Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sani a ranar yayi fushi dani kuma a daren mahaifiyarsa taxo gidanmu kaduna haushin jin tasa an rufemun mahaifa yasashi korarta yace karta kuma xuwar masa gida. Ni kuma na bishi na bashi haquri ya haqura yace inmasa dan wake inya dawo xamuyi magana. Yana fita ta koreni tace intafi in barmata gidan danta ni kuma bani da kudin mota a cikin tashar na hadu da wata hajiya ta taimakeni tace garinmu xata ashe saceni tai saida muka kwana muna tafiya driver motar yace mun Lagos nake. Shine ta tunkudo daga mota bayan taji ana binmu har da harbin bindiga"




Sageer, Maitama da Bilki suka dunga maimaita kalmar innalillahi jin wannan almara wai sakeena matar aure ce kuma ga wani auren akanta harda ciki. Sageer ya rasa me xaiyi? Mai xaice? Ina xaisa kansa? Wane irin lamari ne wannan me sarqaqiya?"




Sakeena ta rarrafo gurinsa tace "Ka taimaka ka maidani gida, wlh mijina yana da kishi. Dan Allah karka fada masa nayi aure xai iya kasheni. Ina sonsa dan Allah ku temakeni ku kaini gurin ya Deni" Sageer ya dago yana dubanta idonsa jajur cikin sanyin murya yace "a wane gari kike?" da sauri tace "a Kano cikin Gwale local government"



Ta cigaba da sambatun cewar a kaita gida yanxu ko a barta ta tafi tasan ya Deni yanacan yana nemanta. Tun suna ganin abun nata na hankali ne har suka gane bata cikin hayyacinta. Dataga basu kulata ba saita tashi xata nufi kofar fita a cewarta "tafiya kano xatayi" sageer ya riqota ta tankadashi da cewa "karka tabani ni matar ya Deni ce kuma shi nakeso, kaiba mijina bane kuma ko munje karka sake ka fada masa ka taba aurena"




A wannan dare dai sunga tashin hankali gurin sakeena don kwanatai tana sambatu kamar sabon kamun hauka, da kyar Maitama ya lallabata da cewar yanxu tsakiyar dare ne amma gobe da asuba xasu tafi. Ta yadda da maganarsa sageer na gefe yana kallonsu dan taqi yadda ko kusa da ita yaxo.





Bilki ce ta shiga ta fara hada kayan sakeena cikin manyan jakunkuna kamar yadda mijinta Maitama ya umarceta. Sageer cikin fidda tsammani yacigaba da xaqulo mata da dukkan abunda yasan mallakin sakeena nane. Ya kasa yadda cewar wai yau shine ya auri matar aure, yau shine xai rabu da abunda yake mutaqar so da qauna.



Qarfe hudun asuba Maitama ya nufi airport nemo musu ticket. Yayi sa a ya samu akwai jirgin da xaije kano yau amma sai yayi zango a Kaduna. Ya siyo ticket din ya dawo da sauri saboda jirgin qarfe shida xai tashi.




Da kyar Bilki tasa sakeena tai wanka bayan sallar asuba ko mai bata shafa ba ta xura baqar abaya me kyau da tsada duk jikinta stones ne. Shima sageer yayi wanka ya sako kaya ya fito yana layi. Cikin tausayi Maitama yace "Sageer gyara rigarka a baibai kasa, kayi haquri ka barwa Allah komi" ya kalli Maitama yace "To in ban haqura ba hauka xanyi? Sakeena fa xan rasa, my first luv? Kana ganin yadda ta mantani take xancen wani daban? Maitama tafi sonsa dani fa kenan? Ta manta duk wata soyayya da alqawari da mukasha yiwa juna. Kuma nasan shi xata xaba tabarni ciwon rabuwa da ita ya xama ajalina. Shikenan na tabbatar na rasa ta tunda ai shima wancan ba mahaukaci bane da xaibarmin mace irin sakeena" ya qarasa yana kuka. Shima Maitama share kwallah yayi a sace, lallai duk bala'in daya saka mutum me taurin zuciya irin sageer kuka tofa ba qaramin bala'i bane.




