Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai." Sageer ya dubi Dr sani yace "amma fa tamun qanqanta Dr" Sani ya kwashe da dariya yace "shege kanasa ran xakai wani abu kenan tunda harka hango tama qanqanta?" Ya hade rai yace "banaso iskanci Sani, na yadda da shawararka amma baxan fadawa umma na ba don auren temako xanyi bana soyayya ba kaga in umma taji baxata bari insaketa ba in lokaci yayi. inaso maganar ta tsaya a tsakanina da kai da Abdulfatah uban gidana sai Maitama abokina shima saboda sheda anan gaba, inaso randa xa a bude mata ido ta ganni a matsayin mijinta." Dr sani ya amsa da cewa "Hakan yayi Allah ya baka ladan alkhairin da kayi da temako"



Daga nan Mr Sageer Victorian island yayi gidan uban gidansa wato controller Abdulfatah. Yayi masa bayanin duk yadda sukai da Dr sani kuma ya fada masa farkawar sakeena shiya hanashi xuwa aiki yau. Abdulfatah yayi naam da shawararsu yace gobe da safe yaxo suje tare masallacin juma a in ansakko a daura aure.





A wannan dare Sageer ya kwana tunani da xuwan aure haka bagatatan a rayuwarsa.



Ya leqa teaching hospital da safe gurin sakeena a gabansa aka shiga da ita aikin Ido ya wuce office. Ana idar da sallar juma a a babban masallacin juma a dake Lagos Abdulfatah ya xama waliyin sakeena yayin da Imam na masallacin ya xama wakilin Mohd Sageer aka daura aurensu da sakeena akan sadaki 100k wanda Abdukfatah ya biyawa Sageer. Maitama yana daukan wedding fatiha din a waya kamar yadda Sageer ya sakashi har aka gama. Suka dan yiwa Sageer wasa irin na abokai shi da Dr sani, Abdulfatah kuma ya bashi sadakin sakeena yace yasan yadda xaiyi ya bata shi yawuce office. Suka watse suka bar Sageer a cikin mota ya kife kai akan sitiyari ya rasa wane irin yanayi yake ciki, farin ciki ko baqin ciki? Fargaba ko murna?


Wannan qaddara ita ta canja mata suna daga SAKEENA ABBAKAR LIMAN xuwa SAKEENA MOHD SAGEER. Me xaratan maxajen aure guda biyu rigis. NURADDEEN LAWAN da kuma MOHD SAGEER ABDALLAH.



Hajia😊


[7/31, 2:21 PM] Reine Ghana: πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€MUQADDARI NEπŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€2018πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€



1⃣7⃣

RAHMATULLAH (Hajia)


MUHAMMAD SAGEER ABDALLAH shine cikakken sunansa haifaffen garin katsina, Babansa tsohon ma aikacin gwamnati ne wato Alh Abdullah da matar Haj kubra yana da rufin asiri amma fa bawai me kudi bane. Su biyu aka haifa Sageer ne Babba sai qanwarsa shafa.



Sageer yayi karatunsa tundaga secondary har na jamia a katsina kuma yana bautar qasa ne Allah yayiwa mahaifinsa rasuwa. Mutuwar ta daga hankalinsu sosai amma ya suka iya? Rai baqon duniya, wanda ya tafi beyi gaggawa ba muda muka rage bamuyu jinkiri ba fata dai Allah ya bamu wucewa lfy amin.



Bayan gama bautar qasarsa Sageer yayi xaman jiran samun aiki amma shiru dake bashi da wanda ya tsaya masa aiki yaqi samuwa.Beyi dogon xama ba ya fara qoqarin komawa makaranta. Ya xaunar da mahaifiyarsu wadda suke kira Umma ya fada mata qudurinsa kuma ya roqeta akan a raba abunda Babansu ya bari abashi nasa ya dauki nauyin karatunsa saboda Msc karatune me cin kudi sosai bayaso abiya masa a dukiyar gado a kwari qanwarsa shafa wacce tun bayan gama nata karatun tai aure. Hakan akayi aka raba aka bawa kowa nasa gidan da suke ciki kuma suka barshi a haka.



