Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kano. Sosai Mommah ta sakewa Ammi godiya, dan ta ga ƙoƙarinta matuƙa. Ta san da wata ce ba za ta zauna ta jira har ta taimaka musu ba. Ba don Allah ya taimake su ya haɗa su da Ammin ba da tuni ba wannan maganar ake yi ba.

"Ki dena min godiya ke kam.." Ammi ta faɗa tana murmushi. Kamar ta katse wayar ba tare da ta tambayi Mommahn yanda ake ciki ba. Se dai tace

"Ya kuwa maganar ɗayan yaron..?" Murmushi Mommah ta yi cike da jin daɗin tambayar Ammin tace

"Cikin ikon Allah an same shi.. Yanzu haka ma yana tare da ɗan uwansa."

"Kai Alhamdulillah.. Allah abun godiya.. Alhamdulillah.." Ammi ta faɗa har cikin ranta tana jin daɗin hakan.

"In Sha Allah zuwa gobe zan shigo.."

"Allah Ya kai mu.." Mommah ta faɗa. Daga haka dai suka yi sallama.

"Se ka ce kun san juna." Murmushi Mommah ta yi tana ajje wayarta a gefe tace

"Mahaifiyarsu Afrah ce fa ashe.."

"Ahh haba?" Daddy ya faɗa yana kallanta.

"Wallahi kuwa.. Shi ya sa ka ga na yi mamaki da ka ce ita ce number."

"Ikon Allah.. Toh Allah Ya saka mata da alkhairi."

"Ameen.." Mommah ta amsa da hakan. A daren shi kansa Daddy ya shiga kiran duk wanda ya kamata ya sanar da shi wannan abun alkhairin da ya faru.


... Washe gari sosai gidan ya tashi da baƙi, kaama daga en uwa ne, abokan arziƙi da maƙota. Abokan Daddy kuwa ba a magana, dan kuwa ƙwansu da kwarkwatarsu har da waɗanda ba a garin suke ba duk sun zo. Masu uzuri ne kawai da waɗanda ba sa ƙasar su kaɗai ne ba su zo ba. Sosai gidan ya cigaba da karɓar baƙuncin mutane, hakan ne ya sa gidan ya zama kamar wanda ake biki. Kafin rana kuwa zance ya baza gari ya baza ko ina. Cewar bayan tsayin shekaru Allah Ya bayyana ɗan gidan Alhaji Matawalle da aka sace ranar da aka haife shi. Se dai a dukka abin da ake ta wallafawa har yanzu babu wanda ya san ga wanda ya aikata laifin. Dan kuwa Daddy ya bar abun ne be sanarwa da kowa cewa Mom ce ta aikata hakan ba. Tun da dai za a hukuntata ba se an tona mata asiri ba. Ragowar abin da ya rage ta je su haɗu da Ubangiji. Wajen azahar Ummeey da Abeey suka iso gidan. Tarba ta musamman aka musu, ba daga wajen abokan Daddy, en uwansa ba, har ma da matayen abokansa da su ma suke cikin gidan. A ranar dai Ummeey da Abeey sun ga karamci, kyaututtuka kuwa sun karɓesu babu adadi. Dan kuwa kowa ya tashi da abin da yake gwangwajesu da shi. Ita dai Ummeey har kuka ta yi saboda irin karamcin da aka nuna musu.


.. Daga inda yake zaune ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana maida dubansa kan Bad Man yace

"Ka ce me?"

"Ba abin da na faɗa." Ya faɗa cikin basarwa. Murmushi Gwani ya yi dan ya fahimce shi, ya ɗauka yana sane ya share shi. Se dai sam ba haka ba ne, be ji shi ba ne, saboda tunanin da ya faɗa. Miƙewa ya yi, har ya soma takawa sannan ya kalli Bad yace

"Ba za ka je ba ne?"

"Ina?" Ya faɗa yana kallansa a kaikaice.

"Masallaci.."

"Eh zan yi a gida." Ya faɗa yana maida dubansa kan waya.

"Ba ka isa ba kuma.. Malam ka tashi mu wuce."

