Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin Daddy ji ya yi tamkar ya fi kowanne namiji dace, ya kuma fi kowanne mutum samun abun alkhairi. A lokaci ɗaya Allah na neman azurta shi da haihuwa biyu. Haka dai ya yi farin cikinsa shi ɗaya, farin cikin da ya kasa ɓoyuwa har a kan fuskar shi.

Lokacin da su Mommah suka dawo cikin gidan, ya yi daidai da lokacin da Mom ke fitowa daga cikin mota ita da Aunt Makiyy da suka dawo daga unguwa. Tuni Maimuna ta iso wajen ta soma yi musu sannu da zuwa. Lura da waɗanda ke kusa da su ne ya sanya Aunt Makiyy saka hannunta ta riƙo hannun Mom cikin er ɗaga murya yanda ta san za su ji ta tace

"Ki yi a hankali Yaya.. kar ki illata uban masu gida." Wani murmushi Mom ta saki jin abin da Aunt Makiyy ɗin ta faɗa, tace tana riƙo ƙugu, gami da tunkuɗo ciki gaba.

"Uhmm ai kam dai.." Ta yi maganar tana satar kallansu Mommah. Idan motar da suka sauka daga ciki ta ɗaga kai ta kalli su Mom, toh su Mommah ma sun kalle su. Baƙin ciki, takaici duk suka haɗu suka dirarwa Mom, ta ji kamar ta je ta kama Mommahn da er uwar tata ta yi ta jibga ko za ta ji sauƙin abin da take ji a ranta.
Se a lokacin ta fahimci wannan izzar Sa'adahn ba ara ta yi ta yafa ba. Da alama a jininsu take. Dan kuwa hatta Yaya Amina ma wani mugun kwarjini ta mata. Ga kuma komai nasu kamar iri ɗaya ne da na Sa'adahn. Wani abun baƙin ciki ma shi ne yanda suka nuna kamar ba su san da wanzuwarsu a wajen ba. Aikuwa ta ƙara shaƙa, ta ƙulu ta ƙulu.

"Ki kwantar da hankalinki Yaya.. Kwana nawa ne ya rage ki koma juya gidan a hannunki.." Aunt Makiyy ta faɗa dan kwantarwa da Mom ɗin hankali.

"Wallahi Hajiya kar ki damu. Da ma fa da gani wannan ƙatuwar matar ke zuga Sa'adahn. Ba dan haka ba ni kaina yanda na yi ƙoƙarin shiga jikinta ko wacce irin zuciya ce da ita ai ya ci a ce ta saki jiki da ni." Maimuna da ke gefe ta faɗa.

"Yoh ba tana tare da munafuka ba.. shegiya." In ji Aunt Makiyy tana bin bayansu da harara.

"Ni dai don Allah ku mu wuce kafin raina ya ida ɓaci." Mom ta faɗa tana yin gaba a fusace. Dan duk da maganar da suka gwaɓawa Mommahn da ta tabbatar ta ji zafinta, (amma fa a ganinta) ƙin tankawar da ta yi ya fi komai yi mata zafi.



Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, har aka ɗauki watanni Mom ba ta san da zaman cikin Mommah ba. Ita kam Mommah a nutse cikin kwanciyar hankali take rainon cikinta babu hayaniya. Ba ta nemi wata er aiki ba, ita ta cigaba da ayyukanta, se wani lokacin Yaya Amina kan zuwa ta tayata aiki, dan a lokacin ba ta da manyan 'ya'ya. Gefe guda dai kam Mom na nan tana cigaba da yaɓawa Mommah magana duk a kan haihuwa, wai ita nan duk dan Mommahn ta shiga damuwa, ta kuma muzanta, dan har lokacin ba ta san da cikin ba. Ita kam babu abin da ya dameta, ta maidata tamkar wata mahaukaciya. Duk da haka kuma ba ta haƙura ba, yin abinta take yi. Da farko ma idan Daddy ya ji ta faɗa mata magana yana tsawatar mata duk da ba komai take yi a gabansa ba, dan ya san halinsa. Daga ƙarshe ma da ya ga abun nata ba na ƙare ba ne, lokacin kuma da ita ma Mommahn aka tabbatar tana da nata cikin se ya rabu da ita ta cigaba da haushinta. Musamman da wadda ake yi dan ita abin be taɓa damunta ba daidai da minti ɗaya kuwa.


