Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalmar a illata rayuwarta. Lalli ta cika me kwakwalwar kifi da duk da bata gane wannan ba sai yanxu. Amma kuma ta godewa Allah da yasa ta farga tun yanxu basai da mai afkuwa ta afku ba taxo tayi fargar jaji.





Ta yanke shawarar tattara duk wani abu daya danganci soyayya ta watsar tunda bata karbeta ba, ita da bata da farin jinin mata ma ba balle maxa? Soyayyar qaninta Nura dake kwance a kabari ma kawai inta riqe ta isa cika mata xuciyarta har ixuwa lokacin da Allah xai kawo mata dan qauye kasashshe wahallale irinta ya aureta suje suyi rayuwarsu ta yadda indai xaiga mutuncinta da qimarta ya fiye mata maxan birni masu kyale kyale. Tana wannan tunani bacci ya kwasheta.



Saida Iya ta tasheta sannan ta tashi tayi sallah, idonta jajur tana xaune akan sallaya kanta yana sara mata. Duk yadda taso kawar da abunda Deni yayi mata amma abun ya gagara, gani take kamar a mafarki wai wanda takeso ta yadda dashi shine yayi mata haka. Ta fashe da kuka Karo na farko tunda abun ya faru, Iya ta katse lazimin da take tace "sakeenatu lfy?" bata kula Iya ba tacigaba da kuka domin tasan baxata taba iya sanar da wani abunda ke tsakaninta da Deni ba balle Iya. Sai da tayi kukanta ma'ishi kana tace da Iya Nura na tuna ya tafi ya barni ni kadai a wannan duniyar mara dadin xama. Iya ma ta share nata hawaye ta dunga aikin lallashin sakeena har tayi shiru.

***** ****** ******* ****


Satittikan da suka biyo bayan wannan lamari sakeena tayisune cikin wata irin nutsuwa, duk da kasancewaarta nutsatstsiya wannan abu daya faru ya koya mata hankali da tarin darasi saboda haka ta kame kanta ta kuma wata nutsuwa akan tata nutsuwar.




Inka ganta a tsakar gida to aiki take ko kuma tana taya Iya girki tana gamawa kuwa xata koma daki, ta tsani koda jin sunan Deni balle ganinsa kuma ta taki sa'a tunda abun ya faru befi sau 2 ko 3 suka hadu ba saboda tana tsananin gujewa hakan.




A tsammanin Iya da sauran ahalin gidan abunda Anty tai mata da kuma rabuwa da Barrister shine yake damunta wanda Iya kan yawan yi mata nasiha akan hakan. Yayin da koya suka hada ido da Amina sai tayi mata gwalo ko dariya, itadai sakeena ita tasan abunda yake nuqurqusarta.



A bangare guda kuma Deni tun sanda Sakeena ta kifeshi da mari ta fita daga dakin shima nadama ta aureshi. Yadda sakeena bata rintsa ba shima a daren haka ya kwana, ya la'anci shedan da son xuciya yafi cikin carbi. Wai shin meyasa ma yayi haka? Meye lefin sakeena don ta nuna tana sonsa? Meya hanashi nuna mata bai gane nufinta ba daga haka harta haqura ta kyaleshi wane tsautsayin ne ya kaishi yunqurin bata mata rayuwa? Gashi yanxu yayi biyu babu uku babu ko daya. Shi baisamu abunda ya nema ba a gurinta sannan kuma ya xubar da mutuncinsa a idon yarinyar abu na qarshe mafi muni shine marin da sakeena tayi masa yarinya qarama saar autarsu tai masa marin da rabonda ko iyayensa suyi masa irinsa shekaru ashirin baya. Amma fa duk munin marin da sakeena tai masa be masa ciwo ba kamar baqar adduar datayi masa na Allah ya kawo mai irin halinsa ya kwatanta abunda yayi mata akan qannensa. Wannan addua ta baqanta masa kwarai da gaske, daya auna saiya kwatanta yadda sakeena taji da kuma yadda yakeji a halin yanxu. Shifa kawai addua tai masa amma abun ya tsaye masa arai ina ga ita da yayi yunqurin batawa? Ya rasa yadda zaisa kansa a wannan dare, tausayin sakeena ya shigeshi karo na farko a rayuwarsa. Ya dunga juyi yana lalubar hanyar da xai gyara kuskurensa da kuma wanke kansa a gurin sakeena, da kyar daga qarshe ya yanke shawarar bin hanyar da yabi wajen nuna mata soyayyar qarya ita xai kuma bi ya gyara kuskurensa amma fa sai yayi amfani da hikima da kuma iliminsa. Wannan shine tunanin Nuraddeen a wannan dare.




