Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba.." Didi ta faɗa tana dariya. Sun ɗan ƙara mintuna suna wayar kafin daga bisani suka yi sallama cike da farin ciki, suna ji kamar kar su dena wayar. Ko kuma su dawwama suna yin wayar tun da dai yanzu ba sa kusa.



.. A palourn baƙin Daddy aka sauki Abba da ke riƙe da hannun Little.

"Abba wai nan ne gidan Didin?" Little ya faɗa yana kallan Abba. Jinjina kai Abba ya yi yace

"Nemi waje ka zauna.. Yanzu za ka ga Didin taku.." Babu musu Little ya haye kan kujerar ya zauna yana jejjefa ƙafarsa. Duk ya matsu ya ga Didin. Bayan wajen minti 10 se ga Daddy ya shigo cikin ɗakin, sanye cikin wasu manyan kaya en ubansu. Malam kayan nan sun gaji da haɗuwa, ga shi kuma sun haɗu da kyakykyawan dattijon da kuɗi da kuma ilimi suka samu wajen zama. Cikin takun nan nasa da ke kama da na masu jinin sarauta. Ko kuma ma in ce sarki da kansa ya ƙaraso cikin ɗakin. Kai tsaye ya nemi waje ya zauna. Hannu ya miƙawa Abba da murmushi kan fuskarsa daidai lokacin da yake faɗin

"Haji Muhammad.." Gaisawa suka yi Abba na faɗin

"Barka da shigowa Yallaɓai.."

"Yawwah an zo lafiya?"

"Alhamdulillah.." Abba ya amsa da hakan.

"Ina kwana?" Little ya faɗa yana kallan Daddy. Mika masa hannu Daddy ya yi ya riƙo shi ya hau da shi kan cinyarsa yace

"Lafiya ƙalau.. Me ye sunanka?"

"Little.."

"Areef dai koh?" Abba ya faɗa yana Mallam. Little da murmushi kan fuskarsa. Se ya jinjina kai shi ma yana murmushi.

"A'ah ka ce yarona ne ma sosai ashe.." Daddy ya ƙare maganar yana gyarawa Little ɗin zama. Shi kam Daddy har yanzu halin Alhaji Matawallen burge shi yake yi. Yanda yake tafi da rayuwarsa babu hayaniya. Babu laifi sun ɗan taɓa hira kafin Daddyn ya masa sallama ya fice daga ɗakin.

"Abba Didi.." Little ya faɗa yana riƙo hannun Abba. Daidai lokacin da Didi ta yi sallama cikin ɗakin cike da zumuɗin son ganin Abbanta da kuma Little. Aikuwa tun kafin ta ida shigowa Little ya tafi a guje ya rungumeta. Ita ma rungume shin ta yi sosai tana jin wata shahararriyar kewarsa. Ji take kamar ta yi kuka.

"Didinmu.." ya faɗa kamar yanda wani lokacin suke kiranta da hakan.

"Littlena.." Ita ma ta faɗa muryarta na ɗan rawa. Sun kai wajen minti 1 a haka sannan ta miƙe hannunta riƙe da na shi suka koma wajen Abban. Cike da farin cikin ganin Abban ta gaishe shi. Shi ma ƙwarai da gaske ya ji daɗin ganinta, dan haka suka ɗan shiga taɓa hira duk da sama sama ce musamman da Abba yace ba daɗewa ze yi ba. Aikuwa be daɗe ɗin bs bayan wasu mintuna ya miƙe. A nutse ya sake kallan Didi yace

"Babu dai wata matsala koh?"

"Eh Abba.." Ta ba shi amsa tana wasa da hannun Little.

"Toh shi kenan.. Allah Ya ƙara haɗa kan ku, Ya bayar da zaman lafiya.."

