Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba.

"Ashe ba zan taɓa samunki ba Afrah.. Wallahi ina sonki.. Ina sonki.." ya faɗa sanda ya kifa kansa a kan steering motar, zuciyarsa na cigaba da zafi. Da ƙyar ya iya tashi ya kunna motar ya tasheta. Cikin ƙarfin hali ya soma driving ɗin zuciyarsa cike fall da tunani.




... "Hero wai me kake nufi ne don Allah?" Shiru Hero ya sake yi a karo na biyu.

"Kace min wani abu mana. Ya ake ciki? Ni dama ban so ka shigo da wani cikin wannan al'amarin ba.. yanzu ga shi komai ya caɓe mana.. kai kanka ma baka san abin da ke faruwa ba.."

"Kin ga Ladi.. Ki ɗan sararamin na yi tunanin abin da ya kamata. Ina ta kiran layinsa tun tana shiga yanzu ma ta dena shiga. Me kike tunani? Kika sani ko ta rutsa da shi ne? Ni daga yanzu ma na dena kiransa kada a gane numberta, idan ma wani abun ne ya rutsa da shi daga baya a zo a binciko ni haka kurum.."

"Toh yanzu me kake nufi?" Ladi ta faɗa tana kallansa

"Mu jira nan da kwana 3 haka, idan dai ban ji daga gare shi ba, toh dole zan san abin yi.."

"Anya kuwa ba zan tura Abida ta je gidansu yarinyar nan ta duba min abin da ke faruwa ba?" Dariya Hero ya yi yana girgiza kai. Ya saki tsaki kafin yace

"Toh maza aikata tunda man kanki ya tsotse.." ya faɗa yana watsa mata wani kallo. Ajiyar zuciya ta sauke dan ta fahimci gatse Heron yake mata, tace

"Shi kenan.. Bari na jiraka.."

"Ya dai fi miki.."



... Kai tsaye ɗakin Daddy suka wuce gaba ɗayansu. A babban parlournsa suka zauna.

"Za ka zauna anan har ka samu ka gama warwarewa gaba ɗaya.." Daddy ya faɗa yana kallan Bad.

"Bana jin komai yanzun.." ya faɗa bayan ya ɗan lumshe idanunsa ya kuma buɗe su a lokaci ɗaya.

"Duk da haka.. Amm zaka iya tuna dalilinka na zuwa gidansu yarinyar nan?" Daddy ya faɗa yana kallansa

"Yarinya?" Ya tambaya sanda fuskarsa ke a tsuke.

"Gidansu yarinyar da ka je ka faɗi a can.. Mene ne ainahin dalilinka na zuwa." Shiru Bad Man ya yi na tsawon sakanni be ce komai ba. Shi sam ya ma manta da abin da abin da ya faru, idan ba yanzun da Daddy ya yi maganar ba.

"I don't know who is she.. ban san waye ya aikota ba. She slapped me! Dats why na bita har gidansu dan na san wanda ya aikota. Na kuma mareta a gaban en gidan nasu, saboda su san babu abin da zasu iya min.."

"Mari kuma Boy? Wace ce ita? Waye ubanta a ƙasar nan? Me take taƙama da shi da har ta mareka? Wa take taƙama ze tsaya mata?" Mom ta faɗa a fusace. Shi kuwa Daddy kallansa kawai yake yi, tunda ya fara maganar har ya ƙare. Cikin takaici yace

"Kafin ka je gidan ina ka fara zuwa? Da wa kuma haɗu?"

"Hero!" Numfashi Daddy ya ja ya ajje. So yake ya ji duk abin da ya faru, hakan ne ya sanya shi faɗin

"Tare kuka je gidansu yarinyar da shi?"

"Yeap.. but a waje ya tsaya.." Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa.

"Koma ka zauna.. bamu gama maganar ba.."

"Amma na gaji Dad.." Be bi ta kan abin da ya faɗa ba yace

"Kafin ku tafi.. ba ka sha wani abu ba?"

"Wani abu? Lyk how?" Ya faɗa yana kallan Daddyn. Se kuma yace

"Ohh.. yes.. but juice ne kawai.."

