Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da take riƙewa ba ya sanya yake ɗan dakatawa da karatun. Be dai bari wani abun ya yi tasiri a kansa ba ya cigaba da karatunsa. Se da ya ida littafin sannan ya rufe baki ɗaya ya ajje su gefe dan babu damar miƙewa saboda yanda ta yi kane_kane a kan cinyarsa. Cigaba da zama ya yi bayan gama karatun kamar me tunani. Can ya ɗan shafa buɗaɗɗiyar kyakkyawar sumar kansa kafin ya lumshe idanunsa cike da fatan bacci ya ɗauke shi saboda yanda yake jin jikinsa gaba ɗaya a sanyaye. Ko minti 2 be yi da rufe idanun nasa ba ya soma jin mutsu mutsunta ya ƙaru fiye da ɗazun. Se ya yi saurin buɗe idanun nasa a kanta dan ganin dalilin hakan. Daidai lokacin da ta ida buɗe idanunta se kuwa suka sauka a cikin na Gwani da shi ma ya sauke nasa idanun a kanta. Saboda baccin da ke kanta ba ma ta fahimci waye ba. Cikin sauri ta miƙe zaune dirshan a kan gadon tana maida idanunta kan hannunta da ta ji alamar abu a ciki. Tana kai idanunta dake cike da bacci kan hannun nata se ganin wani hannun ta yi a ciki. Cikin matuƙar gigicewa ta runtse idanunta da har yanzun bacci be sake su ba ta jefar da hannun a matuƙar razane, ta kuma soma ƙoƙarin miƙewa dan dira daga kan gadon. Fahimtar abin da ze biyo baya tun da ta yi wannan tsoratar ya sanya shi saurin saka hannunsa ya janyota. Cikin en sakanni se ga ta a jikinsa. Ta buɗe baki za ta yi ƙarar da ta saba yinta, babu zato babu tsammani se jin tattausan laɓɓansa ta yi a kan nata red lips ɗin...


MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO48*


___Sabon al'amarin da ta ji wanda ba ta taɓa zata ba, ba kuma ta yi tsammani ba ya sanyata saurin wara idanunta. A matuƙar tsorace zuciyarta na wani irin harbawa kamar za ta bar ƙirjinta. Cikin sakannin da basu wuce a ƙirga su ba ta sanya hannunta bayan ta tattaro duk wani ƙarfi da take da shi ta sanya hannunta tana ƙoƙarin ture shi daidai lokacin da jikinta ya ɗauki rawa. Ba da niyyar komai ya haɗe bakin nasu waje ɗaya ba se dan kar ta yi ihun da ta saba. Se dai kuma yanda ya ji tana cigaba da ture shi a haukace ya sanya shi kamo lips ɗinta na ƙasa ya shiga kissing nata a nutse yana ƙoƙarin ganin ya saka idanunsa cikin ƙwayar idanunta. Se dai yanda cikin ƙanƙanin lokaci wata irin kasala ta rufe shi ya sanya shi lumshe idanunsa daidai lokacin da ya saki lips ɗin nata da niyyar sumbatar na sama. Ta yi wani yunƙuri ta janye bakinta da ƙarfi sannan cikin ƙarfin halin da ta aro ta zame jikinta daga nasa ba tare da samun wani tsaiko ba. Dan kuwa yanayin yanda ilahirin jikinta ke karkarwa ya fahimtar da shi yanda take a tsorace. Don haka kawai se ya saketa har lokacin idanunsa na a lumshe ne. Jikinta na wata irin karkarwa kamar wadda aka watsawa ruwa me masifaffan sanyi ta faɗa cikin wannan ƙaramin ɗakin wanda a nan aka zuba mata kayan kitchen ɗinta kamar wadda aka tunkuɗo. Wani marayan kuka ta fashe da shi lokacin da ta zube a ƙasa kamar wadda aka yi wa mutuwa. Ta kwantar da kanta a dandagaryar simintin ɗakin ta shiga rera kukan cikin matuƙar tsoro da bugun zuciyar da har yanzun be saitu ba. Kuka take kamar wadda aka ce mahaifiyarta ko mahaifinta ya rasu. Kuka irin me tsuma zuciyar me sauraro ɗin nan. Duka hannayenta biyun na kan laɓɓanta tana gogewa da ƙarfi kamar wadda za ta tsinka leɓen. Ta kasa dena kukan, ta kasa yin shiru. Ta kuma kasa dena goge bakinta da take ji har abada Gwanin ya gama cutarta. Hannu ta kai ta taɓa kanta dake a buɗe, ta kuma kalli jikinta dake a buɗe babu hijab bayan ta san da shi ta kwana, kenan duk shi ne ya cire mata? Ta sake fashewa da wani sabon kukan tana curewa waje ɗaya. Ba ta taɓa zaton ɗan iska ba ne shi se yau. Ta sake kai hannunta kan bakinta a karo na barkatai tana kuma dirjewa kamar me wanki. Manyan idanun nan nata sun yi luhu_luhu, har kuma lokacin ba ta dena kukan ba.