"Ameen." Little ya amsa da hakan, duk da ba fahimtar abin da ake faɗa ya yi ba. Dukkansu se suka yi dariya. Daga nan Abba ya fice daga ɗakin bayan sun sake yin sallama ta bayar da saƙon gaisuwarta wajen Ammi. Ta sauke ajiyar zuciya lokacin da Abban ya fice, tana ji tamkar ta baiwa zuciyata haɗin kai ko ta samu ta fashe da kuka dan ta ji sauƙin abin da take ji. Se dai ta din ga mammazewa kawai. Bayan wasu mintuna ta miƙe hannunta riƙe da na Little suka fito daga ɗakin zuwa nasu sashen..


.. Kamar waɗanda suka shekara a tare haka suka gaisa duk da ba wani annuri a kan fuskar kowanne. Se dai da yake halin ne a haka ya sa ko a cikinsu babu wansa ya damu da hakan.

"Ya ƙoƙari? Allah Ya saka da alkhairi.." Gwani ya faɗa lokacin da ya mke gyara zamansa a kan kujerar me zaman banza. Be amsa ba Bad Man har se da ya tayar da motar suka fara tafiya saman mota sannan yace

"Ameen.." Waqa Bad Man ya kunna kamar kodayaushe ya ƙure volume. A haka ya cigaba da driving cikin kwanciyar hankali. Ɗan runtse idanunsa Gwani ya yi saboda yanda yake jin kiɗan na hawar masa kai kamar me. So yake ya yi magana se dai ba ya so ya wuce gona da iri. Amma kuma yana da kyau ya yi maganar. Dan kuwa a irin wannan lokacin ba ma su sa tabbacin za su sauka daga cikin motar sa ransu ko kuma za su mutu? Idan kuma suka mutu suna jin waƙa fa? Se dai kuma ba ya so a ce ya zaƙe da yawa haka. Amma duk da haka gwara ya magantu. Se da ya sauke ɗan numfashi kaɗan kafin yace

"Idan babu damuwa ka ɗan sauke mana waƙar nan mana.." Kallansa Bad Man ya juyo ya yi. Be saba jin umarni daga wajen wani ba idan ban da Daddy. Ciki kuwa har da Mom. Dan kuwa ko ita idan ta tashi saka shi abu se ta haɗa da rarrashi da roƙo. Daddy ne kaɗai ke ba shi umarni kai tsaye ya aikata. Se ga shi Gwanin na ce masa ya yi kaza. Kamar ya share shi, se dai ya rasa dalilin da yasa yake mugun ganin girman Gwanin tun farkon haɗuwarsu. Se ya ɗan yi irin murmushin nan na saman baki kafin ya cigaba da driving. Kamar be ji abin da Gwani ya faɗa ba, se kuma ya kai hannunsa a hankali ya rage volume ɗin waƙar sosai yanda ma ba a yi ji.

"Na gode." Gwani ya faɗa yana ɗan ƙaramin murmushin nan nasa da ya fi kama da na yaƙe. Be ce komai ba Bad Man ban da cigaba da driving da ya yi har zuwa lokacin da suka isa wani police station. Tare suka sauka suna shiga ciki. Bayan kusan awa 1 zuwa da rabi se ga su sun fito tare da wasu en sanda mata da maza su biyar. Motar su daban suka yi. Bad Man da Gwani suna cikin motar Bad Man. Ya yin da su kuma en sandan suke cikin tasu daban. Wadda idan ka ganta ba za ka taɓa cewa en sanda ne a cikinta ba. Daga can baya kuma wata motar na binsu wadda ita kuma na za ka ce tare suke ba.


.. "Malam ya za ka shigo mana gida haka ba tare da an maka iso ba? Me kake nufi da hakan?" Wani ƙaton saurayi ya faɗa yana kallan mutumin da ya shigo cikin gidan kai tsaye haka nan. Se da ya gyara tsayuwarsa sannan yace

"Amma dai la bari ka ji me ya kawo ni koh? Toh ba wajenka na zo ba.. na zo wajen Ladi ne.." Shiru saurayin ya yi ya kalle ma shi sama da ƙasa kafin yace

"Ta san da zuwanka..?"

