Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ɗora da faɗin

"Shi kenan toh.. In Sha Allah."

"Yawwah.. toh Allah ya ba da lafiya." Ummeey ta faɗa tana murmushi.


.. Babu daɗewa Ammi da Little suka iso asibitin. Kai tsaye ɗakin da aka kwantar da Lulun suka nufa. Da sallama Ammin ta shiga cikin ɗakin kanta a kan gadon da Lulun ke kwance. Ummeey dake zaune kan kujera ta amsa tana kallan me sallamar. Ganin Little da ta yi ya sanyata sakin murmushi tana faɗin

"Oyoyo Areef.." Se kuwa ya tafi wajenta shi ma yana murmushi daidai lokacin da ta miƙe tana faɗin

"Sannun ku da zuwa.." ta yi maganar tana kallan Ammi. Da murmushi kan fuskar Ammi ta amsa da

"Yawwah.." tana neman waje ta zauna. Cikin mutunta juna suka gaisa kamar sun saba, dan Ummeey na ganin Ammin ta gane wace ce musamman kuma da ta ganta tare da Little. Yayin da Ammi take tunanin wannan ɗin sirikar Lulu ce. Kallan gadon da Lulun ke kai ta yi, tana iya gano fuskarta lokacin da take bacci. Yanda ta ga ta rame shi ne ya sake tabbatar mata da har lokacin ba ta kwantar da hankalinta a kan auren ba. Ta girgiza kai cike da tausayin ɗiyar tata. Daidai lokacin Gwani ya yi sallama cikin ɗakin, dukansu suka amsa masa. Little dake zaune kan gadon kusa da Lulu ya tashi da sauri ya ƙarasa wajensa. Riƙe hannunsa ya yi da murmushi kan fuskarsa yace

"Areef.."

"Na'am ina kwana?" Ya faɗa yana sake riƙe hannun Gwani. Amsa gaisuwar tasa ya yi lokaci ɗaya yana ƙarasawa cikin ɗakin. Cikin girmamawa ya gaishe da Ammi dake zaune kan kujera. Ta kalle shi dan dama ba ta taɓa ganinsa ba. Haka kawai ta ji a jikinta lallai wannan ɗin shi ne mijin Lulu. Ita dai ba ta san dalili ba lokaci ɗaya ta ji ya kwanta mata. Se ta amsa gaisuwar tasa tana ɗorawa da

"Ya me jikin?"

"Alhamdulillah.." Gwani ya amsa da hakan.

"Allah ya ƙara sauƙi.."

"Ameen" ya yi maganar yana miƙewa dan fita daga ɗakin.



... Tsaki ta ja a fili ta furta

"Wai ba za ki ɗaga kiran ba ne?" Ta yi maganar kamar akwai wani a kusa da ita wanda ze amsa mata maganar da ta yi. Se dai kafin wayar ta tsinke aka ɗaga. Daga can ɓangaren Aunt Makiyy tace

"Yi haƙuri 'yar uwata.. Allah ya huci zuciyarki." Ta yi maganar tana er dariya. Tsaki Mom ta ja a fusace tace

"Wallahi na gama fusata kuwa, dan rashin kirki in yi ta kiran ki ki ƙi ɗagawa.."

"Ai dai na bayar da haƙuri.." Aunt Makiyy ta faɗa. Se a lokacin sannan Mom tace

"Toh na ji.. Yanzu dai ya ake ciki? Na ji ki shiru har yanzu, ko kina nufin har yanzu ba a zo lokacin da kike so a zo ba?"

"Kai Yaya don Allah ki yi haƙuri mana, ki bari mu bi komai a sannu.."