"Waye ya baka?" Daddy ya katse shi da faɗin hakan.

"Dad.." ya faɗa cike da ƙosawa.

"Ka bani amsa.."

"Hero.." ya faɗa a taƙaice. Runtse idanunsa Daddy ya yi, ashe ba a banza ba ya raba Areef ɗin da Hero. Dama tun farko be masa ba, so be ɗauka ma suna tare ba tun bayan barinsa Nigeria.

"Yallaɓai wai tambayoyin nan duka na mene?" Mom ta faɗa tana kallan Daddy.

"Idan zaki iya saurara u're welcome. Idan kuma ba zaki iya ba za ki iya bamu waje.." Jin abin da Daddyn ya faɗa ne ya sanya ta yin shiru kawai. Dan ta ga alama a fusace Daddyn yake.

"Ka san me yasa na rabaka da yaron? Baya sonka da alkhairi.. ya zuba maka wani abu cikin lemon, domin idan ka je gidansu yarinyar ka aikata mata abin da be kamata ba.."

"What?" Bad Man ya faɗa yana kallan Daddy ransa a mugun ɓace. Angry face ɗinsa a haɗe kamar hadari.

"Me na aikata Dad? Pls tell me.." ya yi maganar ɓacin ransa na daɗuwa cike da ƙosawa da son jin amsar da Daddyn ze ba shi. Se da Daddy ya sauke numfashi sannan yace

"Allah ya tsare.. babu abin da ya faru.." Wata ƙatuwar ajiyar zuciya Mom dake gefe ta sauke, yayin da Bad ya dafe kansa yana tunanin dalilin da ya saka Hero ɗin ze yi masa haka.

"Se dai dalilin zuwanka gidan da kuma faɗuwar da ka yi zuwa kaika asibiti yasa mutane sun ganka.. sun kuma ganni, sun kuma ga Mahaifiyarka.. Idan dai zaka iya tunawa ko da zamu fito daga cikin asibitin nan, idanun mutane a kanmu suke.. Ita kanta yarinyar kuma tare aka kawoku asibiti saboda bugewar da ta yi a kanta, wanda hakan ya janyo mata ta suma. Mutane kuma duk sun ga sanda hakan ta faru. Sanin kanka ne bana son duk wani nau'i na zargi, ba kuma na san kai kanka ka shiga cikin waɗanda ake zargi, dan kuwa zargi mugun ƙulli ne.. Wannan dalilin ne ya sanya ni aura maka yarinyar." Cikin matuƙar mamaki, tashin hankali Mom tace bayan ta miƙe tsaye

"Aure kuma Abubakar? Ka aurar min da ɗa ba tare da izinina ba? Ko kuwa dai ka faɗa ne kawai dan nishaɗi?" Mom ta faɗa a fusace, dan matuƙa ranta ya ɓaci da maganar Daddyn. In dai kuma har da gaske abin da ya faɗa gaskiya ne akwai babban tashin hankali a cikin gidan. Yanda ta kira sunan shi kai tsaye, da yanda take iƙirarin ya aurar mata da ɗa ba tare da izininta ba ya sanya shi yi mata shiru idan ta gama ya kulata. Jin tana neman ɗorawa ne ya sanya shi katseta da faɗin

"Ki nemi waje ki zauna.. Wannan abun da kike babu abin da ze sauya, dan kuwa kamar yanda kika ji ne na ɗaurawa Areef aure da yarinyar nan.." Se a lokacin Bad ya fahimci ma abin da Daddyn ke faɗa. Ya fahimci me Daddyn ke ƙoƙarin faɗa. Se dai ya san Daddyn nasa ƙalau yake, ya kuma san mutumin arziƙi ne. Se dai a yau yana da yaƙinin wani abokin nasa shi ma ya zuba masa wani abun cikin lemo ya sha, shi yasa yake irin wannan maganar da har abada ma baya tunanin zata taɓa faruwa. Se da ya ɗan sake lumshe idanunsa sannan ya soma miƙewa a kan ƙafafunsa.

