Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yi da idanunta ƙirjinta na bugawa, lokaci ɗaya kuma wani irin tausayinsa na kamata. Sosai kalamansa ke cigaba da lugude a cikin kunnuwanta. Zuciyarta na cigaba da bugawa da ƙarfin gaske. Kalamansa sun matuƙar tsoratata, sun kuma sanya ta ji duk wani ƙwarin gwuiwarta na zagwanyewa. Ta rasa yanda za ta yi ne. So take ta sake tabbatarwa da gasken ya dena shan komai ko kuwa dai ya yi haka ne dan ta amince da shi ya koma halinsa na baya. Wannan dalilin ne ya sa har yanzun take nuna tamkar ba ta amince da shi ba. Take cigaba da banzartar da shi, take cigaba da share shi. Take kuma cigaba da wana shi. Se dai ba ta sani ba ashe hakan na dab da yiwa zuciyarsa illah. Ba ta tunanin a yau ɗin za ta iya barin wannan ranar ta wuce ya cigaba da kasancewa da tunanin ba ta ƙaunarsa. Ya cigaba da tunanin tsanarsa ta yi. Idan kuwa har ta bari hakan ta faru toh tabbas da ta kasance butulu, muguwa kuma mara tausayi. Runtse idanunta ta yi tana ƙoƙarin buɗewa ta sake jiyo muryarsa yana faɗin.

"Kin ƙi amince min, kin ƙi amincewa na dena shan komai, kin kuma ƙi amincewa ina ƙaunarki. Har yanzun na gaza jin kalmar ina sonka daga bakinki, kalmar da nake ta jira ta fito daga bakinki. Se dai har yanzu shiru. Na yi tunanin zan iya jurewa tsawon lokaci cigaba da kasancewa da ke ba tare da ki na sona ba. Ashe zuciyata ba ta da wannan juriyar. Ban kuma tashi gasgata hakan ba se yau, a yanzun nan. Saboda haka ina so ki sani duk ranar da aka wayi gari aka ga na mutu, toh zuciyata ce ta buga kuma a dalilin sonki." Ya ƙare yana fidda wani huci wanda yake fitowa tun daga zuciyarsa dake zafi. A zabure ta ɗaga jajayen idanunta ta kalle shi. Zuciyarta na wani irin bugawa. Kallansa take yi kalaman da suka hamma fita daga cikin bakinsa na yi mata amsa kuwwa cikin dodon kunnenta. Cikin ƙanƙanin lokaci bugun zuciyarta ya sauya, jikinta ya ɗauki rawa, hawaye suka shiga saukowa a kan kuncinta. Wani irin jiri ta ji yana neman kayar da ita cike da tsoro fargaba da kuma tsananin tashin hankalin da maganar da ya faɗa ta jefata. Kawai se ta tafi da gudu ta rungume shi, ta saka hannayenta duka biyu ta riƙo wuyansa tana fashewa da kuka.

"Ina sonka.. wallahi ina sonka.. Don Allah ka dena faɗar hakan, ka yafe min don Allah.." Cakk numfashinsa ya tsaya na wucin gadi, wanda hakan ne ya sa gaba ɗaya tunaninsa ma ya dakata. Se da ya yi azamar kai wa numfashinsa wata cafka kafin ya dawo fita da sauri sauri. Ji yake kamar ba gaskiya ba ne abin da kunnensa ke jiyo masa. Tsoro yake yi kar ya je wani daddaɗan mafarki ne ke neman yaudararsa. Se dai haka nan kawai zuciyarsa ta ƙi aminta da mafarki yake yi. Shin da gaske ne abin da ke faruwa? Da gaske ne abin da kunnuwansa ke ji? Wannan rungumar da ta masa, jinta da ya yi a cikin jikinsa shi ne abin da ya sanya shi tabbatar da abin da kunnuwansa ya ji gaskiya ne. Ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauke yana gyara tsayuwarsa wani irin farin ciki mara misaltuwa na mamaye ilahirin jikinsa. Cikin azama ya saka duka hannayensa ya rungumeta da ƙarfi kamar wadda za a ƙwacewa ita. Wata irin runguma ya yi mata kamar jaririn da aka haifa yau, wanda muddin aka sake shi ze faɗi ne ƙasa. Idanunsa a lumshe suke, har kuma lokacin zuciyarsa ba ta bar harbawa da ƙarfin gaske ba. Dan kuwa ita da ke jikinsa kowanne bugun zuciyarsa se ta ji shi a jikinta. Tsoron da ta ji ya sake ziyartarta shi ne ya tilasta mata sake ruƙunƙume shi kamar za ta koma cikinsa..



✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO80*


___Daga runguma fa se ga ɗan mutumunku ya soma zarmewa. Dan kuwa yana rungume da ita ya ɗagata gaba ɗaya, be dire ko ina ba se kan gado. Ba ta san shirme ta yi ba se da ta ji sabbin al'amura, ta kuma fuskanci inda Bad Man ɗin ya dosa. Se a lokacin sannan ta soma ƙoƙarin janye jikinta cike da tsoro, kar abin da ta guda rannan yanzu ya faru. Se dai shi kam ya yi nisa ba ya jin kira, gefe guda kuma wutar soyayyar Didi na ƙara masa ƙaimi. Duk da yanda take ji a zuciyarta tana son shi, za kuma ta so abin da yake so tun da har tana son shi, amma yanzu se da ta ji komai na neman sire mata. Ta ji tamkar ma tace ta dena son na shi ko ze rabu da ita. Se dai fa Bad Man yau ɗin be ji wani kira ba, dan kuwa toshe kunnensa ma ya yi, kar a sake maimaita abin da ya faru rannan. Kar kuma tausayin abar ƙaunar ta shi ya hana shi maidata tasa gaba ɗayanta. Hakan ne kuwa ya faru, dan yau ɗin se da Bad Man ya maida Didi ta zama tasa halak malak.


Wata irin soyayyar Didin ke ratsa duk wata gaɓa ta jikinsa, ya rungumeta cikin jikinsa yana ji tamkar ya maidata ciki. Ji yake zuciyarsa na azalzalarsa kamar me, be san me ze ce ya ji sauƙi ba. Kawai se ya lumshe idanunsa yana sake rungumeta. Yana jin yanda numfashinsu ke fita kusan a tare. Daidai lokacin da tulin hawayen da suka daɗe da taruwa cikin idanunta suka sauka a kan ƙirjinsa. Ya runtse idanunsa yana jin yanda zuciyarsa ta harba. A hankali ya ɗan gyara zamansa, ita ma cikin takatsantsan ya gyara mata tata kwanciyar a jikinsa.

"Yi haƙuri my dear.. Kukan nan na min illa a zuciya." Ya faɗa yana ɗan runtse idanunsa, dan tabbas yana nufin abin da ya faɗa ne. Ba ta san me za tace ba, ba kuma ta san ya za ta yi ba. Ba ita take barin hawayen su zuba ba, da kansu kawai suke zubowa, saboda yanda take jin jikinta. Ita da ta san haka ne ma ba za ta taɓa sanar da shi tana son shi ba. Da ta san haka ne ba za ta taɓa rungumarsa ba. Ga shi nan daga runguma an jawo mata jangwangwana, dan ba ta ji ko iya motsa jikinta za ta iya yi. A hankali kuma se ya soma zameta daga jikinsa, ta yi azamar riƙe shi sosai tana runtse idanunta. Ya fesar da iska daga bakinsa yana faɗin

