Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan kalleka na kare kaina ba duk lokacin da irin wannan tunanin ya zo maka ba. Se dai duk yanda na ke kame kaina ashe ba zan iya ba, na ɗauka idan na cigaba da kallan Iftihal tana shige maka ba zan ji komai ba. Se na ga ashe ba haka ba ne. Ban tabbatar da na daɗe da soma sonka ba se da Iftihal ta soma ƙoƙarin shiga rayuwarka. Ina tsoron kar ta ja ra'ayinka musamman saboda ni ɗin da na ƙi baka haɗin kai, shi ya sa zuciyata ta umarce ni da sanar da kai abin da ke cikinta. Ina sonka.." Ta ƙare tana cusa kanta cikin ƙirjinsa, dan ita kaɗai ta san kunyar da take ji lokacin da take furta waɗannan maganganun. Wata irin gingimarin ajiyar zuciya Gwani ya sauke, muryar Lulu na sake yin amsa kuwwa cikin kunnansa. Ji yake tamkar mafarki yake yi, hakan ba lallai ya taɓa faruwa ba. Se dai yanda yake jin amon sautin muryarta cikin kunnuwansa shi ne yake sanyawa ya ji tabbas fa da gaske ne hakan ke faruwa. Da gaske yau Lulu ce ke faɗin tana son shi, bayan tsawon lokacin da ya ɗauka yana sonta. Be ga amfanin maimaita mata tambayar da gaske take ba tun da yanzun ma tabbatar masa take bayan sanar da shi da ta yi a waccan ranar. Ya kai wajen minti 5 ba tare da ya iya cewa komai ba. Se daga baya kafin ya soma faɗin

"Har abada wannan tunanin ba ze taɓa shiga kaina ba. Ba ki ƙi ni dan ba ni da arziƙi ba, kawai ba kya sona ne. Babu kuma dalilin da ze sa na yi tunanin kin fara sona saboda wani abu. Kawai Allah Ya kawo abubuwan a lokaci ɗaya ne. Haƙiƙa na yi farin ciki, na yi farin ciki mara iyaka. Ina son ki kodayaushe, zan kuma cigaba da sonki har abada." Ya ƙare yana ɗago kanta ya zuba mata idanunsa da suka sauya kamar ba nasa ba. Lumsassun idanunta ta zuba masa ita ma tana ji tamkar yau ta soma ganinsa. Se dai har ya gama maganarsa ta kasa sake ko da yunƙurin sake cewa wani abun ne. Haɗe tazarar da ke tsakanin fuskokinsu ya yi
ya shiga sauke mata wasu uban kisses kamar ze cinyeta. Fuskarta yau kam ta ga sumba. Haka zalika bakinta da yau ɗin ya tabbatar me shi ya bayyana. Kai daga ƙarshe ma se jirkitata ya yi ta koma kan gadon, ya shiga aika mata da zafafan saƙonni cike da matsananciyar ƙaunarta.

Ni dai daga haka se na ce Asuba ta gari.




