Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana asibitin da Abeey yake, ya sa Bad Man ne ya wuce ɗauko su Didin. A harabar gidan ya tsaya yana jiran fitowarsu bayan ya shiga sun gaisa da Ammin. Ko a jikinsa, ganin Lulu da ya yi sun fito tare da Didi hakan be hana shi ƙarasawa inda take ba, ya yi azamar jawota jikinsa yana rungumewa.

"Sweetheart.." Ya faɗa yana lumshe idanunsa. Ita kam ji ta yi kamar ƙasa ta tsage ta shige dan kunya. Wanzuwar Lulu a wajen ita ce ta sanyata ji kamar ta fasa ihu. Shi kam da alama ko a jikinsa. Dan kuwa tana jikin nasa ya kalli Lulu da ke ƙoƙarin wuce su kamar ba ta gansu ba.

"Tweenienmu.." Ya yi maganar da ɗan murmushi a kan fuskarsa da yanzun lokuta da dama da wuya ka ganta a yanda ka san shi a da, musamman idan yana tare da Didi. Se a lokacin ta dakata ta ɗan yi murmushi cikin basarwa tace

"Barka da wannan lokaci Ya Areef."

"Barka dai.." Ya yi maganar yana sakin Didi.

"Thank God! Wannan mutumin!" Lulu ta faɗa a kan laɓɓanta, kafin ta fesar da iska daga cikin bakinta. Tura baki Didi ta yi dan ita kam ya gama bata kunya a gaban Lulu. Sarai ya lura da yanayinta, se dai ya basar kawai. Ya lura har yanzu ba ta gane yanda yake jinta a can ƙasan zuciyarsa ba ne. Kwata kwata ba ya ji ze iya ɓoye ƙaunarta da yake, musamman ma kuma da ya kasance a gaban er uwarta ne ba gaban wani can daban ba.

"Uncle.!" Ya jiyo muryar Little da ke tahowa wajen. Yana ƙarasowa ya rungume shi yana dariya. Hannu Bad Man ya saka ya ɗaga shi yana faɗin

"Areef!" Ya ƙare yana murmushi dan ba ƙarya ya yi kewar yaron shi kansa.

"Uncle kai ma ka dawo gidan nan?" Ya tambaya cike da farin ciki, dan shi a tunaninsa har su Didin ma sun dawo ne. Girgiza kai Bad Man ya yi kana yace

"A'ah na zo ne in ganka.. Amma zan dawo."

"Su Didi fa?" Ya tambaya yana buɗa baki kamar wani babba me wayo

"Su ma za su dawo."

"Kai!!" Ya faɗa yanayin fuskarsa na sauyawa. Se ma ya soma taɓe baki kamar ze yi kuka. Da sauri Bad Man yace

"Kar ka damu.. Za su dawo Uhmm?" Ya ƙare yana kallansa. Se ya jinjina kai a sanyaye. Bad Man ya ja kumatunsa yana faɗin

"That's my boy.. Oh yah, give me five!" Ya faɗa yana miƙa masa hannunsa. Se ya ba shi hannunsa suka tafa yana dariya. Se a lokacin sannan ya sauke shi yana faɗin

"Maza shiga gida.." Se da ya juya ya kalli Lulu da Didi da suke kallansa kamar za su yi kuka kafin ya tafi da gudu zuwa cikin gidan. Ajiyar zuciya ya sauke yana tashi tsaye sosai. Ya so ya samu ya gaisa da Abba, se dai har yanzun Abban be dawo ba. Dalili kenan da ya sanya ya haƙura kawai, da niyyar wani lokacin ya zo takanas ya gaishe da Abban.

