Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fashewa da kuka. Ita ma Mamin rungumeta ta yi tana shafa bayanta a hankali ba tare da tace komai ba. Sun shafe wajen minti 1 a hakan sannan Mami tace

"Yi haƙuri.. mu je mu zauna.." ta yi maganar tana janta suka ƙarasa wajen gadon. Se da ta bi gadon da kallo tana wani yamutse fuska sannan ta zaunar da Lulu kana ta zauna ita ma. Se a lokacin ta kalli Lulun cike da tsoro tace

"Na shiga 3 ni Sadiya.. Lulu ke ce kika dawo haka? Kin ga yanda kika lalace a cikin kwanakin nan? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.." ta faɗa tana sake riƙo hannunta. Ita dai Lulu ta kasa cewa komai se sheshsheƙa da take yi.

"Ki yi shiru ki dena kukan kin ji? Matsalar mu ta zo ƙarshe.. Kamar yanda na alƙawarta miki zan fitar dake daga gidan nan, toh hakan ce za ta faru.."

"Amma Mami shi ne kika ƙi zuwa se yanzu?" Ta tambaya idanunta cike tafff da ƙwalla.

"Ki yi haƙuri daughter.. Ai dai ga ni na zo koh? Toh ki kwantar da hankalinki, dan kuwa ban tashi zuwa ba se da na gama samar mana da mafita.." Cikin matuƙar farin ciki Lulu tace

"Da gaske Mami? In tashi mu tafi yanzu?" Ta yi maganar tana ƙoƙarin miƙewa. Maidata zaunen Mami ta yi tana faɗin

"A'ah.. Lulu ai se komai ya yi sannan zan zo na ɗauke ki.. Tafiya ma zan yi dake ballantana ki ce za ki fuskanci ƙyama daga wajen wasu.. Ki na ji na?" Ba tare da tsayawa ta wani fuskanci maganar Mamin ba tace

"Ehh.." Gyara zama Mami ta yi sannan ta soma faɗin

"Ban san yanda aka yi ba, aka samu wani hotonki wani ya rungume ki, cikin wani restaurant. Na san ba halinki ba ne amma dai tabbas hoton nan na gaske ne ba haɗi ba. Amma na yi miki uzuri dan dai kin ɗan yi sharholiya sau ɗaya. Se dai hakan ma mu taimakarmu ya yi. Dan kuwa da wannan hoton na yi amfani, da so na yi ma direct a san yanda za a yi ya je wajen shi wanda aka aura miki ɗin. Se dai kuma hakan ze iya kwaɓe mana. Hakan ne ya sa na saka aka nemo Abokinsa, aka same shi har inda yake aka kai masa zancen cewar matar da Abokinsa ya aura ba mutuniyar kirki ba ce, an rufe Abokin nasa ne ba tare da an sanar da shi ba aka aura masa ita. Idan kuma be yadda ba har sheda suna da ita, suka faɗa masa cewar su ɗin suna ɗaya daga cikin waɗanda ke ƙaunar mahaifin mijin naki shi ya sa ba za su so a cuce shi ba, hakan ne ya sa suka binciko wannan abun. Da farko dai ya so ya ba su matsala, dan ko saurararsu ma ƙin yi ya yi a kan hakan. Amma daga baya da ya ji har da sheda suna da ita, bayan duk uban bayanan da suka masa, se ya tsaya har ma ya tura hoton dan shi ma ya girgiza da ganin hoton. Daga nan ma ko ƙara saurararsu be yi ba ya tafi hankali a tashe. Sun kuma tabbatar min da sun san duk yanda ake ciki se ya nunawa Abokin nasa hoton. Na san tunani ze yi ba ze so cin amanar abokinsa ba, be san hakan mu ya taimakawa ba. In taƙaice miki zance dai wannan hoton ya je wajen Abokin wanda aka aura mikin, na kuma san idan har zuwa yanzu be je gare shi ba, toh yana dab da zuwa gare shi." Se ta ɗan dakata a nan sannan ta cigaba da cewa

