Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, hannunsa ɗauke da wata er ƙaramar farar leda. Da mamaki ya juya ya kalli ƙofar yana tunanin ko waye? Toh ko dai Mom ce? Ya tambayi kansa, dan ya san babu wanda ze zo ɗakin idan ba Mom ɗin ba, hakan ne ya sanya shi miƙewa ya ajje ledar nan kan kujerar ya ƙarasa inda mirror ɗin ɗakin ke nan, lokaci ɗaya yana faɗin

"Come in.." Sautin muryarsa se da ya fita tare da bugun zuciyarta. Yanda ta ji zuciyarta ta wani harba kamar za ta faɗo daga ƙirjinta. Ta sake runtse idanunta tana ƙoƙari wajen ganin ta saita bugun zuciyarta, se dai abun ya citira. Hakan ne ya sanyata ɗora hannunta a kan ƙofar kawai ta turata har lokacin idanunta a rufe. Taku ɗaya ta yi cikin ɗakin ta dakata ba ta sake yin wani ba. Ta ɗan ɗaga idanunta ta sauke su a cikin ɗakin sannan cikin dakiya tace

"Salamu Alaikum.." ta faɗa cikin sanyayyiyar muryarta dake rawa. Juyawa ya yi a mamakance ya sauke idanunsa a kan Didi. Se ya ƙanƙance idanunsa yana kallanta cike da mamakin ƙarfin hali irin nata. Takawa ya shiga yi yana matsawa zuwa inda take tsaye. A yanzu kam suma ne kawai ba ta yi ba lokacin da ta fara jin sautin takawar shi, wanda shi ma ke takawa tare da bugun zuciyarta. Se kuma ya dakata kafin ya ƙaraso inda take. Cikin kakkaura kuma daddaɗar muryarsa yace

"Kee..!!" ya faɗa kamar wani abun aka saka cikin muryar tasa dan har se da ta amsa. Hakan ne ya saka abin da ke hannun Didi suka ɗauki girgiɗi saboda hannunta dake rawa. Babu shiri ta yi maza ta ajje su a ƙasa saboda tsaro ka da ta zubar dasu, ba ta kuma san me ze biyo baya ba.

"Me ya kawo ki ɗakin nan? Wa kike tunanin ke ce? Fita a ɗakin kafin na yi ball dake.." ya ƙare cikin er ɗaga murya. A hankali ta ɗan buɗe idanunta sosai se dai ta kasa ɗaga ido ta kalle shi. Cikin karyayyiyar murya tace

"Baba ce tace na kawo..."

"Will u just shut up ko na nuna miki waye ni? Fita.." Yanzun ma ya ƙare a fusace yana watsa mata wani banzan kallo. Jikinta na matuƙar rawa, hawaye sun cika idanunta fall ta juya tana jin yanda ƙafarta ke rawa, haka ta fice daga cikin ɗakin. Kallan abin da ta ajje ya yi a fusace ya ɗaga ƙafarsa ya yi ball da su zuwa jikin bango. Cikin lokaci ƙanƙani kowanne ya yi nasa wajen bayan sun tarwatse a wajen, coffee ɗin kansa ya zube a wajen. Be bi ta kan komai ba ya koma ya zauna a kan gadon, hannunsa ya ɗauka ya cusa cikin sumar kansa yana jin wani shahararren ɓacin rai na taso masa. Se ya fesar da wata zazzafar iska daga bakinsa yana lumshe idanunsa. Mom ta zo ta sanar da shi lokacin da wannan wasan ze ƙare, idan ba haka ba da kansa ze samarwa kansa mafita ya rabu da wannan wasan.

Se da ta ƙarasa cikin ɗakin sannan ta iya fashewa da kukan. Ta shiga raira shi tana tuna irin wannan cin mutuncin da ya mata. Me ta masa haka da ya tsaneta? A haka za su yi zaman auren? Tana nan kwance tana cigaba da kukan ko zuciyarta za ta yi sauƙi ta dena mata zafi Baba Atine ya shigo ɗakin. Da sauri ta ƙaraso tana faɗin

"Subhanallahi Afrah.. Me ya faru?" ta tambaya tana ɗaga kanta ta ɗora a kan cinyarta.

