Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Deni qirjinta ya buga amma ta danne tacigaba da maganarta a waya. Surayya ta kalleta sosai ko baa fada ba tasan wannan itace sakeena ex wife din Deni. Deni ya qame guri guda yana more kallon sakeena dake sanye cikin jeans skirt da shirt. Hajjo tayo wajen daki jin muryar Deni. Ta tarar dasu tsaye dukkansu suna kallon sakeena, Surayya ta kalli Hajjo tace "wacece wannan Deni ke kallon ta?" cikin in ina Hajjo tace "Ummm haya suke a gidan nan sun kusa tashi saura sati biyu" Surayya ta kalleta shagarere tace "Ba sakeena bace ba? Meye na yimini qarya? Inma hayar suke meye na fada a gabanta wannan ai cin fusakane." sakeena ta cire wayar kunnanta tanawa surayya duban mamaki jin abunda ta fadawa Hajjo, ta kwashe da dariya ta nufi dakin Iya. Hankalin Deni ya dawo jikinsa bayan tafiyar sakeena, Surayya taja hannunsa tace "Taho mu shiga ciki Deen" suka kewaye Hajjo suka shige dakinta suka barta baki a sake.


Acan dakin Hajjo su Hadixa sun gaida Anty surayya kamar yadda suke kiranta cikin tsananin ladabi. Ta amsa tana murmushi da taunar cingam, Amina ce kawai bata gaidata ba tana kwance, ta kalli Hajjo tace "Hajjo mun yini lafiya?" da sauri ta amsa da cewa "Lfy lau Hajjaju makkatu kuna lfy ya baqunta da sabuwar rayuwa?" bata amsa ba tacigaba da danna waya. Deni ya gaida Hajjo ta amsa tana qorafin wata daya cur be nemeta ba ko a waya? Surayya tace "sai haquri Hajjo amarci muke, kuma ma meye abun damuwa dan kunyi wata daya kacal baku ganmu ba aure fa kukayi mana?" jiki a sanyaye Hajjo tace "Babu komai kam Haj Surayya dama a lokacin da nake neman nasa wata yar matsala nake ciki shine nakeson ya kamamun gidan haya in koma kuma har can gurin naku naje a lokacin aka hanani shiga" tace "ya kama miki haya kuma? Da wane kudin? Kuma ke yanxu banda rashin tunani in akace ki koma gida ke kadai saiki koma bakisan ana fama da in security ba?" Kowa ya bude baki cikin mamaki jin Surayya ta kira Hajjo da marar tunani. Deni ya gayyato qarfin hali ya dakawa Surayya tsawa yace "Ke! Uwar tawa kike kira mara tunani?" Surayya ta danyi dum jin kwabarta tayi ruwa tai saurin gyara kuskurenta takai hannu ta shafa sajen Deni tace "I'm sorry Deen kasan ni haka na saba magana, mumy bata hanamu, amma kayi haquri I luv u" bai wani dau mataki ba yace "it's ok"


Surayya ta kalli Amina dake kwance har yanxu tace "Hajjo ita wannan bata da lfy ne? Naga tun daxu take kwance" cikin sauri Fiddausi tace "wai saurayin sakeena takeso shi kuma baya sonta, har asaka musu rana da sakeena daxu ma ankawo lefe" Surayya ta washe baki jin matsalarta ta qare saboda jira take ta koma gida taiwa mumy waya a raba sakeena da xuciyar Deni, ashema wahala ta qare, shi kuwa Deni da sauri ya tambaya waye xai auri sakeena? Fiddausi ta bashi amsa da cewa "sageer kuma saura sati biyu bikin" xumfa ta wankeshi ya miqe yayi waje yace da Surayya xai je gurin friends dinsa. Tace "To karka dade." Ta kalli Amina tace "To micijiya wacce bata ramin kanta sai dai ayi ta shiga, ki xage ki nemi mijinki yadda kowacce mace take nema" ta juya gasu Hadixa tace "ku kuma ko ba a fada ba nasan xaman gidan aurenku ne babu dadi don gashinan jikinku ya nuna. Baya na suka (haqqi yana tambayarku) ni baxance ku koma ba, da ku koma da kuyi ta xama a gida duk daya a gurina amma wlh ku kiyayi kanku, ku kiyayi shiga shirgina da Deni dan ni ba sakeena bace tsaf sai in saka a qulle yarinya, kuma sannan ko hanyar gidana ban yadda kuyi ba don ba gidan Deni bane gida nane" daga su Hadixa har Hajjo kallon ta suke da mamakin wace irin riqaqqiyar mara mutunci Deni ya samo wacce ranar farko da taxo garesu take musu haka?


