Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qaunata kuma soyayyar da kikemun gaskiya ce to karki qara yunqurin hanani wannan abun da nake miki, domin shine qarshen matakin soyayya sannan indai kika bari nayi miki to nima qara sanki xanyi fiye da yadda kike sona" cikin kuka tace "to" shikuma yaci gaba da abunda yake, yayin da sakeena tayi matuqa wajen gayyato dauriya danta nunawa Deni tana sonsa.



Wasan yacigaba Deni ya luguiguita sakeena matuqa kafin daga baya ya nemi maidata cikakkiyar mace, anan labari yasha banban domin sakeena taji wuyar data xarce tunaninta ai saita saki murya ta dunga kunxuma ihu iya qarfinta fadi take "ni ka kyaleni, bana sonka wlh na dena sonka, wayyo Iya yaya Nura xai kasheni" shima Deni xuwa wannan lokaci baya hayyacinsa domin shima nasa surutan yake cikin sambatu da gushewar hankali irin na novice. Inbadan ruwan saman da yaketa kwararawa ba da har maqota sai sun hana bacci da ihunsu bama mutan gidan ba.



Lokacin nutsuwa taxo masa sakeena ta gamayin laushi tiqis, ya kwanta a gefenta yana sharce gumin daya tsatstsafo masa a goshi duk kuwa da sanyin da garin ya dauka. ya dakko fitila ya kunna ya haska fuskarta, ya tarar da ita ido bude jajur dashi tana kallon silin. ganin ya kunna fitila ta lalubi dankwalin kayanta da Deni ya watsar kan katifa ta rufe jikinta. Ya kai bakinsa kan kunnenta yana shafa gashin kanta daya hargitse yace "me kuma xaki rufemun Baby? Ai mun xama abu guda yanxu, babu kunya tsakaninmu" batai masa magana ba shima bai kuma cewa komai ba ya kwantarta qirjinsa yana shafa bayanta tare da kalaman lallashi da godia. Tayi bacci a haka shi kuwa tunani yake, yasamu sakeena yadda yayi zato a matsayin macen data kare mutuncinta har xuwa gidan mijinta kuma dama shi be taba zaton mata shashanci ba. Ya kuma fadawa tunanin abokansa wadanda suke yawan fada masa cewar in mutum nason more dadin aure to ya auri matashiya wato yar shekaru 20 xuwa sama domin a fadarsu auren yar shekaru qasa da ashirin duk bata lokaci ne don basa iyawa namiji komai sai rakin tsiya amma matashiya duk abunda kakeso xata maka a harkar soyayya. To shikam yau ya karyata duk kuwa da cewa shima a nasa raayin yafison matashiiyar ba yarinya ba kamar sakeena, yau dai sakeena qanqanuwar yarinyar yar 17-18 wacce ya kusa ninka shekarunta ta shayar dashi wata irin xuma kuma ta kawar masa da kwayinsa akan ya mace na tsawon shekaru. Ya katse tunaninsa ya tashi daya tuna a gidan haya suke dole ya temakawa sakeena tun a cikin dare basai da safe ba komai a idon mutane. A hankali ya kwantarta kan filo ya xira wando ya fita falo, yana kici kicin kunna risho abun Allah aka kawo wuta saboda ruwan ya tsagaita yayi hamdala ya dakko heater ya dakko bokitin ruwan saman daya tara ya juna, ya koma ya kwanta kusa da sakeena. Kimanin baccin awa daya ya sureshi kafin ya farka a firgice yaje ya duba ruwan harya tafasa. ya fita yakai bandaki yaji dadi daya samu bandakin fes kamar bana hadaka ba, saida ya gama hada komai yakai toilet sannan yaxo ya tashi sakeena ta farka tana kuka ya daura mata xani amma ta kasa tafiya dan haka ya dauketa.



Ta tsuguna domin yin fitsari amma ta kasa sai wani azabar radadi cikin kuka tace "ya Deni na kasa fitsari kuma inaji" ya dafata yace "daure kiyi Baby kinji Allah yayi miki albarka" dakyar sakeena tai wani fitsari me azabar xafi hade da jini bayan Deni ya temaka mata ya riqeta kafin tayi. Haka ya dunga saka sakeena cikin ruwan dumi da gishiri kafin daga baya suyi wankan tsarki su fito, lokacin xaxxabi ya rufeta sosai ya bata paracetamol tasha ya gyara gurin da suka kwanta sannan suka kuma komawa suka kwanta yana rungume da ita.