"Ohh sorry babe." Ya faɗa har jikinsa yana jin wani irin tausayinta na sake ratsa shi. Se da ya sauke numfashi yana tunanin ta ina ze fara, kafin daga bisani ya yi amfani da hannunsa wajen ɗagata gaba ɗaya ya kwantar da ita gefe a hankali, kana ya miƙe. Se da ya ranƙwafo ya manna mata kiss a goshi yana kallan jajayen idanunta da yanzu suke a rufe. Ya sake fesar da numfashi a wahalce yana cigaba da kallanta, kafin ya tashi ya shige toilet. Kai tsaye wanka ya yi, ya kwashi mintuna masu dama kafin ya fito, bayan ya cika bathtub da ruwa me ɗumi. Fitowa ya yi ya ƙarasa ya ɗauki riga da wando marasa nauyi ya saka. Ƙarasawa ya yi inda ya bar Didi, kamar yanda ya barta yanzun ma a nan ya sameta. Ya ɗan yamutsa fuska yana sake jin tausayinta. Ƙarasawa ya yi a nutse, be ce da ita komai ba ya saka hannu da niyyar ɗaukarta. Ta buɗe manyan brown eyes ɗinta da suka ɗan yi ciki ta kalle shi, se ta maƙe kafaɗa da sauri tana kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka. Da sauri ya janye hannunsa, ya kai kan kunnensa ya riƙe da duka hannayensa. Ya ƙanƙantar da idanunsa kafin yace

"A yi min afuwa Sweerie.. Na san na yi laifi, amma a yafe min Uhmm?" Ya faɗa a marairaice. Juyar da kanta ta yi tana ƙoƙarin rufe idanunta ya sake faɗin

"Don Allah fa na ce.." Ya faɗa kamar wani yaron goye. Sake maƙe kafaɗar dai ta yi ba tare da ta juyo ba.

"Shi kenan.. Na ji ko ma me ye ze faru, yanzu dai a lamunce min na taimaka miki zuwa toilet, daga nan kowanne hukunci za a min na amince." Ya yi maganar yana ɗan leƙa fuskarta. Ganin ta kalle shi ne ya sanya shi komawa yana murmushi. Se kawai ta maaze, cike da ƙarfin hali ta soma ƙoƙarin miƙewa. Gaba ɗaya jikinta ya yi tsami kamar wadda ta wuni da ciwon jiki. Dalili kenan da ya sanyata runtse idanunta tana bawa ƙwallar da ta ƙi dena taruwa a idanunta damar zubowa.

"Ohhh.." Ya faɗa yana ɗora hannunsa a kan goshinsa. Se ya miƙe tsaye sosai. Be jira tace ko ya sake cewa komai ba ya saka hannu ya saɓeta gaba ɗaya se toilet ɗin. Duk da yanda take ta zillewa haka ya basar ya kaita. Kai tsaye cikin bathtub ɗin ya sakata ciki, yana jinta tana ta en koke_kokenta. Duk da yanda matsanancin tausayinta ya kama shi hakan be sa ya cireta daga ciki ba. Ya ɗan dinga basarwa dan kar ya fusata ya maidata kan gadon. Ita dai yau Didi ta ga abubuwa, dan kuwa haka tana ji tana gani Bad Man ɗin ya saɓeta tass da sabulu. Tun tana kukan tana zillewa har ta gaji ta haƙura. Wai kuma se da ya gama komai sannan ya kalleta yana riƙe da ita yace

"Na yi laifi a yafe min." I zuwa yanzu ita kam har ta gaji da jin wannan kalmar. Ta daɗe da gano shi, wato ba ya tashi bayar da haƙuri se ya aikata abin da yake so, se ya zo yana marairaicewa. Duk da haka kuma be ƙyaleta ba se da ya samo mata wata riga ya zura mata kafin ya ɗauketa dan sauƙaƙa mata ya direta kan gado. I zuwa lokacin ta haƙura kawai ta zubawa sarautar Allah ido, dan ba ta ga alamar yana da niyyar dena duk abin da ya fara ba. Kawai se komawa ta yi ta kwanta, dan duk da ta ji daɗin jikinta amma har yanzu wani iri take jinta daban. Tashi ya yi ya koma kan gadon, ya saka hannunsa ya jata cikin jikinsa yana kallan idanunta da yau ɗin suka ƙi ko da gajiya ne da tara ƙwalla. Cikin kulawa yace