... "Wai ba ka yi farin ciki da jin namiji zan haifa ba?" Mom ta faɗa tana kallan Daddy. Murmushi ya yi ya nemi waje ya zauna yace

"Na yi mana.. Amma fa kin san ba lallai hakan ne gaskiya ba koh?"

"A'ah wallahi, ni namiji nake so.. kuma shi zan haifa. In Sha Allah se an yi wa Alhaji Matawalle takwara." Kallanta ya yi sosai ganin yanda ta fitittike daga er wannan maganar. Shi ya ɗauka da mace da namiji duk ɗaya ne idan dai Allah Ya baka. Me ye abun damuwa dan ya yi maganar da shi ma ba shi da tabbacinta?

"Toh shi kenan.. Allah Ya ɗayyiba.. Ya kawo shi lafiya." In ji Daddy. Se a lokacin ta yi murmushi tana shafa cikinta tace

"Ameen.. ko kai fa." Daga haka ta miƙe ta fice daga ɗakin, dan ba ta ma so ta cigaba da zama a ɗakin ballantana ya sake yi mata maganar da za ta ɗaga mata hankali.


Kwanaki suka cigaba da tafiya, satika na samuwa, suka kuma bayar da watanni. Har lokacin babu abin da ya chanja cikin gidan. I zuwa lokacin cikin Mommah har ya fito, duk da kasancewarta doguwa hakan be hana cikin nata bayyana sosai ba. Dan kuwa cikin lokaci ƙanƙani ya zarce girman cikin Mom, se ka ɗauka ma ta bata wasu watanni ne, nan kuwa watanninsu ɗaya. Tun daga lokacin Mommah ta ajje fita a gefe. Ya zamana komai za ta yi daga sashenta zuwa sashenta take komai. Shi kansa Daddy hakan ya masa, dan da ma ba kasafai ya cika son haɗuwarsu ba. Se ya zamana rabon da Mommah su haɗu da Mom se da suka ɗauki lokaci me tsayi. Hakan ba ƙaramin damun Mom ya yi ba, dan kuwa har se da ta aika Maimunatu ta gano mata abin da ke faruwa, dan haka kawai hankalinta be kwanta da jin Mommahn shiru ba. Amma haka ta gama gurminta ba ta samu ta ga Mommah ba. Ita kanta abun na bata mamaki, duk kuma sinƙi_sinƙi na ƙwarewarta a gulma haka ta ƙare ta gama ba ta gano komai ba.

.. Mommah na zaune kan kujera sanye cikin wata doguwar riga da ta saketa. Sosai cikinta ya fito se ka ɗauka tana dab da haihuwa ne. Daga fuska kuwa duk da yanda ta ɗan yi ƙiba hakan be hanata yin kyau ba, ta yi wani irin fresh, fatarta ta sake yin haske, kyau da sheƙi. Wayarta da ke gefenta ta yi ƙara, ta saka hannu ta ɗauka tana karawa a kunne. Gaisawa suka yi da Yaya Amina kafin daga bisani tace

"Ya nauyin jiki?" Se da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kalli cikinta tace

"Alhamdulillah Yaya.. Kin ganni ma a palour yau na samu na zauna."

"Toh Allah Ya ƙara lafiya.. Ki dai samu ki cigaba da motsa jiki."

"In Sha Allah.."

"Kin dai ƙi zuwa a ganar mana abin da za ki haifa koh?" Murmushi Mommah ta yi sannan tace

"Ni Yaya Amina na fi so kawai na haifa, se na fi jin daɗin hakan."

"Ai shi kenan.. Allah dai Ya inganta mana.. Ameen." Murmushi kawai Mommahn ta sake yi daidai lokacin da ta ji motsin shigowa cikin sashen. Ba kuma tare da neman izini ba ta ji ana neman yowa ɗakin.

