Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙara da Iftihal ta saki tana fashewa da kuka ita ce ta dawo da shi hayyacinsa. Abin da kuma ya tabbatar masa da lallai ba mafarki yake yi ba. A hankali ya shiga sassauta riƙon da shi da ita suka yi wa juna. Se dai me? Se ji ya yi ta sake riƙe shi gam. Yau kam mamaki ya kusa kashe Gwani. Se dai farin cikin da yake ciki Allah kaɗai ya san yawansa. Ta gabansu Iftihal ta zo ta wuce cikin ɗakin Mommah a zuciye tana cigaba da ƙaramin kukanta. Be iya ganin fuskar wace ce ba. Se kawai ya basar ya maida dubansa kan Lulu ya shiga lalubo fuskarta da har lokacin take kwance a jikinsa. A daidai lokacin Lulu ta sake shi, se ta shiga ƙoƙarin miƙewa daga jikin nasa. Tana idawa kuwa ya yi caraf ya riƙo hannunta. Kasa ɗaga ido ta yi ta kalle shi dan tabbas wannan kalmar da ta faɗa ta mata nauyi. Ba ta san za ta iya faɗinta a irin wannan lokacin ba, se sanda ta ga Iftihal a gabanta. Ba ta san zuciyarta za ta bata haɗin kai har ta furta ba se da ta soma faɗa. Ta kuma kasa dakatawa, kowacce gaɓa ta jikinta kuma ta yi na'am da hakan. Wani irin murmushin farin ciki ke tashi a kyakkyawar fuskar Gwani. Ya ma rasa me ze ce? Me ze yi? Shin da gaske ne abin da ta faɗa? Ashe kenan da gaske kishinsa ya gani cikin idanunta ranar nan? Da gaske ta fara sonsa ɗin kamar yanda ta faɗa? Cikin ƙarfin hali ya tattara wannan maganar..

"Da gaske ki na sona Afaaf..?" Ya tambaya cike da fatan amsar da za ta fito daga cikin bakinta ta kasance daidai da abin da ta faɗa ɗin. Maimakon ta ji tana son ƙaryatawa ko da ba za ta iya faɗa masa kai tsaye ba. Se ba ta ji hakan ba. Se kasa ɗaga ido da ta yi ta kalle shi. Ta kalli hannunta da ke cikin nasa tana ji kamar ta janye kama yanda ta saba, se ta kasa hakan. Se dai kuma da gasken so take ya saketa ko ta samu ta guje masa, ballantana ta cigaba da tuna abin da ya faru a wajen nan.

"Ki faɗa min don Allah.." A karo na biyu ya sake faɗar hakan. Ba za ta iya kallansa tace da gasken take ba, ba kuma za ta iya cewa ba da gaske take ba. Dan haka kawai se ta zame hannunta da sauri cikin azama ta shige cikin ɗakin Mommah. Binta ya yi da kallo yana sake jin wata nutsuwa da farin ciki na kama shi. Lallai idan dai har hakan ta tabbata babu abin da ze yi se dai ya godewa Allah. Lumshe idanunsa ya yi yana ɗora hannunsa a kan sumar kansa da ke a buɗe ya shafa, har lokacin murmushi ya ƙi barin fuskarsa. Ya fi minti 3 a wajen kafin ya ja ƙafafunsa ya wuce sashensu.


.. Hannunta ɗauke da akwati ta fito daga cikin ɗakin idanunta sun yi jajir alamar ta sha kuka ta ƙoshi. Da sauri Mommah ta ƙarasa tana faɗin

"Subhanallahi Ifti me ya faru?" Ta yi maganar tana riƙo akwatin. Ɗauke kai Iftihal ta yi tace

"Gida zan tafi.." Da mamaki Mommah tace

"Gida kuma?"

