Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Qudurat. Ya fara bibiyar texts din yawanci na jaddada qauna ne da kuma kalaman soyayya sai kuma na yadda yake fada mata hanyoyin da xatabi ta gallaxawa shi sageer din, ya saketa. Ya tafi kan chats dinta na wtsaup, ba tare daya kunna data ba shima dai duk daya, kalaman soyayya ne tsantsa wanda da wahala a fadawa mace su bata rufta ba, sai audios da yake mata na muryarsa yana fada mata ya kasa bacci itana sonsa kawai ta fito su koma aure. Bai kama sakeena da lefin komai ba domin yawancin amsarta bata wuce Eh ko kuma A a inkuma yayi mata Kalaman soyayya tayi murmushi ko kuma insakata tayi abu tace to. Ko shi kansa Denin baxaice yana mata maganar batsa ba balle kuma sakeena da maganganunta basu da yawa a gaba days chat din.



Yayi Hamdala bayan ya gama caje wayar tsaf kuma sakeena ta kubuta daga xargin da yake mata, ya gane dalilin fadansu ayau da Deni donta fada masa tana da ciki ne. Allah sarki, saita bashi tausayi shiyasa baa son xato domin xunubi ne. Yayi wa Deni text message da wayar sakeena yace su hadu a can wani kebattacen guri awata unguwa gobe da misalin 11 AM zasu tattauna akan makomar rayuwarsu. Ko minti uku beyiba da turawa saiga amsar Deni.


"To Baby, ko kefa Allah ya kaimu goben, xan bar duk abunda nake inxo saboda kinfi komai mahimmanci a duniyata yanxu, ina qara baki haquri kan abunda ya faru daxu wlh bada niyya nakai hannuna jikinki ba na gigitane da naji kina dauke da cikin Sageer. Sai goben ki fito da shirinki daga nan mu wuce court mu shigar da qara sai kawai acire cikin muyi aure, I LUV U"


Sageer ya jinjina kai cikin yaba jahilci da kuma taaddancin Deni, ya kashe wayar gaba daya ya cire layukan ya cillata jakarsa ta aiki. Yayi dariya yace "Yaro bakasan wuta ba saika taka, bakasan Lagos ba shege dan qauye ka kawo kanka mayanka, Area boyz xansa su dakko min kai su koya maka hankali a gabana inda ko sunan sakeena kaji an ambata saika raxana." ya xaro takaddar sakin daya rubutawa sakeena ya fita kicin ya qonata qurmus ya watsar da tokar a shara, yasan a guntun iliminsa na addini da yake dashi sakin beyiba tunda bai bataba kuma babu wanda yagani koya sani saishi. Cike da farin ciki ya dauki mug ya hada mata tea me kauri da xafi ya nufi bedroom dinta da nufin ya kaimata tasha dan ya tabbatar da bataci komai ba, ya kuma lallasheta yaji dumin babynsu wanda zargi ya kusa yasashi ya xubar dashi da kansa.




Xamu hadu ranar litinin in shaa Allah.



Hajia 😊
[8/21, 12:27 PM] A A Dboy: πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€MUQADDARI NEπŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€2018πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€



2⃣8⃣

RAHMATULLAH (Hajia)


Sakeena ta dawo dakinta bayan miqawa Sageer wayarta ta samu guri ta takure akan gado tana rawar dari garin gaba daya yayi sanyi ga AC a kunne ta kasa kashewa, xaxxabin jiya da ciwon kai ya dawo mata saboda kukan datasha. Mamakin toshewar basirar da tayi takeyi, wai itace yau da aurenta take dating wani har yayi rape attempt dinta? Kuma waninma wai Deni mutumin da ya wulaqantata tayi wani irin xaman aure na wahala a gidansa kafin yayi arxiqi ya fara kunyar nunata a matsayin matarsa, mutumin da ya kasa nema mata lfyar ido duk da yasamu halin yin hakan, mutumin da agaban Iya da Baba ya daketa kuma ya xaxxageta tare da yimata iqirarin tayi xina, mutumin da shi da uwarsa da yan uwansa sukai mata rubdugu suka sakota a gaba ita da uwar riqonta akan abunda ta silarsu ya sameta, mutumin da ranar daya fara ganinta a rayuwarsa ya kafa mata dokar hana taba komi na gidan kamar kuturwa, mutumin da uwarsa tai sanadin da bacin sunanta da fantsama hotunanta a duniya wanda dalilin hakan ita da Iya saida ko xaman tsakar gida ya gagaresu. Ita kuwa wace irin daqiqiyace data dauki Deni masoyi? Ina iqirarin da tayi agaban su Iya da Baba na cewa ta manta dashi? Wai meye ajikin Deni naso da take masa wannan soyayyar ta rashin xuciya? Da farko dai Deni ba asaline dashi me kyau ba balle ace xaa soshi kodan asalinsa, sannan shi bawani addini gareshi ba, gashi kuma bashi da dadin mu'amala saboda saurin fushinsa, baxata kirashi mummuna ba kai tsaye domin baya cikinsu, sannnan gashi sangangan babu fasali kamar tsani, ta bakin Iro yace me qirar yan ta'adda. To wai shin meye abun so ga Nura Lawan ne data kwallafa rai akansa tana sabawa Allah tana kuma baqantawa magabatanta da masoyanta rai akansa? Ta nisa cikin tunanin cewa tsoron Deni takeji, tabbas tsorone irin wanda soyayyar quruciya take haifarwa, wannan dalili shiyasa duk abunda ya sakata sai tayi koda kuwa bataso kuma koda xata batawa kowa rai.