Bata jima ba ta shiga dakin Iya ta rikida ta koma mai tarbiyya da mutunci suka gaisa a mutunce tai mata murnar kawo kayan sakeena. Baba ya shigo tare da Deni ya bude daki suka shiga. Surayya ta kuma rikida ta xama me ladabin gaske ta gaida Baba uwa xatai masa Sujjada shima yaji dadin haka ta ciro turarurruka a jaka ta ajiye masa ya dunga saka mata albarka. Ganin daga dakin Baba xasuyi waje Hajjo ta kira Deni don akwai maganar da takeson fada masa tasu Hadixa ya bibiya a maidasu dakunansu, sannan tai masa complain din Surayya bata da tarbiyya. Yabi Hajjo daki kamar yadda ta buqata, ko fara magana basuyiba saiga Surayya ta biyosu ta riqe labule tace "Deen ina jiranka fa" cikin rawar jiki yace "To surry ganinan" Hajjo ganin babu yacce xatai ta hadiye qorafin Surayya da tai nufin fada tace "Dama cewa xan ka nemi Musa da Yusuf a taushesu su maida yarannan dakunansu tunda malam yanxu baya ta tamu yaqi shiga lamarin." Kafin yayi magana Surayya tai karaf tace "Akan me? Nawa Deen yake da xa'a fara dora masa lalurar gyara aure? Kowa ya iya allonsa ya wanke.Deen taho mu tafi" babu musu ya bita suka fito, ta sunkuya har qasa taiwa Baba da Iya sallama tace da Iya Dan Allah a sanar da ita lokacin biki, Iya tace mata ranar asabar ne ta sama xa ayi komai rana daya.



Hajjo ta koma daki ta dora hannu aka ta saka kukan nadama, to me hakan ke nufi? Ita dai yau ta fara ganin Surayya balle tace sakar mata fuska tayi har raini ya shiga tsakaninsu haka? Kuma ita kadai taiwa haka Baba da Iya duk a mutunce ta gaishesu. Bama wannan ba, meke faruwa taga Deni duk ya xama wani soko bashi da raayin kansa sai abunda Surayya tace? Hadixa ta dafata ta dago ta kantsa mata mari. Ta dafe kunci tace "Hajjo me nayi miki?" tana kuka tace "Wlh nagaji abubuwa sunmin yawa ku kunqi xaman aure bakwa duba ni kaina yanxu a rabe nake a gidannan, sannan ga yar uwarku tana neman haukacewa akan wanda besan tanayi ba shi kuma Deni ya xama mijin tace yana gani matarsa ta cimun mutunci amma ko uffan be ceba. Wayyo Allah na shiga uku baqin ciki xai kasheni." Duk suka dago suna kallon Hajjo. Ta rarumo wayar AV ta nufesu tana duka da cewa "ku hada kayanku kowacce ta koma gidan mijinta tayi haquri ta xauna nima ta kaina nake da wannan wacce ta xauce din (Amina) ta rarakosu har soro suka fice suna kuka. Ta koma ta wuce daki ta kwanta tana kuka. Daga Iya har sakeena da kuma Baba abun ya basu dariya sosai suka hadu suka dungayi.


