Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa gaskiya ne daga nan a cillashi gidan yari. Cikin rawar baki yace "Wlh indai har ka temaka ka rabani da wadannan yaran babu wanda xan fadawa, kuma sakeena na bar maka ita har abada" Sageer ya juya ya fice Deni na kwallah masa kiran "Oga Sageer na tuba kaimun rai zasu kasheni" Aikuwa suka kumayi masa qawanya suka qara tumurmusashi har saida ya suma sannan suka debeshi kamar kayan wanki suka kai mota, suka xare masa waya da yan kudaden jikinsa suka kaishi can gurin da babu mutane suka sashi a motarsa suka ware.


Sai qarfe biyun rana Sakeena ta yakice baccin ta tashi da kyar tayi sallah, batajin yunwa ko kadan dan haka malt kawai tasha ta kuma komawa baccin da har yanxu ya kasa isarta. Qarfe biyar din yamma ta tashi dakyar taje tai wanka tayi sallah tayi axkar ta tsantsara kwalliya saboda tasan duk inda Sageer yake ya kusa dawowa. Ta fito falo tayi kan dinning ta bude food warmer, tai karo da taliya da miya, tai saurin rufewa, ko kadan bata burgeta ba, ta nufi kicin tasamu Inna na aikin girkin dare ta durqusa har qasa ta gaisheta ta amsa tana tambayarta jiki, tace taji sauqi. Ta hada golden morn saboda yunwa takeji, cokali daya tayi ta ajiye taji yana qoqarin sakata amai. Tadau waya ta kira Sageer, ya daga yana cewa "Ran gimbiyata ya dade" tace "Ya Sageer dan Allah inbabu damuwa ka tahomun da shawarma mana" yace "Wace irin damuwa kuma? Ai kawai umarni xaki bayar in cika ranki ya dade, ki jirani nan da qanqanin lokaci" ta kashe wayar tana dariya. Harya karyo kwanar gidan ya juya ya koma yaje ya siyo mata sai da ya jira aka hada tukun sannan ya taho.


Yana sallama ta nufeshi da sauri ta rungumeshi, shima rungumeta yayi suna dariya a tare. Ta jashi bedroom, suka baje ledar shawarmar sukaci tanaci tana bashi abaki shima yana gutsura, saida sukaci ta ishesu sannan ta fitarwa su Inna da ragowar. Suka dawo suka dasa hira tana kwance jikinsa kamar mage, saida lokacin sallah ya taho sannan ya tashi yayi wanka ya fita.

****** ******** ******** ****** ****


Washegari juma a ya fita aiki bayan tayo masa rakiya kamar jiya suka rabu cikin kewar juna, duk da har yanxu bataga sakin jikinta ba tana kunyar abunda tai masa. Amma ta qudure aranta yau xata fada masa abunda takeji game dashi inya dawo.



Acan kuma Deni sai wayewar garin yau wani bawan Allah ya ganshi kwance a mota kamar matacce, ya duba ID card dinsa na aiki yaja motar ya kaishi ma'aikatarsu, sun kidime da ganin haka aka kira police ya tsaya musu asibiti suka karbeshi yace musu suyi haquri daganin wannan aikin Area boys ne ya shiga sabgarsu sukai masa haka. Ya samu kulawa a asibiti sosai suka gyara masa targaden da yayi gurare kusan biyar a jikinsa da kuma muggan raunuka, amma har xuwa wannan lokaci a sume yake be farko ba.