Dake professional masters yayi shiyasa cikin qanqanin lokaci ya gama, ya dawo aka kuma dora xaman jiran aiki. Abun Allah ana cikin haka suka hadu da wani school mate din Babansa. A taqaice dai shiya shige masa gaba ya samu shiga hukumar customs bayan sunyi training na yan watanni ya fito a babban jami i kasancewar da babban kwali ya shiga hukumar. Akai kuma posting dinsa Lagos.



Sageer kyakykyawan baqin bafulatanin Katsina bashi da tsawo kamar yadda bashi da qiba ma ana dai me qaramin jiki, dan kimanin shekaru 39-40 da haihuwa. Baqinsa me hana kyansa fitowa ba kasancewar ba farar fata bace kyau. Yayi shekaru 7 cur yana aiki da hukumar costums kuma ya tara dukiya dai dai misali da kadarori. Ya tsayawa ummansa da shafa yana musu hidima sosai kasancewar basu da gatan da yawuce nasa. Ummansa ta matsa masa akan yayi aure tun shekarun biyar baya amma abun ya gagara a gurin Sageer saboda a bayan idonta wato a Lagos yana taba barinkinsa kadan bame yawa ba a duk sanda ya buqaci kasancewa da mace kuma ya kasa juriya tunda shi ba dutse bane. Saboda haka ya tattara maganar aure ya jefata baya tunda abunda xai samu a gidan auren gashi yana samu a titi inya biya kudi kuma sai wacce ya xaba ya darje, to a ganinsa mexesa ya dakkowa kansa damuwa ya kawo gidansa yasa aransa shi da aure sai dai in yaxo masa a qaddara amma shi babu soyayya aransa balle aje ga wani abu waishi aure kuma shi yadda yayi mugun raina mata ma waxai kalla ya kawo gidansa da sunan aure, shifa a ganinsa ma mafi yawan mata karuwai ne (Da kurawan dai kake mu'amala shiyasa kake ganin haka dan rainin sense 🀨😏)




To kuma ana cikin haka sai gashi auren qaddara na yar qanqanunwar yarinya ya fado masa bagatatan wanda yayishi bada sanin kowa nasa ba kuma baya fata ahalinsa su sani har ayi agama.



Har akai kiran la'asar Sageer yana mota a kwance yana aikin tunani kafin ya yanke shawarar tunkarar matsalar da addua kawai da kuma sadaqa tunda tana maganin masifa. Ya fito ya shiga masallaci yayi sallah yana fitowa ya rabawa yan tsofaffin dake kofar masallacin sadakar dubu dai dai sukaita godiya da fatan alkhairi.



Ya nufi wani qaton shagon sai da golds, ya shiga da nufin siyawa sakeena gold da kudinta na sadaki, aka fara nuna masa golds din dake cikin gilasai da farashinsu. Wani farin xobe yaja hankalinsa yace a fito mai dashi, aka dakko masa ya dibashi farine qal sai daukan ido yake siriri sosai sai wani stone a tsakiyarsa shima kamar jikin xoben fari qal. Aka auna masa shi. Kudinsa ya kama 176k ya dakko sadakin sakeena ya basu, ragowar kudin kuma babu kudi a jikinsa sosai ya bada ATM aka cire through P O S aka bashi receipt yayi mamakin tsadar xoben. Matar dake gurin tace masa 'ai English gold ne kuma stones din dake jikima me darajane sosai. Amma daka taho da Madam din ta gwada da yatsanta ko?' ya danyi jim dan gaskiyane abunda ta fada, yace "karki damu inyayi kadan ko yawa xamu dawo in xanja inda ciko inyi"



Daganan asibiti ya koma gurin sakeena, ya tarar tuni sun fito daga aikin idon amma tana kwance sambal a gado. Likitan ke masa bayanin sun mata allurar baccine data rage radadi saboda dinkin dake cikin idon xata iya kaiwa gobe bata farka ba.