"Koro ni ya yi.." Ajiyar zuciya Atine ta sauke kafin tace

"Toh ya isa haka. Ki dena kuka ka da kanki ya yi ciwo kin ji?" Jinjina kai kawai ta yi ba dan tana da tabbacin kukan ze tsaya ba. Atine ba ta samu cewa komai ba, se da ta ji ta dena kukan sannan ta soma faɗin

"Komai za ki yi ba laifi ba ne Afrah. Ko da ze miki wani abu ki daure ki cije ki yi haƙuri, saboda so nake ke ɗin nan ki zama matar Areef ta har abada. Kin ga ko anan kin karya alƙadarin mahaifiyarsa. Shi ya sa nake so daga yau ke za ki dinga dafa coffee ɗin kina kai masa, ko da ze miki wani abun a farko ne, kuma a farko ne za ki ji zafinsa, idan ya kasance kin saba da abin da yake miki ba za ki dinga damuwa ba. Shi kuma mutum a duk lokacin da yake wani abu dan wani ya ji babu daɗi, toh daga lokacin da ya fahimci wanda yake ƙuntatawan ba ya damuwa dole ze haƙura. Toh haka nake so ta faru tsakaninki da Areef. In Sha Allah nan gaba ze so ki fiye da tsammani. Ki yi haƙuri, ki yi haƙuri, ki yi haƙuri kar ki sare tun yanzu kin ji?" Shiru ta yi na tsawon sakanni masu yawa bayan gama saurarar maganar Atine. Wato kenan tana nufin ta cigaba da kai masa coffee ɗin bayan wannan abun da ya mata? Se da ta yi sheshsheƙa sannan tace

"Don Allah Baba ki bar shi.." Girgiza kai ta yi tace

"A'ah ki dena faɗar haka Afrah. Ke yarinya ce me hankali, kin kuma san fa'idar bin umarnin iyaye, saboda haka ki daure ki yi biyayya a gidan auren ki. Kowacce mace na da nata ƙalubalen, ke wannan shi me naki. Amma idan dai har kika yi haƙuri In Sha Allah ba za ki yi danasani ba.." Wasu hawaye masu ɗumi ne suka zubo mata a kan fuskarta, tana tunanin yanda rayuwarta za ta cigaba da kasancewa a cikin gidan. Se dai ita kanta ba za taso watsawa Abbanta ƙasa a ido ba, dan haka za ta jure duk wani ƙalubale da zata fuskanta cikin gidan, tunda dai Abba da kansa ya aura mata shi, wanda hakan ke nuna ya san wanda ya aura mata. Dan haka za ta yi ƙoƙari wajen ƙin ganin ta watsawa Abban ƙasa a ido.

"Allah ka ba ni iko.. Ka sassauta min.." ta faɗa a kan laɓɓanta daidai lokacin da wasu hawaye suka zubo a kan fuskarta.



... "Abbansu ina so na dinga sanin halin da 'ya'yana ke ciki. Amma babu dama tunda babu waya a hannunsu.." Kallanta Abna dake kan kujera ya yi sannan yace

"Haka ne, hakan na da kyau. Ko babu komai ke ɗin tamkar ƙawa kike a wajen 'ya'yanki. Na kuma san za su fara magana dake ne a dukkan wani abu da ya shige musu duhu. Shi ya sa a kodayaushe nake alfahari dake.." ya ƙare yana murmushi. Ita ma murmushin ta yi har zuciyarta tana jin daɗin wannan yabon da Abban ya mata. Kafin tace komai yace

"Se dai har yanzun ban amince su riƙe waya ba. Saboda haka zan karɓar miki number mazajensu idan ya so se ku dinga magana ta nan. Duk lokacin kuma da suka ga ya dace su fara riƙe waya da kansu se su siya musu.."

"Toh shi kenan Abbansu na gode.." Murmushi Abba ya yi, yana shirin cewa wanj abu, se ga Little ya fito daga cikin ɗaki sanye cikin ƙananan kaya yana murza idanu, alamar daga bacci ya tashi. Kai tsaye jikin Ammi ya faɗa yana tura baki a shagwaɓe.