Ta tsefe kanta ta shiga kitso maqotansu daga can tai gidan Bilki, Bilki tace "Ai kuwa dai naji kunya sakeena, ban shiga dubaki ba sai gaki kin shigo" tana dariya tace "Babu komi Anty Bilki komi sai Allah ya nufa, kuma na warke sosai ma ko yatsana yanxu bayamun ciwo kitso ma naje shine na shigo mugaisa" tace "Allah sarki nako gode qanwata ya gida yadan Babyn mu?" Sakeena tai shiru tana murumushi cike da kunya, Bilki tace "Dama na fada miki sakeena xakiso sageer indai har kika saka kanki, inda ake sonka nan kake gyara xama kayi dirshan, daka so gara a soka, mata yanxu muna bata lokacinmu gurin soyayyar banxa ta wadanda ba sonmu suke da gaskiya ba, munabin kyale kyalen banxa yayin da ga masoyanmu na gaskiya can na jiran yar dama qanqanuwa su gwada yadda suke qaunarmu. Gashi yanxu da kika dau shawara har kun samu rabo, Maitama mamaki yake wai daga ke har Sageer din munafukai ne kunyi cikinku babu wanda yasani" Sakeena tai dariya tace "Hmm nagode Anty Bilki" a gidan Bilki takai har qarfe dayan rana sukaci wainar fulawar da Bilki tai mata sukai sallah sannan ta koma gida, tayi wankanta tai kwalliya tana mamakin meya hana sageer dawowa har qarfe biyun rana tunda yau juma a?


Tagaji da jiransa har kwalliyar tai sanyi, ta kwanta a falo bacci ya dauketa. Be shigo gidanba sai 6 PM, lokacin harta qara wata kwalliyar cikin qananan kayan data lura yanaso, suka nufi dakinsa tana masa qorafin meyasa be dawo ba yau. Ya bata uxurin cewa meeting sukayi sai yanxu suka gama. Ta dakko masa abinci ta kai masa har dakin yaci suna dan taba hira har aka kira magrib, yayi wanka ya fita, itama ta qara gyare jikinta bayan tayi sallah.



Sai bayan sallar isha ya dawo hannunsa dauke da ledojin fruit, ta karba taje ta wankesu ta yanko ta kawo sukasha, tace masa tana xuwa xataje yin aikin lemon tsamiya saboda yarinyar har yanxu bata gama iyawa ba, yatashi yace "muje intayaki" tace "No yi xamanka kaida ka yini xaune a office, kabari ba wani dadewa xanyi ba na hada kawai duddurawa xanyi a robobin" yaqi haqura saidaya bita.


Ko acan dinma ya hanatayin aikin komi, yace kawai ta xauna har yanxu bata gama warwarewa ba. Shiyaketa durawa a jarkokin yana qullewa yana yimata hirar makaman da suka kwace yau anyo fasa kwaurinsu daga qasashen qetare. Itadai tai shiru tana dubansa cike da soyayya da kuma burgewa, can dai ta kasa jurar abunda takeji akansa batasan yadda akaiba sai ganinta tayi xaune kan cinyarsa ta riqo fuskarsa da tafukan hannyenta cikin sanyin jiki dana murya tace "SAGEEER" ya dakata da maganar da yake da kuma dura lemo a jarka yana kallonta, takai bakinta kan nasa ta fara sumbatarsa kamar xararriya, ya watsar da lemon daya debo a cup shima ya riqota yanawa bakinta wani mugun tsotsa, suka sarqe guri guda sai gasu a qasa kwance, tuni sun watsar da lemon dake cikin bokiti basu sani ba, wanda aka dura cikin jarka aka rufe ne kawai ya tsira (πŸ€¦πŸ½β€β™€) da kyar Sageer yayi qarfin hali ya dagata sukai cikin gida suka yada xango a bedroom dinsa, yana balle shirt din jikinsa ya dubeta a burkice yace "Maimaita abunda kika fadamun jiya dana kiraki a waya" idonta cike da kwallah tace "Ya Sageer ina sonka" ya qura mata ido yace "da gaske kike sakeena? Karfa kisa in haukace miki?" ta dubeshi cikin ido tace "Na rantse da wanda ke busamun numfashi ina sonka" bai qara cewa komai ba sai sumbatarta daya farayi tana mayar masa da martani. A wannan rana dai sunsha shagalin da basu taba irinsa ba, Sakeenatu tasa sageer kuka wurjanjan tare da wasu alqawura masu nauyi da yayi mata. Sukai bacci riqe da juna cikin farin ciki.