"Ehh.." Ta bata amsa tana sake riƙo akwatinta. Girgiza kai Mommah ta yi kafin tace

"A'ah me ya faru? Ba se gobe za mu wuce gidan gaba ɗaya ba?" Da sauri Iftihal ta girgiza kai tana faɗin

"A'ah Mommah yau zan tafi.. Don Allah yau zan tafi." Ta faɗa tana ji kamar ta yi kuka, dan ita kaɗai ta san me take ji, ba ze yiwu ta cigaba da zama a cikin gidan nan ba, dan ta ga alama Lulu na da niyyar tarwatsa mata zuciya..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO78*


___Kallanta sosai Mommah ta yi kafin tace

"Ko dai wani abun ya faru ne ban sani ba?" Sake girgiza kai ta yi kafin tace

"Ba komai."

"Toh maza koma ki zauna.. kin san dai ba ze yiwu na barki ke ɗaya ki tafi ba."

"Mommah don Allah.."

"Ki koma na ce Iftihal.." Mommah ta katseta da faɗin hakan. Idanunta da suka cika da ƙwalla ta runtse tana juyawa ta koma cikin ɗakin. Mommah ta bi ta da kallo cike da mamakin dalilin da ya sa take so ta tafin.


... Ya kasa dena farin ciki tun da ya fito daga cikin ɗakin. Hatta fuskarsa kaɗai idan ka kalla za ka tabbatar da lallai yana cikin farin ciki. A haka ya shiga cikin ɗakin Bad Man ɗin. Baƙon abu ne irin haka a wajen Bad Man, ya ga fuskar Gwanin ɗauke da annuri babu wani dalili. Ya riga ya saba ganin fuskarsan nan mara annuri wadda take a haka kusan ko yaushe, kasancewar hakan a halittarsa ne. Dan haka a mamakance yace

"Bro me ya faru ne? Na ga kamar ka na cikin farin ciki." Se a lokacin Gwani ya saki murmushi. Ya juyo gaba ɗaya yana kallan Bad Man yace

"Tabbas yau ina cikin farin ciki.. Afaaf ta furta tana sona.."

"Woww!! Amma na tayaka murna ɗan uwa."

"Na gode." In ji Gwani. Hannu Gwani ya ɗora a kan kafaɗar Bad Man yace a nutse

"Ka kwantar da hankalinka in Sha Allah wannan ranar na nan zuwa. Ka cigaba da addu'a, ka kuma cigaba da kulawa da ita. Gefe guda kuma ka cigaba da istigfari." Ya fahimci abin da yake nufi, hakan ne ya sanya shi ɗan yin murmushin yaƙe kafin ya jinjina kai yana ajje numfashi.


.. Washegari kamar yanda Mommah ta alƙawarta, gaba ɗaya suka shirya zuwa gidan Sarki (Baba Abdullahi). Gaba ɗaya suka tafi har da Lulu da Didi. Baƙin ciki da ɓacin rai kamar su kashe Iftihal, saboda ganin har da Lulu a tafiyar. Abin da ta yi jiya tabbas ya matuƙar tsaya mata. Har yanzu take jin kamar shakka shakkar kallan inda Gwani yake. Se dai duk da haka ta maze tana ɗan satar kallansa. Ita gaba ɗaya zama gidan ma be mata amfani ba. Tun da dama ta zauna ne dan ta samu ko da shaƙuwa ce ta shiga tsakaninta da Gwanin. Se dai ba ta ga alamar hakan za ta faru ba.

Tarba ta musamman suka samu a gidan Sarkin. Irin tarbar da Mommah da Yaya Amina ba su taɓa tsammata ba. Ranar sun ga en uwa, sun ga dangi. Sun ga waɗanda ba su sani ba. Sun ga kuma waɗanda suka sani. Kowa farin ciki yake da zuwansu cikin gidan. Waɗanda suka san abin da ya faru na sake ɗibewa Samira albarka, ana binta da addu'ar Allah Ya saka musu. Ranar se ta kasance wata ta daban a rayuwarsu. Sun yi farin ciki ainun, haka kuma sun yi kuka. Se dai duk da haka farin cikin ranar ya fi yawa.


