda ya yi saɓo. Cikin basar da zancen nasa tace

"Amma Yaya Afaaf fa yarinya ce ƙarama.."

"Ita kuma Afrah fa? Dukkansu yara ne, amma idan basu san sun girma ba yanzu se yaushe? Kin ga shiga maza ki ɗauko kayan ki ki zo mu fita se na sauke ki a gida. Sannan kar kuma na ji labarin kin je a kwanakin nan.. Ke fa kamar uwa kike a wajen Afaaf. Ko ba ma wannan ba, ni dai nace a barsu dukansu su fara sabawa kafin a soma ziyartarsu.." Shiru Mami ta yi saboda yadda maganar Abban ta ɓata mata rai. Ya riga ya san halin Mamin dama, dan haka be jira amsarta ba yace

"Ki yi da hanzari, ina jiranki.." Daga haka ya fice daga ɗakin. Binsa ta yi da kallo tana huci kamar wadda ta yi ko take shirin yin dambe. Kawai se ta koma ta zauna a kan kujerar bayanta har lokacin ta gaza furta komai saboda yadda ranta ya ɓaci a kan yayan nata. Da sallama ta shigo cikin ɗakin cike da fatan ganin Lulu ko Didi cikin ɗakin. Se dai babu ma wanda ya amsa mata sallamar, se Mami kawai da ta hango zaune kan kujera, babu ma alamar ta san da shigowar wata halitta cikin ɗakin. Se ta shiga ƙarasawa inda Mamin take, da farko ma ta ɗauka Amminsu Lulu ce, se kuma da ta kusa ƙarasawa ta lura da ba ita bace.

"Ina wuni?" Abida ta faɗa tana kallan Mami. Takaicin maganar Abba ya sanya Mami juyawa ta watsawa Abida wani kallo kafin tace

"Lafiya malama?" Dan ba ta san ma da shigowar Abidar ba, se maganarta kawai ta ji.

"Don Allah wajen Afaaf na zo.." Kamar ba za ta tanka ba se kuma tace

"An yi aurensu.." daga haka ta ɗauki wayarta dake kusa da ita ta yi cikin ɗakin da suke dan ɗakko kayanta da ta gama haɗawa. Cike da mamaki Abida tace

"Aure kuma?" Ganin Mami na ƙoƙarin barinta a wajen ba tare da jin tabbacin abin da ta faɗa ba, ya sanya ta saurin yin gaba, ta sha gaban Mami tace jiki na rawa

"Aure kuma don Allah..?" Dakatawa Mami ta yi tana bin Abidar da kallo irin na tuhuma. Se da ta gyara tsayuwarta sannan tace

"Wace ce ke?" Ta tambaya cikin tsare gida. Cikin mazewa da yanayin yanda ta shiga shock ta gyara tsayuwarta tana ƙaƙalo murmushi tace

"Uhmm.. ƙawar Afaaf ce fa sosai.." Taɓe baki Mami ta yi kana tace

"Toh ta yi aure.." Daga haka ta yi gaba ta bar Abida a tsaye da ta saki barandar laɓɓa,

Please Login or Register in order to submit comment