"Ban san hanya ba ne?" Ya faɗa yana watsa masa harara. Fahimtar dalilin Bad Man ɗin na fusata ya sanya shi faɗin

"Yi haƙuri ɗan uwa.. Tashi mu je." Ƙwafa Bad Man ya ja yana Murmushi lokaci ɗaya yana furta

"Hmmm.." Daga haka ya sauko daga kan gadon. Binsa da kallo Gwani ya yi, shi dai burinsa a yi masa laifi a ba shi haƙuri. Ya girgiza kai lokacin da suka fara tafiya dan ficewa daga ɗakin. Tare suka jera suna tafiya, cikin shigar da za a iya cewa kusan iri ɗaya. Se ya kasance sun fito sakk a en biyunsu. Tun daga nesa ya hango Kaseem ɗin da ganinsu ya sanya shi nufowa inda suke. Ya tamke fuskar nan tuna abin da ya faru. Ya ɗauke kai kamar be gan shi ba. Dab da za su wuce shi Kaseem yace

"Hello brothers.." Dakatawa Gwani ya yi, kamar Bad Man ba ze dakata ba se kuma ya tsaya. Hannu Kaseem ya soma miƙawa Bad Man. Se da ya ɗaga ido ya kalli Kaseem ɗin kamar me son gano wani abu kafin a hankali ya miƙa masa hannun suka gaisa. Kaseem ya sakar masa murmushi kamar babu wani abu da ya taɓa faruwa tsakaninsu yace

"Congratulations bro.."

"Thanks." Ya faɗa a gajarce. Se ya maida dubansa kan Gwani, shi ma murmushin ya sakar masa kafin ya miƙa masa hannu suka gaisa yace

"Ina maka barka da dawowa gida."

"Ina godiya." Gwani ya faɗa yana maida masa da martanin murmushin. Se ya saki hannun Gwani sannan ya koma inda Bad yake yace

"Pls ka manta da abin da ya faru.. In Sha Allah komai ya wuce.. Ka yi haƙuri da halayena a lokacin." Shiru Bad Man ya yi na tsawon sakanni kafin ya sauke numfashi yace

"Ba damuwa.."

"Na gode.." Daga haka suka jera zuwa masallacin tare.


... Sanye cikin wata atamfa me kyau da wadataccen mayafi Ammi ta fito daga ɗakin. Abba da ke zaune a kan kujera da wani littafi a hannunsa yana dubawa ya ɗaga kai ya kalleta.

"Ma Sha Allah! Sosai kika fito kika yi kyau abinki.." Ya ƙare yana murmushi. Dariya Ammi ta yi jin a yanda Abban ya yi maganar, tace tana neman waje ta zauna

"Toh ina godiya sosai Abbansu."

"Madallah. Kin ida shirin ne?" Se ta jinjina kai tana amsawa da "Ehh." Kafin Abba yace komai aka yi sallama cikin ɗakin. Dukkansu suka amsa sallamar suna kallan masu yinta. Ƙarasowa Mami da Jadwa suka yi, Mami ta nemi waje ta zauna kan kujera, lura da Jadwa da ke neman zama a kan kujera ya sanyata taɓota tana watsa mata harara. Ta haɗe fuska tana ji kamar ta maaze ta yi zamanta. Se dai ta nemi waje ta zauna a ƙasan.

"Barka da wannan lokacin Abban Twins."

"Barka dai Sadiya.. Ke ce a gidan?"

"Ehh wallahi.." Ta faɗa tana murmushi. Se ta maida dubanta kan Ammi suka gaisa sama sama.

"Abba ina wuni?" Jadwa ta faɗa.

"Lafiya ƙalau Jadwa, kuna lafiya?"

"Ehh.." ta amsa da hakan. Shiru wajen ya ɗauka na tsawon lokaci ba wanda ya sake cewa komai. Zuwa can dai Ammi ta miƙe tace

"Bari na wuce Abbansu.. Kar dare ya min."

"Toh madallah.. Allah Ya tsare. Kya musu fatan alkhairi kafin na zo."