"Yaya ina zuwa." Ta faɗa tana ajje wayar. Se ta ɗauki mayafi ta lulluɓa a jikinta, daidai lokacin da Mom ta ida shigowa cikin ɗakin. Da mamaki Mommah ke kallanta. Se ta ƙaraso cikin ɗakin tana cigaba da kallan Mommahn da tun shigowarta idanunta ke nuna mata wani abu da ya fi kama da ciki zaune a jikin Mommahn. Kawai se ta ƙarasa kar gaban Mommahn da ke ƙoƙarin miƙewa a hankali saboda nauyin ciki.
Kafin Mommahn ta kai ga miƙewa Mom ta saka hannu ta yaye mayafin da ke jikin Mommahn muryarta har wani rawa take yi tace

"Ke me nake gani a jikinki?" Mom ta faɗa hannunta na rawa. A fusace Mommah ta saka hannunta ta riƙo na Mom daidai lokacin da ta ida miƙewa, ta watsa mata idanunta masu shegen kwarjini tace zuciyarta na tafarfasa

"Ashe da ma ba ki da hankali? Haukan naki be ƙare a iya baki ba har se da hannunki ya taɓa ni, ki ke neman nuna min shi a aikace?"

"Ni ɗin ce nake miki hauka? Lallai ma yarinyar nan.." Mom ta faɗa duk da mamakin Mommahn ya kusa kasheta, gefe guda kuma tsoro da firgici na neman kayar da ita. Me ye ya shiga kanta? Wanne kalar hauka ne a kanta? Wane kalar sakaci ne wannan ta yi? Har wata nawa Mommahn ta ɗauka ɗauke da ciki ba tare da ta sani ba tana nan tana hauka? "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Ta faɗa tana jin yanda wani irin jiri ke ɗibarta. Hannu ta saka ta riƙo cikinta da take ji tamkar ɗan cikinta ma ya fuskanci tashin hankalin da ke neman durfafar rayuwarsu.

"Ciki ne da ke? Ciki ki ke ɗauke da shi ban sani ba Sa'adatu?" Mom ta faɗa hawaye sun cika idanunta har gani ma se da ta koma ganin dishi_dishi. Sam ta kasa ɓoye zallar tashin hankalin da ta ji a lokacin. Ta kasa ɓoye tsantsar baƙin cikin da ta tsinci kanta a ciki a yanzun. Mamaki, gami da mugun takaicin halin Mom ɗin ya sa Mom ta kasa tankawa, se tsayawa kawai da ta yi tana kallanta. Jin da Mom ta yi idan ta cigaba da tsayuwa a wajen tabbas za ta iya bajewa ya sanyata juyawa dan ficewa daga ɗakin, duk da yanda jiri ke kwasarta. Komawa Mommah ta yi ta zauna a kan kujerar bayan ficewar Mom daga cikin ɗakin. Ta saka hannu ta dafe kanta da ke sara mata. Wannan wace irin rayuwa ce? Shin Mom ɗin wace irin mata ce ita? Me za ta ƙaru da shi dan wata ta haihu bayan ita ma ba a hanata ba an bata? Shin wace kalar zuciya ce da Mom ɗin haka?.

Ɓangaren Mom kuwa zubewa ta yi a kan gado tana fashewa da kuka. Yau ta gama shiga 3 ta lalace. Wannan wace kalar mummunar rana ce ta zo ta risketa. Ashe da ma Mommahn na ɗauke da ciki amma ba ta taɓa sani ba wai da sunan suna cikin gida ɗaya? Kenan ita ma haihuwa za ta yi kamar yanda za ta haihu? Kenan wace riba za ta ci idan su biyun suka haihu? Kenan duk uban gorin da take mata hakan ya tashi a banza? Ashe ba juya ba ce? Ashe ma ta daɗe tana ɗauke da cikin amma ta mata shiru ta barta tana ta haukanta?