Hadixa dai ta koma a sa'a domin anfara bikin Yusuf da sabuwar amaryarsa, don haka ummansa bata tambayi inda taje tai kwanaki ba tace ta xage ta shiga sahun masu aikin abincin biki, duk wanda ya tambayeta a cikin bikin yace ina uwargidan Yusuf kuwa sai tace dataji xaiyi aure tayi yaji tana gidansu. Sai ace ai dole tai yaji ko wata bata rufa ba anyo mata kishiya.


Ita kuwa Fiddausi musa ya tasa ta har shiyyar uwargida sarautar mata ta bata haquri harda durqusawa qasa. Cikin qasaita tace "Hmmm bakomi ai mutum baya fushi da me masa hidima, na haqura sai kici gaba da aikinki kamar yadda kika saba kuma banason sata ki kiyaye gaba. Abunda baki sani ba dukiyata Musa ke juyawa ta gado, munsha wahala tare kafin Babana ya mutu mekudin qauyene a raba mana gado na saida gonaki na na bashi kudin yake juyawa nake kuma bashi ladansa don haka keda shi duk a qarqashina kuke." Fiddausi ta kuma saduda ta saddaqar ta kawo kanta cikin bala'i a garin son auren hutu, ita kam Musa ya cuceta ya mata qaryar cewa dukiyarsa ce wadda ya tara da guminsa ashe kudin matarsa ne. Daga ranar ta xama itace meyin duk wani aiki na gidan har shirya yara xuwa school, bayan haka kuma bata da kwana sai dai da rana inya samu sauqin aikin kasuwa ya dawo yadan rage xafi a gurinta ko kuma ya faki idon Hajiya yaje gurinta kamar wata karuwarsa.


Haka sukacigaba da xama Hadixa cikin mulkin mallakar uwar miji, Fiddausi kuma cikin na kishiya.

********** ********** ****

Ara saura kwana 8 biki Sageer ya sauka Kano, yaxo da kwanduna shaqe da kayan gona wasu kuma kayan lambu hardasu fruit, dake shi dan gatan suruki ne fiye da kowanne suruki a gidan dakin Baba yayi masauki, Iya ta bata abinci ta kai masa da kuma kunun aya. Saida ya kimtsa sannan sakeena ta shiga, suna gama gaisawa taja bakinta ta tsuke, ya qaraci kallonta ya gama tayi kyau ta qara cika saboda shan maganin da takeyi da madara. Yace "Ga IV na kawo na daurin aure ke kuma bansan naki shirin ba shiyasa ban bugo naki ba amma ki fadan abunda xakiyi yanxu sai insa a bugo miki." tana danna waya tace "Ni babu abunda xanyi" yayi murmushi yace "To shikenan ga kayan fitar biki Bilki ta cire cikin kayan lefenki ta dinka miki, wannan kuma ga kudin hidimomin da xakiyi na biki" ya ajiye mata.

Baba ya shigo yana cewa "Sageeru wannan wahala haka fa ta isa, ko bakayi komi ba xamu baka sakeenatu tunda munyi alqawari." ya sunkuyar da kai yace "Baba ai ba wahala bace, wancan abun daga gonata ne nakawo a saka albarka" Baba yace "ashe manomi ne?" sageer yace "Eh akan noma nai degree na farko" Baba yana dariya yace "Da kyau, noma tushen arxiqi" haka dai suka gama hirarsu da Baba da Iya yayi salllama dasu ya tafi da sunan sai Friday xai dawo ana gobe daurin aure.