"Amma fa kar ki ɗauki hakan a matsayin wani abu, kawai duk na saka an yi hakan ne dan mu samu ya sake ki salin alin ba tare da tsayawa wani dogon bincike ba. Shi ya sa muka yi amfani da abubuwa masu ƙarfi, da kuma zazzafar hujja.. Kar ki sake ki gode min kuma, ni ɗin kamar mahaifiyarki ce kin sani, har kuma abada ba zan taɓa bari na ga kin rayu cikin ƙunci ba. Ko da zan rasa wani abun ne kuwa, zan yi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin na ciro ki daga wannan hali.."

Tunda Mami ta soma magana Lulu ke kallanta, zuciyarta na bugawa. Me Mamin ke faɗa ne? A kan me take magana? Me take ƙoƙarin aikata mata a matsayin gyara rayuwarta? Zama ta yi kamar wata saƙaguwa wadda aka dasa a wajen, idanunta dake cike taff da ƙwalla suka tsaya ƙiƙam, ita kanta ƙwallar ba ta san lokacin da ta koma ba. Wani irin bugu zuciyarta ke yi wanda tunda uwarta ta haifeta ba ta taɓa jin irinsa ba, ko kuma ba a faɗa mata ba, ta san wannan bugun ya wuce ƙa'ida. Cikin sakannin da basu wuce 3 ba jikinta ya ɗauki wata irin rawa kamar wadda ake kaɗata. Tashin hankali, tsoro gami da ruɗewa suka mata dirar mikiya. Ji take kamar kunnenta be jiye mata daidai ba a kan abin da Mamin ke faɗa ba. So take ta buɗe baki ta yi magana, ta tambayi Mamin ta sake yi mata bayani a kan abin da take faɗa, ta kuma ji cikakken bayani game da maganar hoton da ta yi. Se dai tsananin ruɗewa ya hanata aikata hakan. Wani jiri jiri ta ji yana kwasarta, har se da ta soma ganin giftawar wasu abubuwa cikin idanunta, wanda hakan ya tilasta mata runtse idanunta da sauri tana dafe saitin zuciyarta da take ji kamar tana ƙoƙarin yin tsalle ne ta fito daga zuciyarta..



✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO37*


___"Ke lafiya kuwa?" Mami ta faɗa tana riƙo hannun Lulu ganin yanda ta birkice lokaci ƙanƙani. Hannu Lulun ta saka ta ture na Mamin lokaci ɗaya tana miƙewa ta soma ja da baya, daidai lokacin da kyawawan idanunta suka soma ƙyalli kamar waɗanda aka zuba wani abu a cikinsu. Se dai ƙwalla ce kawai ta gama cika cikin idanun taff wanda ƙiris take jira ta zuba. Da mamakin dai Mami ta miƙe tana kallanta tace

"Me yake faruwa Lulu?" Kasa riƙe kanta Lulu ta yi se fashewa da kuka da ta yi, ta zube a ƙasa tana yin kukan me cin rai. I zuwa yanzu Mami ta ida ruɗewa, ta ƙarasa da sauri tana sake tambayarta dalilin chanjawar tata a karo na barkatai. Da ƙyar kuma cikin kuka ta iya buɗe baki ta soma faɗin

"Mami me kika min? A kan wane hoto kike magana Mami? Mami ko mene ne ya je wajen Gwani ai ze je wajen Abba. Mami ko da da wasa ne Abba ze iya yanka ni. Mami me ya sa kika min haka..?" Kallanta Mami take yi cike da mamakin abin da ke fitowa daga cikin bakinta. Ba ta taɓa tunanin wannan shi ne abin da ze biyo baya ba, bayan ta sanar da Lulun abin da ta aikata ba, ba ta taɓa tsammanin abin da Lulun za ta mata ba kenan. Se dai dan sake tabbatarwa ya sanyata faɗin