"Yanzu idan ta haifi mace ita kuma Sa'adah ta haifi namiji ya za ta yi? Me ze faru?" Tunanin da ya ɗarsu cikin zuciyarta kenan, wanda ya tilastawa bugun zuciyarta ƙaruwa. Kawai se ta ji hawaye sun tarar mata cikin idanu, a fili ta furta

"Allah kar ka nuna min wannan baƙar ranar." Ta faɗa tana share hawayen. Se kuma ta shiga girgiza kai a filin dai ta cigaba da faɗin

"A'ah.. hakan ma ba ze faru ba. Bayan an tabbatar min da namiji zan haifa, ta yaya kuma zan haifi mace? Hakan ma ba ze taɓa faruwa."


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO63*


___"Lafiya kuwa Hajiya?" Maimuna ta faɗa tana kallan Mom jin sumbatun da take ta yi ita ɗaya. Kawai se ta fashe da kukan da yake fitowa tun daga ƙasan ranta me ɗaci. Da ƙyar ta iya buɗe baki tace

"Maimuna na shiga 3.. Ashe yarinyar nan ciki ne da ita ban taɓa sani ba. Tana nan da tsohon ciki ina nan na sake baki." Sosai Maimuna ke mamakin abin da Mom ɗin take faɗa. Ciki kuma? Amma ba su sani ba? Ta tambayi kanta. Se dai kuma yanzu ba lokacin wannan ba ne idan ta yi la'akari da yanda Mom ɗin take a rikice, hakan ne ya sanyata kwantar da murya tace

"Ki yi haƙuri ki dena damuwa a kan wannan abun. Kin manta likita ya tabbatar miki da cewar namiji za ki haifa? Toh me ye abun damuwa kuma?"

"Ke ni kwata kwata haihuwar ce ba na so ta yi. Ni kaɗai nake so na haihu da Alhaji Matawalle, ba na son kowacce mace ta haihu da shi bayan ni." Mom ta faɗa cikin er ɗaga murya a kuma fusace. Sauke ajiyar zuciya Maimuna ta yi tana tunanin me kuma za ta cewa Mom ɗin ta haƙura. Se dai iya tunaninta ta kasa. Se kawai ta haƙura ta barta ta gama fushin kafin ta zo ta sake lallashinta ko za ta haƙura. Aikuwa ba Mom ce ta saurari Maimuna ba se washegari bayan ta soma dawowa hayyacinta. Da ƙyar da kuma saka bakin Aunt Makiyy suka haɗu suka tausheta sannan ta haƙura. Se dai duk da haka tun daga ranar se ya kasance zaman nasu ma ya chanja. Hatta magana se da Mom ta denawa Mommah, dan idan dai har tace za ta cigaba da mata magana, toh tabbas wataran za a wayi gari a tsinci gawarta saboda baƙin ciki. Ita kam a wajen Mommah hakan ba ƙaramin yi mata ya yi ba. Ko babu komai ta rage mugun iri, ta kuma huta da jin haushin Mom ɗin da kullum ba ta gajiya da shi.

A kwana a tashi, kwanaki na cigaba da tafiya haka zalika kuma cikin kowaccensu na daɗa girma, kwanakinsa na ƙaruwa. I zuwa lokacin duk yanda Mommah ba ta san er aiki se da Yaya Amina ta saka aka nemo mata wata bazawara da mijinta ya rasu ba ta sake aure ba. Ba wata babba ba ce dan ma dai an yi mata auren wuri ne. Baba Atine ita ce wadda Yaya Amina ta samowa Mommah a matsayin wadda za ta din ga tayata aiki, dan kuwa a lokacin Mommah ƙarfin hali kawai take yi. Daddy ma har magana yake mata a kan ayyukan da take yi. Shi ya sa da Yaya Amina ta sanar da shi zancen samar mata er aiki ya yi na'am da hakan ɗari bisa ɗari. Tun daga wannan lokaci Baba Atine ta soma taya Mommah ayyuka waɗanda ba su shafi mijinta ba. Dan kuwa har yanzu duk wani abu da ya shafi Daddy ita ce ke yi, duk da yanda nauyin jiki ya ƙaru. Amma haka take daurewa ta yi komai. Cikin ƙanƙanin lokaci Mommah ta fahimci halin Baba Atinen, mace ce me tsafta da kuma takatsantsan, uwa uba kuma amana. Se ya zamana ba ta wani daɗe cikin gidan ba suka saba, se suka zama tamkar wasu en uwa. Mommah babu ruwanta da cewar Baba Atinen er aikinta ce, janta take yi a jiki kamar er uwatta. Abin da ya janyo shaƙuwa kenan a tsakaninsu. Ta gefe ɗaya kuma Baba Atine ba ta daɗe cikin gidan ba ta fahimci wace ce Maimuna da kuma uwar ɗakinta. Mommah ba ta taɓa mata magana a kansu ba, amma ita da kanta ta ga dacewar ta yi nesa nesa da su kar su ɓata mata aiki. Dalili kenan da ya sanya kodayaushe tana sashen Mommah.


