Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadan surka." ya tasata suka fito ta gaida matarsa har qasa da sunan yar aikice ita sannan ta koma tai jinyar durxar da Yusuf yayi mata, daga wannnan rana kuma kullum inya tashi aiki ko in xai tafi saiya biyo ta gurin Hadixa wacce bata da kwana sai wannan xuwan kuma baya xuwar mata saiya bata pills tasha acewarsa karta dau ciki ta haife masa irin tsiya wato Hajjo, in kuma ya gama ya biyota da baqaqen maganganu, kuma daya abun takaicin shine koda tana cikin aiki kuma ko agaban waye har mahaifiyarsa inyaxo hannunta kawai yake danqa ya jata keee yayi daki da ita kowa yasan abunda yake mata don sau tari suna jiyo ihunta amma babu wanda ya taba magana. Hadixa ta fita hayyacinta ta sare da rayuwar duniya ta fara nadamar da bata da amfani, jarabar Yusuf da bautar da ita da uwarsa keyi ya saka duk jijiya ta fito a jikinta rudu rudu kamar batacin abinci har mamaki take dama maxa haka suke ko kuma Yusuf ne yayi mata lumbu lumbu yayi amfani da kwadayinta na son auren mekudi ya aureta? A duk sanda ta fadawa Hajjo halin da take ciki sai dai tace "Kiyi haquri Hadixa tunda basa barinki da yunwa, ni yanxu anan har horon yunwa akemun ga dan uwanku ko waiwayata bayayi" Hadixa kan fashe da kuka tace "Hajjo to meye abinci inbabu kwanciyar hankali? In Yusuf ya kashemun mahaifa fa?" Hajjo dai sai haquri don babu yacce xatai itama ta kanta take.


Bangaren Fiddausi dai abun da sauqi-sauqi wai naushi a ido, domin ita tunda ta yadda ta xama baiwar Hajiya uwargidan Musa ta xauna lfy intagama aiki har turata ake taje ta dan huta kafin lokacin wani aikin, ana cikin haka ta samu ciki a satar hanyar da Musa yakeyi yana xuwa gurinta. Ranar da cikin ya bayyana sunga jalala gurin Hajiya domin sasu tayi agaba kamar ta kama kwarto da karuwa tana tambayar ya akai Fiddausi tayi ciki tunda bata da kwana? Musa cikin tsoronta yace "Nima bansani ba, domin ba cikina bane ta fadi inda ta samo" Fiddausi cike da tsoron sharrin da Musa yake shirin yimata tace "Wlh azim nasane Hajiya shiyake xuwa gurina in bakyanan ko kuma inbashi da aiki a kasuwa har tsire yake siyomin yana bani inci kafin yayi" Hajiya tai dariya ta gyara xama ta harde qafafunta akan kujera tace "Au ashe amanata kuke ci ko? Ga banxa mara wayo ta baxa dukiyarta kuna ci kuma kuna ha'intata, ai wannan xaku iya kasheni ma, dole in dau mataki da nufin yimuku warning don gujewa fadawa tarkona anan gaba. Musa, Fiddausi ku kiyayeni wlh bani da mutunci ni kaina tsoron kaina nake in nayi wani abun." matakin da Hajiya ta dauka akansu shine burge cikin Fiddausi dan 4 months data gayyato wani likita yayi har gida, Fuddausi tasha wahala ta jigata kamar baxatai raiba ta dunga shatatar da jini amma Hajiya tana xaune tana kallo ko ajikinta a cewarta ma cikin shege ne tunda ba'a nemi ixininta ba kafin ayi shi. Ta jiqa xobo ta dunga durawa Fiddausi a matsayin abunda xai dawo mata da jinin data xubar (wai dama xobo yana dawo da jini? 🤣) Kwana uku Fiddausi tadan watstsake daga azabar kwakwule cikin da akai mata amma tayi fari qal alamar babu wadatar jini a jikinta kuma aranar Hajiya tasa ta karbi aikinta babu tausayi.