Amma ta godewa Allah daya saka ta farga kuma ta dawo rakiyarsa kana ta warke daga mugun tsoron da take masa a yau. Ta dakko tunanin Sageer wanda tsoron Deni ya hanata tasa soyayyar tasiri aranta, Allah sarki bawan Allah me sanyin hali da sonta da kuma kyautata mata. Ta tuno maganar Nura qaninta ana saura yan kwanaki ya mutu, inda yake cemata "Ya Sakeena Allah ya cika miki burinki ya kuma kawo me temakonki" to kodai Sageer ne wanda Nura yake nufi me temakon nata? Tabbas babu makawa sageer ne domin ta hanyarsa kawai take ganin cikar burinta, a qarqashin inuwar aurensa ne ta samu cikakken yanci har ta samu damar yin iskanci don tsabar rashin sanin ciwon kai. Haqiqa Sageer ne, amma meyasa bata gane ba sai yanxu da komai ya tasamma kwabewa? Ta tuno yanayin Sageer tun bayan dawowarsa aiki jiya inda ya dunga hade rai da kuma basar da ita har xuwa kan cewar da yayi indai cikin jikinta dan halak ne yanaso. To meye dalilin wannan furuci nasa? Kodai ya gane tana da gurbatacciyar alaqa da Deni? Menene dalilin waccan magana da canjawarsa tafar daya jiya? Innalillahi wa'innah ilaihi, wane irin bala'i ta janyowa kanta mijinta na aure yana xarginta da yo ciki daga waje ta kawo masa? Lallai tsuntsun da yaja ruwa, yanxu duk haqurin sageer da soyayyar da yake mata ta qureshi kenan? Me gari ya waya? Ta xubar da mutuncinta, ta sabi ubangijinta, ta bata xaman aurenta mijinta yana xarginta. Shikenan ta shiga uku ta lalace, haqiqa duk wanda ya toxarta aure saiya wulaqanta.


Ta qanqame jikinta ta qara sakin kuka, ta kwanta kan gadon tana riqe da gwuiwoyinta haqoranta suna hadewa tana cewa "Sageer kayi haquri ka yafemun wlh banyi fasiqanci ba, cikinka ne a jikina bana Deni ba, ta'addanci na be kai inyi haka ba" Wannan taita maimaitawa har qaramar kwakwkwalwarta ta gaxa daukar damuwar da take ciki ta sume a gurin.


Sageer ya turo qofar dakin ya shigo da sallama, ya fara kiran sunanta a xatonsa bacci take, ya ajiye tea din akan loka ya hauro gadon yana cewa "Tashi sakeenatu kisha tea sai muyi magana" ya dagota, yayi matuqar raxana da yasamu idonta a bude hancinta da yana tsiyayar da ruwa bakinta kuma a datse, jikinta wani irin xafi wanda ya wuce kima. Ya fara jijjigata yana kiran sunanta a raxane, amma ko gixau batai ba. Ya kwantar da ita ya nufi falo da gudu, Maitama da Bilki sun dawo daga unguwa suka biyo ta gidan suna tsaye a falo ganin babu kowa, Sageer ya wucesu ya nufi kicin suna tambayarsa amma be kulasu ba, ya dawo da robar ruwa ya koma daki da sauri suka rufa masa baya.