Ita kam Lulu tamkar er kallo ta zama, dan ba ta taɓa tunanin Bad Man ɗin haka yake ba. Domin kuwa yanzun ma hannu ya saka ya buɗewa Didi ƙofar gidan gaba, ta juya da niyyar kallansa, ya marairaice fuska yana kauda kai ba tare da ya bari sun haɗa ido ba. Se ta juya da niyyar kallan Lulu, ita ma ta yi saurin janye idanunta tana basarwa. Bad Man da ke lura da duk abin da take ya yi murmushi har fararen haƙoransa na bayyana. Kawai se ta shiga ciki, ya kulle ƙofar kafin ya zagaya. Se a lokacin ya juya ya kalli Lulu yace

"Matar ɗan uwa mu wuce koh?" Se ta jinjina kai tana ƙarasowa ta shiga cikin motar. Babu ɓata lokaci ya ja motar suka fice daga cikin gidan. Ko a cikin motar ma duk da driving yake, hakan be hana shi kamo hannun Didi cikin nasa ba. Duk da yanda take ɗan ta babbasarwa saboda wanzuwar Lulu a wajen amma shi ko a jikinsa. Da dai ta ga babu sarki se Allah kawai se ta yi shiru, ta saki hannun nata, ya kuwa riƙe gam idanunsa na kan titi. Sosai Lulu ta ji daɗin hakan, ko babu komai ta san Didin tata ta samu mijin da ke ƙaunarta. Ba ma ita kaɗai ba dukkansu sun samu masu ƙaunarsu. Kawai se ta ji tana kewar nata mijin, ta lumshe idanunta tana jin wani murmushi na ƙwace mata. Yana ida parking na motarsa driver ma na parking motar da ya ɗauki Gwani ciki. Don haka kusan a tare suka sauka. Idanun Gwani na kan inda ze hango tauraruwar tasa. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa ya hangota ta yi kyau, tamkar wadda ta gama shiri yanzun. Ya saki murmushi yana jin wani sanyi na ratsa shi. Yau ɗin da ya wuni be ganta ba duk se yake jinsa tamkar mara lafiya, yanzun kam da ya ganta se yake jinsa zam-zam.

"Ina fata dai ba ka wujijjiga min mata da ɗa ba da wannan driving ɗin naka." Gwani ya faɗa lokacin da ya ƙaraso inda suke idanunsa a kan Bad Man. Buɗe ido ya yi kafin yace

"Umm lallai ka ga me mata da ɗa.. Toh tambayeta mana." Ya ƙare yana rungume hannunsa a ƙirji yana maida dubansa kan Lulu. Jinjina kai Gwani ya yi kafin ya shiga takawa zuwa inda Lulu take. Se ta soma ɗaga kai tana kallan Bad Man da Didi da ke kallansu. Fatanta da addu'arta kawai Allah Ya sa kar yace ze riƙota ko wani abun. Cikin ikon Allah kuwa addu'arta ta karɓu, dan kuwa ƙarasowa ya yi se dai dab da ita. Ya zuba mata idanunsa, ita ma kuma shi take kalla. A hankali kamar me raɗa yace

"Ina fata dai be wahalar min da ku ba?" Har ta buɗe baki cike da mamaki da niyyar tambayar ita da wa? Se kuma murmushi ya ƙwace a kan fuskarta. Ta jinjina kai a hankali tana faɗin

"Ehh.." Juyawa Gwani ya yi yana murmushi, idanunsa a kan Bad Man yace

"Allah Ya taimake ka." Dariya Bad Man har ma da Didi suka yi, dan babu ƙarya abun ya burgesu. Musamman irin kallan da suke bin junansu da shi ɗazun, wanda kallan farko za ka karanto irin soyayyar da kowannensu ke wa ɗan uwansa.



.. Ba a ɗauki lokaci me tsayi ba, shirye-shiryen tafiyarsu Saudiyya komai ya kankama. Dan haka suka sake yin sallama da dangi na kusa kafin suka kama hanya se ƙasa me tsarki. Kowa na yi musu fatan alkhairi, da fatan a yi ibada lafiya, a kuma samu nasara a rashin lafiyar Abeey. A ranar da suka sauka kai tsaye asibitin suka fara wucewa. A kusa da asibitin kuma akwai hotel, a nan suka kama ɗakuna biyu da za su zauna. Kama ɗakin kawai suka yi, suka bar Didi da Lulu. Ya yin da su kuma suka koma asibitin dan ƙarasa duk wasu abubuwa da suka kamata saboda kasancewar yau ɗin shi ne zuwansu na farko. A can asibitin da ma suka bar Ummeey. Dan haka inda suka barta a nan suka zo suka sameta.