"Ki na cikin hayyacinki kuwa daughter? Ina miki magana ne fa a kan raba aurenki da mutumin da ba kya so. Wanda muke ta fafutukar neman hanyar da za ku rabu da shi. Se yau na samo mafita kike ƙoƙarin sace min gwuiwa? Ko dai asiri ya miki ne? Hoto kuma, hoton da aka miki ne cikin wani restaurant rungume da wani, kuma dan ya je wajen shi mijin da aka aura miki ai ba ze bari ya sake fita wani wajen ba, daga nan ze tsaya, ko kin manta malamin addini ne? Abba kuma shi ya sa tun farko na faɗa miki ba wajensu za ki koma ba ni zan tafi dake wajena.." Girgiza kai Lulu ta shiga yi tana sake jin yanda kanta na wani irin sara mata.

"Mami ba ni ba ce.. Mami ba ni ba ce.." ta faɗa tana cigaba da girgiza kan cikin matuƙar ruɗewa. Kafin Mamin tace komai ta ɗora da faɗin

"Me ya sa za ki min haka Mami? Mami rayuwata ce za ta lalace fa har abada.. Na shiga 3.." ta ƙarashe tana riƙe kanta da take ji kamar ze faɗo mata. Dagalo Mami ta tsaya tana kallan ikon Allah. Anya kuwa Lulun ce ko dai an musanya mata ita? Anya kuwa tana cikin hayyacinta ko kuwa me yake faruwa? Yarinyar dake neman hanyar da za ta rabu da wannan auren, yanzu kuma an samo shi ne har ta tsaya tana iya bambance hanya me kyau da mara kyau? Cikin ɓacin rai Mami tace

"Ina ruwanki ne Lulu? Dama ba abin da muke so ba kenan? Babu wata hanya da ta za ɓulle mana, na yi iya tunanina wajen tuno mafitar da za ta saka ya sake ki amma na kasa. Cikin sauƙi kuma se ga wannan hanyar, wadda ita ce mafi sauƙi da ze sawwaƙe miki cikin kwanciyar hankali.. Ai dama abin da nake so ya yi zargi kenan, matar da ya aura ba mutuniyar kirki ba ce ta banza ce.. Idan ya sake ki ba shi kenan ba? Tunda dai kin san ke ba haka kike ba me ye na damuwa.. Saboda haka ki..."

"Ki ƙyale ni Mami.." Lulu ta faɗa tana miƙewa tsaye, duk da yanda ilahirin jikinta ke rawa saboda tsorata da ta yi da maganganun Mamin. Ba kuma ta jira Mamin da mamaki ya kusa kashewa ba ta ɗora da faɗin

"Zuciyata na dab da tarwatsewa Mami ki ƙyale ni.. Na kasa fahimtar abin da kike nufi.. Ban san da maganar hoton da kike yi ba, kuma kina maganar ɓata min suna da sunan mafita. Mami dama ba kya sona?" Ta tambaya muryarta a karye, jajayen idanunta a kan fuskar Mami. Wajen minti 1 amma Mami ta kasa furta komai se kallan Lulun da take yi, a ranta tana saƙa ko dai zuwan yarinyar gidan nan ya taɓa ƙwaƙwalwarta, ko kuma dai aljanu sun shafeta? Yau ita Lulu ke faɗawa magana haka a kan abin da ta yi dan jin daɗinta? Lallai tabbas akwai wata a ƙasa.

"Me kika sha ne Lulu? Ko dai kin samu taɓin hankali ne zamanki cikin gidan nan?" Shi ne abin da Mami ta faɗa tana kallanta sosai. Wasu zafafan hawaye ne suka zubo a kan kuncin Lulu, ta kasa cewa komai se komawa da ta yi ta kifa kanta a kan gadon ta cigaba da kukanta tunda ta ji Mamin ta ƙi tsayawa ta mata bayani yanda za ta fahimta face sake dilmiyar da ita da take yi, a kan lallai da gasken ta yi amfani da wani hoto ne can daban na wata dan cikar burinsu, wanda ita a ganinta wannan ɗin kamar tarwatsa mata rayuwarta ne Mamin ke ƙoƙarin yi. Ƙarasawa Mami ta yi ta ɗora hannunta a kan kafaɗar Lulu, da sauri Lulu ta saka hannunta ta ture hannun Mamin tana sake jin wani irin karyewar zuciya. Runtse idanunta Mami ta yi tana jin yanda tsoro ke kamata. Lallai lamarin ya caɓe mata. Ba ta taɓa tunanin Lulun na da wannan hankalin ba, ba ta taɓa tunanin Lulun kan ɗauki hakan a matsayin ɓata mata suna ba. Ta riga ta san halin Lulu, ta san wace ce ita, ta ɗauka duk abin da ta zo da shi za ta karɓa ne hannu bibbiyu. Se ga shi ta nuna mata ba haka ba ne.

