Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wallahil Azim na rantse da mahaliccina auren sakeena nayi kamar yadda na fada muku, ba xaman haramci mukayi da ita ba kuma lokacin dana aureta bata cikin hayyacinta" Iya ta sauke ajiyar xuciya tayi Hamdalah a fili tace "na yadda da kai Sageeru kuma ina bayanka inaso ka taho da yan uwanka dan suxo ayi hukunci a gabansu kuma su bada shedar auren sakeena kayi."



Faduwar gaba da tausayin Iya lokaci daya sukaxo masa, sai a lokacin ya tuna da Ummansa yayi nadamar boye mata aurensa da yayi. Cikin sanyin jiki yace "Iya kiyi haquri nayi kuskure duk dangina babu wanda yasan na auri sakeena daga abokina sai likitan sakeena sai uban gidana a office a boye na aureta" Iya jikinta yayi sanyi murna ta koma ciki kuma ta fara shakkun anya maganarsa gaskiyace ta cewar auren sakeena yayi?



Ta fada kogin tunani har Sageer ya gama magana bataji me yake cewa ba sai da ya miqe sannan hankalinta ya dawo kansa. Ya dau jakar kayansa yace "zanje in nemi masauki xuwa dare xan dawo" ya fita ba tare data bashi amsa ba.




Acan dakin Hajjo kuwa sun nutse ana tattauna matsala har ankira Fiddausi an fada mata kuma itama ta bada tata shawarar. Suka hadu su uku banda Saddiq dan shi yanxu be cika biye musu ba tun akan batan sakeena. Sun qullah abunda suke ganin shine dai dai suka tafa da sakin shewa ga dukkan alamu duniya ta musu dadi. Hajjo ta dubi Amina tace "saura wannan karon ma ki kwayemun baya inkinji wuya" Amina tayi fari tace "wuce nan Hajjo ai wancan Karon ma dan nasara bata hannunmu ne kuma ankamamu dumu dumu wannan kuwa na tabbatar mune da nasara, ai kodan abi miki haqqinki na bata miki suna da akai da kuma maganar auren Hadixa data watse saina jajurce" Hajjo tace "Yawwa auta Allah yayi miki albarka"



Da photon sakeena na wayar Hadixa wanda akai amfani dashi gurin cigiyar batan ta sukai amfani suka shirya kalamai qazamai kuma kausasa na bata suna suka hada da photon cewar matar Dan uwansu data bata aketa cigiya dai ta dawo bayan ta shafe watanni tana yawan bariki a Lagos ta dawo da tarin dukiyar haramun da kuma tsarabar cikin shege da cutar HIV sannan daya abun tur din harda dadironta ta dawo. Taturawa Amina da Fiddausi. Suma suka dora akan dukkan wata kafar sada muxunta ta xamani da grps grps.




Dake sharrine kuma mutanenmu sun lalace wajen yada sharri a cikin awa guda kacal sai da aka samu wajen mutane 738 da sukayi sharing sannan dubbannai sukai liking da comments. Wasu suna tsinewa sakeena da duk ahalinta, wasu suna aibatata da cewar tayi kyan dan miciji wasu ma cewa suke daga ganinta dama karuwa ce. Masu hankali aciki ne suke yimata adduar shiriya. Acikin wadanda sukasan sakeena wanda sukai makaranta tare da ita suka dunga bin diddigin labarin inda suke biyo su Amina ta inbox, su kuma su suyi musu qarin bayani dallah dallah hadi da qarin gishiri a miya.




Yinin ranar abunda yayan Hajjo suka yini yi kenan, yayin da Baba keta yawo a rana daga gurin wannan malami xuwa wajen wancen dan neman fatawa. Ita kuwa Iya tana lallaba sakeena taci abinci kodan albarkacin abunda ke cikinta wanda baisan ma duniyar ba.