"Kin ga Makiyya wallahi na gaji.. Na gaji da bin komai a sannu, ina kike so a zo ne? Ni fa na kasa gane miki." Mom ta faɗa da iya gaskiyarta. Ajiyar zuciya Aunty Makiyy ta sauke sannan tace

"Shi kenan next week ai dai zan dawo koh? Ina dawowa gidan zan fara zuwa se mu yi maganar.." Ta ɗan dakata a nan. Kamar jira Mom take yi se kuwa ta soma ƙoƙarin magana. Katseta Aunt Makiyy ta yi da faɗin

"Don Allah kar ki ce a'ah.. Ki ce toh kawai." Tsaki Mom ta ja sannan tace

"Na ji." Daga haka ta katse wayar, tana jin haushin kanta da ya shigar da Makiyyan cikin wannan lamarin. Da ta san za ta kawo mata wasa tun farko da ba ta sakota ba. A karo na biyu ta sake jan wani tsakin tana miƙewa dan shigewa bedroom ɗinta. Sallamar da ta ji daga bakin ƙofa ita ce ta sanyata dakatawa. Ta kalli me sallamar cike da mamaki. A nutse a kuma ɗarare Didi dake sanye cikin wata doguwar rigar atamfa da mayafi wadatacce, ta yi matuƙar kyau, ta ƙaraso cikin ɗakin ta zube a ƙasa cikin sanyin murya tace

"Barka da wannan lokaci.."

"Tashi tashi tashi.." Mom ta faɗa tana ɗaga hannunta alamar ta miƙe, ranta dake a ɓace ya sanya fuskar nan tata ta sake haɗewa waje ɗaya. Cikin lokaci ƙanƙani Didi ta ji jikinta ya ɗauki rawa, dama Allah ma ya gani a tsorace take tun kafin ta shigo ɗakin, yanzu kuma da ta shigo se ta ida tsoracewa, se dai duk da haka hakan be hanata miƙewa ɗin ba kamar yanda Mom ɗin ta buƙata. Kanta na a ƙasa ne tana tsoron jin abin da ze fito daga bakin Mom ɗin. Kamar kuwa Mom ɗin ta san me take jira se cewa ta yi

"Me ya kawo ki ɗakin nan? Waye ya aiko ki? Gulma da kinibibi ya kawo ki? Toh wuce ki tafi tun kafin raina ya kammala ɓaci na ci miki mutuncin da ba a taɓa yi miki ba. Fice min daga nan.." ta yi maganar cikin ɗaga murya tana nuna mata hanya. Da ƙyar Didi ta ɗaga ƙafafunta ta soma takawa dan ficewa daga ɗakin cike da sarewa da lamarin cikin gidan nan. Miji ba kirki, haka uwar mijin ma ba kirki. Ba ta san lokacin da ta ji wasu hawaye masu ɗumi sun zubo mata a kan kuncinta ba. Se ta kasa tsayar dasu kawai ta barsu suna zubar tana jiyo lokacin da Mom ke faɗin

"Shashashar banza er gidan talakawa.." Ta runtse idanunta tana jin yanda jikinta ke sanyi, zuciyarta na sake ƙuntata da kalaman Mom ɗin.

"Daughter.." Ta ji an faɗa dab da za ta wuce sashensu. Se ta ɗaga jajayen idanunta daidai lokacin da take share hawayen fuskarta ta kalli Mommah. Da sauri ta ƙarasa tana faɗin

"Subhanallahi.. kuka kuma?" Mommah ta faɗa tana riƙota. Se ta ji kamar Amminta ce, hakan ne ya sanyata faɗawa jikinta ta fashe da kuka. Ko Mommahn ba ta tambaya ba ta riga ta fahimci abin da ya faru, hakan ne ya sanyata rungume Didin cikin rarrashi tace

"Ki yi haƙuri ki yi shiru kin ji? Komai ze zo ƙarshe In Sha Allah.." Ta yi maganar tana ɗan shafa bayan Didin alamar rarrashi. Kasa shirun ta yi, har se da ta yi me isarta sannan ta koma sauke ajiyar zuciya. Se a lokacin ta tashi daga jikin Mommahn tana kan sheshsheƙa saboda kukan da ta yi. Kafin Mommahn tace komai wayarta dake hannunta ta soma ruri. Se ta kalli me kiran sannan ta ɗaga. A nutse ta yi sallama, Daddy ya amsa sallamar tata yana ɗorawa da

"Kin sanarwa da yarinyar ne?"