A memakon ta bari damuwar abunda Nura yayi mata ta dameta saita maida hankali akan karatun jarrabawar da suke kain da nain domin ta gane kamar yadda Baba yake yawan fada mata bata da gatan da yafi na ilimi. Ta dauki tsafta ta riqeta hannu bibbiyu don ta gane tana daga cikin dalilan da suke sa a raina ajinta kuma dama can ita ba qaxama bace aikin gidan Anty ne ya maidata qaxamar qarfi da yaji. 10k din da Barrister ya bata da ita tai amfani gurin siyan kayan candy, taisai ankon material din da sukai ta bada kudin photo album tasai mayafi da sauran tarkacen inner wears. Baba ya basu 2k kowa ita da Amina yace suyi haquri bashi da kudi. Taji dadin kudin Baba taje ta siyo turaren da take masifar so "lailatus sahara" ta sai yan kayan kwalliya masu sauqin kudi ta ajiye yan canjin a gurinta.




Kasancewar wasu jarrabawa daya zasuyi wato WAEC kawai baxasu dawo NECO ba kamar su Amina, shiyasa suka shirya fatin candy ranar da xa ayi jarrabawar qarshe ta WAEC don wasu daga ranar anrabu kenan.




Ana gobe jarrabawar taje qunshinta, aka rangada mata baqi da ja aka kuma yimata kitsonta qanana ta fito shar. Ta nufo gida ana daf da magrib tana tafe tana kuma kallon qunshin hannunta wanda ita kanta ya burgeta. Tana shigowa soron sukai kacibis da Deni wanda da yana xaune a kofar gida amma hangota da yayi yasa ya tashi ya koma soro don tararta. Kuma dama ya dade yanaso yayi magana da ita tun bayan faruwar abun amma ta toshe duk wata dama ta yin hakan.





Ya tare gabanta yace "Sakeena dan Allah ki saurarani," ya miqo mata leda yana duban qunshin hannunta yace "gashi nima tawa gudummawar ce ta candy ayi haquri kyautar talaka babu yawa" ta galla masa wata uwar harara kamar idonta xai fado tace "OH! Daka nemi amfani da son da nake maka ka batamun rayuwa bakai nasara ba shine ka biyo ta hanyar yimin kyauta? To ai kafi kowa sanin bani da buqata domin ni bamai matacciyar xuciya bace irinka da xan xauna sai anbani, kafi kowa sanin Sakeena macece me xafin nema" yayi saurin magantuwa da cewa "Sakeena ya kike daga murya haka? Kar ajiyomu aciki" ta qara volume tace "sai me in aji? Nace sai me in anji ka nemeni da zina naqi yarda" yayi saurin barin soron kafin ajisu a gida afito. Tayi tsaki ta shige ciki.