... A ɓangaren Bad Man kuwa hannunsa ɗauke da wani ƙaramin towel da ke ɗore a kan jiƙaƙƙiyar sumar kansa ya fito, sanye da boxer. Gaba ɗaya gargasar da ke kwance a jikinsa dukka a jiƙe suke se ka ce wanda ya bar ruwan da kansa dan jin daɗi kawai. Kai tsaye wajen mudubi ya wuce dan gyara kansa. Ƙamshin da ya soma shiga cikin hancinsa shi ne ya sanya shi zame towel ɗin da ke kansa ya ɗaga kai ya kalli cikin ɗakin. A kan gadon ya hangeta zaune ita ma kamar Lulu cikin wannan atamfar da mayafi. Lumshe idanunsa ya yi yana ɗan murmushi, wato be san abin nasa har ya kai haka ba, kenan har ta fara masa gizo? Ya tambayi kansa. Kamar ze share se kuma ya ajje towel ɗin gefen mudubin ya shiga takowa zuwa kan gadon. Takunsa da ta ji shi ne ya sanyata yin firgigit ta dawo daga tunanin da ta tafi. Daidai lokacin da ya ƙaraso ta ɗaga dara daran brown eyes ɗinta ta kalle shi. Se suka faɗa cikin nasa kyawawan matsakaitan idanun. Ita janye nata ta yi da sauri tana gyara zamanta a kan gadon. Ba ta ankara ba se jin motsinsa ta yi a gabanta durƙushe. Ɗaga idanu ta yi da niyyar kallan fuskarsa se idanunta suka sauka a ƙaƙƙarfan jikinsa da babu riga, se wannan baƙar gargasar da ta cika ƙirjinsa da kuma hannayensa. Farar ƙafarsa kawai ake iya gani saboda durƙuson da ya yi. Se inda ke a buɗe daga wajen ƙafarsa ya haɗe da jikinsa da babu riga. Cikin matuƙar tsoro da firgici zuciyarta ta buga. Kenan tumɓur yake? Ta tambayi kanta dan ita dai ba ta ga alamar akwai kaya a jikinsa ba. Ba ta yi aune ba se jin hannunsa ta yi kan hannunta. Ai ba ta san lokacin da ta yi wani tsalle ba tana sakin ƙara a gigice lokaci ɗaya tana runtse idanunta cike da tsoro. Cike da tabbatarwa da kansa lallai da gaske ita ɗin ce ba gizo take masa ba, tare kuma da mamakin abin da ya tsoratata ya miƙe da sauri ya yi amfani da hannunsa wajen riƙota ya dawo da ita baya. Sake runtse idanunta ta yi tana cigaba da ihunta jikinta na wani irin karkarwa lokaci ɗaya kuma tana ƙoƙarin fuzge hannunta. Ganin dai ta ƙi nutsuwa ne ya sanya shi janta da ƙarfi kawai ya haɗe bakinsu waje ɗaya. Abin da ya dakatar da ƙarar da ke fita daga sanyayyiyar muryarta kenan. Hakan ne kuma ya ba su damar zubewa a kan gadon har lokacin yana riƙe da ita a hannunsa, bakinta kuma na cikin nasa..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO79*


___ Ya ɗauki wajen minti 1 yana kissing lips nata kafin a hankali ya sake shi yana shafa jiƙaƙƙiyar sumar kansa lokaci ɗaya yana lumshe idanunsa. Wato duk sanda ya sumbaceta jinsa yake wani daban, wani irin taushi ne da bakin kamar wadda ke amfani da wani abun da ze sanya shi laushi. Da hannunsa ya sake yin amfani wajen riƙo fuskarta yana ɗagota dan ta kalle shi, lokaci ɗaya yana furta

"Me ya faru?" Ya faɗa yana jin yanda har lokacin jikinta ke rawa, ta kuma ƙi buɗe idanunta da ta runtse sosai. Kawai se ya jata ya mannata a ƙirjinsa cike da mamaki. Sosai bugun numfashinta ya cigaba da fita da sauri da sauri. Hakan ne ya sanya shi sake yi mata kyakykyawar runguma cike da fatan hakan ya dawo mata da nutsuwarta, ta kuma sanar da shi abin da ya faru. Shiru yanzun ma ba tace komai ba. Se ya yi shiru be sake cewa komai ba yana jin yanda take cigaba da sauke numfashi. A hankali kuma se bugun zuciyarta ya soma saituwa. Se a lokacin ne ta ɗan soma buɗe idanunta. Ta sauke ajiyar zuciya lokacin da ta lura da boxer ɗin da ke jikinsa, lokaci ɗaya tana taune laɓɓanta na ƙasa cikin baki. Ta lumshe idanunta tana sake sauke ajiyar zuciya. A hankali ya soma ɗago da kanta, ya tsayar da shi a saitin fuskarsa yana kallanta.