Hadixa ta miqawa Hajjo hannu tace "ban musha Hajjo, bana fa burinki ya cika sunan sakeena ya gama baci a duniya wlh kuma yadda naga yaya Deni ya harxuqa da matuqar wahala ya kuma xama da ita" Hajjo ta washe baki tace "in shaa Allah Hadixa an rabu kenan. Tunda kika farantamun yau nima gobe xan miki abunda baki taba xata ba xan faranta miki kuma burunki xai cika" cikin xumudi Hadixa tace "mexakimun Hajjo?" tayi dariya tace "Allah ya kaimu gobe xakiji" tayi murmushin farin ciki tace "Allah ya nuna mana goben"



Wajen qarfe taran dare kowa yana dakinsa baayi xaman tsakar gida ba kamar yadda aka sabayi wanda hakan ke nuna cewar xuciyoyi babu dadi. Baba tunda ya fita da safe be shigo ba sai yanxu, Iya tana dakinsa ta kaimasa abinci tana kuma fada masa yadda sukai da sageer bayan fitarsa.



Sakeena xafi ya isheta ta saba xaman cikin AC nan kuma sai fanka danma Allah ya temaketa akwai wutar generator da Deni ya saka a gidan. Ta cire kaya ta fito wanka daure da towel, ta cika bocket da ruwa ta shiga dashi tayi wankanta ta fito. Tana sako kafarta wajen toilet din idonta cikin na Deni dake brush a bakin famfo, ta qura masa ido cikin zallar soyayya shi kuma ya dauke kansa yayi tsaki.



Jiki a sanyaye ta nufi daki, saidata juya sannan yabi bayanta da kallo, ya qurawa qugunta ido wanda ya qara cika ya kuma kalli santala santalan qafafunta farare qal ya hadiye wani irin mugun yawu, ya ayyana wai sakeena ce ta bawa wani namiji wannan jikin nata da yake matuqar so da kishi har yayi mata ciki? Ya fara tuno rayuwarsu da yadda sakeena ke xautar dashi a shimfida ya tuna randa ya fara saninta ya mace irin abunda ya samu daga gurinta yanxu haka wancan ma yaji kenan? Yanda sakeena ke riritashi a shimfida haka taiwa wancan kenan?



Wayarsa ta katse masa tunani, ya cirota daga aljihu ya amsa kiran Bilal wani abokin aikinsa. Bilal yace "Nura ashe anga matarka data bata" cikin mamaki yace da Bilal "a ina kaji?" Bilal yaja tsaki yace "karkayimun rainin wayo mana, sam banji dadin abunda kukai ba kaida yan uwanka na fidda maganar waje har ta gama duniya haka, wannan ai personal life dinka ce kuma be dace duk mugun abun da matarka tayi ku yimata haka ba domin koba komi dole akwai mutuncin kataba aurenta" Deni bai saurareshi ba ya katse wayar. Ya kunna Data dinsa da rabon daya kunna tun jiya. Saqonni suka dunga shigowa kamar su fasa wayar, beyi wani nisa ba yaci karo da posting din su Hadixa da Amina. Ya tsorata ya kuma harxuqa da mugun bacin rai ya daga labulen dakin Hajjo.




Suna xaune sunacin gyada duniya tai musu dadi suna kallon Arewa24. Ya daka musu tsawa yana nuna musu fuskar wayarsa da cewa "meye wannan nake gani?" sukayi bayan Hajjo da sauri suka buya. Ta miqe tsaye cikin nutsuwa da sassauta murya tace "nice na sakasu, kuma saura kaimun ihu da terere maqiyana suji susan kanmu ba a hade yake da kai ba, ya kamata xuwa yanxu kasan cewa bujirewa umarnina ba abu bane da xai haifa maka da me ido, domin tunda Kake bujiremun baka tabacin riba ba. Saboda haka ka kama kanka ka kuma bani hadin kai in kwatar maka yanci."