"A'ah yanzu dai nake shirin faɗa mata." Gyara zamansa Daddy ya yi a inda yake zaune yace

"Areef baya cikin gidan nan sun fita da Kaseem.. saboda haka ki sanar da ita ta shirya driver ze kaita idan ya so in ya dawo se ya je ya ɗaukota."

"Toh shi kenan Rankayadaɗe.." ta ƙare da murmushi a kan fuskarta. Daga haka ta ajje wayar ta maida dubanta kan Didi tace

"Maza ki ke ki shirya yanzu za a zo s ɗauke ki ki ke ki duba 'yar uwakki.." Da sauri ta kalli Mommah jin abin da tace. Gane mamakin da ya bayyana a kan fuskarta ya sanya Mommah yin murmushi dan kawar mata da wani tunanin tace

"Ko ba kya son zuwa?" Ba ta san lokacin da wani murmushi ya ƙwace mata ba, duk da har lokacin da ragowar kukan da be tafi ba. Hakan kuma da ta yi ba ƙaramin kyau ta yi ba. Se ta kai hannunta kan bakinta cikin matuƙar farin ciki tace

"Mommah da gaske?"

"Ƙwarai kuwa.." Mommah ta faɗa tana murmushi. Ba ta san lokacin da ta rungume Mommahn ba cike da maɗaukakin farin ciki muryarta na er rawa ta furta

"Na gode sosai Mommah.." ta yi maganar tsantsar farin cikinta na bayyana har cikin muryarta. Murmushi Mommah ta yi tana jin daɗin yanda ta saka Didin cikin farin ciki.

.. Da sauri da sauri ta shiga shiryawa tana ji kamar ta yi tsintsuwa ta ganta a wajen er uwar tata. Dan tunda Mommahn ta faɗa mata maganar zuwan nata wajen Lulu ta manta da damuwar da Mom ta sanya mata. Cikin wata doguwar rigar abaya ta shirya da wadataccen mayafinta. Ko tsayawa ta shafa wani abun kasawa ta yi se fitowa da ta yi inda Mommah ke jiranta da ta yi. Toh da yake ɗazun da ta fito daga wanka se da ta gyara fuskarta ya sanya har yanzun fuskar tata a gyare take tsaff kamar wadda ta zauna ta shafe awanni tana ƙyalƙyaleta. Nan kuwa banda kwalli, powder da lip gloss babu abin da ta shafa. Amma haka ta fito ta yi wani mugun kyau kamar ka saceta ka gudu.

Har wajen motar da za ta kaita Mommah ta rakata. Se da ta shiga mota sannan Mommah ta ɗora hannunta a kan glass ɗin ɓangaren da take

"A gaida min da ita.." Murmushi Didi ta yi tace

"Tohm.." Cikin ranta tana jin wata irin soyayyar Mommahn, mata me kirki da sanin ya kamata. Se a lokacin sannan Mommah ta soma takawa dan barin wajen, sannan drivern ya ja motar suka bar wajen. Tunda suka fara tafiya bakinta ya ƙi rufuwa, ta kasa dena murmushi, ta kasa dena zumuɗi. Duk da a mota suke amma ji take kamar ba ya sauri, kamar ta fita daga cikin motar ta yi gudu ta isa wajen er uwarta. A haka dai har suka ƙaraso asibitin. Da mamaki take kallan asibitin, a ranta tana tunanin waye ba shi da lafiya? Tuna babu wanda ze iya ba ta amsar ya sanyata yin shiru tana cigaba da bin asibitin da kallo. A daidai lokacin da Drivern ya yi parking Gwani ya ƙaraso inda suke. Da sauri ta saka hannunta ta buɗe murfin motar tana kallan Drivern dan jiran ƙarin bayani. Daidai lokacin da ta hango Gwani kenan, se ta yi shiru kawai har ya ƙaraso inda take. Se a lokacin ta iya buɗe baki tace

"Barka da wannan lokacin Ya mu'allim.."

"Barka dai.." Gwani ya amsa da hakan.

"Lulu ce ba ta da lafiya?" Ta yi tambayar fuskarta babu yabo babu fallasa dan ta ƙagu ta ji abin da ya kawota asibitin.