"Ina kuka bar 'ya'yan nawa?" Ummeey ta tambaya tana kallansu su duka.

"Yanzu haka suna cikin ɗakin hotel ɗin da ke kusa da asibitin nan Ummeey.. Idan ki na buƙatar wani abu se mu je a raka ki." Bad Man ne ya ba wa Ummeey wannan amsar. Ta yi murmushi kafin ta amsa da

"Toh madallah.." Suna nan zaune suna jiran shigowar wanda Daddy ya haɗa su da shi Abeey da ke kishingiɗe a kan gadon ɗakin ya kalli Gwani yace

"Kun dai dage se na samu lafiya." Ya ƙare yana kallan Gwani da ya san ya fi kowa shiga damuwa idan ba shi da lafiya.

"Abeey bayan lafiyar ma kuma, ai ka ga babban abun da ya kawo mu shi ne ziyartar ɗakin Allah." Murmushi Abeey ya yi kafin ya amsa da

"Haka ne.. Allah Ya yi muku albarka. Shi kuma Alhaji Matawalle Allah Ya saka masa da alkhairi." Ya ƙare maganar yana ƙoƙarin komawa ya kwanta. Da sauri Gwani ya ƙarasa ya taimaka masa ya kwanta ɗin yana ɗan sauke ajiyar zuciya. Gwani ya bi shi da kallo cike da tausayawa. A kan laɓɓansa ya furta

"Allah Ya ba ka lafiya me ɗorewa Abeey."


.. A ɗaya ɓangaren kuwa kulle ɗakinsu Lulu ta yi ta koma na su Didi. A nan suka yi wanka, sallah da duk wasu abubuwan. Kafin suka zauna hira. Har zuwa lokacin da Didi ta shiga hamma da alama bacci take ji.

"Wai bacci kike ji?" Lulu ta tambaya tana kallanta. Jinjina kai Didi ta yi tana rufe bakinta da hannunta saboda hammar da ta sake yi.

"Hmm uhmm.. Yanzu wai kwanciya za ki yi?" Ta yi maganar tana kallan Didi da ke ƙoƙarin ɗora kanta a kan ƙafarta. Jinjina kai Didi ta yi tana ida ɗora kan nata a kan ƙafar Lulun tace

"Don Allah kar ki motsa ƙafarki." Ta faɗa tana riƙe ƙafar sosai.

"Na ji." Lulu ta faɗa tana tura baki, dan ita dai so ta yi su cigaba da hirarsu kafin su dawo. Ita kuma wai bacci, haka tana ji tana gani cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya kwashe Didin.

"Lallai ma Didi." Ta faɗa tana kallan fuskarta. Cigaba da zama ta yi har zuwa lokacin da ta ji an yi knocking ɗin ƙofar. Ta saka hannunta ta sauke kan Didi daga kan ƙafarta ta maida kan pillow kafin ta miƙe. Ta sanya key ta buɗe. Murmushi ta yi ganin Bad Man tace

"Aou Ya Areef.."

"Na'am, ina matana?" Ya faɗi abin da ke ransa.

"Oh ni Afaaf.." Ta faɗa a kan laɓɓanta.

"Idan ma Affan ne.." Ya faɗa yana murmushin gefen baki dan sarai ya ji abin da ta faɗa. Ba ta zata ba, hakan ne ya sa ta buɗe baki cike da mamakin yanda aka yi ya ji ta. Se kuma ta murguɗa baki tace

"Habibin guda?" Ba ta jira yace komai ba ta fice daga ɗakin, dan ita kanta ta ba wa kanta kunya. Murmushi ya yi kafin ya shige cikin ɗakin. A kan gado ya hangota tana bacci cikin nutsuwa. Ya ƙarasa fuskarsa ɗauke da mamaki yana kallan fuskarta da ta yi fayau. Ya juya a hankali ya kalli ƙaton agogon da ke manne a jikin bangon ɗakin kafin ya dawo da dubansa kanta.

"Wannan wane irin bacci ne? An ya na lafiya ne kuwa?" Ya tambayi kansa cike da fargabar da lokaci ƙanƙani ta ziyarce shi..




✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO83*
Second to the last page... 😩😭🥳


___ A hankali ya ƙarasa gadon har lokacin idanunsa na kanta. Ya kafe ta da idanunsa na tsawon sakanni kafin ya saka hannunsa ya ɗaga ta ya gyara mata kwanciyar. Ya ja blanket ya lulluɓe ta kafin ya wuce toilet. Ya kwashe mintuna masu dama kafin ya fito. Ya shirya cikin wasu kayan bacci masu kyau. Ya ƙarasa ya kwanta a kan gadon. Se da ya ja ta jikinsa ya rungume kafin ya lumshe idanunsa yana jin yanda numfashinta ke sauka cike da nutsuwa.


... A nutse ya kamo hannunta cikin nasa, dalili kenan da ya sanya ta ɗaga idanunta ta zuba cikin nasa. Se kuma ta ɗan janye daidai lokacin da yace

"Ki na lafiya?" Juyawa ta yi gaba ɗaya tana kallansa cikin mamakin jin tambayarsa. Fahimtar yanayinta ya sanya shi jinjina kai. Se ta yi murmushi dan kawar masa da damuwar da ta gani shimfiɗe a kan fuskarsa, duk da ita ma haka nan kawai take jinta kamar ba lafiya ba. Se dai takamaimai ta kasa gane abin da ke damunta, tace

"Eh fa, ba abin da ke damu na."

"An ya kuwa?" Ya sake yin maganar yana ƙura mata idanunsa. Lumshe idanunta ta yi kafin ta buɗe. Ta ɗauko ɗayan hannunta da ba ya cikin nasa ta ɗora a kan hannun nasa, ta ɗan riƙe sosai kamin ta jinjina kai tana lumshe idanunta a cikin nasa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya fesar da iska daga bakinsa yace

"Alhamdulillah.." Kallansa kawai take yi tana jin ƙaunarsa na ratsa kowacce gaɓa ta jikinta. Kulawarsa a gareta tana da yawa.

"Ko in matso ki cinye ni kawai?" Ya faɗa cike da tsokana yana ɗage girarsa guda ɗaya. Kanta ta ɗora a kan cinyarsa tana faɗin cike da shagwaɓa

"Ni dai.. ni dai Allah kuwa ba na so.." Dariya ya yi kafin ya saka hannunsa ya ɗago ta. Ta kauce jikinta tana sake shagwaɓe fuska. Kawai se ya ja ya rungume cikin rarrashi yace

"Ni ne ba? Toh na tuba na dena." Shiru ta yi tana murmushi ƙasa ƙasa. Sun kai wajen minti 5 a haka kafin ya sake ta ya miƙe yana faɗin

"Tashi mu shirya.. Kar su riga mu shiryawa." Ya yi maganar yana ɗaukarta yanda ze fi masa sauƙi.


... Wayarsa da ta yi ƙara ita ce ta sanya Lulu dakatawa. Da yake ta fi kusa da wayar, hakan ne ya sanya ta ƙarasawa ta dauka, ba tare da ta kalli me kiran ba ta ƙarasa inda Gwani yake yana mayar da takardu cikin wata madaidaiciyar jaka.

"Ana kiranka.." Ta faɗa tana miƙa masa wayar. Maimakon ya karɓa, se kallanta da ya yi. Ta turo baki jin ya ƙi karɓa har tana neman tsinkewa.

"Kiranka fa ake.." Ta faɗa har lokacin ba ta maida fuskarta daidai ba. Hannu ya kai ya karɓi wayar. Maimakon ya ɗauki wayar ita kaɗai, se ya haɗa da me wayar gaba ɗaya ya ja ta se ta koma tana kallan inda yake kalla shi ma. Se da ya nemi waje ya zauna yana gyara mata zaman da ta yi kusan a jikinsa, kafin ya ɗaga wayar da aka yi kira na biyu.

"Ina ta ƙoƙarin kiranki se kuma na sha'afa."

"Toh babu damuwa.."