Be kuma furta komai ba ya juya ya koma daki ya kwanta ya dafe goshinsa ya rasa abunda ke masa dadi. Abokansa sai kiransa suke yaqi dagawa wasu kuma suna masa text da tambayarsa cewar abunda suka gani gaskiya ne? Ko kuma ana masa fadan abunda yayi na taunawa sakeena asiri.





Wajen 9:30 PM Sageer yayi sallama ya shigo gidan, Iya tana dakin Baba ta fito tai masa iso cikin dakin. Ya tsuguna ya gaishesu, ya qara da cewa "Iya dama naxo muku sallama ne saboda gobe xanje can gida Katsina gurin Mahaifiyata in fada mata abunda ake ciki, kuma in hali yayi xan xarce Lagos in taho da shedun da xasu tabbatar muku da aurena da sakeena." Iya batai magana ba sai Baba ne yace "To hakan yayi Mohd kuma ina fata baxaka dau lokacin acan ba" Sageer yace "in shaa Allah" Baba yace "Masha Allah, nima kafin ka dawo xamu hadu da malaman da nayiwa maganar inyaso inkaxo sai axauna aji abunda sharia tace akan ku" yayi godiya ya dakko bundle din 500 ya ajiyesu a gaban Iya yace "gashi Iya a kula da sakeena dasu don bakomi take iya ciba"




Iya ta katseshi da cewa "maxa daukemun kudinka xan iya kula da ita da abunda Allah ya horemun" ya kwantar da kai yace "Nasani Iya kuma ba raina kulawarki nayi ba amma fa yanxu sakeena matatace wajibi ne in dau dawainiyarta har xuwa randa xa ai mana hukunci" Baba ya katse musu muhawarar da cewa "To angode Mohd jeka Allah ya kiyaye hanya muna nan muna sauraranka" Ya fita gidan yana waigen dakin Iya da so samune da sakeena yakeso yagani amma inaaaa yasan hakan bame samuwa bane.



A ranar daga sakeena har Iya da Baba sai kuma Deni babu wanda ya runtsa, Iya da Baba dai bayan sun gama juye juye suka tashi suka duqufa sallolin nafila har xuwa kiran sallah.



Washegari gida ya dade, Baba sassafe ya fita haka ma Deni ya nufi makaranta sai Hajjo wadda Baba na fita itama ta fita su Hadixa kuma sun nufi computer school din da Deni ya saka su ita da Amina tunda sunyi jamb duk basu ciba.




Sakeena tana xaune daki tana shan kunun gyadar da Iya ta dama mata saboda jiya ta yini da yunwa ta kwana da ita tana sha saiga Saddiq ya shigo a gigice ya shiga dakin Hajjo yaga babu kowa, ya dawo saitin dakin Iya yace "Ina Hajjo da su Hadixa?" Iya ta bashi amsa da cewa "Su Hadixa kam sunje makaranta Hajjo kuma bansan inda tayi ba"




Kamar yayi kuka ya bude wayarsa ya nunawa sakeena posting din su Hadixa da kuma photon ta. Ta karanta da kuma comments din mutane akai ta dafe kai ta xunduma ihu. Iya tana tambayar menene a gigice Baba ya shigo shima gidan. Suka hadu suna tambayarta Saddiq ya nuna musu photon tare da bayanin abunda su Hadixa sukai posting.


Baba ya nemi guri ya xauna a kujerun dakin Iya, ita kuma Iya ta fara lallashin sakeena dake kuka tana cewa "shikenan sunana ya gama baci ni sakeena na shiga uku Allah ka dauki raina na huta" Cikin tausayinta Saddiq yace "Basu da lefi Sakeena yaya Deni ne ya basu haddin kai har sukayi miki haka, nima yanxu naci karo da posting nayi nayi in fahimtar da mutanen da suke xaginki amma sunqi. Yanxu abunda sukai ya dace Baba? Wannan fa matsalace ta cikin gida be kamata a fita da ita waje ba" Baba da Iya babu wanda ya kuma magana.