Acikin wannan weekend din sukai wata irin dinkewa da wata kalar soyayya me gardi da suke gwadawa juna, kowa a gidan ya fuskanci haka, xuwa masallaci kawai ke fidda Sageer daga gidan cikin kwanaki biyu. Ranar lahadi da daddare ya bata sabuwar waya qal da sabbin layuka, ya bude mata sabon account na watsap da facebook ya fada mata ya xubar da wadancan layukan nata bayan ya kwafe mata contact dinta wayar kuma ya bawa wani yaronsa a office. Tayi murna sosai don tanason waya Deni kawai take tsoro karya qara binciko number ta amma tunda yanxu sabuwa ce shikenan. Ta dunga zabga masa godiya yana murmushi yace mata gobe xata koma makaranta, ta danyi jimm tace "Ya Sageer nifa na haqura da karatun, xan xauna inyi bautar aure innemi aljanna ta" yasa yatsansa a bakinta yace "shiii, Denin banxa, ai bai isa ya hanaki cika burin da kika girma dashi ba, tun randa naji kinason karatu naiwa ubangiji alqawarin tsaya miki kiyi karatu har sai kince ya isheki, kuma bayan haka ni kaina inason inga matata da ilimi saboda yayanmu" idonta cike da kwallah ta fada jikinsa tace "Nagode ya Sageer" yace "Yawwa qanwata ki shirya gobe xaki koma makaranta ki fara sabuwar rayuwa, ki kwantar da hankali Deni baxai kuma dawowa rayuwarki ba domin nasa anyi maganinsa" tana rungume jikinsa bata tambayeshi beyayiwa Deni ba domin ko sunansa bataso taji an ambata.



Tare suka fita washegari Monday, ya kaita har school kamar yadda ta buqata, suka tsaya a car park ta marairaice tace "To ka rakani class mana" yayi dariya yace "Wannan yarinya da shagwaba take, to muje" suka fito suka jera tana riqe da hannunsa saboda tsaro 😜 har cikin class dinsu, sai dai ajin babu kowa ta fara tunanin ko ancanja venue ne, sai ga wani dan department dinsu, ya kalleta tun kan taimasa magana yace "LIMAN (kamar yadda malamai da wasu daliban ke kiranta) kin dubo result ne?" ta dafe qirji tace "Yaushe aka kafe?" yace "yanxu nima daga gurin nake duk ragowar yan ajin suna can suna dubowa" tai masa godiya taja hannun sageer suka juya duk ta firgice gani take batai abun kirki ba.



Sageer yanata kwantar mata da hankali har sukaje gurin, ya tsayar da ita saboda da maxa a gurin ya kutsa ya shiga dubo mata. Ya jima a ciki tana tsaye a gurin cikinta a qulle su Qudrat na mata magana ma bataji ba. Ya fito ya hada gumi, tayi saurin xuwa gurinsa tace "Ya Sageer yaya akai? Nasamu C/O ko a English Literature?" ya dubeta bece komai ba, ta kwabe baki tana shirin kuka.