"Toh za su ji In Sha Allah.. Ku gaida gida." Ta ƙarasa maganar tana kallan Mami, ba kuma ta jira tace wani abu ba ta fice daga ɗakin. Dan kuwa ita yanzu ta dawo daga rakiyar Mamin, tun lokacin da ta ji labarin abin da ya faru na son kashewa Lulu aure. Dalili kenan da ya sa yanzu take kaffa kaffa da ita. Harara Mami ta bi Ammi da ita a kan laɓɓanta tana furta

"Munafuka." Se da Ammin ta fice gaba ɗaya sannan ta maida dubanta kan Abba tace

"Uhmm da ma Yaya wajenka na zo." Gyara zama Abba ya yi yana kallanta yace

"Ikon Allah! Wajena kuma?" Se ta jinjina kai kafin ta cigaba da faɗin

"Ehh.. Da ma a kan Lulu ne.." Tun da ya ji sunan da ta ambata se ya cigaba da kallanta. Ya yin da ita ta ƙi yarda ta kalle shi. Kawai se ta cigaba da faɗin

"Zuwa na yi na sake baka haƙuri don Allah.. Ina so ne na gyara alaƙarmu ta koma kamar ta da.. Na ji abin alkhairin da ya same su, shi ya sa na ce tun da zafi zafi ni ma na je na musu fatan alkhairi kar a ce ko baƙin ciki nake musu." Daga haka ta yi shiru tana ɗan murmushi. Girgiza kai Abba ya yi, shi kam sam ya rasa gane halin Mamin, wato son zuciyarta ya mata yawa.

"Kamar na riga na faɗa miki ka da na sake jin maganaki a kan Lulu ko abin da ya shafi gidanta ba koh?. Sadiya ban san kuma me kike so da ni ba, bayan ƙoƙarin kashe auren Afaaf da kika yi duk da haka kin kuɓuta daga hannun kuliya hakan be ishe ki ba? Ba zan yanke alaƙarmu ba, amma ki sani tabbas dole mu yi nesa da juna saboda samun zaman lafiya. Afaaf kuwa na riga na rabaki da ita ki sake saka wannan a ranki. Kar kuma na ji labarin kin je gidan nan idan ba haka ba har abada zan datse alaƙarmu da ke ne Sadiya.." Ɗaga kai ta yi ta kalli Abban, ba ta taɓa tunanin hakan daga gare shi ba, dan ta san halinsa a wasu lokutan yana da sauƙin kai, shi ya sa ta yi tunanin ze tausaya mata ya barta su cigaba da alaƙa da Lulu, ko dan wannan abin alkhairin da ya same su. Se ga shi yana faɗin ze yanke alaƙarsu.

"Haba Yaya don Allah? An gama maganar komai fa. An kashe komai wallahi. Yanzu babu abin da ze kai ni wajen Lulu da danginta se alkhairi. Don Allah kar ka ce haka."

"Na gama maganata.. Ruwanki ki je gidan Afaaf, ruwanki ki koma gida.. Zaɓi ya rage gare ki.." Daga haka Abba ya miƙe ba tare da ya jira tace komai ba ya fice daga ɗakin.

"Ke ma Mami ƙi haƙura amma kin ƙi.. Idan kuma kin zaɓi Lulu ne a kan Abba shi kenan."

"Dallah can tashi mu tafi.. Er banza me baƙin hali. Maimakon ki ƙarfafa min gwuiwa, a'ah ke kullum ba ki san wannan ba." Mami ta faɗa tana jan hannun Jadwa suka fice daga ɗakin kamar za su tashi sama. Haka ta din ga sirbiɗiɗin masifa ita kaɗai kai ka ce za ta ari baki ne..