.. "Kun ba ni dama, kun amince na maida kowaccenku ɗakin mijinta?" Mommah ta faɗa tana kallansu cike da fatan amsar da za ta fito daga bakinsu ta kasance "Eh" ce. Shiru ne ya wanzu a cikin ɗakin babu wanda yace komai. Zuwa can Didi tace

"Idan dai har kin ga hakan ya dace Mommah ki yi. Duk abin da kika yanke mu masu biyayya ne a kai, saboda mun ɗauke ki ne tamkar Ammi. Dan haka kawai ki ba mu umarni. Dan mun san ba za ki yanke abin da ze cutar da mu ba." Girgiza kai Mommah ta yi tana ji tana sake ƙaunar Didin. Wato hankalin yarinyar na burgeta. Idan ta yi wani abun se ka ɗauka wata babba ce me shekaru. Nan kuwa hankalinta ne ya fi shekarunta yawa.

"Haka ne Afrah.. Zan yanke hukunci ne a kan rayuwarku tamkar a kan rayuwar 'ya'yan da na haifa. Saboda ku ɗin 'ya'yana ne. Na kuma yanke hukuncin nan ne bayan ganin shi ne ya dace. Ina kuma fatan Allah Ya sanya albarka a ciki, Ya kaɗe fitina, Ya kuma ƙara haɗa min kanku gaba ɗaya, Ameen." Dukkansu shiru suka yi. Mommah ta yi murmushi tana ji a ranta lallai ta yi sa'ar surukai ita kam.



... Washegari da sassafe me gyaran jikin da Mommah ta kirawo ta zo cikin gidan. Ɗaki guda aka ware musu cikin ƙanƙanin lokaci ta soma aikinta. Sosai yau ɗin Mommah ta bayar da wuta, dan so take komai dare a yau ta bawa kowa matarsa. Dan haka ta saka an gyara sashen da kowannensu ze zauna kafin a ƙarasa wanda Daddy ya sa aka fara ginawa. Dan tuni har ya ba da umarni an fara gina inda 'ya'yan nasa za su zauna. Da kuma wanda Ummeey da Abeey za su zauna ciki, amma su se sun dawo daga Makkah.


... Zaune yake cikin palourn hannunsa ɗauke da wani littafin addini yana karantawa. Wajen minti 10 se ya rufe littafin ya kalli tamfatsetsen agogon da ke manne a bangon ɗakin. Ƙarfe 9 daidai ya nuna. Ya ɗan lumshe idanunsa yana jin yanda bacci ke cin idanunsa. Qur'an ɗin da ke ajje a gabansa da wasu littafan ya ɗauka da niyyar shigewa ɗaki ya samu ya watsa ruwa ya kwanta. Sallamar Mommah da ya ji ita ce ta dakatar da shi, ya juya ya kalli bakin ƙofar lokaci ɗaya yana amsa sallamar. Tun kafin ya kai ƙarshen sallamar idanunsa suka sauka a kan Lulu da ke sanye cikin wata doguwar rigar atamfa. Mayafin da ya dace da atamfar saye saman ɗankwalin da ke zaune a kanta. Ta yi wani daƙiƙin kyau kamar ka saceta ka gudu.
Lumshe idanunsa ya yi yana buɗe su a kanta. Sam mantawa ma ya yi tare da Mommah ne suke tare, har se da ya ji muryar Mommah tace

"Toh zauna koh?" Se a lokacin ya tuna a inda yake, ya yi saurin basarwa yana ƙaƙalo murmushi ya nemi waje ya zauna jiki a sanyaye. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke kafin yace

"Mommah.." Ya yi maganar yana iya ƙoƙarinsa wajen ganin be kalli Lulu ba. Lulun da ke zaune gefen Mommah kanta a ƙasa kamar munafuka.

"Na'am.." Mommah ta amsa da hakan tana murmushi. Shiru ne ya wanzu na tsawon lokaci. Shi dai Gwani jira kawai yake ya ji me ye ya kawo Mommah da Lulun cikin ɗakin? Musamman da tun ganinta da ya yi duk baccin da yake ji ya tafi. A hankali Mommah ta soma faɗin

"Areef.."