Shi kuma musa nasa hukuncin shine lafta masa uban aiki a kasuwa wanda xaiyini sur yanayi ta inda bashi da lokacin kansa ma balle ya tuna wata Fiddausi ko da dawo gida ma a gajiye yake kwanciya yayi ta baccin gajiya ko ita Hajiyan baya iya tabuka mata komai balle Fiddausi. Daya matakin kuma shine cire masa duk wani tallafi tunda har yana samun na siyawa Fiddaausi tsire. Da wannan ta rufe qofar alaqar cin amanar Fiddausi da musa (a fadarta) sai dai ya hangi giftawar Fiddausi intana aiki a sashin Hajiya. Kuma dake muguwar shedaniya ce ta Kai Fiddausi gurin teacher aka rufe mata bakinta babu wanda take iya fadawa halin da take ciki balle aimata temako sannan tasakawa qafarta kwado ko shaawar fita daga gidan batayi, babu abunda ta sani sai bautar Hajiya kwatan kwacin irin bautar da sakeena taiwa Bahijja matar Bar Adam, Fiddausi dai yanxu ko Allah bata tsoro yadda take tsoron Hajiya.


Saddiq kuwa har kullum godewa Allah yake da ya farkar dashi da wuri ya dawo daga rakiyar Hajjo kafin rayuwarsa ta watse kamar ta sauran yan uwansa.


Hajjo dai ta rasa yacce xatai yayan da takeso take taqama dasu duk sun watse kowa ya kama gabansa yana fuskantar matsalar abokin xama ita kuma gata a jabe a gida ita da Amina wacce bata da cikakken hankali yanxu saboda rasa Sageer, babu aikin komai sai baqin talauci wanda ko 5 naira din pure water gagararta take, ta fara nadamar barin sana'arta da tayi ta saida gasara, haka kawai ganin hadari yasata wanka da kashi, daganin Deni ya samu aiki ta dena saboda danta yayi kudi tafi qarfin saida gasara, gashi yanxu yayi auren jari ya cika burinta amma matar ta janyeshi. Bata da mataimaki yanxu sai Saddiq wanda bawani abun arxiqi yake samuba a kasuwa sai kuma Zahra da take shafe kusan wata guda bata leqo ba. Ana cikin haka tasamu 500 daga gurin Saddiq da yasamu yan kudi, cikin rawar jiki ta sayi gero tayi gasara ta aika maqota aka fada ta dawo dayin gasara. Abun dariya dai gasara tai kwantai bata siyuba domin Hajjo ta xama mujiya acikin matan unguwar tun akan xuwa kotunsu dasu Laraba, mutum biyu ne kawai suka shigo siya suma kuma yar mata da magana sukayi da habaici da cewar "A a uwar Alh Nura surukar Haj Surayya kuma gasara aka dawo siyarwa? Ya akai aka haihu a ragaya?" qarshe dai gasara dai doyi tayi aka wanketa. Hajjo ranar har kuka tayi don baqin ciki, Amina dataga tana kuka itama ta farayi suka hadu suka dungayi babu me lallashin wani. Ala Dole ta miqe qafa taci gaba da xaman kashe pant sai dan abunda Saddiq ko Zahra suka bata. Yayin da Iya keta fama da arziqi.