Ai basu tashi ganin tashin hankali ba sai wajen qarfe goman safe lokacin Saddiq ya fita Baba ya koma daki ya kwanta saboda ya rasa yadda zaisa kansa. Iya kuma ta tasa Sakeena gaba tana kuka ta kasa lallashinta.



Ana cikin hakane kuma sai suka jiyo muryar Hajjo daga soro tana cewa "A a yallabai shigo da kanka ka bata domin innice xasu dau abun da wasa" Suka jiyo sallamar qaton gardi Iya ce kawai ta Iya amsawa ya miqo mata takadda yace "Gashi daga kotu nake magatakadda ne ni sammacine uwar mijin sakeena ta shigar da sakeena qara akan ta tafi karuwanci da auren danta akanta" Iya ta sandare a tsaye, Baba ya fito daga daki yana wani irin tari yayi qarfin halin karbar sammaci daga gurin mutumin.



Hajjo ta harde hannu a qirji tace "Hmmm soyayya! kaine ma xaka karba mata sammacin? Naka dai shike bada kai, ai kamata yayi kaxo mu hada qarfi da qarfe mu kwatarwa danmu yancinsa gurin sakeena kilaki" Baba bece komi ba ya koma daki yana share kwallah.




Hajjo tai tsaki ta qarasa qafa ta fice wani gurin.



Iya ta koma daki ta tarar da sakeena kwance sanbal a sume, tayi kanta tana wani irin kuka tana kiranta. Baba ya shigo dakin ya dago kan Sakeena ya dora a cinyarsa yace da Iya ta miqo ruwa. Ta fita ta shigo da ruwa a kofi ta bashi yayi tofi ciki ya shafa sakeena a fuska, ta saki ajiyar xuciya ya dura mata ragowar tasha.


Ta tashi xaune ta riqe hannun Baba tace "Baba da gaske ne Hajjo ta kaini qara kotu kuma su Hadixa sun sakani a social media ko kuwa mafarki nake?" bai bata amsa ba sai sunkuyar da kai yayi, ta juya gurin Iya tayi mata irin tambayar, Iya ta fashe da kuka. Ta qara cewa "Baba in gaskene jefe ni xa ai ko? Tunda hukuncin zina da aure kenan ko?"



Haka Baba da Iya sukasa Sakeena a gaba suna kallon ta tana sambatu kamar zararriya har xuwa azahar. Lokacin su Hadixa suka dawo suka bude dakin Hajjo suka shiga.



Basu jima da shigowa ba sai ga Hajjo ta shigo fuskarta tar kamar yau sallah. Ta shigo ta rangada guda, su Hadixa suka fito suna tambayarta meyafaru? Tana kuma rangada guda tace "Daga gidan iyayen Yusuf nake manemin aurenki da yace ya fasa, naje na bude musu komi na fada musu yarinyar da ake xargi na batar dai karuwanci ta tafi Lagos kuma dama tun farko andora abun ne akan xargi domin bani da hannu a batan ta, kuma nayi sa a ana cikin xancen wata qanwar mijinki tace eh taga xancen a waya harta nunamun hoton sakeena nace eh itace. kamar dai yadda nai miki alqawari jiya xan faranta miki yau na cika alqawarin domin uwar Yusuf ta amince kuma tace babansa na xuwa xata fada masa afara shirin kawo kudi" Hadixa tayi tsalle ta dire tace "Dan Allah Hajjona da gaske kike" tace "wlh Hadixa daga can nake, ashe haka suke da arziqi? Kinga uban falon gidan? Ai yayi fuloti guda" Hadixa tayi murmushin jin dadi tace "Hmm ai shiyasa na kuma manne masa saboda nasan xan huta" Hajjo tace "Eh da gaskiyar ki yarnan ai naga zahiri me ake da auren wahala?" Ta ciro yan canji a jakarta tace da Amina "Maxa jeki waje kimun sadaka yau kam farar ranace a gurinmu burina na tsawon shekaru ze cika, so nake kema gurin auren Hadixa ki samu wani me kudin cikin abokan Yusuf ana gama nata aiyi naki kyayi karatun a dakinki." Amina ta karbi kudin ta fita tana hangota itama ta samu me kudi tayi aure tana hutawa tana tuqa mota. Tai tsalle ta dire tace a fili "Allah ya kaimu lokacin."