"Wai Gaddi hayaniyar me nake ji ne? Me ke faruwa?" Ladi dake fitowa daga cikin ɗakin nan nata ta faɗa tana gyara zaman ɗankwalin kanta da shi da babu duk ɗaya. Dan kuwa duk uban tulin attachment ɗin dake kanta ya fito tun daga sama har ƙasa. Sanye take cikin wata riga ta roba irin me kama jikin nan. Se skirt da ta saka wanda ya kamata gam kamar za ta fashe.

"Wannan mutumin ne ya shigo babu izini mana.." Wanda aka kira da Gaddi ya faɗa yana hararar mutumin. Maida dubanta kan mutumin Ladi ta yi ta kalle shi na tsawon sakanni kafin ta maida idanunta kan Gaddi tace bayan ta jefa masa harara

"Bash shi mana.. Be faɗa maka mun yi da shi ze zo ba ne?" Ta ƙare maganar tana ida fitowa daga cikin ɗakin. Jikintan nan na rawa kamar ba jikinta ba. Ita a lallai dole se ta ja ra'ayin koma wane ne.

"Aou toh ai se ya yi magana.." Gaddi ya faɗa yana soma barin wajen. Se ta kai hannu ta daki kafaɗarsa daidai lokacin da take furta

"Toh yi haƙuri sarkin mita." Mutumin ya bi su da kallo kafin ya jinjina kai.

"Mu je koh?" Ta faɗa tana sakin wani shu'umin murmushi.

"Ina dai ke ce Ladin ban yi ɓatan kai ba?" Da sauri ta girgiza kai

"A'ah ko kaɗan ba ka yi ɓatan kai ba.. Ni ce Ladi.. shigo." Ta sake yin gaba tana cigaba da jijjiga jikinta. Hannunsa ya dafe kan Bluetooth ɗin dake kunnensa a hankali yace

"Ku shigo kawai.." Daga haka ya sauke hannunsa. Kafin ƙiftawa da Bismillah se ga en sandan nan sun shigo sanye cikin uniform ɗinsu kowannensu babu annuri a kan fuskarsa.

"Ku kama duk wanda kuka gani.. Yau za a rufe gidan nan.." Ya sake bayar da umarni ta cikin waya. Cikin sakannin da basu wuce 3 ba en sandan suka fara aikinsu. Juyowar da Ladi za ta yi saboda jin da ta yi har lokacin mutumin be taho ba ya yi daidai da lokacin da mutanen cikin gidan suka soma ihu saboda kamasu da aka fara yi. Tuni kowa ya fara neman hanyar tserewa. Ya yin da en sandan suka ƙi basu kowacce dama. Suka dinga cafkesu suna zuwa su jefa su cikin motar nan. Tuni waɗanda ke cikin ɗaki maza da mata suka soma fitowa wasu da gajerun wanduna wasu da ɗaurin ƙirji. Kowa kuma hanyar gujewa en sandan yake nema. Sake buɗe idanunta Ladi ta yi dan sake tabbatar da abin da ke faruwa, dan ta ɗauka mafarki ne. Dan kuwa ba yau ne rana ta farko da ta soma irin mafarkin nan ba. Se dai da yake ta san hakan ba me yiwuwa ba ne ya sanya ba ta damuwa.

"Kamata.." Shi ne abin da mutumin nan ya faɗa yana kallan Ladi. Babu ɓata lokaci er sandar ta riƙota. Se a lokacin sannan ta fara tunanin to ko dai ba mafarki take yi ba. Jin an fara janta ne ya sanyata buɗe baki da sauri tace

"Ke meye haka ne? Wai ma me kuke min haka ne a cikin gida?" Ta tambaya tana jin wani bugun zuciya.

"Wuce kawai.." Ya sake bata umarni. Se ta sake cigaba da jan Ladi. Daidai lokacin da ta yi kukan kura ta fasa ƙara idanunta a kan yanda ake wulaƙanta mata mutanenta. Ake wulaƙanta mata gida, ake ƙoƙarin tozartata. Cike da mamaki da tsoro take cigaba da kallan abin da ke faruwa dan ba ta taɓa tsammanin nan kusa akwai wanda ze zo ya tarwatsa gidan nan ba bayan abubuwan da ta yi duk dan ta rufe bakin mutane.