Ya samu gefen gadon ya xauna bayan fitar likitan, a hankali ya fara qare mata kallo tundaga yatsun kafarta har xuwa gashin kanta. Dake dan duniya ne a harkar sanin mata anan ya gane sakeena ba qaramar qayatacciyar mace xa ai ba inta gama girma kuma tasamu jin dadi. Bayan haka ma ya gane kyakykyawar gaskece.



Ya kamo xara xaran yatsunta na hannu ya cire mata xoben axurfa da abun hannun dake dauke da sunanta bisa shawarar likita na guje tuna mata rayuwarta ta baya har xuwa lokacin da xata tuna dan kanta. Ya ciro xoben daya siyo yanxu cikin box ya mayar mata a gurbin na axurfa ya xauna caraf kamar angwada da hannun. Ya haska hannun sosai, yakai yatsun bakinsa ya sumbata, yayi saurin miqewa a gefen gadon daya tuna itadin fa ba wata bace a gurinsa face yar amana wacce ya aura dan temako.



Sai wajen taran dare ya tafi gida, ya danci abunda kukun ya dafa masa yayi wanka ya kwanta da tunanin irin rayuwar da zasuyi da sakeena inta dawo gidan nan a matsayin matarsa.



Da safe ya tashi da aikin gyaran daya bedroom din dake cikin falon, yaransa suka dunga mamakin oga da wannan aikin da kansa? sai da yaga dakin ya masa yacce yakeso sannan ya shiga gurin Maitama a gidansa dake qasan layin suka gaisa da matarsa Bilki kafin ta taso mijinta dake bacci. Ya fito yana hamma yace "wai kai ka dauka kowa irinkane gwauro da kake xuwarwa mutane gida da safe?" yayi tsaki yace "Ba wannan shirmen ya kawoni ba, so nake Bilki ta temakamun a samowa yarinyar nan kayan sakawa da sauran kayan mata na kwalliya kafin ta farko, yanxu ma nagama gyara mata dakin dake babban falo acan xata sauka banaso tasan komi sabone yanxu." Maitama ya daga gira yana kallon Sageer a kaikaice yace "To danme baxata sauka a dakin kaba? Ba matarka bace? Allah yasa kayi aure wannan damace a gurinka ka yaqi rayuwarka ta bariki. Kuma ai babu matsala dan tasan komi sabone kana iya dora tunaninta akan cewa kunyi aurene kwanaannan tasami matsalar ido shiyasa ka kaita asibiti" Sageer yace "kaga malam bawai na tambayeka bane ka tunamun ni dan bariki ne kawai temako nakeso inxaka temakamun to" Maitama yaje ya kira Bilki shi da Sageer sukai mata bayanin auren sageer da sakeena jiya kuma suka fada mata abun na sirrine. Bilki wayayyar mace tashin Lagos ta tausayawa sakeena kwarai ta fada musu duk yadda xasu tafi da plan dinsu.



Tare suka fita da ita kasuwa Sageer ya kashe kudi wajen siyan kayan da Bilki ta xaba bayan sunje taga sakeena kuma ta aunata, ta xabo kayan da xasu dace da kalar fatarta masu kyau da tsada tasai mata mayuka irin nasu na masu farar fata da su turare. Dake tailor ce itace ta debi kayan duka ta fara aikin dinkasu aranar ta dunga yaba kyan sakeena tana cewa da Sageer ya more mata me kyau.