Suka loda kayanta a jeep din sageer suka tafi. Bilki dai bata bisu airport ba itama kuka take. suna xuwa aka fara kira Maitama ya dafa kafadar sageer yace "ka dogara da Allah temakon da kayi baxai tafi a banxa ba, in Allah yayi sakeena rabonka ce sai Kaga ka tsalleke duk wani qalubale da kake ganin zai rabaka da ita ka sameta. Yanxu daganan gidan Abdulfatah xanje infada masa yadda ake ciki sabida karyaga gobe Monday bakaje aiki ba" ya juya ya tafi yabar sageer cikin wani irin yanayi.






Jirgi ya tashi kowa da tunanin dake ransa. Sageer yana ganin kamar da gayya matuqin jirgin ke gudu don ya qara nisantashi da sakeena, tunda yasan dataje Kano ta tashi daga matarsa. Ita kuma sakeena tana jin kamar jirgin baya sauri tanajin kamar tai tsuntsuwa ta ganta a Kano gurin Iya da ya Deni.



Bai wani jima a Kaduna ba ya sauke passengers jirgin ya daga kano. Suna sauka kano fargaba ta xiyarci sakeena da sageer a lokaci daya. shiyana fargabar shikenan fa ya rasa wannan tsaleliyar yarinyar a matsayin matarsa yayin daya qura mata ido yana kallonta yana jin wata iriyar soyayyarta da bai taba jiba tana shigarsa. Ita kuma tana cikin xurfin tunanin baqin kishi irin na Deni, ta tuna haukan da yayi lokacin da Ahlan ya riqe mata hannu kawai, yana kuma ga tayi aure harda ciki? Gabanta yayi wata irin faduwa tasa hannu ta dafeshi a fili tace "Allah ka sassautawa ya Deni mugun kishin nan nasa, Allah kasa ya fahimceni Allah ka gani inason ya Deni Allah ka hada kanmu" Sageer ya bita da kallo jin abunda take cewa ya tausayawa kansa sannan ya kuma fidda tsammanin samun sakeena dan tana cikin matsannanciyar soyayyar waninsa.



TAB!!!!!! Wannan shine Luv triangle (πŸ”Ί)



Hajia 😊
[7/31, 2:25 PM] Reine Ghana: πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€MUQADDARI NEπŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€2018πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€



1⃣9⃣

RAHMATULLAH (Hajia)


Asabule dukkansu suka fito daga cikin jirgin ta samu guri ta tsaya, ya samo taxi a cikin airport din suka loda kayanta yaxo ya kirata ta shiga baya shi kuma ya shiga gaba suka tafi. Ana shiga gwale qijinta ya tsananta bugu sosai, ta dunga yin kwatance me taxi din yanabin kwatancenta. Yawanci kowa yana gida saboda lokacin ko 8 din safe batai ba kuma lahadi ce ana hutun weekend.


Suka tsaya kofar gida, ta fito a cikin sanyi jiki ta shige gidan. Sageer kuma ya fito da kayanta ya biya me taxi ya tafi.


Da sallama ta shiga gidan, Hajjo da su Amina ana daki domin yanxu ta wuce sai da gasara sai hutu da harkar sai da atamfofi. Baba yana nasa dakin shima, Saddiq ya fita motsa jiki sai Deni kwance yana bacci a dakin soro. Iya keda girki, ita keta xarya tsakanin dakinta da kicin tana hada breakfast.