"Ehh zazzaɓi ne kawai.. Babu wani damuwa.. Mu je.." ya yi maganar yana soma takawa. Da sauri ta bi bayansa cike da zumuɗin son ganin er uwarta. Se dai duk wannan zumuɗin da take tunda ta gansu a asibiti ya ragu, duk se ta ji jikinta ya yi sanyi.

Lulu na zaune a kan gadon da abinci a gefenta se ɓata rai take, tunda ta ji zuwan Ammi asibitin tana bacci yanzu kuma ta fita wai za ta dawo a cewarsu. Ita dai ta musu shiru dan kowa ma haushinsa take ji, har shi kansa Little dake kusa da ita.

"Afaaf ki damu ki ci ko yaya ne kin ji? Ki yi haƙuri Ammin naki ai za ta dawo.. Kiranta aka yi a waya shi ya sa ta fita." Ummeey ta sake maimaita mata hakan. Se kawai ta kuma riƙe plate ɗin tana cigaba da tura baki ba tare da ta kalli Ummeeyn ba. Da sallama Gwani dake gaba ya shigo cikin ɗakin Didi na biye a bayansa idanunta a kan gadon marasa lafiyar dan ganin wanda ba shi da lafiyar da zuciyarta ke ta azalzalarta. Cikin sakannin da basu wuce 3 ba idanunta suka sauka a kan Lulu da kuma Little dake kusa da ita, ba ta san lokacin da ta tafi a guje ba tana faɗin

"Lulu.." Ɗago idanunta da Lulu za ta yi se suka sauka a kan fuskar Didin. Mantawa ma ta yi da ba ta da lafiya, ba ta san inda abincin ya yi bq ita dai ta san ta miƙe a kan ƙafafunta ta riga Didin zuwa inda gadon yake. Rungume junansu suka yi a tsakiyar ɗakin kusan lokaci guda suka fashe da kuka. Little dake gefensu shi ma kukan ya soma ganin da ya yi en uwansa na kuka. Da sauri suka yi ƙasa suna saka shi a tsakiya suka rungume junansu cikin matuƙar kewa da ƙaunar junansu. Sun kai wajen minti 1 a haka kafin suka saki junansu suka koma kan gadon. Se a lokacin sannan Didi ta iya gaishe da Ummeey dake kallansu cike da burgewa, musamman da ta ga kamannin nasu sakk da sakk ne kamar an tsaga kara. Ta amsa mata cike da fara'a tana tambayarta lafiyarta.

"Alhamdulillah.." Didi ta amsa da hakan.

"Toh madallah.. bari na ɗan fita." Ummeey ta yi maganar lokacin da ta fara takawa dan ficewa daga ɗakin, sanin da ta yi za su buƙaci yin hira a tsakaninsu. Aikuwa hakan take dan kuwa tana fita suka shiga hirar yaushe gamo.


.. Cikin rashin fahimta yace

"Ban gane ba Dad?"

"Ina nufin ka ɗauki mota ka je ka ɗauko matarka.."

"Dad.." ya sake faɗa cike da mamaki.

"I mean what i said.." Daddy ya katse shi da faɗin hakan. Cigaba ya yi da kallan Daddyn kamar ba ze ce komai ba se kuma yace

"Sorry Dad.. but honestly i.." Ɗaga masa hannu Daddy ya yi ransa a ɓace da wannan hali na Areef ɗin, taurin kansa na ba shi ciwon kai.

"Umarni nake ba ka.. Idan kuma ba za ka yi ba ne let me know.." Iska ya fesar daga bakinsa yana miƙewa a kan ƙafafunsa, ya ɗan tsaya na tsawon sakanni sannan ya fice daga ɗakin a fusace. Binsa Daddy ya yi da kallo yana komawa ya zauna shi ma hannunsa a kansa yana girgiza kai. Ya san Areef ɗin na da taurin kai, se dai komai taurin kansa ko da ya nuna fushi a kan abin da Daddyn ya saka shi to fa ze yi ɗin. Janyo wayarsa ya yi ya shiga message ya turawa Bad Man ɗin addrees kamar yanda ya buƙaci a tura masa.