... A nutse take takowa zuwa palourn, hannunta dafe da ƙugunta, tana ɗan yamutsa fuska lokaci zuwa lokaci, saboda yanda mararta ke mata ciwo tun ba yanzun ba. Tun ɗazu take jin ciwo, se dai idan ya zo se kuma ya tafi. Haka dai take cigaba da daurewa, kai ba za ka ce akwai abin da ke damunta ba idan ba ganin lokacin da ciwon ya motso mata ka yi ba. A palourn ta tarar da Baba Atine shirye cikin doguwar rigar atamfa da hijabi. Se da ta nemi waje ta zauna a kan kujera a hankali sannan ta miƙa mata ledar hannunta tace

"Ga abin da za ki kai mata nan.. ki ce na gode." Mommah ta faɗa. Hannun Baba Atine ta saka ta karɓa tana faɗin

"Toh shi kenan Hajiya.. Shi kenan?" Jinjina kai Mommah ta yi lokaci ɗaya tana faɗin

"Ehh.."

"Toh bari na wuce." In ji Baba Atine tana ficewa daga ɗakin. Da addu'a Mommahn ta bita da ita tana miƙewa ta shige ɗakin da ta fito. Wayarta ta ɗauko a karo na barkatai tana ƙoƙarin kiran number Yaya Amina, se dai kuma yanzun da yake ta ɗauki mintuna ba ta ji wani ciwo ba ya sanyata ajiye wayar da nufin idan ciwon ya ƙaru se ta kirata, dan yanzu ba ta son ɗaga mata hankali. Se kawai ta cigaba da zama cikin ɗakin tana maimaita sunan Allah a zuciyarta, idanunta a lumshe kamar me jin bacci..

Daidai ta fito daga sashen suka yi kaciɓus da Mom.

"Barka da wannan lokacin.." Ta faɗa tana shirin wucewa, kasancewar kusan kodayaushe gaisuwa ce kaɗai ke haɗata da ita. Bayan ita babu wani abu. Kamar ko yaushe yau ɗin ma dai fuskarta babu yabo babu fallasa tace

"Barka.. Ina za ki je?" Mom ta tambaya tana kallanta. Mamakin tambayar ne ya sanya Baba Atine kallanta, se kuma ta sunkuyar da kanta tana faɗin

"Hajiya ce ta aike ni."

"Toh ya yi.. Da ma ni ma aiken nake so na yi.. kuma ga shi Maimuna ba ta nan. Ko za ki taimaka ki wuce ki siyo min?"

"Toh Hajiya.. Se dai kuma.."

"Se dai kuma me? Idan zuwan ne ba za ki yi ba gwara ki faɗa min tun yanzu na aiki wani." Se ta girgiza kai da sauri tana faɗin

