Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wata ya cika kwana 30 aka bawa sakeena kudinta na aiki dubu 3000 tare da sabulai da kuma kwancen kaya da anty ta bata. Murna gurin sakeena ba a magana ta bawa Iya kudin. Iya tace 'sakeena ai kudinki ne kiyi yadda kikeso dashi' tace "Iya so nake dama ki kaini asibiti a wankemun haqurina da kudin" Iya tace "to sakeena ai haqqin kine ranar litinin sai muje inkin dawo daga makaranta"



Ranar litinin sukaje asibitin murtala, bangaren dental suka biya 2800 huka hau layi. Akaxo kan sakeena ta shiga, mutumin ya haska bakinta ya saka safa yace "ki daure sosai bakinki yayi datti da yawa sai an kankare dakyau amma fa da xafi" sakeena tace "duk zafi xan daure, inaso a dena kyankyamina" yace "yawwa yata ki daure in wanke miki tas" ya fara kankare mata bakin yana jini ta daure kamar yadda tace, ita kanta da aka nuna mata dattin da aka wanko a bakinta saida taji kyama. A qarshe dai sakeena baki yayi tas haqora har daukan ido suke, aka nuna mata mudubi tai dariya sai taji ta burge kanta lokacin da taga jerarrun qananun haqoranta a mirror. Aka saka mata dokar wanke baki da daddare inxata kwanta da kuma da safe.



a ranar dai sakeena duk inda ta shiga sai dariya kamar anmata kyautar miji.


A wannan term din babu lefi sakeena ta tabuka dan taxo ta 36 acikin su 54. Baba yayi murna kuma ya qara qarfafawa sakeena gwiwa. Da aka koma hutu aka canja aji su Sakeena an shiga SS 1.

**** **** **** **** *******


A hankali Bahijja ta maida sakeena baiwarta kamar yadda ta qudure a zuciyarta, da farko aikin sakeena a gidan shara ne da wanke wanke sai kuma taya ta girki. Amma daga baya saita qara mata da rainon Waleed da kuma wankin uniform din yaranta na makaranta kullum. Abu yacigaba a watan sakeena na 5 tare da ita taga sakeenan ta fara wayewa ga kuma tsafta ta fara kankama a jikinta tana kuma kwalliya da kayan data bata saita kori almajirin dake musu wanki duk kuwa da ba ita ke biyansa ba, sannan wankin ya dawo kan sakeena kullum xata wanke kayan da yaranta 4 suka cire sannan ta qara mata da girkin gidan wanda ta koyawa sakeenan tun farkon xuwanta kuma ta iya. Ya kasance kullum tana cikin aiki koda tayo kwalliyarta daga gida intaxo ta fara bauta xaka nemi kwalliyar ka rasa kuma duk a 3000 duk wannnan tarin aikin. Bahijja kuma tayi hakane saboda kar mijinta yaga sakeena da canjin abincin yasa ta xama mace sosai ya kyasa shiyasa kullum tana cikin ruwa tana aiki. Tsakanin Sakeena da Barrister kuwa girmamawa ce irinta bawa da uban gida, dan in yana gidan iyakarta tsakar gida da kitchen a dokar anty Bahijja sai ya fita take da hurumin shiga falo. A bangaren yaran Anty kuwa sakeena bata da matsala ta jasu a jikinta kuma suma basa kyamarta sukan yi mata magana da turanci kamar yadda sakeenan tace su dunga yimata dan ta iya, inbata ganeba su fassara mata. Wani lokacin Alhaji babban dan anty har karatu yake koya mata.



A bangare guda kuma Iya ta tsani wannan aiki na sakeena dan bata da lokacin kanta kullum cikin bautar Bahijja take da danta Iya ne da sakeena ta dade da barin aikin nan duk kuwa da irin temakon da aikin kewa musu amma Iya dake babbace me hankali ta fuskanci yadda Bahijja cikin hikima take dakushe sakeena dan karta samu miji ta bar bauta mata.