A ranar Hajjo yini tayi tana bi kwararo kwararo layi layi tana fadar anga sakeena kuma ta dawo da tsarabar ciki, babu batun tambayar Baba inxata fita. Xancen duniya wannan gayawa wannan kafin kace tak xance ya gama unguwar da maqotan unguwanni.




Hajjo ta dawo da laasar ta dora girkin dare. Ta sheqa tuwon shinkafa da miyar ganyen ugun don yau cikin farin ciki take. Ta gama ta miqawa Iya da sakeena nasu har daki cike da ixgili tace "Sakeena ga abinci naga yau uwar taki batai girkin rana ba ko tausayinki bataji ke da bake kadai ba, saboda ke nai miyar ugun kinsan me ciki sai da kayan qarin jini" ko Iya bata kulata ba balle sakeena da bata cikin hayyacinta tun rana.




Tai kwalliya ta shige dakin Baba dauke da tray da sabbin kwanikan qarau na cin abinci. Ta ajiye tana masa sannu. Ta gama kwarkwasarta da feleqe tsaf, ya dago ya dubeta cikin nutsuwa yace "Na haramta miki shigowa dakin nan da kuma girkin gidana domin na yanke igiyar aurena dake nai miki saki daya ki xauna kiyi iddah a dakinki kamar yadda sharia ta tanada, ban fadawa kowa ba amma inkin fada kin taunawa kanki asiri. Ki dunga girki keda yayanki ni kuma Hafsatu xata dungayi tana bani" Hajjo ta tsure maganar ta daketa fiye da xatonsa. Xatai magana ya daga mata hannu ya nuna mata hanyar waje ta fita da gudu tana tuje daurin da Amina tai mata.




Ya kira Amina yace ta kwashe kayan abincin ta kaiwa uwarta. Ya kwallawa Iya kira, ta shigo ta tsuguna yace "Daga yau na raba muku girki, kowa xai dunga nasa daban, kuma ke xaki dunga bani abinci a tukunyarki kullum xan dunga baki kudin cefananki daban." Dake mata ne irin na Da ta amsa da to bata tambayi baasi ba ta tashi tai waje.




Hajjo ta qule uwar daka tai ruf da ciki kan gado ta saka kuka cikin mamakin wai yau mal Lawan ya sake ta? Mutum me tsananin haquri da kau da kai, lallai yakai maqura wajen bacin rai da tasan matakin da xai dauka kanta kenan da batai abunda tayi ba da tabi komi a hankali, To yanxu da yace ta xauna xuwa gama Idda intagama iddar ina xataje?



Ta cigaba da kukanta da tunanin mafita su Hadixa sukai juyin duniya ta fada musu abunda akai mata taqi. sai da Amina tace "To kinxo kina kuka mun tambayeki me akai kinyi shiru inbaki fada mana ba tayaya xa ai mu samo mafita?" Cikin kuka ta fadamusu yadda sukai da Baba. Suma sun kadu da hukuncin da Baba yayi akan Hajjo Amina ta dafe qirji tace "mun shiga uku yanxu ya xamuyi ya maidake kafin wadancan suji suyi mana dariya?" Hadixa ta dake ta matso ta rage murya tace "Ta qarqashin qasa xamubi abun, kuma kema ki dake karki nuna masa kin damu zai rainaki, ba a yiwa namiji haka kuma karmu fasa duk abunda mukasa gaba, yadda kika tsayamun maganar aurena ta tashi kema baxan bari naki auren ya mutu ba." Hajjo ta saki hawayen farinciki lallai haihuwa mai rana meyafi yaya? wanda bai dashi Allah ya bashi. Ta rungumesu tana cewa "To maganar ta tsaya iyakacinmu mu uku karku fadawa yan uwanku na daki kuma karku fadawa maxan har xuwa lokacin da shirinmu xai kammala"