Bagaren Deni kuwa da amarya Surayya abun suma sai a slow, domin Deni tun ranar daya sheda daurin auren sakeena da Sageer kuma yagansu rungume da juna ana musu photo ya nemi kwanciyar hankali ya rasa, daya abun takaicin Surayya ta dauki wayarsa tayi status da pics din Sakeena da Sageer na aure wanda ta dauka da wayar tasa aka dunga tayasu murna da fadar dacewarsa wasu friends dinsa da sukasan ya taba auren sakeena suka dunga yaba daqiqancinsa na rabuwa da ita, shi sai a lokacinma yasan abunda Surayya tai, cikin sauri ya goge hotunan ya kuma rufeta da fada, bata damuba tace "I'm sorry darling, i luv u" yayi tsaki shi wannan hali nata ya fara damunsa babu dama tai abu ya nuna bacin ransa sai tace masa "I luv u" Kamar batasan abunda kalmar ke nufi ba. Duk da ya goge nasa hotunan be tsiraba domin Saddiq kullum cikin yin sabon statuz yake da hotunan nasu kuma yanayine saboda Deni, gashi shi kuma kamar dole inyatashi saiya duba status din saddiq. Daga haka wata masifa ta aureshi babu dama ya kwanta sai yayi mafarkin sakeena rungume da sageer, ya rasa inda xaisa kansa kullum sai yayi mafarkin kamar ibada, ya xama wani irin mugun masifaffe wanda masifarsa sam bata damun Surayya domin inyanayi sai taita dariya kamar taga sabon kamun hauka ko kuma taita danna waya, inyagama tace "I LUV U DEEN" aikinma ba wani maida hankali yake akaiba donma Allah yasa ya gama karatu da baxai iyashi ba a wannan halin da yake ciki. Inya fita tun safe baya dawowa sai dare, yaxo ya tarar Surayya wacce ta dawo tuntuni daga nata aikin ta caba kwanlliya masu aiki sun gyara gida kuma sunyi abinci wanda hakan baya burgeshi sam.


A cikin wata uku da aurensa da Surayya yayi matuqar gundura da xama da ita saboda wasu halaye nata kamar rashin damuwa dashi da kuma al amuransa indai ba a shimfida ba, tana kulawa da shimfidarsa kodan biyan buqatarta bayan haka kuma babu ruwanta da komi nasa, to ita kanta nata al amuran masu aiki ke matasu. Ta bangaren kwalliya kam babu matsala xai iya cewa a iya wannan xaman nasu na wata 3 betaba ganinta babu makeup ba ko kwanciyyar bacci xasuyi saita caba kwalliya, ta wannan banqare kam Surayya ta samu excellent, takan kashe kala qarshe yawanci tafi saka qananan kaya intana gida, natives kuma sai xata fita. Intasaka qananan kayan kuma da sunan kwalliya Deni kanji takaicin ya rufeshi musamman inya kalli busashshen qirjinta da kuma qarmasassun cinyoyinta da bayanta wanda dasu tayi ciko ta jashi ya aureta, yakanji kamar ya rufeta da duka saboda kayan basa qara mata komi sai qara fito da munin halittarta. Surayya doguwace mara rama wacce datana da cikar halittar qirji da qugu xa ai irin matannan masu cikar halitta da kuma tsaho da kauri (irin halittar Deni) amma saboda rashin wadancan abubuwan dana lissafa saita xama doguwa sololo kamar namiji (ina ruwan sangal modi🤣) intayi shigar takan tuna masa da sakeena wacce yake tuno hips dinta cikin wandon jeans, ya lumshe ido wanda hakan kesa Surayya taita karairaya a xatonta burgeshi tai, ingaji da haukan lankwasar da take da sunan yanga yaja tsaki ya bar mata gurin. Bayan wannan komi masu aiki keyi har gyara gadon baccinsu, har xuwa kan wankin undis dinsa da nata. A tsarin Surayya babu inda masu aiki basa shiga a gidan koda suna kwance takan iya kiran maid ta miqo mata ruwa ko wani abun daban, da kansa yayiwa kansa fada yana tsince undis dinsa yana wankewa domin da kunya maid taga qazantarsa. Baxai ce da Surayya qazama ba duk da masu aiki ke mata komi domin xakajita tana musu tsawar su gyara nan su gyara can ita batason qazanta, sannan duk da bata shiga kicin tana sakawa ayi abincin da koda babu dadi to da tsafta. In kuma bata raayin cin abincin gidan takanyo order akawo mata har gida suci ita da Deni. Xuwa wannan lokaci wato wata uku, kanwa takar tsami kwarnafi ya kwanta, kuma gishiri ya fara sauka daga kan kaxa a tsakanin Surayya da Deni don haka magungunan mata da take amfani dasu wajen mallakarsa basu cika tasiri akansa ba ga kuma qarin damuwar sakeena datasaka Deni ya kuma burkicewa amma dake Surayya bata cika damuwa akan abuba bata lura ba balle ta farga da wuri.