"Me ya tsorataki haka?" Ya faɗa yana lalubo ƙwayar idanunta da yake fatan ta shiga cikin tasa. Girgiza kai ta yi ba tare da ta ɗaga kai ta kalle shi ba. Se dai da ta ga babu mafita kawai ta ɗaga idanunta ta kalle shi, dan idan ta cigaba da kallansa se dai ta yi ta kallan jikinsa da ke a buɗe babu riga. Wanda duk ta kwashe danshin da ke jikin nasa a jikinta. Duk da be wani yarda ba, amma kuma tun da ta nutsu hankalinsa ya kwanta. Dan haka se ya zameta daga jikinsa, ya zaunar da ita kan gadon kafin yace a nutse.

"Ina fatan ganinki da na yi yana nufin kin amince kin dawo ɗakinki?" Ya ƙare yana murmushi cike da fatan abin da yake tunani ya kasance haka ɗin ne. Jinjina kai ta yi, dan fatanta ya bar wajen ko ta samu bugun zuciyarta ya koma daidai. Lumshe idanunsa ya yi kafin ya buɗe. Kamar ba ze ce komai ba, se kuma yace

"Kenan hakan na nufin kin amince ki na sona?" Ya tambaya yana kallanta. Se ta girgiza kai idanunta a kan fuskarsa. Wani irin bugawa da zuciyarsa ta yi shi ne ya sanya shi saurin dafe saitinta. Ya ƙurawa Didi idanunsa da suka ƙanƙance. Da muryarsa da ita kanta ta sauya yace

"Ki na nufin ba kya sona?" Ya tambaya cike da tsoro. Irin kallan da ta ga ya mata, da kuma ganin yanda cikin ƙanƙanin lokaci gaba ɗaya ya sauya, idanunsa kansu sun sauya kamar ba nasa ba, ya sanya ba ta san lokacin da ta yi saurin sake girgiza kai ba, daidai lokacin da ƙirjinta ya buga, ta kuma kaucewa idanunsa da ke kanta. Runtse idanunsa ya yi yana jin yanda bugun zuciyarsa ke tsananta. Murmushi ya yi irin murnushin yaƙen nan da ake cewa ya fi kuka ciwo. Ya sake zuba mata idanunsa kafin ya soma faɗin

"Shi kenan.. Zan cigaba da zama da ke har zuwa ƙarshen numfashina. Ko da kuwa ba kya sona tun da har kin amince za ki cigaba da zama da ni, kuma ni ina sonki." Wallahi ba ta san lokacin da ta ɗaga jajayen idanunta da suka cika taff da ƙwalla ta kalle shi ba. Ba ta taɓa tunanin abin da ze fito daga bakinsa ba kenan. Wani irin tausayinsa ya kamata. Se ta kasa ɗauke idanunta daga kansa. Jin ƙwallar na neman saukowa kan fuskarta ne ya sanyata saurin janye idanunta tana saka hannu ta ɗauketa. Se a lokacin sannan Bad Man ya miƙe, duk da yanda zuciyarsa ke cigaba da masa wani irin zafi hakan be hana shi faɗin

"Ki na buƙatar wani abu ne?" I zuwa lokacin barin hawayen ta yi ya sauka a kan kuncinta. Lallai ya yi chanjawar da ba ta taɓa tunani ba. Har ta nuna ba ta son shi a gaban idanunsa amma ya cigaba da nuna mata kulawa?

"Uhmmm?" Ya yi maganar yana ɗan leƙa fuskarta. Saurin saka hannu ta yi ta goge hawayen tana ɗaga kanta. Cikin rashin fahimta yace

"Kuka kike yi? Me ya saka ki kuka?" Ya tambaya cike da fatan ta ba shi amsa. Murmushi ta ƙaƙalo ta wanzar a kan fuskarta. Ta ɗan ja ajiyar zuciya kafin ta soma faɗin

"Ba kuka nake ba.. Ba na kuma buƙatar komai." Ƙura mata idanu ya yi kamar me son gano wani abu daga kan fuskarta. Ya ɗan sauke numfashi kafin yace

"Ban yadda ba.. Ki faɗa min idan wani abu ke damunki.." Sake girgiza kai ta yi cike da fatan ya ƙyale zancen a nan, ba se ya zurfafa bincike ba. Se kuwa ta ji yace