"Lulu.." Mami ta faɗa tana sake ƙoƙarin kai hannunta kan kafaɗar Lulun.

"Ki ƙyale ni na ce.." ta faɗa cikin kukan dai. Sauke numfashi Mami ta yi tana ɗaukar jakarta da ta ajje sannan cikin sanyin da jikinta ya yi tace

"Zan dawo idan kin huce.." Daga haka ba ta jira abin da Lulun za tace ba ta fice daga ɗakin har lokacin mamaki ya ƙi barinta. Kasa ko da kallanta ne Lulu ta yi se faman sauke ajiyar zuciya da take yi. Babu sautin kuka se hawayen dake ta sintiri a kan kuncinta. Ta rasa ma abin da ya kamata ta yi, gaba ɗaya kanta ya kulle.



.. Cigaba ta yi da kwashe haɗaɗɗen abincin cikin warmers. Har lokacin jikinta babu kuzari, ƙoƙari kawai take yi dan ka da Baba Atine ta ji babu daɗi. Se da ta gama komai sannan ta ɗauko su a hannu ta fito daga cikin kitchen ɗin. Idanunta na a kan ƙofarsa tana tunanin ta inda ya kamata ta yi. Ta san dai idan dai har ta ajje masa abincin ze iya gane ita ke ajje Coffee ɗin nan. Ita kuma ba ta so hakan ta faru, hakan ne ya sanyata tsayawa a bakin ƙofar idanunta a lumshe tana tunanin ta inda ya kamata ta fara. Se da ta yi namijin ƙoƙari kafin ta iya ɗaga hannunta ta shiga knocking na ƙofar tana runtse idanunta da kuma sake ƙanƙame abincin saboda tsaro ka da ya ɓare a wajen, musamman yanda ta ji jikinta na rawa ta san hakan na ita faruwa.

Sanye cikin riga mara hannu da kuma gajeren wando, kunnensa ɗauke da Bluetooth yana jin waƙa. Se da ya gama jin waƙar sannan ya cire ya ajje a kan gadon sannan ya nemi waje ya zauna dan duba wani aiki da Kaseem ya turo masa. Ba dan ya so ba se dan roƙon da Kaseem ɗin ya yi ta masa, hakan ne ya sanya shi soma dubawa. Se ya ji ana knocking na ƙofar. Share wa ya yi kamar be ji ba, se da ya sake ji an yi sannan ya ɗan ja ƙaramin tsaki yana miƙewa ya ƙarasa inda ƙofar take, ya saka hannunsa ya buɗe. Yana shirin komawa ta yi ƙarfin halin tattaro duk wani kuzarinta tace

"Ga abinci.. Baba Atine tace na kawo maka.." Ta faɗa ba tare da ta kalle shi ba, se ƙasa da take kalla saboda yanda yake mata kwarjini, uwa uba kuma shigar jikinsa. Dakatawa ya yi kamar ba ze juyo ba, se kuma ya juya a hankali yana kallan uwar ƙarfin halin nan.

"You??" Ya yi maganar kamar me neman ƙarin bayani, se dai fuskarsa kaɗai za ka kalla ka san ba ƙarin bayanin yake nema ba.