Koda sakeena ta farko daga allurar ancigaba da kula da ita a asibiti, yayin da Sageer kullum sai yaje da safe kan ya tafi aiki haka ma da yamma inya dawo, yakan xauna su danyi hira koya bata lbr wani xubin ya riqeta su tattaka xuwa wajen daki. A gefe guda kuma suna jiran cikar sati daya a cirewa sakeena bandage din aka nade mata ido dashi kamar yadda likita ce.



Ranar juma a sati guda cif sassafe Sageer yaxo asibiti, likitan safe yana xuwa aka fara takan masu irin matsalarta, a hankali aka fara ware mata idon har aka gama ta budeshi tar, da farko haske yaso yayi mata yawa kafin a hankali ta budeshi gaba daya. Likitan ya wawwara mata idon ya haska aka tabbatar babu matsala. Ya nuna mata Sageer dake tsaye yace "kin san wannan? Kinsan waye shi?" cikin sanyin muryarta tace "A a yau na fara ganinshi" yace "mr Sageer ka matso kaiwa matarka bayanin kanka" ya matso a darare kamar me tsoron magana yace "Sunana Mohd Sageer kuma ni mijinki ne anyi mana aure wata daya baya kika samu matsalar ido shine akai miki aiki" ta danyi jim kamar tana shakkar abunda ya fada tace "To sannu da xuwa mijina" sukayi dariya shida likitan jin abunda tace. Yadan gyara tsaiwa yace "ki kirani Sageer kawai babu damuwa" tace "to" likita yagama aune aunensa ya bata wani siririn glass din ido wanda xata dunga sakawa xuwa wani lokacin da idon xai sami kwarin da ake buqata ko kuma inxata kalli waya ko TV ko kuma kallon takadda da qarin magunguna sukayo gida.


Gidan Maitama ya ajiyeta gurin Bilki kamar yadda suka tsara xata xauna nadan lokaci a gidan Bilki xata saitata da koya mata wasu abubuwan na gida. Hannu biyu Bilki ta amsheta tayi mata masauki a dakin danta me shekaru 4 wato haidar. Sageer ya nunawa Bilki yadda xa a dunga bawa sakeena maganinta na ciwon ido dana kwakwalwa ya tafi gida yana cewa aransa nima dai na huta na yan kwanaki na kuma fuskanci aikina.



Bilki ta fara aiwatar da aikinta babu bata lokaci dake itama mijinta Maitama gurin aikinsu daya da Sageer kuma bata aikin gwamnati sai business da dinki shiyasa ta samu lokaci sosai, xatakai kimanin shekaru 27 shiyasa cikin qanqanin lokaci ta karanci sakeena yarinya ce me saukin kai da haquri kuma bata da son jiki. Ta fara tafiyar da sakeena a hankali saboda matsalarta komi inxatayi tare sukeyi kuma tana koya mata gayu irin nasu na masu wankewar ido.



Kwanan sakeena bakwai gidan Bilki ta saki jikinta sosai, kuma xuwan Sageer 2 kacal dubata saboda aikinsa.


A ranar data cika kwana 9 tafiya ta kama su Sageer shida Maitama xasuje Edo state yin wani aiki da ogansu Abdulfatah, yaxo sukai sallama da sakeena kamar masu tsoron juna suka tafi. Wannan tafiya taiwa Bilki dadi, ta dunga fita da sakeena gurare na bude ido kuma tana sai mata kayan kwalliya tana yiwa Sageer list din duk abunda ta kashewa sakeena. Satinsu 2 cur suka gama aikin daya kaisu suka dawo amma banda Sageer ya wuce can Katsina gurin ummansa saboda wata yaxo qarshe.


***** ***** ******* ******


A kano kuma a cikin wata na biyu da batan sakeena suka fidda tsammanin ganinta saboda duk cigiyar da ake ta nemanta babu amo babu lbr Deni ya jigita sosai yayi nadamar wulaqanta sakeena.