Iya ta dunga koda lallen sakeena da cewa "Masha Allah diyata dagayin kitso da lalle kinyi kyau balle kinyi kwalliya? Ai nasan babu ta biyunki, yau gaba daya sai kika komamun mahaifiyarki Aisha sak. Allah sarki Allah ya kyauta makwanci." Hajjo dake tatar gasara ta doka tsaki, Amina kuwa da baqin cikin kyan qunshin sakeena ya hanata magana ta kasa daurewa tace "to ke sakeena da xaki tafi wani gurin ayi miki cewa nai baxan miki ba? Ko inda kikaje fina iyawa akayi? Ga abu anayi a gida kintafi anmiki a wani gurin dan mugun hali, ai da kinbari na miki da kudinki sun huta" sakeena ta juya ta Kalli Amina a sheqe tace "ai nasan kinayi na tafi wani gurin domin bana buqatar da kyautar, mutum da kudinsa ai kinga sai abunda yakeso." Kafin Amina tai magana sakeena ta shige daki tabar Amina da bin sahunta da kallo kuma dama taso sakeena ta kawo kanta gurinra qunshi tai mata na wulaqanci ta bata mata kwalliyar candy. Iya kuwa dariya tayi duk da sakeena bata da magana amma akwai iya maida martani.



A ranar kwana tayi karatun jarrabawar gobe, sassafe ta tashi tayi wanka suka nufi makaranta. Dake ta karantu bata wani jima ba a jarrabawar ta gama ta fito, suna zaune da qawayensu aka gama paper din gaba daya na kusa suka tafi gida domin yin sallah da sako anko, na nesa kuma suka shiga maqotan makarantar.




Sakeena dai saida tayi bacci bayan dawowarta gida saboda jiya bata samu jiba. Lokacin data tashi harsu Amina sun tafi, tai wanka ta shirya tayi kwalliyarta simple daga foundation sai jamvaki da eye liner dan bata da qarfin idon xana jagira duk kuwa da tana da burin taga ta iya kwalliya. Tasa material din dinkin riga da skirt yayi mata das dai dai jikinta tai acuci ta kafa dauri Iya ta miqo mata sabbin dan kunne da sarqa da agogo tace "ungo saka" ta washe bakinta tace "Iya yaushe kika saimun?" iya tana tata dariyar tace "me ya mace ai a hankali yake tanadi kedai kawai saka saurauniyar kyau yau kam ni kaina uwarki kin burgeni" ta gama saka komai tahau takalminta me tudu sabo ta yafa sabon mayafi da jakarta swaga ta dubi kanta a madubi, gaskiya gyara yana da dadi kamar ba itaba fatar jikinta tayi kyau tun bayan rabuwa da aikin Anty fuskarta tayi qal haskenta ya qaru saboda amfani da man nevea, jan bakin data saka dark purple (anti daba) ya qara haska fuskarta, idonta kuwa yasa eyeliner da mascara ya qara fitowa. Ta fesa turarenta taiwa Iya sallama ta fito, Su Hajjo sukayo waje don ganin kalar kwalliyar sakeena. Suka sameta yadda basu taba xata ba. Hadixa tace "kai sakeena kinyi kyau wlh kamar ba keba" ta dakko wayarta a daki tace "bari inmiki photo" duk da basu cika dasawa ba bata kwale Hadixa ba ta tsaya ta dauketa photo wajen guda 10 a wayarta sannan tace "to jeki kar a gama raba take away bakyanan" taiwa Hadixa godiya ta fita.