Zazzafar iska Gwani ya fesar lokacin da ya ji ta fashe da kukan. Be yi tunanin za ta ɗauki tsawon lokaci tana irin wannan kukan na tashin hankali ba. Dan kuwa har wani tsayawa take yi ta ajje wasu taggwan ajiyar zuciya sannan ta ɗora.

"Ya ilahy.." ya yi maganar yana ɗan shafa goshinsa. Yana zaune yana jiyo ta tana cigaba da kukan kamar ba ta da niyyar denawa. So yake ya tashi ya je duk da ya san ba ze iya rarrashinta ba ko me kuwa ze yi. Dan ya san idan ma zuwa ya yi dan rarrashin nata se dai ta tara masa jama'a. Kai yana ma da tabbacin ba za ta saurare shi ba. Ya ɗan taune lips ɗinsa na ƙasa lokacin da ya gama tunanin. Lumshe idanunsa ya sake yi jin da ya yi har yanzu akwai zaƙin bakinta a kan nasa. Kamar wadda ta saka wani abu me zaƙi a kan laɓɓan nata. Ya miƙa hannu ya ɗan shafi lips ɗin, ya kalli hannun kafin ya ɗan yi wani murmushin yaƙe kana ya girgiza kai. Har bayan shuɗewar wasu mintuna masu yawa Lulu ba ta dena kuka ba. Se dai ba kamar ɗazu ba yanzu ta rage sautin ne da alama muryarta ta soma gajiya. A hankali ya miƙe daga kan gadon ya shiga takawa a nutse zuwa dakin. Tana zaune cure waje ɗaya tana cigaba da raira kukanta. Hannayensa duka biyun saƙale a ƙirjinsa ya shiga kallanta kamar me nazari.

"Ita wai ba ta gajiya da kuka ne?" Ya tambayi kansa har lokacin yana kallanta.

"Ki yi shiru ki dena kukan.." ya yi ƙarfin halin faɗin hakan a nutse. A matuƙar zabure ta miƙar da kanta daga kan cinyarta ta juya dan tabbatar da muryar da ta ji. Se kuwa suka yi 4 eyes. Ta buɗe baki da niyyar ƙwalla ƙara saboda yanda ta tsorata. Se ta tuna abin da ya faru yanzun nan, abin da ya sanyata fasawa kenan. Se ja da baya da ta yi a tsorace cikin muryarta da ta dashe saboda kukan da ta sha tace

"Ka fita.. ka fita.. ni ka fita.." ta faɗa tana girgiza kai wasu hawaye na zubowa a kan fuskarta lokaci ɗaya tana sake ƙanƙame jikinta. Ya gaji da ganin kukan gaba ɗaya dan haka cikin kwantar da murya yace