Sukayi mugun ganin sakeena a sassanqame, ya dagota Maitama ya bude ruwan ya watsa mata a fuska. Bilki ta fita da sauri taje maqotansu ta kira matar abokin su Sageer wacce ke aikin asibiti, jin cewa sakeena ce babu lfy ta debo kayan aiki a chemist dinta dake cikin gidan suka juya tare da Bilki. Sun tarar dasu Sageer sunata aikin watsa mata ruwa amma ko gixau batai ba. Da sauri nurse din ta xauna suka bata guri ta fara auna BP din sakeena sannan ta dakko wata allura ta hada tayi mata. Ta qara dakko wata allurar ta dubi Sageer tace "Tana da ciki ne?" cikin sauri yace "Eh na sati 3 ne cikin" Maitama da Bilki suka kalli juna a tare. Ta maida allurar, ta dakko drip tayi wata allurar aciki ta jona mata, ta qara auna BP dinta da kuma bugun xuciyarta, tasa Sageer ya kawo jiqaqqen towel ta ninkashi ta dora mata akan goshinta saboda xafin da kan yayi. Ta miqe tana hada kayan aikinta tace "Babu damuwa stress ne yasata suma ga kuma xaxxabi jininta yadan haura kadan, amma babu damuwa komi ya dai daita namata allurar bacci"


Suka hada baki gurin yimata godiya, Sageer ya bita ya ciro kudi ya bata kudinta amma taqi amsa tace kudin kayan aiki kawai xata amsa ai xaman tare yafi komi. Ya dawo ya dora kan sakeena akan cinyarsa, su Maitama suna masa tambayar yadda hakan ta faru, yace ya dawo office ne yayi wanka ya shigo daki ya sameta haka.


Sakeena ta bude idonta a firgice ta kalleshi sannan ta maida idonta kansu Maitama tace "Anty Bilki kubawa Ya Sageer haquri na masa lefi yayi fushi dani kuma Allah baya yafe haqqin wani saiya yafemun Allah xai yafemun, inna mutu a wannan halin wuta xan tafi" suka dubeshi da alamar tambaya, ya waske da cewa "xafin xaxxabi ne yasata surutai" Maitama ya qura masa ido yace "Wannan maganartata ba sambatu bane, gaskiyan abunda ke xuciyarta take fadi, kuma da alamu ta dalilinka ta shiga wannan halin, be dace ace xaka wulaqantata ba a daidai lokacin data saduda ta kwantar da kai danku xauna lfy" ya sunkuyar da kai yace "Eh wai wayarta ta yar inata kira ba a daga ba ni bansan ma ta yar ba saidata dawo dake fadamun wayan ya fadi shine nayi mata fadan sakacin da tayi saboda wayar me tsadace"



Bilki ta riga Maitama magana "Haba Sageer mecece waya acikin arxiqinka da har dan tayar xakai mata fada? Ai ko ita da kanta tana iya sayawa kanta waya duk tsadarta bare kuma kai, dan Allah karka qara Sakeena qaramar kwakwkwalwa gareta yanxu dubi yadda ta xama adalilin wata banxa waya" yayi saurin cewa "In shaa Allah baxa a kuma ba Haj Bilki" Maitama dai bai yadda da maganar Sageer ba yayi shirune kawai saboda qure mutum babu dadi kuma kowa yana da sirrinsa wanda bayaso kowa yasani amma yasan tabbas ba haka xancen yake ba. Sakeena kuwa kallon Sageer take babu ko qiftawa cikin yadda da soyayyar da yake mata, ya rufe lefinta don kare qimarta da martabarta ga babban amininsa ya dorawa kansa lefin, lallai ta kusa taiwa kanta asarar rasa babban masoyi irin Sageer. Da haka har allurar da akai mata ta soma aiki bacci ya kwasheta, ya gyara mata kwanciya suka fita dasu Maitama xuwa masallaci ya kira Inna yace ta kula da ita kan yadawo karta cire drip din.