"Na'am Mommah." Ya amsa da hakan yana ɗaga kai ya kalleta. Se ta cigaba da faɗin

"Ga Afaaf nan na dawo maka da ita.. Ba na jinka in Sha Allah.. Se dai duk da haka ina me roƙonka da ka riƙeta amana. Ka kuma kula da ita gwargwadon iyawarka." Be san sanda ya lumshe idanunsa ba, yana jin wani irin farin ciki na ratsa shi. Kenan idan dai har ya fahimci zancen Mommahn tana nufin ta dawo masa da matarsa kenan?

"In Sha Allah Mommah ba za ki kuka da ni ba.. Na gode Allah Ya ƙara girma."

"Ameen.." Mommah ta faɗa tana murmushi, daidai lokacin da ta maida dubanta kan Lulu. Babu buƙatar yi mata faɗa ko wata maganar, dan duk wani abu da ya kamata ta faɗa mata ta faɗa musu tun kafin su fito. Dan haka kawai hannunta ta kamo tace a hankali

"Bari na wuce Daughter.." Se a lokacin sannan Lulu ta ɗaga kai ta kalli Mommah cikin sanyin murya kamar Didi tace

"Tohm." Daga haka ba ta sake cewa komai ba. Ita ma Mommahn ba tace komai ba se ficewa daga ɗakin da ta yi. A hankali ya ɗaga kansa ya kalli Lulu da ta cigaba da zama a kan kujerar tana wasa da yatsun hannunta. Miƙewa ya yi a nutse ya koma ya zauna a kan kujerar da take kai. Yanda ta yi ƙasa da kai hakan ba ƙaramin ba shi damar kallanta ya yi ba. Ya ƙura mata ido kamar wanda ya soma ganinta yau. Se ya ga yau ɗin ta sake wani irin kyau, ta sake murjewa, farar fatar jikinta ta yi fresh ban da sheƙi babu abin da take yi. Be san sanda ya sake lumshe idanunsa a karo na barkatai ba saboda wani irin ƙamshi da ya daki cikin hancinsa. Ya buɗe idanun a hankali yana kokawa da zuciyarsa. Hannunsa ya saka ya kamo hannunta cikin nasa. Se a lokacin sannan ta ɗaga kai a hankali ta kalle shi. Tana shirin janyewa ya girgiza kai yana faɗin

"A'ah.. kar ki janye don Allah.." Se ta ɗan runtse idanunta kawai tana buɗewa a kan fuskar tasa. Murmushi me ƙayatarwa ya sakar mata wanda ta ji shi har cikin zuciyarta. Se dai ta basar, daidai lokacin da ya soma faɗin

"Kin yi kyau.." Ya ƙare yana sake aza mata idanunsa. Yanzu kam ba ta san lokacin da ta janye idanun nata ba. Se ya yi murmushi yana faɗin

"Tashi mu je." Ya faɗa har lokacin be saki hannunta ba. Miƙewa ta yi har lokacin ba ta sake kuskuren kallansa ba. A haka har suka ƙarasa cikin ɗakin. Gefen gado ya ƙarasa ya zaunar da ita, yana cigaba da mamakin sauyawar Lulun gaba ɗaya. Kwata kwata ta sauya, ta zama kamar ba ita ba. Duk ta yi wani irin sanyi. Hannunta ya saki a nutse ya furta

"Ki na buƙatar wani abu ne?" Girgiza kai ta yi ba tare da tace komai ba.

"Bari na shiga wanka." Ya faɗa yana kallanta. Ba ta ɗauka yana buƙatar amsa ba ne. Se dai jin idanunsa a kanta ya sanyata ɗaga kai ta kalle shi. Se ya langaɓar da kai kamar wani maraya. Ba ta san lokacin da murmushi ya ɗan suɓuce a kan laɓɓanta ba. Da sauri ta jinjina kai.
Se a lokacin ya miƙe sosai kai tsaye toilet ya faɗa yana murmushi. Se ta samu kanta da binsa da kallo har ya shige toilet ɗin. Ta dawo da kanta cikin ɗakin tana sauke numfashi. Bayan shuɗewar wasu mintuna se ga shi ya fito. Kai tsaye wata tattausar jallabiyya mara nauyi ya ɗauka ya sanya. Se ya sake fitowa kamar balarabe ya yi kyau sosai. Musamman kuma da ya kasance kwantacciyar sumar kansa a buɗe take. A inda ya barta a nan ya sameta. Ya ƙarasa ya ɗan rusuna kaɗan yace

"Na haɗa miki ruwa.." A hankali ta miƙe tana gyara zaman mayafin jikinta. Ya kalleta yana jira ya ga me za ta yi next. Se ya ga tana ƙoƙarin yin hanyar toilet ɗin da duk kayan jikinta. Da sauri ya riƙo hannunta, wanda hakan ya sanyata juyowa.