"Ina zaka je? Dawo ka zauna, ka kuma sake tabbatar da abin da kunnuwanka suka jiye maka.." Daddy ya faɗa yana kallan Bad Man dake ƙoƙarin barin ɗakin. Juyowa ya yi, kawai se ya tsaya yana kallan Daddyn kamar wanda ya ga sabuwar halitta. Jira kawai yake Daddyn ya sake maimaita abin da ya faɗa ɗazun sannan ya san abin yi.



... "Kama gidan haya ba mafita bace.. Saboda tsaro gwara a yi abin da ze yiwu.." Abeey ya bawa Ummeey amsa.

"Toh kai Affan.. ya kake ganin za a yi?" Ummeeyn ta faɗa tana kallansa. Shiru ya yi na ɗan wani lokaci. Duk da baya jin daɗin maganar, amma ya zama dole ya tsaya a yi maganar, ko dan farin cikin iyayen nasa.

"Abeey ina ganin kawai a gyara mata ɗakin can se ta zauna a ciki.."

"Ja'iri.. ce maka aka yi er aiki ce aka kawo? Da za a bata ɗaki ita ɗaya? Malam me ze hana kamar yadda ya faɗa ɗin a gyara ɗakin nan, duk da dai ba girma gare shi ba, amma ko yaya ne dai za a samu abin da ake so. Idan yaso se a shigar da shi cikin ɗakin Affan.. A samu ko ɗan fenti ne a yi, se ta zauna anan ɗin koh?" Ummeey ta ƙare maganar tana kallan Abeey..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO25*


___"Ka fahimci abin da na faɗa? Za ka iya tafiya.."

"Idan shi ya gane, ai ni ban fahimta ba. Me kake so kace ne? Wallahi har yanzu na kasa gane abin da kake nufi da ɗana.." Mom ta faɗa tana ji kamar ta saka ihu.

"Waye mahaifin Areef..?" Daddy ya faɗa yana kallan Mom.

"Kai ne..!!"

"Toh na ɗaura masa aure. Period.." Daddy ya faɗa a ɗan fusace yana dakatawa. Se kuma ya ɗora da

"Za ki iya fice min daga ɗaki.."

"In je ina? Babu inda zan je se ka tabbatar min da gaske wannan abun da kake faɗa."

"Tabbatarwa kike buƙata? Toh ki jira ranar juma'a za ki tabbatar.. Kada ki sake furta mun komai cikin ɗakin nan, idan ba haka ba wallahi zan saɓa miki.." Shiru Mom ta yi tun bayan da Daddyn ya gama magana. So take ta ƙara cewa wani abu, amma kuma ba ta so ta kai Daddyn bango. Hakan ne ya sanyata kallan Bad Man daidai lokacin da yake faɗin

"So da gaske aure ka min Daddy? Se kace wasan yara?" Ya faɗa sanda jijiyoyin kansa suka tashi har a kan goshinsa. Idanunsa suka sauya kala, haka zalika muryarsa ma se da ta sauya, sannan kuma yana kallan Daddyn ne cikin ido dan sake tabbatar da abin da yake faɗa ɗin.

"Areef.. Kada ka biyewa mahaifiyarka, ka yi ƙoƙarin ƙuntata min ko kuma bijire min. Kai ba mace bane ballantana ka yi tashin hankali dan na aura maka yarinya."

"But kana magana ne fa a kaina Dad.. Ta yaya zan yi shiru?" Ya yi maganar sanda ya kai hannunsa kan kujerar dake gefe ɗaya ya yi watsi da duk wasu abubuwa da ke kai. Nan take suka zubo daga kai, waɗanda suke na glass suka tarwatse a wajen. Be haƙura ba ya ɗan runtse idanunsa sannan yace

"Meye wani aure? Meye amfaninsa? Har ka yi min shi without my knowledge.. phhuuuu.." ya ƙare yana fidda wata zazzafar iska daga bakinsa.

"Hey Areef.. Kada ka manta wanda kake tare da shi.." Daddy ya faɗa yana kallansa, yana riƙe kansa dan kar ya mare shi.