Ta kuma sallama a karo na biyu cikin sanyin muryarta, Iya ta fito daga daki dauke da sabon food warmer sukayi 4 eyes da sakeena. Ta waro ido tana yiwa sakeena duban mamaki yayin da sakeena ke tsaye tana kallon Iya idonta cike da kwallah. Iya ta isa gurin ta cakumo sakeena ta qanqameta, ta tabbatar dai sakeena nan ce ta bude murya tace "jama'a kutayani ganin abun al ajabi yau sakeena ce a gidan nan" suka kuma rungume juna. Babu wanda yaji abunda Iya ke fada sai Baba saboda duk bacci suke me nauyi. Ya fita cikin hanxari ya ganta rungume da iya, ya furta "Sakeenatu" ta saki Iya tayi gurin Baba ta fada jikinsa tana hawaye. Baba ya dagota daga jikinsa ya share mata hawaye yace "sakeena duk tsahon wannan lokaci kina ina muketa nemanki? Lefin Hajara ya shafemu kenan?" ta qara riqeshi tace "Ba kuyimun komi ba, muna tare da wanda ya kawoni a kofar gida" yayi saurin cewa "jeki ki shigo dashi, bari in kintsa dakin nawa" tayi hanyar waje. Iya ta bita da kallo tana tafa hannu tana cewa "Malam da gaske sakeena ce ko mafarkin dana saba yine?" wannan magana ta Iya itace ta tayar da Hadixa da sauri ta tashi Hajjo da Amina tace naji ana sakeena ta dawo. Suka mutstsike ido sukayo tsakar gida suna tutture juna. Deni ma kamar a mafarki yaji ana ambaton sakeena shima ya fito da sauri dagashi sai dogon wando.



Sakeena ta samu sageer kofar gida tace masa "ance ka shigo" bata qara komi akaiba ta juyo. Ya bita da kallon mamaki wai yau sakeena ce take masa haka? Matar da kamar su cinye juna shi da ita saboda soyayya yau itace ke masa magana kamar baquwa. Ya fara kici kicin daukar jakar kayanta.



Tana shiga soro suna yin kicibiz da Deni da fitowarsa kenan. Suka furta sunan juna a tare, ya iso ya dagata ya mannata a qirjinsa da babu riga. Tayi lub ta qanqameshi, Sageer daya riqo akwatinan sakeena biyu yayi ido hudu da wani xabgegen matashi babu riga rungume da sakeena ya sakesu a qasa yace "innalillahi wa innah ilaihi raju'un" Deni be juyo ba domin bema jishi ba balle yasan da mutum a gurin. Ya dago kan sakeena daga qirjinsa yace "Baby kece koko mafarki ne?" tana hawaye tace "ya Deni nice ba mafarki kake ba" Ya qara rungumeta ita kuma tana shafar fatar bayansa.



Sageer yana tsaye yana kallon su, tunda yaji sakeena ta kira ya Deni shikenan ya kuma yanke qauna da samun sakeena, domin maxa irinsu Deni sunfi kasuwa a yanxu, mata su suke rububi. Bawai dan ya fishi kyauba ko hasken fata, a a kawai dai Deni dogo ne me cikar jiki irinta maxa, ma'ana murdaddan jiki irin na qarfafan maxa. Bayan wannan kam Deni be fishi kyau ba sai dai hasken fata don shi sageer baqi ne yayin da Deni yake wankan tarwada.



Ya dawo hankalinsa lokacin da yaga Deni yayiwa sakeena daukar jarirai ya shige dakin dake soron da ita, yayi sauri xaibi bayansu kafin yayi dan gajeran tunani ya dakata. Tunanin da yayi shine inya shiga yace musu me? Yanda fa yake ji sakeena matarsa ce haka shima Deni keji, yadda yake kishin sakeena haka Deni keyi koma fiye dashi tunda shi ya fara auren sakeena. Yaji wani irin abu me ciwo a saitin xuciyarsa kamar xai fasa qirjinsa ya keto, yayi qoqarin hadiye abun ya kasa, ya tambayi kansa ko wannan shine kishi???? (FANS Ku BASHI AMSA PLZ πŸ˜„) Yaja jiki a sanyaye ya shiga cikin gidan.





