Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta bar shi ze yi. Da ma kuma ita kanta yau ɗin ba ta wani ji daɗin jikinta ba, dalili kenan da ya sanya ta kwantawa kamar yadda ya umarce ta. Haka har washegari ma, dan dai ta tabbatar masa da ba ta jin komai a jikinta ne kafin ya barta fitar da za su yi zuwa asibiti. Ko da ya gama shirya ta cikin doguwar rigar abaya da mayafinta. Be ƙyale ta ba, se ya saƙala hannunsa cikin nata. Ta juya ta kalle shi da sauri, tace kamar me shirin fashewa da kuka.

"Babe za mu haɗu da su Gwani fa.." Taɓe baki ya yi kafin yace cikin basarwa

"Me na aikata?" Se ta kalli hannun nasa, ya basar kamar be gani ba yana cigaba da tafiya har suka fice daga ɗakinsu. Daidai lokacin da Gwani da Lulu suka fito daga cikin nasu ɗakin, su ma sun yi kyau sosai abinsu.

"Madallah, ba za a wahalar min da mata ba." Bad Man ya faɗa yana ƙarasawa inda suke. Girgiza kai Gwani ya yi yana ɗan murmushi. Kafin ya maaze yace

"Malam me ye haka?" Ya faɗa yana watsa masa idanunsa. Se da ya ɗan yamutsa fuska kafin ya ɗan marairaice ta yace

"Amma dai bro a gabanka jiya ta kusa faɗuwa koh? Kuma ma dai likita tace ta dinga hutawa." Ya ƙare yana ɗan satar kallan Didi da ke ta taɓo shi alamar ya yi shiru. Se ta yi amfani da wannan damar wajen zame hannunta. Ya kalle ta kana ya jinjina kai, irin za ki sani ɗin nan. Ta turo baki tana kautar da kanta.

"Me yake damunki Didi?" Lulu ta faɗa lokacin da ta ƙarasa kusa da Didin, tana jin tashin hankali na zuwar mata.

"Ba komai fa Lulu.." Didi ta ƙare maganar tana kallan Bad Man. Se kuwa aka yi sa'a su yake kalla. Ta girgiza masa kai, ya maƙe kafaɗa yana murmushi gami da kautar da kai. Ta rausayar da kai tana ji a ranta shi kenan a gaban Gwanin ze tona mata asiri.

"Wallahi ba wani nan.. Yaya areef me ke damunta?" Lulu ta faɗa idanunta cike fall da ƙwallar da ta taru lokaci guda. Se da ya saci kallan Didi kafin su haɗa ido ya dawo da dubansa kan Lulu yace

"Amm.." Ya ɗan yi shiru yana shafa kwantacciyar sumar da ke kwance luff a ƙeyarsa.

"Yaronki ke wahalar da ita.." Ya yi maganar ƙasa ƙasa. Daga farko sam Lulu ba ta fahimci abin da yake nufi ba. Se kuma daga baya ta yi shiru tana sake nazarin maganarsa. Idan dai har ta fahimta da kyau, yana nufin kenan Didin na ɗauke da ciki? Ai ba ta san lokacin da ta juya ba, da gudu ta ƙarasa ta rungume Didi da ke tsaye tana ta raba idanu. Hannu Gwani ya kai kamar me shirin tare ta. Dan tsoro ya ji kar ta faɗi. Garin wani farin cikin a tarwatsa wani.

"Wayyo Allah Didina.." Shi ne abin da ta faɗa kawai tana ƙanƙame er uwar tata, ita sam ta ma manta akwai abu a cikinta. Tsananin farin cikin da Didi ta gani a kan fuskar Lulu shi ne ya sanya ta sakin murmushi, har se da ta ji ƙwalla ta tarar mata cikin idanu. Ta rungume er uwar tata, wani farin cikin na sake lulluɓe ta.

"Ina taya ka murna.. Na kusa zama uban 'ya'ya biyu kenan." Gwani ya ƙare maganar yana murmushi idanunsa a kan Bad Man.

"Godiya nake bro.. Ƙwarai kuwa.." Bad Man ya amsa yana jinjina kansa hannunsa cikin na Gwani da ya miƙa masa suka gaisa. Kawai shi ma se ya rungume ɗan uwan nasa yana faɗin

"Ina taya mu farin ciki gaba ɗaya.. Allah Ya dawwamar mana da zaman lafiya me ɗorewa.."