"Ko kuwa dai kamar yanda Mom ke tunani u're just joking.." ya faɗa yana buɗe idanunsa a kan Daddyn.

"Wait and see.."

"Till when..?" Ya yi saurin katse Daddyn da faɗar hakan. Shiru Daddy ya masa kamar be ji abin da ya faɗa ba. Yana shirin sake cewa wani abu Daddy yace

"If u dare say something again, I will definitely deal with u wallahi.. Get out.." ya faɗa yana nuna masa hanya. Mom dake zaune har lokacin bata sake cewa komai ba, ta kalli Bad da har lokacin huci yake fitarwa.

"Dad.." ya faɗa da ɗan ɗaga murya.

"I said get out.." Daddy ya faɗa ba tare da ya kalle shi ba. Juyawa ya yi a fusace, ya sake dukan wani glass dake gefensa da ƙarfin gaske. Nan take ya fashe lokaci ɗaya kuma jini na soma zuba daga hannunsa. Duk kuma da hakan, be damu ba, be kuma bi ta kan hannun ba ya cigaba da takawa se dai yanzun cike da sassarfa, farar fuskarsa ta haɗe waje ɗaya ta sake yin ja, haka zalika idanunsa ma sun yi ja kamar waɗanda aka watsawa garwashi. Cikin sauri Mom ta miƙe tana faɗin

"Na shiga uku ni Salma.." ta faɗa tana bin bayan Bad da ya hau haɗaɗɗen step ɗin dake cikin ɗakin. Cike da kuzari yake haɗa step har zuwa sanda ya gama hawa, kawai ya faɗa cikin wani ɗaki. Mom ba tayi ƙasa a gwuiwa ba wajen bin bayansa. Runtse idanu Daddy ya yi bayan tashin Mom daga wajen. Dama kowa akwai tasa kalar ƙaddarar, shi kuma ɗansa ne ƙaddarar tasa. Duk da yanda yake ƙoƙari da jajircewa wajen bawa Areef ɗin tarbiyya da sakawa rayuwarsa ido, da tsawatar masa a kan duk wani abu da be dace ba, hakan be sanya shi zama kamar kowanne ɗa da uba ze yi alfahari da shi ba. Be zama cikin 'ya'ya masu biyayya ba, se me jayayya dasu, me kuma iya maida musu da martani. Ba dan shi ɗin tsayayye bane, gefe ɗaya kuma yana haɗawa da addu'a, da be san yanda zata dinga kayawa tsakaninsa da Areef ɗin ba. Se dai yana fatan wannan auren ya zamo sanadiyyar shiryuwarsa. Ko kuma Allah ya kawo wata hanyar da za ya gyaru ya zama mutumin arziƙi wanda kowa ze iya alfahari da shi.

"Allah ka shiya min yaron nan.." ya faɗa a hankali kuma a sanyaye.


... A ɓangarensu Twins kuwa tun bayan da kowaccensu wahalallen bacci ya ɗauke su, basu farka ba se bayan shuɗewar wasu awanni sannan Lulu ta soma buɗe jajayen idanunta da suka kumbura kamar wadda ta yi fama da ciwon ido. Ɗakin ta shiga bi da kallo kamar wadda ta ta soma ganinsa a yau ɗin. Tamkar wadda ake faɗawa se ta shiga tariyo duk abin da ya faru. Ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske, kada dai ace ba mafarki take yi ba? Juyawa ta yi ta kalli Didi dake gefenta tana bacci, tana sauke numfashi a hankali, wanda hakan ke nuna mata tana bacci ne cikin kwanciyar hankali. Ashe mafarki take yi bata sani ba? Se ta lumshe idanunta, se dai duk da yadda ta fahimci mafarki take yi hakan be sa jikinta dake a sanyaye komawa daidai ba. A hankali ta sauko daga kan gadon daidai lokacin da Ammi ta shigo cikin ɗakin

"Kin tashi?" Ammi ta faɗa tana kallanta. Ba ta yi tsammanin ma Lulun zata iya faɗin wani abu ba saboda tashin hankalin ɗazu amma se ji tayi tace

"Ehh Ammi.." Cikin matuƙar farin ciki da fatan shiryuwar ɗiyar tata tace

"Toh ki watsa ruwa a jikinki za ki ji daɗi sosai.."