Bata taba gajiyawa da aikin da take ba duk kuwa da tasan tana yini akan qafafunta cur, hakan na nufin rashin wayonta ko rashin sanin ciwon Kai ne? Kudin aikinta suna toshe mata abubuwa da dama duk kuwa da qanqantarsu, aciki take temakon Baba da rage masa nauyin siyan sabulun wanka ko man shafawa duk wata dan tana tausayin dattijon me qoqarin ganin ya sauke nauyin iyalansa amma kuma hakan nafi qarfinsa saboda tsadar da kayan masarufi suke shiyasa kullum al amarin gidan qara damewa yake. Acikin kudin dai takan dora jarin Iya na kayan miya Inya nemi karyewa, A gefe guda kuma takan dan ajiye wani abu a banki domin tunkarar matsalarta ta ido don abun na damunta sosai. Bata da matsalar abinci don ta samu cima me kyau a gidan Anty dan ita Bahijja sam abun hannunta be dameta ba duk abunda akaci xata ajiyewa sakeena nata, saboda haka safe, rana, dare sakeena nada kwano a gidan kuma abinci be kyau intaga dama taci acan intaga dama ta taho dashi suci da iya wani lokacin har su Hajjo kan samu dan sakeena ke xubawa kanta abinci inta gama kuma koxata kwashe duka Anty bazatai magana ba tawannan bangaren bata da matsala. A duk sanda Iya tayi mitar bautar da Sakeena kewa Bahijja tayi yawa sakeena kanyi dariya tace "iya aini ma ina morarta, ta bani abinci sau uku a rana babu geji, ta bani kwancen kayanta harda su turare inta rage duk tabani ta bani sabulu in wanke kayana da naki sannan ta koyamin girki wanda ke kanki kinji dadin hakan, sannan yayanta su koyamun karatu qarshen wata a bani 3000 kuma da sallah suyumin dinkin sallah. Nikam kome xan mata ban fadi ba kuma ban taba daukan bautar da nake mata mugunta ba, a dalilin haduwata da Anty wadanda suke kyamata sun xama qawayena Iya kiyi haquri wataran sai labari, aikin nan yana rufa mana asiri" A bangare guda kuma ba tun yauba Sakeena ta gane ta fada soyayyar yaya Deni irin makauniyar soyayyar nan wacce ake yinta babu ji babu gani, ada bata fuskanta ba amma tun randa ya raba fadansu dasu Amina ya riqe mata hannu ta gane tana sonsa kamar ta cinyeshi duk kuwa da qaracin shekaru irin nata. Abun na damunta duk kuwa tana mutuqar qoqarin dannewa amma hakan kan faskara a duk sanda taga yaya Deni jikinta kan kama rawa babu ji babu gani kamar mazari ga faduwar gaba a duk sanda taji muryarsa ko aka ambaci sunansa. Amma kash! Ta fuskanci Deni yana mantawa ma akwai wata halitta me sunan sakeena a gidan. A waje guda kuma tana ganin wani gagarumin yaqi a gabanta a duk sanda asirinta ya taunu tanasan Deni. Mutumin da uwarsa da yawansa suke burin ya auri yar hamshaqin me kudi dan su huta sukaji SAKEENA ABBAKAR LIMAN na azabar sonsa wacce a gurinsu take wulaqantacciyar yar qauye kuma baiwar Bahijja kamar yacce suke kiranta yanxu.




Duk sakeena na wannan tunani ne yayin da take kan hanyarta ta dawowa gida daga gidan Anty don xuwa makarantar islamiyya ta yamma. A fili tai magana bayan gama tunaninta a inda take cewa "To inma nidin baiwar Anty Bahijja ce kamar yadda yawan mutane ke fada sai me? Nidin ai ba wata tsiya bace da xan damu dan na xama baiwar wacce ta fini ku..., " maganarta ta katse yayindata kwabxa karo a dai dai qofar dakin su saddiq, ya riqeta yayin datake shirin kaiwa qasa ya girgaxa kafadunta yace "ke mahaukaciya ce? Kina tafe kina magana ke daya ba dole ki buge mutane.... " shima tasa maganar ta katse lokacin da ya tsinci manyan idanun sakeena cikin nasa xuciyarsa tai wata irin bugawa, ita dai sakeena batasan sanda ta washe masa fararen jerarrun haqoranta ba. Yayi gaggawar runtse idansa tare da sakinta ta fadi qasa shi kuma yayi waje. Ita dai sakeena tun daga lokacin har ixuwa kwanciyar baccinta ta jita cikin wani irin nishadi wanda tunda Allah ya halicceta bata taba jin irinsa ba, lokaci xuwa lokaci takan yiwa kanta murmushi ta shafa kafadarta gurin da hannun Deni ya taba tai dariya. Iya dake lura da ita tun daxu tai tsaki tace "sakeenatu! Anya kuwa lfyarki yau? Tun daxu kike dariya ke kadai sai magana nake miki kin share ni" tai saurin dawowa hayyacinta tana sunne kai tace "Yi haquri Iya banji ki bane, dama mafarki nayi naci jarrabawar qualerfiying"




A wata na gaba Deni ya tafi kwara state (illori) bautar qasa, ranar daya tafi sakeena ta labe a bandaki taci kukanta kuma tundaga ranar ta samu kanta cikin kunci, bata magana sai ta xama dole in antambayeta tace bata da lfy a lokacin ta lura soyayyar Deni itace qaddararta kuma akwai qalubale a gabanta babba.