"Ameen Ameen.." Gwani ya faɗa, cikin ransa yana sake yi wa ɗan uwan nasa addu'a.

Yau ma kamar jiya, yini suka yi a asibitin, se dare sannan suka koma masaukinsu.

A kwanakin da suka biyo baya sosai Abeey ya soma samun sauƙi. Musamman da ya kasance kuɗi sosai Daddy ya zube wanda za a kula da Abeeyn sosai. Ta ɓangaren ma'auratan kuwa se ya zamana shaƙuwa ce sosai take sake shiga tsakanin kowannensu. I zuwa lokacin kowacce ta zage dantse wajen kula da mijinta, da kuma ƙoƙarin ganin ta farantawa mijinta. Sun kwashe sati biyu a asibitin kafin suka soma gabatar da ibada har da Abeey da jikinsa ya yi kyau sosai. Shi kansa ya ji daɗin jikinsa, ya kuma tabbatar yanzun da gaske yana samun sauƙi.

Ba su suka baro ƙasar ba se da jikin Abeey ya yi sauƙi sosai. Ya kasance an gama masa komai, an kuma ɗora shi a kan magani. Ta gefe guda kuma sun gama ibadarsu kafin suka baro ƙasar cike da kewa. Wadda ta gina musu tarihi masu wuyar mantawa. Lokacin da suka dawo kai tsaye tamfatsetsen haɗaɗɗen gidan da Daddy ya saka aka gina musu suka nufa. Haka su ma Abeey da Ummeey, na su haɗaɗɗen gidan suka nufa. Mommah da Daddy da kansu suka zo yi musu sannu da zuwa. Ganin jikin Abeey kuma ba ƙaramin faranta musu ya yi ba. Duk da da ma shi Daddy lokaci zuwa lokaci su kan yi waya ya ji jikin Abeeyn. Ta ɓangarensu Didi da Lulu kam shau shau da mai abinsu. Domin kuwa kowaccensu se da ta tarar da akwatinan da za a iya kiransu na lefe jibge a cikin ɗakinta. Akwatina haɗaɗɗu masu ɗauke da danƙara danƙaran kaya na gani na faɗa. Haka zalika hatta furniture sabbi aka zuba musu a sashe daban. Waɗancan ɗin nasu su ma nasu sashen daban. Takanas suka ɗauki jiki zuwa gidan Mommah dan yi musu godiya. Suna zaune a ƙasan carpet ɗin da ke shimfiɗe a tsakiyar ɗakin Daddyn. Murmushi Daddy ya yi kafin yace

"Ashe ma ku ba 'ya'yana ba ne.." Ya yi maganar kamar me tambaya ko kuma faɗa kawai ya yi. Dalilin da ya sa dukkansu suka ɗaga kai suka kalle shi kenan. Se kawai suka girgiza kai kusan a tare.

"Toh idan dai har haka ne mu cigaba da hirarmu.." Ya ƙare yana murmushi.

"Ni ma dai ta wajena haka ɗin ne." Mommah da tun ɗazu ba tace komai ba, yanzu ta faɗi hakan ita ma tana murmushin. Su ma murmushin suka yi dukkansu kowacce na ƙara yabawa da halin kirki irin na Daddy da Mommahn.


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya. Kullum zaman lafiya da ƙaunar junansu ƙaruwa yake yi. Kowa ba shi da burin da ya wuce ya farantawa ɗan uwansa. I zuwa lokacin soyayyarsu suke sha babu kama hannun yaro. Ta gefe guda kuma lokaci ɗaya kowa na taya matarsa rainon ciki, cike da so, ƙauna da kuma tarairaya. Kwanaki na tafiya, satika na tafiya, suka haɗu suka bayar da watanni..


Daga haka se na ce mu haɗe a LAST PAGE 🎉😩😭💃

Ina yi wa kowa barka da sallah. Fatan an yi sallah cikin ƙoshin lafiya. Allah Ya mamaita mana.


