Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah abun godiya.. Yanzu ya za a yi kenan?"


... Sallamar da aka yi cikin ɗakin ita ce ta sanyasu amsawa. Daddy ya kalli me sallamar daidai lokacin da shi ma ya kalle shi. Cike da mamaki dukansu suke kallan juna, kafin Abeey ya ƙaraso ya miƙawa Daddy hannu suka gaisa.

"A'ah Malam.. Barka da zuwa.." Daddy ya faɗa cike da girmamawa.

"Barka dai Yallaɓai.." Abeey ya amsa da hakan yana neman waje ya zauna bayan sun gaisa da ragowar mutanen da ke cikin ɗakin.

"Ikon Allah kwana da yawa ba mu haɗu ba.. Ba mu kuma taɓa kaiwa juna ziyara ba.. Gaskiya duk mun yi laifi.." Murmushi Abeey ya yi. Shi kullum sake ganin mutuncin Daddyn yake yi, dan tun farko be yi tunanin haka yake ba. Se da ya mu'amalance shi sannan ya fahimci halinsa. Yace

"Gaskiya kam.. Ka san da yake kwana biyu ban ji daɗi ba shi ya sa.. Toh yanzun ma dai wani muhimmin abu ne ya kawo ni cikin gidan nan.."

"Ikon Allah!! Toh Allah Ya ƙara sauƙi."

"Da ma kun san juna ne?" Dattijon mutumin nan ya faɗa yana kallansu cike da mamaki. Jinjina kai suka yi kusan a tare, kafin Daddy ya amsa da

"Ƙwarai kuwa.."

"Ikon Allah!!" Mutumin ya faɗa yana jinjina kai. Duk kuma se suka cigaba da kallansa daidai lokacin da ya fara faɗin

"Malam waɗannan su ne mutanen da na faɗa maka.. Wato ina nufin iyayen yaron nan.." Da sauri Abeey ya ɗaga ido ya kalli Daddy wanda shi ma shi yake kalla.

"Yallaɓai, Malam Abubakar shi ne wanda ya ɗauki yaron ya riƙe shi tun ranar da aka haife shi. Shi ne yaron da kowanne uba ze yi alfaharin kasancewarsa ɗansa. Ina tayaka murna." Shi fa Daddy har yanzu kansa ya kulle. A karo na barkatai ya sake kallan Abeey yace

"Wanne ɗa ake magana a kai?" Murmushi Abeey ya yi wanda iyakarsa kan fuskarsa. Wato duk da ya daɗe yana jiran wannan rana, yau ɗin kuma da ta zo tun a yanzun ilahirin jikinsa ya yi sanyi. Dan kuwa duk wata alama da ke nuna iyayen Affan sun bayyana a yau ɗin ta bayyana. Abin da be sani ba kawai me ze faru nan gaba?

"Ɗa ɗaya ke gare ni shi ne Affan.. Shi ne wanda ake magana a kai yanzu, kuma shi ɗin ne dai wanda kake tunani, yaron da na aurawa er uwar tagwaitakar sirikarka.."

"Allah buwaya gagara misali.." Daddy ya faɗa yana jinjina kai cike da mamaki. Duk da ba taɓa ganinsa ya yi ba amma tun ranar da aka ɗaura auren ya san shi a baki. Shi ya sa abun ya matuƙar ɗaure masa kai. Ashe kenan Malam ɗin ba shi da ɗa ko ɗaya se Affan? Yaron da yanzu ake magana a kansa cewar shi ne ɗan nasu da suke nema?. Sun shafe kusan rabin awa a cikin ɗakin, kafin Abeey ya miƙe a sukwane yace

"Ina ganin ya kamata ku tashi mu je can gidan.." Mommah ta riga kowa miƙewa, murmushi ya ƙi barin kan fuskarta, wato ita kaɗai ta san farin cikin da take ji a yau ɗin. Ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta cikin gidan da za ta ga ɗayan yaron nata. Saɓa Little Bad Man ya yi a kafaɗa, shi kansa ya ƙagu ya gan shi cikin gidan ko dan ya ga ɗan uwansa. Daga haka bayan sun sake yiwa Mutumin nan godiya suka fito daga ɗakin zuwa harabar gidan. A yanzu ma Daddy da kansa ya jasu. Duk suka yi ƙwam da su a baya kusan dukansu kamar su yi tsuntsuwa su gansu a gidan Abeey.