"Shi kenan.. amma idan na sake ganinki ki na kuka toh tabbas se kin sanar da ni abin da ke damunki." Ɗaga kai ta yi ta sake kallansa yau ɗin a karo na barkatai. Wato ko wacce magana ya yi da kalar sinƙin mamakin da ze sanyata ciki. Shi ma tsayawa ya yi yana kallanta, cikin zuciyarsa yana mamakin yanda yau ɗin ba ta jin kunyar kallansa ko kaɗan. Se kuma kunya ta kamata ta yi saurin saukar da idanunta cikin basarwa. Ya ɗan fesar da iska daga bakinsa yana fatan damuwar da yake ji yanzun ta ragu tun da dai yana tare da Didin. Komawa ya yi gaban mudubin, shiryawar da be yi ta a nutse ba kenan, kawai ya saka kaya ya feshe jikinsa da turarukansa masu ƙamshi.

Ganin da ta yi yana gyara gadon ne ya sanya ta miƙewa daga inda take zaune. Ta ƙarasa, ba tare da tace komai ba ta kama tattausan bedsheet ɗin ta shiga gyarawa cike da ƙwarewa. Be lura da tahowarta ba se ganinta kawai ta yi ta soma gyarawar. Se ya miƙe hadda wani sauke numfashi irin wanda ya sha aikin wahalar nan, dan da ma karanbani ne kawai ya sanya shi gyara gadon ba don ya iya ba. Tass tass haka ta gyara gadon. Se a lokacin ta saka hannu ta ɗauki ɗaya daga cikin pillown da ke kan gadon tana shirin wucewa ta jiyo muryarsa yana faɗin

"Ina za ki je?" Dakatawa ta yi tana sake riƙe pillown sosai kamar wanda za a ƙwace.

"Bacci nake ji." Ta faɗa tana ɗan rufe idanunta da ke ɗauke da bacci sosai.

"A ina za ki kwanta ne?" Ya tambaya cike da mamaki yana kallanta. Kujerar da taso daga kanta ta nuna tana ɗan cuno baki. Ya bi kujerar da kallo kafin ya maido da dubansa kanta yana jinjina kai.

"Lallai!" Ya faɗa a kan laɓɓansa. Soma takawa ya yi zuwa inda take. Lura da hakan ya sanyata sake riƙe pillown da kyau. Hannu ya saka ya riƙo pillown. Se ta ɗaga kai da sauri ta kalle shi. Narai narai ta yi da fuska ganin da gaske karɓa ze yi. Tace kamar za ta yi kuka

"Don Allah kwanciya fa zan yi." Be ce komai ba ya karɓe pillown, dan ya fahimci manufarta. Ajje pillown ya yi kan gadon kafin ya dawo da dubansa kanta yace

"Za ki kwanta kan gadon ne ko na kai ki da kaina?" Kallan gadon ta yi kafin ta ɗauke kai tace

"Na bar maka." Murmushin gefen baki ya yi kafin yace

"Ba na so.. Mu je ki kwanta ko kuma na.." Tun kafin ya ƙarasa maganar ta juya da sauri saboda ganin da ta yi yana maganar yana matsowa kusa da ita. Hawa kan gadon ta yi da sauri ta kwanta. Ta ja ƙaton blanket ɗin da ke ajje gefen gadon ta kima a kanta. Be san sanda dariya ta ƙwace masa ba.