Deni dake daki ya daga labule dan yaga wucewarta, dan yanxu sakeena tsoro take bashi. Ya shaqi qamshinta tunkan ta qaraso, ya qura mata ido har ta wuce tai waje, bai gaji da kallonta ba ya bita kofar gida yana kallonta harta bacewa ganinsa. Ya sauke ajiyar xuciya haka kawai saiya samu kansa cikin farin ciki wanda besan dalili ba. Ya koma daki yana naxarin maganar sakeena ta daxu inda ta kirashi da mai "matacciyar xuciya" duk da ransa ya baci da maganar amma kuma in anduba maganarta gaskiyace tsantsa. Tunda ya gama service yaxo ya xaune a gida yana jiran aiki kuma aikin yaqi samuwa sai dai ya xauna abashi abinci yaci kuma hajjo ta bashi kudin kashewa kamar mace? Ga dattijon ubansa da kullum qarfinsa qarewa yake yana buqatar temako shi da yake babba a gida ya xaune wai shi graduate yafi qarfin Sana'a sai aikin gwamnatin da babu ranar samu (kuskuren da matasa ke tafkawa yanxu) ba dole suma qannansa su koyi xaman banxa ba xaman mutuwar xuciya? Tabbas ya xama dole ya tashi ya yaqi xaman mutuwar xuciyar da yake ya nemi Sana'a kowace irice koya samu ya daina amsa sunan me matacciyar zuciyar da sakeena ta kirashi.




Acan makaranta partyn candy ya kankama kafin sakeena taje, Amina tayi mamakin ganin sakeena aka dunga yaba kyan da tayi gurin qawayensu suka dunga photuna da ita a ciki kuwa harda qawayen Amina da Aminan wadanda basa kulata ada, yaudai sungane ashe sakeenar itama ba baya bace wajen kyau da kwalliya. Su Amina anje gidan kwalliya sunsha make up, anyi kitson gashin kanti anyi dinkin bayyana tsaraici ga kuma bleaching da akayi duk dan qarawa kwalliyar candy armashi. Amma sai sukaga sakeena da batai irin wannan haukan da sukaiba da kuma bayyana tsaraici sai ta fisu kyau, da kuma burgewa. Ashe dai kwalliyar hauka da baiyana tsaraici ba shine kyan kwalliya ba.





Sunyi party lafiya anraba snacks da lemo an gama an watse lfy ansha hutuna anrabu ana neman yafiyar juna dan wasu sai dai ku hadu a qiyama. Allahu Akbar dama rayuwar kenan (Allah ya jiqan ummana, Allah ya haska kabarinta ya saka kabarinta ya xama raudhul jannah ita da sauran Al ummar musulmi Aminnnn πŸ˜₯)

***** **** ****** *****



Xaman gida ya biyo baya bayan kammala jarrabawar WAEC kafin NECO kuma duk abunda ke hannunsu dashi sukayi amfani wajen kammala makaranta. A dan tsakanin sakeena ta fahimci mahimmancin aikin Anty a wajenta domin koba komai tanaci ta qoshi harma wani ya samu yanxu ma tanaci ta koshi kuma tsafta ta xauna mata amma fa dole ba kamar a gidan Anty ba wacce sakeena kejin su Hadixa na gulmarta wai Barrister yayi mata kishiya yarinya qarama irinsu Amina yan gigin candy kuma ya hadasu ya gwamuxasu a gida daya kullum Anty tana yawan kai qarar Barrister da amaryarsa gurin uwar mijinsu. Sakeena tai mamaki wato Barrister matakin daya dauka akan Anty kenan? Iya kuwa hamdala ta dungayi tana cewa haqqin sakeena ne ya fara tambayar Anty.



Da xaman gida ya ishi sakeena ga kuma babu saita shawarci Iya ko xata bata dama taje wata private skul da aka bude a unguwar neman koyarwa koda ta yan nursery ce? Iya tayi nazari kafin ta kalli sakeena tace "sakeenatu kuma xaki iya koyawa yaran abunda ake buqata?" sakeena tayi dariya tace "in shaa Allahu xan iya koda yan primary aka bani, ai yanxu da da ba daya bane Iya na sami ilimi dai dai gwargwado babu abunda xance muku sai dai ince Allah ya saka muku da alkhairi" Iya tace "to Masha Allah, ai baxan hanaki nema ba tunda Allah yayiki haziqa me xuciyar neman nakai, yau xan miki adduar sa a gobe kuma in Allah ya tashemu saiki je" Sakeena tace "yawwa Iya Allah ya barmu tare"