"Shi kenan.. Amma dai ki dena kukan nan" Daga haka ya fice daga ɗakin cike da mamaki. Shi kam har yanzu idan Lulun ta yi wani abu se ya dinga ganin kamar ba ita ba. Da ma haka take? Se tsiwa amma tsoro kamar farar kura. Daga sumbata kawai duk ta bi ta susuce ta rikirkice. Cigaba da zama ya yi a kan gadon se dai gaba ɗaya hankalinsa na cikin ɗakin ne. Ta ɓangarenta kuwa ko dan kar ya yi tunanin maganarsa ta ji shi ya sa ta dena yin kukan ya sanyata cigaba da yi cike da haushinsa da ya kasa sakinta. Har se da ta yi me isarta, ta gaji, jikinta ya mutu, kuzarinta ya ƙare sannan ta yi shiru ta koma sauke ajiyar zuciya. Se a lokacin sannan shi ma ya sauke wata ajiyar zuciya yana sake furzar da iska daga bakinsa.

"Wannan yarinya.. Wannan yarinya.." ya faɗa a kan laɓɓansa yana girgiza kai.

Har wajen asuba daga shi har ita babu wanda ya runtsa. Shi hankalinsa gaba ɗaya na kanta, yayin da ita kuma take tsoron ta kwanta abin da ya faru ɗazu ya sake faruwa. Duk da wani irin gumi da take ta haɗawa cikin ɗakin saboda babu fanka amma hakan be sanyata fita daga ciki ba. Kafin asubar ta yi se ya miƙe ya faɗa toilet ya yi wanka kafin ya ɗauro alwala kamar ko yaushe. Be kalli ɗakin da take ba kai tsaye ya fice dan zuwa Masallaci. Ita sam ba ma ta san da fitarsa ba. Haka ta cigaba da zama cikin ɗakin kamar wata marainiya. Mintuna masu ɗan dama ya kwashe a masallacin kafin ya dawo duk dan saboda kar ya zauna ya dawo ya tarar da ita ba ta motsa a inda ya barta ba. Aikuwa kamar yanda ya tsammata ko da ya leƙa ɗakin tana nan zaune inda ya barta kamar wadda aka dasata. Ya girgiza kai yana sauke ajiyar zuciya.

"Tashi ki je ki yi sallah.." ya yi maganar lokacin da ya koma ainahin Gwaninsa. Shiru ta yi kamar ba ta ji ba tana cuccuno baki gami da haɗe rai. Ya fahimci ta ji abin da ya faɗa hakan ne ya sanya shi ƙarasa shigowa cikin ɗakin yace

"Shi kenan yi zamanki bari na taimaka miki.." ya yi maganar yana nufarta gadan gadan. A million ta miƙe jikinta na soma rawa ta fice daga ɗakin har kusan tuntuɓe ta yi. Ya yi murmushi me ƙayatarwa yana girgiza kai. Ficewa ya yi daga ɗakin ya nemi waje ya zauna dan yin karatu. Be sake bi ta kanta ba ya barta dan ta samu ta yi abin da ya dace. Aikuwa hakan ba ƙaramin daɗi ya mata ba. Dan kuwa har wanka se da ta yi, sannan ta dawo ta ɗebi kayanta ta wuce wannan ɗakin da yanzun zan iya kiransa da kitchen saboda kayan da ke cikinsa. Ko bayan ta gama abin da zata yi ma se ta cigaba da zama a ciki tunani fall cikin zuciyarta.


... "Ki ɗauka ki kira Abbanki.." ya yi maganar yana ajje mata wayar a gabanta. Ba ta ɗaga ido ta kalle shi ba se murguɗa baki da ta yi tana ɗauke kai. Shi ma be jira amsarta ba ya fice daga ɗakin. Bayan wajen minti 20 be sake shigowa cikin ɗakin ba. Wayar tasa kuma na ajje kusa da itan dai. Se a lokacin ta saci kallan wayar tasa. Se kuma a hankali ta miƙe cikin takatsantsan ta shiga leƙa palour dan tabbatar da yana ciki ko baya nan. Se da ta tabbatar baya nan sannan ta dawo ta ɗauki wayar cikin zumuɗi ta danno number Abba. Tun da ta soma ringing fuskarta take murmushi har zuwa lokacin da ya ɗaga.