Ana tsaka da hakane office dinsu suka debi xaqaquran ma'aikatansu don turasu wani cox a head office dinsu dake Lagos. Kuma cikin sa'a akai dace sunan Deni yana ciki. Ranar ya dawo cikin dare kamar yadda ya saba a yan kwanakin nan. Tuni Surayya ta kwanta bacci kamar yadda ya xata. Ya kimtsa yayi shirin bacci yaje dinning area ya saka tuwon shinkafar da akai a matsayin dinner amma ko loma biyu beyi ba ya rufe ya tashi duk kuwa da yunwar da yakeji, dalili kuwa shine tuwan ya jiqe cakaf ya narke kamar ba a daren akayishi ba wanda hakan ke nuna anmaka masa ruwan sanyi bayan antuqa shi. Ransa ya baci ya nufi bedroom yana tunanin girkin sakeena lokacin da suke tare duk da suna cikin baqin talauci amma duk randa suka dan samu damar yin girkin maneji takan yishi cikin tsafta kuma me dadin gaske kamar girkin da aka kashewa kudi. Ya kuma jan tsaki dayaga Surayya kwance cikin wata yar ficiciyar rigar bacci wacce ta qara fito da rashin qirarta, ya tabbatar da ajikin sakeeena yaga wannan rigar saiya kusa rasa hankalinsa saboda kyan da xatai mata. Ya qarewa Surayya kallo a jikinta fatartace kawai me kyau sai fuskarta suma kuma albarkacin mai ne ka kuma makeup. A fili yace "Me ake da mace irin wannan marar fasali wata dokekiya da ita kamar doki? wanda ko ni da nake namiji kuma dogo ta kusa kereni. Ai mace madaidaiciya itace mace kaita cilla abarka sama kana cafewa kuna wasan soyayya kamar sakeena" Ya nemi guri ya kwanta cikin tunanin yadda xai dawo da rayuwarsa ta baya, ya yadda koda xai rasa aikinsa amma su dawo rayuwarsu shida sakeena cikin wannan room nd falo din. Ya kasa baccin ya xauna ya jingina da allon gado ya dakko tabar sa daya siya yake busawa a yan kwanakin nan in tunanin sakeena ya sakoshi a gaba, ya xaro guda daya ya kunna ya fara xuqa yana fesar da hayaqin cikin tunani da shauqin sakeena. Warin sigarin ya tashi Surayya daga baccin da take, ta tashi ta dora kanta a kafadarsa ta xare tabar dake hannunsa a tunaninsa hanashi sha xatai tunda bai taba sha a gabanta ba, amma ga mamakinsa sai yaga Surayya tayiwa tabar wata kyakykyawar xuqa ta fesar da hayaqin ta hanci da baki cike da kwarewa. Ya qare waro ido yana dubanta yana kuma tuna ranar da sakeena ta fara kamashi yanashan taba yacce ta raxana ta rude kuma tayi yunqurin hanashi. Cikin mamaki yace da Surayya "Dama kinashan taba ne?" tayi murmushi tace "A a shisha kawai nakesha itama sai nasamu flavourn da yayimun dadi" yayi saurin kwace tabar da taketa aikin xuqa ya murjeta cikin ash tray na kan bed side, shi dinma ya fasa sha tunda yanxu bashi da gata babu sakeena a kusa me sonsa wacce xata hanashi, ya tabbata in zaisha abunda ya wuce taba Surayya baxata hanashi ba sai dai ta tayashi ya gurbata rayuwarsa da shaye shaye.