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO72*


___ A ɗaya ɓangaren kuwa babu daɗewa Ammi ta isa gidan Alhaji Matawallen. A palourn Mommah ta sauka, inda nan Ummeey ta dawo bayan gama gaisawa da matan abokan Daddy. Didi, Lulu, Little har ma da Baba Atine duka suna zaune cikin ɗakin. Baba Atine da Ummeey suna ɗan hira jefi jefi. Ammi ta yi sallama cikin ɗakin. Kamar a mafarki suka ji sallamar Ammin, gaba ɗaya suka ɗaga kai suka kalleta, dan tabbatar da ita ɗin ce ba kunnensu ke jiyo musu ba daidai ba. Gaba ɗaya manta a inda suke suka yi, suka tafi da gudu suka rungumeta lokaci ɗaya suna furta

"Ammi.." Ita ma rungumesun ta yi cike da kewarsu. Ummeey da ke zaune ta yi murmushi tana kallansu. Da ƙyar suka iya sakin Ammin kafin suka tako zuwa cikin ɗakin. Se dai duk da haka sun kaasa sakin hannun Ammin. Shi kam Little da ma tuni ya riƙo mayafin Ammin saboda ma kar ta tafi ta bar shi. Neman waje suka yi suka zauna. Ammi suka gaisa da Ummeey sosai kasancewar sun shaida juna. Tuni har Little ya fara yi wa Ammi hira, en biyunta na zagaye da ita kamar za su haɗiyeta. Daidai lokacin Mommah ta shigo cikin ɗakin, ta yi matuƙar kyau cikin wani tsadadden lace, ta yi ɗaurin da ya dace da shigarta, wanda ya zauna ya mata kyau sosai. Shi kansa mayafin da ta ɗora a kan kayan ya yi mugun kyau, ya kuma hau da lace ɗin. A taƙaice dai duk abin da Mommahn ta saka sun mata kyau, sun kuma karɓi jikinta sosai. Kai idan ka ganta ba za ka ce ta ajje 'ya'ya kamarsu Gwani ba. Ƙarasawa ta yi ta nemi waje ta zauna a kan kujera, tana kallan Ammi da murmushi kan fuskarta tace

"Barka da ƙarasowa."

"Yawwah.. barka dai.. Ya jama'a?"

"Alhamdulillah.."

"Madallah.." Sake yi mata jajen abin da ya faru Ammi ta yi. Mommah ta sake mata godiya tana kuma amsa addu'ar da Anmin ta yi a kan 'ya'yan nata.

Sosai Ammi ta yi mamaki lokacin da ta ji cewar Gwani Affan shi ne ɗan Mommahn. Wato dai kenan mazajen da Lulu da Didi suka aura en biyu ne. Se ga shi Allah Ya haɗa su sun auri juna ba tare da sanin da akwai babbar alaƙa a tsakaninsu ba. Haka ta cigaba da jajanta al'amarin kafin daga bisani ta cigaba da biyewa en biyunta da ke ta kawo mata hira. Se ta biye musu musamman da Mommah da Ummeey suka fita daga ɗakin, se ya kasance saura su kaɗai. Dan haka sosai suka yi hirar da suka daɗe ba su yita ba. A nan ne kuma cikin hikima ta din ga fahimtar wasu abubuwan. Sosai ta ji daɗi yanda duk cikinsu babu wanda ya yi ƙorafi a kan auransa, hakan ba ƙaramin faranta mata rai ya yi ba musamman idan aka yi duba da farkon auren. Kamar ko yaushe haka cikin dabara ta cigaba da yi musu faɗa, da ba su shawarwari, gami da sake ji daga bakinsu ko suna da wata matsalar. Haka dai yammacin ya kasance musu cikin farin ciki. Se bayan magribh sannan Ammi ta fara shirin tafiya saboda Abba da ya zo ɗaukarta, da kuma ta ya su Daddy farin cikin abin da ya faru.

"Ammi tare za mu tafi koh?" Little ya faɗa yana kallanta.

"Aou har ka gaji da nan ɗin?" Ta tambaya tana murmushi, duk da da ma ita ma da niyyar tafiya da autanta ta zo. Se ya matso kusa da ita ya rungume hannunta yana cuno baki yace

"Ni dai ke zan bi."

"Iyee.. Lallai ma Little.. Za ka ƙara nemana ne." Didi ta faɗa tana karkaɗa kai.

"Bare kuma ni." Lulu ta faɗa tana harararsa. Shi dai be ce komai ba se sake rungume Ammin da ya yi. Ta yi murmushi dan ta san kwana biyun da ya yi ba ya ganinta ne ya sanya shi kewarta, har ya ƙi zama duk da ga en uwansa cikin gidan.