"Wannan yarinya.." Ya faɗa yana girgiza kai. Ya ɗauki fiye da awa ɗaya zaune cikin ɗakin bayan kwanciyarta yana karatun Alqur'ani. Bayan ya idar ya shiga istigfari. Abin da ya zamar masa jiki kenan yanzu. Kullum kafin ya kwanta se ya yi. Haka kuma duk lokacin da ya idar da Sallah ma se ya yi, saɓanin da da se ya kwana fiye da 3 ma be yi karatun ba. Ninke daddumar da ya tashi daga kanta ya yi ya maidata inda ya ɗauka kafin ya kalli kan gadon. Fuskarta a buɗe take, ya yin da ilahirin jikinta ke a rufe ruff. Bacci take hankalinta kwance, kai ba za ka ce akwai abin da ke damunta ba. Ya lumshe idanunsa yana ji kamar kar ya dena kallan kyakykyawar fuskarta. A hankali ya ƙarasa ya hau kan gadon. Kai tsaye hannu ya saka ya yaye bargon da ta lulluɓa da shi ɗin. Dan garin ba zafi ake ba haka kuma ba sanyi ake ba. Gyara mata kwanciyar ya yi, saboda yanda ta kwanta ɗin a takure. Ji yake tamkar ya barta a jikinsa ko da ze samu baccin yau ɗin ya kasance na daban, ya yi baccin da ya daɗe be yi irinsa ba. Se dai ba ya so ya zama sanadin hanata bacci, hakan ne ya sanya shi komawa gefenta ya kwanta. Se dai duk da haka kasa ɗauke idanunsa ya yi daga kanta. Cikin ransa yana ji damuwar da ke cikin ransa kaso me yawa na raguwa daga cikinta.


Washegari.. Sauri sauri take ta fito daga wankan ta shirya kafin ya shigo ɗakin. Dan tun ɗazu take so dama ya fita, amma be fita ba se yanzu. Hakan ne ya sa tana gamawa ta fito, kai tsaye wardrobe ta nufa inda ɗazun ta gan shi ya jera mata kayanta ciki. Daidai lokacin ya shigo cikin ɗakin hannunsa ɗauke da babban tire, wanda ya karɓa yanzun nan daga hannun Baba Atine.

"Good morning my dear.." Ya faɗa yana ajje abun hannunsa a inda ya dace. Ita dai kawai se ta bi shi da kallo ganin fuskarsa ɗauke da annuri kamar wanda aka yi wa albishir da gidan aljanna. Se dai ba ta sani ba duk farin cikin dawowarta cikin rayuwarsa ne ya kasa ɓoyuwa. Se da ya ajiye kafin ya juyo inda take tsaye ta kasa aiwatar da komai. Cikin kulawa yace

"Kin tashi lafiya?" Ya faɗa yana zuba mata idanun nan nasa. Duk se ta dibirbirce ta ɗan soma gyara tsayuwarta. Murmushi ya yi yana kallan cikin wardrobe ɗin. Hannu ya saka ya ɗauko wata riga coffee colour da adon milk colour a jikinta.

"Zan iya taimaka miki?" Ya faɗa dan ba ya so ya yi wani laifi kuma. Da sauri ta girgiza kai tana saka hannu ta riƙo rigar hannun nasa.

"Zan saka don Allah.." Ta faɗa a marairaice. Sakar mata rigar ya yi yana yin gefe ya bata hanya wai dan ta wuce. Da sauri ta ɗaga ƙafa dan matsawa daga wajen ko ta samu ta saka rigar a nutse. Se dai yanda ta tafi ɗin da sauri, ya sanya ba ta lura da abin da ke gabanta ba, ta kuwa yi tuntuɓe, se kawai ta yi baya kamar za ta faɗi. Daidai lokacin da shi kuma ya zo zama a kan gadon se kawai ganinta ya yi za ta zube a ƙasa. Ya yi azamar tareta da hannayensa, se kuwa suka koma kan gadon gaba ɗayansu. Ajiyar zuciya gaba ɗayansu suka sauke. Didi ta lumshe idanunta dan ta riga ta gama saddaƙarwa a ƙasa za ta jita. Miƙewa ta zo za ta yi, ya saka hannu ya maidata, yana juyo da ita sosai ta koma kallansa.

"Kin gani ko jikinki be amince ki yi nisa da ni ba." Ya faɗa yana kafeta da idanunsa. Duk da ta ji abin da ya faɗa ɗin, amma ta basar tana kuma sake yunƙurin tashi ya sake yin baya, wanda hakan ya bata damar sake ƙarasa faɗowa jikinsa gaba ɗaya. Ya saki wani miskilin murmushi yana kallan fuskarta da ta yi rau rau kamar za ta fashe da kuka.