Koda ya dawo masallaci sata yayi agaba riqe da hannunta yana kallonta cike da soyayyarta da kuma tausayi, bai iya saka komai a cikinsa ba har lokacin da ruwan ya qare ya cire mata ya samo towel da ruwa ya goge mata jikinta tas kamar yadda nurse din tace sannan ya saka mata rigar bacci marar nauyi ya gyara mata kwanciya shima ya kwanta kusa da ita. Ta farka can tsakiyar dare, ta tashi xaune takai dubanta ga Sageer dake bacci a gefenta ta qura masa ido kafin tunanin qalubalen dake gabanta ya fado mata, ta sauka daga kan gadon a hankali saboda karta tadashi, ta fita falo jikinta yayi sauki babu xaxxabin sai dan ciwon kai kadan, ta qara bude qofar falon wacce ake rufewa saboda dare ta fita ta xauna akan barandar gurin iskar damuna na kadawa tana ratsanata, ta lumshe ido ta fada kogin tunanin yacce xatai Sageer ya yadda cikinsa ne a jikinta, tayi iyakar tunanin ta taga bata da mafita da wuya ya yadda da ita tunda ya fara xarginta kuma aurensu ya gama lalacewa tunda zargi ya shigo ciki. Ta fashe da kuka irin na rashin tudun dafawa.


Acan daki kuma Sageer ya juya tare da bude ido, yakai dubansa makwancin sakeena yaga wayam babu ita, ya tashi da sauri ya leqa toilet bata nan, ya fita falo nanma babu ita, hankalinsa yakai kan qofar shigowa falo dake bude da sauri ya nufi kofar yana ayyana kardai sakeena fita tayi a cikin wannan tsohon daren. Yana fito yaci karo da ita xaune dirshan tana sanaar tata wato kuka. Jiki a sanyaye yakai hannu bayanta ya tabata yaname xargin kansa da sakata cikin wannan halin, ta juyo a firgice tai arba dashi cikin muryar kuka tace "Ya Sageer wlh banci amanarka ba, na rantse da Allah cikinka ne a jikina, ni din tun ina kwana da yunwa tun bani da me bani koda ruwan sha ne kyauta, tun ina gararin bauta da aikatau, tun ina daukar nauyinmu ni da Nura qanina, tun ina daukar nauyinmu ni da Deni banyi fasiqanci ba sai yanxu? inbaka yarda ba kaban Al Qur ani in rantse dashi" ya runtse ido cikin tausayinta a xuciyarsa yace "Lallai Deni xai dandana kudarsa tunda yayi sanadin xubar hawayenki tundaga jiya xuwa yau" ya riqo hannunta ya dagota xuwa jikinsa suka shiga ciki, ya ajiye kan kujera ya tsuguna a gabanta yace "Sakeena bana xarginki wlh, kuma koda na xargeki a baya yanxu gaskiyarki ta fito kin kubuta daga xargina, kiyi haquri ki daina kuka ina sonki ina kuma son abunda ke cikinki" yakai hannunsa kan mararta ya shafa, ta ware ido tana kallonsa tana tunanin da gaske yake ko kuwa dan ya kwantar mata da hankali ya fadi haka? Ya katse mata tunani da cewa "Bari in hado miki shayi kisha ko?" ya tashi yaje ya hado mata cikin mug da cake a plate, amma qiriri taqi sha tace sai dai susha tare, hakan yayi masa dadi don shima yanajin yunwa, ya dunga diba da spoon yana bata shima yana sha sunacin cake din har suka gama, ya dauketa suka koma dakinta suka wanke baki suka kwanta tana rungume dashi.


Koda safe shine ya temaka mata tayi wanka ta shirya batasa a ranta xata makaranta ba shima kuma beyi niyyar taje ba don bata gama watstsakewa ba, yasa kayansa na aiki suka fito kan dining sukasha tea tare yaci dumamen tuwon shinkafar da Inna tayi jiya basu ci ba, ita kuma tana gama shan tea din ta kame akan kujera tayi tagumi tana kallonsa. Ya dubeta yace "Baby wannan kallon duk ni daya? Naga bakici me nauyi ba nasan kuma kina tare da yunwa" tayi murmushin jin kunya ya kamata tana kallonsa, tace "Ni dan wake xanci shi nake sha'awa" ya waro ido yace "Dan wake yanxu da safe Baby?" tayi dariya gami da marairaicewa tace "Yaya tun jiya da dare nake mafarkinsa" ya danyi dariya yace "Sry Baby, bebina yanxu xaitasaki ciye ciye ko baki so" ya miqe ta miqa masa tissue paper ya goge bakinsa, ya ciro wayarsa a cikin aljihu qarama ya miqa mata yace " Ungo riqe a hannunki wayatace da layina ciki ba kowane ya sanni da layin ba, xan kiraki inji jikin naki" tayi baya da sauri tana girgixa kai tace "A a Ya Sageer ni yanxu banason waya tsoronta nakeji, xamana haka babu ita yafiye mun kwanciyar hankali" ya kamo hannunta ya danqa mata wayar yana cewa "Haba haj sakeena me kunun aya karbi mana babu komi da xai faru tunda kina da Muhammad Sageer, in banji yanayin jikin naki ba hankalina xai gaxa kwanciya" ta karba don karta bata masa rai ta riqe a tsorace gani take kamar Deni xai kirata duba da yacce suka rabu jiya.