Ya kwanta yana cigaba da tunaninsa, Surayya ma ta biyoshi ta kwanta akan qirjinsa tana cewa "Deen tundaxu naketa kewarka baka dawo da wuri ba har nagaji nai bacci, I LUV U" kalmar da Deni yafi tsanar yaji surayya ta fada kenan, domin tun tana fada yanajin dadi harta gundureshi saboda yawan fadar da takeyi kuma a guraren da bai dace ba harya fara tunanin Surayya batasan maa'nar kalmar "I LUV U" ba ta fara shafar sumar qirjinsa kafin daga baya ta haye masa ruwan ciki. Yasa qafa yayi wancakali da ita, yace "Haba kin dameni, ke babu abunda kika sani sai aita kwanciya dake? Ko cewa akai miki wannan ita kadaice soyayya ko kuma auren? Baki gajiya kamar sex machine kedai kullum burinki a danneki, tun abun yanamun dadi harya fita akaina ya salance ya gundureni aita abu daya kamar cin tuwo" ya tashi a xuciye ya fice a dakin ya banko mata kofa, Surayya ta bishi da kallon mamaki.


Yana tsaye a veranda riqe da karfen da aka kewaye gurin dashi yana kallon harabar gidan da haske tayar gurin shiru alamar kowa yana bacci ya fara tunanin abunda xai fishsheshi duk fa wannnan masifar da wannan damuwar baxata kaishi ba domin wacce yakeyi akanta sakeena bata san yanayi ba, kuma indai yana buqatar dawowar farin cikinsa da walwalarsa tofa kawai ya dawo da sakeena cikin rayuwarsa, amma kuma tayaya? Ya qara xurfafa tunanin maganganun mutane da suke cewa bason sakeena yake ba yaudararta yake, wanda ya tabbatar da masu fadar hakan sun fahimceshi ba dai dai ba, to asakama hakanne abunda suke fada yaudararta yake acan baya ko kuma sha'awarta yake, to yanxu dai lokaci yayi da yaji yana mugun son sakeena fiye da komai a rayuwarsa, bayan zamansa da surayya ya fuskanci tarin baiwar da ex wife dinsa sakeena keda ita, inta tabbata yaudarar sakeena yayi abaya yanxu kam reshe ya juye da mujiya domin yagano kansa ya yaudara ba sakeena ba tunda gashi ita yanxu tayi aure tana gidanta cikin kwanciyar hankali shi kuma tabarshi da tunaninta da kuma bitar xamansu na baya.


Gashi dai ya samu mata me kyale kyale fiye da yadda ya dade yana buri, amma kuma ya gaxa son Surayya koda rabin son da yakewa sakeena ne, a wannan lokacin ya gano materialistic luv (soyayyar kyale kyale) yake yiwa Surayya yayin sakeena kuma itace true nd first luv dinsa. Da qarfi ya dunga fadin "Sakeena ban yaudareki ba, kaina na yaudara dana kasa gane kece true luv dina, wlh ina sonki bani da wani jin dadi inbabuke a rayuwata, na shirya rabuwa da komai da kuma kowa in xauna dake ke kadai" ya fashe da kuka kamar qaramin yaro ya samu guri ya takure yana tunanin mafita.


Abunda ya fara xuwa ransa shine sakeena tana sonsa fiye da komai a rayuwarta kuma ya tabbata a rashinsa sakeena ta auri sageer, lokacin yayi da xai kwaci abarsa, ya tuno tafiyarsa Lagos next week kuma sakeena a Lagos take, abu na farko da xaiyi shine fara samo number sakeena domin su farfado da tsohuwar xuma. Da wannan tunani ya samu sauqi da kuma kwarin gwuiwa.