Shirye shirye sunci gaba, inda saura kwana biyar biki yan Baggadano suka kawo kayansu na gudummawar sakeena, Masara buhu biyu gero ma buhu biyu, sai jarkar mai mecin kwalba 35 guda biyu da garjejen rago da kayan miya harda busassu sukace a xuba mata a gara da kudi dubu goma. Iya tayi murnar wannan karamci da sukayi. Ganin haka ta shawarci Baba suka hada kudaden hannunsu kaf da ragowar na gurin sakeena da sageer yake bata da kuma kudin aurenta aka shaqo kayan gara tun daga kan hatsi har xuwa kan kayan xaqi har gurasa Iya tasa akai musu buhu guda, a cewarta tunda ba kayan daki xasuyiwa sakeena ba gara ayi mata gara akaiwa dangin sageer can katsina don a saiwa sakeena mutunci a idonsu.


Hassana ta dira Kano ranar talata bata wani jima a gidaba ta taho gurin sakeena dame gyaran jiki. Ta fara aikinta a take, xuwa yamma saiga jikin sakeena yayi qal dake farace har ya nuna ajikinta. Haka sukaci gaba dayi kullum Hassana ke xuwa da ita suyi xuwa dare su tafi ranar Friday ta kawo mata dinkunanta da mama ta diba ta bayar akai mata kuma ranar aka rangada mata qunshi hannu da qafa ana gamawa suka fice saloon. Ita dai sakeena abun ba wani dadarata yayi da qasa ba domin bason sageer take ba har wata rama tayi a yan kwanakin nan.



Su Amina da Hajjo dai ana daki duniya tai musu atishawar tsaki. Saddiq kuwa ya xage dashi ake komai har gida ya kaiwa Deni katin auren sakeena ya bawa megadi ya kai musu. Ranar jumaar da yamma Iya ta samu labarin xuwan dangin Sageer Kano don daurin aure da kuma mata domin karbar amanar sakeena kuma sun sauka gidan abokinsa. Ta shirya aka samo mota ita da Inna da wasu matan biyu da sukaxo daga Baggadano aka loda kayan gara shatara ta arxiqi aka nufi masaukin dangin sageer domin kai musu. Anxo tafiya kenan saiga Hajjo ta dakko mayafi xata bisu, Inna ta dakatar da ita tace "An gayyaceke ne?" Hajjo tace "Kema ainasan ba gayyatarki akaiba duk labarin mugun abun da kikaiwa sakeena yaxo min bakece matar ubanta ba wacce kika kashe Nura qaninta?" Inna tai dariya tace "Ai kinfini mugun hali domin ni bantaba silar batan dan mutum ba, amma duk da haka ban tsiraba da Allah ya tashi sakawa su sakeena xaluntarsu da nayi saiya hadani da makirar suruka kuma gida daya muke xaune taci ubana son ranta kuma Dan nawa wato mijinta baya ganin lefinta saboda batayi a gabansa. Daga qarshema saidata karyani garin duka da girmana da komai taimun duka na karye kana taimun tsirara kafatanin mutanen Baggadano dai dai kune basuga duwawuna ba ta wullani rijiya tace fadawa nayi tayi kururuwa akaxo a ka cironi bani da bakin cewa qarya take saboda babu mai yadda. Sai da nayi wata hudu ina jinya sannan na warke kuma ita ke jinyata tunda gidanmu daya. Dole na saduda na tsawar da makamaina na nemi afuwar wadanda na xalunta na kuma nemi shiri da ita domin ta fini iskanci da makirci. Me laya ya kiyayi me xamani. Dan haka kijira naki karshen nasan sai yafi nawa muni tunda kinfini tsula tsiya" Inna na gama fadar haka ta cangala qafarta da surukarta tai silar mayar mata da ita haka, tabi su Iya da suka fice. Tabar Hajjo baki bude cikin tsoro harta hango ta tana cangala qafa itama matar Deni ta ballata.



Acan gidan abokin sageer an tari su Iya da mutunci kunsan katsinawa babu magana wajen nan (su Anyt sis da maryam sani mani 😜) samari suka shigo da uban kayan gara suka dunga jibgewa Iya ta musu bayanin garar sakeena suka kawo saboda a jirgi zasu tafi ita da sageer babu dama a tafi da kayan abinci su kuma daganan babu me xuwa katsina shine suka kawo in yan daurin aure xasu tafi su juya da ita katsina.