Kamar yacce yake ga al adar mace me irin shekarunta itama tayi samari, duk da in akaxo sallama da ita ba fita take ba sai Iya ta tilasa mata amma itama iya daga baya ta daina tilasawa sakeena fitar tun bayan da sakeena ta xauna tai mata bayanin yawancin masu xuwa gurinta ba santa suke ba da yawa daga ciki in sunxo suna amfani da talaucinta da suka fuskanci sakeenan na cikine suna tallata mata soyayyar watsewa wanda hakan yasa ta tsani wani ya bude baki yace yana sonta.




Ana haka jarrabawarsu ta qualafyn ta fito cikin rashin sa a sakeena dai bataci ba, yayin da Amina kuma taci wanda hakan ke nuna sai anbiyawa sakeena kudin jarrabawar NECO da WAEC daga aljihun babanta taci kukanta dan tasan bata da gatan da xa a biya mata yayin da Amina dadi kamar ya kasheta dan tana ganin qarewar karatun sakeenan yaxo.


Baba ya rasa inda xaisa kansa akan matsalar kudin jarrabawar sakeena dan yanajin kunya ace ya kasa biya mata wannan kudin yarinyar da tasan ta dauke masa wata wahala amma shi tata tazo ya kasa tabuka wani abun kirki? Dan haka yaje gurin Alhajin da yakewa aikin driving ya roqe ya ranta masa kudi wanda yace ya dunga diba duk wata a albashinsa na har yagama biya. Dake yaji harkar karatu ce ya bashi babu musu.




A gefe guda kuma Iya da sakeena na nasu kokarin inda aka fasa bankin sakeena amma abunda yake ciki bekai ko rabin kudin jarrabawa daya ba kamar yadda suka xata. Sakeena yau a gidan aikinta jikinta a sanyaye qalau lokaci xuwa lokaci tana share hawayen yankewar karatunta ko kuma maimaita ajin SS 2. Alhaji babban dan Anty ya ganta tana kuka yaje ya fadawa Anty. Bayan dogon lallashi da ban baki dakyar anty tasha kan sakeena ta fada mata matsalarta.





Sai data gama aikinta tsaf ta dauki kwanon abincinta wanda damuwa ta hanata ci xata tafi gida Anty tai kiranta ta amsa kiran anty ta bata qunshin kudin da batasan ko nawa bane tace "gashi sakeena kyauta na baki kije ki biya kudin jarrabawa, duk sanda kike buqatar temako a kan karatu ki fadamun xan temaka miki ki dage da neman ilimi dan muma dashi muke taqama" godiyar da Sakeena tayi har saida anty tace ya isa ta taho gida cikin wani irin farin ciki da kwarin gwiwa da farin ciki take fadawa Iya. Itama Iyan taji dadi wannan abu da Bahijja tai ya faranta ranta kwarai. Da Baba ya xauna cin abinci suka sameshi da wannan xancen shima yayi murna kwarai kuma ya ciro kudin daya karbo ya bawa sakeena yace shima ga nasa temakon sakenna ta dunga kuka tana masa adduar gamawa da duniya lfy, suka hada kudi 30k wanda hakan ke nuna sakeena ta samu kudin jarrabawa guda 2 wato waec da neco a memakon su Amina da gwamnati ta biya musu kudin jarrabawar WAEC kawai. Amina dai murna ta koma ciki Sakeenan datake rainawa ta fita, dama haka lamarin ubangiji yake.




Baba da kansa yaje biyawa sakeena kudaden jarrabawar ya kawo mata receipt. Suka kuma durfafa karatun jarrabawar kammala secondary.