"Toh me kuma ya faru?" Ammj ta faɗa tana ɗauke hannunsa daga kan fuskarsa.

"Lulu da Didina.." ya faɗa kamar ze yi kuka. Kallan Abba Ammi ta yi se kuma ta maida dubanta kan Little ɗin tace

"Toh ya isa haka uhmm?" ta faɗa tana kwantar da shi a jikinta. Miƙewa ya yi da sauri yana fashewa da kukan lokaci ɗaya yana faɗin

"Ni dai Ammi su Lulu.." Ya faɗa yana sake buɗe baki. Sauke numfashi Ammi ta yi, dan ta fahimci yau ɗin da gaske yake, rigimar ganin en uwansa yake. Kafin ta kai ga cewa komai Abba yace yana miƙa hannunsa ya ɗauke shi

"Je ka maza Ammi ta shiryaka ka zo na kaika.." Dariya me suna dariya Little ya yi yana sauka daga jikin Abba, ya kalli Ammi yace

"Ammi Abba yace ki shirya ni.." ya faɗa yana cigaba da dariyarsa.

"Aou har ka gama kukan?" Ammi ta faɗa tana murmushi. Se ya cuno baki kawai yana murmushi.

"Ahh toh ba ya samu abin da yake so ba?" Abba ya faɗa yana murmushi.

Cigaba da zama Abba ya yi cikin d'akin, yayin da Ammi ta shige cikin d'akin dan shirya Little. Sallamar da aka yi cikin d'akin ita ya sanya shi juyawa yana amsa sallamar. K'arasowa Fatima ta yi cikin d'akin ta zube a k'asa, cike da ladabi tace

"Abba ina yini?"

"Lafiya k'alau, ku na lafiya?"

"Alhamdulillah.." Se ta d'an dakata a nan, sannan ta d'ora da

"Abba Ammi ba ta nan?"

"Tana ciki.." Ya yi maganar yana nuna d'akin da Ammi ta shiga. Mik'ewa Fatima ta yi ta shiga d'akin yanzun ma da sallama a bakinta. Ammi ta amsa sallamar tana mamakin ganinta. Dan ita dai kam ta d'an jima ba ta ganta ba. Gaisawa suka yi da Ammi cike da sabo kamar yanda suka saba. Fatima ta mik'a hannu wajen Little tace

"Little zo ina za ka je.?" Mak'e kafad'a ya yi yana fad'in

"A'ah.. Ammi in tafi.?" Ya tambaya yana kallan Ammi. Se ta girgiza kai tana fad'in

"A'ah jira ni mu fita tare.." Komawa gefen Ammin ya yi ya zauna yana d'an wuwwulga k'afa, har lokacin murmushi ya k'i barin fuskarsa.

"Ammi da ma wata magana na ji, shi ne na ce bari na zo dan tabbatarwa.. Ammi na d'an kwana biyu ba na garin, se yau na dawo. Shi ne nake ji wai an yi bikinsu Lulu" ta faɗa a sanyaye. Sauke numfashi Ammi ta yi, se da ta ɗan ja lokaci ka min tace

"Ki yi haƙuri Fatima.. Ba laifin kowa ba ne se na akasin da aka samu ba kya garin. Auren ne ya tashi bagatatan shi yasa ma ba ki ji labari ba. Amma ki yi haƙuri.." Ita Fatima ji take kamar wasan yara ko kuma wani labari. Yau ba da ban Ammi da kanta ta faɗa mata wannan maganar ba, da babu abin da ze sa ta yadda. Se dai ga shi kamar yanda ta ji labari, da gasken Masoyiyar tata ta yi aure ba ma ta san da hakan ba se yanzu.

"Allah ya sanya alkhairi Ammi.. Bari na je gida.."

"A'ah Fatima dawo ki zauna.. Dama yanzu Abbansu ze kai Little gidan Lulu, dan haka ki tashi ya kai ku, se ki ganta, ni ma kuma ki gano min yanda take.." Ammi ta ƙarasa da murmushi a kan fuskarta. Murmushin ita ma Fatima ta yi tana faɗin

"Ammi ai ban faɗawa Umma ba.."