.. Ko komawa ɗaki be yi ba ya wuce inda motarsa take. Ya hau ya figeta da wani irin gudu kamar ze tashi sama. Ransa a mugun ɓace yake driving ɗin. Idan ba dan Daddy Daddy ba ne da babu wanda ya isaya dinga saka shi abin da be yi niyya ba, ballantana kuma a kai ga zuwa ɗauko yarinyar nan daga wani waje kamar wani Drivernta. A harabar asibitin ya yi parking motarsa har lokacin fuskarsa babu yabo babu fallasa. Ya shafe wajen minti 5 zaune a cikin motar ba tare da ya yi yunƙurin aikata komai ba. Se dai kuma fahimtar da ya yi ko da ze shekara ne a wajen idan dai har be je ba ba za ta san ya zo ba ballantana ta zo su tafi. Ya ja tsaki yana jin wani irin haushi na cika shi. Me ya sa Daddyn ze masa haka? Ganin dai yana cigaba da ɓatawa kansa lokaci ne ya sanya shi fitowa daga cikin motar, cikin haɗaɗɗen takun nan nasa ya soma takawa zuwa ciki angry face ɗinsan nan a haɗe musamman da ransa ke a ɓace.

.. Ganin Didi da ta yi gaba ɗaya ya sanyata kasa yin musu a kan duk abin da ta sakata yi. Abincin haka ta zauna ta ci da taimakon Didi, haka maganin ma ta sha dukka da taimakon Didin. Sosai suke hirar yaushe gamo duk da jefi jefi suke yinta. Se dai sun kasa yin shiru, haka suka dinga biye wa Little dake ya surutunsa kamar yanda suka saba. Se suke jin yau ɗin ta daban, suke jinsu kamar a gidansu. Abubuwa da dama yau ɗin ta tuna musu, dan haka se ta kasance rana ta musamman a wajensu. Ummeey da Gwani tare suka shigo ɗakin a yanzu haka. Cike da fatan da suke yi kuwa se suka ga Lulun zaune tana kallan Little har da su dariya kamar ba ita ce mara lafiyar ba. Har ran Ummeey hakan ya yi mata daɗi sosai. Gwani ya ɗan yi murmushi yana sauke ajiyar zuciya, ko babu komai yanzu kam ze iya fita ya je ya samu Abbati su yi magana.
Kamar an ce ta juya se kuwa ta hange shi tsaye a bakin ɗakin yana kallan ciki. Ɗan rufe idanunta ta yi ta buɗe su a kan shi dan sake tabbatarwa kanta fuskar da take gani, ta ɗan runtse idanunta na tsawon sakanni sannan ta buɗe still dai a kansa. Ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske lokacin da ta ida shaida fuskar, cikin sauri kuma ta ɗaga hannunta ta shiga nuna shi se dai kuma ta gaza furta komai. Didi, Ummeey har ma da Gwani gaba ɗaya bin inda take kalla suka yi da kallo cikin sauri. Bad Man na tsaye hannayensa duka biyun cikin aljihunsa. Didi dake kan gado ta yi saurin saukowa daga kan gadon cike da mamakin ganinsa cikin asibitin. Yayin da Gwani ya sake maida dubansa kan Lulu da har lokacin ba ta dena nuna Bad Man ɗin ba, kuma ba tace komai ba. Tsantsar mamakin da na gani a kan fuskar Ummeey shi ne ya sanya ni kallan fuskar tata daidai lokacin da ta miƙe tsaye tana kallan Bad Man.
Daidai lokacin da shi kuma ya soma takowa zuwa cikin ɗakin Lulu ta yi ƙarfin halin kallan Gwani tace

"Shi ne..!!" Sanda wasu kyawawan hawaye suka zubo a kan kuncinta. Maida dubansa kan Bad Man Gwani ya yi bayan ya ji abin da Lulu ta faɗa, daidai lokacin da shi ma Bad Man ɗin ya saukar da idanunsa a kan Gwani. Kamar wanda aka dakatar se shi ma ya dakata yana kallan Gwanin. Kamar wasu zakaru haka suka shiga kallan kallo kowanne da abin da ke cikin ransa..