"Tohm.." ta amsa da hakan tana shigewa cikin toilet ɗin lokaci ɗaya tana sake tuna wannan mummunan mafarkin da tana tunanin da bata tashi daga shi ba dab zuciyarta take da bugawa, mafarkin da ke ƙoƙarin yi mata shamaki da farin ciki na har abada. Babu daɗewa ta fito daga toilet ɗin tana mamakin yanda idanunta suka kumbura, duk da yanda zuciyarta ke son hararo mata kamar abin nan da ya faru gaskiya ne, hakan be hanata dannewa ba, tana sake ƙaryata kanta da kuma sake tabbatarwa da kanta cewar mafarki ne ta yi. Babban abin da yasa ta sake yadda mafarkin ne shi ne yanda ta ji babu wanda ya sake yin maganar, daga Ammi har Abba. Ita dai Didi se ta zama tamkar mara lafiya, miskilancinta ya ƙaru, se dai ta nemi waje kawai ta zauna ta yi shiru, tana tunanin makomarsu ita da er uwarta.


... "Didi Abba na kiranku.." Little ya faɗa tun kafin ya ƙarasa shigowa cikin ɗakin.

"Tohm.." suka amsa a tare suna miƙewa. Tare suka fito daga cikin ɗakin zuwa parlour, inda Abba da Ammi ke zaune. Suka ƙarasa suka nemi waje suka zauna a ƙasa.

"Abba ga mu.."

"Yawwah.." Abba ya amsa da hakan yana gyara zamansa. Se da ya ɗan yi gyaran murya sannan ya soma faɗin

"Kamar yanda na shaida muku ne tun ranar farko, toh yau ma zan maimaita muku, na ɗaura muku aure.. Se dai wannan kiran ya sha banban da wancan, dan kuwa wannan ɗin ina so ne na sanar daku cewar gobe idan Allah ya kai mu za a ɗauki kowacce a miƙata gidan mijinta.. Ina fatan ba zaku bani kunya ba, za kuma ku nuna irin tarbiyyar da muka muku.. Ke Afrah bana jinki hakan ne ma yasa ban damu da sanar dake ko waye mijin naki ba, duk da dai baki san shi ba, amma na san gobe zaki san shi idan Allah ya yadda.. Sunansa Areef.. Ke kuma Afaaf ina saka rai a kanki, ko dan faɗan da zan muku, don Allah kar ki zubar min da mutunci.. kar ki nuna bamu isa dake ba. Ki yiwa Allah da Annabinsa ki zauna da mijinki lafiya, kar in ji kar in gani. Affan yaron kirki ne In Sha Allah ze kula dake, ze riƙe amanar da na damƙa masa. Matuƙar dai zaki saukar da kanki ƙasa, ki kuma gane yanzun fa a ƙarƙashinsa kike.." Tunda Abba ya soma magana Lulu ke girgiza kai, ba tare da ta shirya ba, wasu zafafan hawaye suka soma zarya a kan fuskarta. Ashe ba mafarkin ta yi ba gaskiya ne komai? Gwani shi ne wanda Abba ke kiran ya aura masa ita. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.. Da ƙyar ta iya buɗe bakinta ta soma faɗin

"Abba me na maka? Abba wane laifi na maka ka hukuntani da wannan hukuncin? Abba me yasa zaka min haka? Abba don Allah ka aura min kowane ne amma banda Gwani.. Abba ka min wannan alfarmar don Allah.." ta ƙare tana sakin wani sabon kuka. Ƙasa da kanta Didi ta yi itama hawaye na sakkowa daga cikin idanunta. Bayan duk waɗannan maganganun da Abban ya faɗa, da abubuwan da suka fi kama da roƙo gami da neman alfarma a wajensu, da wane ido zata kalli Abban tace wani abu a kan wannan auren da ya musu? Ta buɗe baki tace mene ne bayan tarin ƙaunarsu da Abban ke yi. Tun ba ma wannan ba, ko a iya roƙon da ya musu, da nuna ya isa dasu ɗin da ya yi ba ta ji zata iya furta komai bayan godiya, duk da yanda zuciyarta ke mata zafi.