"Babu damuwa ni da kai na zan sanar da ita.. Wuce mu je.." Ammi ta faɗa tana miƙewa tsaye hannunta riƙe da na Little. Fatima ba ta sake cewa komai ba se yin gaba da ta yi. Ammi na bayanta suka fito daga cikin ɗakin. Abba na tsaye yana amsa kira. Ammi ta saki hannun Little ta ƙarasa inda Abba yake. Se a lokacin sannan Little ya yadda Fatima ta kama hannunsa, ganinsa ga shi ga Abban da ze fita da shi. Se da Abba ya ida wayar sannan Ammi tace

"Abbansu ga Fatima nan za ta muku rakiya. Se ka ajje su tare da Little ɗin idan babu damuwa.." Kallan Fatima Abba ya yi sannan ya dubi Ammi yace

"Ba na son tarayyarsu da ƙawaye ta cigaba da tafiya har yanzun.." Girgiza kai Ammi ta yi kafin tace

"Babu komai Abbansu. Na yadda da Fatima, na san halinta, babu abin da ze faru In Sha Allah. Ba halinsu ɗaya da Lulu ba, dan kuwa ta fita hankali, shi yasa ma na bar tarayyarsu har zuwa wannan lokacin.." Ajiyar zuciya Abba ya sauke yace

"Shi kenan. Allah ya ƙara tsarewa.."

"Ameen ya rabbi.. A gaida mim da ɗiyata.." Ammi ta faɗa har ranta tana jin farin ciki kamar ita ce za ta je ganin Lulun.

"Za ta ji In Sha Allah.." Abba ya faɗa shi ma yana murmushin.

"Saura Afrah.." Jinjina kai Abba ya yi yana faɗin

"Da so samu ne har gidanta zan kai yaron nan. Se dai kin san yanayin ba ɗaya ba ne. Dan haka gwara a bari idan an kwana biyu se na kai shi ita ma ya ganta." Cike da gamsuwa da maganar Abban Ammi tace

"Haka ne.. Toh Allah ya tsare." Se da Abba ya amsa da "Ameen" sannan Ammi ta juya ta kalli Fatima dake tsaye nesa da su tace

"Yawwah toh zo ki wuce ku tafi.. Ki gaida min da Lulun" Murmushi ta yi kafin ta amsa da

"Toh za ta ji" Daga haka ta soma takawa. Little bakinsa ya kasa rufuwa saboda farin ciki, dan haka yanzun ma ko kula Ammi be yi ba se tsallensa yake. Se da suka kusa giftata sannan ta riƙo hannunsa tana faɗin

"Aou haka ne abun?" ta faɗa tana murmushi. Shi ma murmushin ya yi lokaci ɗaya yana faɗin

"Ammi mun tafi.."

"Toh se kun dawo.." Ammi ta faɗa tana ɗaga masa hannu. Kai tsaye compound ɗin gidan suka nufa, inda Abba tuni ya tayar da motarsa. Dan haka babu ɓata lokaci suka ƙarasa suka shiga. Abba ya tashi motar.

Har ƙofar gidan Abba ya kai su, ya yi parking motarsa sannan ya kalli Fatima yace

"Ku shiga ciki. Zuwa anjima In Sha Allah zan zo na ɗauke ku.. Ki faɗa mata takanas zan zo ganinta idan dai har ta kwantar da hankalinta da wannan auren."

"Toh Abba" Fatima ta faɗa tana buɗe ƙofar motar ta fita cike da zumuɗin son ganin masoyiyarta. Da sallama ta shiga cikin gidan, se dai a hankali kasancewar baƙon waje ne kuma ba ta ga fuskar kowa ba. Ummeey ce ta amsa mata sallamar. Ta yi murmushi duk da ba ta shaida fuskar ba tace

"Shigo mana.." Ita ma Fatima murmushin ta maidawa Ummeey sannan tace

"Ina yini?"

"Lafiya ƙalau.." ta ƙarasa maganar tana kallan Little da shi ma ke gaisheta. Se kawai ta ji yaron ya burgeta, musamman da ƙananun shekarunsa amma ya san ya gaida babba. Ta amsa masa tana haɗawa da tambayar sunansa.