Ranar asabar da wuri ya tashi ya shirya be kula breakfast din da akaiba a gidan domin ko Surayyan yanxu saita qure yake mata magana. Ya saka me gadi ya shiga store inda aka jibge kayan garar Surayya ya fito masa da komai buhu biyu su taliya kuma komai kwali biyu da su jarkar mai aka xuba masa a bayan mota ya shiga ya nufi Gwale gidansu wanda xaije ne da nufin samo digits din sakeena wanda albarkacin hakan suka samu arxiqin wannan kayan abincin. Dake da safe ne ya samu Baba a gida kuma direct dakinsa ya nufa, ya tarar Iya ta kaimasa abinci kenan ya shigo. Al majirai suka dunga shigo da kayan da yaxo dasu, ya tsuguna ya gaishe da Baba ya amsa fuskarsa a sake har yana tambayar lfyr surayya. Deni yace "Baba ga kayan abinci nan asaka mana albarka" ya dakko 20k din daya ware ya ajiye a gaban Baba. Baba yayi murmushi yace "A a ka riqe arxiqinka mal Nura, nikam bani da buqata gaisheninma da kaxo kayi nayi arziqi kuma nagode sosai, ai kana gani rashin xuwanka bai rageni da komai ba, inaci inasha cikin ni'imar ubangiji, uwarka ce ke buqatar temako saika kaimata" Deni da damuwar rashin sakeena ta sakoshi a gaba ga kuma sabon abu Baba na fushi dashi kawai saiya saka kuka. Baba da Iya suka tsaya suna kallonsa. Ya matsa jikin Baba ya kwanta yana cigaba da kukan yace "Baba Dan Allah kayi haquri nasan namaka ba dai dai ba tun akan rabuwa da sakeena amma tun kafin aje ko ina nafara gane kurena, duniya taimun xafi narasa inda xansa kaina inji sanyi" Baba yayi shiru yana shafa kan Deni kukansa ya taba masa xuciya sosai, yana son Deni domin a kansa ya fara samun haihuwa bayan shafe tsahon shekaru yana nema, kuma yasan duk abunda ya faru koda da lefin Deni to be xuce kasa haquri da daukan qaddarar da Allah ya dorawa sakeena ba. Cikin sanyin jiki yace "Babu komai Nuraddeen haka Allah ya shirya kai da sakeena iyakar xamanku kenan gashi cikin qanqanin lokaci kowa ya samu abokin rayuwa. Ka dunga addua kuma ka qara haqurin xama da iyalinka domin be xama lallai taimaka irin biyayyar da sakeena tai maka ba duba da gidan data fito" Deni ya jijjiga kai cikin yadda da maganar Baba kuma cikin xuciyarsa yana cewa "Baba xamanmu da sakeena be qare ba domin saina qara xabaro xuciyar sakeena munyi aure mun haifa maka jikoki. Yace "Baba inka haqura to ka karbi abunda na kawo kasa albarka" yace "To Nura na karba Allah yayi muku albarka" ya dauki kudin kuma ya kira Saddiq yace ya dauki komai guda daya akai dakin Hajjo daya kuma dakin Iya. Deni ya juya ya gaida Iya, itama cikin sakin fuska ta amsa tana tambayar surayya da gajiyar biki. Ya dakko 10k ya bawa Iya amma qiri qiri taqi karba tace "Inna karba kam na maka mugunta Deni ban nemi komai na rasa ba sakeena bata rageni da komai ba, kayan abinci dai tunda malam ka bawa na karba" jikin Deni yayi sanyi ya tabbata in akwai wanda xai kawo cikas a komawar aurensu da sakeena to fa Iya ce. Baba yana jinsu bece komai ba, ya saka Deni ya wanko hannunsa suka karya da ruwan Lipton da pancake.