Ya kyalkyale da dariya yace "To sarkin shagwaba congrats, result dinki yayi kyau sosai kece ta uku a department dinku a mata" ta daka tsalle ta rungumeshi, ya cirota a jikinsa ya manna bakinsa a nata yana tsotsa yace "Kinga yadda akeyi in farinciki ya samu banason choge" Gaba daya kallo ya dawo kansu ganin abun nasu ya wuce runguma harda kiss a bai nan nasi, ta toshe baki cikin kunya ganin idanu akansu, suka kuma kallon juna ita da Sageer suka saki dariya a tare. Qudrat uwar gulma ta matso ta xunguri sakeena cikin rada tace "Keena waye wannan handsome din naga kuna kissing juna?" Sakeena ta fallara mata harara tace "Banason kallon qurullah mijina ne" Maijidda ta matso tace "Shege Liman daman ke matan aurene baki taba fada mana ba?" Sakeeena tai fari πŸ™„ tace "Bagashi yau kun gani ba" Sageer yana jinsu yana musu dariya, suka gaisa dashi a mutunce xai tafi ya yafito sakeena, cikin sauri taje tace "Nagode ya Sageer, Allah ya saka maka da gidan aljannah Allah ya jiqan mahaifinka" yaji dadin adduarta yace "kema Allah ya jiqan naki, kuma nine da godiya da kika dage kikai karatu naji dadin ganin result dinki kin qaramun qarfin gwuiwar biya miki kudin makaranta, tunda ba asarar kudina nake ba" tana murmushi tace "Ya Sageer na maka alqawari saina buge mutum biyu matan da sukasha gabana saboda ka kawarmun da rudanin da xai hanani karatu (Deni)" yace "Yawwa keena haka nikeso baby na. Yanxu ki jira in kun gama lectures xanxo daukarki ko muje shopping, wannan kyakymyawan result naki ai saida kyauta" tace "To Ya Sageer xan jiraka, I luv u" ya amsa da "Luv u too my angel" suka rabu suna waving juna.

******** ******** ***********


Bangaren mal Deni kuwa saida yayi kwana biyu cur a sume sannan ya farko, ya faracin abinci da magana, koda yan office dinsu suka tambayeshi abunda ya faru dashi sai gilla musu qarya da cewa wasu ne suka tareshi sukai masa fashi suka kuma yimasa duka, koda aka tambayeshi ko xai iya gane fuskokinsu, da sauri ya girgixa kai domin ya tsorata a aika aikar da akai masa kuma garin Lagos ya fita a ransa gani yake kamar xasu qara biyoshi su dakeshi.



Ranar kwana ta biyu da farkowarsa wanda yayi dai dai da kwanakinsa hudu cur a gadon asibiti tsakar dare me jinyarsa yana bacci ya sulale ya gudu daga asibiti ya nufi gidan da suke ciki na ma'aikata ya tattara komatsansa kaf ya loda a molalliyar motarsa ya nufi Kano ba tare daya kammala course din daya kawoshi ba, da nufin shi da Lagos sai dai a kawo gawarsa ko ragowar kwanakin da yayi bayan dukan Area boys dandai baya cikin hayyacinsa ne. Tuqi yake na ganganci cikin wani irin gudu na wuce sa'a sai kwaraf kwaraf yake a tsakiyar titi shida motarsa raunukan jikinsa yana kuma tsami.


Ikon Allah ya kawoshi kano cikin gidansa qarfe goman safe, xuwa lokacin ya gama jigata kwarai da gaske domin ko me gadin gidan be shedashi ba saidaya masa bayani da nuna masa ID card dinsa. Ya fito yana dingisa qafa ya nufi falon gidan.



Ya tarar da Surayya hakince a falo cikin shigar dayafi tsana ya ganta da ita wato English wears, kome ya hanata fita aiki oho. Ta miqe ciki da farin ciki ta nufeshi yayi saurin yin gefe yana cemata "Yi a hankali ciwo na" ta dubeshi saroro sai a lokacin ta lura da duk jikinsa bandages ne. Tace cikin sauri "Deen meya sameka haka?" a taqaice yace "accident nayi a hanyar tahota, kwanana hudu a KD a asibiti sai yau na farko shine na taho" ta kamashi ta taimaka masa ya xauna a kujera tana cewa "Ashsha! sannu Deen Haqqina ne yasaka yin accident wlh ka barni cikin masifar soyayya da kewarka"