"Areef.." ya faɗa a hankali.

"Sannu Areef ka ji?"

"Don Allah Afaaf nake tambaya.." Fatima ta faɗa da ɗan sarewa, dan har ta fara tunanin ko sun yi ɓatan kai ne. Murmushi Ummeey ta yi tace

"Tana ciki.." ta faɗa tana nuna musu ɗakin Gwani.

"Mun gode" Fatima ta faɗa da murmushi a kan fuskarta. Da sauri ta ƙarasa ta buɗe ƙofar ɗakin har lokacin hannunta na riƙe da na Little. Zaune take ruwan da da shi take rayuwa shi ne a hannunta tana sha. Se dai sallamar wadda ta ji ne ya sanyata saurin ɗaga kai dan tabbatarwa. Kamar a mafarki kuwa se ganin Masoyiya da Little ta yi tsaye bakin ƙofar. Wurgi ta yi da cup ɗin hannunta ta taso a miliyan ta ƙaraso inda suke. Babu ɓata lokaci suka rungume junansu Little na tsakiyarsu. Kawai se ta fashe da kuka cikin rashin sanin abin yi.

"Lulu me ye kike kuka? Dukanki aka yi?" Little ya faɗa yana goge mata hawayen. Kallansa ta yi ba ta san sanda ta yi murmushi ba tana sake rungume shi.

"Little.." ta faɗa cike da matsananciyar kewarsa. Shi ma rungumetan ya yi yana faɗin

"Ina Didi?" Ɗago shi ta yi tana kallansa, zuciyarta na komawa ga tunanin er uwarta da aka raba su. Ko yanzun tana ina? Se ta miƙe tana riƙe da hannun Little tace

"Taho.." Ta yi maganar tana jansu dukansu bayan ta riƙo hannun Fatima.

"Masoyiya.. Kin zo tafiya da ni ne koh?" ta tambaya tana kallan Fatima. Cikin mamaki Fatima tace

"Tafiya dake kuma? A'ah fa Abba ne ya kawo mu mu zo mu gan ki.." Kamar wadda aka tsikara ta miƙe da sauri tana faɗin

"Abbanmu? Yana ina?" Hannunta Fatima ta riƙo tana faɗin

"Ya tafi fa, yace ze zo ganinki idan kin kwantar da hankalinki a kan auren nan.. Masoyiya zo ki zauna me ya faru ne wai? Me kike magana a kai?"

"Gwani shi suka ce sun aura min.. Ni kuma ba zan iya zama da shi ba. Masoyiya tunda kin zo ki tashi mu tafi kawai.."

"Ban gane ba? Yi min bayani yanda zan gane wane Gwani?" Wata uwar harara Lulu ta jefa mata tana faɗin

"Wanne kika sani? Toh Affan.." ta faɗa tana ji kamar ta fasa ihu. Shiru Fatima ta yi tana cigaba da kallan Lulun, gaba ɗaya kanta ya kulle. Gwani kuma? Toh ta ya ya aka yi auren? Tunda dai ta san babu wanda ke son wani a cikinsu? Kenan ta ya ya hakan ta kasance?.

"Lulu nan gidan kika dawo?" Little ya faɗa sanda kansa ke ɗore a kan cinyar Lulu. Girgiza kai ta yi tace bayan ta ɗauke kanta daga kallansa.

"A'ah yau zan koma gidanmu.."


.. Hannunta Fatima ta kamo tace

"Ki yi haƙuri Masoyiya, haka Allah ya ƙaddara cewa mijinki ne. Ki yi haƙuri ki karɓi hakan, ki yi biyayya a kan abin da su Abba suka miki. Kin san da cewa ba za su taɓa yi miki abin da ze cutar dake ba saboda suna sonki.."

"Yanzu ba sa sona.." ta faɗa muryarta na rawa se dai a fusace. Murmushin yaƙe Fatima ta yi tana girgiza kai tace

"Sam ba haka ba ne Masoyiya.. Tsantar sonki da suke yi ne ya sanya su zaɓa miki Gwani a matsayin mi.. "

"Kee kin ga ya ishe ni haka. Ki rabu da ni, ki ƙyale ni.." ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa.