Dole aka tada bikin Fiddausi, Baba bashi da kudin yimata kayan daki amma yayi iya qoqarinsa ya hada 70k da kudin aurenta 50k ya tashi 120k ya bawa Hajjo yace a siyo mata abunda ya sawwaqa me hali baya fasawa ta raina kudin daya bata tace a wannan xamanin da rayuwa tai tsada 120k mexata siya a kayan auren budurwa? Yace shikam iya qarfinsa kenan. Tace "malam basai kaiwa Deni magana ba ya kawo wani abun ahada" yace "ke me xai hana kiyi masa ko ba danki bane ko kina xaton besan da bikin ba?" taja baki tayi shiru domin yanxu kunyar Deni take saboda abunda tayiwa sakeena kuma abunda ta kakkarba a gurinsa da sunan yiwa Fiddausi siyayyar aure duk sun qare abun malamai na raba sakeena da Deni da kuma mallakewa Fiddausi mijin da xata aura da kishiya. Kafin Deni ya dena bata saboda ta kore masa mata da tayi.



Haka biki keta qaratowa amma Hajjo babu kudin yin bushasha kamar yadda ta qudiri niyya gashi kuma gidan kishiya xa a kai Fiddausi. Dole tasa gonarta a kasuwa amma abun Allah akaqi koda tayawa balle asiya.🀣



Fiddausi kullum sai tayi kuka saboda abunda ya samu sakeena suke dariya na shirin samunta wato aure babu kayan daki. Har gara ma sakeena nata mijin saurayi ne kuma na gida. Ita kuwa gashi bare ga kishiya gashi ta gamayi masa qaryar har gara xa a kawota da ita saboda yayanta na aiki a wani babban company, kamar yadda Hajjo tasha alqawaranta mata.


Daga qarshe dai Iya da suka raina kuma suka dauketa maqiyiyarsu itace taiwa Deni magana ganin daga Baba har Hajjo kowa ya kasa tararsa da xancen kuma biki ya rage yan kwanaki kadan. Lokacin da tayi masa maganar hade rai yayi yace "Iya ai tunda sukai silar rasa sakeena sun dai nacin ko sisina" tace "a a Deni ai hannunka bai rubewa ka yanke ka yar, dole yan uwanka basu da wani sai kai tunda kana da hali ka duba Allah da kuma mahaifinka ka fiddasu kunya" kwallah ta cika idonsa yace "shikenan Iya sunci darajarki da kuma soyayyar da nakewa sakeena xan duba inga abunda xan iya"



A yinin ranar sai ga motar company dauke da kayan Dubai yan dauri set din gado dana kujeru da qatuwar katifa. Aka shiga da kayan mamaki ya rufesu domin basusan wanda ya aiko dasu ba, Fiddausi baki yaqi rufuwa sai washe baki take tana shafa kayan.


Da daddare an xauna cin abinci Deni a gaban kowa ya fadawa Baba Iya ce tasashi ya sayi kayan kuma Fiddausi taci darajar Iya ne da sakeena shiyasa ya saya. Baba yayi godiya da fatan Allah ya qara budawa ya kuma sakawa Iya albarka da kyakykyawan aikin da tayi. Fiddausi ma ta juya babu tirjiya ta godewa Iya da Deni dan tasan badan Iya ba datasha kunya a bikinta. Hajjo ta kuma tsanar Iya da sakeena wato ita da danta bata isa ba har sai wata banxa uwar riqon matarsa tasa baki sannan yayi mata abu ita da yayanta kenan? Suma dai Hadixa da Amina irin tunanin Hajjo sukayi Saddiq kuwa dama bayanan.



Sati na xagayowa akai bikin Fiddausi aka kaita dakin mijinta a tudun yola gidansu daya da kishiyar amma kowacce da part dinta kuma babu lefi dakin Hadixa yayi kyau an fita kunya amma fa ba kamar yadda ta shirgawa mijin qarya ba, a hakan ma dan anhada da sadakinta kuma ba aimata garar da take buri ba.