"Haba mana wifey, kukan ya isa haka. Girma ne fa ki ka yi. Kin ga yanzu kin taddo Afaaf, ni ma kuma na taddo ɗan uwa, yanzu haka kanmu ɗaya." Ya ƙare yana murmushin gefen baki. Ita dai waɗannan zancen nasa sake tsundumata suke cikin kunya da sake tuna abin da ya faru be sani ba. Shi kuma da alama ko a jikinsa. Da ze gane da ya yi shiru ya barta ta ji da abin da take ji. Ba ta gama dawowa daga wannan kunyar ba ta sake jiyo muryarsa yana faɗin

"Na san ni jarumi ne.. Yanzu haka da za a auna ki se an tabbatar mana da na yi ajiya.." Tun kafin ya kai karshen maganar tasa ta soma ɗan buga jikinta tana yi kamar za ta soma kuka, lokaci ɗaya kuma tana cusa kanta cikin ƙirjinsa tana jin wata matsananciyar kunya na kamata. Shi dai wallahi sam ba ya da kunya ko kaɗan. Ya gama abin da yake so ya barta da kunya da wahala, ga shi kuma ya zo se kunnota yake yi da maganganunsa da suke sawa ta ji kamar ƙasa ta tsage ta shige. Murmushi ya yi yana ɗan cije lips ɗinsa.

"Shi kenan na dena.." Ya ƙare yana sakin ƙayataccen murmushin gefen baki lokaci ɗaya yana sake rungumeta cike da matsananciyar ƙaunarta. Ita dai ko motsi ba ta yi ba, ta yi shiru a jikin nasa cike da fatan kar ya motsa. Dan idan tana waje ɗaya ta fi jinta normal, da zarar ta motsa kuma se ta ji kamar ta fashe da kuka saboda yanda take jin jikinta.


.. A karo na biyu ya sake kallanta, a nutse yace

"In zo in taimaka miki?" Girgiza kai ta yi tana runtse idanunta cike da fatan ta ji ta koma daidai, ta dena jin komai. Se dai kamar ɗazun yanzun ma komawa ta yi tana ɗan sauke numfashi. Miƙewa ya yi ya ƙaraso kan gadon, ya ranƙwafo yana ƙura mata idanunsa. Cikin kulawa, kuma muryarsa ƙasa ƙasa yace

"Har yanzu dai?" Se da ta buɗe lumsassun idanunta ta kalle shi, kafin ta jinjina kai a sanyaye tana sauke idanunta. Hannu ya miƙa mata yace

"Kama ki tashi mu ga." Miƙa masa hannun ta yi, ya taimaka mata ta miƙe yana lura da yanayinta. Ya ɗan sauke numfashi kafin ya maidata kan gadon daidai lokacin da yake faɗin

"Kwanta ina zuwa.." Babu musu ta koma ta kwanta ɗin. Dan da ma ta fi jin daɗin kwanciyar. Ya sake zuba mata idanunsa yana jin jikinsa na ƙara yin sanyi.

"Kar fa ya je ya yi wa er mutane illah?" Ya tambayi kansa har lokacin idanunsa na kanta. "Ko kuwa dai yanda ya kula da ita ne ba haka ake ba?" Ya tambayi kansa. Shiru ya yi yana nazari, toh yanzu Mommah ze je ya samu ko kuwa ya ya? "Lallai da na kasance tantirin mara kunya." Ya raya hakan cikin zuciyarsa. A fili kuma se ya sauke ajiyar zuciya, kafin a fili ya furta

"Yess!!." Kallan inda take kwance a kan gadon ya sake yi a karo na barkatai ya ɗan sauke numfashi kafin ya fice daga ɗakin.


.. A ɓangarensu Gwani kuwa tun washegarin ranar da Lulun ta dawo, se ya zamana kamar ana ƙara masa soyayyarta ne. Cikin kwanakin nan sosai ya zage dantse wajen janta a jiki ko dan ta samu ta saki jiki da shi, musamman da ya kasance har lokacin ta kasa sakin jikin da shi gaba ɗaya. Duk da ta san tana ƙaunar ta shi, amma har yanzu ba ta saki jikin ba. Shi kuma so yake shaƙuwa sosai ta shiga tsakaninsu, hakan ne ya sa yake iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya samar da hakan.