Suka fito tana rungume a gefen jikinsa tayo masa rakiya, yasa jakarsa a mota ya dago ya sumbaci goshinta, don ya gwadata yace mata "Yanxu me xakiyi?" tace "xuwa xanyi inyi danwaken inci sai in kwanta bacci nikeji sosai" yace "yawwa Baby, to ki ajiye wayar a kusa xan kiraki" tace "To" yana shirin shiga mota ta sumbaci lebensa ta xura da gudu tai cikin falo, ya saki murmushi cikin mamakinta ya shiga mota yana goge lip dinsa inda ta shafa masa lipstick.


Kamar yadda ta fada dan wake tayi na fulawa taci da manja da yaji tasha kunun aya ta koma bedroom ta miqe a gado.



Wajen qarfe goma Sageer ya dawo gidan ya ajiye motarsa a waje, yaxo ne domin ya tabbatar da gaskiyar abunda ta fada masa na cewa bacci xatai karyaje ya yadda da ita ta fice su hadu da Deni. Yayi sa'a bakowa a falon, direct ya wuce dakinta ya sameta kwance tanata sharar baccinta. Ya saki ajiyar xuciya ya koma da baya a hankali ya qara tambayar me aikinta dake xaune harabar gidan yace "Madam ta fitane?" tace "A a tunda ta rakoka daxu ta koma ciki bata qara fitowa ba" ya jijjiga kai ya fita ya kirawo yaran da yasaka su dakko masa Deni ya fada musu inda xasuje da kuma gurin da xasu kaishi in sun dakko shi.



Ya koma office yaci gaba da aikinsa hankali kwance, ya gama yadda da matarsa ya tabbatar da nutsutstsiya ce wannan dan iskan ke neman kangarar da ita. 11:17 AM suka masa waya da cewa komai ya kammala, ya xari key din mota yayiwa gurin tsinke.


Ya shiga dakin da yasa aka kai Deni, suna tsatstsaye shi kuma yana xaune a kujera bakinsa a fashe, ya kallesu yana tambayarsu yadda akai, Babbansu yace "Oga ya danso yayi mana taurin kaine akan waccan gwangwanin (mota) shine muka mommolata muka dan silalashi saboda ya nemi ya kawo raini shine ka ganshi haka fa, shege ashe mugun ragone, ajawo kawai, gashi da jikin qarfafa amma ana tabashi yayi tubus."



Sageer yayi dariya ya xare glasses din fuskarsa yana kallon Deni, shima Denin shi yake kallo ya miqe yana nunashi yana cewa "Dama kaine kasa aimun haka? Kaine ka kawoni nan gurin?" Sageer cikin murmushi yace "Eh nine nai amfani da wayar sakeena nasa aka dakko ka domin amsa wasu tambayoyi da kuma yimaka tarbiyyar da gyatumarka ta gaxa yimaka" Deni cike da fada ya tasowa Sageer yana cewa "Karka qara sako uwata cikin wannan maganar, sannan inka isa kai namiji ne mukara ni da kai ba wadannan qartin banxan xakasa su dakkoni su dakeni ba, Sakeena kuma tawa ce kuma na tabbatar indai tasan abunda kaimun wlh ta gama xama dakai" ogansu ya tashi ya nufi Deni, Sageer ya daga masa hannu, ya daga qafa ya kaiwa Deni wani duka a qirji sai gani a qasa wanwar, ya dago da mamaki yana duban Sageer. Sageer yayi dariya yace "Ai ba girman jiki bane abun, qarfin xuciya ne. Sannan ka fadamun dalilin da yasa kake bibiyar matata da kuma son kashemun aure"


Deni yayi qoqarin shanye dukan Sageer, yayi dariyar qarfin hali yace "Kana nufin dan wannan abunda kaimun shi xaisa in saduda? To bari kaji na shirya shanye duk wata aquba akan Sakeena" Sageer yayi dariya yaja baya yace dasu "Ku tambayeshi" ogansu ya matsa ya cire tabar da yake xuuqa ya mutstsukewa Deni ita a tafin hannunsa, ya saki qarar axaba, ogan yace "bashi amsar tambayar da yayi maka" Deni cike da ixxa yace "Baxakaji komi ba duk abunda xakaimun" daya daga cikinsu ya sheqe da dariya yace "Lallai wannan besan Area boys ba, guys mu tambayeshi" suka rufar masa da duka kota ina suna takashi da banyan takalman qafafunsu yana ihu cikin tsabar axaba daga qarshe daya a cikinsu ya kaiwa hantsar Deni bugu da qafarsa, Deni ya shide cikin axaba yace "Kuyi haquri xan fada. Wlh sonta nake nakasa jure rashinta shiyasa nasaka ta kashe aurenta mu koma aurenmu saboda nasan itama tana sona"