**** ****** ******* *****


Acan Lagos kuwa sakeena tayi tas da ita a qarqashin kulawar Bilki tayi bulbul saboda babu abunda ke damunta ko dogon tunani ba a bari tayi bisa shawarar likita. Ana gobe xai dawo kamar yadda Maitama ya fadawa Bilki tasa aka gyarawa Sakeena gashi a saloon duk da sakeena tafison kitso amma Bilki tace a barmatashi a tsefe akai retouching aka dora steaming yayi tsaho sosai aga nadeshi a band yana qamshin mayuka, har gida ta kira me qunshi tayi mata ja da baqi yayi tar akan farar fatar ta. Bilki da kanta ta xauna ta cirewa sakeena gashin fuskarta tas, abunda bata taba yiba tunda take a rayuwarta. Tasa ta qalqale duk wani gashi na jikinta.




A ranar Saturday ya dawo bayan ya shafe 6 dayx a Katsina, ya kwanta yayi baccin gajiya har xuwa yamma ya tashi ya gyara bedroom dinsa da baya bari masu aikin gidan su shigar masa. Xuwa magrib yayi wanka ya nufi masallaci har xuwa sallar isha a nufinsa inya fito daga sallar isha xai leqa gidan Maitama duba yarinyar can.




Acan kuma sai da magrib tayi Bilki ta tabbatar Sageer ya nutsu ya huta sannan ta saka sakeena tai wanka ta tsala mata kwalliya cikin wani baqin material cotton da akaiwa riga da skirt wuyan high neck da akayi da net har xuwa hannyen rigar tayi mata light makeup ta baxa mata perfumes masu sanyin qamshi da tsuma xuciya taci takalmi heel wanda Bilki tace dole ta koyi tafiya dashi tunda bata da tsawo sosai. Sakeena tai kyau kamar bestie na ranar award night 😜 tana sallar isha ta hada kayan sakeena tsaf a akwatina masu aiki suka tayata dauka duka nufi gidan Sageer, Bilki aranta tana cewa "ai dole yau gidan mijinki xaki kwana sakeena saboda tsaro irin wannan kyau da kikayi ai xamanki gidana hatsari don baka shedar namiji πŸ˜„" suna tafiya a hankali tana qara nunawa sakeena salon tafiyar dauke hankali ba yadda take buga sauri ba kamar be karbo Al jannah.




Sunje sun tadda Sageer bayanan sukai xango a falo Bilki na nuna sakeena yanayin gidan ta kuma shigar mata da kayanta dakin da Sageer ya gyara don sakeenar. Suna xaune kuku nata aikin jera abinci a dinning tana qara fadawa sakeena kullum tayi wanka da kwalliya sau biyu da safe da kuma yamma kan Sageer ya dawo tace "kuma karki adana kaya kiyi ta sakawa mijinki mai kudine shagon sutura guda ma xai iya saya miki indai kika iya jan hankalinsa" ita dai sakeena duk abunda aka fada mata cewa take to kuma tana riqeshi daram a kanta tunda kwakwalwar babu komi a ciki.




Acan kuma su Bilki na fita Sageer yana shigowa, suka danyi hira da Maitama yake fada masa sun tafi gidansa yanxu. Suna xaune a falo sai gashi ya shigo yace "ai yanxu daga gidan naku nake naje ganota akace kun taho" Bilki tana dariya tace "Eh na dawo maka da ajiyarka ne" cikin basarwa yana bude fridge din dinning area yace "kingaji da xama da ita kenan shiya kika dawo da ita ban nema ba" Bilki tai saurin tareshi da cewa "A a wlh ai sakeena bata da matsala balle a gundura da xama da ita, kawai dai naga kyan mace gidan mijinta shiyasa na dawo da ita" yace "hmmm amma dai kin fadawa dalibar taki banason shishshigi da takura da kuma shiga abunda be shafeka ba ko?" tai murmushi cikin duniyanci tace "karka damu na fada mata kuma dama ai nadawo da itane na jarraba kwaxonta inga ko ta dauki karatun dana kusa 1 month ina mata" haka dai sukai hirarsu ya gayyacesu cin abinci Bilki tace "a a munqoshi ko sakeena?" tace "Eh munci wata kaxa me daci da madarar da aka saka magani ko anty Bil... " Bilki tai saurin xungurarta jin xata tauna musu asiri, tai shiru. Ya xunkuda kafada na nuna be damuba.