"Ku dena wannan abun.. Kar ku kama min mutane.. Me muka yi muku? Ku su waye? Ashe dama kai yaudarata ka yi?" Ta ƙare tana kallan Mutumin nan. Ba tare da ya kalleta ba ya soma takawa dan barin wajen. Wanda hakan ya bawa er sandar damar jan Ladi da ƙarfin da take da shi.

"Wai ba za ki ƙyale ni ba.. Ki sake ni mana.. Ku kuma ku bar abin da kuke yi na faɗa muku ku dena.. ku dena nace.. Yau na shiga 3." Ta ƙare tana sake daƙirewa. Jin komai take kamar ba gaske ba. Kuka kawai Ladi ta fashe da shi lokacin da suka fito daga cikin gidan. Daidai lokacin da wani daga cikin en sandan ya saka key ya datse gidan da shi ta soma ƙoƙarin zubewa a wajen. Er sandar da yake ƙaƙƙarfa ce ta sake riƙota. Se kawai ta cigaba da fiffizgewa kamar wadda ta tayar da aljanu tana ta sumbatu..

"Kar ku min haka.. Ku ƙyale min gida.. Na shiga 3.. Wai gaske ne abin da ke faruwa? Na sake shiga 3 me na yi wa malam ze min haka.." Makamantan abin da take faɗa kenan har lokacin ta kasa yadda gaskiya ne abin da ya faru. Amma idan kuma gaskiyar ne toh tabbas Malam ne ya rage yi mata aiki saboda bijire masa da ta yi a karo na ƙarshe da ta je wajensa kan cewar se ya kwanta da ita kamar yanda aka saba sannan ze mata aiki. Ita kuma tace za ta je ta dawo ya yi mata aikin. Ta ɗauka ze mata aikin ne kawai dan ita ta ƙuɗurtawa ranta ƙin dawowar a wannan karon. Se ga shi ya mata ɗanyan aiki. A haka Ladi na ihu na komai aka shigar da ita cikin mota. Daga haka suka ja ta suka bar wajen.


.... Sun yi nisa suna hirar ita da Little abinta cikin matuƙar kewarsa. Kamar wadda aka tsikara ta tashi ta dubi agogon dake manne a bangon ɗakin. Da sauri ta zaro manyan kyawawan idanunta masu kyau tace

"Kaii!!" Ta faɗa ganin da ta yi har ta gota lokacin da take kai masa Coffee ɗin.

"Didi mene ne?" Little ya faɗa a shagwaɓe yana kallanta. Se ta yi saurin ƙaƙalo murmushi ta saka a kan fuskarta daidai lokacin da take faɗin

"Ba komai fa.. Tashi mu je ka raka ni kitchen.." ta yi maganar tana zamowa daga kan gado. Shi ma sakkowa ya yi da sauri dan karta fita ta bar shi. Ta kama hannunsa suka fita tare daga ɗakin, suna tafiya Little na cigaba da bata labarin abin da ya faru sa basa nan. Ita dai duk hankalinta ya tafi kan kar ta wuce lokacin da ya saka mata ya zo ya dinga mata hayaniya. Kai tsaye kitchen suka nufa. Ta samarwa Little waje ya zauna yayin da ta shiga abin da ya kawota. Tana yi suna cigaba da hirarsu gwanin burgewa. Kai idan ka ganta se ka ɗauka da wani ƙaton mutum me hankali take hira, nan kuwa da Ash_sheik Areef Little take hira, wana ta yi kewarsa mara misali.

"Jira ni a nan.. bari na je na dawo." Ta faɗa lokacin da suka fito hannunta ɗauke da plate ɗin dake ɗauke da cups ɗin Coffee guda 3.

"Didi.." ya faɗa yana riƙo hannunta. Se ta sakar masa murmushi kana tace

"Yanzu fa zan dawo.. Ka zauna Uhmm?" Ta ƙare tana jan kumatunsa. Ba dan ya so ba ya ɗaga kai. Hannunta ɗauke da Coffee ɗin ta soma takawa zuwa ɗakin Bad Man.