... Da sallama Abeey ya shigo cikin gidan. Lulu da ke zaune kusa da Ummeey da plate ɗin yaɗiyar da ta ji kayan haɗi da ƙuli da Ummeey ta kwaɗa a gabanta tana ci.

"Sannu da zuwa Abeey.." Lulu ta faɗa tana tsayawa da cin yaɗiyar.

"Yawwah 'yata Sannu ka dai.." Ya faɗa yana ƙarasowa cikin gidan.

"A'ah Malam.. Da ma ba daɗewa za ka yi ba ashe?"

"Wallahi kuwa.." Ya amsa mata da hakan.

"Toh sannu da zuwa.."

"Yawwah... Mu na da baƙi fa.." Ya yi maganar yana kallanta. Se ta tashi daga inda take zaune tana faɗin

"Ikon Allah baƙi kuma?"

"Ƙwarai kuwa.. Ki shirya yanzu za su shigo." Babu musu ta amsa da "Toh." Ba tare da ta tambayi su waye ba. Dan ta san da da buƙatar ta sani ɗin ze faɗa mata tun kafin ta tambaya. Lulu na shirin miƙewa Abeey yace

"Yi zamanki ɗiyata.. kar ki je ko ina.. Zauna ki ci abinki." Babu musu kuwa ta koma, dan da ma har ga Allah ba ta ji daɗin katsewa ba. Se kuwa ta cigaba da cin abarta da take ji kamar ta ma fi ta ranar nan da ta ci daɗi. Bin Abeey Ummeey ta yi da kallo lokacin da yake ƙoƙarin ficewa daga gidan. Ita dai tun da ya shigo se take ganin kamar yanayinsa duk ba daidai ba. Jikinsa a matuƙar sanyaye yake, dan hatta maganarsa ma a sanyi yake yinta. Ba dai tace komai ba musamman da ta ji yace akwai baƙi. Se kawai ta shiga ɗakin bayan ta furta

"Ce musu su shigo.. Bari a shimfiɗa tabarmar.."


.. Didi da Mommah ne suka fara shigowa cikin gidan. Duk da Ummeey ba ta shaida fuskar Mommah ba hakan be hanata faɗin

"Maraba lale.." Ta ƙare tana kallan Didi. Se ta yi murmushi fahimtar da ta yi wannan ɗin er uwar tagwaitakar Lulu ce. So se ma ta ɗauka ko wadda suke tare ita ce babarsu. Kamar an ce ta ɗaga kai se idanunta suka sauka a kan Didinta. Ba ta san lokacin da ta cire hannu daga cikin plate ɗin ba ta tashi da gudu tana faɗin

"Didina.." Ta ƙare lokacin da ta rungumeta bakinta kamar ze tsage saboda murmushi. Rungumeta ita ma Didi ta yi cike da mamakin ganin Lulun cikin gidan.

"Shi ne ba ki faɗa min za ki zo ba?" Lulu ta faɗa tana turo baki.

"Ni ma ban san zan zo ba Lulu." Ta yi maganar lokacin da suka saki juna. Se a lokacin sannan ta gaishe da Mommah, Mommah ta amsa da ƙawataccen murmushi a kan fuskarta. Tsananin kamar da Lulu ke yi da Didi shi ne abin da ya sa ta kasa ɗauke ido daga kansu, dan babu ƙarya sun mata kyau sosai. Musamman da suka haɗu, se kyawunsu ya ƙara fitowa sosai. Hannun Didi Lulu ta kama suka nemi waje suka zauna, ita dai Didi se bin Lulu take da kallo saboda yanda ta ga ta ɗan chanja. Se ta ga kamar ba ita ba, ita idan ma ba idanunta ke mata ƙarya ba gani ta yi Lulun ta yi ƙiba, har haske ma ta ƙara. Gaisawa Mommah da Ummeey suka yi da fara'a kamar sun san juna. Kafin Didi ta gaishe da Ummeey cike da girmamawa. Ta amsa cikin fara'a ita ma tana sake kallan kamannin Lulu da Didin. Zuwa can babu daɗewa Abeey suka yi sallama tare da su Daddy. Suka ƙaraso suka nemi kan tabarmar suka zauna. Se suka gaisa da Ummeeey. Ta amsa tana tambayarsu sun zo lafiya?. Daga haka se wajen ya yi shiru na tsawon sakanni, kafin Abeey ya katse shirun da faɗin

"Ina yaron nan?"