"Don Allah ka sake ni."

"Na ƙi ɗin." Ya faɗa yana kwaikwayon yanda ta yi maganar a shagwaɓe. Ɗauke kai ta yi, dan ta lura so yake ya din ga kunnata. Ba ta ankara ba se ji ta yi ya zame rigar hannun nata. Ya gyara mata zama a jikinsa. Fahimtar abin da yake ƙoƙarin yi ne ya sanyata saurin dafe hannunsa tace

"Don girman Allah ka sake ni.." Ta faɗa tana kallansa da narkakkun idanunta. Sauke numfashi ya yi tuna cewar har yanzu fa shi me laifi ne. Daga dawowa jiya ya kamata ya kama kansa kar ta kwaɓe masa. Hakan ne ya sanya shi faɗin

"Shi kenan.." Ya faɗa yana miƙewa bayan ya saki rigar. Ita kuma ya zamar da ita daga jikinsa ta koma kan gadon. Se a lokacin Didi ta sauke ajiyar zuciya. Se da ta tabbatar hankalinsa ba ya wajen kafin ta saka rigar.

Mamaki ya cigaba da bata, lokacin da ya tasata a gaba ta ci abinci. Abin da be sani ba ita duk kasa sukuni take idan yana wajen. Haka dai ta haƙura saboda yanda ya takura ta tsakuri abincin saboda idanunsa da suka hanata sakat. Sosai ya cigaba da kula da duk wani motsinta. Ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ta yi se ya kalleta yace

"Ki na buƙatar wani abu ne?" Ita dai binsa kawai take yi da kallo. Yanda ya chanja cikin ƙanƙanin lokaci se ta ga kamar ba shi ba. Haka duk yanda take ta babbasarwa dan kar ya gane ta haƙura amma se da ta sassauta saboda abin da yake yi. Kwata kwata a ranar be fita ko nan da can ba. Idan ban da masallaci da ke fitar da shi babu inda yake fita, yana nan zaune da ita yana kula da ita. Dan gani yake kamar idan ya yi nisa da ita ze dawo ne ya tarar ta sake barinsa. Tana jinsa ɗazu ma yana waya da Kaseem ɗin da yanzun ta gano ɗan uwansa ne, a kan ba ze samu fita ko ina ba saboda wani ƙwaƙwƙwaran dalili. Ita mamaki yau ɗin nan ya kusan kasheta. Yau ita ce ƙwaƙwƙwaran dalilin da ze hana fita? Lallai Allah me iko.


.. A kwanaki uku da ta yi tare da Bad Man cikin ɗaki ɗaya, se da ta fahimci lallai da gaske ya sauya. Ya zama kamar ba shi ba. Idan ya yi wani abun har mamaki yake bata. Wata irin kulawa yake bata ta musamman. So yake ya fanshe rashin kulawar da be baya ba tun auransu. Komai take ji yake kamar ya maidata ciki. Ita kanta har mamakin irin soyayyar da yake nuna mata take yi. Shi kansa wani sa'in ya kan zauna ya yi ta mamakinsa shi ɗaya, se kuma idan ya tuna abin da ya yi da kuma yanzu abin da ke faruwa, se ya ga kamar Allah ne ya sakawa Didi ta hanyar jarabtarsa da matsanancin sonta, ya yin da ita kuma ta nuna ba ta yinsa. Sosai take lura da duk wani motsinsa. Ta riga ta san idan wani abun ze sha ba kunyarta ze ji ba tun da hakan ta faru a da. Se dai yanzun ma kafin ya fita ana daɗewa. Idan ba abu muhimmi ba ma ba ya matsawa ko nan da can daga cikin ɗakin. Yana nan kusa da ita yana kulawa da ita. Dan ya ɗauki maganar Mommah, idan dai har kulawa na janyo soyayya toh In Sha Allah za ta jawo masa a wajen Didi. Ze zage damtse, ze yi aiki tuƙuru da jiki da hannayensa, ko da Allah ze dube shi ya sauƙaƙa masa ya sanya Didi ta karɓi soyayyarsa ko ze samu su fara gina rayuwarsu.