Wannan alheri da Bahijja taiwa sakeena ya kuma saka sakeena tsunduma cikin bautar Bahijja ka in da na in yayin da Bahijjan ta kuma sakankancewa ta miqe qafa ya xama ita da gidanta kofi sai taga dama take daukewa komai Sakeena keyi mata. Yayin da gefe guda kuma Barrister mijin Anty yake saka ido a duk lamuran sakeena da irin bautar da takewa gidansa da yayansa ba tare daya bari shashar matarsa ta gane yana da alaqa da wanzuwar sakeena a gidan ba, dan ita a ganinta tana da wayo yayin da ya raina wayonta kuma yake amfani da nasa wayon da kwarewar aiki cikin nata wayon.



Hajia ☺
[7/31, 2:01 PM] Reine Ghana: πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€MUQADDARI NEπŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€2018πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€



5⃣

RAHMATULLAH (Hajia)


Yau sun tashi da baquncin Deni zai dawo bayan kammala Bautar qasarsa a kwara, yayin da su Sakeena suke dab da fara fara xana jarrabawar kammala secondary.


Dake wata yayi 20 ya xamana babu kudi a hannun Baba, tun safe ya fita da nufin samo dan abunda ya sawwaqa asamu a dafa kodan dawowar Deni bai dawo ba sai bayan laasar ya shigo jikinsa a sanyaye dan haka ya gama gararinsa bai samo komai ba. Hajjo naganinsa hannun babu komai tai kicin kicin da rai tace "Tun dazu nake jiranka ga magruba ta kawo kai ko karfanfana babu a gidan balle abunda yarannan xaici inya dawo" jikinsa a sanyaye yace "wlh Hajjo tun daxu nake yawon neman abunda xan kawo muku bansamu ba, Dan Allah ki ranta kudi ayi duk abunda xa ai inasamun fansho na xan baki" tai saurin katseshi da cewa "bani da ko sisi kudina tun jiya nasai geron gasara dashi, kuma ai muguntarka akan yayana yake tashi canike kwanaki haka kawai dan san gwaninta ka dauki kudi ka biyawa sakeena kudin jarrabawa amma ni yanxu nawa dan ya tafi shekara guda yau xai dawo amma ko ruwan naira 5 baka siyo da sunan inyaxo yasha ba" ta qarasa tana hawaye. Jikinsa ya qara sanyi domin shi ba a son ransa dansa xai dawo amma babu ko kwayar hatsi da xa a dafa a gidansa. Iya dakejinsu tana cikin daki ta tattaro duk cinikinta ta fito ta miqawa Baba tace "gashi malam iyakacin abunda yake hannuna kenan kayi haquri" ya karba yace "Allah yayi miki albarka Hansatu" ya miqawa Hajjo yace "gashi asamu ko shi kadai a dafawa taliya yaci, mu kuma bari inkuma fita inga abunda hali xaiyi" ta harari kudin tare da cewa "ni kuma Allah ya tsine min ko? wlh bazan karbi kudin kishiya ba taji dadin yimin gori" ya ajiye kudin yafita lokacin ana kiran sallar magrib.



Sakeena dai dake yau alhamis tana gidan Anty tundaga tasowarta daga makaranta har yanxu da ake sallar magrib, da kyar ta yakice aikin taje tai sallah ta dawo tana lazuminta na HASBUNALLAHU da Iya tace ta dungayi kullum da magriba 313 da asuba ma 313. A gefe guda kuma tana duba girkinta yayin da Anty da yaranta kecan falo suna kallo. Abun na Anty babu ko shaawa keda gidanki ace kin koma kamar baquwa sannan mutum tun qarfe daya yake tsaye yana miki bauta kamar inji. Sakeena na gama girki ta juyeshi a kula takai kan center carpet din falo ta ajiye tare da kawo ragowar kayan cin abinci ta jera taje ta tsuguna tana wanke kayan da tai amfani dasu. Tun dazu ya shigo yake tsaye yana kallonta duk da alamar gajiya a tare da ita dan ta yini tana aiki amma hakan be nuna ba a yanayin kazar kazar dinta. Ya lura yarinyar kyakykyawace irin kyan da saika nutsu xaka ganshi ba tafar daya ba, kuma yanaga shine dalilin Bahijja na takura mata da bauta dan ta dakusar da kyan nata. Ta dago bayan ta gama wanke wanken gabanta ya yanke ya fadi ganin Barrister a tsaye yana kallonta, ta tsuguna tana yimasa barka da dawowa. Bai amsa ba sai qara kafeta da idonsa da yayi, sakeena taji duk ta takura duk da doguwar riga ce a jikinta burmemiya wacce Anty ta bata kuma ta hana a rage mata ita acewarta maje gaba ce. Ya miqo mata tulin ledojin dake hannunsa masu dauke da tambarin gidan abincin JALSA tasa hannu xata karba ya hada hannunsa da nata hannun ya riqe tare da ambatar "SAKEENATU" tai saurin sakin ledojin tai kicin tana haki ta dafe kirjinta. Batasan iya lokacin data shafe a gurinba sai ji tai Anty na kwala mata kira. Ganinsa a xaune a kusa da matarsa kamar bashi ya riqe mata hannu yanxu ba yasa gabanta faduwa kodai ya fada mata abunda ya faru yanxu? "sakeena dauki kular abincin nan ki tafi da ita gida, kinga dear yayo mana take away" maganar Anty ta katse mata tunanin ta, ta janyo ledar kayan daya siyo ta dibawa sakeena kayan kwalam dangin su burger da shawarma sai gasashshiyar kaza ta hada mata da kwalin chivita tace "ga naki, sai da safe ki gaida Iya gobe ki tahomun da bushashshiyar kubewa tuwo xaki mana gobe" da sauri tabar dakin bayan ta dauki ledar da kular abincin saboda kallon da Barrister ke binta dashi.