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO84_85*
Last page 😩😭💃


____ Fitowarta kenan daga cikin kitchen ɗin Baba Atine ta yi sallama cikin ɗakin, hannunta ɗauke da abincin da kullum se Mommah ta saka ta kawo. Saboda Didin da jikinta ya ƙi ƙwari har yanzun. Aiki kaɗan za ta yi ta dinga haki da jiri kenan. Shi ya sa Mommah tace ta huta ta dena girkin, kullum daga gida ake kai na safe, rana da kuma dare. Didi ta amsa fuskarta ɗauke da murmushi.

"'Yata kar dai ki ce min girki kika yi?" Girgiza kai Didi ta yi tana ɗan lumshe idanunta, dan duk da ba wata daɗewa ta yi a tsaye ba amma jiri take ji. Girgiza kai ta yi tana sake ƙaƙalo murmushi ta wanzar a kan fuskarta kafin tace

"A'ah fa Baba Atine.."

"Toh zauna don Allah.." Ƙarasawa Didi ta yi ta nemi waje ta zauna tana ɗan sake lumshe idanunta. Ajiye abin da ta shigo da su Baba Atine ta yi. Kafin ta koma ta zauna kusa da Didi da ta sake yin wani kyau kamar me. Fuskarta ta yi wani irin luwai-luwai ta yi kyau abinta.

"Ba kya buƙatar komai?" Baba Atine ta tambaya tana kallan Didin. Girgiza kai Didi ta yi kana ta amsa da

"A'ah fa Baba ba na buƙatar komai." Daidai lokacin Bad Man ya sauko daga haɗaɗɗiyar matattakalar da ke cikin ɗakin, hannunsa ɗauke da waya kare a kunnensa, da alama waya yake yi. Miƙewa Baba Atine ta yi yana ƙarasowa suka gaisa cikin sakin fuska kamar koyaushe. Sallama ta yi da shi kafin ta wuce. Ya ƙarasa takowa zuwa cikin ɗakin. Be ankara ba Didi ta miƙe da niyyar kwashe abincin ta haura da su sama. Wani jiri da ya kwasheta ya tilasta mata komawa ta zauna a inda ta tashi.

"Ya salaam!." Ya faɗa yana ƙarasa zama kusa da ita hannunsa a kan nata hannun. Riƙe kanta ta yi idanunta a lumshe.

"Me ya sauko da ke ƙasa Uhmmm? Ba na hana ki sauka idan dai har ba na kusa ba?" Ya tambaya yana kallanta. Buɗe idanunta ta yi ta kalle shi kafin ta buɗe baki tace

"Ka yi haƙuri Babe, na yi laifi." Ɗaya daga cikin abin da ke sakawa ya sake jin Didin kane-kane cikin zuciyarsa shi ne taushin zuciya, da kuma saurin bayar da haƙuri ko da kuwa abu be kai ya kawo ba. Ya yi murmushi yana lumshe idanunsa. Komawa ya yi ya zauna kusa da ita sosai. Be ce komai ba se danna wayarsa da ya yi na tsawon wasu sakanni, kafin ya kafa a kunnensa.

"Mommah ko dai er aiki zan nemar mata?" Ya faɗa bayan sun gaisa da Mommahn. Murmushi Mommah ta yi kafin ta girgiza kai.

"Ba da ni ba Areef. Er aiki kam ba a gidan nan ba.. Idan dai kuna so zan iya ba ku Atine aro na wani lokaci.. Amma ka dena zancen er aikin nan." Shi ma da ma ya faɗa ne kawai be sani ba ko Mommahn ta sauya ra'ayi. Se dai be sani ba ashe har yanzu tana nan a kan bakarta.

"Toh shi kenan, hakan na mun gode sosai Mommah.. Allah Ya ƙara girma da lafiya."

"Ameen Areef." Daga haka ya ajje wayar gefensa. Ya maida dubansa kan Didi da ke kallansa. Ya yi dariya dan idan tana masa wannan kallan dariya take ba shi.

"Ki shirya dawowar Baba Atine sashen nan.."