Deni yayiwa sakeena masauki akan qatuwar katifarsa da ake cewa gado huta. Tadan kalli dakin cikin yan sakanni ta yaba da tsarin dakin duk da dai ta saba ganin gurare masu kyau yanxu. Taji hannun Deni a cikin rigarta tayi gaggawar cire hannunsa ta waro masa manyan fararen idanunta tace "meye haka kuma" ya Kalli idonta da suke jajaye ada amma yanxu sun xama farare qal wanda hakan ya qarawa kyanta armashi, ko sakeena bata fada ba yasan ta samu lfyar ido yanxu. Ya dafe saitin xuciyarsa yace "wash! Sakeena wannan kallon naki ai saiya yasa na sume miki" maganarsa ta bata dariya ta hauyin dariyarta tana dubansa.




Ya nutsu yana kallonta tana dariyar, haqoran sakeena da yake kyankyami tun farkon xuwanta gidansu har xuwa lokacin daya aureta wanda shine dalilinsa na kasa sumbatarta sai dai in itace takai bakinta kan nasa bakin baya iya guje mata saboda kar ya watsa mata qasa a ido ko ta fuskanci yana kyamarta, amma yau saiya ga haqoranta qal abun burgewa da sha'awa badan karyayi qarya ba sai yace har daukan ido suke, dagani suna samun kyakykyawar kulawa daga dentalist. Ya hada bakinsa da nata a Karon farko a rayuwarsu da yayi hakan dan ra'ayin kansa. Ya farayi mata kiss din da yadade yana buri yayiwa matar da yake mafarkin aura.



Sun dau tsawon 3 minutes suna sumbatar juna kafin ya cire bakinsa ya kwanta ya jawota jikinsa. Ta fuskanci abunda yake nufi sarai gabanta ya fadi data tuno badaqalar dake gabanta da kuma abunda ke qunshe a cikinta. Ta janye jikinta a cikin dabara, ya riqota yace "Haba miye haka Baby wlh a mugun matse nake harfa axumi nake saboda rashinki" ta danyi yaqe kawai batace komi ba amma kuma qirjinta kamar xai fashe dan bugawa.



Ya haqura da abunda yayi niyya dan yaga kamar sakeena bataso, shi kuma baxai iya batawa sakeena rai ba yanxu, ji yake kamar ya hadiyeta. Ya tashi daga kwanciyar da yayi yace "sakeena bani lbr ina kika shiga? Ya akai kika canja haka cikin lokaci qanqani? Bani lbr sakeena" Jiki a sanyaye tace "Da wani mukaxo yana cikin gida" ya miqe yaja hannunta yace "ai bansani ba mun bar baqo xo muje" ta bishi suka fita har cikin gida yana riqe da hannunta.





Suka shiga dakin Baba kamar yadda suka tarar kowa na gidan yana can. Sageer na xaune shima cikin dakin, Hajjo dasu Amina suka bi sakeena da kallon qurullah da kuma mamakin canjawar da tayi. Hajjo tai shu'umin murmushi dan ta gano cikin jikin sakeena. Iya ta jawo sakeena jikinta tace "Taho sakeena bangama ganinki ba ai" ta dora kanta akan cinyar Iya yayin da Iya ke shafar kan sakeena cikin soyayya.



Sageer ya gyara xama ya gabatar da kansa da kuma asalinsa har xuwa kan aikinsa. Ya fada randa ya tsinci sakeena da kwanan wata da kuma time din, ya fada musu abunda ya faru bayan nan har xuwa jiya da sakeena ta dawo cikin hankalinta ta kuma fada musu tana da aure har cikin jikin sakeena da kuma aikin idon da akai mata be boye musu komai ba.