"Hello Abba." Ta faɗa tana jin wani irin rauni na zuwar mata.

"Na'am Afaaf..." Daga can ɓangaren Abba ya faɗa yana jin daɗin jin muryar ɗiyar tasa. Kawai se ta shiga rera kuka kamar wadda aka yi wa wani abu. Miƙewa Abba ya yi daga inda yake zaune yace

"Me ya faru Lulu? Wani abun ya faru ne?" Girgiza kai ta shiga yi kamar Abban na gabanta. Se da ƙyar ta buɗe baki tace

"A'ah Abba babu komai.. Barka da wannan lokaci.." ta yi maganar a haɗe lokacin da ta goge hawayen fuskarta. Se a lokacin sannan Abba ya sauke ajiyar zuciya a ransa yana fata da addu'ar Allah ya sa i zuwa yanzu ɗiyar tasa ta yi haƙuri ta dangana da wannan aure.

"Toh kukan ya isa haka uhmm?" Kamar yana gabanta ta sake ɗaga kai tana murmushi. Babu laifi sun taɓa hira sosai irin wadda rabon da su yi ta tun kafin aurensu Lulun. Kafin daga bisani ya haɗata da Ammi dan su gaisa. Sosai suka yi hira inda Ammin ke sanar da ita ɗazun suka gama waya da Didi. Se da Lulu ta yi yanda za ta yi ta karɓi number da za ta samu Didi sannan suka cigaba da hirar.

"Babu dai wata damuwa koh?" Ammi ta tambaya cikin kulawa. Hannu Lulu ta saka ta sake goge bakinta se kace wadda aka ce mata Ammin za ta iya fahimtar wani abu. A shagwaɓe tace

"Babu komai Ammi."

"Toh madallah.." Daga nan suka yi sallama bayan ta yi wa Abba da ita kanta Ammin godiya na kayan da aka mata jere da su. Dan babu ƙarya ta ji daɗinsu. Cike da jin daɗi Ammi ta ajje wayar tana sake yi wa ɗiyar tata fatan shiriya. Kai tsaye call logs ta shiga bayan gama wayar tasu ta goge number Abban da ta kira gaba ɗaya dan ma kar ya gane ta ɗauka wayar tasa ta yi kira bayan a farko ta nuna ba ta so. Se ta maida wayar inda ta ɗauketa ta sannan ta koma can nesa da wayar ta kama kanta.



... "Mommah bari na koma." Didi ta faɗa tana miƙewa.

"A'ah tafiya za ki yi Daughter?" Murmushi Didi ta yi tace

"Ehh.."

"Tohm shi kenan.. Ki na ji na?" Mommah ta faɗa tana kallanta. Se da Didin ta amsa da "Ehh" sannan Mommah ta fara faɗin

"Kar ki gaji da yin duk abin da ya dace wa Hajiya Salma In Sha Allah nan gaba kaɗan komai ze zama tarihi bi iznillahi.'

"Toh Mommah na gode sosai.. Allah ya saka da alkhairi." Murmushi Mommah ta yi tana sake yabawa da hankalin Didin kafin tace

"Babu godiya tsakaninmu Daughter kullum ina faɗa miki." Martanin murmushin Didi ta maidawa da Mommah sannan tace

"Toh Mommah na gode.." Girgiza kai Mommah ta yi tana dariya jin da ta yi ta sake yin godiyar. Ta fahimci ta riga da ta saba ne, shi ya sa komai ƙanƙantar abun da ka mata se ta yi godiya. Binta da kallo Mommah ta yi lokacin da take ficewa daga cikin ɗakin cikin nutsuwar nan tata.

"Allah ya shiga lamuranki Afrah.." Shi ne abin da Mommah ta faɗa tana ɗaukar remote dan chanja channel.

A nutse take takawa a ƙatuwar harabar cikin ainahin inda ginanen gidan suke, tana tafe tana tunanin er uwatta kamar ko yaushe. Dukka hankalinta na ƙasa wato inda take kalla, hakan ne ya sa ba za ta iya sanin abin da ke gefenta ba.