Baba dai har aka kira sallar isha yana neman abunda xai kai a dafa a gidansa amma bai samu ba, sai bayan ya idar da sallah ne ya yanke shawarar xuwa wurin wani mai kanti domin karbar bashin garin rogo da suga duk kuwa da tsanar karbar bashi da yayi amma kuma inya duba iyalansa nacan na shirin kwana da yunwa sai yaga gara ya karya billensa ya karbi bashin. Yana rabe a gefen kantin yana jira mutanen dake siyan abu su ragu don yana jin kunyar fadar abunda ya kawoshi a gabansu kuma be xama lallai mai kantin ya bashi ba saboda tun wata yana da 10 yake cin bashinsa kamar yadda aka saba wanda xuwa yanxu kudinsa sun taru akansa sosai.



Sakeena na tafe tana tunaninta, me abunda Barrister yayi mata yake nufi? Shima dan iska ne kamar sauran maxan da ke neman yan aikin gidansu ko me? Amma bataiwa Barrister zargin hakan dan anata tunanin in akace ta fadi maza masu halin kirki yaya Deni shine no 1 a gurinta bayan shi kuma Barrister ne na 2. Harta gota Baba tana tunani bata ganeshi ba, har tayi gaba sai kuma ta dawo ta matsa kusa dan ta duba ko shidinne kuma meyake a dai dai wannan lokaci da akasari anfi samunsa a gida cikin iyalansa. Babu wutar lantarki shiyasa saida taje dab dashi ta shedashi, ta rage tsawo tace "sannu Baba, baka tafi gida ba?" yace "yawwa sannu sakeenatu andawo daga aikin ne?" tace "eh har na wuce na ganka nace bari injiraka mutafi gida tare" ya danyi shiru kafin yace "kayya sakeena da kin tafi tunda nasan a gajiye kike, ni ina jira aragune in karbo mana abunda xamuci" wani irin tausayin dattijon ya dirarwa sakeena, lallai Baba mutumin arziqi ne a wannan zamanin masu hali ma ba duk suka damu da sauke nauyin iyalansu ba bare mara hali. Tai qasa da murya tace "Baba kaga taho mu tafi taja hannunsa," babu musu ya bita dan shi dinma ya gama yarda da halin kirkin sakeena. Suna tafiya a hankali tace "ai Baba basai ka karbo komai ba, kaga abinci na taho dashi daga gidan aikina bayan nagama me gidan yaxo musu da abincin otel shine sukace intaho da wanda na dafa ka ganshi?" ta fada tana nuna masa kular. Yace "to Alhamdulillahi kuma zai ishemu sakeena?" tace "sosai kuwa Baba ai cikin kular ne riqe kaji" yana dariya ya daga kular cikin yabawa da quruciyar sakeena mai cike da nutsuwa. Ta nuna masa ledar tace "wannan kuma kaza ce a ciki da wasu kayan yan gayu" yayi dariya suka rankaya gida. Kamar tare suke da Deni yana shigowa suma suka shigo, aka kacame da murnar dawowarsa. A taqaice dai a wannan dare dai fried rice din da sakeena taxo da ita daga gidan Anty akaci aka qoshi harda kazar da aka bata Iya ta rarraba.