Washegari maqota suka fara shigowa yiwa Iya jaje da kuma ganin sakeena wacce kowa ya ganta sai yadda da maganar Hajjo gaskiya ce don ga alamar cikinan jikin sakeena. Ranar da aka fara hakan sunga bala i domin yini sur akai ana abu daya.



Kafin ranar shiga kotu tayi wato sati daya kenan masifar da Iya da sakeena suka shiga baxata faduba, domin sai da takai sakeena harta dena fitowa tsakar gida da rana sai dai Iya takai mata baho daki tayi alwala. Iya kuma ta xama kamar Hajjo lokacin batan sakeena wato ta shiga tsangwama da bakin mutane har takai andaina siyan kayan masarufin da take siyarwa kuma bata da sukuni ana tsine mata ita da sakeena ana cewa yarta tayo cikin shege da aure kuma taqi korarta. Gida ya xama na Hajjo da su Hadixa kawai suke bushasharsu yadda suke so.




Iya da sakeena suna daki a boye, Baba baya yini gidan saboda baqin ciki kwanciyar bacci ke kawoshi. Saddiq da Zahra sunyi baqin cikin abunda Hajjo tayi sun hadu xasuyi mata nasiha tayi musu cin mutunci tace xata tsine musu dole suka rabu da ita suka xubawa sarautar Allah ido, amma suna tausayin Iya da sakeena. Deni kuwa tun ranar Monday daya bar gidan ba a kuma ganinsa ba kuma ko awaya ba a samunsa kusan 1 wk kenan.


Iya tun tana jiran xuwan Sageer harta fara fidda ran xuwansa ganin gobe xa a shiga kotu. Ta gama qaryatashi da cewar auren sakeena yayi domin in aurenta yayi meyasa me fadawa iyayensa ba? Kuma meyasa tunda ya tafi be dawo ba, ko waya be bugo ba, su kuma sunyi batan basira basu karbi no dinsa ba. Duk da wani shashin na xuciyarta yana yabon Sageer da cewa yaron kirki ne kuma baxai mata qarya ba. Gabanta ya fadi data tuna wani abu, kardai ace Sageer gudawa yayi ya raina musu hankali ya durkawa yarinya ciki ya gudu ya barsu da jiran gawon shanu? Ta dafe qirjinta tace "Allah ka rufa mana asiri ka dubi rauninmu ka bayyana gaskiya ka kuma kawo mana Sageeru kafin gobe. Ita da Baba sun kwana suna sallah da tawassuli da ayyukan da sukai kyawawa yayin da sakeena ta kwana ido soye tana kallon rufin daki kukan ma ya gagara. Ita kuwa Hajjo da bata kulle yanxu tabi gidajen qawayenta tana tuna musu gobe nefa xuwa kotu. Duk inda taje suna yimata alqawari da cewar xasu fitar dango domin mara mata baya ta kwatarwa Deni yancinsa.



Qarfe goman Safe a kotun taiwa Iya da Baba da kuma sakeena wacce ta xama kamar tsumma ta saka hijab har qasa tana kare fuskarta saboda masu daukanta photo a waya. Hajjo ta shigo da jama arta da suka kusa cike kotun wasu ma suna tsaye da kuma su Hadixa wadanda basuje makaranta ba sun taho marawa uwarsu baya.