Suka hau godiya da yaba bajintar su Iya. Yayar umman Sageer ta miqe ta kirawo su Baffan sageer a daya falon sukaxo harshi sageer din. Yaji dadi kwarai ganin haka don bayaso a raina masa sakeena suka dunga godiya aka kirawo Umma a waya aka fada mata ta dunga godiya tana cewa da Iya sunyi jere acan Lagos kuma sun kuma yin gara antadasu xaune tsaye saboda ansaka bikin lokaci kadan. Jikin Iya yayi sanyi tasan Sageer ne yayiwa sakeena kayan daki yace su sukayi. Ta qara yadda sakeena bata da masoyi a duniya kamar sageer. Sun rabu cikin mutunci.


Amina ta samu Baba a daren tana kuka tace "Baba ka yafemun duk abunda na biyewa su Hajjo mukai kuma Dan Allah ka roqi sageer ya aureni ko ata biyu ne, wlh ina qaunarsa kuma xanyi masa biyayya shi da sakeena baxan daga musu hankali ba na canja yanxu na rasa inda xansa kaina" Baba ya tusayawa Amina sosai yayi mata nasihar haquri da sageer kuma yayi mata nuni da wannan shine illar abunda sukai su da Hajjo sakeena na son Deni amma suka banqara suka dage suka rabasu yanxu gashi Allah ya jarrabeta da soyayyar da tafi ta sakeena xafi yayin da sageer bemasan tanayi ba. A qarshe yayi mata fatan samun miji nagari.


Sakeena sai kusan 9 na dare suka dawo daga saloon tai arba da yan Baggadano sun cika dakin Iya tai tsalle ta dire ta dunga rungumesu daya bayan daya suna mata dariya. Hassana tai musu sallama ta juya gida tace sai gobe da sassafe xata dawo. Kusan raba dare sukai suna hira Sadiya tasa sakeena gaba saidata cinye kaxar da akai mata tas. Iya ta bata rubutun ta shanye.


Suma basuyi bacciba kwana sukai soyar naman abincin gobe da kuma miya. Asubar fari aka kafa runfuna a kofar gida gari na wayewa saiga su Dahiru dukkansu sunxo daurin aure cikin fararen shadda sabuwa dukkansu iri daya sak sunyi kyau.



Gida ya fara cika yayin da sakeena gabanta ya tsananta faduwa sosai Hassana taxo tasa sakeena wanka ta tsantsara mata light makeup ta saka daya daga cikin kayan da sageer ya kawo mata a dinke ranar farin lace qal me taushi dinkin buba da xani wanda yayi mata das ya maisheta Fulani/Igala sosai. Kowa saiya yaba kyan da tayi. Surayya tai sallama ta shigo ta rangada guda cike da farin ciki ko dakin Hajjo bata kalla ba tai xamanta cikin yan uwan sakeena a falon Iya ta karbi a shoken da Hassana ke kici kicin nadawa Sakeena cikin few minutes sai gashi tayiwa sakeena nadi me masifar kyau ta rataya mata na kafada aka saki shewa. Hajjo ta fito dakin sanye da doguwar rigar shadda samfurin buhu tana kici kicin daura dan kwali ta dauki taliya da nufin ta taya su karyawa, matar Dahiru wacce itace ta saita Inna ta wafce tace "Koma daki bamu saki ba, daga ganinki akwai abunda kika fito yi na sharri yanxu hakama guba kika qullo xaki watsa mata cikin abincin tunda abaya kinyi yunqurin kashe sakeena baki samu nasara ba" ta daga murya tace "Na cikin daki ku fito ku cajemun makirar matar nan inaga gubace a qugunta a soke" dajin haka Hajjo taja doguwar rigarta ta koma daki. Surayya ta kwashe da dariyar iskanci.