Yau kam zaqin amarci yasa Deni makara, basuyi sallah ba sai da gari ya waye sosai suka tashi. ya shigo da ruwan katuwar jarkar daya tara musu cikin daki, ya debi wani a bokiti ya jona musu ruwan wanka. sakeena nakan sallaya tana kallonsa. ya tashi ya share dakin fes lokacin ruwan wankan ya dahu ya kaimata toilet yazo ya tsuguna yace "ranki ya dade nakai miki ruwan wanka taso kije kiyi kinji Baby" tai dauriya kwarai ta cije ta daura xani ta saka hijab ta fita tsakar gida. Ta tarar da matar gidan tana aikin sharce tsakar gidan ta sunkuya ta gaisheta, itama ta amsa da fara a tana tambayarta kwanon baqunta. Ta shige tayi wankanta tsaf ta fito tana tafe tana ware qafa saboda azaba. Ta samu ya fito mata da kaya ta shirya shi kuma ya tafi nasa wankan. yaji dadi lokacin daya fito ya samu tayi kwalliya tasha jambaki tana juye ruwan xafin daya jona cikin tea flask. yayi saurin karbarta yace "koma ki xauna sarauniyata ki jira na ida hada mana abincin" ta koma ta xauna kamar yadda yace, ya shige daki few minutes ya fito shima ya shirya yana qamshi. ya hado musu kayan breakfast tea da bread sai yan kayan shayi na sachet, ta duqar dakai ta gaisheshi ya amsa yana cire mayafin data lulluba yace "daga yau na haramta miki xama da mayafi a daki sai inxaki fita tsakar gida. Ya hada musu tea suka sha yaje ya wanke cups din ya dawo.



Yaxo ya dora sakeena akan cinyarsa suka qule uwar daki, tun tana dari dari harta sake suna hira yana qara fada mata yadda yake qaunarta. Bai fita ba ko kofar gida yace mata anbashi hutun 7 days a kasuwa. Da lokacin dora abincin rana yayi da kansa ya siyo kayan miya ya gyara xai fita kai markade matar gidan tace ya bawa danta Amir yakai masa duk aiken da yake buqata ma ya aiki Amir din. Yayi godiya ya bashi




Da kansa ya shirya musu miya da ragowar kazar jiya da sukaci ya dafa musu taliya ita sukaci kuma tayi dadi kamar ba girkin namiji ba koda yake ai yayi bautar qasa a wata jahar dan ya iya girki ba abun mamaki bane.




Da dadadre ya kuma sakata wanka shima yayi suka kwanta gabanta na faduwa kar akuma irin ta jiya amma kuma saiya rungumeta yana mata hira har ta Saki jiki yayi wasanninsa da ita sukai bacci.

**** ***** ***** ***** ****



A iya kwanakin hutun Deni 1 wk sunyi wata rayuwa me dadi shida sakeena, baya xuwa ko ina sai masallaci yayin da suke yini tare suyi wasanninsu suyi hirar soyayya ko kuma ya sa musu kallo a wayarsa. Tuntana dari dari dashi harta sake ganin be kuma neman komai a gurinta ba. Bata aikin komai sai wanka da sallah komai shike mata har girki. Ranar daya koma kasuwa ranar ta fara girki, sun rabu cikin shauqin juna ta yini a salube cikin kewa gashi yace karta fito tsakar gida indai ba aiki xatai ba. Ta gama girkinta kafin ya dawo tayi wanka tayi kwalliya, yaji dadi sosai lokacin daya dawo yaga har ruwan wanka takai masa. Yayi wnka yaje sallah suka xauna sukaci cous cous din data dafa musu sukasha lemon xaqin daya shigo dashi. suka kwanta bayan sallar isha suna hira a lokacin Deni ya kuma neman haqqinsa na aure a karo na biyu amma kash ya tarar da sakeena bata da tsarki, yana dubanta yace "yaushe yaxo kenan?" cikin kunya tace "daxu da azahar" ya koma ya kwanta yana cixon lebe. Ya dakko wayarsa ya kunna musu film din Dadin kowa yace "so nake insamu yan kudi ayiwa su Baba girki muje mu gaishesu Hajjo kullum saita kirani tana tambayar lfy muke wai so take ta ganmu. sakeena tanaji anyi xancen gida cikin sauri tace "ya Deni inada 1000 da Iya ta bani naxo da ita basai ayi girkin da itaba muje" yana kallonta yace "Allah ya sawaqe ban bakiba in karba sakeena ki riqe abarki ki dunga kashewa tunda bani da halin baki kudin kashewa akwai shirin da nake ina gamawa xamuje"




Kamar yadda ya fada ranar da suka cika kwana 14 wato 2 wks kenan saigashi da kaxarsa da kayan miya da safe. Sakeena ta karba cikin murna da axama ya tayata sukai stew ta debi taliya biyu cikin kayan abincinsu ta dafa suka cika sabbin food warmers din Sakeena da taliya da miya suka shirya sunyi kyau sosai ya riqe daya ta riqe daya suka hau napep suka nufi gwale gida.