"Kai Babe.." Hannunsa ya saka ya riƙe laɓɓanta guda biyu kafin yace

"Ba na son jin komai.. Babyn nan namu ba ya son wahala, ga yadda yake wahalar min da ke ko me kika yi. So gwara ki zauna ki huta ba se kin yi komai ba har ki haihu." Se da ta tura baki kafin tace

"Toh idan kuma garin hakan na zama ƙatuwa fa?" Ta ƙare yarintarta na bayyana. Dariya ya yi, kafin ya saka hannunsa ya juyo da fuskarta ta koma kallansa sosai

"Ko a ya ya kike ina son aba ta a haka.. Ni ke nake so." Ya yi maganar sounding seriously. Ta lumshe idanunta tana jin daɗin maganarsa. Yana shirin miƙewa daga zaman da ya yi wanda sam be masa daɗi ba tace

"Ka min wata alfarma." Ta faɗa tana riƙo hannunsa. Dawowa baya ya yi ya kafe ta da idanunsa, ya lumshe idanunsa cikin nata alamar yana ji.

"Ba na son sunan da wasu ke kiranka da shi." Buɗe idanunsa ya yi kafin yace

"Wanne?" Turo baki ta yi tana kallansa. Ya rausayar da kai gefe yana faɗin

"Da gaske fa.." Ya ƙare kamar wani maraya. Se da ta ɗan sake tura bakin kafin tace

"Bad Man!!" Murmushi ya yi kafin ya sauke ajiyar zuciya yana maida fuskarsa ta bar murmushin.

"In Allah Ya yarda daga yau an dena shi.." Ya faɗa cike da tabbatarwa. Dan ya san daga zarar ya nunawa duk masu kiransa da sunan ba ya so za su dena ko dan sanin halinsa.

"Don Allah da gaske?" Ta tambaya tana jin wani irin daɗi. Jinjina kai ya yi yana murmushi. Kawai se ta rungume shi sosai tana faɗin

"Na gode sosai Mijina.." haɗa ta ya yi da ƙaramin cikin nata da yanzun ya fito ya rungume, ya yi shiru abubuwa da dama na bijiro masa. Ya yi watsi da su yace

"Kin fi ƙarfin hakan Matata.."

Aikuwa washegari se ga Baba Atine da kayanta. Ɗaki ɗaya aka ware mata cikin ɗakunan da suke ƙasa. Nan ta sauka, aikuwa ranar Didi yini suka yi suna hira da Baba Atinen, saboda da ma da ƙyar yake fita wai yana tsoron kar ya barta ita ɗaya. Duk da Lulu na kusa, amma gani yake kowaccensu tana buƙatar kulawa ne ba ta kula da wata ba. Yau ɗin da Baba Atinen ta zo se ya samu nutsuwar fita daga gidan.



... A ɗaya ɓangaren kuwa da mamaki Gwani yake kallan cikin ɗakin. Be yi tsammanin ze ga ba ta cikin ɗakin ba kasancewar ya barta kwance kamar me shirin yin bacci. Da sauri ya fice daga ɗakin, kai tsaye kitchen ɗin saman ya nufa. Aikuwa kamar yadda ya tsammata tana ciki, tsaye take, ba ya iya hangen abin da yake yi se bayanta da yake hange. Tana sanye cikin ƙaramar riga mara hannu, se buɗaɗɗen skirt da ya ɗan tsuke daga sama kaɗan, kana ya buɗe sosai ta ƙasa. Kanta sanye cikin wata hula me taushi, wadda ta zame ta kusan rabin kanta a buɗe yake. Kan nata da ke a tsefe, a gyare kuma a kwance tsaff. Da sauri ya ƙarasa yana faɗin

"Ƙalb.." Dakatawa ta yi daga abin da take, ta juyo ta kalle shi. Ya girgiza kai yana faɗin

"Ba dai girki za ki ɗora ba?" Ɓata fuska ta yi tace kamar za ta yi kuka.

"Yunwa nake ji." Bin ta ya yi da kallo yanda take wani kwaɓe fuska kamar wadda ta ga tutu.

"Wancan ɗin ne ba kya ci ina koh?" Ya tambaya yana kallanta. Ta jinjina kai ita ma tana kallan nasa.

"Toh shi kenan.." Ya dakata a nan yana nannaɗe hannun rigarsa. Kawai se ta tsaya tana kallan ikon Allah. Se da ya ida ɗauke hannayen rigar tasa kafin ya kamo hannunta, a nutse ya soma takawa da ita har zuwa kan wani ƙaramar kujera da ke cikin kitchen ɗin. Ya zaunar da ita a hankali kafin yace

"Zauna ki kalli yanda mijinki ze girka miki abinci me daɗi." Buɗe ido ta yi da sauri. Ta ɗan gyara zamanta tana kai hannu ta ɗora a kan cikinta da ɗan ciki ma ya motsa.