Yayi shiru kamar be jita ba don bayason surutunta na hauka. Ta matso kujerar da yake ta xauna tana cewa "Ashe taji warning dina har ta karya asirin da taimana ta kadamun kai, dama sabariyya tanata bani shawarar inje inkatsa mata warning inaqi ashe maganarta akan gaskiya take" Cikin mamaki Deni ke kallonta yace "Waye kikaiwa warning wai?" cikin rashin damuwa tace "Hajjo mana" ya xaro ido yace "Wace Hajjon?" tayi dariya tace "Haba mana Deen Hajjo nawa muke da ita? Hajjo tamu ta gargajiya ita naiwa warning akan asirin da taimana ka tafi Lagos ka barni, saboda naji duk yadda tai asiri ta rabaka da Sakeena shiyasa naje na jamata kunne na fada mata ni baxan dauki hakan ba ta karya asirin ta sakomun kai mucigaba da soyayyar mu ko?" Al ajabi ya hana Deni ce mata komai.



Ta qara shigowa jikinsa tana cewa "Ai gara daka dawo Deen kacigaba da shan tabarka inasan qamshinta, wlh bayan tafiyarka wata jarraba Allah yayimun babu abunda nikeso kamar qamshin sigari, dana rasa yacce xanyi sai nake kiran maigadi yaxo nan ya xauna anan falon yayi ta busawa inajin qamshin. Saida abun ya isheni naje hospital wai akace ciki gareni, atake nasa aka burge shege akaimun wankin ciki aka daure mahaifar"


Cikin matuqar fushi da harxuqa Deni yace "Surayya cikin nawa kika xubar dan ubanki?" ta dubeshi tana dariyar data saba yimasa inyana masifa tace "calm down Deen banfa sha sigarin ba gate man nace maka yanasha inajin qamshin, nasan tabace bakaso insha ko? To bansha ba duk da inaso saboda kar inbata maka rai." a qufule yace "Ni ba tambayarki nake kinsha taba ko baki sha ba, wannan ba abunda ya shafeni bane inma kinga dama ki xama drug abuser, ina tambayarki da gaske kinsamu ciki kuma kin xubar?"



Ta gyada kai tace "Eh mana gaskene kasan ni aibana qarya" ya xaro mata ido yace "ke wai dan Allah wace irin yar iskar macece? Dan halak kuma danmu na fari kika xubar kuma kike fadamun babu kunya babu tsoron Allah?" ta dafe goshi πŸ€¦πŸ½β€β™€ tace "OH! Haba Deen wlh bansan shouting, calm down mana meye acikin common abortion? Bakasan yanxu ma andaina aure haka ba sai anje an daure mahaifa? Sai mutum yaga yanayin xama da mijin sannan ya fara haihuwa? Kawai ka share, I luv u Deen" tabi jikinsa ta kwanta.



Hawaye ya wanke masa fuska, wannan wane irin bala'i ne ke binsa bi da bi? Rana xafi inuwa quna, taciwa uwarsa mutunci bata saurari abunda xaice ba ta fada masa ta cire ciki harda sakawa a rufe mata mahaifa, wai ina xaisa kansa ne? (kadan ka gani baka tasarwa rusa auren wani ba? Da kuma neman aure cikin wani auren? 🀨) Wai waxai fadawa damuwarsane ya samu salama? Shin Surayya wace irin macece? Dawane suna xai kirata? Yar iska ko mahaukaciya? Ko haqqin sakeena ke bibiyarsa tunda adacan abu kadan intayi xai fara masifa amma gashi yanxu inyayi masifar ma dariya ake masa, gashi kuma abun ya kuma canjawa ko damar yin masifar ma Surayya bata bashi ba, wace irin matace gareshi da yadawo duk jikinsa rauni babu sannu ko hutawa beyiba ta sanar masa bad News?