Sakeena kuwa sai satar kallon Deni take wanda a wata 11 da tai bata ganshi ba babu abunda ya ragu daga soyayyarsa dan yana daya daga cikin dalilinta na qin kula mane aurenta dan ta rasa da wane ido xata fara kallon wani namiji daba Deni ba, ta rasa da wace zuciyar xata fara son wanin Deni, bata da wannan qarfin halin ko kadan. Tana cikin azabar soyayyar me matuqar wahala wacce batasan ta inda ta shiga ba balle tasan hanyar da xata fiddata. Ta lumshe ido dai dai lokacin daya gifta ta kofar dakin Iya ta shaqi qamshin turarensa mai qarancin kudi cikin sanyin murya ta furta "Nuraddeen" wannan furuci karaf a kunnansa yayin da yake shirin fita. Ya juyo ya kalleta idonta a lumshe batasan ma yana gurin ba, tabbas xatonsa ya xama gaskiya wannan yarinya ta dade da fadawa tarkonsa. Yayi shuumin murmushi ya fita yana cije lips dinsa a ransa yana cewa "tsuntsu daga sama gasashshe"



A washegarin dawowarsa suna xaune da safe suna shan hantsi saboda yanayin sanyi da aka fara, Amina kewa Fiddausi qunshi saboda bikin qawarta da akeyi kuma yau da yammaci xasuje luncheon. Fiddausi ta kalli Amina tace "Amina yanaga kinamun wani abu kaman bishiyar dogon yaro? So nake aimin dan banxan qunshi kinsan mijin nata me masifar kudine kuma abokansa xasuxo luncheon din inasone nima insamo nawa mijin a cikinsu mu warke" Amina ta harareta tace "da Allah malama ke gajen haquri ne dake ki bari mana kiga nagama inbe kyauba sai kiyi qorafi" ta qarasa tana murguda baki kamar ba fiddausi ce gaba da ita ba. Hajjo dake uwar banxa ce sai tace "ke Amina kiyi mata me kyau kinji ko? Kema intasamo me kudin ai a dadinki, dama nagaji da wannan xaman naku rida rida babu miji kema gashi kina shirin gama makaranta" Amina ta zunburo baki tace "to Hajjo wazai ganmu yace yana so bamu da kaya? Ai yanxu samari basa kula macen da bata da kaya" Hajjo tace "amma ina iya qoqarina akanku ko? Duk jarina ina yake tafiya? Ko kun taba kawo anko banyi muku ba?" Hadixa dake gefe guda tana danna waya tayi kwafa tasaka baki cikin xancen tace "ai de yaya Deni ya gama karatu, in shaa Allahu ya kusa samun aiki mu huta wannan talaucin, Hajjo da kike cewa munqi aure ai yanxu ba a auren diyan talakawa" Fiddausi ta dora da cewa "ai wlh in talaka ma ya haifeka ya cuceka, da ana bada xabi yaushe xaka xabi gidan talaka a matsayin gidan ubanka?" Sakeena dake yankewa Iya farce ta shiga cikin hirar da cewa "ku godewa Allah, haka Allah yaso ya ganku kuma banda abunku ina lefin Baba? Yana iyakar qoqarinsa akanku. Ni ina fatan inama na girma da nawa uban koda gyartai ne inkirashi da BABA in nunashi a ko ina ina alfari da ubanane" Amina ta katseta da cewa "to monitan dawanau uwar yan tsari munji rufe mana baki munafuka wai ita me hankali, bazaki burgeni ba sai kin auri gyartai tunda naki uban be xama gyartai ba sai ki xama matar gyartai" Sakeena da yanxu bata cika ragawa Amina ba tace "wlh wanda nakeso ko yafi gyartai qasqanci ina sonsa a haka kuma indai shima yana sona kamar yadda nake sonshi to a shirye nake da in zauna dashi koda xan kwan da yunwa nidai kawai abunda nasani ina sonsa qarshen soyayya" a tare da fiddausi da Hadixa suka hada baki wajen cewa "wanene wanda kike so din? 😳" Sakeena tai fiki fiki da ido kardai ta saki layi har sun harbo jirginta tanason Deni? Dariyar Amina ta katse mata tunani a inda tana dariyar tace "kuma dai in banda abunku wannan kucakar ce tasan wata soyayya? Itafa wannan babu abunda tasani sai bautar gidan Bahijja, kun tsaya kuna kula shirmenta. Ai kawai Allah ya kawo mana me kudi lokaci daya mu tashi mubarta dan wannan kan asamu me kwasa za a dade kullum tana yawo burum

Please Login or Register in order to submit comment