"A'ah ba haka ba ne.. Kawo." Ta yi maganar tana miƙa hannu ta karɓi aiken da Mom ɗin ke faɗin za ta mata. Se da ta kwatanta mata inda za ta je da abin da za ta mata sannan Baba Atine ta yi hanyar fita, ya yin da Mom ta yi cikin gida. Se da ta tabbatar Baba Atinen ta fita sannan ta dawo a hankali cike da takatsantsan ta shige sashen Mommah. Duk da yanda take ji a jikinta kamar ba ƙalau take ba, hakan be hanata jefa idanunta ko za ta hangi Mommah ba. Se dai har ta gama hangenta ba ta gano kowa ba. "Toh tana ina?" Ta tambayi kanta. Se ta cigaba da takawa a hankali yanda ta san ba za a ji takunta ba ta ƙarasa har ƙofar bedroom ɗin Mommah, ta saka hannu ta tura shi a hankali. Cikin sa'a kuwa se ga shi ƙofar a buɗe take. Se ta soma leƙa idanunta dan ganin Mommahn na ciki ko kuwa ba ta ciki? Sauke numfashin da ta ji an yi ne ya sanyata sake buɗe ƙofar sosai yanda za ta iya ganin komai. Mommahn na kwance kan gadon bayan tahowar ciwon da take tunanin ze tafi kamar yanda yake mata ɗazun, se dai har yanzu shiru, babu abin da yake se ƙaruwa. I zuwa lokacin gaba ɗaya ba ta da kuzarin da za ta iya kiran waya. Ilahirin jikinta rawa yake yi, wayar da ke hannunta tuni ta kama gabanta ta yi nata wajen. Hannunta na riƙe da ƙugunta tana cigaba da kiran sunan Allah a hankali, ban da gumi babu abin da ke tsatstsafowa a kan goshinta. Mom ba ta san lokacin da ta saki ƙofar ba har tana neman yin tuntuɓe garin son shiga cikin ɗakin. Se kuma ta dakata kamar wadda aka tsayar. Idan ta shiga an ya ba ta yi hauka ba? Shin Sa'adahn haihuwa za ta yi ko kuma yaya? Me ya kamata ta aikata a irin wannan lokacin da ya fi kama da na ɗaukar fansa? Wannan lokacin da ya fi kama da lokacin cikar burinta? Duk ita kaɗai take lodawa kanta waɗannan uban tambayoyin da ko shakka babu babu wanda ze amsa mata a yanzu dai kam. Cigaba da murƙususun da ta lura Mommah na yi ne ya sanyata dawowa cikin hayyacinta, ta yi shiru tana sake nazarin abin da ya kamata ta yi. Zuciyarta babu ko ɗigon tausayin Mommahn da ke juyi a kan gado ita ɗaya tana neman agaji. Duk kuma da yanda ita kanta take jin ɗan cikinta na juyawa yana dunƙulewa waje ɗaya ba ta bi ta kan hakan ba. Burinta kawai rayuwar Sa'adah da abin da ke cikinta su wuce inda ba a dawowa a yau ɗin nan. Ta saki wani murmushi tana jan ƙofar ta rufe, ta yi amfani da mukullin jikin ƙofar ta kulle ɓam, sannan ta zare mukullin. Murmushin ta sake saki tana dafe cikinta. Ta riga ta san Sa'adah kam ta ƙare mata a yau ɗin nan. Babu wanda ze yi tunanin tana ciki, ko da ma an ji motsinta tana da tabbacin kafin a kai ga taimaka mata rai ya yi halinsa. Ɗaga mukkulin ta yi tana juyawa tana kalla da idanunta, murmushi ya ƙi barin fuskarta. A fili ta furta

"Allah Ya ji ƙanki Yallaɓiya." Daga haka ta ja jikinta ta fice daga cikin ɗakin, duk da yanda take cigaba da jiyo motsi da kuma sautin maganar Mommah. Kai tsaye nata ɗakin ta wuce har lokacin dafe da cikinta. Maimuna da ke kallanta tace

"Hajiya lafiya kuwa?" Se da ta ɗan yi shiru tana runtse idanunta kafin can ta buɗe tace

"Ba na tunanin haka.. Ina ga haihuwa zan yi."

"Toh Hajiya kawo a kirawo Alhaji a sanar da shi. A kuma kira Hajiya Makiyya a sanar da ita." Girgiza kai Mom ta yi kafin tace

"Ba na buƙata.." Daga haka ta wuce nata ɗakin. Maimuna ta bi ta da kallo cike da mamaki da tausayawa, dan ta lura da yanda uwar ɗakin nata ke cigaba da yamutsa fuska. Amma ba ta san dalilin da ya sa tace ba ta so a kira kowa ba.