A gajiye ya dawo gidan, duk da be tsaya an gama komai a gabansa ba. Ya bar Gwani ne a can ɗin ya taho. Dan haka kai tsaye kayan jikinsa ya fara ragewa dan ya samu ya watsa ruwa a jikinsa. Ya soma ɓalle maɓallin rigarsa aka yi knocking ƙofar ɗakin. Se ya dakata yana ɗaga idanunsa ya kalli ƙofar kamar me nazari. Se kuma ya maida dubansa kan hannunsa ya duba lokaci. Tabbas ya san ita ce. Se dai kuma ya tuna da rashin mutuncin da ta tsira yanzu. Wanda ba karamin ɓata masa rai yake ba. A ganinsa wannan ɗin ai salon raini ne ba komai ba. Ɗauke kai ya yi kamar be ji an yi knocking ɗin ba ya cigaba da abin da yake yi cikin basarwa. Daga ɓangarenta kuwa kwaɓe fuska ta yi jin har lokacin shiru. Se dai ta sake yin shahada ta kuma ƙwanƙwasa ƙofar cike da fatan ta ji takunsa ta juya ta bar wajen dan kuwa har Allah Allah take ta koma su cigaba da hirarsu da Little. Se dai sam, ko kusa ko alama ba ta ji takunsa ba har lokacin, ba ma ta ji motsin komai ba se kawai ganinsa ta yi a ƙofar ɗakin idanunsa a kanta. Da sauri ta ja da baya dan ba ta yi tsammanin ganinsa a wajen ba. Ta yi maza ta sauke kanta ƙasa. Se ta soma ƙoƙarin ajje Coffee ɗin dan ta juya. Lura da hakan da ya yi ne ya sanya shi buɗe baki yace a fusace

"Kar ki soma ajjewa.." Abin da ya dakatar da ita kenan daga abin da ta yi niyya. Da nufinta ta ɗaga kai ta kalle shi se dai sam ta kasa. Dan haka kawai se ta miƙe a kan ƙafafunta daidai lokacin da yake faɗin

"Wuce ki je ki ajje.." Yanzu kam ba ta san lokacin da ta kalle shi a mamakance ba. Ya ɗauka shi da kansa yace mata kar ta sake shiga ɗakin? Har da yi mata warning a kai. Se yanzu kuma ze ce ta shiga? Kai an ya ma shi ne kuwa? Ganin da ya yi kawai rarraba ido take yi kamar ba ta fahimci abin da yake nufi ba ya sanya shi sake faɗin

"Ke!! Na ce ki shigo koh?" Se ta girgiza kai da sauri ba tare da ta kalle shi ba. A karo na farko tace

"A'ah.. Ka ce kar na sake shigowa."

"Yanzu kuma na ce ki shigo." Ya yi maganar kamar ransa a ɓace.


MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO55*


___Juyawa ta yi a hankali ta kalli Little da ke ta kalla kallansa. Se kuma ta dawo da kanta kamar za ta sake cewa wani abu se kuma ta kama bakinta. Dan ba ta san yau ɗin me ya taka ba. A nutse ta sake ƙanƙame abin da ke hannunta sannan ta soma takawa. Se kuma ta ɗan dakata saboda yanda ya yi bake bake a bakin ƙofar. Se da ya watsa mata wani kallo sannan ya juya ya koma ciki. Se a lokacin ta taka ta shige ɗin sum sum ta isa inda ta saba ajiye wa a da. Ta ajiye sannan ta juyo dan ficewa daga ɗakin. Se dai har ga Allah tana jin tsoro kar ta je ta sake yin laifi. Dan haka a hankali ta ɗan saci kallansa. Kamar be san da zaman wata halittar cikin ɗakin ba. Dan kuwa cigaba da abin da yake yi ya yi. Daidai lokacin da ta kalle shi ɗin ya ɗaga ido ya watsa mata wani kallo da ya fi kama da na gargaɗi. Se ta yi saurin kauda kanta tana jin bugun zuciyarta na ƙaruwa. Kawai se ta nemi waje ta zauna a sukwane tana ji kamar ta fasa ihu. Ƙwafa shi kam ya yi a ransa yana sake saƙa yanda ze barta ta cigaba da zama cikin ɗakin har zuwa wani lokaci. Ko ba komai ya san ba za ta sake rashin kirkin da ta tsiro da shi ba. Se da ya ida ɓalle maɓallan rigar gaba ɗaya ya zamana tana jikinsa ne be kai ga cireta ba sannan ya nemi waje ya zauna. Hannu ya kai ya ɗauki coffee ɗin ba tare da ya kalleta ba ya soma sha yana danna wayarsa har da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Har bayan shuɗewar wasu mintuna yana cigaba da shan abinsa hankali kwance. Da alama ma ya manta da zamanta cikin ɗakin. Sake satar kallansa ta yi. Ji take kamar ta tashi ta yi tafiyarta. Musamman saboda Little da ta bari a waje shi ɗaya. Lura da ba ya ganinta ne ya sanyata soma miƙewa cike da takatsantsan. Daidai lokacin da aka soma ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin. Dakatawa ya yi da abin da yake yi. Ya juya ya kalli ƙofar cike da mamakin wanda ke knocking ɗin. Se ya ajje cup ɗin ya miƙe zuwa wajen ƙofar ya buɗe. Se kawai ya tsaya yana kallan Little ɗin da shi ne yake ƙwanƙwasawa. Waye wannan ɗin? Ya tambayi kansa.

"Didina ta shigo?" Little ya yi maganar kamar ze fashe da kuka.

"Didi.." ya maimaita sunan a kan laɓɓansa fuskarsa na cigaba da nuna mamakin da ya ke ciki.

"Waye hakan?" Ya tambaya yana kallan Little.

"Didina.." ya sake maimaita sunan kawai. Da sauri ta sake miƙewa jiyo muryar da ta yi. Se kawai ta ƙaraso bakin ƙofar tana kallan Little ɗin. Daidai lokacin da ya ɗaga kai ya kalleta se kawai ya tafi da gudu ya rungumeta. Hannu ta saka ta rungume shi tana murmushi. A hankali ya kalli Bad Man sannan ya ɗaga kai ya kalli Didi kamar me raɗa yace

"Uncle?" Se da ta saci kallan Bad Man ɗin sannan kawai ta jinjina kai tana ƙaƙalo murmushi a kan fuskarta. Sakin hannunta Little ya yi ya tafi wajen Bad Man yace yana murmushi

"Uncle ina kwana?"

"Uncle.." ya sake maimaita sunan a kan laɓɓansa idanunsa a kan Little. Ya ɗan taɓe baki sannan yace

"Ka na lafiya?" Ya yi maganar yana wucesu. Daidai yana shirin giftata ta yi ƙarfin halin faɗin

"Don Allah mu tafi?" Dakatawa ya yi ba tare da ya kalleta ba. Se kuma a hankali ya ɗaga kai ya kalleta.

"Da wa ya zaunar da ke?" Ya yi maganar cikin basarwa. Ba ta san lokacin da ta ɗaga idanunta ta kalle shi ba, cike da mamakin furucinsa. Se kuma ta yi saurin ɗauke kanta saboda yanda ta ji waɗannan idanunsa masu madaidaitan girma sun mata wani irin nauyi. A take ta ji wani irin ɓacin rai da kuma takaici sun haɗar mata. Ji ta yi kamar ta fashe da kuka saboda haushi. "Lallai ma mutumin nan, yau na sake tabbatarwa ba shi da kirki ko kaɗan." Ta faɗi hakan a cikin ranta. A fili kuma se ta kama hannun Little da sauri ta ja shi suka fice daga ɗakin. Ko da suka koma ɗaki ma duk se ta kasa sukuni, maganar da ya faɗa mata ɗin tana ta dawo mata.

"Didi wai nan gidan kika dawo?" Tambayar Little ta katse mata tunanin da take yi. Se ta dawo da dubanta kansa. Ta ƙaƙalo murmushi tace

"Ehh.."