"Me kika min kuwa Afaaf? Tsananin ƙaunarki da nake yi, da son inganta gobenki ya sanya ni aurawa Malam Affan ke. Ina kuma fatan ba zaki bani kunya ba.." da dai ta fahimci ba ta da wata mafita se karɓar Gwanin a matsayin mijinta ne ya sanyata faɗin, har lokacin bata dena kuka ba

"Abba ka sa shi ya sake ni, ka aura min koma wane ne don girman Allah.." Sauke numfashi Abba ya yi yana ɗan dafe kansa. A karo na barkatai ya sake ɗaga kansa ya kalli Lulun yace

"Ba ni da wani zaɓi da nake son haɗa ki da shi bayan Malam Affan.. Saboda haka ki karɓe shi a matsayin miji.. Allah ya yi wa rayuwarku albarka, ya saka albarka a rayuwar aurenku, ya kaɗe duk wata fitina. Ya kuma saka muku da alkhairi bisa biyayyar da zaku yi na karɓar wannan auren, yasa nan gaba ku gane gata na muku.." Daga haka Abba ya miƙe ya bar ɗakin. Ammi ta bi shi da kallo cike da tausayinsu su duka. Sabon kukan da Lulu ta fashe da shi me ƙarfi shi ne ya dawo da Ammi ta juya ta kalleta. A wajen ta zube ta shiga dirzar kukanta cikin rashin sanin mafita. Kuka take kamar ranta ze fita, ji take inama Allah ya ɗauki ranta ta huta da wannan masifar. Ji take inama ba tazo duniyar ba ballantana har wannan abu ya faru. Me yasa Abba ze mata haka? Me yasa Abba ya shammaceta haka? Laifin me ta aikatawa Abban da ya hukuntata da wannan mummunan hukuncin?

"Allah ka kawo mana mafita cikin al'amarin nan.." Ammi ta faɗa sanda ta ɗora kanta a kan kujera har lokacin kukan Lulu na cigaba da tashi cikin ɗakin. Kallanta kawai Didi take yi, se dai itama duk yadda taso ta daure se ta kasa, se kawai ta shiga taya er uwar tata kukan se dai ita nata a hankali take yi dan har kanta ma yana cikin hijab ne. Da dai Ammi ta ji kukan Lulun bana ƙare bane, se ta shiga rarrashinta cike da tausayawa, tana bata baki, amma ina, kukan ta cigaba da yi kamar ma turata take yi. A wannan dare, idan nace wani daga cikin en gidan nan ya runtsa toh Little ne.


... Washegari tun da safe gidan ya fara karɓar baƙin kusa. Dan Abba yace baya son wani taro, waɗanda zasu ɗauki amare kawai ake buƙata. Tun safe Mami da Jadwa suka yiwa gidan dirar mikiya. Farin ciki a wajen Mami abin ba a cewa komai. Burinta na son haɗa Kaseem da Jadwa ta san ze cika, tunda ga shi cikin sauƙi yanzu babu shi babu Didi. Se da ta gaisa da waɗanda ke cikin parlourn sannan tace

"Ina 'ya'yana?"

"Suna ɗaki.." Ammi ta faɗa. Miƙewa Mamin har ma da Jadwa suka yi zuwa ɗakinsu Twins. Da sauri Mami ta ƙarasa zuwa kan gadon tana faɗin

"Daughter.." Shiru babu amsa, duk da kuma idanun Lulun a buɗe suke, se dai ta kafe waje ɗaya da idanun nata ne kamar me kallan wani abu.