"Yanzun nan ya fita.. Amma ba daɗewa ze yi ba yanzun za ka gan shi.."

"Toh madallah.." Abeey ya amsa da hakan. Cigaba da zama suka yi. Daddy, Bad Man, Mommah har ma da Didi duk sun ƙagu su ga wa za su gani a matsayin ɗan uwan Bad Man.

"Ke wai me ye wannan?" Didi ta faɗa ƙasa ƙasa tana kallan Lulu da ta ga alamar satar kallan mutane take idan ta ga babu idanun kowa a kanta ta ci abinta.

"Kwaɗo ne mana.. Ki ji Didin nan."

"Oh da ma ki na ci ne?" Didi ta faɗa tana kallanta.

"Oho ni dai yanzu ina ci.." Ta faɗa tana ɓata rai. Daidai lokacin da Gwani ya shigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, sanye cikin shigarsan nan dai da kuka sani. Kansa ma nannaɗe kamar ko yaushe. Ya yi kyau na musamman, musamman kuma da ya kasance kalar kayan da ke jikinsa me duhu ne. Se ya mugun hawa kan fatarsa, ya yi kyau ainun. Kallan Gwanin Didi ta yi, daidai lokacin da wani abu ya saƙu a zuciyarta. Duk da an kira sunan Affan a farko, sun kuma zo cikin gidan nan ta ga Lulu, hakan be sa ta kawo komai ba se yanzu. "Kenan Ya mu'allim shi ne twin brother ɗinsa? Ɗayan ɗan Mommah?" Ta tambayi kanta. Ƙarasawa Gwani ya yi cikin girmamawa ya gaishe da waɗanda ya kamata. Mommah dai kawai kallansa take yi tana jira ta ji abin da Abeey ze faɗa. Sosai tarbiyyar yaron ta burgeta, yanayin shigarsa da kuma nutsuwarsa, se take ji ina ma ina ma..?
Se ya miƙawa Bad Man hannu yana murmushi yace

"Kai ne a gidanmu yau?" Kawai miƙa masa hannu Bad Man ya yi ba tare da yace komai ba. Dan lokacin tuni zuciyarsa ta fara saƙa masa wani abu. Jira kawai yake Abeey ya yi magana. Kamar kuwa Abeey ya san me yake saƙawa se kuwa cewa ya yi

"Wannan shi ne Affan.." Shi ne abin da ya furta kawai yana kallan Gwani. Gaba ɗaya en wajen se suka ɗaga kai suka kalli Gwani, ciki kuwa har da Lulu da Ummeey kamar waɗanda ba su taɓa ganinsa ba. Duk se ya ji ya tsargu. Kawai se ya juya da nufin barin wajen, daidai lokacin da Mommah ta miƙe. Muryarta a sanyaye tace

"Affan.." Se ya dakata yana juyowa. Daidai lokacin da Mommah ta ƙaraso, kawai se ta kamo hannunsa ta kalle shi, a cikin ranta tana ji lallai wannan ɗin shi ne ɗan uwan Areef. Shi ne ɗayan ɗan nata da take nema.

"Lallai tabbas na ji a jikina ɗana ne wannan.." Ta yi maganar tana jin wasu hawaye masu ɗumi na zubowa a kan kuncinta. Cike da mamaki Gwani ke kallanta, yana mamakin jin abin da ke fitowa daga bakinta. Sam ya kasa fahimtar inda zancenta ya dosa. Hakan ne ya sa ka na ganinsa ka ga wanda yake a dame. Ba tare da lura da hakan ba, ta ja shi ta rungume. I zuwa lokacin fa kansa ya sake kullewa. Se dai be san dalilin da ya sa lokacin da ta rungume shi ɗin ya ji wani sanyi cikin zuciyarsa ba. Wani irin sanyi ne ya shiga ratsa Mommah, makamincin wanda ta ji lokacin da ta rungume Areef bayan sanin ɗanta ne. Gefe guda kuma wani farin ciki mara misaltuwa na mamayeta, irin farin cikin nan me sanya me yinsa kuka.