"Daga yanzu wancan ne Uncle koh?" Ya sake tambaya yana murmushi. Ji take kamar tace masa a'ah saboda haushin da take ji. Se dai ta san halin Little ɗin, idan ta faɗi hakan shi kenan ta zauna masa a kai.

"Ehh shi ne.."

"Tohm.." ya faɗa yana murmushi. Ta ɗauki mintuna masu yawa kafin ta iya mantawa da abin da Bad Man ɗin ya mata. Ta dawo da hankalinta kan Little suka cigaba da hirarsu.




.. "Sannu da hutawa Ummeey.."

"Yawwah sannu ka dai.. ka dawo?"

"Eh Ummeey.. Abeey na ciki kuwa?" Gwani ya tambaya yana kallan ƙofar ɗakin Abeey.

"A'ah ya fita kam babu jimawa.."

"Ohk.."

"Wai ni kam ba daga kasuwa kake ba ne?" Se da ya kai hannunsa ya ɗan shafa kansa kafin ya girgiza kai

"A'ah Ummeey ba daga nan nake ba."

"Oh ni 'yasu.. Wai Affan me kake so ka zama ne? Kai ba ga kasuwar ba, kai ba ga zama ka kula da er mutane ba?" Shiru ya yi kamar ba ze yi magana ba se kuma ya ɗan gyara zama kafin yace

"Ki yi haƙuri Ummeey.. Amma ba wani abun ba ne. Kawai dai akwai wani dalili da yake saka ni fitar. Amma In Sha Allah ya zo ƙarshe. Kasuwa kuma Ummeey yanzu ina da damar bawa wani riƙo ya riƙe min ba lallai se na je ba." Jinjina kai Ummeeey ta yi sannan tace

"Duk da haka dai Affan.. Ya kamata ka din ga zuwa ɗin kullum."

"Shi kenan Ummeeey In Sha Allah.." ya faɗa da murmushi a kan fuskarsa.

"Toh Allah ya yadda."

"Ameen" ya amsa da hakan yana cigaba da zama a wajen. Bayan shuɗewar wasu mintuna ya sake satar kallan ɗakinsa. Se kuma ya maida dubansa kan Ummeeey yace

"Ummeeey bari na je."

"Toh madallah.." Ummeeey ta faɗa. Ba tare da ya sake cewa komai ba ya miƙe a nutse ya wuce ɗakin. Da sallama ya shiga ɗakin a hankali. Idanunsa a kan gadon da yake da tabbacin tana kai. Aikuwa ilai tana kai ɗin se dai saɓanin yanda yake tunanin ze ganta a kwance se ya ganta zaune kan gadon kamar wadda aka yi wa dole. Ya riga ya fuskanci taɓarar da take ji da ita yanzu dan haka ba tare da ya ce da ita uffan ba ya saka hannu ya ɗauki wayarsa cike da fatan ta yi wayar kamar yanda ya bar mata wayar dan ta yi kira. Kai tsaye call logs ya shiga. Da alama ta manta ba ta yi deleting contact ɗin ba bayan ta gama. Ya yi murmushi har ransa yana jin daɗin hakan. Dan ko babu komai ya san za ta rage damuwa kaso me yawa daga cikin wadda take ciki.

"Ki na lafiya?" Ya tambaya yana kallanta. Sarai ta ji maganar tasa. Se dai ba tace komai ba se ɗauke kai da ta yi tana ji kamar ta tashi ta masa duka saboda wannan tambayar da ya yi mata. Ya san tabbas ta ji shi, ya kuma san har yanzu haushin nasa take ji shi ya sa ta nuna kamar ma ba ta san da wanzuwarsa cikin ɗakin ba. Jinjina kai ya yi yana cije lips ɗinsa gami da murmushin gefen baki dukka lokaci guda. A hankali ya shiga takawa zuwa wajen gadon. Duk da ta ji motsinsa hakan be sanyata juyowa ba. Dan ta riga ta san idan ya gama

Please Login or Register in order to submit comment