"Ba dai da dukka kayan nan za ki shiga ba?" Ya tambaya yana bin duk jikinta da kallo. Duk se ta ji wani iri saboda kallan da ta ga yana binta da shi. Se ta yi saurin jinjina kai tace

"A'ah zan cire."

"Na sani.. Amma ya kamata ki rage daga nan." Girgiza kai ta yi bayan ta kalle shi. Ya bi narkakkiyar fuskarta da kallo, se ya yi murmushi dan tabbas ta ba shi dariya saboda yanda ta marairaice fuska kamar wadda za a yanka. Se kawai ya jinjina kai yana faɗin

"Toh je ki." Ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauke tana wucewa toilet ɗin. Komawa ya yi ya nemi waje ya zauna. Gaba ɗaya baccin nan da yake ji tuni ya nemi nasa wajen. Ban da tsananin farin ciki babu abin da yake ji. Ta kwashe mintuna da yawa kafin ta fito daga ciki. Sanye da madaidaicin towel ta yafa mayafin jikinta. Tun da ta fito ta soma jin wani irin ƙamshi na tashi cikin ɗakin. A haka dai ƙamshin abinci ne me ɗan karen daɗi, se dai cikin lokaci ƙanƙani ƙamshin ya soma ɗaga mata hankali. Mazewa ta yi ta shiga takowa zuwa cikin ɗakin. Se dai duk taku ɗaya se ta ji ƙamshin na sake cika mata cikin hanci. Daidai lokacin da ta isa inda kayan da Mommah ta saka aka ɗinka musu haɗi da abayas da duk sauran kayan buƙata dai na mata ya shigo cikin ɗakin. Da sauri ta ɗaga kai ta kalle shi. Se kawai ta dakata ba tare da ta ɗauka ɗin ba. Daidai lokacin da ya ƙaraso. Hannu ya saka ya buɗe akwatin da ke kusa da shi ya ɗauko wata doguwar riga yana ɗagowa se ya ganta daf da toilet kamar za ta shige. Ya ɗauka ko ganinsa da ta yi ne ya sanya za ta koma cikin. Hakan ne ya sanya shi yin gaba ya yi saurin riƙota. Jan hannunta ta yi tana ƙoƙarin ƙwace jikinta saboda aman da ya taho mata saboda ƙamshin da kwata kwata be yi mata ba. Abin da shi kuma sam be fahimta ba. Dan kuwa riƙota ya sake yi da niyyar juyo da ita. Se kuwa ta shiga yi a jikinsa, duk yanda take ƙoƙarin riƙewa dan kar ta yi.

"Ya salaam.." Ya faɗa yana riƙe hannunta sosai. Ganin tana cigaba da yunƙuri ne ya sanya shi janta zuwa toilet ɗin. Hannu ya saka ya zame mayafin jikinta ya ajje shi gefe guda. Se kuwa ta cigaba da abinta a wahalce. Cike da tausayawa yake kallanta. Sosai ta wahala duk da yunƙurin ya fi aman da ta yi yawa. Taimaka mata ya yi yana riƙe da ita ta wanke bakinta. Kafin ya fito, kai tsaye kaya ya chanja. Babu jimawa se gata ta fito daga cikin toilet ɗin gaba ɗaya jikinta a sanyaye kamar mara lafiya. Da sauri ya miƙe ya ƙarasa ya riƙo hannunta.