"Didn't i warn u? Ko kanki ba ƙwaƙwalwa ne? Ko kina so ne a yanzun nan na datse abin da ya bar ki kike zama cikin gidan nan?" Ya ƙare a zafafe yana kallanta. Se da ya ɗan sauke ajiyar zuciya sannan ya ɗora da

"Idan kika bari na sake ganin ƙafarki a nan.. wallahi zan shata miki cin mutuncin da har ki mutu ba a taɓa miki irinsa ba.. Shashasha.. Bar nan.." ya ƙare cikin ɗaga murya yana nuna mata hanya. Jikinta har wani karkarwa yake yi bayan da idanunta suka gama cika da ƙwallar da har ta fara zubowa kan fuskarta. Tana ƙoƙarin juyawa abincin hannunta ya suɓuce saboda yanda hannunta ke rawa. Nan take ya ɓare a wajen gaba ɗaya. Cikin ɓacin rai ya sauke idanunsa a kan abincin lokacin da take ƙoƙarin barin wajen, nan ma dai a tsawace yace

"Heyy.. wait." Kamar kar ta tsaya, se dai yanda ya yi maganar ya tsoratata hakan ne ya sanyata dakatawa, kafin kuma ya ƙara mata bayani, tunda ta fahimci abin da yake nufi se ta juyo har lokacin ta kasa kallansa, yana nuna abincin yace

"Oyah.. kwashe.." Tun kafin ya sauke maganar ta saka hannu ta soma kwashewa hawayen idanunta na ɗigowa har ƙasa. Amma duk wannan ba damuwarta ba ce. Damuwarta ɗaya ta bar wajen gaba ɗaya ma ta dena ganin wannan halittar mara kirki. Se da ta kwashe tass sannan ta miƙe ta wuce kitchen ta ajje kana ta fito daga cikin kitchen ɗin ta wuce ɗaki. Kan gado ta faɗa tana fashewa da kukan da tun ɗazu ta ƙi barinsa ya fito fili. Kanta kife a kan pillow take kukan kamar ranta ze fita. Tabbas ta ji mugun zafin abin da ya yi mata, ta kuma rasa dalilinsa na yi mata hakan. Me ta yi masa? Me ya sa ya tsaneta? Me ya sa halayensa suke haka? Cigaba ta yi da kukanta me cin rai tana sake tuna abin da ya faru. Ko fuskarsa ma ita ba ta son gani a halin yanzu. Saboda haka ko mene ma ita ba za ta sake yi masa ba, hatta Coffee ɗin ma ta dena. Dan ba ta ga amfanin kyautatawa mutumin da be san darajarka ba ko kaɗan. Ji take kamar ta ɗauki waya ta kira Ammi ta faɗa mata matsalarta, se dai kuma sam ba ta son ɗaga mata hankali, ba ta so kamar yanda hankalinta yake a tashe na Ammin ma ya tashi. Wata irin kewar er uwarta ta shiga ratsata tana jin yanzu haka da tana kusa da ita da ta samu wadda za ta faɗawa damuwarta, ta kuma ɗora kanta a kafaɗarta ta yi kuka ko ta ji sanyin abin da take ji.


... Tsaki ya ja a karo na biyu yana faɗin

"Ya haka?" Ya yi maganar sanda ya ɗauki wayarsa ya shiga dannawa. Number Mom ya danna ya kira ya kara a kunnensa. Babu daɗewa Mom ta ɗaga

"My boy.." shi ne abin da Mom ta faɗa. Be bi ta kan hakan ba yace

"Mom. Coffee ɗin.."

"Coffee kake so? Bari na saka a kawo maka yanzun nan.." Cikin mamaki yace

"Nake so kuma? Wanda kike ajje min fa?" Ita ma cike da mamakin tace

"Ni kuma? Yaushe?" Ta tambaya tana ɗan ƙanƙantar da idanunta.

"Ki na nufin ba ke ba ce..?" Ya tambaya hannunsa cikin baƙar kwantacciyar sumar kansa. Miƙewa tsaye Mom ta yi tace

"Me ya faru ne wai?"

"Just tell me pls.."