Kaseem ke driving yayin da Bad Man ke wajen me zaman banza yana latsa wayarsa da Bluetooth cikin kunnensa yana jin waƙa wadda ya ƙurewa volume kamar kunnensa ze tsage. Wanda shi a wajensa hakan ko kaɗan be dame shi ba, se ma ɗan jijjiga kai da yake yi wani lokacin alamar kiɗan na masa daɗi. Yana gama parking duka su biyun suka sauka. Babu ɓata lokaci suka soma takawa zuwa cikin gidan.

"Kaddai fa mu je ba ya nan.." Kaseem ya faɗa yana duban Bad Man da yanzun ya cire Bluetooth ɗin.

"I don't think so.." ya yi maganar a gajarce. Ɗaga kafaɗa Kaseem ya yi ba tare da yace komai ba suka cigaba da takawa. Daidai lokacin da suke dab da sashensu Bad Man Didi ta zo wucewa a nutse. Cikin sakannin da basu wuce 3 ba idanun Kaseem ya sauka a kanta lokacin da take ƙoƙarin shiga cikin sashen..


MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO49*

___Be iya ganin fuskar wace ce ba, se bayanta kawai da ya iya gani. Saboda yana ɗagowa ita kuma ta shige sashen. Se ya taɓe baki kawai yana mamakin yanda ya ji ya so ganin fuskar. Babu wanda ya sake cewa komai har suka isa sashen Daddyn.



... Be samu zuwa wajen Hero ɗin ba saboda abubuwan da suka cakuɗe musu shi da Kaseem, dan haka ya yanke bari se gobe ya je.

A bakin titin ya sauka daga napep ɗin da ya ɗauke shi tun daga bakin layinsu. Be fi minti 2 da tsayuwa wajen ba haɗaɗɗiyar motar Bad Man ta tsaya a gabansa. Be ƙarasa inda motar take ba se da Bad Man ya sauke glass ɗin motar sannan Gwani ya ƙarasa ya buɗe ya shiga. Hannu ya miƙa masa a nutse lokaci ɗaya yana furta

"Salamu Alaika." Hannu Bad Man ya miƙa masa suka gaisa sannan ya amsa sallamar lokacin da ya maida kansa kan titi. Babu wanda ya sake cewa komai Bad Man ya ja motar suka bar wajen.

A bakin wani madaidaicin joint ya yi parking. Gwani ya kalli wajen a nutse kamar me nazartar wani abun. Se kuma ya sauke numfashi yana dawo da dubansa kan Bad Man.

"Za ka shiga ne?" Bad Man ya tambaya. Jinjina kai Gwani ya yi, dan ya fi so ko meye za a yi a yi shi a gabansa.

"Olright.." ya faɗa yana ɓalle murfin motar ya fita daga cikin motar. Babu ɓata lokaci shi ma Gwani ya fito, kusan a tare suka shiga wajen kowanne na taku cike da mazantaka da burgewa.

Tun daga nesa yake kallan Bad Man dake tunkaro inda yake. So yake ya ƙaryata hakan, se dai kuma ya kasa. Dan haka kawai se ya zuba ido ya cigaba da kallan Bad Man ɗin har ya ƙaraso inda yake. Kallon kallo suka shiga yi a tsakaninsu. Bad Man ya sake tamke wannan fuskar. Kamar ba ze zauna ba se kuma ya nemi waje ya zauna daidai lokacin da Gwani ke jan kujera ya zauna. Maida dubansa Hero ya yi kan Gwani ya kalle shi na tsawon sakanni sannan ya maida kan Bad Man

"Da ma ka na nan?" Hero ya yi ƙarfin halin tambaya yana kallansa.

"Yeap. Ina wayarka?" Bad Man ya yi maganar yana kallan cikin idanunsa.