"Daughterna.." ta sake faɗa sanda ta ƙarasa dab da ita. Ta saka hannu ta riƙota, motsi da jajayen luhu_luhu ɗin idanunta Lulu ta yi har lokacin ba tace komai ba. Tun jiyan bayan ta gama kukan ta godewa Allah se ya zamana kawai ta koma waje ɗaya ta yi shiru kamar me tunanin wani abu, ta riga ta fuskanci komai ya riga ya faru, aikin gama ya riga ya gama. Ta rasa mafita, ta rasa abin yi, ta rasa me bata shawarar abin da za ta yi, ta rasa me faɗa mata abin da ya dace ta aikata, se rarrashi kawai da sake bata baki a kan maganar auren. Gaba ɗaya kanta ya kwance, ji take kamar ba ita ba, jinta take kamar an sauyata, ta kasa magana, ta kasa cewa komai, ta kasa aikata komai, se tunani kawai. Har gwara Didi baiwar Allah da ta riga da ta fawwala Allah komai, ta yi addu'ar Allah yasa hakanne mafi alkhairi, ta kuma cigaba da janyo duk wata addu'a da tazo mata a zuciya. Daga baya ma se ta ɗauki Qur'an ta shiga karantawa ko zata samu zuciyarta ta yi sanyi. Cikin mintuna kaɗan kuwa ta soma ji komai na sauya mata, se kawai ta cigaba da yi cikin nutsuwa duk da yanda tunani ke son yi mata shamaki. Har Mami ta gama surutanta Lulu ba ta tanka mata ba, ba tace da ita ko uffan ba. Daga ƙarshe da ta gaji se kawai ta jata jikinta ta rungume tana rarrashinta. Se a lokacin hawayen da a yanzun ba sa mata wahala suka soma zubowa a kan fuskarta.

"Ki yi haƙuri kin ji daughter.. Kukan ya isa haka, kada ki yi wa kanki illa.." ta faɗa cikin rarrashi.


Tun safe dama Abba ya fice daga gidan shi da Little, ya kuma faɗawa Ammi ko da kai yaran aka tashi yi kada ta tsaya yi musu faɗa ko kuma nuna yanda za ta yi kewarsu saboda kada ta kuma kwaɓa al'amarin. Dan haka tun lokacin da Ammi ta fahimci lokaci na ta ƙaratowa, se ta shiga ɗakin nasu, cikin rarrashi ta samu ta soma yiwa Didi jagora zuwa toilet dan yin wanka. Zuwa lokacin zuciyar Didi ta gama karyewa, haka dai ta shiga wankan tana yi tana sharɓar kukanta. Se bayan ta fito ne sannan ta sake wani sabon lalen na saka Lulu shiga wanka.

"Don Allah Lulu, don Allah kar ki yi abin da be dace ba. Idanun kowa a kanmu suke, saboda haka ki yi ƙoƙarin ɓoye duk wasu halayenki ko da na yau ne a gama taron nan lafiya.. Kada ki bar mana abin faɗa.." Da wannan maganganun Ammi ta samu Lulun ta shiga wankan. Se da ta shafe fiye da 1hour sannan ta fito har lokacin hawayen fuskarta kamar ana kunnosu. Ammin da kanta ta shirya kowaccensu cikin riga da zani na atamfa sabuwa dall me kyau da tsada, ta feshe su da turare me ƙamshi sannan ta yane musu kansu da mayafi shi ma iri ɗaya. Rungumesu ta yi tana jin wata iriyar kewarsu na kamata, se dai ta yi ƙoƙari wajen saita kanta dan saboda kada ta sake karyar musu da gwuiwa. Se a lokacin kowaccensu ta fiddo da kukan nata fili, suka shiga yin kukansu cikin rashin sanin abin yi. Lulu kam kukanta cike yake da abubuwa da dama, ga an dakeka an hanaka kuka. Ta rasa abin da ya kamata ta yi, ji take inama ace wannan ɗin shirin film ne da ta ɗauki ƙafa ta gudu daga garin. Ji take inama zata iya kallan Abba da Ammin ta faɗa musu ko me zasu yi ba zata taɓa zama da Gwani ba. Se dai ta ma kasa buɗe baki tace wani abu, dan ta san kome zata faɗa ba ze chanja komai ba, kome za tace ba ze hana abin da su Ammi suka yi niyya ba. A yanzu dai

Please Login or Register in order to submit comment