washegari sakeena ta nufi makarantar da qarfin gwiwar Iya bayan ta sambada mata adduoi. Taje ta samu shugabar makarantar mace me kirkin gaske a haife xata haifi fiye da sakeena, ta karbeta hannu bibbiyu sakeena ta sheda mata abunda ya kawota cikin kwantar da kai. Matar ta nemi sanin matakin karatunta ta fada mata tayi jarrabawar kammala secondary. Matar ta bata haquri cikin tausasawa ta fada mata sunfi buqatar masu shedar karatun NCE da kuma Degree. Sakeena gwiwarta tai sanyi kwarai tayi godiya ta tashi xata tafi. Matar ta kuma kallonta ta karanta yanayin sakeena a fuskarta a matsayinta na uwa baxataso tata yar taje neman aiki aqi bata ba, amma gurbin aikin da suke dashi dakyar in sakeena taso shi amma bari ta fada mata da hannau gara mannau.



Har sakeena taxo fita ta tsaidata tace "zo diyata" sakeena ta dawo ta tsuguna ta sunkuyar da kanta. Tace "inkinason wani aikin saina baki, amma fa na lura da yara in zasu shiga bandaki ki rakasu in sunyi tsuguno kiyi musu tsarki." sakeena ta washe baki tace "wlh xanyi Hajiya aini dinma banfi qarfin hakan ba nagode Allah yasaka da alkhairi in shaa Allahu gobe xan fara xuwa aiki" tana dariya tace "ai baki tambayi nawa xan dunga baki ba, amma tunda baki raina aikin dana baki ba xan dunga biyanki 5000 duk wata" sakeena ta washe baki ta dunga godiya ta tafi bisa alqawarin gobe qarfe 8 xata fito aiki.




Koda taje gida bata bayyanawa Iya kalar aikin data samu ba kawai tace mata andauketa aikin gobe xata fara xuwa da albashi dubu biyar duk wata domin tasan Iya bazataji dadin cewa aikin tsarki xata dunga yiba duba da yadda ta tsani aikin gidan Bahijja. Ta qudure a ranta xata qoqarta matuqa ta tattala abunda xa a bata domin ta tunkari matsalarta ta ido wacce tana samun sauqi in shaa Allahu xata dora akan karatunta xuwa jami a.




Kamar yadda ta alqawaranta washegari ta fara xuwa aiki kuma Hajiya taji dadin ganinta sosai yarinyar ta burgeta bata raina neman nakanta ba. Data fara aikin ma sai taga aikin ma ba wani bane domin mafi yawan yaran fitsari kawai take rakasu in sun gama tai musu tsarki ta rakasu aji, sai ta koma tai xamanta dai dai kune sukeyin tsuguno. Shikenan aikin nata sai tajita kamar mai xaman banxa bame aiki ba kodan ta saba da wahalar gidan Anty ne? 12:30 pm ake tashi daganan tai gida sai kuma gobe.




A kwananta na hudu da fara aiki ne tana shigowa gida daga gurin aikin su Fiddausi suka kwashe da dariya kuma abin takaici har Hajjo. Sakeena ta waiwaya fuskarta na alamar tambayar me sukewa dariya? Amina tsagera ta fara magana "waini me ilimi na tafi makaranta neman aikin koyarwa, memakon aikin koyarwa sai na samu aikin tsarkin kashin yara" ta fada cike da izgili su Hadixa suka kuma saka dariya. Iya dake karya taliya a ruwan dake kan murhu ta tsaya kamar ansaka mata pause ta dunga bin sakeena da kallon tuhuma. Sakeena ta qanqance ido cike da bacin rai ta kallesu tayi tsaki tace "Alhamdulillah amma dai nafi mai xaman banxa xuciya a mace an jibge ana xaman jiran me kudi" ta juya ta shige daki. Hajjo ta kalli yayanta tace "ga dukkan alamu yarinyarnan ta riqa ta goge kaushi anci jar miya, wato harku takewa gorin aure" fiddausi tayi kwafa tace "hmm kedai bari Hajjo ni kaina abun ya ban mamaki ni banxaci ta iya rashin kunyq haka ba" Hadixa kuma tace "wai harmu takewa gorin aure shegiya sekace ita tayi auren?"