Qarfe goma dai dai sukaji shelar daurin auren sakeena da Muhammad sageer ta cikin mic akan sadakin mota wacce sageer ya sai mawa sakeena tun farkon xamansu. Aka saki guda da kururuwar sakeena tayi goshi a dakin Iya ita kuma gabanta yayi wata irin bugawa amma ta daure ta furta "ALHAMDULILLAH" Deni da Surayya ta kawoshi gurin daurin auren domin ya sheda ya kuma qarasa cire sakeena a ransa ya xubar da hawaye. Saddiq ya matsa kusa dashi yace "Sakeena tayi kyakykyawan qarshe Allah ya bata me qaunarta da gaskiya" Deni ya bishi da kallo.


A cikin gida kuma ana sanarwar kammala daurin auren Amina ta yanke jiki ta fadi a sume. Hajjo tayi kururuwar a temaketa suka shareta wadanda sukai yunqurin temakawar ma Surayya tace suyi xamansu suman qarya tai saboda baqin ciki so take ta bata taron bikin. Baba ya shigo riqe da hannun sageer yana cikin farin ciki ya kama hannun sakeena yace "Sageeru ga sakeena nan amana ko bayan raina ka tuna amana na baka" ya damqe hannun sakeena qam yace "Na karba Baba kuma nayi maka alqawarin wlh baxanci amanarka ba" Baba ya kauce saiga Deni a tsaye a gurin idonsa jajur yana tuna kwatankwacin wannan rana da Baba ya bashi amanar sakeena shima yayi alqawarin riqewa amma bai cika alqawarin ba. Surayya ta matsa jikinsa tana nuna masa su sageer tana cewa "kallesu Deen yadda suka riqe juna so romantic" tana lura da yanayinsa amma ko ajikinta. Aka dunga photo da wayoyi da kuma cameras sakeena na jikin sageer wanda ya hade acikin wani farin yadi qal me rasha rasha duk da bata sonsa yayi mata kyau sosai, shi kuma sai qara rungumarta yake anai musu photo. Surayya ta ciro wayar Deni daga aljihu tayiwa su Sakeena hotunan kana ta mayar masa taja hannunsa suka tafi ba tare da yaga uwarsa ba balle gaisheta. Aka gama photuna sosai na farin ciki sannan Sageer ya tafi shida abokansa.


Wani yayan sakeena mai suna Iro ya shigo ana cikin hutuna wanda yake sakonta ne yace "Ke sakeena shegiya ai naga tsohon mijin naki da kika nacewa har ana xagin Babanmu akansa inbanda ke banxace meye kikagani ajikin wancan me qirar yan ta'addan wani gansansan dashi? Har uwarsa na xagin babanmu ai wlh da a lokacin anfadamun abunda tayi da sai nasa kokara na baje shegiya itadin banxa ta xagi Baba wacce illa gareshi har ake cewa baki da usuli duk ke kika jawo da kika laqewa shegen dannata" Sageer ya qunshe dariyar jin ankira Deni me qirar yan ta'adda ya riqo Iro yace "Yi haquri yaya Iro ai maganar ta wuce" yace "Ai wlh sageer da bata aureka ba da babumu babu ita"


Ancigaba da shagalin biki wanda ya tara jamaa fiye da xaton Iya, sakeena tayi shiga ta alfarma sosai. Yayin da Hajjo ta yini daki tunda taji ana xancen saka kokara a maketa, ko fitsari a baho suke ita da Amina. Da magrubar fari saiga dangin sageer mata sunxo daukar sakeena xuwa gurinsu can masauki ta kwana acan kamar yadda umman sageer ta umarta.