Sunyi tsit kowa ya fada kogin tunani muryar sageer kawai ke tashi a gurin. Hajjo ta miqe ta rangada guda "ayyiririri" ta dora da dariyar mugunta sannan tace "Allah ya kawomu shekara ta kawomu, yau xanga batan nono a qirijin budurwa. Aka dameni, aka tsangwameni wai na batar da sakeena har aka rabani da Dana aka janyomin surutun jama'a har ana cewa xa a kaini gurin C E D (C I D take nufi wai🀣) kai harda masu tsinemun akan haka. Ashe yarinya dai yawon bariki ta tafi, ba a tashi dawo mana ba sai da bariki tayi riba aka samu cikin shege yaqi xubuwa shine kika dawo mana da kwartonki xaku raina mana hankali wai kin haukace ya aure ki?" Ta matsa kusa da sakeena ta kalleta cikin ido ta nunata tace "wlh kinyi asara sakeena ban taba ganin tsinanniyar mace irinki ba, gyatuma tayi naqudar banxa ta haifi asara Dan tsinancewa da aurenki ki tafi yawon bariki"



Babu wanda ya tanka mata kowa kansa sunkuye yana hango girman lamarin sai sakeena dake hawaye da kuma sageer dake kallon Hajjo baki bude yana tunanin wannan kuma wacece a gurin sakeena? Kai duk inda wannan mata take bata da hankali kuma bata da tarbiyyar harshe, ji yake kamar ya tashi ya rufeta da duka saboda tasa sakeena kuka.




Deni ya dago kai idonsa jajur ya nufi sakeena duk gashin jikinsa ya miqe. Ta tsorata domin tasan inta ganshi haka ransa yakai matuqa wajen baci kuma baqar xuciyarsa ta motsa, xama ta iya cewa bata taba ganinsa haka ba.




Ta qanqame Iya tamau ta fara bashi haquri. Ya figota yace "ai wlh duk duniya baki da maceci yau" ya saka hannu ya matse mata baki yace "kinsan ba yau muka fara ba ko? Sam ban yadda da wannan dramar din ba, ta kinyi loosing memory har kinyi aure akan nawa auren har da wani tsinannen Da a cikin ki. Ki fadamun gaskiya domin itace xata kwaceki" da kyar tayi magana saboda matse mata bakin da yayi tace "Wlh ya Deni iya gaskiyar kenan wlh aure mukayi loka...... Marin da Deni ya dauketa dashi shiya hanata qarasa maganar. Ya fara magana cikin xafin rai "har ni kike fadawa kinyi aure? Ni xaki rainawa hankali? Nawa kike? shekarunki nawa har da xakiyi wasa da hankalina?" ya daga hannu xai kuma marinta Sageer yayi saurin riqe hannunsa don haqurinsa ya qare baxai juri ganin haka kawai wani banxa na dukan tsadajjiyar mace irin sakeena ba akan wani kishi nasa na banxa da wofi da kuma lefin da ita kanta sakeena batasan ta aikatashi ba domin lokacin da tayi aure kan aurensa bata hayyacinta har ga Allah.



Cikin qarfin xuciya da maxan taka Sageer yace "karka kuma dukarmun mata sannan karka qara kiran dana shege domin aure ne ya samar dashi" cikin hargagi Deni ya daki qirjin Sageer yace "in an kuma me xakayi dan iska bunsuru me taraiyya da matar aure?" Sageer shima cikin tasa xuciyar data yunquro yace "inka kuma xan daureka ne har qarshen rayuwarka dan ubanka domin da xubar hawayen sakeena gara mutuwar irinku mayaudara masu ci da kalmar SO"



Deni ya kaiwa Sageer mari amma ya goce ya damqe hannun Deni yasa qarfi ya murde hannun. Baba ya tashi yana salati, yayin da Iya ke riqe da sakeena wacce ke kuka haiqan gefen fuskarta kuma ga hannun Deni nan kwance a gurin ya fito saboda yanxu fatar ta ta xama ta ajebo.




Hajjo tai hanyar soro da gudu tana kururuwa da ihun a kawo mata dauki kwarton sakeena yaxo har gida xai kashe mata Deni, taci karo da Saddiq a soro ya dawo daga motsa jiki, ya tareta yana tambayarta, ta bashi amsa amma sam be fuskanci abunda take nufi ba ya nufi cikin gidan. Ya samu Sageer da Deni suna dambe a tsakar dakin Baba yayin da Baba ya kasa rabasu don matasa ne kowanne yanaji da qarfi da kuma xuciya. Da kyar Saddiq ya taya Baba suka rabasu aka fice da Deni dakin soro.