Toh Alhamdulillah! Daga haka zance se Allah ya kai mu bayan Sallah. Allah ya sa mu shiga watan Ramadan a sa'a, ya sa mu yi ibada karɓaɓɓiya, ya sa muna daga cikin bayinsa 'yantattu. Ameen ya rabbi.



MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO43*


___ Cikin en sakannin da basu wuce 5 ba Bad Man ya ɗauke idanunsa daga kan Gwani ya maida su zuwa cikin ɗakin, daidai lokacin da Lulu ta sake kallan Gwani da idanunta da lokaci ɗaya suka ciko da ƙwalla. Haɗa idanun da suka yi ne ya sanya ta sake faɗin

"Shi ne.."

Rashin fahimtar abin da take nufi ya sanya shi soma takawa zuwa cikin ɗakin har lokacin be ɗauke idanunsa daga kanta ba, kamar yanda ita ma ba ta ɗauke nata idanun daga kansa ba. A nutse ya ɗan ranƙwafa saitinta ba tare da yace komai ba ya ɗan karkatar da kansa yana sanya idanunsa cikin nata.

"Na cikin hoton nan.." shi ne abin da ta furta lokacin da ta zame ƙwayar idanunta daga cikin nasa. Tana ida faɗa ya miƙe a kan ƙafafunsa ya juya yana kallan Bad Man da ya maida wayarsa cikin aljihu sannan ya soma cigaba da takawa zuwa cikin ɗakin. Sake juyawa Gwani ya yi ya kalleta, fahimtar abin da yake nufi ya sanya ta jinjina kai cike da tabbatarwa. Haka nan kawai take jin wani irin sanyi na ratsata, se dai kuma ta kasa fahimtar dalilinsa na zuwa cikin ɗakin da take kwance. Didi da ta fahimci lallai tabbas Bad Man ne, ta kuma san babu abin da ze kawo shi nan ɗin idan ba ɗaukarta ya zo yi ba kamar yanda Mommah ta faɗa mata. Hakan ne ya sanya ta miƙewa da sauri cikin zuciyarta tana jin babu daɗi kwata kwata, yayin da take Allah Allah su fita daga cikin ɗakin kafin ya nuna musu halinsa na rashin kirki. A ɗan ɗarare ta kalli Ummeey da zuwa lokacin ta koma inda ta tashi ta zauna a sanyaye. Kamar yanda ta ji sunan a bakin Little tace

"Ummeey bari mu tafi.." ta faɗa tana wani yaƙe, haka nan kawai take jin bugun zuciya. Da mamaki Ummeey ta kalleta bayan ta kalli Bad tace

"Mijinki ne?" Satar kallan shi ta yi lokacin da ya watsa mata idanunsa dan ya tabbatar da ta gan shi kafin ya fita. Se ta ɗauke kanta tana ƙaƙalo wani murmushi lokaci ɗaya tana jinjina kai a sanyaye. Kallan Bad Man Ummeey ta yi daidai lokacin da yace

"Ina yini..?" Ya faɗa kamar ba shi ba..

"Ikon Allah.." Ummeey ta faɗa fuskarta na nuna zallar mamaki. Ba ta iya amsawa ba se da ta juya ta kalli Didi, Lulu har ma da Gwani sannan ta dawo da dubanta kan Bad Man tace

"Lafiya ƙalau.." Shi be ma ji ta ba dan yana gama yin gaisuwar ya fice daga ɗakin saboda ya riga ya tabbatar wadda ya zo dominta ɗin ta gan shi. Se a lokacin sannan Gwani ya ƙaraso yana kallan Ummeey yace

"Ummeey bari na ɗan fita.." Da "toh" ta amsa masa, shi kuma ya fice daga ɗakin. Dama tunanin yanda ze yi maganar a gaban Ummeey yake yi, ba ya so ko kaɗan ta ji maganar. Yanzu kuwa da Bad ɗin ya fita se ya ji har cikin ransa hakan ya masa. A gaggauce Didi ta yi wa Lulu sallama, duk da tarin tambayoyin da suke yawo a ƙwaƙwalwar Lulun amma yanda Didin ke sauri ya sanya ta adana su. Har cikin ranta ba ta ji daɗin tafiyar tata ba, se dai sanar da ita da Didin ta yi za su din ga waya ya sanya ta jin sanyi a ranta. Hankalinta gaba ɗaya ya rabu gida da yawa, tunaninta gaba ɗaya ya cukurkuɗe. Kawai se ta kwantar da kanta ta ɗan lumshe idanunta cike da tunani barkatai.