"Idan mun dawo In Sha Allah zan sanar da ke.." Abubuwan da Gwani na ji yana faɗa kenan, waɗanda suka fi kama da bayar da amsa. Kasancewar ba na jiyo abin da ake faɗa a can ɓangaren ya sa ban fahimci zancen gaba ɗaya ba. A hankali kamar wadda ta ga wani abun ta shiga tashi daga jikinsa, duk da yanda ya riƙe ta, amma se da ta fuzge jikinta ta miƙe zaune sosai. Kallansa ta shiga yi da narkakkun idanunta har zuwa lokacin da ya ajje wayar. Se kuma kawai ta soma shirin miƙewa, ya yi azamar saka hannunsa ya maida ta inda ta tashi. Jikinta ta ƙwace tana jin yanda ƙwalla ta cika mata cikin idanu. Se da ya juyo da ita, ya tabbatar suna kallan juna ne kafin yace

"Me ya faru?" Ya tambaya yana kallan cikin idanunta. Runtse idanunta ta yi ba ta so hawayen su zubo, dan kuwa ba ta shiryawa zuwansu ba, kawai jinsu ta yi. Ba kuma ta so ya gani, hakan ne ya sanya ta sake yunƙurin tashi.

"Toh ka bar ni na tafi ka cigaba da wayarka mana." Ta kai ƙarshen maganar tana jin zafi har cikin zuciyarta. Shi wallahi se yanzu ma ya fahimci dalilin fushin nata. Be san sanda murmushi ya ɗan suɓuce a kan fuskarsa ba. Ya basar dan kar ta gan shi ta dira wata shagwaɓar tata.

"Malama Amina ce.. Magana ce kuma a kan musabaƙa da muke shiryawa, wadda za a gabatar nan ba da daɗewa ba. Idan kuma ba ki amince ba ga wayar nan ki kira." Ya ƙare maganar yana miƙa mata wayarsa. Bin wayar ta yi da kallo kamar wata doluwa, kafin a hankali ta maida dubanta kansa, lokacin da ƙwallar idanunta ta soma tsotsewa dan kanta. Duk se ta ji kunya ta kama ta. Tabbas ta yadda da shi ɗari bisa ɗari, amma kishinsa da take na da tasirin da ba za ta iya dannewa ba muddin ta ji shi yana waya da mace. Hannu ta kai ta sake goge ƙwallar gaba ɗaya murmushi na ɗan ƙwace mata, ta kuma kasa ɗaga ido ta kalle shi. Ya lumshe idanunsa yana jin wata nutsuwa. Se da ta ɗago kafin ta saka hannu ta tura hannunsa da ke ɗauke da waya baya. Ta girgiza kai tana kaucewa idanun nan nasa. Murmushi ya yi kafin yace

"Kin amince da ni?" Har lokacin ba ta kalle shi ba ta jinjina kai. Ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin

"Na gode wa Allah!" Ya ɗan dakata kafin ya ɗora da faɗin

"Ni fa rashin kallan nan nawa kan jefa ni cikin yanayi.. A kalle ni ko sau ɗaya ne mana.." Ya ƙare yana langaɓar da kai. Tilas ta ɗaga kai ta kalle shi tana murmushi.

"Ki saka a ranki Affan naki ne ke ɗaya har abada.. Kar ki kuma sakawa ranki tunanin zan kula wata ne da sunan soyayya.. Ke ɗin nan kin ishe ni, musamman ma kuma da nan da kwanaki kaɗan za mu ƙaru mu zama mu uku." Ya ƙare yana saukar da idanunsa kan cikinta. Hannu ta kai ta dafe cikin nata tana lumshe idanunta. Ya kai nasa hannun ya ɗora shi ma yana lumshe nasa idanun. Kusan a tare suka buɗe idanun. Gwani ya sauke numfashi yana sake kafe ta da idanunsa.

"Ina son ganin wannan kishin nawa a cikin idanunki. Yanayin kan sa na ji ni cikin nishaɗi, na kuma sake tabbatarwa matata na sona."

"Aou fushin nawa kake so?" Ta ƙare a shagwaɓe. Da sauri ya girgiza kai yana kamo haɓarta ta koma kallansa sosai yace

"Fushinki daban, haka zalika kishinki daban. Yanayin ba iri ɗaya ba ne. Ni kaɗai na san halin da nake tsintar kaina idan na ganki cikin fushi. Ke ba na ma fatan sake ganinki ciki har abada. Ina fatan ɗorewar farin ciki a rayuwarmu har abada. Allah Ya tabbatar da hakan."