"Shi kenan amma dai ki dawo ki ci abinci.." Fatima ta faɗa tana kallan abincin da Ummeey ta aiko musu da shi.

"Ke ba zan ci komai ba..ko da kuwa zan mutu. Da ma na fi so a ɗauki gawata daga cikin gidan nan.." Ta faɗa a fusace tana kallan Fatiman, kuma abin da ta faɗa ɗin har cikim ranta tana nufin hakan. Dan kuwa ko yanzu ma yunwar take ji, amma taurin kai, da baƙar zuciya sun hanata cin komai tun zuwanta gidan.

"Lulu wannan fa ba maganar wasa ba ce. Ba maganar da za ki dinga ɗaukarta kamar wasa ba ne. Wannan fa ana magana ne a kan rayuwarki, rayuwar aurenki fa. An riga fa an ɗaura miki aure da Gwani, ina ganin kwantar da hankalinki ki karɓi auren nan a matsayin ƙaddara shi ne kaɗae mafita Lulu. Lulu don Allah ki zama me biyayya. Ki yi koyi da Didinmu mana plsss.." Fatima ta ƙarasa tana riƙo hannun Lulun. Fizge hannunta ta yi tana faɗin

"Idan kin san wannan maganar ce ta kawo ki don Allah ki tashi ki fita, ba na buƙatarki. Idan dai har ba zuwa kika yi ki ba ni shawarar yanda zan rabu da auren mutumin man ba toh ki ƙyale ni. Ki bar ni na yi abin da na ga dama. Dama na daɗe da cire ran wani ze taimake ni, tun lokacin da Mami ta ƙi taimakona. Dan haka ga hanya nan ki tashi ki tafi, amma ki sani nan da kwana biyu za ku zo ku ɗauki gawata.."

"Wai me ye haka kike faɗa ne masoyiya? Me ye haka ne wai?" Fatima ta faɗa cikin er ɗaga murya. Ko kallanta Lulu ba ta yi ba se miƙewa da ta yi ta barta a wajen a fusace. Dan ita sam ba ta ga amfanin zuwanta ba, kawai se ta ja Little duk da yanda zuciyarta ke zafi amma haka ta zauna tana jin hirar Little ɗin da ta yi missing nata. Ganin da Fatima ta yi sam Lulun ba ta buƙatar wannan hirar ya sanyata haƙura ta dena mata ita, sannan ta kuma yin iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta ci wani abun amma hakan ya citira. Dan firr ta ƙi cin komai se zaunawa kawai da ta yi tana kallansu su lokacin da suke cin abincin. Har Isha suna gidan, se da aka idar da sallah sannan Abba ya zo ɗaukarsu. Se da Lulu ta gama shan kukanta cikin ɗaki sannan ta samu damar fitowa daga cikin ɗakin har lokacin hannunta riƙe da na Little. Fatima ta miƙa masa hannu tana faɗin

"Zo mu tafi.. Za mu dawo.."

"A..ah" ya faɗa yana sake lafewa a jikin Lulu.

"Ka taho ka ji.. Abba na jiranmu.."

"A'ah.." ya sake faɗa yana kautar da kansa gefe. Hannu Fatima ta saka dan ɗaukarsa se kuwa ya fashe da kuka da ƙarfi yana riƙe Lulu. Ita ma kukan take ji, kawai basarwa take yi, dan ba ta ga amfanin yinsa ba a wajenta, ita da ta sallamawa rayuwa. Gwara ta sauƙaƙawa kanta, se dai kuma har cikin ranta ba ta san tafiyar Little ɗin. Ji take tamkar idan ya tafi ba za ta sake ganinsa ba.

"A'ah me ya faru? Kukan mene ne?" Abeey da fitowarsa kenan daga ɗaki ya faɗa yana kallansu. Kasancewar ɗazun sun gaisa ya sanya Fatima cewa

"Wai tafiya za mu yi shi ne ya ƙi yarda.."

"Toh a bar shi mana.." Abeey ya faɗa yana murmushi. Kallan Little ɗin da yaƙi kallanta ta yi sannan tace

"Ai Abba na waje yana jiranmu.."