Hajia 😊
*_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[8/21, 11:52 AM] Zongo Gal: πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€MUQADDARI NEπŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€2018πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€



2⃣9⃣

RAHMATULLAH (Hajia)



EIDIL ADHHA MUBARAK TAQABBALALLAHU MINNA WA MINKUN.😊



Yacigaba da tunaninsa me kama da nadama, wato yanacan yana rusa rayuwar auren wani ashe shima tasa tuni ta rushe? Yanacan yana shirin raba sakeena da cikinta na halak ashe shima nasa cikin tuni yabi rariya, yakai dubansa kan Surayya dake kan cinyarsa tana danna waya, ya rasa wani irin hukunci xai mata ya huce abunda tai masa, yaja tsaki ya tashi ya shige bedroom. Dakansa ya hada ruwan wanka yayi, yasha tea yasha magungunan da aka bashi a asibiti ya kwanta.


Bai tashi sanin tinkiya yake aure ba saida dare yayi Surayya ta fara lalubeshi tana neman biyan buqata, ya fara masifa yaga abun baxai fishsheshi ba ya lallasheta da cewa tayi haquri ya warke yanxu duk jikinsa ciwo yake baxai iya komai ba.



Wajen goman safiya ya isa gidansu, yayi saar samun Baba yana gida. Sunyi mamakin ganinsa a haka, suma qarya yayi musu da cewa fashi akai masa a hanya. Suka jimanta masa harda Iya, ya samu ya shige dakin Hajjo ya sameta itama kamarsa tana dingisa qafa tayi wata irin xabgewa jikinta duk ya saki.


Suka xauna bayan gaisawa itama tayi masa jajen fashin da akai masa, ya qara kallonta a karo na barkatai yace "Hajjo meya sami qafarki naga kina janta haka? Ga wata muguwar rama da kikayi kamar me ciwon qanjamau" kamar jira take ta fashe da kuka, be hanata ba domin shima da akwai hali kukan zaiyi na rashin sakeena, sai datayi ya isheta sannan ta fara bashi labarin abunda ya wakana bayan tafiyarsa.



Hajjo dai bayan tafiyarsa ta hadu da ciwon sugar wato Diabetes, wanda rashin ankara da wuri yasa yaci qarfinta sosai kafin Saddiq ya kaita asibiti a gano kuma a dorata akan magani tare da gindayamata sharaidai masu dinbin yawa akan canja cima. Bayan nan kuma ta debi ruwan xafi a bokiti xatakai toilet tayi wanka ta xame ta fadi ta samu targade da tsagewar qashi a qafarta ta hagu, shine har yanxu be warke ba saboda jikin girma.



Abu na gaba kuma shine dumuwar halin da su Hadixa ke ciki wacce ta rasa matemaki, itadai Hadixa har yanxu tananan jiya iyau a qarqashin ikon surukarta da kuma axxalumin miji wanda duk yadda aka kai ga ganin mijinta abun yaci tura, ba a ganshi ba balle a kwatar mata yanci. Saida Saddiq da Baba suka tsananta bincike sai suka gano wai mijin nata yatafi wani course a qasar waje tare da amaryarsa, ita kuma uwar mijin ta hana Hadixa fita ko bakin gate a cewarta amana mijin Hadixan ya kawota babu inda xataje har sai ya dawo.