"Sannu.." ya faɗa cike da tausayawa. Kawai jinjina kai ta yi dan da gaske wannan yunƙurin da ta yi duk ya wahalar da ita. Ashe haka Ammi ta sha wahala kafin ta haife su? Ta tambayi kanta idanunta na kawo ruwan hawaye. Ita mantawa ma ta yi towel ne kawai a jikinta. Haka ya kamata zuwa kan gadon ya zaunar.

"Ba na son ƙamshin.." Ta faɗa tana girgiza kai. Kallan inda take kalla ya yi. Se yanzu ya fahimci dalilin aman nata. Wato abincin da Baba Atine ta kawo ne ba ta san ƙamshinsa. Da sauri ya ƙarasa ya ɗauka ya fitar da shi daga cikin ɗakin. Se a lokacin ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe idanunta lokaci guda tana ɗan sauke numfashi a jere a jere. Babu daɗewa ya shigo cikin ɗakin. Ya ƙaraso inda take, cikin kulawa yace

"Me za ki ci? Ki na so a dafa miki wani abu ne?" Kallansa kawai ta yi, kamar ba za tace komai ba se kuma tace

"Ba na son cin komai." Numfashi ya ɗan saukar a hankali ya girgiza kai yace

"Dole za ki ji yunwa. Tun da abin da kika ci ɗin kin zubar.." Ya ɗan dakata a nan kafin ya ɗora da faɗin

"Ko za ki ci abincin gidan Ummeey na je na kawo miki yanzun?" Se ta sake girgiza kai tana ɗan runtse idanunta. Fuskarta ya bi da kallo tausayinta na ƙara kama shi. Kawai se ya juya da nufin ficewa daga ɗakin. Ta yi saurin sanya hannunta ta riƙo hannunsa. Dakatawa ya yi saboda be tsammaci hakan ba. Ya bi hannun nasu da kallo kafin a hankali ya juyo ya zuba mata idanunsa da ke cike taff da tausayinta.

"Ba zan iya ci ba Allah kuwa.. Ba na jin yunwa ko kaɗan. Idan kuma na ce zan gwada ci, ragowar na cikina ne ze dawo." Ta yi maganar da iya gaskiyarta. Iska ya fesar daga bakinsa yana cigaba da kallanta. A nutse ya shiga takawa zuwa inda take. Kai tsaye kusa da ita ya nema waje ya zauna. Cike da tausayinta ya ja ta cikin jikinsa ya rungume. Babu musu ta kwantar da kanta tana lumshe idanunta. Numfashinta da ke sauka da ɗan sauri sauri ya cigaba da fita a haka. Cikin kulawa yace

"Allah Ya miki albarka, Ya albarkaci abin da ke cikinki.. Kowacce uwa kafin ta haihu akwai kalar abin da take fuskanta. Ina fatan Allah Ya fito mana da shi lafiya. Ke kuma Ya ƙara miki lafiya." Ya yi maganar yana sake riƙota sosai cikin jikinsa. Kawai se ta sake runtse idanunta sosai tana jin soyayyar abin da ke cikin nata na ratsata. Burinta ɗaya ta ga ranar fitowar shi ta kalle shi a ce wai ɗanta ne. Sun kai kusan minti 10 a haka kowanne na saurarar bugun zuciyar ɗan uwansa. Zuwa lokacin numfashinta ya saitu ya koma fita daidai. Jin ta soma sauke numfashi a hankali ya sanya ya fahimci bacci za ta yi. A hankali ya ɗan zameta daga jikinsa yana komawa ya kishigiɗa kan gadon sosai. Ya kalli inda take se ya ga har ta farka, da alama dama baccin be yi nisa ba.

"Afuwan na tashe ki." Se ta ɗan yi murmushi tana binsa da kallo. Sauƙin halinsa na burgeta, abin da da ba ta san yana da shi ba, dan ba ma ta bawa kanta damar fahimtar hakan ba. Miƙa mata hannu ya yi yana ɗan yin ƙasa da kansa alamar ta zo. Kawai se ta bi shi da kallo. Se a lokacin ta tuna abin da ke jikinta. Ta girgiza kai tana ƙoƙarin jan bargo dan lulluɓe jikinta. Sauka daga gadon ta soma ƙoƙarin yi. Rashin fahimtar abin da ze saukar da ita ya sanya shi faɗin

"Wani abu?" Se ta girgiza kai tana ɗan turo bakinta gaba. Ya yi murmushi bayan ya kalli kyakkyawan ƙaramin bakinta da ta turo. Ba ta jira ya sake cewa komai ba ta yi yunƙurin sauka. Ya yi saurin saka hannunsa ya riƙota se gata ta faɗo a jikinsa. Ta buɗe ido da sauri tana ji kamar ta fashe da kuka.