Sanye take cikin wata riga da skirt na wani yadi mara nauyi, ɗan ƙaramin mayafi ne wanda ta yane kanta da shi. Ta yi mugun kyau, sosai fatarta ta sake fitowa ta yi kyau, ta kuma sake murjewa. Shi ne ya zaɓar mata kayan da kan shi, duk da ta so musawa saboda yanda kayan suka ɗan kamata ranar da ta fara gwadawa, amma se ta kasa kawai ta ɗauka ta saka ɗin. A karo na barkatai ya ɗaga kai ya kalleta, daidai lokacin da itama ta saci kallansa. Se suka sakarwa juna murmushi, tana shirin janye idanunta ya katseta da faɗin

"A'ah fa.." ya yi maganar yana girgiza kai. Turo ɗan ƙaramin bakinta ta yi tana gyara zama a inda take zaune. Daidai lokacin da aka soma knocking ɗin ƙofar ɗakin. Kallan ƙofar bedroom ɗin suka yi kusan a tare. Lulu na shirin miƙewa Gwani ya katseta da faɗin

"A'ah zauna na je na duba." Babu musu ta koma ta zauna. Ya bita da kallo har lokacin be dena fatan ta koma asalin Lulunta ba. Dan ya san ko ta koma Lulun da, rashin kunyar dai babu ita. Se dai har yanzun ba ta koma ba. Abin da yake ta ƙoƙari kenan ya ga ya samu. Se dai yanzun ne gaba ɗaya ta koma wata shiru shiru kamar ba ita ba. Littafin da yake rubutu cikinsa ya ajje kafin ya miƙe kai tsaye ya fice daga ɗakin. A bakin sashen nasu ya samu Bad Man dake kamar a hagitse, kamar kuma ba a hargitse ba.

"Wai da ma kai ne?" Gwani ya tambaya yana kallansa.

"Ni ne fa.." Ya ƙare yana ɗan ajje numfashi kaɗan.

"Toh ai ma je ciki koh?" Gwani ya faɗa yana kallansa. Girgiza kai ya yi kafin ya amsa da

"A'ah ɗan uwa, sauri nake yi wallahi.." Jinjina kai Gwani ya yi kafin yace

"Ohk.." Se da suka gaisa kafin Bad Man ya ɗan shafa sumar kansa kana cikin basarwa yace

"Bro Afaaf na ciki ne?" Da ɗan mamaki shimfiɗe kan fuskar Gwani yake kallan Bad Man. Ya sake babbasarwa yana gyara tsayuwarsa.

"Ehh.." Gwani ya amsa da hakan.

"Taimaka ka yi mata magana, Afrah na son ganinta." Se kuma Gwani ya yi dariya, dan yanda ɗan uwan nasa ya zama a kan mace shi kansa wani lokacin har mamaki abun ke ba shi. Kamar ya tambaye shi abin da ya faru, se dai kuma tun da be sanar da shi ba may be babu buƙatar ya sani ɗin ne. Dan haka yace

"Tohm." Daga haka ya juya ya koma ciki. Lokacin da ya shiga ta shiga cikin kitchen ne. Dan haka kai tsaye can ɗin ya nufa, daidai lokacin da ya zo shiga ita kuma ta zo fitowa, se ta yi baya dan ta ba shi damar wucewa, ya basar kamar be lura ba ya shiga cikin kitchen ɗin. Ƙarasawa ya yi inda take tsaye, kawai se ta saki baki da ido tana kallansa. Ya haɗe tazarar dake tsakaninsu sosai, ya zamana waje kaɗan ne ya raba su.

"Me ya tsorataki haka ne?" Ya tambaya yana kallanta cikin idanunta. Girgiza kai ta yi da sauri kafin tace

"Ba komai fa.."

"Ban yadda ba." Ya faɗa har lokacin yana kallanta. Kwaɓe fuska ta yi dan ba ta san kuma me za tace ba, ga shi kuma se ƙoƙarin haɗe er tazarar da ta yi ragowa a tsakaninsu yake.