... Hango shi da ta yi yana dab da ƙarasawa inda motarsa take ya sanya ta ɗaga ƙafa, se dai duk ƙwaƙwar mutum ba ze iya fahimtar hakan ba. A daidai tana dab da ƙarasawa se ta hangi Gwani ya riga ta ƙarasawa inda yake. Da matuƙar mamaki ta kalle shi daidai lokacin da ya ƙarasa inda Bad Man ɗin yake. Se kawai ta dakata a inda take tana cigaba da kallansu.

A nutse ya ɗaga kai ya kalli me ƙarfin halin da yake ƙoƙarin riƙe ƙofar da ze buɗe dan shiga cikin motarsa.

"Assalamu Alaika.." Gwani ya faɗa fuskarsa babu yabo babu fallasa yana kallan Bad Man irin kallan nan na ido cikin ido. Dakatawa Bad Man ya yi shi ma yana kallan Gwani cike da mamakin waye shi? Me ya kawo shi wajensa?. Irin kallan da yake masa ya fi kama da na wanda ya kama wani me laifi ko kuma wanda ya kama wani da ya aikata aikin saɓo. Samsam be ga ya masa kama da me neman taimako ba, dan kuwa daga yanayin halittarsa har kayan dake jikinsa ba su yi nuni da wanda ke cikin wahala ba. Se dai shigar tasa da ta fito da ainahin kamalarsa, da kuma yanda kallo ɗaya mutum ze masa ya fahimci Malamin Addini ne. Dab da dab suke, kowanne na ma ɗan uwansa kallan tuhuma.

"Who are you?" Bad Man ya faɗi hakan lokacin da ya ƙanƙantar da madaidaitan kyawawan idanunsa. Se a lokacin Gwani ya buɗe baki kamar ze ce wani abu se kuma ya fasa. Ya sanya hannunsa cikin aljihu ya fito da wayarsa. Ya yi danne danne na en wasu sakanni sannan ya miƙawa Bad Man yana kallansa. Yanayin shigar Bad Man ɗin kaɗai ta isa ta nuna maka ko dai shi ɗin ya kasance ɗan gidan wani shegen ne ko kuma shi kansa wani shege ne. Se dai duk da haka, hakan be sanya gwuiwar Gwani ta yi sanyi ba, be kuma sanya ya sassauta ko ya ƙasƙantar da kansa ba. Tunda har Lulun ta nuna masa shi a matsayin na jikin hoton ya ji ko mene ne ze faru se ya tabbatar ya ji gaskiyar lamarin. Ze kuma so ya samu Lulun matsayin me gaskiya. Cikin rashin fahimta Bad Man ya bi wayar da wani banzan kallo sannan ya maida kansa kan Gwani ya karkatar da kansa alamar "Mene ne?" Sake miƙa masa Gwani ya yi ba tare da yace komai ba. Yau ɗaya ya ji yana son sanin waye wannan ɗin, me kuma yake son nuna masa a waya? Shi ɗin da abubuwa masu muhimmanci ma ba tsayawa yake yi ya bi ta kansu ba, se ga shi ya miƙa hannunsa ya karɓi wayar hannun Gwanin. Kusan sakanni 10 ya ɗauka yana kallan hoton kafin ya ɗaga kai ya kalli Gwani.

"Me ye ma'anar wannan ɗin?" Ya tambaya cikin er basarwa. Gyara tsayuwa Gwani ya yi yace

"Me kake nufi da tambayar? Dalilin da ya sa ka saka aka ɗaukar maka hoton nake so na ji kafin na kai ga ɗaukar mataki.." Gwani ya faɗa kamar ba da Areef ɗan gidan Alhaji Matawalle yake tare

Please Login or Register in order to submit comment