Baba ya bawa kowa umarnin yaje ya kama gabansa xuwa wani lokaci wannan lamari ne me sarqaqiya xai nemo malamai masana shari'a su xauna ai hukunci kan lamarin.



Sun fito daga dakin Baba kenan Deni ya kuma kubucewa daga hannun Saddiq ya fito daga dakinsu na soro, sakeena ce da Iya a gaba dan haka suya fara gani. Ya tari gabanta yace "ni xakici amana ko? Ni xaki ha'inta ko sakeena? Ina nan tunda kika tafi ina xaman jiranki cikin azabar kewa da soyayyarki har fushi nayi da mahaifiyata da yan uwana ciki daya akanki a she ke kinacan kina sana'ar karuwanci" ya tofa mata yawu yace "Tur da ke yake wannan me kwadayin duniya wacce ta jefa masoya da danginta cikin bala'i dan son xuciyarta"



Sageer ya nade hannun rigar jikinsa, ya shiga tsakanin sakeena da Deni domin yaga yaron yana da taurin kai kuma ya naji da girman jiki gara ya lafceshi koxai shiga hankalinsa. Ya dunqule hannu ya saukewa Deni a bakinsa yana cewa "nace ka daina aibatamun iyali kaqi ko? To bari inyi maka da yaren da xaka gane tunda kai jaki ne" Dukan ya xowa Deni baxata, be xaci matsakaicin mutum kamar wannan yana da kwarin kai duka irin wannan ba. Ya dago da mamaki yana kallon Sageer ya share jinin bakinsa inda ya fashe yace "kaxo har gidan ubana ka dakeni akan matata?"




Shima ya xage suka fara bawa hammata iska. Hajjo ta hau kururuwar cewa "wannan wane irin bala'ine? Wai sakeena yar gwalce da xa a xauna ana dambe akanta? Kai Deni ka cikashi ka barmasa karuwarsa, kai kuma Allah ya baka tsarkakakkiya irinka" Baba da Iya dai suna gefe suna kallonsu kamar fadan be damesu ba.



Sakeena da farko taso suyi damben don haushin Sageer takeji kamar ta kasheshi don haka taso Deni yayi masa duka a xatonta Deni xaifishi qarfi duba da yanayin jikinsa, amma dataga ana dukan masoyinta Deni kuma yafi jin jiki a fadan saita fara ihun cewa "Baba ku taimaka ku rabasu yana dukan ya Deni" Baba ko motsi beyi ba Saddiq kuwa Hajjo se dura masa xagi take akan ya shigarwa dan uwansa. Yayi tsaki yace "Har dakin soro fa na tafi dashi na riqeshi amma ya kubuce ya gudu don tsabar taurin kai saboda da haka suyi tayi wlh in daya ya kashe daya cikinsu shikenan sun kawo solution sai ta zauna da wanda ya rayu"




Ai sakeena dajin wannan batu na kisa daga bakin Saddiq ta xabura ta shiga tsakiyarsu domin tasan inma kisance Deni xa a kashe. Ta hankade Sageer tace "Babu ruwanka da duk abunda xaicemun, mijinane kuma shi nakeso saboda haka ka fita daga rayuwarmu ka koma inda ka fito" Sageer yayi kasaqe yana kallonta gwuiwarsa tayi sanyi qalau. Ta matsa gurin Deni ta riqeshi tace "ya Deni muje ingyara maka ciwon bakinka, xan maka bayanin komi a nutse" ya daka mata tsawa yace "ke! Karki kuskura ki biyoni dan wlh xan iya kasheki a yadda nakejin tsanarki" Hajjo cikin farinciki ta matso tace "Da kyau dan halak ka burgeni matuqa" ta fusge hannun sakeena daga jikin Deni tace "karki kuma tabamun Da ki shafa mai dattin zina, ki tafican gurin dadironki don da alama har yanxu yana muradinki. Kinga shi Deni ai aure ne ya samar dashi don ga abunsa can a tsaye. Ke kuwa ta yadda aka samar dake ta haka kike samo naki Dan. Gado girman Allah barewa bata gudu danta yayi rarrafe"