"Ameen Mijina.." Ta ƙare tana kwantawa a jikinsa. Rungume ta ya yi cikin jikinsa yana jin yanda wata irin soyayyarta ke sake ratsa ilahirin jikinsa.

Kusan a tare suka gama shiryawa, dan haka tare suka fita. Kai tsaye asibitin suka nufa. Wuni suka yi a cikin asibitin. Ranar gaba ɗaya Lulu da Didi na tare da Ummeey. Wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya mata ba. Se da dare kafin suka soma shirin tafiya.

"Tafiyar ce?" Ummeey ta faɗa tana kallansu.

"Ehh Ummeey.. Ina tunanin na zauna saboda kar ki buƙaci wani abu kuma ba na kusa." Gwani ya faɗa. Girgiza kai Ummeey ta yi kafin tace

"A'ah, yau ɗin ma In Allah Ya yarda ba zan nemi komai ba.. Ai ba za ka bar 'yata ita ɗaya ba. Ku je Allah Ya muku albarka."

"Ameen." Suka amsa kusan a tare, kafin su ma suka mata sallama kana suka fice.


.. Tun ɗazu yake lura da ita, yanda yanayin tafiyarta ya sauya.

"Didi" Lulu da ke gefenta ta kira sunanta. Sake dafe kanta ta yi tana lumshe idanunta. Se dai duk da haka ba ta dena takawa ba. Wani jiri da ya kwashe ta shi ya tilasta mata dakatawa, ba tare da ta ankara ba ta tafi da niyyar zubewa. Ya yi saurin ƙarasawa ya saka hannunsa, hakan ne ya sanya ta faɗawa jikinsa. Ajiyar zuciya ya sauke lokaci guda ƙirjinsa na bugawa dan babu ƙarya ya tsorata. Gwani da Lulu kansu sun tsorata, dalili kenan da ya sanya dukkansu su ma suka dakata. Hannu Bad Man ya saka ya tallafo fuskarta da idanunta ke a rufe, dan ita kanta ta tsorata. Cikin kulawa yace

"Babe!" Se a lokacin ta shiga buɗe idanunta, ƙirjinta na harbawa da ƙarfi. Tashi ta soma ƙoƙarin yi, ya barta ta miƙe amma duk da haka tana jikinsa.

"Da ma ba ki da lafiya shi ne ba ki sanar da ni ba?" Ya tambaya yana kafe ta da idanunsa da suka ɗan sauya. Girgiza kai ta yi cike da gaskiyarta tace

"Lafiyata ƙalau." Iska ya fesar yana runtse idanunsa. Ya buɗe su yana kallan nata dai.

"Ba ki da lafiya.." Ya faɗa kamar shi ke da jikinta.

"Lafiyata.."

"Shhh.." Ya faɗa yana ɗora hannunsa a kan bakinsa. Kawai se ta yi shiru ta cigaba da kallan yanda cikin ƙanƙanin lokaci yanayinsa gaba ɗaya ya sauya. Kai ba za ka taɓa cewa shi ne ɗazun ba. Ita dai ba ta sake cewa komai ba har zuwa lokacin da ya miƙar da ita sosai.

"Bro za mu koma asibitin, ku ƙarasa kawai.." Bin Didi da kallo kawai Lulu take yi da idanunta da ita ma suka sauya, cike da tunanin abin da ke damun er uwar tata.

"Allah Ya ƙara sauƙi." Gwani ya faɗa.

"Ameen." Bad Man ya amsa da hakan yana juyawa, ya kama hannun Didi suka fice daga cikin hotel ɗin da ba su yi nisa da shigo shi ba.

"Mu je koh?" Gwani ya faɗa yana kallan Lulu da ta bi su da kallo. Ganin yanda duk ita ma yanayinta ya sauya ne ya sanya shi ƙarasawa kusa da ita sosai. Cikin rarrashi yace

"Ki kwantar da hankalinki, babu abin da ze faru In Sha Allah.." Ya yi maganar yana kallanta sosai.

"Didina ba ta.."