Bayan sun gama ya nufi dakin Hajjo, tana jin shigowarsa ta tashi ta qura masa ido, shima kallonta yake cikin mamakin yadda duk ta xube yace "Hajjo ciwo kikai ne?" bata bashi amsa ba sai kwanciya da tayi a cinyarsa ta saka kuka, ya tausaya mata sosai uwa uwace koda kuwa mahaukaciya ce. Cikin kuka tace "Deni duniya ce taimun xafi rayuwa ta juyamun baya, mutane basa sona kowa ya tsaneni ku kuma yayana kun kama gabanku ko waiwayena bakwayi" yana share mata hawaye yace "Yi haquri Hajjo ai gani na dawo" ta dago tace "yan uwanka da sukai aure babu wacce take cikin kwanciyar hankali ga kuma wannan (ta nuna Amina) ta xama kamar xararriya saita yini batai magana ba sai kallon hoton sageer a waya" ya dan hade rai yace "Hajjo ki dainamun xancen su Hadixa domin wlh na tsanesu tunda suka xugaki kuka rabani da sakeena, duk abunda xai samesu su ya shafa da suka samuma aka auresu duk mugun halinsu. Ita kuma Amina xan kuma sai mata jamb tayi intaci shikenan inbataci ba tayiwa kanta, dan ubanta angaya mata soyayya qarya ce ba ganinmu suke mahaukata ba lokacin da mukeson juna ni da sakeena, gashinan Allah ya jarrabeki kiji yadda mukaji." ya ciro 10k ya bawa Hajjo Amina kuma 2k, suka dan taba hira da Hajjo wacce duk qorafi take akan baya xuwa da kuma abunda Surayya tai mata, ba abunda ya kawoshi ba kenan dan haka ya solata ya bata haquri yace xai dunga xuwa. A gidan ya yini kuma yayi sa'ar kwafar digits din sakeena cikin wayar Baba a lokacin da Baba ya shiga wanka. Cikin farin ciki ya nufi gida da daddare bayan sunci tuwon Iya kwano daya da Saddiq kuma ya bawa Saddiq din 10k kuma yace masa gobe yaxo can gidansa ya karbi wasu kayansa daya ware xai bayar.

********** ****** ********


Acan Lagos kuma sakeena me kunun aya angama registration da komai, ranar da xata fara xuwa school Sageer da kansa ya kaita bayan sun shirya shi da ita, tai shigar mutunci cikin zani da rigar atamfa da lulluba mayafi aka, a motarta suka fita shi yake ja tana gefe sunyi matuqar kyau sun dace da juna, suna tafiya yana nuna mata hanya har suka shiga cikin jamiar. Sakeena ta ware ido cike da qauyanci tana kallon wata qaramar duniya a matsayin university din da xatai karatu ciki. Lallai sageer ya kashe kudi daganin wannan jamiar sai dan wane da wane. Sukai amfani da time table dinta sukaje venue din da xatayi lecture, ya nuna mata ajin wasu daliban har sunxo sun shiga ta juya ta kalli ajin nasu yayi matuqar haduwa kamar ba lecture room ba. Ta juyo tana kallon sageer da shima ita yake kallo tayi murmushin farin ciki ta sanya hannunta cikin nasa tana murxa yatsunsa suna kallon kwayar idon juna ta fada jikinsa ta rumgumeshi yayi seqeqe yana jin sakeena a jikinsa kamar a mafarki, ta dago ta faki idon dai daikun mutanen gurin ta manna masa kiss a lips dinsa tace "tanxz alot" tayi cikin ajin da gudu tana daga masa hannu. Sageer ya suma na wucin gadi kafin ya farko ya shafa lips dinsa gurin da sakeena ta sumbata ya saki murmushi yace "u'r welkum my luv" yana tsaye yana kallonta ta nemi guri ta xauna ita kadai, ba jimawa malami ya shigo ta maida hankalinta kansa tasaka glasses dinta. Sageer sai lokacin ya juya ya tafi cikin wani irin mugun farin ciki. A office ma kowa yasan yau yana cikin

Please Login or Register in order to submit comment