"Wayata kuma?" Ya maimaita cikin rashin fahimta. Jinjina kai Bad Man ya yi dan sake tabbatarwa Hero abin da ya faɗa

"Babu waya a hannuna ban da wannan.." Ya yi maganar yana nuna keypad ɗin da ke a hannunsa. Be ce komai ba Bad Man se wayar Gwani da ya ɗaga ya ɗora a kan bench ɗin dake gabansu ya turata. Riƙeta ya yi kafin ta iso wajensa, kafin ya ɗauka ya riƙeta a hannunsa yana ɗora idanunsa a kai daidai lokacin da Bad Man yace

"Gaskiyar al'amari za ka faɗa mana.." Na tsawon sakanni Hero yake kallam hoton kamar yau ya fara ganinsa. Kaddai binciken ainahin inda hoton ya fito suke yi? Idan kuwa haka ne ba ze faɗi gaskiya ba. Idan ma wani abun suke son ji se dai ya sako maganar Jakadiya Ladi.

"Ban san komai ba.." ya yi maganar yana turo wayar gaban Bad Man. Murmushin gefen baki Bad Man ya yi kafin ya girgiza kai. Da ma ya san za a rina, don kuwa sarai ya san waye Hero.

"Ina ga ka manta ranar da aka ɗauki hoton mu na tare koh?" Ya ƙare maganar yana kallansa.

"Kashhh.." Hero ya faɗa a kan laɓɓansa tunawa da ya yi lallai tabbas suna tare abin ya faru. Idan kuwa haka ne lokacin da yake ta jira ne ya zo. Lokacin da ya ci wa Ladi alwashi ita ce ta zo. Hakan ne ya sanya shi gyara zama. So yake ta ɓaɓewa Ladi ta zame mata jagwal, ya yin da ze tsaya a gefe ba tare da ya shiga ciki ba. Dan kuwa ze san yanda ze yi ya zame kansa daga cikin wannan case ɗin.


"Kar ka ɓoye min Hero.. Kawai mu na son sanin gaskiya ne. A yi komai a nan a gama.. idan kuma ba haka ba ka san halina, ka san waye ni, ka san abin da zan iya, ka kuma san wanda ba zan iya ba.." ya ƙare still dai yana kallansa. Shi ma Heron kallansa yake yi kamar masu shirin fara dambe.

"Da laifina ne cikin harkar nan ba zan faɗa muku komai ba. Amma saboda ka san me hannu ciki ya sa zan sanar da kai.." Ya riga ya san halin Bad Man ɗin. Ya san idan har yace ze yi taurin kai ba ze ji da daɗi ba. Duk da shi ma ba ya ji amma kuma Bad Man ya fi shi taurin kai, uwa uba kuma kuɗin da suke da shi. Sosai Gwani ke kallansa jin da ya yi ze faɗi gaskiyar abin da ya faru. Cikin ƙankanin lokaci ya sanar da su duk wani abu game da Ladi tun lokacin da ta jawo shi cikin harkar. Shiru suka yi gaba ɗaya suna nazarin maganganun da ya faɗa ɗin. Kamar babu wanda ze ce komai se can Gwani yace

"A ina take da zama?" Da sauri Hero ya kalli Gwani kamar da mamaki a kan fuskarsa. Se dai ya basar kawai ya faɗa musu inda za su sametan. Ya ƙare da faɗin

"Amma yanzu ba ta cikin Kano.. amma cikin satin nan za ta dawo."

"Ya aka yi ka sani?" Bad Man ya faɗa yana kallansa. Murmushi Hero ya yi kana yace

"Uhmm manta kawai.."

"Zan nemeka..." Bad Man ya faɗa lokacin da ya miƙe a kan ƙafafunsa.

"Ohk." Hero ya amsa da hakan. Miƙewa Gwani ya yi yanzun ma kamar haɗin baki a tare suke tafiya gwanin burgewa. Binsu da kallo Hero ya yi har suka fice. Se can kuma ya yi dariya yana girgiza kai.