Mom na shiga ɗaki kai tsaye jefar da mukullin ta yi a kan kujera, ta nemi waje ta zauna tana ƙaƙalo murmushi. Ba ta jin ko me take ji za ta iya barin cikin gidan nan ba tare da ganin an fito da gawar Sa'adah da abin da ta haifa ba. Dan a yanda ta hangeta idan ta ɗauki lokaci me yawa ba tare da taimakon kowa ba za ta iya sheƙawa. Tana kuma da tabbacin babu wanda ze ganta tun da babu me shiga ɗakin se Daddy. Baba Atine iyakacinta palour ne. Idan ma za ta iya jin motsinta ga mukullin a hannunta babu damar buɗewa. Ballantana ma tana sane ta kaɗata aike waje me nisa da nufin ta aikatawa Mommahn wani abu. Se ga shi cikin mintina kaɗan ba tare da ta saka hannu ba Sa'adahn ta kusa sheƙawa ita da abin da ke cikinta. Tana nan zaune cikin ɗakin ta kasa zaune ta kasa tsaye. Ɗan cikinta ya mata wani ƙebebe, ya hanata sakat. Ta kasa zama ta kuma kasa tsayuwar, se zagaye take tana cigaba da daurewa, saboda abin da take jira. Se dai ina.. cikin ƙanƙanin lokaci naƙuda ta tasarma Mom gadan gadan. Tun tana ganin za ta iya har ta haƙura, ta buɗe baki da ƙyar ta kira sunan Maimuna. Maimuna da ke zaune a palour tana jin wannan uban kiran ta miƙe da sauri se ga ta cikin ɗakin. A halin da ta tarar da Mom ɗin ne ya sanyata ruɗewa. Ta yi maza ta ɗauki wayar Mom da niyyar kiran Daddy, da sauri Mom ta janyo hannunta wayar ta faɗi.

"Ki taimaka min kawai.. Babu inda zan je wallahi.." Shi ne abin da Mom ta faɗa tana sauke numfashi a wahalce. Maimuna ta sake binta da kallo jikinta na matuƙar karkarwa. Ta rasa yanda za ta yi, ta kuma rasa fa'idar Mom ɗin na hanata kiran Daddy. Hakan ne ya sanyata zubawa sarautar Allah ido. Aikuwa cikin taimakonsa babu ɗaukar wani lokaci Mom ta haihu a kan gadonta. Ta sauke wata ƙatuwar ajiyar zuciya tana komawa kan gadon idanunta a rufe tana sauke ajiyar zuciya. Ta kai wajen minti 1 a haka tana jiran jin kukan jinjiri ko hakan ze alamta mata jinsin da ta haifa, se dai ba ta ji komai ba. Ita sam ba ta jikinta take ba, ba ta lafiyarta ko lafiyar abin da ta haifa take ba, a'ah ita burinta kawai ta ji Maimunan tace mata namiji ta haifa. Hakan ne ya sanyata kallan Maimuna da Babyn ke hannunta tace

"Me na haifa? Maza ki faɗa min me na haifa?" Kallanta Maimuna ta yi, fuskarta kamar ɗauke da farin ciki, kamar kuma ɗauke da akasin hakan. Muryarta a ɗan raunane tace

"Namiji!!" Komawa Mom ta yi ta baje a kan gadon tana faɗin

"Allah na gode maka.. Alhamdulillah." Ta faɗa tana lumshe idanunta.

"Hajiya duba shi ki ga.. kamar ba ya motsi." Maimuna ta faɗa bayan shuɗewar wasu mintuna tana cigaba da tattaɓa yaron ta ji ko yana motsi. Ƙirjin Mom ya buga da ƙarfin gaske. Ta ɗaga jajayen idanunta ta watsawa Maimunan da take ji kamar ta miƙe ta

Please Login or Register in order to submit comment