... Ƙarar da ta ji wayar ta sake yi ne a karo na barkatai shi ne ya sanyata ɗaga kai ta kalli inda wayar ke ajje. Ta ɗan sauke numfashi cike da ƙosawa da yanda ringing ɗin ke katseta daga zarar ta soma karatunta. Ajiye littafin ta yi ta miƙe ta sake kallan ƙofa ko za ta ga shigowarsa, se dai har yanzu shiru. Kawai se ta ƙarasa inda wayar take ta sanya hannu ta ɗauka. Ba tare da ta damu da ganin me kiran ba ta ɗauka ta kara a kunnenta. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya aka sauke daga ɗaya ɓangaren. Kafin a kai ga cewa komai Didi tace

"Ba ya kusa.."

"Don Allah.." Muryar wata budurwa ta daki dodon kunnenta. Zame wayar ta yi da nufin ajjeta inda ta ɗauketa tun da dai ta riga ta faɗi abin da za ta faɗa. Daidai lokacin da ya ƙaraso wajen. Tana jin yanda bugun zuciyarta ke ƙaruwa amma ta basar, tana juyowa ta gan shi. Se ta fasa ajiye wayar ba tare da ta kalle shi ba ta miƙa masa, a sanyaye tace

"Ana kiranka.." Binta ya yi da kallo yana ƙoƙarin fahimtar yanayinta. Kafin daga bisani ya mayar da dubansa kan wayar da take miƙa masa. Hannu ya saka ya karɓa kawai, ba tare da ya kalli me kiran ba ya kara a kunnensa.

"Salamu Alaika kyakykyawa.." ɗin da aka faɗa cikin wayar shi ne ya sanya shi sauke wayar daga kunnensa cike da mamakin jin muryar mace, se kuma ya kalli me kiran nasa. Kamar yanda ya tsammata kuwa baƙuwar number ce, abin da ya sanya shi jan tsaki kenan yana katse kiran ya jefa wayar inda ta ɗaukota. Duk da yanda ransa ke neman ɓaci, hakan be hana shi juyawa ya kalli Didi ba. Duka idanunta na kan littafin da take karantawa. Se dai duk yanda ta yi ƙoƙarin ɗauke hankalinta daga kansa zuwa kan littafin abin ya citira. Ya kafeta da idanunsa kamar wanda ya soma ganinta a yau. Soma takowa ya yi zuwa inda take, har zuwa lokacin be dena kallanta ba. Gaba ɗaya se ta kasa sukuni saboda yanda take jin idanunsa a kanta. Hakan ne ya sanya ta fara ɗan gyara zama kamar wadda ke shirin tashi daga wajen. Se dai ko kaɗan yanayinta ne chanja ba daga yanda take karatu tun ɗazu.

"Wai ko kaɗan ba kya kishina?" Ya yi tambayar a raunane, kai se ka rantse ba Bad Man ba ne. Tambayar da ta sanyata ɗaga kai ta kalle shi kenan cikin mamaki, dan ita ma se da ta yi tantamar shi ɗin ne ko ba shi ba. Ba ta san amsar da za ta ba shi ba, idan kuma ta cigaba da zama toh tabbas yanayinta ze iya fallasata. Dan haka ta miƙe ba tare da ta kalle shi ba tana ƙoƙarin barin wajen ta ji ya sake faɗin

"Da gaske ne kenan abin da na faɗa? Rashin son nawa har ya kai haka? Wata ta kira ni a waya babu damuwa ko kaɗan kika sanar da ni kika kuma cigaba da harkarki ba tare da kin damu ba.. Shin ni kuwa me na miki? Wace kalar tsana kika min haka? Wane laifi na miki da na cancanci irin wannan tsanar? Wane irin rashin so ne wannan?" Kawai kafe shi

Please Login or Register in order to submit comment