"Ba ni ba ce Areef.. Wani abun?" Ta tambaya tana jiran jin amsar da za ta fito daga bakinsa. Se dai be sake cewa komai ba se katse kiran da ya yi fuskarsa a yamutse ya tattare girar sama da ƙasa kamar me nazari. Idan dai har ba Mom ke kawo masa Coffee ba wa ke kawo masa kenan? Ko dai Mommah ce?

"Exactly.." ya faɗa a kan jajayen laɓɓansa dake zagaye da kwantacciyar ƙasumbar da ta sha gyara har wani santsi santsi take yi. Babu ɓata lokaci ya saɓi jiki se sashen Mommah.


... "A'ah Areef.." Mommah ta faɗa tana kallansa lokacin da ya shigo cikin ɗakin. Ƙarasawa ya yi ya nemi waje ya zauna, ya ɗauki ƙafarsa ɗaya ya ɗora a kan ɗaya sannan yace

"Mommah.."

"Na'am.."

"Coffee ɗin da kike turawa a kai min shi na biyo.." ya yi maganar yana kallan Mommahn. Da mamaki Mommah tace

"Coffee kuma? Anya kuwa ni?" A'ah zuwa lokacin fa kansa ya kulle, toh kenan idan dai duk cikin su biyun ba su ba ne, wane kenan yake masa Coffee ɗin. Jin da Mommahn ta yi be ce komai ba ya sanyata faɗin

"Kamar matarka ke yi maka fa.." ta faɗa tana kafe shi da idanu dan ganin reaction ɗinsa.

"Me ye hakan?.." ya faɗa cikin basarwa yana riƙe ƙafarsa ɗaya dake kan ɗayar ƙafar. Ta riga ta san halin Areef ɗin, ta kuma san yanzun ma yana sane yace hakan, ta kuma san ko za ta kwana tana sake maimaita masa kalmar ba ze nuna ya gane ba. Dan haka tace

"Yarinyar dake zaune a sashen da kake ita ce take yi maka.." Kallan Mommah ya yi na tsawon sakanni ba tare da yace komai ba. Ta yaya ma ze yadda da hakan? Yarinyar da tun ranar farko ya gargaɗeta da shiga masa ɗaki ballantana a kai ga kawo masa wani abun? Anya kuwa? Ƙaramin tsaki ya saki yana ɗan lumshe idanunsa sannan ya buɗe su a lokaci ɗaya. Daidai lokacin da Mommah ke faɗin

"Ka fahimta koh?" Kamar ba ze ce komai ba dan gaba ɗaya kansa ya kulle, ashe be sani ba ya jima yana shan abun hannun yarinyar bq tare da ya sani ba? A karo na barkatai ya sake jan tsaki yana ji kamar ya miƙe ya bar ɗakin kawai. Se dai be tashin ba ya cigaba da zama har kuma lokacin be ce komai ba. Da dai ya fahimci da gasken Mommah ke yi ita ɗin ke yi masa, se ya gyara zamansa yana sake cunkune fuska

"Ya za a yi na dinga samu?" Ya faɗa cikin basarwa. Ɓoye murmushinta Mommah ta yi sannan tace

"Toh ni dai a shawarce ka sameta da kanka ka mata magana a kan ta dinga yi maka, ai hakan ba komai ba ne.."

"Wa?" Ya tambaya a sheƙe irin kuma cikin rainin hankalin nan.

"Kai mana.." Mommah ta faɗa tana kallansa. Girgiza kai ya yi yana taɓe baki sannan ƙasa ƙasa ya furta

"Yarinyar dake jiran takaddarta? Idan da na sani ma ko kallan inda Coffee ɗin yake ba zan yi ba.. Who is she? She is just like a maid fa." Ya ƙare yana yamutsa fuska. Ajiyar zuciya Mommah ta sauke cikin kwantar da murya tace

"Babu komai fa Son.. ka na ji koh? Just ka ɗauketa as a maid ɗin, se ma ya fi sauƙi. Kawai faɗa mata za ka yi ta dinga yi maka, kafin zuwan ranar.." Mommah ta faɗa a ranta cike da fatan juyewar reshe da mujiya. Cike da fatan ya amince da abin da ta faɗa masa ɗin. Cike da fatan hakan ya zama silar daidaituwarsu shi da Afrahn.