... "My boy.." Mom ta faɗa tana murmushi. Ƙarasowa ya yi inda take bayan ya maida mata da martanin murmushin yace

"Mom.. kin san dai." Ta riga ta san ƙorafi ne ze biyo baya hakan ne ya sanyata saurin katse shi da faɗin

"Naa ji.. nemi waje ka zauna." Babu musu ya nemi waje kamar yadda ta faɗa ɗin ya zauna. Se da suka sake gaisawa sannan tace

"Dis week In Sha Allah zan je ganin likita.. And ka san lokacin da nake ɗauka kafin na dawo.. So ba na so na barka cikin gidan nan saboda ban san me za a maka idan ba na nan ba. Shi ya sa na ce bari na maka magana idan za ka bi ni well. Idan kuma ba za ka bi ni ba se ka je wata ƙasar ranar da na tafi, idan ya so se mu dawo tare." Shiru ya yi yana kallan Mom ɗin lokaci ɗaya kuma yana nazarin maganar tata. Sam wannan ba abun kamawa ba ne. A yi masa wani abu jariri ne shi?

"Mom ƙaramin yaro ne ni?"

"No Areef.. Amma ka san a wajena yaron ne koh? Kuma ba ka san halin mutane ba ne, ni kuwa ina jin tsoro." Girgiza kai ya yi ba tare da ya kalli Mom ɗin ba yace

"Ki yi haƙuri Mom.."

"Ka na nufin ba za ka je ba?"

"Mom.. ba na son zuwa ne.." ya katseta da faɗin hakan a ƙagauce.

"Ba za ka iya yin wani abu dan ni mahaifiyarka ba?" Shiru ya yi yana mamakin wannan abu na Mami. Dan dai ta bar yi masa zancen ya sanya shi faɗin

"Shi kenan. Zan yi tunani a kai.."

"Sure?" Ta tambaya tana kallansa. Se ya jinjina kai yana ajje numfashi a nutse. Daga haka ya tashi fice daga ɗakin. Mom ta bi shi da kallo, a ranta tana fatan a ce ya yadda da wannan ƙudurin nata.


.... Duk abin da take yi jikinta a matuƙar sanyaye yake. Tana kuma yi cike da takatsantsan musamman saboda ciwon da ke ƙafarta. Ita ji take ma kamar kar ta yi komai. Se dai kuma idan ta tuna da Mommah se kawai ta haƙura ta cigaba da abin da take yi. Se da ta gama komai sannan ta sauke numfashi tana ɗaukar Coffee ɗin dan wucewa da shi ɗakin Bad Man.

Mayukansa masu mugun ƙamshi kaɗai ya shafe jikinsa da su. Ko bi ta kan sumar kansa be yi ba. Sumar da ko da ze ɗauki tsawon sati ba tare da ya taɓata ba babu wanda ze fahimta, saboda yanda take a gyare, a kwance tsaff tsaff. Towel ɗin da ke kan ƙugunsa ya zame ya maida shi ma'ajinsa kafin ya dawo cikin ɗakin inda ya ajje abubuwansa da ɗazun bayan rabuwarsa da su Hero ya taho da su cikin takatsantsan ɗin nan dai da ya saba ba tare da an gan shi ba. Saboda shi ya fi so ko da kwalɓewar ze yi ya yi a gida ba se ya je wani wajen ba, ballantana ma wasu su gan shi. Idan kuma ya yi a wajen toh kamawa ta yi, amma dai ta fi ganewa a dan. Kwata kwata ya ma manta da wani kulle ƙofa idan ze kwalɓe. Ya nemi waje ya zauna. Hannu ya kai ya ɗauka kwalbar ya shiga juyata cikin hannunsa. Be san wace kala ba ce, shi dai kawai yana buƙata ne shi ya sa ya siya duk da be taɓa shan kalarta ba. A cikin ɗan ƙaramin cup ɗin nan ya zuba ya kai bakinsa. Lumshe jiƙaƙƙun idanunsa ya yi lokacin da ya ji ta cikin bakinsa. Se ya buɗe idanunsa ya cigaba da kwankwaɗa kamar babu gobe. Se da ya gama tsaff sannan ya miƙe yana ɗan wawwara madaidaitan idanunsa, ya maida

Please Login or Register in order to submit comment