"Wai kai?"

"Ƙwarai kuwa.. Bari ki ga.." Ya ba ta amsa irin da gasken nan iyawa ya yi. Dariya ta yi tana binsa da kallo, lokacin da ya ƙarasa inda ta baro. Tace har lokacin tana kallansa.

"Habibi toh fitar kuma fa?" Dan yanzu tare suke fita da Bad Man.

"Bari zan kira shi." Ya faɗa yana ɗaukar wuƙar da ke a ajiye. Se ta sake gyara zama tana kallan yadda za a gabatar da wannan girkin. Cikin ƙanƙanin lokaci ya soma yanka albasar gabza-gabza. Tana daga gefe tana riƙe dariyarta, ya yin da shi kuma ya taƙarƙare aiki yake me kyau.

"Wai Habibi haka ake yanka albasar?" Ta faɗa dan ta kasa yin shiru. Juyawa ya yi yana kallanta, cikin basarwa yace

"Yankan ƙwararru ake gaya miki.." Ba ta san lokacin da dariya ta ƙwace mata ba. Har se da ta saka hannu ta sake dafe cikinta da zuwa lokacin ya fito sosai. Se ya shagala da kallanta, shi ma murmushi na tashi a kan kyakykyawar fuskarsa. Se da ta gama dariyar kafin yace

"Gama dariyar ki zo kina santi." Kafin ya kai ga juyawa ya ga abin da yake yi ya cigaba da yanka albasar. Inda cikin rashin sa'a maimakon ya yanka albasar se ya yanki hannunsa. Da yake idanunta gaba ɗaya na kai ya sanyata gani. Idanunta ta buɗe da sauri, har ba ta san lokacin da ta miƙe ba. Duk da nauyin jikinta hakan be hana ta saurin ƙarasowa inda yake ba, ta kama hannun da ya riƙe yana kalla tace idanunta cike fall da ƙwalla.

"Sannu Habibi.. Sannu.." Ta faɗa tana cigaba da kallan hannun. Hannun ya karɓe yana kalla yanda ta ruɗe gaba ɗaya. Ya ja ta jikinsa ya rungume kafin yace

"Babu komai fa Uhmmm?" Girgiza kai ta yi tana barin ƙwallar ta sauko daga cikin idanunta tace

"Ban yadda ba.. Ni dai ka zo mu je asibiti."
Murmushi ya yi yana sake jin ƙaunar Lulun na ratsa shi. Yanda take magana kaɗai ya isa ya nuna maka yanda take a ruɗe. Ballantana kuma ka kalli yanayinta.

"Me zan yi ki yarda da ban ji ciwo ba.. Ko na ƙarasa girkin?" Ai ba ta san lokacin da ta tashi daga jikinsa ba, ta shiga girgiza kai tana faɗin

"A'ah, ba na jin yunwa.. Na ƙoshi Allah kuwa." Ta faɗa tana riƙo hannayensa dan ma kar yace ze cigaba. Murmushi ya yi kafin yace

"Toh shi kenan.. Amma dai ki yi murmushi." Maƙe kafaɗa ta yi tana ɗan rufe idanunta ta buɗe a lokaci ɗaya. Shi ma ɓata fuska ya yi, kafin a ɗan marairaice yace

"Haba mana Matata Uhmm? Matar Gwani Affan..?" Tilas maganar tasa ta sanya ta dariya. Ya sake rungumeta yana faɗin

"Dats my baby girl.." Sun kai wajen minti 2 a haka kafin ta tashi. Yace yana kallanta

"Me za ki ci yanzu? Kar ki ce min kin ƙoshi, idan ba haka ba zan cigaba da girkina ne."

"Ba na son cin komai yanzu Allah kuwa.."

"Toh se me za ki ci?" Ya tambaya cike da kulawa. Shiru ta yi tana nazarin abin da za ta faɗa. Se ta jiyo muryarsa yana faɗin

"Ko za ki ci abincin gidan Ummeey?" Murmushi ta yi tana jinjina kai. Shi ma murmushin ya yi cikin ransa yana jin daɗin mafitar da ya samu, dan ya san da ba lallai ta ci ba.