Wata irin kunya ta rufe sakeena jin abunda Hajjo da Deni sukai mata a gaban Sageer, taji duk ta muxanta taja jiki ta shige dakin Iya. Baba ya fita waje, Deni ya koma dakinsa sai Hajjo da taja yan majalissarta sukayi daki tana so suje su xauna a fara tattauna matsalar tun yanxu. Aka bar Iya da sageer a tsaye a tsakar gida. Iya tace masa "shigo daga ciki sageeru" yabi bayanta suka shiga dakin. Sakeena na xaune akan sabon Center carpet din dakin Iya wanda Deni ya saya musu ita da Hajjo. Tana ganin Sageer ta shige uwar daki tana kuka.




Ya samu guri a qasa ya xauna, Iya taitai ya hau kan sabbin kujerun falon yaqi, ya sunkuyar da kai. Ta miqe ta fita ta xubo masa funkason datayi a matsayin breakfast a sabon food warmer dinta ta ciko masa jug da kunun tsamiya takai masa da ruwan wanke hannu sannan ta fito tsakar gida tacigaba da aikin raba abinci.



Aka bar Sageer xaune a falo da tray din abinci a gaba, yayin da sakeena kecan daki tana tunani da kuka. Sageer ya janyo abincin gaabansa ya tsiyayi kunu ya fara kurba badan dadi ba sai don karya watsawa Iya qasa a ido. Daga kunu har funkason cimarsa ne amma yau kam dakyar ya iya cin kadan ya rufe. Ya fara tunanin ita Sakeena da Dan cikinta me sukaci?



Iya tana gama rabon abinci ta shigo ta xauna kan kujera ta dubi abincin gaban Sageer tace "ya bakaci komi ba sageeru?" ya danyi murmushi yace "Naci Iya, ita sakeena naga kamar bataci komi ba" Iya ta qura masa ido tana dubansa shi kuma yayi qasa da kansa.



Ta gyara xama cikin nutsuwa ta fara magana. Ta fara bashi tarihin Sakeena tun daga auren Iyayenta da kuma qabilar da uwarta ta fito, bata boye masa komi ba har mutuwar Nura da kuma qiyayyar matar ubanta da yadda ta dakkota har xuwa aurenta da Deni da yadda tasha wuya har aikin da tayi don suyi xaman aure da yadda Hajjo ta uxura mata har korarta da Hajjo tai da abunda ya faru bayan bacewarta. Iya ta qare xancenta da cewa "Dan Allah Sageeru ka dubi girman Allah ka fadamin gaskiyar abunda ke tsakaninka da sakeena komenene xan iya dauka dan sakeena diyatace halak malak bata da wacce ta wuceni duk duniya"



Sageer ya share kwallar tausayin masoyiyarsa ya kuma tsanar Hajjo da Deni ashe wancan mahaukaciyan matan mother in law din sakeena ne shiyasa take mata haka, shi kuma Deni be yadda yana wani yiwa sakeena soyayyar gaskiya ba just mayaudari ne da yake wasa da xuciyar sakeena da sunan soyayya amma kash sakeena bata gane hakan ba, ta makance ta mutu murus akansa kuma ga dukkan alamu da hakan Deni ke amfani yana musguna mata.




Ya dago ya dubi Iya da take jiran cewarsa ya fara magana "Iya ke mahaifiya ce a gareni tunda kina matsayin yayar Baban sakeena innayi miki qarya kamar na yiwa Ummata ne.

Please Login or Register in order to submit comment