"Lallai babu musu kam Affan shi ne ɗanku.." Abeey ya faɗa jikinsa a sanyaye. Ai babu shiri Gwani ya tashi daga rungumar da Mommah ta masa. Ya kalli Abeey da ya ji ya yi maganar. Bugun zuciyarsa tuni yanayin fitarsa ya ƙaru. Hatta idanunsa har sun soma chanjawa. Cike da fargaba yake kallan Abeey cikin son jin ƙarin bayani a kan abin nan da yake faɗa, da kuma abin da ya ji Mommah ta faɗa. Idan dai har ya ji da gaske me suke nufi da hakan?. Cikin ƙarfin hali ya soma faɗin

"Ban gane abin da kake faɗa ba Abeey.. Don Allah ka sanar da ni abin da na ji ka na ƙoƙarin faɗa.. Na kasa ganewa Abeey.. Ummeey me Abeey ke ƙoƙarin faɗa ne a wajen nan?" Ya ƙare maganar yana kallan Ummeey. Ai ko wuƙa aka saka a wuyan Ummeey ba ta tunanin za ta iya furta komai a irin wannan lokacin. Gaba ɗaya ta ruɗe, ganin abun take kamar mafarki. Ba ta yi tunanin ranar za ta zo mata a haka ba duk da yanda ta tsammaci zuwanta. Kawai se ta kautar da idanunta daga kan Gwanin, saboda yanda zuciyarta ta cigaba da karyewa. Ya girgiza kai yana ji kamar zuciyarsa za ta tsarwatse

"Babu wanda ze min bayanin abin da ke faruwa?" Gwani ya faɗa cike da sarewa. Se a lokacin sannan Daddy ya soma faɗin

"Ka kwantar da hankalinka Affan.. Har yanzu Malam shi ne mahaifinka, matarsa kuma ita ce mahaifiyarka, dan kuwa har abada ba ka da kamarsu.. Se dai yanzu ana magana ne a kan sanin wane ne kai tun ranar da ka zo duniya.. shi ya sa aka sakomu cikin maganar. Tabbas mu ne iyayenka Affan.." Daga nan Daddy ya shiga faɗa masa abin da ya faru tun lokacin da aka haifesu. Raba su da aka yi, da kuma yar da shi da aka yi a bakin gidan marayu. Ba Ummeey kaɗai ba, hatta Lulu ta jijjiga da jin abin da ya faru. Tsananin tashin hankali ya sanya tuni jikinta ya soma ɓari, ta shiga kallan Gwani kamar yau ta soma ganinsa. Ummeey kanta kallan Gwanin take yi har ma da Bad Man. Ita kanta ta shiga matuƙar mamaki, da tashin hankali bayan ta ji abin da ya faru. Ba ta taɓa tunanin za a iya samun mutane marasa imani kamar waɗannan a gaske ba se yau. Tausayin Affan ɗin ya kamata. Ba ma shi kaɗai ba har da mahaifiyarsa da ɗan uwansa.

Dumm haka Gwani ya ji kunnansa ya yi masa bayan gama saurarar abin da ya faru. Tuni kyawawan idanunsa sun kaɗa sun yi wani irin ja kamar garwashi. A hankali ya shiga zamewa kan tabarmar da Bad Man ke zaune ya zube a kanta. Ya runtse idanunsa yana jin wani jiri na kwasar shi. Kansa ya kifa a kan hannunsa cikin rashin sanin abin yi. Gaba ɗaya kansa ya kulle, gaba ɗaya komai ya tsaya masa cakk. Ummeey da Abeey ba iyayensa ba ne? Su ɗin ɗaukarsa suka yi daga gidan marayu? Ainahin iyayensa su ne waɗanda yake gani yanzu haka a zaune? Kawai se ya cigaba da ajje numfashi saboda yanayin yadda bugun zuciyarsa ke fita da sauri da sauri, kamar wanda ya yi tsere. Shi kam yau ya ma rasa a cikin wane fanni ze saka wannan rana. Sam ya kasa tunanin komai, ban da abin da ke faruwa yanzu babu abin da yake tunawa. Ummeey da Abeey ba iyayensa ba ne, iyayen Abokinsa Areef da suka haɗu babu daɗewa su ne iyayensa. Ya yin da shi kuma ya kasance ɗan uwan tagwaitakarsa. Shi ne kawai abin da yake tunani.