"Kar ki ce komai.. Babu abin da ze faru Uhmm?" Se da ta sauke wani dogon numfashi kafin ta jinjina kanta jiki a sanyaye. Haka suka ƙarasa ɗakinsu zuciyarta fall tunanin Didinta.



.. "Ina taya ka murna, matarka na ɗauke da juna biyu.." Shi ne bayanin da likitar ta faɗa masa bayan gwajin da aka yi wa Didi. Kallan likitar yake yi lokacin da take bayanin, amma be san lokacin da idanunsa suka koma kan Didi ba. Tun daga nan kuma be sake fahimtar abin da take faɗa ba. Ita ma Didi kanta kallansa take yi, tana jin abun kamar a mafarki. Da gaske matar take ciki ne da ita? Lallai Allah me iko. Ba ta san lokacin da Bad ya ƙaraso inda take ba, se ji ta yi kawai an ɗaga ta gaba ɗaya ana juyi da ita cikin ɗakin. Cikin matuƙar farin ciki ya rungume ta yana ji kamar ya maida ta cikinsa. Sun kai wajen minti 1 a haka kafin ya sauketa a kan kujerar da ya ɗauke ta daga kai, ya sake zuba mata idanunsa da kalarsu ta chanja. Iya su kaɗai ko fuskarsa kaɗai za ka kalla ka fahimci farin cikin da yake ciki. Ya kasa furta komai, jin abin yake kamar almara. Ita kam likitar murmushi kawai take yi tana kallansu, dan babu ƙarya soyayyar tasu ta burge ta matuƙa. Yanda farin cikin Bad Man ɗin ya kasa ɓoyuwa ya burge ta.

"Allah Ya miki albarka, Ya biya miki dukkanin buƙatunki, Ya albarkaci rayuwarki, Ya inganta abin da ke cikinki, Ya fito mana da shi lafiya, rayayye kuma lafiyayye. Ameen." Ita dai Didi babu baki se binsa kawai take da kallo ta kasa furta komai.

"Ina tuni dai, a dinga barinta tana hutawa.." Likitar ta sake faɗa lokacin da take ƙoƙarin ficewa daga cikin office ɗin nata da ya fi kama da wani tanƙamemen palour me kyau da ƙayatarwa. Ya jinjina kai yana murmushi dan sam ɗazu be ji ta ba ma saboda farin cikin da ya samu kansa a ciki.


.. "Ki faɗa min duk abin da kike buƙata a faɗin duniyar nan, wanda zan ɗauka in ba ki shi a matsayin tukwuici." Ya ƙarasa maganar yana kallan cikin asibitin, kafin ya dawo da dubansa kanta yana gyara zamansa a kan kujerar. Murmushin da ita kanta Didi ya ƙi barin fuskarta ta yi, har yanzu jin abin take kamar wasa, wai tana da juna biyu.

"Ni kai nake so.."

"Ni kuma?" Bad Man ya tambaya yana nuna kansa. Se ta jinjina kai cike da tabbatarwa. Ya girgiza kai yana murmushi

"Da ma tun can ni ɗin ai naki ne.. Wani abun za ki zaɓa.."

"Allah kuwa da gaske ni kai nake so.. So nake ka mallaka min kanka har abada." Ta ƙare maganar a narke. Kwantar da kansa ya yi kan kujera ya kalli saman motar. Be ma san ta inda ze soma mata bayanin ya mallaka mata kansa har abada kamar yanda take buƙata ba. Se dai kawai ya sake dawo da dubansa kanta. Kusan minti 1 yana kallanta, cike da so, ƙaunarta da kuma abin da ke cikinta.

"Idan dai har ni ne, toh ki saka a ranki da ma can ni naki ne.. Se dai tun da ki na son ki sake tabbatarwa, toh ni Areef na mallaka miki kaina gaba ɗaya ki yi yanda kika ga dama da ni. Allah Ya yi miki albarka, Ya ƙara miki lafiya.. Ina sonki.." Ya ƙare yana haɗe ta da jikinsa.

"Ni ma ina sonka.." Ta maida masa da amsar tana sake rungume shi idanunta a lumshe.


Tun a daren ranar komai hana ta yi ya yi, daga ta so yin abu ze ce

Please Login or Register in order to submit comment