"Ni fa tsoron nan ne ba na son gani." Ya yi maganar yana sake matsar da fuskarsa kusa da tata. Kawai se ta runtse idanunta dan ta saddaƙar, dan ta fahimci abin da yake shirin yi. Har ya kusa kaiwa dab da bakinta se kuma ya matsar da fuskarsa baya yana ɗan murmushi. Dena jin numfashinsa da ta yi a kan fuskarta ne ya sanyata buɗe ido. Ba ta san lokacin da ta sauke ajiyar zuciya ba.

"Matsoraciya." Ya faɗa yana lakutar hancinta. Kafin tace komai ya sake faɗin

"Ban san yanda za a yi ba ranar da Babyn nan ya tashi zuwa duniya.." Ya ƙare yana kai hannunsa kan cikinta. Hannun nasa da ke can ƙarshen cikinta ta bi da kallo. Haka nan kawai ta ji fargaba ta kamata. Se kawai ta ɗora nata hannun a kan nasa tana lumshe idanunta. Ya sake yin murmushi cike da fatan ɗorewar zaman lafiya da kuma ƙaunar juna a tsakaninsa da Lulun.

"Areef na neman ki." Ya faɗa tuna abin da ya shigo da shi. Da mamaki tace

"Ni?"

"Ehh Afrah ke son ganin ki." Murmushi ta yi kafin tace

"Ta zo nan ne?" Girgiza kai ya yi yace

"A'ah.." Se ta soma takawa za ta fice daga kitchen ɗin. Ya marairaice fuska da murya tamkar yaron goye yace

"A nan za ki bar ni?" Ya ƙare yana zabga uban tagumi. Dakatawa ta yi kafin ta juya ta kalle shi. Yanda ya yi ɗin se ya bata dariya, kawai se ta yi murmushin tana dawowa baya.

"Toh mu tafi." Ta faɗa tana kallansa. Se a lokacin ya yi murmushi kafin ya soma takawa. Tare suka fito cikin ɗakin, kafin ita kuma ta yi waje inda Bad Man yake. Gaisawa suka yi kafin yace

"Wani taimako za ki min pls.."

"Tohm." Ta amsa duk da cikin zuciyarta fall mamaki ne.

"Amm.. Ina so ne ki ɗan kular min da Afrah pls, ba ta jin daɗi ne.." Ya yi maganar cikin er basarwa, wai duk dan kar ta ga fuskar tambayarsa ko lafiya? Wani irin bugawa da zuciyarta ta yi shi ne abin da ya sa ta ma manta da wani tambayarsa ko lafiya. Muryarta har ta soma karkarwa tace

"Tohm." Daga haka ba ta jira ya sake cewa komai ba ta bar wajen. Ya sauke ajiyar zuciya, a ransa yana fatan a ce babu wani abu da ya faru.

Ko sallama kasa yi ta yi, kai tsaye cikin ɗakin ta faɗa. Ta yi tunanin za ta ganta cikin palour, se dai babu ita babu alamunta. Hakan ne ya sanyata faɗawa cikin ɗakin da take da tabbacin za ta sameta ciki. Hangota kan gado da ta yi ba ƙaramin sake tayar mata da hankali ya yi ba, cikin lokaci ƙanƙani idanunta suka tara ƙwalla. Se ta ƙarasa da sauri tana faɗin

"Didi.." Ta yi maganar tana saka hannu ta taɓo fuskarta. Buɗe idanunta Didi ta yi da sauri tana kallan Lulu cike da mamakin jin muryarta. Ba dai zuwa ya yi ya sanarwa da Lulun abin da ya faru ba? Ta tambayi kanta tana kallan Lulun.

"Me ke damun ki Didi?" Wannan tambayar da Lulun ta mata, ita ce ta sa ta jin ɗan sauƙi. Se ta ƙaƙalo murmushi kafin tace

"Ciwon jiki." Ta ƙare maganar tana sake riƙo hannun Lulun da ke taimaka mata dan ta miƙe.

"Wayyo.." Didi ta faɗa tana ɗan runtse idanunta.