Shiru wajen ya ɗauka tamkar babu kowa a wajen, kowa kuma se ya samu damar yin magana da zuciyarsa. Ita dai Ummeey gaba ɗaya ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne, hankalinta gaba ɗaya na kan Affan ɗinta. Wanda zuwa wani lokaci da ta ga har yanzu be ɗago ba se ta ɗaga kai ta kalli ɗan uwansa da ta shaida fuskarsa ɗazun. Se yanzun ne ta gane dalilin da ya sa tun farkon jin muryar Areef ta kasa sukuni, dan kuwa bambancin kaɗan ne, shi ne shi Bad Man muryarsa a ɗan tsaitsaye take, ya yin da ta Gwani ke a kwance. Lol.. Dan kuwa kasancewarta haka ne ya sanya take kama da ta larabawa musamman idan yana larabci. Tun a lokacin ta shiga tunanin ko dai ɗan uwan Affan ne? Amma kuma idan ɗan uwansa ne me ya raba su? Ina iyayensu? Rashin bawa hakan muhimmanci ya sanyata watsarwa gaba ɗaya, se ta bar shi a ikon Allah ne kawai ya sa muryar tasu ke kama. Ita kanta Didi se a yanzu abubuwa da dama suka dawo mata. Ba tun yau ta soma jin kamanceceniyar muryar Gwani da Bad Man ba. Se dai fahimtar ba su da wata alaƙa ya sanyata watsar da lamarin dan ta san ba shi da muhimmanci. Ashe ba haka ba ne.. Ashe ikon Allah en biyu ne. Shi ya sa sau da dama ma se ta ga idan ya yi wani abun ya yi mata kama da wani. Ashe da ɗan uwansa Gwani ne.

Zuwa can Gwani ya ɗaga kansa da ke sara masa, daidai lokacin da Bad Man ya kalle shi. Kallan kallo aka shiga yi tsakanin Gwani da Bad Man, kowanne mamaki ya kasa barinsa, ta yanda har se da ya bayyana a kan fuskar kowannensu. Ganin abun suke kamar almara, su ɗin en biyu ne? Ashe sun kwashe lokaci suna tare ba tare da sun san cewa su ɗin jini ɗaya ba ne? Jini ɗayan ma kuma en biyu? Waɗanda suka rayu cikin ciki a lokaci guda, se da ranar zuwansu duniya ta yi ƙaddara ta raba su. Lallai ikon Allah ya wuce misali.

Har i zuwa lokacin Mommah ba ta sake cewa komai ba, ta bawa Affan ɗin lokaci ne ya gama fita daga shock ɗin da ya shiga yau ɗin. Ta riga ta san dole ne ƙwaƙwalwarsa ta kasa samun nutsuwa, ta kuma damu saboda jin wannan abu. Abun da be taɓa kawo yiwuwarsa ba se ga shi ya faru. A gefe guda kuma yau ɗin Mommah jinta take tamkar ta fi kowacce mace farin ciki a ranar. Jinta take daban, ta kasa bayyana wani irin farin ciki take ciki a ranar. Amma ita kaɗai ta san abin da take ji. Godiya ga Allah kam ta yi ta har ba ta san adadi ba. Daga zarar ta kalli en biyunta zaune a waje ɗaya tana kallansu kawai se ta lumshe ido, a kan laɓɓanta tace