Sageer ya tako a hankali ya hanasu dukansa yace "Kayi kuskere Nura domin yanxu sakeena ta tsaneka kuma da hannunta ta kawomin wayarta tare da yimun bayanin duk abunda kasata tayi" Deni ya share hancinsa da jini ke fita yace "Indai gaskiya kakeson ji to wlh nine wanda sakeena keso kamarta mutu kuma na tabbatar da baxata qara son wani ba bayan ni" Sageer yayi murmushin takaici yace "Ni bana abu babu Hujja bari in tabbatar maka da Sakeena yanxu bata sonka.


Ya ciro wayarsa ya kira layinsa daya bawa sakeena daxu ya sakata a hands-free. Tana bacci kiran wayar ya tasheta, ta dauka cikin sassanyan murya tace "Ya Sageer ina sonka" Ba Deni ba hatta Sageer kalmar ta dokeshi kuma ta bashi mamaki, ba don ya tabbatar da sakeena batasan ya dauke Deni ba da sai yace da gayya ta fadi haka. Ya shanye mamakinsa yace "Sakeena nima inasonki, ya jikin naki? Ya kuma Baby na?" cikin muryar shagwaba tace "Jiki da sauqi, ina cikin baccina me dadi da mafarkinka ka tasheni, Babyn ka kuma lfy sai duminka da yayi missing" yace "Ayya! sry my luv koma baccinki nima sonki ne ya addabeni shiyasa na kiraki inji muryarki" Deni ya fara ihu da kiran sunanta, Sageer yayi saurin disconnecting kiran ya dubi Deni dake ihu yana cewa "Wayyo Sakeena ki ceci rayuwata, karkimun haka ina sonki munsha wuya tare kixo muji dadi yanxu, karki yaudareni ki yafemun abunda nai miki abaya inkika barni rayuwata xata watse"



Sageer kallonsa yake da mamaki, yaran kuwa dariya kawai suke ganin duk akan mace yake wannan ihun banxan. Yace "musu ku cika aikinku ayi masa tarbiyyar dauke ido daga kan matar wani" suka fito da gorori suka rufar masa, ya fara ihu yana ambaton sunan Sakeena, Sageer ya qara cewa "Aita dukansa har saiya daina kiran sunan sakeena" sukacigaba da dukansa tun qarfinsu, sai gashi Deni ya fara kiran "Wayyo Allah na" Sageer ya kwashe da dariya yace "Ku kyaleshi ya dawo hanya, wannan ba dukan lefin da kayimun bane kawai, harda dukan da kaiwa sakeena lokacin da tana kurkukun gidanka." ya dakko bundle na 1k ya cilla musu, suka chafe tare da ambaton "Sai oga da girman kujerar ka" ya qara cemusu "Nagode sosai, ku daukeshi ku sakashi a akwalar motarsa ku ajiye inda kuka tabbatar baxa'a ganshi ba balle a temakeshi sai xuwa lokacin da jikinsa yayi tsami" suka amsa da "angama oga" ya juya xai tafi Deni ya bishi da kallon tsoro yana cewa "Dan Allah karka barni da wadannan marasa imanin qarasa kasheni xasuyi, kaga kai musulmi ne dan uwana kuma dan arewa kodan haka ka taimakeni" Sageer ya kuma yin dariya ya juyo ya dawo yana kallon Deni yace "Yawwa na manta ban fada maka ba, inkanaso in tabbatar da kai dan iskane to ka kaini qara ka fadi abunda nai maka kaga daganan sai reshe ya juye da mujiya irin yadda mahaukaciyar uwarka tai qarar sakeena qarshe abun ya dawo kanta" Deni ya kuma tsorata da Sageer kamar yasan abunda yake shiryawa kenan yana fita daga nan gurin, amma kuma yanxu ya fasa domin Sageer yana iya budewa hukuma abunda yayi kuma sakeena ta bada shedar

Please Login or Register in order to submit comment