Acan dakin Iya kuma sakeena tunani take a ina sukaji labarin ta samu aikin makaranta har bata samu koyarwa ba sai tsarki wa yara? A iya saninta dai Baba ne kadai Iya ta fadawa dan bata boye masa komai to a ina su Amina suka sani?





Iya ta shigo dakin ta fallarawa sakeena harara kafin ta rufeta da fadan cewa batasan bata dauketa uwa ba sai yau tunda har ta boye mata kalar aikin data samu sai a tsakar gida taji. Sakeena a rude tahau bawa Iya haqura tace " Iya inkinyi fushi dani gurinwa xanje kenan? Ki tuna bani da uwa bani da uba bani da dan uwa ke daya kika ragemun wlh saboda karki hanani aikin shiyasa na boye miki naga bakyason inyi aikin wahala" Iya daga fada ta koma lallashi suka shirya da yar diyarta sakeena πŸ˜„ Daga haka sakeena tacigaba da aikinta sannan kuma tana tafiya da littafanta tana bitar karatun jarrabawar NECO.




A bangaren Deni kuwa tun washegarin ranar da Sakeena tai candy ya samu Baba da neman shawararsa xai fara Sana'a tunda aiki be samu ba. Baba yayi murna da wannan shawara ta Deni, ya kalleshi yana murmushi yace "Nuraddeen kodai wata kakeso tace sai ka nemi Sana'a xata aure ka?" Deni ya kalleshi cikin mamaki yace "Baba in mutum nasan mace sai yayi duk abunda take buqata?" Baba yana dariya yace "kwarai kuwa da alama wannan suruka tawa jajirtacciya ce tunda ta zaburar dakai ixuwa neman nakai" Baba yacigaba da magana "tunda da kanka ka nemi hakan naji dadi kwarai kuma xan kaika gurin alhajin da nakewa aikin driving yana da shaguna akwari ya baka jiran shago kafin Allah ya baka naka jarin ko ya baka aiki" Da haka Deni ya samu jiran shago a gurin Alhaji wanda in sunyi ciniki ake sallamarsa da 500 kullum in kuma babu ciniki a bashi 300 kullum amma aciki Deni kanyi kudin motar xuwa kwari daga gwale da kuma kudin motar komawa dan haka abunda yake samu ya riqe bashi da yawa amma duk da haka yana jin dadin aikinsa kuma yana alfahari da hakan. Ranar da aka fara bashi 500 a matsayin abunda ya nema da guminsa har kuka yayi saboda farin ciki kuma ya jinjinawa sakeena bisa tsayawarta akan nema da guminta tun tana qaramarta. Amma a bangare guda yayi iya qoqarinsa su kebe da sakeena ya bata haquri ya wanke kansa amma taqi kuma ga mamakinsa abun ya tsaye masa arai wanda ya rasa dalilin hakan. Su Amina da Hajjo kuwa duk inda suka xauna sai kaji suna ai Deni yana kasuwanci a kwari kai kace shagon nasane. Alhajin da Deni yakewa aiki wanda ada baiso aikin Deni ba don bashi da yadda amma a hankali saiya lura yaron yana da amana sannan gashi da ilimi wanda hakan tasa idan Alhaji yayi baqin yan china zai sai kaya sai Deni yayi masa tafinta saboda shi bai iya turanci ba. Duk sanda akai irin wannan baqi yakan sallami Deni da kudi mai tsoka kamar 2000 shi kuma ana bashi xai kashesu yasai abunda xa a amfana a gida Baba najin dadin hakan dan Deni ya fara nuna yasan ciwon kansa. A gefe guda kuma duk sanda Deni yayi irin wannan bajinta xakaji Hajjo na mitar cewa ya dunga tanadi domin duk wanda yaga ya xama me kudi saida ya tattala dan abunda yake samu amma shi daya samu kudi saiya hau gwaninta dasu ga wadanda basusan yadda yayi ya samu ba. shi kuma kan yawan fada mata na neman albarka yakeyi dukiyar da ake arxiqi da ita daban Allah yake kawota baisan cewa ita Hajjo kyashin Iya da sakeena suna na morar duk abunda ya kawo take ba.