"Ni ma da ma da kai zan tafi Autana.." Ammi ta faɗa tana sake rungumo shi.

"Kai Ammi.." Suka haɗa baki wajen faɗin hakan. Har compound suka raka Ammi cike da kewa. Ba su san da zuwan Abba ba se da suka raka Ammi har inda motarsa take.

"Laaa Abba.." Suka kusan faɗa a tare cike da tsananin farin ciki.

"Na'am Afaaf.. Afrah.." Abba ya faɗa yana murmushi shi ma cike da farin cikin ganin 'ya'yan nasa. Gaisawa suka yi sosai. Abba dan farin ciki ji ya yi kamar ya yi me. Ya san halin Didi, da ma ba shi da matsala da ita. Se dai a yanda ya ga Lulun babu damuwa ko kaɗan a tare da ita ya sa ya fahimci sun yi nasara. Da alama kuma ta karɓi auren, ta haƙura. Sosai hakan ya faranta masa rai. Ya yi musu faɗa sosai da kuma nasiha sannan suka yi sallama suka tafi ya yin da su kuma suka koma cikin gidan. Duk se suka ji zaman gidan babu daɗi, yau ɗin se ta zama ta tuna musu da rayuwarsu ta gida. Ba su wani zauna hira ba tun kafin dare ya yi sosai duk suka kwanta bacci.


... "Wai me ke damunki ne Lulu? Ba za ki faɗa min ba kin gwammace ki zauna da yunwa?" Girgiza kai Lulu ta yi kafin tace tana yamutsa fuska

"Zuciyata tashi take Didi.. Ba na son ƙamshin wallahi." Ta ƙarasa maganar tana sake yamutse fuska. Sauke numfashi Didi ta yi kafin tace

"Toh ki gwada ci ko yaya ne Uhmm?" Ta yi maganar cikin rarrashi tana matsar da plate ɗin kusa da Lulu. Da sauri ta saka hannu ta janye plate ɗin ta maida shi inda Didi ta ɗakko tace duk ranta babu daɗi

"Wallahi ba zan iya ci ba Didi."

"Yau na ga ikon Allah ni er nan.. Toh me ye za ki ci?"

"Ba komai.." Ta faɗa tana turo baki. Daidai lokacin Mommah ta shigo cikin ɗakin. Ta dubi abincin da ke gabansu tace

"Wai har yanzu ba ku ci ba?" Ta tambaya da mamaki tana kallansu su duka.

"Mommah cewa ta yi wai ba za ta ci ba." In ji Didi. Se ta maida dubanta kan Lulu tace

"Me ya faru? Me ya sa ba za ki ci ba?" Gyara zamanta Lulu ta yi kamar me shirin yin doguwar magana, tace a hankali

"Ba zan iya ci ba Mommah.." Neman waje Mommah ta yi ta zauna a kusa da ita. Ta dafata sannan tace

"Me ya sa Uhmm?" Ɗaga kai ta yi ta kalleta kafin ta maida ƙasa tace

"Ba komai.. Ƙamshin ne ba na so." Kallanta Mommah ta cigaba da yi kamin can tace

"Toh shi kenan.. A dafa miki wani abun?" Girgiza kai Lulu ta yi. Mommah ta sake faɗin

"Toh idan aka siyo miki za ki ci?" Ba dan tana da tabbacin hakan ba, se dan yanda ta ga Mommahn ta damu ne ya sanyata faɗin

"Eh."

"Toh ku fito palour yanzun nan. Ai ba a zauna haka da yunwa ba.. Ku je ko ma me kike so a nemo yanzun nan ki zo ki ci." Ta yi maganar tana ficewa daga ɗakin.

Neman waje suka yi suka zauna bayan sun fito daga ɗakin. Ba su daɗe da zama ba se ga sallamarsu Gwani cikin ɗakin. Se dai saɓanin kwana biyu da Gwani kan yi shiga irinta Bad Man yau ya fito a Gwaninsa sakk, ya yi shigarsa irin wadda ya saba, ya yi kyau abinsa. Ba su san yanda aka yi tun shigowarsu kowanne ya fahimci ga matarsa nan ba. Duk da ba gaba ɗaya fuskokinsu ne ke a waje ba. Amma kallan farko kowanne ya gano matarsa.