"Na shiga 3 Didi me ya same ki? Duk ciwon jikin ne?" Lulu ta faɗa tana share hawayen da har sun soma zuba a kan kuncinta. Jinjina kai Didi ta yi, dan ita dai ba ta fata Lulun ta gane abin da ya faru. Haka kawai.. Kawai se ta tattaro duk wani ƙarfinta da ya rage, ta miƙe tsayen. Lulu ta taimaka mata ta zaunar da ita a kan kujera. Kallanta Lulu ta cigaba da yi, har zuwa lokacin da ta ɗan karkace ta kwantar da kanta a kan hannun kujerar.

"Didi ko dai..?" Lulu ta faɗa tana saka hannunta a kan bakinta. Babu shiri Didi ta buɗe idanunta tace

"Me?" Girgiza kai Lulu ta yi tana dariya ƙasa ƙasa, dan se yanzu ta fahimci abin da ke faruwa.

"Ba komai fa." Ta ƙare cikin basarwa, tana kuma riƙe kanta dan kar ta sheƙe da dariya. Lura da hakan da Didi ta yi ne ya sanyata yin kici kicin da fuska tace

"Toh ma me ya kawo ki ɗakin nan?"

"Toh ni fa da ma Yaya Areef ne yace na zo na kula da ke.."

"Haka yace miki?" Didi ta tambaya kamar xa ta yi kuka.

"Eh wai ba ki da lafiya." Lulu ta faɗa tana ƙunshe dariyarta. Kawai shiru Didi ta yi dan ba ta san kuma me za tace ba. Kunya dai kam ya riga ya gama bata.

"Allah zan miki rashin mutunci Lulu." Didi ta faɗa cikin ƙarfin hali, tana kuma galla mata harara.

"Toh ni me na yi?" Ta yi maganar tana tura baki. Shiru kawai Didi ta yi ba ta sake cewa komai ba. Tana kallan Lulu ta shige toilet, bayan wasu mintuna se gata ta fito. Kamar yanda Ummeey ta umarceta da yi lokacin suna gida, haka ta saka Didi ma ta yi. Haka dai Didi tana ji tana gani ta koma ita ce ƙanwar, Lulu kuma babba. Haka dai ta din ga basarwa, tana aro jarumta duk dan kar Lulun ta rainata. Ita kuwa Lulu dariyarta take sha ƙasa ƙasa dan ta riga ta san kawai mazewa take yi. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa se ga shi ta ji jikinta ya saki sosai, ta ji daɗinsa sosai.

"Kin ga Didi idan za ki saki jiki ki yi abubuwanki ki yi.. Ni ba wanda zan faɗawa." Ta faɗa lokacin da take nesa da Didi. Juyawa Didi ta yi ta rarumi pillown da ke bayanta ta jefawa Lulu. Lulu ta kauce tana sheƙewa da dariya. Ta bita da kallo, ba ta san lokacin da murmushi ya ƙwace mata ba. Soyayyar er uwatta na sake ratsata. Babu ƙarya zuwan Lulun ya mugun mata amfani, dan ƙila da tuni har yanzu tana nan a kwance. Abun kuma ya burgeta yanda yau ɗin Lulun ta zama ita ce yayar.

"Allah Ya sauke ki lafiya Habibty." Ta faɗa a kan laɓɓanta tana cigaba da kallan Lulun da kullum sake kyau da murjewa take yi.



... Murmushi ne ya wanzu a kan fuskarsa lokacin da ya ga number da ke yawo a kan wayar tasa. Ya ɗauka yana karawa a kunnensa. Se da ya nemi waje ya zauna kafin yace komai, daga can ɓangaren aka ce

"Affan.."

"Na'am Ummeey.." Ya amsa da hakan.

"Ka na ina ne?" Ta faɗa muryarta a sanyaye, tana kuma bayyana damuwar da take ciki. Haka nan kawai ya ji faɗuwar gaba ta zo masa, jin muryar Ummeeyn tasa. Ya ɗan sauke numfashi yana gyara zamansa, yace

"Ina gida."

"Ka taho gida toh.. Ka ga Abeeynka ne babu lafiya." Be san lokacin da ya miƙe tsaye ba daidai lokacin da bugun zuciyarsa

Please Login or Register in order to submit comment