Sunyi saar tarar da Baba a gida domin ga kekensa nan a soro. Sakeena ta rigashi shiga saboda shi ya tsaya biyan dan sahu. Amina ce ta fara ganin sakeena tayi shar ta kuma haske a 2wks kawai baqin ciki ya kamata tace "kinacan shar dake kinajin dadi Baba ya kwashe kudinsa yayi miki aure mu kuma an barmu da yunwa." sakeena bata kulata ba ta nufi dakin Iya ta kwada sallama kuma lokacinne Deni ya shigo Iya ta qanqame sakeena tana farin cikin ganinta yayin da acan tsakar gida Hajjo ta rungume Deni anata murnar ganinsa aka hadu duk a dakin Baba anata murna da gaisawa Baba bakinsa yaqi rufuwa ganinsu kuma da gani lfy suke xaune dan daga sakeenar har Denin sun canja. Sakeena ta ajiye flasks din a gaban Baba tace "Gashi Baba ya Deni yasa akai muku" Baba ya dunga godiya suka fito sakeena tabi Hajjo har dakinta ta kuma gaisheta, Hajjo tana kallon sakeena a sace a xuciyarta tana fata Allah yasa Deni bai dirkawa sakeena cikiba ganin irin wannan kyau da tayi, inko hakane ta makara domin shiyasa ta dunga zabgawa Deni waya dan suxo ta aiwatar da plan dinta kan sakeena.




Sakeena ta miqe xata koma dakin Iya Hajjo tabita da kallo tace "ina xaki sakeena? Aini yanxu na xama uwa a gareki ya wuce kixo dakina ki tafi, kiyi sakewarki da nan dakin da dakin Iya duk daya ne." Sakeena dai ta xauna a takure saboda kallon qurullar da Hajjo ke mata ta miqe qafa Hajjo ta qurawa qafar ido ganin tayi fari tas tayi luwai luwai, can dai dataga ta kasa gane komai saita kira sakeena uwar dakinta ta xaunar da sakeena cikin hikima da nuna kulawa tace "Sakeena dama a matsayina na uwa a gareku ke da Deni naga ya kamata in tunasar daku abunda quruciya ta hanaku tunawa. Ni a ganina be kamata yanxu ku xauna haka ba babu tsarin iyali duba da yadda akai aurenku kuma ga halin rashi da kuke ciki ga Deni babu halin riqe mata ma balle kuma Da shine nace mai xai hana kiyi tsarin iyali koda na shekara daya ne mugani xuwa lokacin ko abubuwa sun warware saiku fara haihuwar" Sakeena tai dan gajeren tunani irin nata na quruciya taga tabbas maganar Hajjo gaskiyace yanxu in sun haihu ya xasuyi da Dan? Ta kalli Hajjo tace "Eh gaskiya ne Hajjo xan fadawa ya Deni inyaso ya kaini asibiti aimun" Hajjo tayi mata daquwa tace "gidanku da inaso Deni yaji ai da shi xan fadawa bakeba, bakomi ake fadawa namiji ba ni yanxu uwa nake gareki tunda kin amince xan tura Hadixa gurin malamar asibitin qawarta ce tai mata bayani inyaso in anjima saita rakaki kuma sannan wannan maganar ta tsaya dagani saike karki fadawa waccan uwartaki kinji ko yata" sakeena tace "to Hajjo babu wanda xan fadawa" ta kuma kallon sakeena tace "anya ma kuwa sakeena wannan kyau da kikai babu ciki jikinki? yaushe rabonki da al ada?" cikin kunya tace "yau nagama daxu nai wanka" Hajjo ta sauke boyayyar ajiyar xuciya. Tana fita Hajjo ta kira Hadixa sukai qulle qullansu suka gama.