Aikuwa gidan Ummeeyn suka nufa kai tsaye bayan ya shiryata da kansa. Sanda suke shirin shiga Abeey da jikinsa ya yi kyau sosai ke shirin fita. Suka dakata suka gaisa.

"Ga shi kun shigo ni kuma zan fita.." In ji Abeey.

"Wallahi kuwa Abeey." Gwani ya faɗa.

"Ko za ka zo mu je ne? Karatu ne zan gabatar, na ɗauka ayyuka sun maka yawa shi ya sa ban sanar da kai ba." Girgiza kai Gwani ya yi kafin yace

"A'ah Abeey, bari na shiga mu gaisa da Ummeeey se na fito."

"Toh shi kenan.."

"A dawo lafiya Abeey." Lulu ta faɗa.

"Allah ya sa ɗiyata.." Ba ta sake cewa komai ba ta bi bayan Gwani suka wuce cikin gidan. Gaisawar kuwa kawai ya yi da Ummeeyn ya faɗa mata fitar da za su yi da Abeey kafin ya yi sallama da abar ƙaunar ta shi kana ya fito suka fice da Abeeyn. Da ma in dai Lulun ta zo gidan, Ummeey ba ta zama haka nan. Dalili kenan da ya sa ta miƙe kai tsaye ta faɗa kitchen dan ɗora mata wani abu me sauƙi da za ta iya ci kafin ta gama girki. Cikin sa'a ma kafin ta fito Lulun ta ɓingire se bacci.


... Har sun soma tafiya dan ficewa daga wajen, Sadik yace

"Bad!" Juyawa ya yi ya kalli Didi da ta wani haɗe rai. Ya yi murmushin gefen baki yana ɗan cizar laɓɓansa. Ya juya daidai lokacin da Sadik ɗin ya ƙaraso inda suke.

"Areef!" Buɗe ido Sadik ya yi kafin yace

"Ka san Allah har manta sunanka nake yi.. Kawai ka bar ni na cigaba da kiranka da hakan." Da dai ya ga ba fahimta ze yi ba kawai se cewa ya yi

"Madam ba ta so." Buɗe ido ya yi yana kai hannu bakinsa yace ƙasa ƙasa

"Masu abu da abinsu.. Toh a mana afuwa mun tuba."

"An yi muku." Areef ya faɗa yana murmushi, kafin ya saci kallan Didi. Murmushi ita ma ta yi, ya sauke ajiyar zuciya. Se da suka ƙara magana kafin suka sake yin wata sallamar Sadik ya koma ciki, ya yin da Areef ya ƙarasa inda ya bar Didi suka wuce.



_BAYAN WASU WATANNI_


... Sanye cikin wasu tausasan kaya na sanyi dukka suke. Waɗanda suka mugun yi musu kyau. Kai idan ba ka san daga inda suka fito ba se ka ce da ma can en asalin ƙasar ne. Saboda yanda suka fito suka yi kyau, suka kuma saje da en ƙasar. Waje ne me kyau, shiru babu hayaniya, se korayen shuke-shuke da suka mugun ƙawata wajen. Sun kai awa ɗaya a wajen, kowanne na tare da matarsa cikin farin ciki da ƙaunar juna. Se lokacin da suka miƙe za su tafi. Hannun kowannensu na saƙale da na matarsa. Ya yin da daga Lulu har Didi cikin kowaccensu ya fito ya yi acan-acan cikin wadatacciyar rigar jikinsu. Idan ba ka sani ba ma se ka ɗauka watannin cikin nasu duka ɗaya ne, dan Didi na da girman ciki ne ya sa girman cikinta ya zo ɗaya da na Lulu da ta shiga watan haihuwa.

"Za ki iya ƙarasawa ko na ƙarasar da ke?" Areef ya faɗa yana kallan fuskar Didi. Girgiza kai ta yi kafin ta amsa da

"A'ah fa Babe zan iya.." Ta yi maganar ƙasa ƙasa tana cigaba da takawa a hankali. Sake riƙota ya yi sosai dan ta ji daɗin tafiyar, cike da takatsantsan suka cigaba da takawa. Daidai sun fito daga wajen Lulu ta dakata daga tafiyar da take da ƙyar. Bayan ta ɗan ajje numfashi tace tana kallan Gwani da shi ma ya dakata.