"Affan, ka ɗauki Afaaf ka je ka yi maza ka nemo mata abin da za ta iya ci. Ta kaasa cin wannan ɗin, kuma yunwa take ji." Mommah ta faɗa tana kallan Gwani.

"Tohm.." Ya ƙarasa faɗa yana satar kallan Lulu da ke zaune kamar mara lafiya, ta yi zuru zuru da ita. "Me ke damunta?" Ya tambayi kansa duk da ya san babu me ba shi amsa. Ɗan sosa kai Bad Man ya yi yana fakar idon Mommah ya kalli Didi, duk da yanda yake ƙoƙarin kama kansa ya ƙi kallanta ko kuma ya ƙi furta abin da yake son furtawa ya kasa daurewa. Ya kalli Mommah yace

"Amm Mommah bari mu je tare.. Idan tana buƙatar wani abun se ta ɗauka ita ma."

"Wace..?" Mommah ta faɗa tana kafe shi da ido duk da ta fahimci wadda yake nufi. Se ya basar yana ɗauke idanunsa. Runtse idanunta Didi ta yi kamar me bacci, daidai lokacin da yake faɗin

"Mommah.."

"Uhmm.." Tana girgiza kai. Da so samu ne, da kuma su kaɗai ne a wajen cewa za ta yi ashe ya san matarsa ce da ma yake ta yanƙwanasu tuntuni? Se dai ba ta faɗa ɗin ba. Ta kalli Didi tace

"Afrah ta shi ku je.. Idan kun dawo se ki yi baccin." Ji ta yi kamar tace ita babu abin da take buƙata, se dai ta yi shiru kawai ta miƙe.

"Ban ce ku daɗe ba.. Siyowa kawai za ku yi ku dawo sa ci a gida."

"Toh Mommah.." Daga haka duk suka fice daga ɗakin. Lulu ce ta soma fara hawa gidan baya ta shiga, Didi na shirin ƙarasowa ta shiga Gwani ya yi fuska ya shige bayan. Yi ta yi kamar ba ta gan shi ba, se dai ta so Didinta ce ta zauna a gidan bayan ba shi ba. Kamar ta fasa ihu haka ta ji, se ta ƙarasa kawai ta tsaya a wajen me zaman banza da ta san nan suke nufi ta zauna. Ba ta yi kankanbar buɗewa ba, dan ba ta sani ba ko har yanzu akwai ragowar halinsan nan. Ya kalleta ta cikin glass. Ya girgiza kai yana miƙa hannunsa ya buɗe ƙofar. Se kuma ya maida dubansa kan shirin tada motar da yake yi. Se a lokacin sannan ta shiga, ta saka hannu ta rufe murfin motar. Tun da suka fara tafiya babu wanda yace komai. Ba su yi wani nisa ba ya sanya hannunsa ya kunna waƙa, da yake volume ɗin a kusan ƙarshe yake se ya kasance waƙar ta soma tashi da ƙarfi ne. Soma bin waƙar ya yi a nutse kuma a hankali yana cigaba da driving. Ita dai Didi ta kame waje ɗaya dan gudun ma kar ta yi laifi. Duk da driving yake, gefe guda kuma yana bin waƙar hakan be hana shi yin amfani da damar da ya samu ba wajen satar kallan Didin ba. A karo na biyu Gwani ya kalli Bad yana jira ya ji tsawon wane lokaci ze ɗauka yana saurarar waƙar, se ya ga abun na shi ba na ƙare ba ne. Hakan ne ya sanya shi faɗin

"Ka ɗan cire mana wannan waƙar."

"Me ka ce?" Ya faɗa da ɗan ɗaga murya saboda waƙar da ta cika motar. Sake maimaita abin da ya faɗa Gwani ya yi. Bad Man ji ya yi kamar ya share shi, se kuma ya kasa. Cikin sa'a ma kuma lokacin inda yake so a waƙar ya ƙare, dan haka se ya kasheta ma gaba ɗaya ya cigaba da driving. A haka har suka ƙarasa wajen.