Iya ta dubi sakeena bayan ta dawo dakin tace "xaman me kikai a dakin Hajjo harda qulewa uwar daka? cikin basarwa sakeena tace "bakomi Iya" Iya ta kuma kallonta tace "kidaiyi hankali da ita dan wlh bata qaunarki aurenku da danta ma dan anfi qarfinta ne" ta amsa da "to"



Suka dunga hira da iya cikin farin ciki har Iya ta yi mata kitso a tsefaffan kanta. Iya ta kuma duban sakeena a karo na barkatai tace "sakeena yace ko ba shafe shafen nan naku na yaran xamani kika fara ba naga kinyi wani fau dake" sakeena tana dariya tace "wlh Iya cocoa butter muke shafawa ni da ya Deni kawai xaman guri daya ne." Iya tace "lallai kuwa xaman ya amsheki kinyi tas dake" Haka sakeena ta yini dakin iya suna hira yayin da Deni ya wuni gurin abokansa na unguwa suna hira, Baba kuwa duk abunda ya fita ya gani saiya siyo ya kawowa sakeena duk saida ya qarar da yan kudin aljihunsa. Su Hadixa kamar su suke sakeena.



Can bayan laasar Hajjo ta kwallah kiran "sakeena fito kuje Hadixa ta rakaki gaida qawata sabuwa tanata zancenku nace inkunxo na turaki ku gaisa" sakeena ta gyara fuskarta ta fito suka tafi da Hadixa Hajjo ta bisu soro tace cikin rada "ke bafa gidan sabuwa xaku ba gurin malamar asibitin xaku" sakeena cikin rashin damuwa tace "to Hajjo" ita harta manta xancen ma.



Sukaje gidan matar ta dubi Hadixa bayan sun gama gaisawa tace "duk ukun xa ayi at the same time? Hakan fa yana bada matsala" Hadixa tace "to wai ba angama magana dake ba? Kuma inba ai ba yanxu ina xa a dunga ganinta duk wata 3 ana mata kawai ki mata" matar ta cika sirinji da allurai 3 dam ta dannawa sakeena. Ita kuma xuciyarta daya bata kawo komai ba, allurar da akeyinta duk bayan wata uku 1 Hajjo tasa anwa yar mutane ta wata 9 lokaci daya dan tsabar rashin imani da dalili mara maana.




Suka dawo gida sakeena ta koma dakin iya bayan Hajjo ta jaddada mata inta fadawa wani wannan maganar wlh saitasa Deni ya saketa.



Haka suka gama yininsu bayan sallar isha sukaci tuwo sukai wanka, Iya ta hada musu kayan miya irin wanda take siyarwa Hajjo kuma ta basu garin tuwo da gasara cikin jug. Su Amina suka rakasu har bakin titi sukahau napep suka tafi.




Suna xuwa gida sukai shirin bacci, a ranar dai Deni ya

[7/31, 2:13 PM] Reine Ghana: πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€MUQADDARI NEπŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€2018πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€



1⃣1⃣

RAHMATULLAH (Hajia)



Wayewar garin lahadi suka tashi da baquntar matar daya dakin gidan dake rufe sundawo daga tafiyar da sukayi me suna Mariya. Da fitar Deni sakeena ta hado yan kwanikan da suka karya ta fito tsakar gida sanye da hijabi kamar yadda Deni yayi mata umarni. Tana aikinta suna hira da umman amir wato daya matar kamar yadda suke kiranta. Mariya tai but ta fito daga dakinta tana mutstsuke ido alama daga bacci ta tashi ta dubi sakeena kallo na qurullah sannan ta maida kallon ga umman Amir tace "wannan itace amaryar gidan namu?" Umman amir ta bata amsa da "eh itace sunanta sakeena mijinta kuma Nura" ta dubi sakeena tace "sannu sakeena, amma kuma meye na fitowa da hijabi ai duk mazajenmu sun fita" sakeena tayi dariya tace "eh nasani umarnin mijinane hakan" Mariya ta tabe baki, ta koma ta debo nata aikin ta fara tanayi tanawa sakeena hira don ta shige mata amma saitaga sakeena bata damu da ita ba.



Tana gama aikinta ta tashi ta koma daki. Inda ta manta cokali a gurin, da sauri mariya ta dauka ta nufi dakin sakeena don taga meye aciki, tayi sa a sakeena na uwar daki a kwance dan haka babu neman izini ta banka uwar dakin tana qarewa komai kallo tace "sakeena ga cokali kin manta" ta karba tace "nagode amma inkinxo ki dunga sallama ko ki tsaya iya falo" ta tabe baki tace "kinji yarinya daga gwaninta?" ta fice fuu bayan ta gama ganin abunda takeson gani.