"Nooo.." ya faɗa yana miƙewa cike da jin haushin abin da ya faru. Shi dai ba ya tunanin ze iya tsayawa ya saka yarinyar yi masa abu, har hakan ya sa ta fahimci ma ze iya cin abin hannunta ba, se dai Coffee ɗin nata ne kamar ana saka masa wani sinadari me matuƙar daɗi da ƙayatarwa. Ya ɗan lumshe idanunsa yana buɗewa a fili ya ja tsaki yana sake mamakin yanda aka yi ya kwashe kwanaki yana shan Coffee ɗin ba tare da ya fahimci me kawo masa ba..


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO38*

__ A hankali ya ƙarasa inda take yana kallanta da fuskarsa ta masu bacci, se da ya je dab da ita sannan ya zauna yace kamar ze yi kuka

"Lulu me aka miki? Waye ya dake ki?" Ya tambaya yana saka hannunsa kamar ze iya ɗagota. Tun bayan fitar Mami se a lokacin ta iya ɗago kan nata, ta kalli Little da jajayen idanunta da suka taasa saboda kukan da ta yi. Se kawai ta rungume shi ta cigaba da kukan me cin rai. Da dai ya ga babu wata mafita kawai se shi ma ya biye mata suka dinga yin kukan tare. Se da ta ji har kukan Little ɗin na nema yafi nata ƙarfi sannan ta soma tsagaitawa ta shiga sauke ajiyar zuciya kamar za ta shiɗe. Cikin ƙarfin hali tace

"Ka yi shiru ka ji?" Se da ya ji ta yi shirun kuwa sannan shi ma ya yi shirun yana cigaba da kallanta kawai. Babu jimawa kuma ya koma baccin, se ta kwantar da shi a kan gadon ta koma ta cigaba da zama har lokacin ƙirjinta be dena bugawa da ƙarfi ba. Wani irin tsoro take ji duk da har yanzu ta kaasa fahimtar inda ainahin wasu daga cikin zancen Mamin suka dosa.

A nutse a kuma yanda jikinsa ke a sanyaye tun ɗazun, uwa uba kuma ɓacin ran dake ta taso masa ya saka hannu ya buɗe ƙofar ɗakin ya shiga. Ko sallama a iya kan laɓɓansa ya iya yinta. Tunda ya shigo yake jiyo sautin ajiyar zuciyar da take ta saukewa. Be yi tunanin komai ba tunda dai ya san babu ta yanda za a yi ta san da wannan hoton. Se ya ƙarasa cikin ɗakin a nutse ya yaye labulen. Tana zaunen dai kamar wadda aka dasa, ya ɗauke kansa yana mayar da shi kan gadon da Little ke kai. Kai tsaye nan ya ƙarasa, ya saka hannu ya ɗauke shi ya fice daga ɗakin zuwa ɗakin Ummeey. Wajen minti 5 se ga shi ya dawo cikin ɗakin. Sam ba ta san da shigowarsa ba, ba kuma ta san da ficewarsa ba saboda yadda ƙwaƙwalwarta ta yi nisa cikin tunani barkatai. Ya shafe tsawon minti 1 a tsaye ba tare da yace komai ba, ya ma rasa ta inda ze fara. Se ya ji yana so ya zargeta se ya ji ya kasa, haka kawai duk da komai a bayyane yake amma zuciyarsa ke son kawo masa zato me kyau a kanta. Ya ɗan lumshe idanunsa yana buɗe su sannan ya fiddo da madaidaiciyar wayarsa daga cikin aljihu, ya ɗan yi danne_danne na en sakanni kafin ya ɗauke kansa, ya maida dubansa kan Lulu yace muryarsa a ɗan shaƙe, wadda idan ka san Gwanin ka na

Please Login or Register in order to submit comment