Kafin ta fito daga gida sai da Saddiq ya sunkuya har qasa ya roqeta ta janye qarar nan, ya tuna mata lokacin da tayi silar batan sakeena sun roqi Baba akan karya kaita gurin jami an tsaro ya haqura dashi da Iya suka barwa Allah duk da girman lefin da tayi na batar da dan mutum. To itama ta duba wannan halacci da sukayi ta janye qarar adawo gida ayi shariar a sirri. Ta bashi da cewa "Ai ita sakeena bata da gata ne shiyasa maganar tabi ruwa, amma shi kuwa Deni yana da gata dan haka saita bimasa haqqinsa na yawon dandi da sakeena tayi da aurensa" tana fadar haka Saddiq ya bata hanya ta wuce yana kuka yana nadamar abubuwan da yayiwa sakeena a baya.



Al qali yana xuwa aka fara gabatar da shariar wadan da suka dau lauya kamar yadda yake a dokar kotu, aka sallamesu sannan aka fara shariar marasa lauya kuma shariar su Sakeena ce a farko aka kirata aka kira Hajjo suka fita gaban dubban jama a sakeena kanta a sunkuye gabanta na faduwa.



Alqali ya nemi Hajjo ta fadi abunda take qarar sakeena akai. Ta ware murya tana kwararo tarihin xuwan sakeena gidansu da yadda ta hargitsa musu gida ta dunga qarya da qara batawa sakeena suna. Daga can baya Hadixa ta samu wasu yan jarida wakilan gidajen radio masu xaman kansu da sukaxo daukar wasu shariar tace suje su dauki shariarsu ta basu dama. Babu bata lokaci dan abun nema ya samu suka fara nadar muryar Hajjo dake batawa sakeena rayuwa da kalaman qarya. Ta gama tas, aka samu noise a kotun na mamakin abunda sakeena tai da kalaman tur, mutane suka fara daukarta a photo wasu kuma nayin vedio. Ta kare fuskarta da hijab kanta a qasa tanaji kamar qasa ta tsage ta shige dan kunya da muxanta. Iya ta dafe kai tana kuka shima Baba hawayen yake.





Al qali ya buga guduma akayi shiru ya juyo ga sakeena ya tambayeta abunda aka fada gaskiya ne? Domin Hajjo ta kawo shedu aciki harda cikin jikin sakeena. Anfi minti 5 ana jiran cewar sakeena amma ta kasa cewa komi, da kyar ta bude baki tace "Sunana Sakeena Abbakar Liman kuma duk abunda ta fada gaskiyane har cikin dake jikina, Dan Allah ayimun hukuncin da sharia ta tanada akaina" Al qali yayi kabbara mutane kuma aka dau tsinuwa da fatan shiriya. Ya qara buga guduma akai shiru, yace "Tunda wacce ake qara ta amsa laifinta mun ajiye rana itayau wato ranar litinin a matsayin ranar da xa ai hukunci kuma a tabbatar da anxo da mijin sakeena na farko" aka shiga wata shariar.



Baba ya riqo hannun sakeena da Iya suka fito daga kotu mutane na binsu, yan jarida ma na binsu sunawa sakeena tambayoyi da daukanta a photo.


Yana xuwa wajen kotu ya tari napep ya xuba su ciki ba tare daya fada musu inda xashi ba shima ya shiga yace muje. Hajjo kuwa tanacan yan jarida sun kewayeta anata hira da ita suna nadar muryarta.



Hajia 😊
[7/31, 2:26 PM] Reine Ghana: πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€MUQADDARI NEπŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€2018πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€



2⃣0⃣

RAHMATULLAH (Hajia)



Assalamu alaikum, inawa dinbin masoyana ko ince masoyan rubutu naπŸ˜„ fatan alkhairi. Yar taqaitacciyar sanarwa ce nake tafe da, inaso masu karanta littafin muqaddari ne su sani, wannan

Please Login or Register in order to submit comment