Yauma kamar ragowar kwanakin kafin ya dawo ta gama girkinta tuwon masarar da Hajjo ta basu jiya da miyar kuka tayi wanka tayi kwalliya ras. Ta kintaci lokacin dawowarsa taje ta wanke toilet wanda dawowar Mariya yasa ya fara daukan qazanta. Tana fitowa daga bandakin dauke da tsintsiya a hannu saiga sallamarsa. Ta cillar da tsintsiyar ta tafi da gudu ta daneshi, shima ya rungumeta yasa hannu ya dauketa sukai daki yayin da Mariya ke leqensu ta tagar dakinta.



Ya direta a tsakar dakin yana kallon kwalliyarta yace "kinyi kyau sosai Baby, amma meyasa bakisa hijabi na sameki a tsakar gida haka gashi kinyi kwalliya?" Ta dan marairaice tace "kayi haquri naga xan shiga bandaki ne kuma ba kowane namiji a gidan amma kayi haquri daga yau xan kiyaye" ya rungumeta yace "na haqura Baby, ki dunga kiyayewa kinji, inada tsananin kishi akanki" sukai murmushi tare yayi shirin wanka takai masa ruwa ya fito dan shiga, Mariya tai saurin fitowa qofar daki ta kafeshi da kallo. Ya shiga ya gama ya fito tana xaune dandamalin kofar daki, sakeena ta miqo masa ruwan alwala yanayi. Ya gama ya miqe ya farga da kallon da Mariya ke masa yayi saurin shigewa daki yana tsaki.




Bayan sallar isha sunci tuwonsu a kwano daya cikin soyayyar juna suka wanke baki bayan sun gama Deni ya dora sakeena kan cinyarsa suna kallon shirin dadin kowa sabon salo a wayarsa wanda aka haska jiya kuma dama duk sanda xasuyi kallo haka yake dora a cinyarsa sunayi yana mata wasannin soyayya. Bayan sun gama suka kwanta kamar jiya yauma haqqinsa ya nema ta kamo hannunsa tace "wai ya Deni dadin wannan abun kakeji ne?" yana lumshe ido yace "dadin baxai fadu da baki ba Baby" ta kada kai tace "to nikam banaso wlh da xafi kuma sam ni banjin dadinsa" ya toshe mata baki yace "shiiii ki daina fadar haka, malaiku xasu tsine miki kuma bana ce miki in kina bani qara sonki xanyi ba? To kawai ki dunga haquri xafin na dan lokaci ne xaki daina ji" tace "to" haka yayi amfani da wayonsa da kuma qarancin shekarun sakeena yasha budurinsa san ransa, ya kwantar da ita a qirjinsa bayan komai ya lafa yace "Sakeena" ta dago ta kalleshi dan a yan kwanakin nan be cika fadar sunanta ba sai dai yace Baby idonta taf bacci ga gajiyar daya saukar mata yanxu tace "naam ya Deni" ya sumbaci goshinta yace "tanxz, thank u very, kin inganta rayuwata kin temakeni kin kareni daga fadawa halaka kin rufamun asiri, inason aure sosai ina buqatarsa saboda shekaruna sun kai amma ina hango aure a matsayin wani babban lamari gareni wanda baxan yishi kwana kusa ba duba da yadda auren yayi tsada, sanin hakan yasa shedan ya kitsamun fadawa halaka Allah yasa kika bijirewa hakan sannnan kika rufan asiri a qarshe kikaiwa mahaifina biyayya ta hanyar karbar aurena hannu bibbiyu, duk da bani da komai kuma ban miki komai ba Nagode sakeena Allah ya bani ikon riqeki da gaskiya" ta amsa da "Amin ya Deni, amma ni da kai duk mun rufawa juna asiri ne, yanda kake talaka mara kudin aure haka nake yar talakawa wacce ba a da kudin aurar da ita kaga mun hadu munyiwa juna rufin asiri" yana shafa kanta yace "a a Baby ke xaki iya samun Mai kudi yace bai buqatar komai sai ke kodan kyanki da farar fata" ta toshe bakinsa tace "ni kuma kai nakeso bakomi ba" haka dai sukai bacci cikin sambatun soyayyar juna. Da safe ta dama musu koko da gasarar da Hajjo ta basu, ta dumama musu tuwon jiya suka karya dashi Deni yana ta santin cewa wai sakeena waya tsiro da yin dumame? Tace tana dariya gama ci na baka lbr πŸ˜„ shima yana dariya yace to gaskiya yayi basira, ta qara sautin dariyarta tace na fika sanin haka, ya kintse tasa dariyar yace ke bafa santi nike ba πŸ˜„