"Alhamdulillah.." Idan dai ba ikon Allah ba wa ya isa ya yi mata wannan kyautar. A rana ɗaya ta gano tana da 'ya'ya har biyu bayan tsayin shekarun da ta ɗauka tana tunanin ba ta da ɗa ko ɗaya. Se ga shi a rana ɗaya ta haɗu da 'ya'yan nata. Cikin hikima kuma ta Ubangiji se ga shi wanda ya tashi a cikin gidan da take be samu tarbiyya kamar yanda wanda ya tashi a wani waje can daban ya samu ba. Wato ko haka ya ishi mutum ishara, Allah Ya sa mu dace. Ba tare da Ummeey ta yadda kowa ya ganta ba, bayan ta faki idanunsu ta ga hankalin kowa na wani wajen se ta miƙe ta faɗa cikin ɗaki. Tuni zuciyarta ta daɗe da karyewa, ban da bugu babu abin da zuciyarta ke yi. Ita kanta ta daɗe tana fatan idan dai har iyayen Affan ɗin na raye Allah Ya bayyanasu. Se dai yau ɗin da suka bayyana se ga shi zuciyarta ta kasa jurewa. Kawai se ta runtse idanunta tana barin kukan da ke ta taho mata hawayen suka shiga sauka a kan fuskarta. Ta riga ta san iyayensa sun zo dan su ɗauke shi ne, dan ta san tsawon shekarun nan da suka ɗauka yanzu haka suna mararin kasancewa ne da shi, musamman ma mahaifiyarsa. Se dai duk da haka tsoronta guda ɗaya ne shi ne yanda za a rabata da Affan ɗinta, ɗanta guda ɗaya ƙwallin ƙwal, ɗanta da take so take ƙauna kamar ita ta haife shi. Ita ta ma daɗe da manta cewar ba ita ta haife shi ba, kullum kallansa take yi a ɗan da ta tsuguna ta haifa. Se ga shi rana ɗaya wannan soyayyar na neman rabuwa a cikin yini guda, ba ta tunanin zuciyarta za ta iya jurewa..


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO70*


___Bayan shuɗewar wasu mintuna babu wanda ya sake cewa komai a tsakar gidan. Zuwa can Gwani ya miƙe ya shiga ɗakin Ummeey. A zaune ya sameta ta yi shiru, zuwa lokacin ta dena kuka, se dai ta yi shiru da alama tunani take yi. Ƙarasawa ya yi ya zauna a kan tabarmar. Ya saka hannunsa ya kamo na Ummeeyn. Ya kalleta da jajayen idanunsa yace

"Ummeey.." Kawai se ta ji zuciyarta ta sake karyewa. Ta lumshe idanunta tana buɗewa lokaci guda. Da ƙyar ta iya furta

"Affan.." Cikin son bata ƙwarin gwuiwa duk da shi ma nasa kaɗan ne yace

"Ummeey ki dena kuka haka nan.. Don Allah ki dena." Murmushin yaƙe Ummeey ta yi tana girgiza kai.

"Dole ne na yi kuka Affan.. Ya zan yi? Bar ni na yi kukan, duk da ba wai ina butulcewa Allah ba ne, a'ah kawai yana zuwa ne dan kansa ba da sanina ba. Ka ga kuwa yinsa ya zama dole." Shiru kawai ya yi, dan ya ma rasa wace amsa ze baiwa Ummeeyn. Kawai se ya cigaba da kallanta, tausayinta da nasa har ma da na Abeey na kama shi. Cigaba suka yi da zama cikin ɗakin kowa da abin da yake tunani. Zuwa can Abeey ya shigo ɗakin, shi ma kawai mazewa yake yi, amma shi kaɗai ya san abin da yake ji cikin zuciyarsa. Umarni ya basu da su fito waje, babu musu kuwa suka fito. Gyaran murya Daddy ya yi kafin ya soma magana.