.. "Ki fito mu je se ki zaɓi abin da ya miki.." Girgiza kai ta yi dan haka kawai ta ji ba ta sha'awar komai na wajen. Ji take kamar ta fasa ihu, ita har ga Allah abun ya fara damunta. Me ke damunta ne haka? Allah ma ya gani abincin gidan Ummeey take son ci.

"Lulu me za ki ci ne?" Didi ta faɗa tana kallanta. Muryarta a sanyaye tace

"A siyo ko me ye."

"Kin tabbatar za ki ci?" Didi ta sake tambaya dan tabbatarwa. Se ta jinjina kai ba tare da tace komai ba. Komawa Gwani ya yi cikin wajen, ya duba wainar shinkafa ya siyo mata. Shi dai Bad Man kawai rakiya ya yi, be kuma tambayi Didi ita me take so ba kawai suka fito daga wajen. Motar ya tasa suka bar wajen. Kai tsaye gida ya nufa. Tun da ta ga inda suka nufa se ta ji gaba ɗaya zuciyarta ta karye. Tun tana tunanin daurewa se ta kasa, ba ta san lokacin da hawaye suka soma zubowa a kan kuncinta ba. Kamar an ce ya kalleta, se kuwa idanunsa suka sauka a kan hawayen da ke saukowa daga idanunta zuwa kan fuskarta.

"Subhanallahi.. Me ya faru?" Ya yi maganar yana ɗan matsawa kusa da ita. Ba ta ce komai ba hawayen kuma ba su dena zuba ba. Ganin haka ne ya sanya shi ƙarasa matsawa, ya saka hannunsa ya kamo nata hannun cikin sanyin murya yace

"Me ya faru Uhmm?" Zame hannunta ta yi tana ƙoƙarin kwantar da kanta a kan ƙofar motar. Ya yi saurin riƙota ta dawo jikinsa. Ya riƙeta gamm yana jin hawayen na sauka a jikinsa.

"Faɗa min me ya faru?" Ya faɗa yana ɗora kansa a kan fuskarta da ke jikinsa. Sam ya ma manta ba su kaɗai ne a motar ba. Dan kukan da ta soma tuni ya ruɗa shi.

"Ni abincin gidan Ummeey nake so." Ta faɗa kamar a shagwaɓe, se dai ba ta san a hakan ta yi maganar ba. Ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗe. A ransa yana mamakin wannan soyayyar da ke tsakaninta da girkin Ummeey. Jin ya yi shiru ne ya sanyata ƙoƙarin tashi. Ya sake riƙota cikin rarrashi yace

"Shi kenan.. bari mu wuce gidan." Daga haka ya ɗaga kai ya kalli Bad Man. Se a lokacin ya tuna inda suke, ba dan son ransa ba ya saketa sannan yace yana kallansa

"Ɗan uwa taimaka ka juya da mu zuwa gidanmu." Cike da mamaki Bad yace

"Wanne?"

"Gidanmu.. gidan Abeey.." Ya faɗa yanda ya san ze fahimta. Cike da mamakin dai ya sake furta

"Me ze kai mu gidan kuma a yanzu?" Ya yi maganar saboda dab suke da isa gida.

"Ba za ka taimaka ba..?" Gwani ya faɗa bayan ya kalli Lulu da ta yi shiru kamar marainiya. Se raba ido take yi kamar mara gaskiya. Be sake cewa komai ba Bad ya juya da motar zuwa gidan Ummeeyn. Se a lokacin ta sauke ajiyar zuciya, har ba ta san lokacin da murmushi ya ƙwace mata ba. Gwani ya yi murmushi yana jin daɗin murmushin da ya gani a kan fuskarta.

.. "Ba za ka shiga ba?" Gwani ya tambaya yana kallan Bad Man.

"Sorry bro.. Bari na jiraku kawai.." Ya yi maganar yana ɗan kallan Didi. Hannu ta saka ta ɓalle murfin motar ta fice, ya bita da kallo kamar wani dolo.

"Ahh.." Ya faɗa yana cigaba da binta da kallo. Ya zauna ne

Please Login or Register in order to submit comment