"Ina za ki je?"

"Kaya zan saka fa." Ta faɗa tana yamutsa fuska.

"Kaya kuma? Wannan me ye a jikinki?" Ya tambaya yana kallan jikinta da ke tashin wani irin ƙamshi na musamman. Yanda ta ji idanunsa a kanta ne ya sanya ta yin baya wai dan ya dena ganinta. Se dai ba ta san hakan ba ta dama ya yi ta sake shigewa cikin jikinsa ba. Ya kuwa sake mata kyakkyawan masauki a jikin nasa.

"Don Allah.." Ta faɗa tana sake yunƙurin tashi.

"Ni wannan ya ishe ni.." Ya yi maganar cikin basarwa yana zagayeta da hannayensa. Maganar da ya yi ne ta sanyata ɗaga kai ta kalle shi. Se ya kashe mata ido ɗaya. Babu shiri ta janye kanta. Ita dai har yanzu ta kasa dena mamakin Gwanin. Da dai ta da gasken ba sakinta ze yi ba, se kawai ta haƙura. Tana jinsa yana gyara mata kwanciya. Ya kwantar da kanta a saman ƙirjinsa yana sake gyara kwanciyarsa sosai. Shiru ya wanzu na tsawon lokaci. Duk ta kasa sukuni, se gyara kwanciyar take yi. Zuwa can Gwani ya buɗe idanunsa da ke a lumshe.

"Afaaf.." Ya kira sunanta kamar ba muryarsa ba. Ɗaga kanta da ta yi shi ne ya tabbatar masa da ta ji shi. Hakan ne kuma ya sanya shi ɗorawa da faɗin

"Don Allah ki ce ki na sona Afaaf.. Ina ƙaunar jin wannan kalmar daga bakinki. Na daɗe ina dakon soyayyarki cikin zuciyata, na kuma sanar da ke. Se dai har yanzu ban samu amsata ba. Ki taimaki wannan zuciyar ki agaza ki amshi soyayyata. A yanzu ne kaɗai zan iya tabbatar da kalmar da kika faɗa min har cikin zuciyarki ki na nufin hakan." Ya ƙare a raunane. Shiru ta yi tana jin yanda zuciyarta ke bugawa. Har cikin ranta ta ji maganar nan ta shi. Ta kuma rasa me za tace, ta ina za ta fara? Shin da gaske abin da ta faɗa ɗin ya fito ne tun daga cikin zuciyarta ko kuwa ganin Iftihal ne kawai ya sanyata faɗin hakan? Girgiza kai ta yi tana jin ƙwallar da ba ta san dalilinta ba na tarar mata cikin idanu. Yau kam dole ta magantu, ya zama dole ta ce wani abu, ko ta huta, ta hutar da kyakykyawar zuciya irinta Gwani Affan.

"Don Allah ka yi haƙuri.. Wallahi ban san lokacin da hakan ta faru ba." Da ƙarfi zuciyarsa ta harba jin abin da ta faɗa. Kenan tana nufin ba ta sonsa?

"Ya ilahy.." Ya ambata a kan laɓɓansa. Se dai maganarta ta katse masa tunanin, sanda ta cigaba da faɗin.

"Tabbas ina sonka.. Se dai ban soka saboda kai wani ne ba. Ban soka saboda gano asalinka ba. Ban san lokacin da hakan ta faru ba, ban kuma yi niyyar bari ka sani ba saboda kar ka yi irin wannan tunanin nawa. Na yi ƙoƙarin cigaba da kasancewa asalin Luluta se dai na kasa. Duk yanda zan yi na kasa. Ban san da wanne ido

Please Login or Register in order to submit comment