"Wato har abada ba za mu taɓa samun abin da za mu biya ku da shi ba. Ba kuma mu da bakin da za mu iya gode muku a bisa wannan abu da kuka mana. Kun taimakemu, kun ɗauki Affan..yanzu ga abin da ya zama.. Yaron da har abada ba za ka dena alfahari da shi ba. Ni ma kuma kaina daga rana irinta yau zan soma alfahari da shi har na koma ga mahaliccina, kuma duk ta sanadiyyarku ce hakan ta faru. Allah Ya saka da alkhairi, Allah Ya biya muku dukkanin buƙatunku na alkhairi.." Addu'a sosai Daddy ya shiga zuba musu, Mommah na taya shi. Sun rasa da bakin da za su gode musu. A yanzu haka kuma sun ma rasa me ya kamata su yi musu wanda ze sanyasu cikin farin cikin da suka sanyasu ciki a yau.

"Affan ze cigaba da zama a wajenku kamar da.. dan duk da mu ne iyayensa amma mun yi kaɗan mu raba ku.." Daddy ya ƙare yana murmushi. Idan na ce Abeey ko Ummeey a cikinsu ga wanda ya fi farin ciki toh na yi ƙarya. Dan kuwa kowannensu wani shahararren farin ciki ne ya ziyarce shi.

"Ubangiji Allah Ya bar zumunci.. Allah Ya saka da alkhairi.." Makamantan waɗannan addu'o'in Ummeey da Abeey suka shiga yi. Mommah ta yi murmushi tana jin daɗin farin cikin da suka saka su a ciki, gefe guda kuma tana sake jinjina irin ƙaunar da sukewa Affan ɗin.

"Kun fi ƙarfin haka.. don Allah ku dena godiya.. Se dai alfarma ɗaya nake nema idan babu damuwa.. Ku ba ni Affan da matarsa na tsawon sati 1 ko da dangi ne su gan shi su ma." Duk se kunya ta kama Ummeey, wai Mommahn da kanta ke neman alfarma a kan ɗanta. Ta girgiza kai tana faɗin

"Ki dena irin wannan maganar don Allah.. wallahi duk se na ji na muzanta.."

"A'ah hakan shi ne daidai.. Dan har gobe ke ce za ki cigaba da amsa sunan mahaifiyar Affan."

"Ina godiya sosai.. Ina godiya.. Allah Ya bar zumunci." Ummeey ta faɗa muryarta a sanyaye. Se bayan isha'i sannan suka fara shirin barin gidan. Duk da tafiyar ta sati ɗaya ce kamar yanda Mommah ta faɗa, amma haka nan kawai ya ji ba daɗi, duk da ba wannan ne karonsa na farko na zuwa wani wajen ya kwana ba, se yake ji yau ɗin kamar yana shirin rabuwa ne da su Ummeey. Haka dai aka yi sallama cikin mutunci suka bar gidan. Daga Mommah har Daddy babu wanda ya ajje musu komai, dan ba sa so su ga kamar suna neman biyansu abin da suka yi ne. Dan haka kowanne yana tsara abin da ya kamata ya yi musu na musamman. Har ƙofar gida Abeey ya rakosu. Se da suka shiga mota dukaninsu kafin yace

"Allah Ya tsare.."

"Ameen.. Allah Ya saka da alkhairi.." godiyar da ya kasa dena fita daga bakinsu Daddy ta sake fita yanzun ma. Murmushi kawai Abeey ya yi yana juyawa ya koma cikin gida, shi kuma Daddy ya ja motar suka bar layin. Tun da suka fara tafiya Mommah na lura da 'ya'yanta da ta kasa ɗauke idanu a kansu. Sosai take ankare da Bad Man tun da suka soma tafiya. Duk da wani lokacin ya kan saci kallan Didi, Amma daga zarar ya ga za a iya ganinsa se ya basar yana wani muzurai.

"Zan yi maganinka ne Areef.." Mommah ta faɗa tana murmushi gami da girgiza kai. Lokaci ɗaya kuma se ta lumshe idanunta a kan laɓɓanta ta furta

"Allah Ya shirya min kai.." A yanzu ba ta da wani fata da ya wuce ta ga Areef ɗin ya shiryu, ya koma kamar ɗan uwansa, ko da ba duka ba ne. Fatanta Allah Ya sa lokacin shiriyarsa ne ya zo, Ya sa ɗan uwansa ya zam wani ɓangare da ze taimaka mata wajen ganin sun ceto Areef

Please Login or Register in order to submit comment