Su Inna suka shirya sakeena cikin sauri duk da baxata abun yaxo musu. Aka tafi da ita tana kuka. Acan masaukinsu sun karbi amanarta hannu bibbiyu suka budeta aka dunga yaba kyanta. Wadanda suka kawota suka juya akabarta gurinsu. Sageer jin ankawo ya shigo abokan wasa suka tasashi gaba da tsiya dole ya fita yana shafa sumarsa, shida a niyyarsa a bashi abarsa suje dakin da yake amma kuma a duk sanda ya tuna sakeena bata sonsa jikinsa kanyi mugun sanyi.


Suka kwana suna riritata da alamar diyar kanawa ta samu karbuwa gurin katsinawan Dikko. Da sassafe sukai wanka suka fara shirin tafiya, shima sageer suka shirya don jirgen 10 xasubi xuwa Lagos.



Abokinsa ne ya jasu xuwa gidan Iya don yimusu sallama da diban kayan sakeena bayan sunga dagawar yan katsina. Aka dunga fita da kayan sakeena ana lodawa a motoci harda wasu kayan girki da Iya ta hada mata. Baba ya kuma yimusu nasiha sosai Iya sai hawayen rabuwa da sakeena take. Baba ya danqa mata key din motarta da sageer ya bayar jiya. Sukaxo fita daga gidan sakeena tana kuka tace da yan rakiyar da suka rakota waje "yanxu babu wanda xai rakani har Lagos din kamar bakwa sona? Inya siyar da nifa?" Sageer yana dariyar abunda tace yace "Kinga kuwa kanki xaiyi mugun kudi" aka saka dariya jin ya maida abun wasa har iya abun ya bata dariya. Suka rabu ana waving juna motar ta nufi airport.




Xamu hadu ranar Sunday in shaa Allah


Hajia 😊
[8/5, 9:55 PM] Zongo Gal: πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€MUQADDARI NEπŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€2018πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€



2⃣4⃣

RAHMATULLAH (Hajia)


SAQON NA MASOYA NE πŸ’Œ

Assalamu alaikum, inawa dukkan masoyana fatan alkhairi a duk inda suke a fadin duniya, wanda muka hadu da kuma wadanda Allah be hadamu ba. Saqonku na samuna ta ko'ina kuma inajin dadi da kuma qara samun kwarin gwuiwar yin rubutu. Masu bugomun waya da masu yin text da kuma masu bina PC duk ina godiya. Sannan Dan Allah masoyana masu gayyatata xuwa grps Dan Allah kuyi haquri ban cika xuwa grps ba saboda wasu dalilai da baxan iya bayyanawa ba, amma dai nasan dukkan abunda mutum yayi ko yakeyi akwai dalilinsa nayin hakan, rashin kuma xuwana grp baxai rage komai na soyayyar da nake muku ba. Daga qarshe ina qara jaddada muku babban dalilina na rashin yin daily post saboda uxurin aikin gida da kuma kasuwancin amma bawai jamuku rai nike ba kunsan baxata yiwu ace mutum bashi da aiki ba sai danna waya. Nagode kwarai ina sonku ina qaunarku a duk inda kuke. Muna tare 🀝🏽 godiya ta mussanman ga ZAUREN BIEBEE ISA
(HAJIA ce 😊)



Xaune cikin jirgi amarya da angonta wato sakeena da sageer kusa da juna, sageer kallon sakeena yake idonsa taf da soyayyarta tayi shar cikin yellow colour super wax (Sheraton) ta yafa veil shima yellow ya kai idonsa kan yatsun hannunta da suka sha jan lalle da baqi sunyi kyau kamar da qunshin aka haliccesu. Ya kai nasa hannun ya riqo yatsunta yace "Sakeenatu" ta dago ta bude masa manyan idanunta akansa tace "menene?" yana murxa yatsunta yace "kiyi haquri a wancan auren da mukai na xarge akan abunda bani da sani akai, lokacin bansan kin taba aure ba, ki yafemun kinji my luv" ta fusge hannunta ta dubeshi tace "OH! Ka dauka nima yar

Please Login or Register in order to submit comment