A bangaren Fiddausi kuwa Zahara da kanta taxo tasawa Baba kuka akan yasa baki a lamarinta domin bauta da tsoron takewa kishiyarta Hajiya ya wuce makadi da rawa. Dole Baba ya shiga lamarinsu tunda duk lalacewarsu yayansa ne kuma abunda ya gudar musu kenan a auren mekudi amma sukaqi sauraransa. Dashi da Saddiq da kuma Zahara sukaje gidan Fiddausi suka tarar da ita kace kace cikin bauta kamar yadda aka labarta musu, babu kunya babu tsoron Allah Hajiya a gabansu ta kira Fiddausi tace ta kawo musu ruwa taje ta kawo jiki na bari, basu gama mamaki ba saida sukaga Fiddausi ta koma gefe ta rabe kamar bata sansu ba, Hajiya tayi murmushi tace da ita ki gaishesu mana ko baki shedasu ba, Fiddausi ta juyo tana gaishesu hadi da waigen Hajiya. Suka jinjina wannan qatoton lamari, wato yau ga wacce ta dama Hajjo ta shanye a bin bokaye. Baba ya shanye duk wani bacin ransa yace dama sunaso suje gida da Fiddausi ne gyatumarta babu lfy xataje taga jikin nata. Tun kafin Hajiya tai magana Fiddausi tace "Nikam babu inda xani Baba, Allah ya bawa Hajjo lfy, aiba sai lallai naje ba saboda aiki yamun yawa" ido waje suke kallon Fiddausi da kuma kaduwa dajin kalamanta. Zahara tai qarfin halin cewa "Kidai daure muje ki ganta, munyi alqawari xamu dawo dake da kanmu" Saddiq kuwa cikin harxuqa yace "Dan ubanki saiki bimu ko kinqi ko kinso ace uwar taki babu lfy kice aiki ya miki yawa?"



Hajiya ta muskata fuskarta cike da murmushi ta dagawa Saddiq hannu gami da cewa "Dakata dan samari, ba amun hayaniya a gida, ko baku da labarin nan gidan mallakinane? Saboda haka ku tashi ku bacemun daganan tunda kunji da bakinku tace baxataje dubiyar ba, ni kuma bansan takurawa bil adam dan haka baxan tilasa mata xuwa ba" suka tashi suka nufo gate Hajiya ta umarci Fiddausi da tayi musu rakiya, babu musu ta biyosu, Saddiq yayi amfani da wannan dama ya sunkuceta ya saba a kafada megadi ya dunga kwallawa Hajiya kira da cewar baqin da akai xasu gudu da Fiddausi, hankali kwance ta fito tana takun qasaita da kuma dariyar yadda dakai tacewa megadin ya bude musu gate su tafi, ta dunga daga Fiddausi hannu tana cewa saikin dawo Fiddausi agaida Hajjo da jiki.



Har dakin Hajjo Baba ya shiga yayi mata bayanin yadda sukaga Fiddausi cikin gidan tare da fada mata mugun asiri Hajiya tayi ta cafke xuciyar Fiddausin. Hajjo ta dunga kallonta tana kuka tare da bawa Baba haquri. Ya daga mata hannu da cewa "Nikam Hajara ai bakimun komi ba kanki kikayiwa, ga sakamakon abunda kika shukanan tun kan aje ko ina ya fara bibiyar yayanki da suka tayaki haqa ramin muguntar, abun takaicin kuma shine kun haqashi da xurfi shiyasa kuka rufta gaba daya kuka kuma kasa fita" sunyini suna gadin Fiddausi kamar yadda ta yini tana fushi akan sun dakkota daga gidan mijinta.



Baba ya fita yanata yawo gurin malaman Allah da annabi yana nemarwa Fiddausi temakon karya sihiri. Koda dare yayi an rufe gida kowa yasa haqarqarinsa don ya huta Fiddausi ta sulale ta bude gida ta gudu ta koma gidan mijinta qarqashin mulkin hajjaju makkatu. Saida asuba suka tarar da gida bude Fiddausi kuma ta fece. Da wannan Baba ya rufe kofar temakon Fiddausi qarqari dai yana sata a addua. Hajjo kuwa ta yini sur tana kuka.



Ana cikin haka kuma Surayya ta bullo da tata kalar tijarar, sukai takakkiya ita da wata qawarta Sabariyya suka qarewa Hajjo cin mutunci da sunan warning, Sabariyya harda dungurewa Hajjo kai tare da cemata "Ke ba a haihuwa aka haifa miki naki mijin? Akan me duk wacce ta auri danki sai kinyi tsafi kin rabasu? To mu ba Sakeena bane wlh Surry ta fiki iskanci kurace tai lfy, amma in baki

Please Login or Register in order to submit comment