"Toh mu je kawai.." Abeey ya faɗa yana yin gaba. Se da Fatima ta kalli Lulu ta sakar mata murmushi sannan tace

"Na tafi Masoyiya.. Allah ya baku zaman lafiya ya kaɗe fitina, ya gyara tsakaninku.." Wata banzar harara ta jefa mata manyan idanunta kamar za su faɗo, tana ɗauke kai ba tare da tace komai ba. Ita dai Fatima ba ta damu ba ta fito daga gidan.

.. "A'ah Malam da kanka?" Abba ya faɗa yana miƙawa Abeey hannu. Murmushi Abeey ya yi yace

"Toh ya za a yi.." Se da suka gaisa sannan Abeey yace

"Wato dama maganar wannan yaro ce Areef.. Me ze hana ka ɗan bar mana shi ya kwanar mana ko 3 ne, tunda dai ka ga yanzun haka ma kuka yake"

"A'ah Malam idan babu damuwa ka bari ko zuwa nan da sati ɗaya ne, ni da kaina zan kawo shi.."

"A'ah wannan kam alfarma ce nake nema, idan dai har za ta yiwu toh a yi min ita." Abeey ya katse Abba da faɗin haka. Ɗan karkatar da kansa Abba ya yi kafin yace

"Toh babu damuwa zuwa gobe se na wuto na ɗauke shi." Murmushi Abba ya yi yace

"Ai kawai ka bar shi ni da kaina zan dawo muku da shi. Yanzu dai a aiko mana da kayansa.."

"Toh shi kenan Malam.." Daga haka suka yi sallama. Fatima ta shiga motar Abba ya tada suka bar gidan cike da kewa. Fatima ji take kamar kar ta tafi ta bar ƙawar tata.


.. "Toh ka yi shiru ai dai Fatiman ta tafi.." Lulu ta faɗa tana shafa kan Little. Cuno bakinsa ya yi har lokacin hawayen ba su dena zuba ba yace

"Ba za ta kuma zuwa ba koh?" ya tambaya yana kallan Lulu. Se ta jinjina kai lokaci ɗaya tana faɗin

"Ehh.." Duk da hakan dai be saketa ba, ya sake rungumeta dan gani yake kamar idan ya saketa ba ze sake ganinta ba.

"Kawo shi nan mu je wajena. Dan da alama yaron nam ba ze yi bacci ba idan ba kya wajen." Kallanta Lulu ta yi a zuciyarta tana saƙa abin da take nufi. Kenan Little ɗin ba a wajenta ze kwana ba? Se dai ta kasa tambayarta, dan ba ta san me yasa ba matar ke mata kwarjinin da tun zuwanta ta kasa mata musu a kan komai. Maƙe kafaɗa Little ya yi yana sake rungume Lulu. Ummeey ta yi murmushi tana faɗin

"Lallai yaron nan ƙiwarka shahararriya ce.." ta yi maganar tana yin gaba. Se kawai ta bi ta har cikin ɗakin ta nemi waje ta zauna. Har kuma lokacin Little na jikinta. Ba su daɗe da zama ba Gwani ya yi sallama cikin ɗakin. Tunda ta ji sallamarsa gaba ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke, fuskarta ta wani haɗe har da kautar da kai kamar ba ta san wani ya yi sallama cikin ɗakin ba.

"A'ah ka dawo?" Ummeey ta faɗa tana kallansa.

"Ehh Ummeey" ya yi maganar a nutse, yana kuma lura da wanzuwar wasu halittun bayan Ummeey.

"Toh sannu da dawowa. A zubo abinci ne?" Ummeey ta yi maganar lokaci ɗaya. Girgiza kai ya yi kaɗan yana ɗan yamutsa fuska yace

"A'ah.. Zan ci anjima"

"Ka tabbatar?" ta tambaya cikin kulawa, dan tafi kowa sanin halinsa. Se da ya yi murmushi sannan ya amsa da

"Ehh.." Miƙewa Ummeey ta yi ta fice daga ɗakin, dan ba ta sani ba ko ganinta da Lulu ta yi ne ya sanyata

Please Login or Register in order to submit comment