Hajia ☺
[7/31, 2:08 PM] Reine Ghana: πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€MUQADDARI NEπŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€2018πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€



8⃣

RAHMATULLAH (Hajia)


Koda sakeena ta fara jarrabawa sai ya xamana ba kullum take xuwa gurin aiki ba, amma dai kafin hakan ta fadawa Hajiya inda tace bakomi duk randa xatai exam ta dauke mata aikin ranar. Jarrabawar taxo mata da sauki saboda tayi karatun waec.




A wata ranar laraba ta dawo daga skul kimanin 6:00 na yamma ta shigo soron gidan ta gaji liqis don English sukai tun safe take makaranta sai yanxu suka kammala ga uwar yunwa na sakadarta sannan ga idonta dishi dishi take gani saboda tsabar kallon farar takadda da tayinin yi.



Deni shima da dawowarsa kenan daga kasuwa ya tari gabanta cikin harzuqa yace "wlh babu inda zakije yau sakeena sai kin tsaya kin saurareni domin nagaji da halin ko in kula da kike gwadamun." ta nemi hanyar wucewa ta gefensa ya tare, ta kalleshi ranta a bace tace "rufa maka asirin da nayi shine ya baka damar kuma attempting dina?" ya marairaice yace "Sakeena dan Allah kiyi haquri ki saurareni, abunda nayi miki bawai da gaske nayi shine har cikin xuciyata ba kawai gwadaki nakeyi amma a lokacin da kin bani dama da kinga qarshen film din"




Sakeena ta saki baki tana sauraran wani kalar rainin hankali daga Deni, sai da yagama qarairayinsa tas tana sauraransa sannan tayi tafi tana dariyar rainin hankali ta kalleshi ido cikin ido ta fara magana"Da kyau! A nace da kyau Nuraddeen LawanπŸ‘ŒπŸΎ. Kayi qoqarin kwarai wajen shirya wannan wasan kwaikwayon amma sai dai kayi kuskuren samun masu sauraro domin sakeenar da ka dauka ada can baya har kuke kiranta da akuya yanxu ba itace a gabanka ba. Ka rasa da abunda xaka gwadani sai da zina? Meyasa baka gwadani da sata ba? Meyasa baka gwadani da addini ba? Meyasa baka gwadani da tsafta ba? Ko tsoron Allah? OH! Sai da zina? Saboda inna baka kaina shikenan sai kai amfani da hakan daganan kuma kaga sai na wakilci ragowar mata duk inda ka xauna hira sai kace ai duk mata yan iskane ko? Ko kuma inkaje gurin wata itama saika kuma gwada ta? Wannan kalma ta GWAJI da ita samari irinka masu tsatsar xuciya suke amfani suna bata rayuwar yayan mutane. OK na yadda ka gwadani, kaima Allah ya kawo wanda xaiwa yar cikinka abunda kaimun da sunan gwaji" tana gama fadar haka ta kewayeshi ta wuce ta barshi cikin wani irin Al ajabi.



A wannan dare kamar wancan rana Deni be rintsa ba, lallai ya yadda da ake cewa yayan qauye hikima ce dasu da basira yau sakeena da ya raina wayonta da iliminta ta shayar dashi mamaki,

Please Login or Register in order to submit comment