"Ka ga se harbi na yake yi koh?" Ta faɗa kamar za ta yi kuka.

"Waye?" Ya ƙare yana buɗa idanunsa, dan sam be fahimci abin da take nufi ba.

"Babyn nan mana." Ta ƙare tana nuna cikinta. Bin tirtsetsen cikin nata ya yi da kallo, wanda rigar jikinta ta ɓoye girmansa, kafin ya yi murmushi gane abin da take nufi. Se ya gyara tsayuwa kana yace

"Shi ma ya ƙagu ya ga Abbunsa.." Ya ƙare yana murmushi. Turo baki ta yi kafin yace

"Aou ban da ni koh?"

"A'ah har da ke mana.. Amma ya fi so ya ganni.." Ya faɗa cike da tsokana.

"Ni dai ban yadda ba." Ta faɗa tana ɓata fuska.

"Toh shi kenan, yana son ganinmu duka Uhmmm?" Ya faɗa yana kallanta fuskarsa ɗauke da murmushi. So yake kawai ta amsa da ehh dan su wuce, saboda ba ya son wannan tsayuwar kar ta wahala, abin cikinta ma ya wahala. Se kuwa ta jinjina kai tana murmushi. Ya sauke numfashi yana sake riƙo hannunta suka ƙarasa inda motar take.

"Mommah ce.." Ya ƙare maganar yana kallan Areef da ke kallansa lokacin da wayar ke hannunsa. Buɗe ido Areef ya yi kafin ya ɗan yi murmushi. Daidai lokacin da Gwani ya ɗaga wayar. Daga can ɓangaren Mommah tace bayan sun gaisa

"Affan.."

"Na'am Mommah.."

"Wai yaushe za ku dawo min da 'ya'ya ne? Ina fa sane da Afaaf ta shiga watan haihuwarta.. Me kuke jira ne? Ko so kuke su haihu a inda ba su da kowa?" Harara ya jefawa Areef da ke kallansa, ya yi dariya ƙasa-ƙasa yana ɗauke kai.

"In Sha Allah cikin satin nan za mu taho.."

"Toh ku ƙoƙarta dai.. Allah Ya ƙara lafiya."

"Ameen Mommah." Ya amsa da hakan yana ajje wayar. Ya dubi Areef yace

"Malam ko da me kake tafiya cikin satin nan za mu koma gida.. Haka kawai?"

"Duk abin da ka ce ai haka za a yi Oga." Ya ƙare maganar kamar irin yaron da ke gaban Ogansa. Tilas ya yi dariya dan yanda ya yi maganar ba ƙarya ya ba shi dariya.


A ɗaya ɓangaren kuwa bayan da Mommah ta sauke wayar, Daddy da ke gefenta yace

"Ke da 'ya'yan naki ne?"

"Wallahi kuwa Rankayadaɗe, sun riƙe yara sun ƙi dawowa, haka nan kawai su haihu a can.. Gwara su dawo nan cikin dangi se ya fi." Murmushi Daddy ya yi kana yace

"Gaskiya dai kam.. Toh Allah Ya dawo da su lafiya."

"Ameen." Tana kai ƙarshen maganar ɗaya daga cikin sabbin ma'aikatan da Daddy ya zuba ya ƙaraso inda suke. Cike da girmamawa yace

"Yallaɓai ka ba mu izini mu fitar da wata mata daga cikin layin nan.. Tun ɗazu take nacin se ta shigo, dalilin da ya sa muka ƙi barinta ta shigo kuma kamar akwai alamun rashin hankali a tattare da ita. Se dai mun yi ƙoƙarin korarta, lura da hakan ya sa muka ƙyale ta. Se dai har yanzu tana can wai ita a lallai dole kai take son gani." Cike da mamaki Daddy yace

"Ni kuma?" Ya faɗa mamakin na bayyana a kan fuskarsa.

"Ka ce me rangwamin hankali ce, ya aka yi kuka san abin da take nufi?" Daddy ya tambaya yana kallansa.

"Yallaɓai ba na ce ba.. Amma tabbas haka take ta faɗa,

Please Login or Register in order to submit comment