"Amma dai mijinki a bazawara ya aureki ko?" itace tambayar da Mariya ta fara taryar sakeena da ita lokacin data fito wanke wanke. Sakeena tai sakato tanabin Mariya da kallon mamaki, tayi murmushi tace "abunda yasa na tambayeki naga ba aimiki kayan daki bane, mu kuma a garinmu auren baxawara ne kawai akeyinsa babu gado" ran sakeena ya baci da wannan cin fuska na Mariya daga haduwa jiya ta watsawa mata harara tace "A bariki ya auroni ba a baxawara ba" Mariya taja baya tace "a a yi haquri daga tambaya? Kuma ma ai naga baku fito wankan tsarki ba da asuba shiyasa na kuma tabbatarwa baxawara ce ke, ai da budurwa ce kullum sai yayi saboda doki kinga ni lokacin da nake amarya salisu har da rana dawowa yake daga aiki yayi" kafin sakeena ta bata amsa umman Amir ta fito ta tsawatar musu saboda taji duk abunda suke.




Koda Amir ya dawo daga makaranta ummansa tace duk me aike ta kawo zai tafi cefane Mariya ta bayar sakeena kuwa batai niyyar girki ba sabida tana da ragowar dumame xataci da rana da daddare kuma xatai musu jellof din shinkafa da daddawa da barkono wadanda Iya ta bata kuma tayi hakanne don nemawa Deni sauqi. Mariya taxo har qofar dakinta tace "amarya naga baki bada kudin cefane ba?"sakeena cikin hargagi tace "ke ni inada komai na girki" ta kada kai ta fita, sakeena tai tsaki daga jiya xuwa yau kawai ta fara gundura da halin shishshigi da bin kwakwkwafi na Mariya. Abun mamaki tana gama girki wajen azahar sai gata da kwano shaqe da abinci ta kawowa sakeena har daki, a lokacin ita sakeena ma har ta gama cin tuwonta tana karatun novel. Ta ajiye kwanon tare da cewa "amarya gashi naga baki girki ba shine na kawo miki" ta miqe daga kwance ta dauki kwanon tare da danqar hannun Mariya duk kuwa da cewa xata bata ratar wajen shekaru 7. Ta kaita waje ta damgwarar mata da kwanon tace "gashi ni naci abinci bani da buqata kuma daga yau karki kuma shigarmun daki tunda nima bana shiga naki" bata jira amsar da xata bata ba ta koma daki.



Da daddare sunacin abinci da Deni take fada masa yadda sukai da Mariya, yace "da kyau Baby, kamar yadda kikai yau ban yarda ki karbi abincin kowa ba kuma kema ban yarda ki bawa kowa ba, su riqe nasu na arxiqi muma mu riqe namu na takauci"

**** ****** ***** ****** *



Watanni biyu sun shude da bikinsu kuma a lokacin ne rayuwa ta fara garasu, domin dan kayan abincin da suke dasu sun qare, gashi abunda Deni ke samowa a kasuwa be wani taka Kara ya karya ba a times kudin kan tafi ne a transport dinsa daga gida xuwa kasuwa. Sauqin abun ma Iya kan mata aiken dan kayan abinci da kayan miya a duk sanda Deni yaje amma duk da hakan suna dandana kudarsu kuma suna rayuwa irinta hannu baka hannu kwarya. Bata qara xuwa gida ba kamar yadda duk cikin yan uwan Deni babu wanda yazo inka dauke zahra kuma duk sanda sukai waya da Iya ta wayar Deni intai mata korafin rashin xuwanta Iya kance "to sakeena ai bamayi ta xuwa gidan yara ba da girmanmu tunda kuna xaune lfy shikenan" sau tari sukan kwana da yunwa ita da Deni in akai rashin dace ba ai ciniki a kasuwa ba wanda hakan kesa 300 din da aka bashi su tafi a mota ya dawo da 100 gida wacce ke tilasta musu cin awarar naira 100 ko garin kwaki su kwana haka ya tafi yabar sakeena da safe da neman abunda xataci kota yini da yunwa kafin ya dawo ya samo dan abunda xasuyi maleji.




A gefe guda kuma Mariya yar hayar gidan ta bude wuta kwarai wajen takura rayuwar sakeena,




A dan xaman watanni biyu sakeena ta fuskanci wacece Mariya ciki

Please Login or Register in order to submit comment