Bilki ta sunkuya taiwa sakeena radar cewa "kul kika fada masa na baki wani magani inba haka ba xai dakeki, bakomi ake fada ba kinji?" cikin tsoro tace "to" jin ance xai daketa. Ya kallesu yana daga kan table yanacin abinci yace "Allah yasa dai ba gulmata ake ba naga kun koma rada" sukai dariya Bilki tai musu sallama ta tafi.



Sakeena taci gaba da xaman takura irin na baqunta ixuwa lokacin da Sageer ya gama cin abinci ya dawo kan kujera shima ya kunna TV, sai a lokacin ya lura da kwalliyar sakeena da fitinannen qamshin da take yayi saurin dauke idonsa a kanta ya mayar kan TV don karta kamashi yana kallon ta ta rainashi. Sunyi kusan rabin awa suna xaune shi yana kallon ball, ita kuma tana xaman kare a karofi babu rini ba matsa. Ta fara bacci yasa hannu ya kwantar da ita kan kujerar ya qurawa qunshin hannunta ido yakai hannunsa ya shafa, shi dai yana son qunshi. Tara nayi ya kashe kayan kallon, ya dauki sakeena ya kaita dakinta ya qara kallon qunshin kafar ta ya sumbaci tafin qafar ya kashe mata fitila ya fita.




Tana cikin baccinta ta farka a raxane, duhu ya mamaye dakin ta laluba kusa da ita taji babu kowa ta miqe don fita daga dakin ta kwabxa karo da sif din dakin ta quma kanta, ta rangada ihun axaba. Sageer dake shirin fita harkarsa ta bariki ya jiyo ihunta ya doka tsaki yace "abunda nake gudu kenan yanxu xata hanani rawar gaban hantsi, mtseww me ake da aure?" Ya nufi dakinta ya kunna fitila ya sameta tsaye dafe da goshinta tana kuka, yana kunna fitila ta nufeshi ta rungumeshi tana cigaba da kukanta. Yayi seqeqe tsaye da hannaye a sake yanajinta jikinsa dake dama a cikin yanayin yake sai yaji gaba daya ya kasa komi, yayi qarfin halin kai xuciya nesa ya lallabata ya kwantar da ita tare da bar mata fitila a kunne. Sai dai me ?ya kadata dambu taliya taqi xama a dakin ita kadai a fadarta wai tsoro takeji ta riqeshi tamau ta hanashi fita. Ala dole ya tafi da ita dakinsa da yaga tana kuka. Ta samu gefen gadonsa ta xauna shi kuma ya cire kayan da yasaka don fita ya canja xuwa na bacci. Lokacin kuma yarinyarsa wacce sukai yanxu xasu hadu a gidanta ta kirashi me suna chinaxo yar qabilar Ibo, be daga ba sai test yayi mata saboda ganin yadda sakeena ke binsa da ido. Yace mata kawai xasu hadu gobe Sunday yanxu bashi da lfy.




Ya kwanta a gadon ya juya mata baya yayin da take xaune tana kallonsa jimawa kadan ya tashi ya kashe fitila yace "To kinxo kiyumun dundurus inbaxaki kwanta ba ki tashi ki fita falo, kin hanani fita keba wata tsiyar xaki iya bani ba" Ya koma ya kwanta yana mitar "haka kawai daga temako na debowa kaina jangwam tun kan

Please Login or Register in order to submit comment